Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hannun dangin babansa. Tun lokacin da suka zo yaron yake hannunsu, to abun ka da gudan jini suna marmarinsa. Wannan d’in sunanta Aunty Aisha kuma ‘yar Baffan Haydar ne, wanda zai mayar daku gida kuma d’anta ne. Ahmad idan ka sauk’esu akwai kayansu a booth ka cire musu.” Hajiya Maryam ta d’age yaron a cinyar Umma ta rufe musu k’ofar. Cikin girmansa Ahmad ya ce, “To Aunty Maryam.” Kana ya ja motar suka fara tafiya bayan ya kunna a.c. Muna da Umma kuwa suna bayan mota a.c na bugarsu sai zare idanu suke yi, Umma ce ta yi k’arfin hali ta ce, “D’an nan ku d’in dangin mijin Laila ce?” Murmusawa Ahmad yayi bai kawo komai a ranshi ba ya ce, “Eh, shi kawuna ne k’anin mamana. Ina zan kai ku?” Umma ce ta mishi kwatance ya kaisu har bakin k’ofar gidan sannan ya fitar musu da take away d’in su tare da souvenirs ya kai cikin gidan sannan ya fito ya koma gida. Yana fita Umma ta saka kuka wanda ya sa Nazifi ya fito daga d’aki yana tambayar ko lafiya? “Ashe an gane dangin mijin Lamla shine baka fad’a mini ba? Kai wannan abun bai mini dad’i ba ta bani kunya a cikin jama’a ana ta mini dariya.” Dafe kai Nazifi yayi yana tausayin mahaifiyarsa da irin tsanar da ta yiwa Laila har bata son farin cikinta. Dangin Haydar sai yamma suka tafi aka cikasu da take away da kuma souvenirs. Laila rufe side d’in Haydar ta yi suka koma sashenta aka cigaba da hidiman suna. Suna zaune ana hira sai ga Shema’u y’ar Tabawa ta shigo falon. Tun bayan rasuwar Babansu Tabawa ta sayarwa Madu takunta da na ‘yarta na gidan gadon nasu sannan suka koma Wudil in da iyayen Tabawa suke da zama. Tun auren Shema’u da su Laila suka je aka musu wulakanci basu sake komawa ba, haka suma basu nemesu ba a haka zumuncin nasu ya lalace. Bayan an gaisa ana tambayar bayan rabuwa Shema’u ta ce, “Marwa ce ta je har Wudil ta fad’a mana kin haihu tare da rok’on muci gaba da zumuncin mu kar mu watsar. Mama tace a gaisheku ciwon k’afa ba zai barta ta zo ba.” Da haka ta ciro rigar yaro da kuma zanin abunku ta mik’awa Laila tace ga abun sunansu ita da mamanta. Har cikin ranta Laila ta ji dad’in wannan kaya ta kuma kai cikin wardrobe d’inta da niyyar d’inkawa duk da cewa zanin wankanta ya fishi tsada. Sati d’aya shema’u ta yi a gidan Laila sannan ta bi Yayarsu Ajidde gidanta a kan itama zata mata kwana biyu sai ta koma Wudil, aka bar Laila ita kad’ai da mijinta da kuma Bundle of joy d’insu. Haydar bai dawo d’akin Laila ba yace ya gaji da je-ka-ka-dawo tsakanin sashenshi da nata. Dolenta ita ta shigo sashensa suna kwana tare, idan abun nashi suka motsa sai ya d’age Bundle of joy ya nemi a mishi dabarun mata tun da har lokacin bata gama bik’i ba. Wata biyu da haka Laila ta fara ziyara ga ‘yan uwa da abokan arzik’i a matsayin yawon arba’in. Daga nan har Wudil suka je gaishe da Tabawa in da suka kawo ta asibitin Kano ganin ciwon k’afar tata yana wahalar da ita. Shema’u ke jinyarta yayin da Haydar ya d’auke nauyin komai bayan yayi k’aramar musu da Mas’ud akan cewa shi zai biya. Tana samun sauk’i suka koma garinsu suna zuwa ganin Likita idan lokacin komawarsu yayi. Mas’ud Junior wanda ake kiranshi da sunanshi na yanka ya cika wata shida har yana rarrafe, yaro ne d’an lukuti kyakkyawa gwanin ban sha’awa kuma ga shiga rai. Kulawan da yake samu daga kowa yasa yake da son mutane da kuma son a d’aukeshi a fita yawo. A wannan ranar ne kuma Kaala Abdi ya kira Laila ya fad’a mata Abul yana hanya zai dawo gida. Laila kasa zama ta yi tsabar murna da kuma fargaban yanda Abul zai yi idan ya zo ya sameta tare da d’an Haydar duk da cewa yana da labarin ta haihu, zata iya cewa rabon da ta yi magana dashi tun ranar da ta fad’a mishi ta haihu ya d’auki fushi da ita yau wata biyar kenan. Ko da ta je Maiduguri dubashi kuwa bai d’ago kai ya dubeta ba balle d’an dake hannunta. Haydar ta kira a waya ta sanar dashi ya dawo gida yana tayata murna amma sai ya lura ita damuwa take ciki. “Menene damuwar ki Maman Mas’ud?” Ya tambayeta yana jawota jikinshi tare da d’ansu wanda ke wasa da gemun babansa. “Abul.” Kawai ta fad’a ya kuma gane me take nufi. “Karki damu. Insha Allah babu abun da zai faru. Me da me za’a shirya mishi?” Haydar shi ya taya Laila girkin da zata sauk’i Abul dashi duk ta bata da tabbacin ko zai ci. Har yamma liss suna zaune suna jiranshi suka ji k’arar bud’e k’ofa Laila tayi saurin isa bakin window tana lek’awa. Abul ta gani tare da Baba maigadi suna gaisawa fuskarsa d’auke da fara’a kamar bashi ba. Yayi k’iba ya tara gemu da saje yana rataye da jakarsa a bayanshi ya nufo mashigar falon Laila ta yi saurin sake labulen ta koma gefen Haydar ta zauna zuciyarta na bugu. Abul yana shigowa suka dubeshi cikin fara’a amma shi hankalinshi na kan yaron da ke hannun Haydar wanda ya tabbatar shine d’an mamanshi. Mas’ud junior na jin k’arar bud’e k’ofa ya kalli wanda ya shigo ya 6are baki yana dariya yana tafa hannayensa alamar a d’aukeshi a tafi yawo. K’arshe sauk’a yayi daga jikin babanshi ya rarrafa zuwa gurin Abul ya kama wandonshi yana ja yana gwalantoyi. Laila tsoro ne ya kamata kar Abul yayi kwallo da d’anta amma Haydar ya rik’o hannunta yana kallon yanda Abul ke battling da zuciyarsa game da yaron dake jan wandonsa yana mishi dariya bakinshi babu hak’ori ko d’aya. Mun Fateey 👌RUWAN ZUMA 🍯 Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) 09023713064 (52) Abul d’age k’afarshi yayi a hankali ya wuce Mas’ud junior yana cewa, “Mama ina wuni?” Bai jira amsarta ba ya bud’e d’akinshi ya shiga kana ya rufe k’ofar har da saka makulli. Mas’ud J kuka ya saka yana saka yatsunsa a baki idanunsa na tsiyayar hawaye yana kallon iyayensa. Haydar ne yayi saurin isa gurinshi ya d’aukeshi suka fita waje kamar yanda tun farko ya so a mishi. Laila bata ji dad’in hakan ba har ta taka zata je d’akin Abul sai ta tuna maganar Kaala Abdi da yake cewa kar ta yawaita mishi fad’a, wani lokacin ta barshi da kanshi ya gane abun da yayi bai dace ba. Abul yana shiga d’akinsa ya dafe kanshi wanda ya fara ciwo nan take dalilin kukan yaron da ya fara ji, sakanni kad’an da haka ya ji Haydar ya d’aukeshi yana rarrashinsa suka fita waje. Runtse idanunsa yayi yana tuna kwayar idanun yaron wanda suka tara ruwa a ciki da bai d’aukeshi a kan lokaci ba. Girgiza kanshi yayi ya daina wannan tunanin kana ya zauna a bakin gadonshi yana kallon yanda aka gyara mishi d’akinshi ko’ina na tashin k’amshi. Ya jima a haka sannan ya tu6e kayanshi ya shiga wanka. Yana fitowa ya samu sabbin k’ananan kaya har guda goma a kan gadon nashi, kamar ba zai saka ba amma ya za6i riga da wando three quarter ya saka kana ya fita falo. A falo ya samu Laila tana kallo ya zauna can nesa da ita shima ya fara kallon, juyowa tayi ta kalleshi tana jin kamar ta je ta rungumeshi tsabar kewarsa da tayi amma ta hana kanta gudun kar ta tunzurashi. Gyara zamanta ta yi ta dubeshi cikin nitsuwa ta fara magana cikin yaren Shuwa ta ce, “Ya kake ya ka baro mutanen Maiduguri?” “Suna lafiya. Ummii tace a gaisheki.” Ya bata amsa ba tare da ya kalleta ba. Laila idanunta ne ya tara hawaye wai Abul ne yake mata magana cikin nitsuwa haka? Yaushe rabon duniya da ayyiriri? Shiru suka sake yi na wasu sakanni sannan Laila ta lura da kayan jikinshi fara’arta ta k’aru ta ce, “Naga ka sanya kayan da Haydar ya sayo maka sun yi maka daidai duk da cewa bai san size d’inka ba. D’azu fitansu shi da Mas’ud J suka sayo maka.” “Waye Mas’ud J?” Yayi tambayar yana kallonta a karon farko tun shigowarsa falon. Da d’an mamaki Laila ta dubeshi ta ce, “D’ana, kaninka. Mas’ud ya yiwa takwara ai.” Shiru Abul yayi bai ce komai ba sannan ya tashi zai tafi Laila ta tsayar dashi tana tambayar ina zai je? “Zan je in cire kayan ne.” Marairaice fuska ta yi ta ce, “Don Allah kar ka cire Abul. Tun da har ya iya zuwa ya sayo maka alhali ko magana bata had’aku godiyar da zaka mishi shine ka sanya kayan. Please.” Ya kai seconds talatin a tsaye sannan ya juyo zai zauna Laila da farin ciki ya kamata tana godewa Allah ta ce, “Ga can abinci na maka your favorite.” “Sai anjima zan ci.” Ya bata amsa yana k’ara zama. Hira take janshi dashi yana amsawa sam-sama, wani lokacin ma sai yayi kamar bai ji ta ba amma bata hak’ura sai ta k’ara mishi wani maganan. In baza ta manta ba rabon da ta zauna da Abul haka a gida suna hira suna tad’i shekara guda kenan har da watanni biyu zuwa uku. Har yanzu bata daina mamakin wai Abul ne zaune a falonta suna hira ba. Ana kiran sallah Haydar ya fito daga falonshi tare da Mas’ud J wanda ke tsotsan strawberry yana yamutsa fuska. Laila tana ganinsu fara’arta ta k’aru ta kar6eshi yana saka mata a bakinta wai ta ci. Duk yawunshi ne a jiki amma haka ta saka baki ta gutsiri kad’an sannan ta had’iye tana kad’a kai ta ce, “Dad’i.” Bakinshi ya bud’e yana dariya kana ya k’ara turawa a bakinshi yana dannawa da dasorinshi har ya gutsiri kad’an ya kuma 6ata fuskarsa don strawberryn akwai tsami kad’an. “Abul ya gajiyan hanya?” Haydar ya mishi tambayar yana zama a wani kujeran daban. “Lafiya.” Ya amsa kamar wanda aka mishi dole kana ya tashi yana cewa, “Mama na tafi masallaci.” “Mu je tare.” Fad’in Haydar yana mik’ewa tsaye ya bi bayan Abul wanda ya k’ara sauri baya son su had’a hanya. Abul na gaba Haydar na baya haka suka tafi masallacin suka yi sallah amma Abul ya rigashi dawowa gida ya je kan dinning table ya zuba abinci yana ci, a haka Haydar ya shigo ya sameshi ya ce, “Ina ta nemanka ashe kai ka dawo gida.” “Eh.” Kawai yace kana yaci gaba da cin abincinsa ba tare da ya kalleshi ba. Ganin haka yasa Haydar ya wuce sashensa yana jin babu dad’i a zuciyarsa domin yana iya bakin k’ok’arinshi wajen ganin ya zauna da yaron lafiya amma shi baya ko ganinshi da daraja balle maganar arzik’i ta shiga tsakaninsu. Yana cin abinci Laila ta fito daga d’akinta da alama sallah ta yi hannunta d’auke da Mas’ud J yana kad’a abun wasanshi hankalinshi a kwance. Itama Laila zama ta yi a kan kujeran dinning kusa dashi tana cewa, “Har kun dawo? Ina Haydar d’in?” “Yana can.” Ya nuna mata hanyar sashensa. Kad’a kai ta yi ta fara d’iban abincin tana tambayarshi yanda makarantarshi zata kasance tun da an mishi step down. “Ni fa bazan koma makaranta ba, sana’a zan fara yi.” “Ikon Allah. Wace sana’a kenan? Ka fasa zama Computer scientist d’in kenan?” “Tun lokacin dana rasa computer ta na ji abun ya fita a kaina saboda komai nawa yana ciki. All a had.” Ya fad’i maganar kamar zai yi kuka yana ajiye spoon d’insa cikin plate d’in. “Tatatataatata.” Suka jiyo muryar Mas’ud J yana mik’awa Abul abun wasanshi yana murmushi. Zura mishi ido Abul yayi fuskarsa babu yabo babu fallasa ya ce, “Me yake yi hakan kenan?” Laila da dad’i ya cikata kamar ta mutu ganin Abul ya fara kula d’anta ta ce, “Yana son bawa mutane abunsa musamman idan ya ga basa dariya. Yanzu ma ina ganin ya ga ka 6ata rai ne shine ya mik’o maka abun wasansa don kaima kayi wasa ka daina fushi.” Abul mik’a hannunshi yayi ba tare da ya shawarci zuciyarsa ba Mas’ud J ya dangwala mishi abun wasan yana cigaba da 6angala mishi dariya. “To nagode.” Ya fad’a yana murmushi kad’an wanda bai ma san yayi ba sai Laila ce ta lura da hakan ta kuma ji dad’i bana wasa ba. Mas’ud J d’aga hannayensa duka biyu yayi yana neman barin cinyar Laila wai Abul ya d’aukeshi. “Not so fast young man.” Fad’in Abul yana ja da baya amma bai ankara ba Laila ta ajiye mishi yaron a cinyarsa. Ganin Mas’ud junior zai fad’i k’asa Abul yasa hannayensa ya tareshi yana kallon abu d’an k’arami a hannunsa yana mishi dariya, sai tafa hannayensa yake yi yana rocking jikinsa. “Kun yi kyau tare.” Fad’in Laila tana murmushi har hakwaranta na bayyana. Abul har zai mik’a mata Mas’ud yaji yaron ya kama gemunshi yana wasa dashi, hakan yasa ya dakata yana kallonshi yana jin wani iri a zuciyarsa wanda ya kasa gane menene, amma abunda ya sani shine ba zai k’ara saka yaron kuka kamar yanda ya sakashi d’azu ba. Mas’ud junior ya dad’e a jikin Abul yana wasa Laila kuma na cin abinci suna hira wanda yawanci a kan Ummii ce da ta kafe baza ta dawo Kano ba, can ya fara mik’a hannu zai koma gurin mamanshi, hakan yasa Laila ta gane me yake so ta ce, “Yunwa yake ji bari in had’a mishi kunu a kitchen.” Ta fad’i hakan tana tashi tsaye. Yana ganin mamanshi ta tashi ya saka kuka Abul ya ce, “Mama ki kar6eshi yana kuka.” “Wallahi ko na tafi dashi ba zai barni in had’a kunun cikin kwanciyar hankali ba. Ka rarrasheshi zuwa nan da minti biyu ka dawo mini dashi.” Ta fad’i hakan tana shigewa kitchen ganin Junior da gaske kukan yake yi. Abul jijjigashi ya fara yi yana cewa, “Yi shiru, bari ta gama ta kawo maka. Ka ji?” Amma ina! Yaron bai ma san me yake cewa ba domin shi in yana jin yunwa to babu zaman lafiya, akwai wani lokaci da Haydar ya ta6a cewa ‘Allah kar Ya nuna mini ranar da zaka ji yunwa talauci ya hanani saka abinci a bakinka Mas’ud’. Ana rarrashin a falo har aka fita waje bai daina kuka ba, Abul kuwa tuni kanshi ya fara ciwo yana jin haushin kanshi don a tunaninsa ko abun da ya yiwa yaron d’azu ya tuna yake son barin gurinshi. Haydar ne ya fito falonshi da ya ji kukan yayi yawa ya samesu a waje Abul na cewa, “I’m sorry, please ka yi shiru.” “Meya sameshi ne?” Haydar ya tambayeshi yana kar6an Mas’ud J wanda ya rage kukan ganin babanshi da yayi. “Ta je had’a mishi kunu ne shine yake ta kuka.” “Ai haka yake idan yana jin yunwa ba’a gane kanshi. Bari in je in duba ko ta gama had’awa.” A kitchen Haydar ya samu Laila ta gama dama kunun tana shirin fitowa suka had’u a bakin k’ofa yana murmushi ya ce, “Ya aka yi ya d’aukeshi?” “Long story, bari in bawa wannan angon Ammin abinci kar ya fasa mana gida da ihu.” Da haka ta yi gaba zuwa falo ta zauna Haydar ya ajiye mata Junior a cinyarta ta fara bashi kunun. Kiran sallah da aka fara yasa Haydar ya shafa kan d’an nashi yana cewa, “Bari in je sallah in dawo Bundle of scream d’ina.” A masallaci Haydar ya had’u da Abul yana alwala amma babu wanda ya kula wani har suka shiga masallacin aka tada sallah, ana idarwa suka kama hanyar gida wannan karon Abul bai yi saurin wuce Haydar ba, ganin haka yasa Haydar ya fara mishi magana yana cewa, “Yaushe zaka shiga school kayi registration? Na ga Sabrin har sun fara karatu kar lokaci ya k’ure maka.” “Sana’a zan fara.” Ya bashi amsa bayan ya d’auki dogon lokaci bai amsa ba. “Why?” Haydar ya samu kanshi da fad’i sanin irin yanda Abul ya kwallafa ranshi a kan Computer har ana kiranshi da Computer Geek. “Babu.” Da haka suka shigo cikin gida Haydar dai bai daina mamakin canjawar ra’ayin Abul ba. Haydar sashensa ya nufa yayin da Abul kuma ya shiga nasu ya samu Laila na goye da Mas’ud junior yana gyangyad’i alamar bacci zai yi. Waya take yi wanda a take Abul ya gane da Sabrin ce ya nemi ta bashi wayar su gaisa in ta gama maganar. “Sabrin.” Ya kira sunanta yana murmusawa bayan ya juyawa Laila baya. Daga d’ayan gefen Sabrin ta kwala ihu ta ce, “Yaya Abul? Kai ne? Yaushe ka dawo?” “Hey calm down mana, wani tambaya d’aya zan amsa miki?” “Yaushe ka dawo Yaya Abul?” Ya jiyo muryarta na karkarwa alamar kuka take yi. “D’azu da yamma, Mama bata fad’a miki bane?” “Bata fad’a mini ba wallahi, ina ce kana gida? Bari in zo yanzun nan ka jirani don Allah.” “No, kiyi zamanki a gidanki gobe zan zo Insha Allah.” “A’a Yaya Abul ka bari in zo don na dad’e ban ganka ba.” “Yaushe kika koyi musu dani ne Sabrin? Dare yayi bai kyautu ki taso daga gidanki cikin daren nan ki zo gida ba. Gobe Insha Allah zan zo har gidanki ki ganni, kin ji?” Gyad’a kai tayi tamkar tana ganinshi sannan ta share hawayen fuskarta ta ce, “Allah ya kaimu goben ina nan ina jiranka. Yaya Abul...” Ta kira sunanshi. “Na’am, ya aka yi?” “Don Allah kar ka sake tafiya ka barmu.” Shiru yayi na wasu sakanni sannan ya ce, “Ina nan.” Basu jima a wayan ba ya mik’awa Laila wacce ta yi sallama da Sabrin bayan ta fad’a mata dalilin da yasa ta k’i sanar da ita dawowanshi, domin Kaala Abdi ne yace kar a fad’awa kowa ya dawo kar a zo a cika gidan ya kasa samun hutu, domin a yanzu so ake yi ya samu nitsuwarshi ya kuma saba da ganin Haydar da Laila a matsayin mata da miji ba tare da hakan ya bashi haushi ba. Though bata fad’a mata duk wannan bayanan ba. Suna gama waya Abul ya mata sai da safe ya shige d’akinsa ya kulle domin bacci yake ji dalilin gajiyar da ya kwaso a hanya, ai kuwa yana kwanciya ko minti biyar bai yi ba bacci yayi awon gaba dashi. Laila wanka ta shiga bayan ta kwantar da Mas’ud junior, tana fitowa ta yi shirin bacci ta mulke jikinta da humra kamar yanda kullum take yi kana ta d’auki d’anta suka tafi sashen maigida d’awisu ko ba tsuntsaye namanka sai sarki. Abinci ta samu yake ci, suna had’a ido suka sakarwa junansu murmushi ta isa can in da gadon Mas’ud yake ta shigar dashi ciki ta kwantar dashi. “Sarkin rigima yana recharging na gobe.” Fad’in Haydar yana d’aukan plate d’in da ya gama cin abincin ya fitar zuwa falo ya ajiye a kan dinning. “In baka daina cin abinci a cikin d’akinka ba zaka jawo mana 6era fa.” Fad’in Laila tana zaune a bakin gado tana shafa cream a k’afarta wanda ke sawa yayi laushi. “Na saba da hakan ne, a d’akin Ammi nake cin abinci kullum. Baki bani labarin Abul da Mas’ud J ba.” Ya canja maganar yana hawa kan gadon bayan ya tu6e singlet d’insa. A nan Laila ta bashi labarin duk yanda aka yi ta k’arishe da cewa, “Yanzu damuwata shine ya fara maka magana yana darajaka, ko kai ba mijina bane ai ka girmeshi.” “Baby step Laila, baby step. Komai a hankali zaki bi sai kiga ya tafi yanda ya kamata. D’azu a sallahn magrib bai tsaya muka dawo tare ba, amma a sallan isha tare muka dawo har yake fad’a mini ba zai koma makaranta ba shi sana’a zai yi.” Cikin mamaki da kuma farin ciki Laila ta dubeshi ta ce, “Shi d’in ya fad’a maka haka? Ya yarda yana maka magana? Ya Allah nagode maka.” Haydar dubanta yayi yaga tsantsan farin cikin da take ciki sai yayi shiru bai fad’a mata ainihin abun da ya faru ba, ai hakan ma shima ya ji dad’i tun da Abul ya iya amsa mishi. Gyara zamanta ta yi ta dubeshi sosai ta ce, “Ya fad’a mini wai ya rasa Laptop d’insa da duk abun da yake ciki wanda hakan ne yasa ya ji ya fasa cigaba da karatun da yake yi. Ina ganin idan na saya mishi sabo zai fasa sana’ar ya koma makaranta.” “Anya kuwa? Ya san zai iya samun sabon Laptop amma na shi yake so wanda abubuwanshi suke ciki. Watak’ila sayarwa yayi, amma dai zan gwada mishi magana ko za’a iya tracking d’inta.” “Zai yi wuya Abul ya sayar da Laptop d’inshi ko da kuwa ya rasa abun sakawa a bakinshi ne, ina tunanin sace mishi aka yi ko kuma ya sha kayan maye ne ya mance in da ya jefar.” “Hakan ma zai iya yiwuwa amma dai zan gwada trying, watak’ila hakan ma zai sa ya k’ara sake jiki dani.” “To Allah yasa amma ni nafi son yaci gaba da karatunshi wallahi.” Fad’in Laila tana kwanciya a kan k’irjin Haydar. “Kiyi addu’a Allah ya za6a mishi mafi alkhairi kawai. Mutane nawa ne suka yi bokon amma babu aiki sun ajiye kwalin suna sana’a? Duk shawarar da ya yanke in har mai kyau ce kiyi supporting d’insa ko a gaba zai iya yin karatun Insha Allah.” “Allah ya za6a mana mafi alkhari to.” “Amin Amin.” Ya amsa yana k’ara jawota jikinshi. “Haydar.” Ta kira sunanshi a hankali. “Na’am Matar Haydar.” “Kamar ciki nake dashi fa.” Ta fad’a tana d’ago kanta suna kallon cikin idanun juna. “Meyasa kika ce haka?” Ya tambayeta amma nan zuciyarsa sai da ta buga da k’arfin gaske yana addu’an Allah yasa akwai cikin. “Kawai haka nake jin changes a jikina kamar lokacin da nake da cikin Junior.” “To Allah ya kawo mai albarka amma gobe ki gwada mu gani.” Gyad’a kai ta yi ta k’ara kwantar da kanta a k’irjinshi tana sauraran bugun zuciyarsa hankalinta a kwance domin murmushi ne ma a fuskarta, kuma tana fatan Allah yasa cikin ne a jikinta saboda bayan ta haihu Haydar ya nemi ta yi planning tun da bata son d’aukan ciki amma ta tuna mishi alk’awarin da ta d’auka a lokacin da ya dawo, wanda take cewa zata cigaba da haihuwa har lokacin da ta isa menopause d’inta. Farin cikin da Haydar yayi a ranar har sai da ya sakata ta yi hawaye saboda shima hawayen yake yi ya rungumeta yana mata godiya tare da saka mata albarka babu k’akk’autawa. Yanzu watan Mas’ud J shida kenan amma bata samu ciki ba bayan duk hiran da suke yi kusan kullum sai dai in ita ce ta nuna ta gaji yake d’aga mata k’afa. “Yau ma akwai hiran ne?” Ta tambayeshi tana kai hannunta jikinshi in da yafi buk’atarta. “Kullum, sai dai in ke kika ce a’a.” Ya fad’a yana kashe wutan d’akin. “Make less noise don yanzu yaran biyu muke da su.” Ta furta a hankali cikin kunnenshi. “An gama Matar Haydar.” Washe gari da asuba Haydar ya bugawa Abul k’ofa suka tafi masallaci tare, suna dawowa Abul ya sake komawa bacci shine bai tashi ba har k’arfe goma na safe. Wanka yayi sannan ya fito ya samu babu kowa a falon sai mai aiki da take shara ta gaisheshi ya tambayeta ina mamanshi ta fad’a mishi tana d’akinta. A cikin d’aki ya samu Laila na yiwa Mas’ud junior wanka wanda shima bai jima da tashi daga baccin ba, yana ganin Abul ya fara buga ruwan ciki bahon yana dariya irin ya ganeshi d’in nan. “Morning to you too young man.” Abul ya fad’a yana isa cikin d’akin ya zauna a bakin gado

Chapter 29 of 32