Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da yake sabo tana tsoron kar ya kunce. "You are so innocent amma not so innocent in bed." "I will take this as a compliment." Ya fad'a cikin jin kanshi irin an yabeshin nan. "Big head." "Baki da kunya ko?" Ya ture kanta kad'an ta juyo tana hararanshi ta ce, "Ka dinga bina a hankali fa, haihuwa na yi." "Don kin yi rashin kunya an miki hukunci?" "I love you Haydar." Ta fad'i hakan with sincerity in her words tana shagala da kallonshi. "I love you more Laila. I love you so much." Bayan sun koma gida aka fara yiwa jaririn wanka Haydar na tsaye a kan Kalti Ajidde yana cewa ta yi a hankali kar ta karya mishi d'a. "Haydar ka fice ka bani guri ko ni in baka wankan ka mishi." "Ki yi hak'uri amma dai kiyi a hankali nace, ki duba yanda kanshi yake tangal-tangal an ya kuwa ba karyewa yayi ba?" Laila dake cikin band'aki tana wanka ta kwashe da dariya don yau Haydar na bata dariya ba kad'an ba. Kalti Ajidde tashi tayi tsaye jariri a hannunta d'aya yana callara ihu ta tisa k'eyar Haydar ya fita daga d'akin kamar zai yi kuka. Yana fita ta rufe k'ofar har da mak'ulli tana banbamin fad'a wai Haydar bashi da kunya yana saka mata ido a aikinta. Shi kuma tsayawa yayi a bak'in k'ofar yana sauraran kukan d'anshi kamar ya shiga ya kwatoshi. A nan Mas'ud da Naana suka shigo suka sameshi yana kaiwa da komawa, Naana ta gaisheshi tare da mishi murna tana tambayar ina Laila ta ke, ya fad'a mata tana wanka. Suna zaune a falo Sabrin ta shigo cikin sauri bakinta har kunne tana tambayar ina Mamanta take da Jaririn, "Suna d'aki." Haydar ya bata amsa yana jin dad'in yanda take nuna murnar ta a fili. Sai a lokacin ta nitsu ta gaishesu amma bata zauna ba don isa bakin k'ofar tayi ta kwankwasa, Kalti Ajidde ta bud'e mata ta shiga ita da Naana aka sake rufewa. Haydar da Mas'ud suna hira Sabrin ta fito hannunta d'auke da jaririn ta mik'awa Haydar wanda dama yana ganin an fito dashi ya gyara zamanshi bakinshi har kunne yana murmushi. An yiwa yaron wanka an saka mishi kaya farare masu kyau sai k'amshin Johnson Baby powder yake yi. Shinshinar shi Haydar yayi k'amshin na mishi dad'i yace, "My bundle of joy." K'arar camera ya ji ya d'ago kanshi ya duba Sabrin ce ta mishi hoto kana ta tura family group d'in su na zuriya gaba d'aya da caption d’in ‘My stepfather da Bundle of joy d’insa.’ A ranar 'yan uwa da abokan arziki suka yi ta zuwa barka, Madu da matarsa Hajja tare da 'yayansu su ma sun zo, dangin Haydar na wajen uba irin su Aunty Aisha da su Hajiya Hadiza da matan Alhaji Shettima suma sun zo tare da alk'awarin sauran dangi ma suna hanya. Sai su Hajiya Shatu da Hajiya Maryam suma sun zo suna tsokanar Laila wai ta sake jiki yaro ya mata ciki. "Tun da har ya iya yin cikin shi ba yaro bane kenan." Ta basu amsa ganin babu kowa a d'akin sai su kad'ai. "Ni dai kin k'i bani labarin ya abun yake." Fad'in Hajiya Shatu tana dariya. "Allah ya shiryeki matan nan, zawarci yasa kin koyi maganar banza wallahi." Fad'in Laila itama tana dariya Hajiya Maryam na tayata tana cewa, "Wai baki san meya faru ba, kwanaki wani abokin mijina ya nemi aurenta amma matan nan kallo d'aya ta mishi tace bata so. Saboda sanin halinshi na kirki ne yasa nayi ta damunta ina bata baki a kan kar ta bari ya su6uce mata, da taga na takura mata sai ta fito fili 6aro-6aro wai tumbinshi yayi k'ato ya shanye abun auren." Wani wawan dariya Laila ta saka har hawaye na taruwa a idanunta tana rufe bakinta da hannunta, Hajiya Maryam ma sai da tayi maganar ta ji abun ya bata dariya itama ta saka tata. Hajiya Shatu ta harari Hajiya Maryam tace, "Ke ba'a sirri da ke wallahi. Kin ga tashi mu tafi kar dare ya mini a hanya gwara ke kina da aure, yau tun safe muke gidan nan mun kasa tafiya." Da haka suka tashi suka shirya suna tsokanar juna Hajiya Maryam dai ta kasa ajiye jaririn sai kallonshi take yi tana jin son haihuwa a ranta, amma tunanin abun da haihuwar zai iya jawo mata yasa ta ji ba zata iya ba. Laila ta gane halin da k'awar tata take ciki tace, "Ki cire implant ki samu albarkar aure Hajjajo, tun zuwanki na lura kina rik'e da yaron nan ko an kar6eshi zai dawo hannunki." "Ni da nake shirin aurar da 'ya ne zan sake haihuwa? Yaran yanzun nan basa son su ga iyayen su sun girma kuma suna haihuwa, wasu zasu iya bud'an baki su ce miki hakan abun kunya ne, kad'an daga cikinsu ne zasu yi supporting d'inki kuma su kwantar miki da hankali har ki haihu su kuma so k'anin nasu ba tare da sun ji kunyar fita dashi ba." Fad’in Hajiya Maryam tana girgiza kai. Laila ta dafa kafad'arta tace, "Abun da nayi learning a rayuwa shine duk abun da zaka yi in dai bai kauce Shari'a ba kuma ba zai cuci kowa ba ka aikatashi in har ranka yana so. Menene ba'a fad'a ba akan aurena da Haydar? Wace irin fitina ce ban gani ba akan hakan? A dalilin wannan auren d'ana ya lalace amma saboda a kan gaskiya nake sai Allah bai barni haka ba ya dafa mini ya kuma kwato mini hak'k'ina a kan duk wanda ya cuceni Ya kuma shirya mini d'ana. Idan kina son haihuwar ki nema sannan ki toshe kunnenki ga duk masu sukarki tun da ba cikin shege kike yawo dashi ba. Yara kuma ke kike haifesu basu isa su tsara miki rayuwarki ba. Sau da dama muna barin farin cikinmu don gudun maganar mutane, sai dai duk da hakan bama tsira wallahi sai an samu masu zaginmu ta wani gurin. Wani abun mamaki kuwa shine; su kansu masu zagin da aibatamun basu tsira ba, kuma don rashin tsoron Allah a hakan sai kiji suna cewa an saka musu ido ana musu hassada ko makamantasu, alhali sun manta da cewa duk abun da ka yiwa wani sai an rama mishi watakila ma wanda yafi wanda ka mishi." "Kuma kin yi gaskiya Hajiya Laila. Har ga Allah ina son haihuwa amma mijin nawa ne baya son tara yara, yace guda hud'un da muke dasu sun ishemu ba don ba zai iya kula dasu ba, a’a, sai don wai haka tsarinsa yake. Amma wallahi zan cire implant d'in in sake haihuwa ko sau d'aya ne in yaso duk abun da zai yi yayi." "Baki ta6a fad'a mana cewa shine baya so ba, na yi zaton duk shekarun nan da kika d'auka baki haihu ba kece bakya so." Fad'in Hajiya Shatu cikin tausayawa k'awartata. "Bana son yin maganar ne shiyasa na 6oye muku, amma yanzu kam wallahi sai dai ya ji na fara zuwa Anti Natal idan har Allah ya bani." "Kar hakan ya jawo muku matsala fa Hajiya Maryam." Fad'in Laila tana ji wa k'awar tata abun da haihuwar zai iya jawo mata. "Allah zai dafa mini kamar yanda kema ya dafa miki." Ta amsa mata tana murmushi cikin dakewa. "Allah ya kawo mai albarka ya k'ara yiwa wanda muke dasu albarka." Laila ta musu addu'a suka amsa da Amin, kana suka mata sallama suka tafi. A daren ranar misalin k'arfe goma bak'i 'yan barka suka watse hatta Sabrin da tace kwana zata yi sai da Laila ta koreta ta saka Salman ya zo ya d'auketa. Laila tana cikin d'akinta tare da Haydar yayin da Kalti Ajidde kuma ke falo tana kallo duk da cewa bacci take ji amma Haydar ya k'i fita balle ta samu ta kwanta. Haydar kwance yake a gefen Laila ya d’aura yaron a saman k'irjinshi yana bacci suna hira a hankali gudun kar yaron ya farka. "Ammi bata ji dad’in rashin samun flight ba gani take yi gobe ya mata nisa, tace kowa ya ga jaririn ita bata gani ba.” Fad’in Laila tana kallon yanda Haydar ke shafa bayan d’ansa. “Ai ta damu ba kad’an ba, da ba don k’afan Baba yana ciwo ba da babu abun da zai hanata zuwa a mota. Ni fa bacci nake ji, ki gyarawa Bundle of Joy kwanciyarsa mu yi bacci.” “A ina d’in?” Laila ta tambayeshi tana tashi zaune. “Ban gane ba.” Fuskarsa cike da rashin fahimta. “A ina zaka kwana kake nufi?” “A nan mana! Da a ina nake kwana Laila?” Yayi maganar yana harararta kad’an. “To ita Kalti Ajidde a ina zata kwana?” Sai a lokacin ya tuna wai ashe tana falo, ya ta6e baki yace, “Ta kwana a d’akin Sabrin mana, akwai d’akuna da yawa a gidan nan ai.” Laila nitsuwa tayi ta lankwasa kanta kad’an kamar abun tausayi don ta san maganar da zata mishi ba lalle bane ta mishi dad’i ko kuma ya d’auka ba, ta ce, “Haydar zai fi kyautuwa ka koma can side d’inka ni kuma in dinga kwana da Kalti Ajidde a nan. Zaman ka a nan d’akin zai takurata sannan masu zuwa barka a ina zasu zauna? Ai babu dad’i a dinga ganin kana shiga da fice a d’akin nan. Kar kace zaka yi fushi don Allah ka fahimceni, mai d’aura ruwan wanka jego ita ke kwana da wacce ta haihu.” “Na ji. D’aukeshi in tattara kayana.” Ya fad’a ranshi a 6ace. “Na had’a maka tun d’azu da rana na kai maka can side d’in.” Ta sa hannu ta d’auki jaririn ta rik’eshi a hannunta ganin ya farka yana lalu6en nono zai fara kuka. Yana callara k’ara Laila ta saka mishi nono a baki ya fara sha tana jin zogi har cikin ranta domin a take mararta zai fara ciwo kamar mai nak’uda, wanda Kalti Ajidde ta ce hakan yana faruwa ne idan mahaifar na komawa normal shape in jaririn ya fara tsotson nono. Zuba musu ido Haydar yayi can ya had’iye yawu yace, “Manya basa sha ne?” Hararanshi tayi tace, “Baka san ya nake ji bane shiyasa har kayi tunanin hakan. Azaba nake ji wallahi ga yaron nan ya fiye tsotso kamar wanda dama lokacin da yake cikin nawa nonon yake sha.” Ta k’arisa maganan tana kallon yanda jaririn yake ware yatsunsa yana shilla kafanshi a hankali idonshi a rufe. “Sai da safe.” Fad’in Haydar yana tashi daga kan gadon. Rage tsayinsa yayi ya sunkuya ya yiwa jaririn kiss a kumatu sannan ya matsar da bakinsa ya ciji Laila. “Wash Haydar!!” Ta fad’a tana zare nonon daga bakin yaron wanda kamar jira yake yi ya bud’e baki ya fara kuka wanda babu shiri ta mayar mishi nonon tana shafa in da Haydar ya cijeta. “Cizo na kayi fa! A nan!” Ta fad’i hakan cikin rashin yarda tana nuna mishi gurin. “Nima ki ji abun da na ji.” Kasa magana tayi illa kwafa da tayi ta juyar da kanta gefe tana tura baki gaba alamar ta yi fushi. Bai kulata ba ya je bakin k’ofa ya tsaya yace, “Sai da safe Bundle of joy. Mamanka ta mini rowar kwana da kai kuma zan had’u da ita idan aka yi suna kowa ya watse.” “Zaka jima kuwa, saboda wannan had’uwar sai an yi wata biyar kafin a yi ta.” “Karya ne wallahi.” Ya fad’a flatly amma sai da zuciyarsa ta buga domin watakila maganarta ne gaskiya saboda bashi da masaniya a kan irin wad’annan abubuwan. D’inkin da tace an mata ma sai d’azu ta mishi bayani ya nemi ya gani ta hanashi. Murmusa kawai tayi tana kad’a kai alamar abun ya mata dad’i tace, “Ka bincika ka ji.” “Sai da safe.” Ya k’ara maimaitawa ya fice daga d’akin zuwa falo inda Kalti Ajidde ke gyangyad’i. Fitowanshi yasa ta farka tace, “Ka gama ne ko zaka k’ara komawa?” “Ta hanani ai.” Ya bata amsa wanda yasa ta murmusa tana girgiza kanta tace, “Sai da safe.” “Allah ya tashemu.” Ya amsa yana kashe kayan kallon ya wuce sashensa. A can ya samu Laila ta gyara mishi da’kin sai k’amshi yake yi, ta kuma adana mishi kayanshi tsaf a cikin wardrobe tare da takalma sa. Kwanciya yayi a katifar ya ji kamar yasa ihu, ba rashin lafiya ba ba komai ba saboda wata banzar al’ada wai ba zai kwana da matarsa da d’ansa ba? Ai shi ma yasan menene haihuwa kuma ba zai ta6a neman Laila ta biya mishi buk’atarsa ba in ma hakan suke gudu. Tsaki ya ja mai sauti kana ya jawo wayarsa ya shiga Google ya fara rubutu kamar haka... ‘Sex after pregnancy’ Article d’in da ya fara cin karo dashi yasa yaji kamar ya had’a wayar da gini, don wani gurin an ce sai bayan sati hud’u ko shida, wani gurin ma cewa aka yi wata uku ko hud’u. Dama gaskiya Laila take fad’a kenan ba karya ba? Ya jima a haka yana tunane-tunanensa sannan ya k’ara jawo wayar ya kirata. Sallama ta mishi a hankali tace, “Baka yi bacci ba? Lafiya kam?” “Lafiya kalau. Na duba na gani ashe gaskiya kike fad’a.” “Uhm.” Kawai tace. “Ke hakan ya miki kenan?” Kafin ta amsa yaji muryar Kalti Ajidde na magana, Laila kuma tace mishi ‘sai da safe’ ta kashe wayar. Ajiye wayar yayi a gefe ya rufe idanunsa yana rok’an Allah yasa bacci yayi saurin d’aukarsa. A can kuma d’akin Laila, Kalti Ajidde ce ke fad’a kamar dama jira take yi, “Tun d’azu kuna tare ban takuraku ba har sai da kuka hak’ura don kanku ya fito ban yi magana ba, yanzu kuma na zo zan kwanta shine zaku dameni da waya? A kan ku aka fara soyayya ko kuma menene? Idan bakwa son zaman nawa sai in canja d’aki ko kuma in tafi gidana in da ake sona, ai gadonki bai fi gadona dad’i ba amma a haka na hak’ura na zo kula dake da jaririnki. Wallahi idan kika biyewa yaron nan da bak’ar jarabarsa sai kin yi wani cikin kafin ki yi arba’in Laila. Ki kiyayi kanki in ba haka ba ke zaki wahala shi namiji babu ruwansa.” Laila dai hak’uri kawai take ta bawa Kalti Ajidde don ta lura ta d’auki zafi ba kad’an ba, sai dai tunawa da tayi cewa tun asuba Kalti Ajidden take kanta suka dawo gida ta d’aura mata ruwan wanka ta yiwa jaririn ma wanka, sannan take kaiwa da kawowa tsakanin kitchen da d’akin jegon don tace ita zata dinga yiwa Laila girki don bata yarda da girkin masu aikinta ba wai baya nuna yana jawo basir. Dole ne tana buk’atar hutawa amma ta biyewa Haydar suka hanata bacci har yanzu. “Kiyi hak’uri Insha Allah ba zamu sake ba. D’okin jaririn yasa yake haka wallahi amma ba halinsa bane.” “Kwa ji dashi dai. Yaro sai rawar kai kaman angon kare, Allah ya kawo Ammi gobe, wallahi zan fad’a mata matukar bai canja halinsa ba.” “Kiyi hak’uri abun bai kai haka ba Kalti Ajidde. Allah ya huci zuciyarki. Idan kina karatun littafina kina jin dad’in sa kuma a kyauta kike karantawa please support me, next time idan nayi book ki saya ba sai kin jira an fitar muku ki karanta ba. A yanzun ma ban yi Allah ya isa ko mummunar addu’a ga kowa ba saboda ba halina bane. All I ask is for you to support me in samu na sayan data. Yanzu ma Zaki iya biyan kudin Ruwan Zuma ba zan k’i ba 😄. Thank you. Mum Fateey 👌RUWAN ZUMA 🍯 Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) 09023713064 Littafan marubuciyar; 1-Matar K'abila 2-Fatu a Birni 3-Ruwan Zuma This whole book is dedicated to my Mother who supported me since day one. Shin na fad’a muku cewa tana karanta books dina ko I skipped that part? Yeah, she read all my books saboda ita tsohuwar mai karatun littafan Hausa ne, amma a yanzu bata karanta na kowa sai nawa saboda condition na idonta. Allah ya k'ara miki lafiya da nisan kwana Hajiya, I love you. (51) Washe gari da misalin k'arfe goma na safe jirgin su Ammi ya sauk'a a Kano, Alhaji Abdul shi da kanshi ya je ya d'aukosu suka fara ajiye kayansu a gidan sannan ya kawo su zuwa gidan Haydar. Har cikin gidan ya shigo da motar suka fiffito sannan ya kira maigadi ya shigar da wasu ledoji manya har da akwati cikin gidan, daga nan kuma ya fara k'okarin juyawa zai fita Ammi ta dakatar dashi tana cewa, "Ina kuma zaka je? Ka ce mini kaima baka ga Jaririn ba." Murmusawa yayi wanda iyakarta fatar baki yace, "Sai daga baya zan zo Ammi, yanzu dai Baba ya gama ya fito mu tafi." "Ka fito mu shiga tare, menene amfanin zaman ka a waje?”Fad'in Baba yana tsareshi da ido. Ganin da gaske sun kafe dole sai ya shiga yasa yayi ajiyar zuciya yace, "Haydar ba zai so ganina a cikin gidansa tare da matarsa ba. Ko haihuwan nan bai fad'a mini ba sai a bakinki na ji Ammi, bana son in yi abun da zai k'ara tunzurashi ya k'ara tsanata. Gaisuwan da muke yi ma na godewa Allah kuma ya isa haka, ku yi hak'uri ba musu nake yi daku ba illa gujewa fitina." Yana rufe baki Haydar ya fito daga k'ofar falonsa yana ganinsu fara'arsa ta yawaita ya tako zuwa gurinsu. Ammi ya fara runguma yana cewa, "Na jima ban ganki ba Ammina." Yayin da ita kuma take murmusawa tana cewa, "Kai dai Ali baka girma. Da d'anka kake sakalci?" Saketa yayi ya koma gurin Baba wanda ya mik'a mishi hannu suka gaisa kana ya dubi Alhaji Abdul wanda har lokacin yana cikin mota yace, "Sannunka. Ya yau?" "Lafiya kalau. Mun samu k'aruwa." "Eh." Kawai Haydar ya fad'a fuskarsa babu wannan fara'ar ta d'azu. "Allah ya raya mana Baby boy." Alhaji Abdul ya mishi addu'a kana ya tayar da motar yayi reverse zai je waje ya jira Baba. "Baba, Ammi mu shiga ciki ku ga Bundle of joy." Haydar Ya fad'i hakan yana jawo hannun Ammi wacce ta bishi bayan ta lura da halin da Baba ya shiga bayan ya ga yanda Haydar ya yi treating Yayansa. Babu musu suka bishi a baya zuwa falonshi kana ya bud'e k'ofar da ke tsakanin falonsa da na Laila ya je ya kar6o Baby a hannun wasu bak'i ya mik'awa Ammi. Ammi tana ganin yaron fuskarta ta washe sai murmushi take yi bakinta har kunne. Baba ma da yake gefenta murmushin ne shinfid'e a fuskarsa yana shafa kan yaron a hankali cikin so da k'auna. "Yana kama da kai sosai Ali, lokacin da kake jariri fuskarka sak irin nashi sai dai ya fika girman jiki ne." Fad'in Ammi tana duba yaron wanda ke bud'e idonshi a hankali yana juya kanshi zai nemi nono. "Ya farka ko? Yanzu zai saka kuka idan ba'a bashi nono ba." Fad'in Haydar yana duban bakin k'ofa in da Laila ta shigo sanye cikin hijabi tana aiko musu da murmushi tana cewa, "Marhaba, sannun ku da zuwa." Kana ta fara k'ok'arin zama a k'asa Ammi tayi saurin dakatar da ita ta ce, "Kul, zauna a sama. Kina jego ai zaman k'asa ba naki bane Laila." Laila da dama tunanin yanda zata zauna a k'asan take yi ta mik'e ta zauna a kujera a hankali don har lokacin tana jin ciwon d'inkin da aka mata. Ammi ta mik'awa Baba jaririn wanda da kyar ya iya rik'ewa sai da ta gyara mishi kan yaron don tangal-tangal yake yi. "Rabon dana rik'e jariri har na manta, ina ga tun haihuwar Abdul." Maganar Baba kenan da yasa kowa a mamaki. "Lallai abun ya jima." Fad'in Ammi cikin tausayawa mijin nata, saboda tana tuna irin kwallafa rai da yayi a cikin Haydar amma Allah bai bashi ikon rik'e d'an nashi ba sai da ya girma har yayi aure. Gaisawa suka yi cikin marmarin ganin juna, sannan Baba ya rik'e kan yaron ya fara mishi addu'a yana tofa mishi har na wasu mintuna sannan ya gama ya mayar wa Ammi yaron ta k'ar6a. Baba ya tashi tsaye yana cewa, "Mun ga jariri Allah ya raya mana shi. Lu’a idan kin gama ki kira Abdul ya dawo da ke gida.” “Zan mayar da ita Baba.” Haydar yayi saurin fad’a yana tashi tsaye zai raka Baba. Ammi ce ta mishi wani mugun kallo sannan tace, “Maganarka za’a bi ko ta Babanka?” Sai a lokacin Haydar ya gane yayi laifi yayi saurin gyara zancen sa da cewa, “Ina nufin kar ya wahala ne wajen zuwa d’aukoki, tun da ni ina nan sai kawai in mayar da ke. Amma ku yi hak’uri in hakan bai muku dad’i ba.” Baba murmushi yayi yace, “Duk yanda kayi ya yi daidai Aliyu Haydar. Sai anjima.” Da haka ya fita daga falon Haydar ya mara mishi baya har zuwa gurin motar ya bud’e mishi suka tafi. Yana dawowa cikin falon ya samu Laila na bawa jariri nono yayin da Ammi tayi shiru fuskarta babu fara’a ko kad’an. “Ammi lafiya na ganki haka? Baki da lafiya ne?” Shine Abun da ya fara fad’a yana neman zama a kusa da ita. “Koma can Ali.” Tace dashi tana nuna mishi gurin da ya zauna tun d’azu. Babu musu ya koma ya zauna amma hankalinshi ya tashi da yanayinta yana ta kallonta. Ammi ce ta fara magana bayan ta mayar da hankalinta kanshi ta ce, “Yanzu kai abun da kake yi ya dace? Haihuwa aka maka amma ka kasa sanar da d’an uwanka jininka sai dai ya ji a gari? Yaushe ka zama mai rik’o haka? So kake yi ka zama mara godiya ga Allah ga duk abun da yayi maka?” Laila ce ta d’ago kanta ta dubi Haydar wanda ke mata ido alamar ta tafi, ba shiri ta d’auki d’anta ta mik’e Ammi ta dubeta tace, “Ina zaki je? Ai laifin bashi kad’ai bane har da naki, zauna.” Laila komawa ta yi ta zauna tana cewa, “Wallahi Ammi ina fad’a mishi hakan da yake yi bai dace ba, k’arshe kafa mini doka yayi ya ce kar in sake d’auko mishi maganar baya so. Na yi iya bakin k’ok’arina domin in nuna mishi fushin da yake yi da d’an uwansa yayi yawa har ina bashi misalin tsakanina da Yaya Madu yanzu babu gaba sai zumunci mun ajiye komai a gefe tamkar ba’a yi ba. Ki yi hak’uri Ammi amma abun ya fi k’arfina ne shiyasa na yi shiru.” Ta k’arisa maganan tana kallon Haydar wanda ya had’a girar sama da k’asa kansa a k’asa yana murza yatsun hannunsa. “Ali kaine mai taurin kan kenan?” Ammi ta watso masa tambaya wacce tasa ya d’ago kanshi yana rage tsumewan ya ce, “Ammi don Allah idan zaki mini fad’a ki daina yi a gabanta bana jin dad’in hakan. Yanzun ma ban ga amfanin zamanta a nan d’in ba tun da ni zaki yiwa fad’an ba ita ba.” “Zaka nuna mini abun da ya fi dacewa kenan kamar yanda ka so nunawa Babanka d’azu ko? Yaushe ka zama haka ne Ali? Wallahi wannan ba tarbiyyar dana baka ba kenan.” Shiru yayi ya sadda kanshi k’asa bai ce komai ba, Laila kuma na ganin haka ta dubi Ammi tace, “Na yi bak’i wanda suka zo ganin jariri na taho nan bamu gaisa ba Ammi.” “Tsoron Alin kike ji shine kike neman guduwa daga nan ko?” Ta wutsiyar ido Laila ta kalli Haydar ta ga da gaske baya son kasancewarta a gurin kana ta mayar da dubanta ga Ammi ta girgiza kanta ta ce, “Ba haka bane Ammi.” “Tashi ki tafi.” Fad’in Ammi tana jin sanyi a ranta ganin Laila na bawa d’anta girma a matsayinshi na mijinta. Tana fita Ammi ta dawo da dubanta ga Haydar wanda shima tafiyar Laila yasa ya sassauto kad’an ta ce, “Meyasa kake mu’amala da Abdul kamar ba jininka ba? Ina son sanin laifin me yayi maka da har ka kasa koyan

Chapter 27 of 32