yana murmushi.
“Ka tashi?” Laila ta tambayeshi tana jin zuciyarta kamar zata fashe tsabar murna da farin ciki.
“Na tashi. Ina kwana Mama?”
“Lafiya kalau. Ya gajiyan hanya.”
“Alhamdulillah.” Ya amsa yana kallon Junior da yake k’ok’arin barin cikin bahon wai zai zo gurinshi.
“Ka tsaya in d’auraye maka jikinka sai ya d’aukeka mana.” Ta fad’a tana rik’eshi yana neman yin kuka.
Cikin sauri ta gama mishi wankan ta mik’ashi ga Abul ko towel babu a jikinshi, sannan daga baya ta bawa Abul towel d’in ya lullu6eshi yana goge mishi kanshi suna yiwa juna dariya babu gaira babu dalili.
“Mama meyasa baku mishi kaciya ba har yanzu?”
“Babanshi yace sai ya cika shekara biyar ko shida.” Ta tashi tana shigar da bahon cikin band’aki sannan ta dawo tana goge gurin da mop.
Bayan ta mayar da mop d’in ta dawo ta samu Abul na shafa mishi man shafawa bayan ya bashi abun wasa yana kad’awa. Tsayawa ta yi a kansu tana jin hawaye na taruwa a idanunta domin har yanzu bata gama yarda wai Abul ne zaune kusa da ita yana ta6a d’anta da Haydar ba. A zatonta zai tsani d’an har yayi k’ok’arin yi mishi mugunta amma sai gashi cikin k’ank’anin lokaci har sun saba da juna, wato jini ba abun wasa bane.
Sai da ta gama shirya Mas’ud J sannan suka dawo falo Abul ya zuba abinci yana ci ita kuma tana bawa Mas’ud J nono. Har Abul ya gama cin abinci ya dawo falo shi bai daina shan nonon ba, zama yayi a kujera ya ce,
“Baya k’oshi ne?”
“Waye? Ohh Mas’ud? Haka yake, amma idan ya k’oshi shi da kanshi zai juyar da kai.” Ta fad’a tana murmusawa.
“Mama are you happy? A hakan?”
Laila ta jiyo tambayar a bazata wanda hakan yasa ta sunkuya ta dubi yaron dake kan cinyarta yana ci daga jikinta yana mata murmushi ta d’ago kai ta kalli Abul ta ce,
“Ina cikin farin ciki Abul saboda a yanzu ina jin kaina complete ba tare da na ji kamar na rasa wani 6angare na jikina ba. I am happy because I found love again bayan na cire rai da samun hakan. I’m happy saboda a yanzu babu mai kirana da sunan karuwa sai dai ace na auri yaro wanda baya damuna saboda nasan hakanne babu k’arya a ciki kuma ba sa6awa Allah nayi ba illa kwaikwayo da nayi da Manzon Allah SAW, amma ka ga kwanaki da ake mini k’azafin zina? Na shiga damuwa sannan na ji bak’in ciki mara misaltuwa. I’m happy Abul, and Ina son in mutu cikin wannan farin cikin.”
“Then nima I’m happy for you Mama. Wannan rayuwarki ce wanda ke kike da ikon tsarashi yanda kike so, I’m sorry I couse you pain da kuma bak’in ciki. Everyday fucking day ina regretting yanda na 6ata tawa rayuwar akan abu da kika tsarawa taki rayuwar, I don’t know what got in to me da har nayi tunanin hakan zai sa ki rabu da mijinki ki yi rayuwa kamar yanda nake so. Kaala Abdi said I’m selfish and I agreed, everything I did is about me not about you or Sabrin, nine ya kamata in kula daku amma sai ya kasance ku kuke kula dani I failed as a man. Babana ba zai ta6a yin farin ciki dani ba idan yau ya samu labarin halin da na jefa kaina a ciki don kin nemi farin ciki a karo na biyu. Kaala Abdi said all that and I believed him, I’m so sorry Mama don Allah ki yafe mini bak’in cikin dana sakaku a ciki. I promise to support you duk da cewa I hate your husband amma I will like to see you happy ko da kuwa dashi ne. I’m sorry Mama.”
Laila kuka ne ya kwace mata wanda hakan yasa Mas’ud J ya sake nonon yana dubanta shima fuskarsa a kwaye alamar zai yi kuka. Ganin haka yasa ta yi saurin share hawayen fuskarta tana juyar da kan yaron ga barin kallonta, sai dai shima Abul d’in hawaye yake yi kanshi a gefe kamar wanda baya son a ga me yake yi.
“After all that happened Abul, na koyi yafiya ga mutane ko da kuwa sun mini cuta mafi muni kuma na koyi zama da su da suka canja halayensu. Kullum idan na zo bacci sai na furta yafiya a gareka saboda bana fatan Allah ya kamaka da alhakina a ranar gobe balle har ace a dalilina ka shiga wuta. Komai ya wuce Abul, ka manta da komai kamar ba’a yi ba. Na yafe maka duniya da lahira, da abun da ka mini a baya da wanda zaka mini a gaba duk na yafe maka, sai ka nemi yafiyar Allah domin shi ka fi sa6awa da ka kauce hanya da hankalinka da kuma iliminka. Allah ya yafemu gaba d’aya.”
“Nagode Mama.” Ya fad’a yana share hawayen fuskarsa.
Itama hawayen nata ta share kana ta mik’e tsaye ta ce,
“Ka je kaci abinci sai ka tafi gidan Sabrin d’in domin tun da safe ta kira na fad’a mata kana bacci.”
“Ki bar abincin kawai domin nasan ta mini a can.” Ya fad’i hakan yana komawa d’akinsa ya d’auko abu ya dawo falon ya mik’a mata.
Laila k’ar6a ta yi tana dubawa cikin farin ciki domin laffaya ce a cikin ledarta mai kyau, ya ce,
“Tsarabarki ce, ga nan ta Sabrin.” Ya nuna mata na hannunshi wanda ke cikin leda.
“Ka kyauta sosai nagode, a ina ka samu kud’i haka?” Ta fad’a cikin d’oki tana warware laffayar ta fara d’aurawa bayan ta mik’a mishi Mas’ud J.
“Sauran kud’in da kike ajiye mini a gurin Kaala Abdi ne.”
“Masha Allah gashi kalar ta mini kyau, shukran habibi.”
Tana gama nad’awa ta shiga d’aki ta d’auko jakarta da kuma baby bag d’in Mas’ud J ta fito tana cewa,
“Mu tafi.”
“Ina zaki je?” Ya tambayeta.
“Shago zan je, ai tun lokacin da Sabrin ta fara zuwa school ni kuma ya zama kullum sai na je.”
“Ohh!”
Da haka suka fita zuwa tsakar gida Laila ta rufe gidan kana ta mik’a mishi key d’in motar tana cewa,
“Mu je ka ajiyemu a shago sai ka tafi gidan Sabrin d’in. Idan na tashi zan kira Haydar ya dawo dani gida.”
Bai yi musu ba ya kar6i key d’in ya shiga itama ta shiga gaba sannan ta kar6i Mas’ud J daga hannunsa ya kunna motar suka fita daga gidan suna hira gwanin ban sha’awa.
A bakin shagon yayi parking ta fita daga motar amma Mas’ud J na ganin shago za’a shigar dashi sannan ga wani a mota zai tafi yawo sai ya fara kuka yana mik’a hannun zai tafi gurin Abul.
“Mas’ud hoo, kai kenan kullum a dinga yawo da kai baka son zama guri d’aya? Ya Salam!” Ta fad’i hakan tana gyara gyalenta da yaron yake k’ok’arin yaye mata shi.
“Kawo shi mu tafi tare, I hope akwai kununshi a cikin jakar nan?” Ya nuna baby bag dake bayan seat.
“Are you sure? Ko da yake sometimes ana kaishi gidan Sabrin yayi awanni ma.”
Da haka Laila ta sakashi cikin car seat d’inshi ta saka mishi belt kana ta rufe marfin motar tana cewa,
“Ku gaisheta.” Murna fal fuskarta. Bata ma shiga cikin shagon ba ta kira Haydar ta sanar dashi abun da ya faru sannan ta kira Mas’ud shima ta sanar dashi wannan abun farin cikin wai Abul d’inta ne ya shiryu yake kuma huld’a da ita kamar da.
Abul yini yayi a gidan Sabrin tare da Mas’ud J wanda da yaji yunwa zasu bashi kunu ya sha ya k’oshi, da ya gaji da kunun ne ya fara neman nono hakan yasa Abul ya yiwa Sabrin sallama suka dawo gida da yamma bayan la’asar. A falo suka tarar da Laila da Haydar suna zaune amma Abul bai kula Haydar ba, yana mik’a mata Mas’ud J kuwa ya shige d’akinsa ya barsu a nan. Da daddare Mas’ud da matarsa Naana da ‘yar su Sultana mai wata d’aya a duniya suka zo yiwa Abul Sannu da dawowa, Abul ya gaishesu cikin mutunci ya k’ar6i snacks d’in da Naana ta mishi ya shige d’akinsa ya barsu a falo suna hira da Mamanshi da Haydar.
Bayan kwana biyu da haka, a weekend da safe Haydar ya tarar da Abul zaune a falo yana danna sabuwar wayar da Laila ta saya mishi. Zama yayi a gefenshi sannan yace,
“Ka fad’a mini cewa baza ka koma school ba, sai daga baya Mamanka ta fad’a mini cewa saboda ka rasa Laptop d’inka ne shiyasa ka ji karatun ya fita a ranka. Idan sacewa aka yi let’s try tracking it ko za’a samu, I know zaka iya hakan. In kuma 6aci yayi let’s get you a new one ko da kuwa sana’ar zaka yi.”
Shiru Abul yayi yana tunani domin shima yana son ya samu laptop d’in amma idan ya tuna cewa a gidan Sadistic Faruk ya bari sai ya ji gwuiwowinsa sun yi sanyi don ya tabbata Faruk zai lalata ko kuma ya k’ona. Amma an ce ‘A man can dream’, deep down yana ji a ransa Faruk bai lalata laptop d’in ba, sai dai ta yaya za’a iya zuwa a ce ya basu? Basu da wannan connection d’in yanzu, sannan ba zai yarda su sake had’uwa ba saboda har yau bai manta irin wasa da rayuwarsa da yayi ba.
“Yana Abuja gidan Senator Gambo Umar.”
Haydar da bai yi tsammanin zai samu amsar Abul ba ya gyara zamanshi ya ce,
“A gurin waye yake? Sannan meya faru har ka bari a can?”
“It’s a long story, but a gurin d’anshi Faruk yake. Sannan mun yi rabuwar babu dad’i saboda shi ya mini wannan lahanin a k’afata wanda har yanzu da d’ingishi kad’an nake tafiya.”
“Banney told me yanda aka kawo musu kai, but he never tell me abun da ya faru a gidan ba. Ya ce labarinka ne idan ka ga dama zaka iya fad’a mini.”
Duk abun da Haydar ya fad’a Abul sunan Banney kad’ai ya rik’e ya juyo cikin sauri ya ce,
“Kana tare da Banney har yanzu? Don Allah ina yake?” Yanda yayi maganar with desperation in his voice yasa Haydar ya ciro wayarsa daga aljihunsa ya bashi numbern Banney wanda a yanzu shima ya shiryu har ya koma makaranta bayan an sha daga, domin da kyar aka d’aukeshi a fannin Medicine bayan sun samu labarin ya ta6a shaye-shaye. Sai dai ilimin da yake da shi yasa suka d’aukeshi a kan duk ranar da aka kamashi da kayan maye ya daina medicine kenan har abada ko da kuwa zai canja k’asa ne.
Abul yana jin Banney ya d’auki wayar ya tashi a gurin ya wuce d’akinsa yana kiran sunan Banney kamar bai gaskata dashi yake waya ba.
“Stepdad d’inka ne ya baka number na ko? Yaushe ka dawo gida ko har yanzu kana Maiduguri ne?”
“Shine ya bani kuma na dawo gida. Meyasa baka nemeni ba all this while Banney? Where are you?”
“Bana son in yi waya da kai in ji kana cikin wannan halin da na bari ne Abul, ina garinmu har na koma school na fara daga farko. Guess duk shekarun da nayi ina karatun sun zube a yanzu. How are you? Don’t tell me you are fine, ka fad’a mini halin da kake ciki nake so.”
“Na dawo gida, na rok’i mamana gafara and my fucking stepdad ya bani adorable stepbrother. I will send you his pictures together with me. What about you.”
“First of all, I’m who I am today saboda wannan fucking stepdad d’in naka, shi ya tsaya mini har na samu makaranta ya kuma d’auki nauyin duk expenses d’ina ba tare da ya gaji ba. After every two months yana zuwa dubani a school in da nake zama saboda ban koma gidan mahaifana ba and he understands why bayan na sanar dashi duk labarina. Abul har yanzu iyayena basu canja ba, they are still dogs.”
Abul runtse idanunsa yayi domin labarin Banney ko shi baya son ji bare wani, sannan shi bai ga bak’in cikin da Banney ya gani ba a rayuwarsa dalilin k’azamar rayuwar da iyayensa suke ciki. Amma a hakan Banney ya gyara rayuwarsa sannan yaci gaba da karatunsa don ceto wanda yake da niyyar cetowa tun farko. Shi kuma me aka masa ma? Don uwarsa ta auri yaro shine har yake da guts d’in lalata rayuwarsa? Ya aka yi ma ya bari maganar mutane ta yi tasiri a zuciyarsa har ya za6i wannan jakar hanyar a matsayin mai 6ullewa.
“I’m sorry dude.”
“Ka tayani yi musu addu’a, ka kuma tayani yiwa Uncle Haydar godiya saboda shi ya taimaki rayuwata ya cironi daga gagari. Na kusa samun hutu na sati biyu, kuma I promised him a gidanku zan yi. Be nice to him or I will kill you with doctor’s scissors.”
Dariya suka yi dukkansu Abul ya ce,
“I missed you man.”
“You sound gay mallam. I mean it, be nice to that man. Yana son mamanka tsakani da Allah kuma yana kareta daga shiga depression ta hanyar halal saboda tsawon shekarun da ta d’auka bata da auren nan zai iya messing da brain d’inta.”
“Fuck off man, this is my mother we are talking about.”
“Call it Doctors intuition but your mother sound happy idan nayi waya da ita, idan zan samu ni tawa mahaifiyar ta zama haka I will literally worship that man. I respect your stepdad, so idan kayi disrespecting d’insa a gabana I swear zan manta duk abotanmu in ci.....”
“Kar ka zagi uwata.” Abul yayi saurin warning d’insa yana murmushi saboda yayi missing d’in Banney ba kad’an ba.
“I will never! Nima uwata ce kuma ta fi daraja akan wacce ta haifeni.”
Sanyi Abul ya ji a zuciyarsa domin zai iya cewa Banney shine abokinsa da yake jin sonshi har cikin zuciyarsa, jin yana cikin farin ciki a dalilin Haydar kuwa yasa yaji sassauci game da tsanar da yake yiwa mijin uwar tashi.
Sun dad’e suna waya wanda Abul har yana mamakin yanda Banney ya san komai na gidansu, domin har fad’a mishi yayi cewa shi zai tura mishi pictures d’in Mas’ud J tun yana jariri har zuwa yanzu. Wannan abu yasa Abul yaji kishi kad’an domin wani bare ya fi shi sanin k’aninshi.
Suna gama waya ya koma falo don yiwa Haydar godiya amma sai ya samu baya nan, komawa d’akinsa yayi ya bari a kan cewa zasu had’u a masallaci sallan magrib.
Haydar kuwa yana ganin Abul ya shiga d’akinsa ya tashi ya fita daga gidan yana danna wayarsa. Ana d’auka yayi sallama yace,
“Brother I need your help.”
Mum Fateey 👌
RUWAN ZUMA 🍯
Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey) 09023713064
Wannan page naki ne ke kad’ai K’awata Phaty BB. Allah ya bar zumuncin da ke tsakaninmu. I love you fisabilillah.
(53)
Haydar gidan yayanshi Alhaji Abdul ya isa aka bud’e mishi gate ya shiga wanda zai iya cewa wannan ne zuwan shi na hud’u gidan tun bayan da suka shirya.
A lambun gidan ya samu yayan nashi da wani Ustaz yana koya mishi karatun addini, sai da ya bari suka gama sannan ya iso gurinsu ya gaisa da su kana Ustaz d’in ya tafi.
“Na ga kayi nisa a karatunka.” Fad’in Haydar yana kallon littafin dake hannun Alhaji Abdul yana murmushi.
Alhaji Abdul tattara littafan yayi guri d’aya shima yana murmusawa ya ce,
“Har yanzu kan nawa yana ja, idan na d’auki shafi d’aya kafin gobe zan haddace matuk’ar aiki bai mini yawa ba. Ina d’ana? Na dad’e ban ganshi ba.”
“Yana gida, baka da mata ne da na kawo maka shi ya yini.”
“About that...” Alhaji Abdul ya tafa hannayensa wanda yana yawan yin hakan ya cigaba da magana, “Dama nima ina nemanka zamu yi shawara. Amma kafin nan wani taimako kake nema?”
Ajiyar zuciya Haydar yayi kana ya fad’awa Alhaji Abdul niyyarsa ta d’aukowa Abul laptop d’in sa a gidan Senator Gambo Umar, ya karishe maganan da cewa,
“Allah yasa kana da wani connection da zai iya kaimu gidan har mu kar6o.”
“Ni ban sanshi personally ba amma ina ga kwanaki can da yake rik’e da kujerar Senator sun ta6a wani kasuwanci tare da Baba ya sayar masa da wata kwangila. In ka shirya mu tafi Abuja gobe, idan mun dawo kuma zaka je nema mini aure.”
“A ina ka samu matar?” Haydar ya fad’a cikin farin ciki domin har cikin ranshi yake son yayan nashi yayi aure ya daina zama haka.
“Yarinyar da ke hannun Ammi ce, naga ka san mahaifinta shine nake so kai ka fara nema mini izinin magana da ita. Amma kana ganin zan samu aurenta kuwa?”
Haydar shiru yayi yana tunani idanunshi kyar a kan yayan nashi, ya san Meenat nitsatstsiyar yarinya ce in ka cire son da ta mishi har ta kasa 6oyewa kowa ya sani. Alhaji Abdul kuma a da yayi bidirinsa da duniya sai yanzu Allah ya shiryeshi ya samu ya nitsu a yanzu da yake da shekara arba’in da bakwai, shin had’uwarsu zai yi kyau kuwa domin shi yana tsoron cutar da d’aya daga cikinsu domin ita Meenat ta zama tamkar ‘ya a gurin Amminshi don yanzu ma haka tana Abuja a gurinsu, ta d’ayan gefen kuwa Alhaji Abdul yayansa ne jininsa kwalli d’aya rak a duniya, basu da kowa sai junansu.
“Ta yi k’arama ko? Ammi ta fad’a mini shekarunta ashirin ne ciff, ban san ma meyasa nayi tunanin aurenta ba me zata yi da tsoho irina.” Ya fad’a cikin karayar zuciya annurin fuskarsa na raguwa.
“Ni ban ce ba, ai age is just a number. Idan kuma nace banbancin shekaru zai hana aure to na zama munafuki. Idan har kana sonta tsakani da Allah kuma zaka rik’eta da amana ni zan nema maka aurenta da yardar Allah.” Haydar yayi saurin katseshi ganin ya karaya nan take.
“Zan rik’eta tsakani da Allah Haydar ba zan cuceta ba.”
“Allah ya baka iko. Zan mana booking d’in jirgin safe Insha Allah.”
“Shikenan.”
Haydar bai bar gidan Alhaji Abdul ba sai k’arfe tara na dare, dalilin magana da suka yi a kan kasuwancinsu.
A can side d’insa ya samu Laila har ta kwanta ga can Mas’ud J ma yayi bacci,
“Har kin kwanta?” Ya tambayeta yana rage kayan jikinsa.
“Eh, Sannu da dawowa. Yau ka yi dare.”
“Na je gidan Alhaji Abdul ne. Ya samu mata zamu je nema mishi aurenta.”
Har cikin ranta Laila ta ji dad’in wannan magana domin ta san Alhaji Abdul ya so ta har son ya koma obsession, an ce wanda ya nuna maka so ya kamata ka mishi fatan alkhairi ko baka mayar da son ta yake maka ba. Lokaci kuma yayi da ya kamata ya yi aure domin kullum tsufa yake k’ara yi mutuwa kuma bata sanarwa take zuwa. Sannan ya kamata ya ajiye d’an da ko bayan mutuwarsa zai mishi addu’a, wai bahaushe yace ‘ko gudu kake yi ka haifa ka jefar watarana d’an zai maka rana’.
“Hamdallah Allah ya tabbatar da alkhairi yasa a yi damu.”
“Baki tambayi wacece matar ba.” Haydar ya fad’a yana tu6e duk kayan jikinshi ya yi hanyar band’aki.
“Wacece? Duk dama ba dole in santa ba.”
“Meenat ‘yar d’akin Ammi.”
“Kai wannan abun namu kamar a littafin Hausa. Shi ya so ni bai sameni ba, ita kuma ta so ka amma bata sameka ba shine suka had’e with their second choices.” Laila ta yi ‘yar dariya tana girgiza kai.
“Zan fad’a mishi sak’onki.” Haydar ya fad’a yana shigewa band’aki.
“Sarkin had’a fad’a.” Ta furta a hankali tana jawo wayarta gudun kar bacci ya d’auketa kafin ya fito.
Minti uku da haka Haydar ya gama wanka ya bud’e band’akin yace Laila ta mik’o mishi sabon towel a cikin wardrobe.
D’aukowa ta yi kana ta tako har bakin band’akin ta mik’a mishi hankalinta na kan wayarta, shi kuma zuba mata idanu yayi yana kallon surar jikinta cikin kayan baccin da ta saka wanda dashi da babu duk d’aya. Bata yi aune ba sai ji tayi ya kamo hannunta ya jawota cikin band’akin, tana tirjewa tana dariya ya rufe k’ofar ya ce,
“Wanka zan miki.”
Washe gari tun safe jirgin su Haydar ya tashi, har lokacin Abul bai samu ya mishi magana ba a lokacin da zasu je masallaci sallah asuba, akan cewa sai da safe in yana karyawa zai fito ya mishi wannan godiyar. Sai dai yana fitowa k’arfe bakwai da rabi ya samu Laila na tattare gurin da Haydar d’in ya ci abinci, gaisheta yayi kana ya ce,
“Ina yake?”
Cikin rashin fahimtan waye yake nufi Laila ta ce,
“Waye?”
“Umm.. Baban Mas’ud J.”
“Ohh yayi tafiya, yanzun nan ya fita zasu je Abuja da yayanshi gurin Babansu. Lafiya kam?” Laila ta tambayeshi tana zama a kan kujeran dinning table d’in ganin shima ya zauna.
“Lafiya kalau, kawai zan mishi godiya ne kan taimakon da ya yiwa abokina Banney. Na ji dad’in hakan domin Banney ya taimakeni a rayuwa ba kad’an ba, shi yayi jinyata har na fara takawa ina fita waje bai barni na mutu da ciwukana ba.” Ya k’arisa maganar yana tuno yanda sauran abokan shashancin nasu suka wofintar dashi lokacin da direban Sadistic Faruk ya kawoshi shagon Ima, amma shi Banney ya tsaya kai da fata yayi jinyarsa wanda har kashi Abul d’in yake yi a leda Banney na jefarwa a bola ba tare da ya nuna mishi kyama ko sau d’aya ba.
Laila dubanshi ta yi a natse ta ce,
“Na ce bana son a k’ara tayar da zancen amma ina son jin su waye mutanen da kake harka dasu har suke maka dariya a kan auren da nayi, ka ta6a fad’a mini cewa daga wani abu wai dark web suke wanda kuke yin abubuwa tare. Sannan ina son sanin wace irin rayuwa kayi a Abuja kafin Haydar ya sameka. Abul kar ka 6oye mini, I want to know everything.”
“Baza ki so sani ba Mama.”
“Tell me.”
Ajiyar zuciya ya sauk’e kana ya fara magana kamar haka,
“Mama sanin computer da nayi ciki da waje yasa watarana na fad’a cikin wata k’ungiya wacce ko da ka iya computer ba lallai bane ka gane k’ungiyar ta kafu ba ko kuma a yi inviting d’inka ka shiga ba. Na shiga ne ta hanyar Micheal abokina wanda shima yana cikin wannan k’ungiyar ya zama mu biyar ne kaf fad’in Kano a wannan worldwide group d’in.”
“Me kuke yi a ciki?” Laila zuciyarta ce ta fara bugawa tun da taji ya ambaci k’ungiya ta yi saurin tambayarsa kwakwalwarta na kawo mata kala-kalan abubuwan da suke yi a ciki wanda kaf cikinsu babu mai kyau.
Kallonta yayi idanunsa na nuna tsantsar nadama ya ce,
“Duk abun da kika sani mara kyau ana biyanmu muna yi. Muna bud’ewa mutane website da zasu d’inga Fraud dashi Mama, ana yin transactions na smuggled guns and bombs a k’ungiyar mu saboda kar Gwamnati ta biyo sahu a gane wanda suka yi, amma mu zamu iya yi sannan mu goge duk wani evidence da zai nuna an yi wannan harka a doron k’asa. A dark web ana human trafficking, child pornography, illegal Gambling, Drugs sannan muna hacking d’in phones da kuma computers d’in mutane idan buk’atar hakan ta taso. K’aramin aikin da muke yi shine tona asirin mutane idan abokan gabansu suka nemi mu yi hakan. Sau da dama mu muke watsa nudes ko maganar sirri na wani d’an siyasa, mai kud’i ko wani babban mutum da ake son a 6atashi a idon jama’a, zamu iya hakan ta hanyar hacking d’in wayarsa ko kuma computer ko kuma aika voice detector har cikin gidanshi a lokacin da muke tsammanin zai yi maganar da ake son ji. Wani lokaci kuma har Drone zamu tura ta d’auko mana pictures da videos, Mama a haka na samu video d’in Alhaji Abdul a Abuja bayan wani abokin harkana sadistic Faruk ya tura drone jikin window gidanshi.”
“Duk
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 32