Reading KALBIM BOOK 2 BY MAMUHGEE Chapter 6 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata kiss a tsakiyar kai tana cewa

"I will be waiting for you guys"

Numfashi Falaq ta sake tareda gyada Kai ahankali tana furta "safe landing" a taqaice.

"Thanks my LIMBAs precious" inji Nicky tana sake rungume brothernta tana jin tsananin sonsa da kaunarsa na saka idanuwanta cikowa da hawaye kafin ta sakesa it sake rungume Mama kafin ta juya ta wuce suna mata bye bye.

Suna barin airport din ba jimawa jirginsu Nicky din ya tashi suma zuwa Nigeria.


****Adaidai wannan lokacin kuma Jannah ce kwance jikin Ummanta idanuwanta rufe jikinta a sanyaye tana jin kewan Umman na ciko mata da kwalla a ido sbd ta dauki lokaci me tsayi bata kwanta jikin Ummanta b sbd yanayin jikinta sai yau din Umman da kanta taxo ta janyota ta kwantar da ita jikinta tana Shafa mata kai cikeda wata irin kauna da babu sirki itama tayi tsananin kewan Jannah din dan haka yau ta janyota da kanta.

Hawaye ne masu dumi suka gangaro idanuwan Jannah ahankali sbd kewan mutum da har abada bazata taba denawa ba bakuma zata taba dena jin radadi da ciwon rashinsu ba wato Miminta da Wanda bai mutu ba Amma a gurinta a zuciya da rayuwarta ya mutu.

Ganin hawayen dake gangarowa idanuwan Jannah ya saka Ummah ma idanuwanta cikowa da hawaye kawai suna gangarowa batareda tasan daliliba Amma dai tasan a rayuwarta idan har zataga hawaye idanuwan Jannah to itama nata idanuwan basu kasa zubo da hawayen ba hakama duk duniya batasan tsana ba amma da zataga abinda yake saka Jannah dinta kuka to zata tsanesa da dukkanin zuciya da ruhinta.

Saukan hawayen Umman akan gefen fuskanta ya sakata bude idanuwanta ahankali ta zubawa Ummah idanuwanta tanajin kaunar da batasan ta inda take fitowa ba ga Umman,

Ta rasa wace irin kauna me tsananin tsafta da girma takewa Ummah wadda bata jinin komai da itaba Amma tanajin kaunarta har jininta kamar yanda ta rasa wace irin kauna Ummah ke mata.

Sharewa Umman hawaye tayi tana komawa ta kwanta a kafafunta tareda lumshe ido wannan karon baccin me dadi da nutsuwa tayi a jikin nata.


Se dare sosai ta farka taga Umman na dakin nasu har lokacin wato bata tafi gurin Dad ba Wanda gabaki daya yake cikin damuwar ko ta samu tayi baccin.

Rufa tai mata tareda addua kafin ita kuma ta miqe ta fada toilet tayo fitsari tayi alwala ta fito tafara nafilolin dare ta jima tana adduoi kafin ta miqe taje ta kwanta take bacci me nutsuwa ya dauketa.


Washe gari tinda asuba aka tada Ammar akai masa sauyin aiki aka basa key din lafiyayyar sabuwar motar BMW iX tareda suna da hoton Nicky Managern kamfanin 4&4 ya kawo masa yace yaje airport ya dauko matar gidan.

Baiji komaiba ya amshi sauyin aikin cikeda girmamawa ya fice daga gidan ya kama hanyar airport Yana kallan gari cikin sanyi da nutsuwa.


Yana isa babu bata lokaci ko wahala ya samu damar ganinta ya zuba mata ido kafin ta iso gurinsa Yana kallan halfcast din macen da kana ganinta bazakai mata tinanin musulma kai tsaye ba duk da doguwar Arabian gown ce jikinta dark brown Amma yanayin yanda ta Dora gyaralen ne fiyeda rabin gashinta a fili.

Dauke idanuwansa yayi daga kanta Yana qarasowa gurinta cikin nutsuwa yace

"Welcome"

Kallansa tayi kafin tace komai ganin sunan 4&4 baro baro dake jikin shirt dinsa me kyau da jeans ya sakata kai tsaye sanin drivernta ne ya iso.

Fasa amsa gaisuwarsa tayi ta miqa masa kayanta wanda ya karba ya tura har mota ya saka bayan ya bude mata motar ta shiga ya zagaya ya shiga ya tayar batareda ya sake furta komaiba har suka isa gida.

Kallo daya tayiwa gaban 4&4 mansion din ta tsayar da idanuwanta akan sunan sbd bata dauka har gidan da AZIZ LIMBA zai zauna ba a qasarsa bazai saka masa sunansa ba sedai numbers da haryanzu basuda maanar komai.

Cikeda girmamawa dukkanin securities din gidan suka taso suka mata barka sauka aka bude gate din suka shige da motar.

Maheer ne da Dad suka bude gate din na biyu a tare Wanda ya saka zuciyar Ammar dake kallansu wani irin ciwo da radadin ganinsu suna bude kofar gidan wani.

Shigowa yayi yai parking ya fito ya zagayo ya bude mata kofar suma su Dad din cikeda sosuwan zuciya suka sauke idanuwansu daga kallansa.

Fitowa tayi su madam Sisi na fitowa tarbanta cikeda girmamawa aka fara mata barka da zuwa duka cikin turanci sbd ba hausarta bata irin karfin nan ba dik da tanaji sbd tsawon shekara biyun datai dasu mama ta koya sosai.

Ciki akai da kayanta tana tafe bayansu kafin ta dakata ta kalli Ammar ta ciro 100 dollar ta miqa masa tace ya nemo mata layin Nigeria me kyau.

Karba yayi Yana cewa ok.

Lafiyayyan sitting room din farko data fara sako kafarta ta sake sauke ajiyan zuciya akusan Karo na biyar sbd ta tabbatarda taxo inda zatai rayuwa irin Wadda takeso sbd duka luxuries na rayuwar duniya babu Wanda babu a 4&4 mansion dan haka AZIZ LIMBA kawai ya rage mata ta mallaka Wanda a cikin gidan nan takeson tafara Haifa masa yayan da zasu sauya rayuwarsa gabaki daya su bata lasisin zamowa rayuwarsa har abada.

Lafiyayyan bedroom din dayake hade da wani nutsatsen palo aka kai kayanta Wanda tini aka gyaresa aka kunna ac da qamshi da komai hatta su towels da toiletries an siyo an jeresu tas.

Wanka kai tsaye ta fara shiga tana fitowa ta saka riga da wandon bacci sallarma da kyar tayi ta haye gado tareda kashe hasken dakin t shige duvet bacci me nauyi ya dauketa.

Fatma ce taxo ta duba tana bacci dan haka baa sake zuwa ba sbd kada a dameta saida ta tashi dan kanta karfe biyun rana kafin ta sake wanka ta fito sanyeda doguwar riga mara hannu da qaramar scarf na Versace akanta tana fidda qamshi ahankali.

Madam Sisi ce da kanta tayi serving dinta abinci lafiyayye varieties taci tana gamawa ta koma palo daidai nan Jannah ta sako kai a natse cikin rashin hayaniya sanye da Doguwar riga boubou daidai jikinta da hula hannunta riqe da jakar MTN da Ammar ya bata ta kawo mata.

Muryan Jannah dince data gaidata cikin fluent English dinta dayake bayyanarda kai tsaye su din a turai aka haifesu kuma suka taso...

Hakanne ya saka Nicky dago idanuwanta da sauri ta sauke akan Jannah din tareda zubawa fuskanta ido tana kallanta batareda ta iya dauke idanuwanta akantaba.

Jannah dinma dago idanuwanta tayi jin shiru ta sake magana a natse tana miqo jakar tareda tarin canjin kudin dake cikin jakar da layin yake ciki.

Hannu Nicky ta miqa ta karba Jannah din ta juya zata fice ta bude baki tace ta dawo ta saka mata layin sbd bazata iyaba.

Dawowa Jannah tayi ta karba tareda karban wayar ta saka mata ta juya t fice zuwa aikinta.

Da daddare Jannah ce tayi serving dinta abinci tanaci tana waya da mama hankali kwance batareda jin kadaici ko wani abin ba.



Washe gari kai tsaye tace aikin Jannah takeso a komai sbd tafi iliminda zata ringa fahimtar abinda takeso dan haka Jannah ce ta koma me aikinta komai bata iyayi sai anyi mata.

Nicky haka kawai ilimi da kyan Jannah tareda wani irin class datake dashi Wanda a jininta yake sai take ganin kamar girman kai Jannah din ke nunawa ita kuma ta tsani Wanda yake qasanta yafita kowane irin abu dan haka tanason raba Jannah da wannan nutsuwar datake dashi dan haka duka ayyukanta n wahala ne Jannah keyi gashi Jannah din bata wani cika magana ba komai tace tayi zatace ok shikenan.

Ammar ma ta nasa bangaren aikin yawon wahala ne sukeyi sosai dan kullum sai anfuta da ita gashi batasan koina b shine me kaita harta gama shigarda report na zuwanta zatai hutun satika kafin ta fara zuwa aikin.

A hakan sati ya zagayo gabaki daya Nicky ta rikita gidan da murnan zuwan sauran familyn gidan da zasu iso a Daren ranar amma banda mai gidan a yanda suka ji.

Sabbin motoci aka kawo da wasu drivers din daga kamfani na mahaifiyarsa da 'yarsa dan haka karfe 1 jirginsu zai suka na dare dan haka duka motocin suna airport tin 11 na dare dan daukansu zuwa gida.
#MAMUH
#JANNAH ZAD
#AYSHNICKY
#ZAADENS
#LIMBAS

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
Mamuhgee

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss Xoxo

ADUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

09033181070
09032345899*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 12

Sai dare sosai motocin da suka dauko su Mama daga airport suka iso bakin main gate na 4&4 mansion aka bude musu cikeda girmamawa da farin cikin zuwansu motocin suka shige tin kafin su iso second gate Maheer da Dad suka wangale gate din suna rabewa gefensa suna musu hannu alaman barka da isowa Wanda babu Wanda ma ya lura dasu a cikin motocin harsuka wuce kurya sukai parking.

Madam Sisi da Nicky ne suka fito suka tarbesu suna musu barka da zuwa kafin sukai ciki dasu kowannensu a tsananin gajiye dan haka babu abinda suka tsaya sukai ciki.

Suna wucewa ciki su Maheer na gama rufe gate din suka nufo motar ganin Jannah itama sai alokacin take isowa sbd tsayawa yiwa Ummah addua datai sbd haka kawai taketa hawaye ba kakkautawa.

Uban akwatina ne nasu masu shegiyar tsada designers na LV dasu Versace dasu Fendi set set,

Jan kayan suka fara Jannah da Fatma da Amina suna kaiwa cikin gida a first sitting room da babu kowa sai madam Sisi datake kokarin fara hada dining kafin su sugama shigowa da kayan sbd masu gidan sun riga sunyi ciki.

Sun dade suna shigowa da kayan kafin suka gama shigowa dasu tas

Kafin daga palo suka sake daukansu daya bayan daya suna kaiwa bedrooms nasu Wanda kowannensu Yana toilet babu wanda suka tarar a daki,

Suna gama kaiwa suka sauko suna barin palon zuwa kitchen dake palon suka cigaba da hada dining da warming wasu abubuwan da duk aka dafa musu.

Suna gama shirya dining din suka wuce sbd madam Sisi ce keda hurumin serving nasu.

Dakunansu suka koma sukai abinda zasuyi suka kwanta.


Washe gari tinda safe suka tashi tinda yanzu masu gidan sun dawo aikin daban yake dana baya dan haka kai tsaye wanke Jannah tafara yi ta kafin Fatma suka shirya tsaf a natse suka nufi cikin gida.

Jannah ce me aikin sitting rooms dan haka ta fara wucewa sama tafara aikinta a natse.

Fes ta gyare koina ta kunna AC da qamshi ta sauko tafara na palon kasa shima ba jimawa ta gama koina ya sake daukan kyau da qamshi me nutsuwa da dadi tareda tsit sbd babu wanda ya tashi bacci.

Kitchen ta nufa Wanda Fatma da Amina sunyi nisa a aiki dan haka ta saka hannu suna dan fira sama sama Banda ita bata wani cika saka baki ba hakama firar bame hayaniya ba sbd kada a tada masu gidan.

Sbd abincin kusan kowa da Wanda yakeci a menu da aka basu dan haka basu gama aikinba sai kusan 10 dan haka suka jere dining tsaf ita kuma ta fara gyara kitchen din da wanke kayan da akai amfani dashi.



10:30 masu gidan suka fara fitowa ciki hadda fiddausi Wanda ta dade da zama limba itama kawai dai sbd sabo ne wani abin idan ba ita tayiba sai su Falaq din basa jin dadinsa.

Zaunawa sukai dukkaninsu a dining suka fara cin abinci madam Sisi da Fatma ne sukai serving nasu Jannah da Amina na kitchen na fama da sauran aikin.

Sosai suka samu nutsuwa da komai na breakfast din dan haka duk complain din Mama da Falaq basu ce komaiba har aka gama saima Nicky dake kokarin nunawa Mama maids din gidan ba laifi.

Suna gamawa suka bar dining din suka haye sama dukkaninsu babu Wanda ya sake jins dan haka masu aiki suka hau aikinsu a natse.

Jannah ce ta gyare dining din ta sake gyare koina,
Fatma kuma sai lokacin taje sama ta gyaro bedrooms dinsu duka ta sauko.

Lokacin sallah nayi sukaje sukayo sallah bangarensu suka taho suka Dora abincin rana Wanda shima bame hayaniya sukeso ba dan haka Jannah ce yawanci datasan kan abincin mutan turai suke barwa gurkin suna ji da sauran ayyukan walahar.

Hidima suka wuni sunayi sai magrib suka baro bangaren,
Jannah ce ma tafara wucewa tana gama girkin ta zuba a warmers da sauran abubuwan
Su kuwa sai bayan sun gama shirya dining tsaf da tsaftace kitchen din kamar baayi aiki a cikinsa ba suna kokarin ficewa fiddausi ta shigo tana sakewa dasu harda Jan su dan surutu ta dafawa Mama Arabian shayi ta kai dining suka sake gyare gurin suka fice zuwa bangarensu sbd fiddausi ce zatai serving nasu tace.

Jannah na isa dakinsu wanka tayi Tai sallah ta nufi gurin shan iskansu itada familynta ko data isa suna kan qatuwar dadduma Ammar na sallah da bai samu a jam'i ba sbd shegen yawon da Nicky ta fita dashi wai siyan facesheet dinta daya qare.

Maheer da Dad na zaune suna magana Ummah na gefen Dad din Yana bare mata lemun bawo da qaramar wuqa Garba kuwa ruwa ne yaje kitchen din girkin masu aiki ya dauko musu.

Tana isowa zaunawa tayi gefen Maheer tana miqa masa hannu a gajiye tace

"Nima zansha oranges din,am just so tired"

Kallanta Sukai dukkaninsu suna ce mata sannu.

Miqawa Ummah nata Dad yayi cikin kulawa Yana cewa

"Gashi kisha Amma karki sha da 'yayan ki zubar shima idan yayi Miki tsami karki sha a yanka Miki wani kinji"

Gyara masa kai tayi tana rabawa biyu ta basa tace

"Kasha kaima"

Karba yayi yakai bakinsa yasha Yana jin baida tsami yace

"To nasha Kisha kema zan yanda Miki wani"

Fara Sha tayi shikuma ya fara yankawa Jannah Maheer kuwa kafafunta data miqe yafara dan Danna mata sbd jikinta ya rage gajiya yanajin kaman ya cire gajiyar da duk takeji ya dawo da ita jikinsa.

Ammar na gama sallah juyowa yayi yana yanka mata lemun harda cire mata yayan yana bata Yana basu labarin tsinannan yawon da matar gidan ta jasa shikuma Dad yaci gaba da yankawa Ummah suna firarsu hankali kwance.

Fatma na isowa bayan taje itama tayi wanka da sallah suka fara cin abinci duk da baa kwano daya bane sun saba tare suke ci suna firarsu wadda take cikeda kulawan da sukewa juna da yanda suke tsananin kaunar juna.

Ummah da Dad a plate daya sukeci Wanda duk rabi ita yake bawa saita koshi kafin yaci,

Maheer da Jannah da Ammar kuwa suma a plate daya suke ci wata ran kuma Ammar da Jannah din zasu tare Maheer yaci shi kadai.

Fatma da Garba da suke uwa daya uba daya kwata kwata babu sabo ko shakuwa ko tsananin kaunar juna a tsakaninsu a baya Amma zama cikinsu Zaadens din a yanzu kauna da shakuwa ce me girma a tsakaninsu sbd suma a ko yaushe yanzu tare suke ci dan haka suke samun nutsuwa da kwanciyar hankali sbd duk wunin da kowa zaiyi Yana aiki da anyi magrib suna tare har dare sosai sungama shan iska da fira kafin kowa ya shige.


Gari na sake wayewa hkaa kowa ya sake kama aikinsa kamar koyaushe Jannah na gamo gyran sama tana kitchen tana aikinta Wanda tana gamawa zata koma bangarensu kawai dai abu dayane take fuskanta yanda Nicky haryanxu bata son aikin kowa sai nata din Wanda zatai so goma tace bai mata ba ahaka zatai rabin wuni tana wahala a dakin Nicky din.

Tana gano quntata mata da cin zarafinta Nicky din takeson yi sai bata taba nuna damuwa ko gazawa ba akan duka wahalar datake bata ba sbd kada ta nuna gazawa familynta tsaf zasu aje aikin sbd ita su tafiyarsu su hakura da duk abinda zasu samu ita kuma tinda basuda wani xabi gashi ko gurin zama basu dashi batason ta zamo sanadiyar sake jefasu wani hali sai kawai tana shanye duk wata quntatawa da wahalar datake fuskanta.

Tinda masu gidan suka dawo koyaushe suna sama basa saukowa idan ba abinci zasu ci ba dan haka kaf masu aikin gidan bayan Madam Sisi da Fatma data taba ganinsu kokuma ace datake ganinsu sbd lokacin datake zuwa gyaran dakunansu sun tashi suna gurin cin abinci ztaje ta gyaro ta sauko.

Babu wani me aiki dayake da ikon ganinsu sai da babban dalilin dan hakanne ma da sun gama ayyukansu suke ficewa zuwa bangarensu fiddausi ce me aikin serving nasu da sauran ayyukansu dan haka basu damu da masu aiki ba kaman yanda masu aiki basu taba samun dama ko hurumin tinanin ganinsu ba.

Basa yawo koina sai Nicky datake yawon fita aiki da kuma yawonta na banza koyaushe a cikin kashe kudi a banza a wofi take dan haka ne ma koyaushe tana gurin yawo tana dawowa zataita saka aikin rashin dalili sbd Mama ta tsaya mata kaf masu aikin gidan babu Wanda yasan cewa bawai asalin matar me gidan bace da babu aure a tsakaninsu shiyasa ake tsakanin girmamata da bin dukkanin umarninta.
#MAMUH
#ZAADENS
#LIMBAS


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
Mamuhgee

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss Xoxo

ADUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

09033181070
09032345899*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 13


Kusan watansu fiyeda daya da dawowa babu Wanda ta taba fita a tsakanin Mama ko su Falaq koyaushe suna sama hutu da rayuwar hutu kawai.

Suna cika wata biyu da dawowa Mama ta shirya tayi tafiya zuwa kauye dan haka aiki ya dan rage musu sbd an rage yawa sbd tareda fiddausi ta tafi daga Falaq sai Nicky ne.

Ahankali ahankali kawai Nicky taji batama kaunar Jannah kawai sbd har yau ta kasa ganin gazawarta hakama a yanda tai mata tambayoyi taji makarantikan da qasashen datai yawo take taji ta qyamaceta sbd har abada batason Wanda ya fita sbd idan aka fita jin takeyi zata iya hallaka ka ko illataka sbd ka koma nakasu akanta,

Akan marks na school tasha tura yara da yawa a staircase na school tin tana yarinya har zuwa gama karantunta Tasha taka mutane da mota ta ayi case din a gama sbd bata yadda da zuwa bayan wani ba a komai na rayuwarta dan hakanne ma takejin batada nutsuwa har abada koda ta samu AZIZ LIMBA saita San inda matarsa ta farko take idan tana raye ta kawar da ita daga duniyar gabaki daya hankalinta zai kwanta shiyasa ta dagewa zuwa Nigeria sbd tasan tabbas a Nigeria take Amma babbar matsalar datake tokare da zuciyarta shine kaf familyn har Mama babu Wanda ya taba fada mata komai na rayuwarsu na baya bata Sani ba waye matar?
meya rabasa da ita?
Tana raye ko mace?
Rabuwa sukai ko rasuwa tai?
Matarsa ce ta haifi Falaq kokuwa Ummitah?

Duka wannan abubuwan babu Wanda ya taba fada mata su ta kuma rasa tayaya zata Sani sbd AZIZ LIMBA sai Abinda yaso a Sani akansa ko familynsa ake Sani dan rayuwarsa a tsari da wani irin tsaro da privacy yake yinta.

Yayanta Dr Nico har haukarta tashi tayi akan ya fada mata Amma yaqi fada sbd sirrin dake tsakaninsa da LIMBA da yawa sedai idan sun mutu Amma akwai Amana me karfin gaske a tsakaninsu dan haka bangarenta daban bangaren LIMBA daban a rayuwarsa.

Wannan dalilin ne ya saka batada cikakken bayani komai akan tsohuwar matar LIMBA Amma tayi alkawarin bazata taba samun nutsuwa da kwanciyar hankali ba idan bata nemo ta ba.

Sosai taji ta tsani Jannah a gidan dan haka kai tsaye tace a nemo replacement dinta batasonta a mansion din kwata kwata.

Hakan ya saka Madam Sisi ba tareda tinanin komaiba ta dauki tsana itama ta dorawa Jannah din sbd sake samun gindin zama a gurin Nicky wadda manyan kudi ta direwa Madam Sisi tace tanason kota halin yaya ta nemo mata komai gameda matar LIMBA tshohuwa.

Indai ga kudi babu abinda Madam Sisi bazata iya yiwa Nicky ba dan haka itama goal dinta ya zama daya shine koda zata bata saita nemo labarin tsohuwar matarsa duk da tini Mama ta saki kudi masu yawan gaske aka goge labarai da komai daya shafi auren AZIZ LIMBA da JANNAH ZAD.


***Satin Mama biyu ta dawo d yamma motarsu ta shigo harabar gidan wanda Maheer dake gefe taya Ammar goge mota jin horn da sauri ya nufi gate din
Dad ma dayake baya da sauri ya fito jin horn ya nufo gate din shikuwa Ammar juyowa yayi Yana kallan motar dake shigowan su Dad da Maheer suka bude gate din a tare suna fitowa a tare daga bayan gate din wanda yayi daidai da dagowan Mama dake waya da AZIZ LIMBA ta kalli gabanta bakinta na rawa ahankali cikin wani irin sauti bugawan zuciya na shirin kamata tace "ZAADENS"


Shiru AZIZ yayi sbd yanda sunan ya sauka cikin kunnuwansa ahankali ya isa kirjinsa Yana yanka wani budadden ciwon dake dabaibaiye da kowane irin lungu na zuciyarsa,

Ahankali ya kashe wayarsa batareda ya iya furta kowace kalma ba sbd sanin koma menene Maman bata hayyacinta tinda bakinta ya furta kalman da itace tace bata yafe kowa a ahalinta ya fada ba.

Ajiye wayarsa yayi gefensa Yana dago idanuwansa da suka sauya take ya kalli baqin da Sayd ya shigo dasu Yana miqewa dan basu hannu su gaisa a natse cikin steeze dinsa dayake boye kowane irin yanayinsa.

Kallo daya Sayd yayiwa idanuwansa ya sauke kai Yana juyawa ya fice dan dauko takardun daya baro office dinsa Wainda dasu zasu zaman da baqin.


***Mama da bugun zuciyarta ke tsananta numfashinta na neman sarkewa ko tsayawa motar bata gama yi ba ta Dora hannuwanta dake wata irin rawa akan murfin motar zata bude sai kuma ta fasa da sauri ta janye hannunta tana zubawa fuskar Dad idanuwanta dake qanqancewa tsabar shock da masifaffen tashin hankali.

Fiddausi ma dake gaban motar zaune akan fuskar Ammar Zad idanuwanta suka fara sauka take numfashinta ya tsaya cak a rikice ta juyo da sauri ta kalli Mama dake baya taga numfashinta na neman daukewa idanuwanta kafe akan fuskar Dad.

Da sauri fiddausi ta juya inda Maman ke kalla itama nata idanuwan suka sauka fes akan fuskar Dzad kafin ta riqe numfashinta dake futa da karfin gaske Maheer ma ya bayyana a bayan Dzad din dukkaninsu sanye da shirts masu dauke da sunan 4&4 mansion Wanda babu tantama hakan na nuni da a cikin maaikatan gidan suke,

Shin sun San a inda suke kuma suka zauna suna aiki kokuwa basu Sani ba??
Shin wace sabuwar masifar ce zata afko ayanzu da katsam Allah ya bayyanardasu a cikin gidan bayan rantsuwa da alkawarin da duka ahalin gidan suke daure a cikinsa na Mama.

Kokarin dawo da kanta daidai Mama tayi cikin karfin hali da hadiye duk wata tafasan zuciya da baqin cikin daya taso tayi ta sauke ajiyan zuciya kafin ta dawo da idanuwanta ahankali akan fiddausi da har jikinta rawa yake dan yi.

Numfashi me zafi Maman ta sake sakewa kafin ta iya bude bakinta tana kame fuskanta sosai ba sakewa ko kadan tace

"Ko a cikin mayen hauka karki yadda ki fadi abinda kika gani,
Baki ga kowa ba,
Bakima San kowa ba idan wannan maganar ta shiga kunnen Falaq ko Sayd da zai iya kai zancen kunnen 'dana ki Sani zamanki da Falaq a limbas ba ma ya qare kwata kwata har abada,
Ina fatan kin fahimta kin kuma San abinda kikeyi?

Jajir idanuwan fiddausi sukai take sbd girman magana da abinda Maman take shirin aikatawa na hana kowa sanin Zaadens na mansion din duk da tasan zaiyi wuya gobe a wayi gari dasu a mansion din batareda ta tabbatarda sun bata ba.

Tayaya zata boyewa Falaq Zaadens na tareda su a mansion daya Wanda ta tabbatarda Jannah bata nesa tana kusa idanma bata cikin mansion din sbd zaiyi wuya Zaadens su iya tafiya koina batareda jannarsu ba?

Tayaya tana kallo Falaq na kuncin rashin Jannah suna guri daya Amma ta kasa gaya mata har sai Mama ta korasu inda bazata taba samunsu a kusa ba kila?

Amma kuma hukuncin Mama yayi mata tsaurin da batada xabi saina binsa dan haka ta sauke idanuwanta ahankali jikinta a tsananin mace tace

"Inshallah Mama"

Ajiyan zuciya Maman ta sauke kafin ta dauke kai daga kallan fiddausin ta cewa driver yakaisu ta gurin hanyar shigar Mai gidan idan yana gari.

Daman bai kashe motan ba ya jata zuwa gaba sosai har bakin inda motan me gidan take ta kofa ta Musamman yayi parking.

Su Dad bayan motar suka bi da kallo da mamakin kodai Mai gidan ne a ciki y dawo tinda akai can ciki sosai da ita.

Basu wani damu ba suka koma bakin aikinsu a natse hankali kwance.

Ita kuwa mama bude mata motar driver yayi ta fito ta shige ciki har lokacin zafin zuciyarta bai sauka ba.

Fiddausi jiki a sanyaye ta fito ta shige ciki da kayansu itama zuciyarta gabaki daya a sanyaye da kuma fargaba.

Suna shiga suka haye sama fiddausi takai kayan Mama har bedroom dinta tukuna ta fito ta nufi nata dakin tkaia kayanta ta kasa fitowa taje dakin Falaq sbd yanda takejin kaman bazata

Please Login or Register in order to submit comment