Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yi ba tare da yace da ita uffan ba. Guri ta samu kusa dashi ta zauna tana lek’en zanen da yake yi amma ya rufe yana harararta, ita kuma ta murmusa tace, “Abul babu gaisuwa ne?” “One of my classmate called, kina fad’a musu cewa ina Maiduguri an kulle ni ko?” Ya yi maganar cikin 6acin rai wanda hakan bai sa Laila ta yi ko gezau ba. “Ya tambayeni ina kake nace ka je Maiduguri hutu kuma babu waya a hannunka, shi ya fad’a maka nace an kulleka Abul ko dai you are just assuming things?” Ta kafeshi da ido wanda hakan yasa ya kawar da nashi ba tare da ya amsa mata ba. “Baka son mutane su san halin da kake ciki ne?” Ta k’ara mishi wata tambayar wacce tasa ya dawo da hankalinshi kanta ya ce, “I don’t care. Ki fad’awa Kaala Abdi ya sakeni in koma gida saboda na daina shan kayan maye kuma ba zan k’ara sha’awar yi ba.” “Why can’t you just leave?” “Because I can’t! Kullum idan nayi yunk’urin guduwa sai in ji bazan iya ba, nasan shi yayi mini tsafi ya zaunar dani guri d’aya.” Murmushi Laila tayi wanda har ya bayyana hakwaranta tace, “Kaala Abdi ba ya yin tsafi Abul, addu’a yake maka.” Bai ce komai ba illa tashi da yayi ya shige d’akin da yake kwana ya barta a gurin ita d’aya. Ta jima tana zaune tana tunani sannan ta tashi ta fita bayan ta masa sallama amma bai amsa ba. Laila tana komawa ta samu Mas’ud ya kira wayanta har sau biyu, gefe ta koma in da babu hayaniya ta kirashi, “Kun isa lafiya?” Ya tambayeta. “Lafiya kalau Alhamdulillah. Ka kira bana kusa na je duba Abul.” “How is he?” “Yace baya sha’awar kayan maye Mas’ud, wannan magana tasa naji dad’in da baka tsammani. Baka tunanin ya kamata a sakeshi ya dawo gida? Ni fa ina ganin ya nitsu.” “Dama Kaala Abdi yace ya bar kayan maye har abada, amma halinsa na rashin ganin girman mutane shi suke aiki a kai, and you have to trust him kar ki matsa masa a kan ya sakeshi.” “Na isa Mas’ud? Ai ni duk yanda yayi bazan musa ba, ko shekara yace Abul zai k’ara yi yayi daidai.” “Bayan tafiyanku Madu ya zo ya sameni a shago ya nemi mu matsa gefe zai yi magana da ni. Kalti ashe duk shirun nan da muke ji game da case d’in Madu a kotu Alhaji Abdul ne ya shige masa gaba. Shi ya fad’a mini cewa ya biya marayun kud’insu da suke binshi dama saura kad’an, sannan an bar mishi gidansa ba’a sayar ba. Sai dai an k’ar6e shagon yaran da yake hannunsa yanzu ya zama bashi da komai Kalti. Yanzu so yake yi ki saka baki Ummii ta yafe mishi sannan ya dawo su ci gaba da zama kamar da, ya kuma yi alk’awarin canja halayyarsa gareki kuma kema yace ki yafe mishi.” Shiru Laila ta yi tana mamakin al’amarin rayuwarsu da kuma yanda ya canja a lokaci d’aya duk da cewa itama a wani gurin Allah ya kamata da laifi kuma ta tuba. Su kuma su Madu a da sun ci nasara a kanta sun hanata sukuni amma sai gashi yau su suke neman yafiyarta da yardarta. Wai dama an ce duk wanda ya rik’e Allah ba zai ta6a ta6ewa ba. “Tun da na iya yafewa Alhaji Abdul zan iya yafewa Yaya Madu. Ka fad’a mishi na yafe mishi amma shi ya sani bani da wani power a gurin Ummii da zan iya mata magana ta ji, har da laifinsa a ciki wajen ganin na taso babu shak’uwa tsakanina da ita. Tun da tafi sonshi ta kuma fi jin maganarshi yayi k’ok’arin ta koma gidanshi amma ni babu bakina a ciki.” “Kin burgeni Kalti, kuma hakan yayi daidai. You can’t eat your cake and have it.” Fad’in Mas’ud yana dariya a hankali cikin farin ciki. Magana suka k’ara yi na wasu mintuna sannan ta kashe wayarta ta koma cikin mutane ta ga ana shigowa da goro da minti, ko ba’a fad’a ba tasan auren Baba da Ammi aka mayar domin su da shirinsu suka zo bayan Kaala Abdi ya nuna musu cewa zai basu aurenta. Laila ta duba cikin jama’ar don tana son ganin farin cikin da zai kasance a fuskar Ammi amma bata ganta ba, ko da ta tambayi wata ‘yar uwarsu inda Ammin ta ke cewa tayi Kaala Abdi yayi kiranta tun lokacin da ita Lailan ta tafi gurin Abul. Laila ta san a yanzu Haydar na cikin murna saboda yana son a mayar da auren mahaifansa bana wasa ba, hakan yasa shi da kanshi ya kira Kaala Abdi ya sanar dashi halin da ake ciki sannan ya nemi a d’aura musu aure a ranar da zasu zo. Itama Ammi shi Haydar d’in ne ya yi magana da ita a kan ta amince a d’aura auren, dama k’addara ce tasa ta rabu da mijinta ba don ta daina sonshi ba babu musu ta amince har ta fara amsa wayar Baba suna gaisawa. Gida tuni ya zama gidan biki sai d’aura tukwane ake yi ana sauk’ewa, Haydar kam kamar yafi kowa murna domin shiga da fice yake yi tsakanin waje da cikin gida bakinshi har kunne yana mu’amala da ‘yan uwansa ana kuma fad’a mishi sunayensu da kuma dangantakarsu. Da dare Haydar ne zaune a bakin gadon Ammi yana had’a mata kayanta wanda zata tafi dasu Abuja washegari tare da Baba yana mata hira, ita dai tayi zugum tana sauraranshi. Ganin ta dad’e bata yi magana ba yasa ya d’ago kanshi ya dubeta yaga ta zabga tagumi tana kallonshi. Jikinshi ne yayi sanyi ya dakata da abun da yake yi yace, “Ammi ko dai bakya son auren ne?” Girgiza kanta tayi ta murmusa kad’an ta ce, “Bana son k’ara yin nisa da kai ne Ali, tun tafiyar ka zuciyata ta kasa sukuni ina fata da kuma addu’an Allah Ya bayyana mini kai in cigaba da rayuwa da kai, sai kuma gashi daga ganinka yau wai zan k’ara yin nisa da kai. Idan kuma nace maka bana farin ciki da komawana d’akina na maka k’arya, kana nesa ina nesan ne bana so wallahi.” Ta k’arisa maganar fuskarta zallan damuwa. “Shine damuwar ki?” Ya matsa kusa da ita yana rik’o hannayenta. Gyad’a kai tayi hawaye na cika a idanunta tace, “Shine.” “Ki daina damuwa Ammi saboda duk in da kike a fad’in duniyan nan kina raina kamar yadda na san nima zan kasance a ranki. Dama kuma dole ne akwai lokacin da zai zo ni da ke zamu yi nesa da juna a dalilai irin haka Ammi, amma idan kin tuna cewa ba mutuwa bace sannan kuma zan iya ziyartarki haka kema zaki iya ziyartata zaki ji sanyi a ranki ki gane bamu rabu ba muna nan tare. Idan Laila ta haihu zan baki d’an ki rik’eshi kina kallonshi a matsayin ni.” Ya k’arisa maganan cikin zolaya ba tare da ya gane Ammi ta d’auki maganar har zuciyarta ba. “Shikenan na yarda, Allah ya maka albarka ya k’ara zaman lafiya a aurenku. Ali kai d’a ne da kowacce Uwa zata yi alfaharin samu, Allah ya bar mini kai ya k’ara mini tsawon rai in ga ‘yayanka har da jikokinka.” Dariya yayi ganin fuskarta ta washe tana jindad’i yace, “Ameen Ammina. Ki tashi mu tafi Baba yana jiranki a waje, kinsan jirgin safe kuke dashi.” Gyad’a kai tayi kana ta tayashi suka k’arisa had’a mata kayan wanda duk sabbi ne da Kaala Abdi ya mata bayan ta dawo gabanshi. Shi ya fitar da akwatuna biyun ya saka a motar da zata kaisu hotel ya samu Babanshi yana jiranta a cikin motar. Haydar ya lek’a cikin motar ya dubi Baba wanda daga ganin fuskarsa zaka gane yana cikin farin ciki yace, “Baba Ango.” Dak’uwa Baba ya mishi yana murmusawa yace, “Hingo naka ja’irin yaro.” Dariya Haydar yayi duk da cewa zagin shi aka yi ya d’aga kanshi yana ganin yanda mata suka fito da Ammi kamar wata Amarya har da lullu6i a fuskarta ana wak’a ta yarensu wanda shi bai ma san me suke fad’a ba, amma yaci alwashin koya a gurin Laila domin hatta d’anshi da yaren zai tashi kamar yanda su Abul da Sabrin suka iya. Shi ya bud’e musu k’ofar aka zaunar da ita a gefen Baba wanda annurin fuskarsa ta k’ara k’aruwa, rufe motar Haydar yayi kana ya tura kanshi ta cikin window ya yiwa Ammi kiss a kanta yana cewa, “I love you Ammi.” Rik’o hannunshi tayi ta sumbata tace, “Nima Ina sonka Ali na. Ka kula da kanka don Allah.” “Karki damu Ammi, sai mun yi waya. Allah ya tsare hanya. Take care Baba.” A haka suka yi sallama motar ta tashi suka tafi, Haydar komawa ciki yayi ya shiga sashen da Abul yake don tun da suka zo bai samu ya ganshi ba. Abul yana ganinshi ya murtuk’e fuska tamau yace, “Uban me kake yi a nan? Kar kayi tunanin don ka zama dangi kayi tunanin zan daina tsananka. I still hate you.” “Kana lafiya?” Haydar ya yi kamar bai ji shi ba. Abul juyawa yayi ya shige d’akinsa ya barshi a gurin kamar yanda ya yiwa Laila da duk wanda ya tsani ya ziyarce shi. Kaala Abdi ne kad’ai baya iya yiwa rashin kunya ko musu idan ya sakashi abu. Washe gari da rana Haydar da Laila suka koma Kano tare da su Alhaji Shettima amma ban da Sabrin wacce tace zata yi sati biyu a can. Baba da Ammi kuwa tuni suka isa Abuja har tayi waya da Haydar tana fad’a mishi gidanta yana nan ba’a canja komai ba hatta suturunta da kuma kayan jarirai da suka saya ita da Baba a wancan lokacin. Ummii bata biyo su Kano ba kamar yadda Madu yayi ta rok’anta, k’arshe cewa tayi ta dawo Maiduguri da zama gaba d’aya. Yaran nata basu ji dad’in wannan matakin da ta d’auka ba, amma Mas’ud ya fad’awa Laila su barta na wani lokaci ta huce tukunna sai su nema mata gida a Kano ta dawo kusa dasu, saboda zata fi samun kulawa idan tana cikin ‘yayanta. Zaman Haydar da Laila zama ne na jindad’i da kwanciyar hankali da kuma mutunta juna, biyayyar da take mishi a yanzu har ya ninka na daa saboda tana tsoron rasa mutum irinsa a rayuwarta. Cikinta kuma ya girma ya shiga wata na tara haihuwa yau ko gobe. Zumunci sosai take yi da Aunty Aisha da sauran ‘yan uwan Haydar wad’anda basa kushe aurenta da shi, tun da a cikinsu akwai masu mata habaici da kuma fad’a mata bak’ar magana cikin wasa wai ai ta haifi Haydar. Madu ya sayar da gidanshi ya samu k’arami ya koma ciki, sauran kud’in kuma yayi jari da yake yanzu an kwace arzikin da yake tak’ama da su, da kyar ya samu Hajja ta dawo gidanshi bayan Mas’ud ya mishi bikonta. Alhaji Abdul ya bar nauyin Lu’a Ventures a hannun Haydar bayan Baba ya tilastawa Haydar d’in ya kar6a, akan cewa shi kuma Alhaji Abdul zai kula da sauran kar nauyi ya mishi yawa. Zumuncin su kuwa har yanzu bai yi gaba ba, saboda in banda gaisuwa da kuma maganan business babu abun da yake shiga tsakaninsu sannan basa ziyartar juna. Hakan yana damun Baba ganin kusan wata shida kenan amma sun kasa daidaita kansu. Ammi ta yiwa Haydar fad’a haka ma Laila tana yawan mishi magana a kan hakan amma baya gyarawa. Wata ranar lahadi Haydar na gida yana matsa k’afar Laila wacce ta kumbura yace, “Kin wuce EDD d’inki fa jiya.” “Mun yi maganar Haydar, na fad’a maka ba lallai bane dama in haihu a wannan ranar saboda kawai tsammani suke yi. Ai haihuwa sai Allah ya kawota, kai dai ka tayani da addu’a in samu in haihu da kaina kar a mini C.S.” “Kina tsoron C.S Laila, Insha Allah ke da kanki zaki haihu.” “Allah yasa. Nagode ka bar matsan k’afar ya daina zogi.” Gyara zaman shi yayi ta kwanta a jikinshi ya bud’e cikinta yana ganin yanda Baby ke naushinta gwanin ban sha’awa da kuma al’ajabi. “Duk ranar da aka ce kin haihu ban san wani irin murna zan yi ba.” Ya kalleta cikin so da k’aunarta. “In baka wani labari?” Ta tambayeshi tana d’aura kwalban Nutella a saman cikinta wanda yayi tozo sosai. “Ina jinki.” Ya bud’e mata marfin ya d’ebo a cikin k’aramin spoon ya bata ta kar6a da hannunta ta fara sha. “Lokacin da nake da cikin Abul na kusa haihuwa kamar haka, muna wasa da babansu yana mini cakulkuli faya ya fashe na fara nak’uda.” Shiru Haydar yayi kamar bai ji ba, ganin shirun yayi yawa yasa ta juyo da kanta tana kallonshi, a nan ta gane bai ji dad’in hirar ba. Gyara kwanciyarta ta yi a jikinshi tace, “Sorry.” “Ki tashi mu je mu kwanta, dare yayi.” Ya taimaka mata ta tashi zaune kana ta mik’e tsaye ta mayar da abun da take sha kitchen, shi kuma Haydar kashe kayan kallo yayi kana ya rufe k’ofar falon suka shiga d’aki. Wanka suka yi tare kamar kullum sannan suka yi shirin bacci suka kwanta. Kamar wanda dama jiranta ake yi ta kwanta mararta ta fara ciwo wanda tana ji ta fara tunanin haihuwa ne yazo kusa, kuma tana son Haydar ya samu nitsuwa daga gareta saboda ya dad’e bai nemeta ba. Kallonshi tayi yana saka mata pillow a bayanta tace, “Akwai hira ne?” Ya dakata daga abun da yake yi cikin mamaki ya dubeta yace, “But mun ce no more sex, saboda kina wahala.” “I know. But I need you.” Yanda tayi maganar kamar wata yarinya ya yiwa Haydar dad’i bana wasa ba yayi murmushi mai k’ayatarwa yace, “An gama Matar Haydar, but stop me idan na fara hurting d’inki. Kin ji?” “Aye Aye Captain.” Mum Fateey 👌RUWAN ZUMA 🍯 Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) This page is dedicated to Fatima Umar (Maman Iman) mai tilasta mini yin karatu a GSU, sai Fatima Bako, Ummi Hafsat Matar Umar, Kawata Hauwa Usman Isah, Matar Kawuna Muhibbat, K'anwata Nafisa Hadi, Yayata Rabi'atu Zagada, sai Mom Simra mai S-Square Fashion da duk wani mai k'aunar littafin Ruwan Zuma. Love you all. (50) Kafin asuba Laila ta yi nisa a nak'uda amma ta k'i su tafi asibiti a cewarta bata son su je a ce su dawo gida haihuwar ba yanzu ba, wannan kuma zai zama kaman abun kunya a gareta da girmanta ace ta kasa ganewa. Haydar kasa bacci yayi duk da cewa Laila ta ce yayi kwanciyarsa haihuwar ba yanzu ba ne. Duk wani nuk'urkusu da dukan bango da take yi yana jinshi ne har cikin ranshi, tausayinta kuma ya cika mishi zuciya har yana dana sanin yi mata ciki. Ita ce mai wahala amma shine mai tara kwalla a idanunsa yana maimaita sannu har Laila ta fara jin haushinsa. "Don girman Allah ka daina mini sannun nan ya isa haka. Ni idan ka fad'a ma k'ara mini ciwon yake...... Hasbunallahu wa....waa... Wayyo Allah na." Ta fad'a da k'arfi tana damk'e kan kujeran mirrow tamkar zata 6allata. Tsayawa tayi cak idonta a zare dalilin irin azabar da ya mamaye duk ilahirin jikinta kamar an watsa mata ruwan dalma. Haydar da yake gefenta yayi saurin isowa gurinta a razane yana cewa, "Yanzu kam abun ya isa haka dole mu tafi asibiti, ki duba irin azabar da kike sha amma kina cewa baza mu tafi ba. Ta yaya zaki ce this is normal?" Tsayawa yayi a gabanta zai ta6ata tayi saurin d'aga mishi hannun tace, "Bani hijabi, saka mini hijabi mu tafi." Ai dama kamar jira yake yi ya bud'e wardrobe ya d'auko hijabin ya sanya mata sannan ya kama hannunta suka fara takawa d'aid'ai har zuwa bakin motarsa in da kayan jaririn yake adane tun wancan satin. Gudu yake shararawa wanda cikin mintuna kalilan suka isa asibiti aka tayar da Nurses suka shiga da Laila labour room. Haydar ya zaro wayarsa ya kira Mas'ud wanda ringing d'aya ya d'auka yana cewa, "Haihuwar ne?" "Eh, yanzu muka zo asibiti. Don Allah ka je ka d'auko Kalti Ajidde ta zo ta ga halin da Laila take ciki ko akwai abun da zata mata, wannan nak'udan ya fara bani tsoro fa." Ya dubi bakin d'akin nak'udar in da wata Nurse ta fito tana cewa, "Ina kayan haihuwar?" Haydar da yake cikin rud'u har ya manta da wani kayan haihuwa, ashe dai zasu buk'ata. "Yana cikin mota. Ta haihu ne?" Yayi saurin tambaya domin baya son ya k'ara jin Laila ta wahala irin wanda ya gani a gida. "Ta kusa. Ka d'auko da sauri." Ta tsaya a nan shi kuma ya je ya kawo mata ta k'ara shigewa ciki. Minti ashirin da haka Mas'ud ya shigo tare da Kalti Ajidde wacce tana ganin halin da Haydar yake ciki ta fara mishi tsiya duk da cewa shi d'in a matsayin d'anta yake kuma surkinta. "Kai ma kana nak'udan ne na ganka kamar mai kuka?" "Kalti Ajidde ki shiga ki duba ko akwai abun da za'a iya mata, wallahi tana wahala sosai." Ya yi maganar kamar mai shirin zubar da kwalla. Kalti Ajidde da ta lura da gaske Haydar ya shiga damuwa sai ta nemi kwantar mishi da hankali ta ce "Ka kwantar da hankalinka sannan kayi ta mata addu'a don shi ta fi buk'ata a yanzu. Sannan kasa a ranka cewa kowacce mace haka take wahala idan zata haihu sai dai na wata ya fi na wata. Bari in shiga." Itama ta kutsa kai cikin d'akin inda ya jiyo muryar Laila tana addu'a cikin sauri-sauri, sai dai ana rufe k'ofar ya daina jiyo muryarta. Mas'ud da yake gefe yana zaune a wani benci dake bakin d'akin yace, "Haydar ka zo ka zauna." Girgiza kai kawai Haydar yayi domin addu'a yake yi baya son abun da zai sa ya tsaya. Minti biyar da haka Kalti Ajidde ta lek'o fuskarta cike da annuri da kuma murna ta ce, "Ta haihu an samu yaro d'a namiji kuma duk suna cikin k'oshin lafiya. Idan aka gyara yaron za'a kawo maka, sai ka ganshi wollah kyakkyawa Masha Allah." Fad'in murnar da Haydar yayi har ba'a cewa komai domin Kalti Ajidde kam kunya ya bata ta shige ciki tana mishi dariya. "Ta haihu, ta haihu Mas'ud. Alhamdulillah, Allah nagode maka." Haka yayi ta fad'a yana kaiwa da kawowa. Can kuma ya je bakin k'ofar ya kasa kunnensa wai ko zai ji kukan yaron. Mas'ud ma yayi farin ciki bakinshi a washe yake kallon murnar da Haydar yake yi yana cewa, "Allah abun godiya wai Haydar da d'a." Sai da Haydar ya nitsu sannan ya kira Ammi wacce tashinta kenan zata yi sallahn asuba ta ga kiran nashi. Tana d'auka ya sanar da ita abun farin ciki wanda itama nan take fuskarta ta washe ta koma bakin gado ta zauna hawaye na cika mata ido. "Ali na samu jika. Kai Alhamdulillah Mun godewa Allah da wannan kyauta. Ina Lailan take?" Ta tambayeshi tana duban Baba wanda ya fito daga band'aki cikin tsorita jin tana waya da farar asuba haka, ganinta da yayi tana hawaye tana dariya yasa ya gane abun da ya faru. Kafin Haydar ya bata amsa Baba ya kar6i wayar yana cewa, "Me aka samu? Da fatan dukkansu suna lafiya?" "An samu d'a namiji Baba sannan suna lafiya babu wata matsala." "Kai Alhamdulillah, Alhamdulillah. Wannan abu yayi dad'i sosai, anjima zamu dawo Kano Insha Allah na san Amminka zata hanani sukuni in bata kalli d'an Alinta ba." "Allah ya tsare hanya sai kun zo." Fad'in Haydar yana dariya. Sai a lokacin Baba ya mik'awa Ammi wayar ta k'arba tana maimaita tambayarta, "Tana ciki basu fito ba. Sannan lafiyansu kalau." Ya amsa mata. "Masha Allah, Allah ya bata lafiyar shayarwa ya kuma raya mana d'an Ali." "Amin Amin Ammi. Sai kun zo." Suna tsaye Kalti Ajidde ta fito da jaririn lullu6e a cikin zani an saka mishi kaya har da hula sai motsi yake yi yana juya kansa idan hannunshi ya ta6a bakinshi. Haydar ta fara mik'awa wanda sai da ya zauna sannan ya k'ar6eshi hawaye na taruwa a idanunshi. "My bundle of joy." Yayi maganar wacce bata buk'atar martani illa murmushin da suka bishi dashi. "Ni kam ban ga suna kama ba." Fad'in Mas'ud yana lek'en Jaririn. "D'an hassada. Ka jira naka sai mu ga ko zai yi kama da kai." Haydar ya harareshi sannan ya mayar da dubansa ga d'ansa wanda ke bibiyar hannunsa zai tsotsa. "Kar ka mini gori saboda ka san nima watanni kad'ai nake jira in rik'e nawa bundle of joy din." "Allah ya nuna mana ya kuma sauk'eta lafiya itama." "Amin." Mas'ud ya amsa yana tuna matarsa Naana mai d'auke da cikin watanni biyar. "Ka mishi addu'a a mayar dashi gurin mamanshi ta bashi nono, daga ganin yanda yake bin hannunsa yunwa yake ji." Fad'in Kalti Ajidde tana janye yatsar yaron daga bakinshi. "Yaushe zata fito? Ko zan iya shiga yanzu?" Haydar ya kasa hak'uri ya tambaya don ya kosa ya ga jarumarsa Laila. "Tana hutawa ne, zuwa anjima da safe zasu sallameta." Gyad'a kai yayi kana ya d'ago Baby ya fara kiran sallah a kunnenshi yana jin kamar mafarki yake yi zai kuma tashi nan ba da dad'ewa ba. Mas'ud da hakan ya burgeshi ya saita wayarshi kansu ya fara musu video yana cewa, "Allahu Akbar ga d'an Ammi da d'ansa." Haydar murmushi yake yi har ya gama kana ya mik’a jaririn ga Kalti Ajidde ta shige dashi ciki yana jin kamar kar ta tafi bai gaji da rik'e yaron ba. "Ka tashi mu je muyi sallah kar mu rasa jam'i." Mas'ud ya yi gaba shima Haydar ya bishi a baya suka tafi masallacin dake cikin asibitin, bayan sun idar da sallah suka wuce wajen biyan kud'in asibiti Haydar ya biya sannan suka dawo bakin labour room suka tsaya. Suna isa aka fito da Laila a kan wheelchair hannunta rik'e da Baby tana shafa fuskarsa. D'ago da kanta da zata yi ta hango Haydar tsaye a can nesa hannunsa cikin aljihun wandonsa, murmushi kuma shimfid'e a fuskarsa yana aiko mata da kallon k'auna da wani abun daban wanda ita kad'ai ta iya ganewa. "Ba zaka k'ara mini wayo ba." Ta fad'i hakan a hankali yanda ita kad'ai ta ji kayanta. "Maman Baby." Ya furta yana takowa ya iso gurinta kana ya tsugunna yana duban fuskarta wacce take nuna alamun gajiya da son bacci. "Baban Baby." Ta amsa tana murmusawa. "Thank you, Allah ya biyaki da Aljannah." Hawaye ne ya taru a idanunta ta dubeshi cikin so da k'auna tace, "Amin tare da kai da Baby." "Ban da mu kenan?" Mas'ud ya 6ata musu moment d'insu. Sunkuyar da kai Haydar yayi k'asa yana dariya kana ya d'ago yace, "Mas'ud you are annoying wallahi. Wai me kake jira a nan ne baka tafi ba?" "Kar kasa in zageka, uban waye ya kirani in ba kai ba." "Nine na kiraka amma tun da kayi aikinka ai sai ka tafi." "Ba zan tafi ba. Fad'in Mas'ud yana isowa gurinsu ya d'auki jaririn a cinyar Laila yayi gaba abunsa. Kalti Ajidde dama tun da ta hango Haydar na tahowa ta bar gurin tana rik'e da akwatin haihuwar. "I will take it from here." Haydar ya fad'awa Nurse d'in dake tura Laila ya rik'e handle d'in wheelchair ya fara turata zuwa parking space. "Haydar haihuwa da wahala." "Ba laifi kam, kuma na ga k'ok'arin ki ba kad'an ba. Thank you once again." "Har d'inki aka mini fa." Ta k'ara fad'a don so take ya gane ta wahala sosai. "Wow, kenan idan sun ga mace ta wahala sosai sai mu mata d'inki? Shi zaki saka a ranar suna kenan ko wanda aka d'inka miki?" Dariya mai k'arfi ne ya su6ucewa Laila amma ta yi saurin yin shiru dalilin d'inkinta

Chapter 26 of 32