Reading KALBIM BOOK 2 BY MAMUHGEE Chapter 26 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hotonsu tareda recording wasu daga maganganunsu akan cikin kafin ta samu dakyar tayi zooming result din hannun Fatma data Kafe da ido tana kuka inda sunan Jannah Zad ya fito baro baro da tabbacin cikin jikinta Sati Bakwai.

Miqewa tayi ya fice batareda sun ganta ma sbd su halinda suke ciki ya ishesu.

Sun jima cikin kuka da jimami kafin suka yanke shawarar qin barin kowa ya sani kafin su samu mafita musamman AZIZ din da yana Jin cikin zai iya bayyanawa kowa ba ruwansa da duk Wanda ciwon zuciya zata kama.


Fitowa sukai bayan sun karba tsadaddun maganin da aka rubuta mata suka wanke fuskansu suna kokarin komawa daidai.

Suna barin asibitin gurin cin abinci Fatma tace akaisu sbd Jannah din tasamu taci Dan ana komawa gida ba iya ci zataiba sbd tana ganin su Dad zata iya shiga sabon tsoro.

Wani babban lafiyayyan Eatery suka tafi sukaci abinci sosai me Kyau da tsada suka koshi suka fito.

Basu tafi gida Kai tsaye ba Saida sukai Dan zagaye dukkaninsu suka sake sakewa tukuna suka iso gida.

Gabaki daya Zaune suke a palo sunata jiran dawowansu,

Ummah na zaune gefen Dad Wanda yake kwantar mata da hankalin lafiya kalau inshallah,

Maheer sai Kiran wayar Fatma yakeyi Bata shiga Ammar Kuwa Shiru yake a dayan gefen Ummah ya kasa cewa komai haka kawai yakejin jikinsa yayi sanyi fatarsa kawai ciwon Jannah ba wani serious ciwon bane da yamafi tinanin maleria ce ta sauron kauye ko Kuma yanayin ruwa da cimar kauyen ta taba ta tinda tayi fiyeda shekara koma fiye Bata ci ba.

Suna shigowa Fatma ta Dan sake fuskanta tana kallansu itama Jannah din daurewa tayi tana sakewa suka qaraso suna zaunawa Maheer ya Kalli Fatma yace

"Meyasa wayarki ayita kira ne bata shiga?

Dan marairaicewa tayi sbd sake basar da yanayin tace

"Tace wlh Yaya Maheer nima bansaniba kila network ne"

Maida kallansu kowa yayi akan Jannah suna mata sannu ta amsa tana murmushi a sake tace

"Nafa ji sauki since malaria ce da yanayin sauyin cima kawai amma sun bamu magani tin acan ma naji na fara samu sauki"

Ummah data riqe hannunta cikin nata sauke ajiyan xuciya tayi tana Hana su Maheer da Dad magana tace

"Buqatanmu lafiyarta da Kuma fatan ba wani babban ciwon bane Dan Haka mu godewa Allah"

Shima Dad sanyi da nutsuwa yaji ya qara mata sannu yana cewa taje tai wanka taci abinci ta kwanta ta huta.

Maheer binsu yayi da ido itada Fatma din da suka miqe take suna nufar daki kaman munafukai.

Ammar daya kasa cewa komai maganin yaso karba ya gani amma yanda Fatma ta riqe ledan maganin kaman rai da yanda tafin hannuwan Jannah sukai wani irin hasken daya sakasa kafesu da ido ya saka har suka shige bai samu cewa komaiba.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 58


Suna shiga daki Fatma ta isa gaban dresser ta janyo drawer ta saka ledan maganin ta rife ta nuf toilet da sauri sbd fitsarin tsoron kar a ganosu kaman zai zubo mata.

Jannah ma zama tayi bakin gadon tana sauke ajiyan xuciya tanajin ma kaman da gaske ciwon ya fara tafiya,

Falaq ce ta shigo da fiddausi dauke da tray na snacks da paper meat me dadi da sukai garnishing dasu cabbage and potatoes da mayonnaise.

Fiddausi ce ta hada mata ita Kuma Falaq ta hado smoothie Dan gasar yi mata girkin akai.

Murmushi tai tana kallan yanda suka ajiye mata komai akan table ta taso daga bakin gado tana dawowa kan couch ta zauna tana kallan samosa data balain shiga ranta tace

"Aikuwa duka zan cinye"

Miqewa tayi ta nufi bathroom da Fatma ta fito tayo wanka da alwala daga can daure da qaton towel daure a jikinta ta fito.

Fadawa tayi itama tayo wanka tareda alwalan tana fitowa sallah tafara yi kafin ta shirya cikin freesize riga da wando ta zauna gaban kayan tafara ci tana Jin Wani dadin papper meat din na ratsata tana Sha da smoothie da juice duka.

Fatma data dawo daga Palo dauko ruwa a fridge itama zaunawa tayi tana saka hannu suka fara ci kaman basa cikin damuwa komai.

Hadda fiddausi da Falaq din suke ci gabaki dayansu suna fira hankali kwance a sake.

Bayan suna gama magani Jannah Tasha daga nan ta Dan miqe kwance tana Jin jikinta da cikinta suna mata dadi ta ringa lumshe ido suna fira tana jinsu.

Falaq data ga yanda takeyi ta fara massaging mata kafarta cikin kauna da kulawa.

Har ishai suna dakin Saida Ummah ta shigo da Kanta ta kirasu suka fito anan dining din palonsu zaadens sukaci dinner gabaki dayansu harda Ummah dasu Falaq da fiddausi masu aiki suna serving nasu.

Suna gamawa anan akaita fira har dare sosai tukuna fiddausi ta kama Falaq suka koma samansu.

Jannah ma duk yanda Ammar yaso samun daman fira da ita sbd kewanta da yayi bai samu damar ba sbd baccin dayake cike da idanuwanta.

Shigewa tayi itada Fatma Maheer daman yana daki yanata process din nema musu aiki mekyau daya duqufa kwanakin a laptop.

Garba ma yana daki ya shiga wanka yana fitowa yayi shirin bacci da saka turare me kamshi da sanyi Wanda a yanzu Shima ya riga ya saba da wata irin tsafta da qamshi tareda sanin darajar Kai sbd zama cikin zaadens musamman Ammar dayake kokarin sauyasa sbd yanason duk inda zasu su tafi dashi Dan ingantasa ya maidasa tsayayyen namijin daya San kansa.

Ammar ma miqewa yayi bayan shigewan Jannah ya yiwa ummansa Saida safe ta amsa cikeda kulawa tana Masa addua kafin ya yiwa Dad ya nufi daki.

Dad da umman ne kadai suka rage a palon Dan haka Ummah taje fridge ta daukowa Dad din ruwan dayace yana buqata ta doro a tray me kyau da cup ta dawo ta ajiye gabansa tana Daukan roban ruwan ta bude ta zuba Masa ta miqa masa ya karba yana kallanta a natse cikeda kulawa.

Ruwan yasha a natse yana riqe hannunta cikin nasa yace

"Thank you Allah Miki albarka"

"Amin" tace tana murmushi ta Dan kallesa tana son janye hannunta ya sake riqewa cikin nasa yana cewa

"No Fatima"

"Hanya ta kalla tana murmushi tace

"Yara fa zasu iya sake fitowa"

Baice komaiba ya miqe yana riqe da hannunta suka nufi hanyar bedroom dinsa yana cewa

"Koyaushe zancenki Yara,
Kulawanki ma yanzu duka akan Yara ne Fatima"

Shigewa dakin sukai tana kasa basa amsa sbd zame hannunta datai ta nufi bathroom sbd alwalan sallan ishai da bataiba se yanzu.


Mama da tin tafiyar AZIZ tayi tafiya kauye washe gari sai gata ta dawo bayan fiddausi da Falaq da sukai murna da dawowanta babu Wanda yabi ta Kanta tinda daman dai Zaadens ba Shiri sukeyiba hakama Nicky tinda ta dawo asibiti take cikin damuwa da kunci madam Sisi ce kawai take kulawa da ita sai fiddausi dake kokarin ganin koyaushe ta fito taci abinci sbd kusan kulawan duk ahalin LIMBA kaman a hannun fiddausin take yanzu.

Tsaraban kayan ciye ciyen kauyen da mama ta saba ita ta kawo musu su fiddausi sukaita murna Jannah ma da suka shiga ranta sosai da ita aka cinye tas da Fatma.

Se dare Jannah ta Taho har sama har dakin Maman itada Fatma suka gaidata cikeda girmamawa tareda mata barka da dawowa.

Zubawa Jannah idanuwa Mama tayi bayan ta amsa gaisuwan tana kallanta gabaki daya tana ganin sauyi me yawa a tattare da ita.

Bata kawo tinanin komaiba itama sbd sanin ko aure Jannah din batada shi bare ma wani yayi mata tinanin ciki indai ba andaura mata aure da Ammar bane bayan Bata nan har aka samu cikin.

Ficewa sukai suna fitowa Ummah na isowa kofar dakin Maman wadda haryanzu basu fuskanci juna ba sbd AZIZ na tafiya Mama tayi tafiyarta se yanzu.

Ajiyan xuciya Ummah ta sauke a hankali tana sake Jin dukkanin damuwa da Wani dattin tinani akan Sakina yana sake wanke mata sbd duk laifin da Sakina da kuskuren datai kauna da irin riqo da sadaukanwa da uwa data zama ga AZIZ da Ummitah ya take duka laifin da kuskuren Dan har ita har AZIZ har Ummitah babu abinda zasu iya biyanta dashi har abada,

Kuskuren datai shedan ne Dan zuciya sukaci galaba akanta sbd irin kaunar datake wa AZIZ da kishin uwa akan danta daya shigeta Wanda babu Wanda ya wuce Hakan ta faru dashi a cikin uwaye da dama,

Hakama duka kafin wannan ita kanta bazata manta wacece Sakina a rayuwarta ba sbd itace ta zama gatanta Dana AZIZ tin Bata haifi Ummitah ba bayan rasuwar mijinta.

Ita a gurinta komai ya wanke ya wuce tinda shi kansa AZIZ din baiyi fushi da itaba duk girman laifin ya barshi tinda dai uwarsa ce ba yanda zaiyi da ita dole sai hakurin Dan a gurinsa idan har zai iya dagawa Ummah murya to zai dagawa Mama idan Kuma bazai iyaba to har abada bazai iya dagawa Maman ba Dan dagawa Mama murya kaman dagawa Ummah ne shiyasa ma kawai ya hadiye bacin ran da fushin ya kaurace mata sai bayan da ya gama digesting abin Kuma ya sameta da kansa.

Hannu Ummah ta miqa a natse ta buga kofar dakin Maman tana Dan dakatawa.

Mama data gama waya da AZIZ din Wanda yayi mata barka da sauka lfy ajiye wayar tayi tana cewa

"Yes waye ne?ya shigo"

Bude kofan Ummah tayi a natse tana shigowa fuskanta a natse babu fushi babu matsewa babu komai.

Kallanta Mama takeyi cikeda mamaki da wata irin kunya da damuwa kafin ta dauke Kanta tana kasa kallanta a sanyaye tace

"Bismillah zauna"

Zaunawa Ummah tayi a kan lallausan sofan dake dakin tana kallan Maman tareda kokarin kawar da Jin nauyin junansu tace

"Barka da dawowa,ya hanya?ya mutan gidan?

Batareda mama ta kalleta ba nauyinta na qaruwa tace

"Lfy kalau alhmdllh,mutan gida ma duk lfy suna can"

Shiru sukai babu Wanda ya sake cewa komai sbd Mama Bata sa ta inda zata fara ba Dan kunya da baqin cikin duk abinda ya faru datake ji.

Umman ce ta sake motsawa tana Dan sake murmushi me sanyin sauti tace

"Sakina kiyi hkr da duka abinda ya faru Wanda ya faru ne bana cikakkiyar hankalina,

Kuma yanzu Dana dawo daidai din nayita son magana dake amma ban samu damar ba sai gashi kinyi tafiya"

Mama da jikinta ya dauki dumin sanyi da kunyar duniya gabaki daya dagowa tayi bakinta na nauyi tace

"Fatima kina bani hakuri ne sbd ki ragemun girman kunya da abin kunyar dana aikata ne,

Girman kunyar danake ji ai bazai ragu ba sbd nayi kuskuren daya kusan batar Dani gabaki daya amma ki sani wallahi tallahi Fatima banyi komai Dan wata boyayyar manufa danake da ita ba sai akan tsoro da fargaban rasa AZIZ Wanda nake Jin tsananin kishinsa a matsayin Dana bana kaunar duk Wanda zai rabani dashi ko nesantani dashi shine kawai abinda ya rife zuciyata, tinanina da Imani na amma bayan wannan walhi Fatima ban taba binki da Wani sharrin ko manufarba ke da yayanki.......

Katse Ummah tai da girgiza kai tana cewa

"Sakina ban taba zargin da wani abin ba nima bayan wannan Kuma tinda Allah ya kawo saukin abin ai shikenan,

Sannan babbar maganar da nakeson fada Miki itace ki sani ABDULAZIZ danki ne wlh duniyar nan har lahira,

Ban dawo da rabaki dashi ba sbd kece kika fini saninsa a yanzu Dan kece kikai rayuwar datafi tsayi dashi akan ni,
Duniya ma batasan kowace uwar AZIZ din ba bayan ke,
Kece uwarsa a baya Kuma kece uwarsa a yanzu,
Bazan iya rabaku ba sbd akwai shaquwa da kauna tareda girmamawa a tsakaninku,

Ni ina da wasu Yayan a yanzu da zan zame musu uwa har karshen rayuwata Dan haka kema bazan rabaki da naki ba,

Dawowana rayuwarku babu abinda zai sauya Miki keda AZIZ sbd shi kansa bazai yadda wai ya juya ko sauya Miki ba Dan Kuwa shi din Dan halak ne Dan haka ina fatan basai munyi janye janye ba komai ya wuce zamu yafi juna"

Ajiyan xuciya da numfashi Mama ta sauke hawaye na gangaro mata sbd AZIZ da mahaifiyarsa sun nuna mata kyakkyawan zuciyar data Fi tata tsafta.

Ummah ganin hakan ta qara Bata hakuri tana Dan kokarin Jan Maman da firar baya sbd son su sake kaman yanda suke tin farkonsu.

Kuka sosai Mama ta fasa a gaban umman tana Bata Wani irin hakuri harta saka Umman kuka sukai abinsu suka Shirya daga nan suka koma Tina baya Dan shine zai dawo musu da cikakkiyar kaunar da sukewa juna me karfi da tsafta.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 59


Har dare Ummah na tareda Mama Dan haka ma ko dinner tare sukai gabaki dayansu anan bangaren Bata je gurinsu Dad ba.

Jannah ma a cikinsu tayi dinner tareda su Falaq Maman nata kallan Jannah tanajin zuciyarta Bata nutsu ba da sauyin dayake tattare da ita sbd AZIZ dinta daya gama mutuwa akan Jannah din gashi kaman da akwai matsala.

Ita dai Jannah Bata wani riqe Maman a rai ba sbd haryanzu ita takewa kallan mahaifiyar AZIZ dinta Ummah Kuma ummanta ce kawai.

Sun gama dinner a dakin ummah tayi kwanciyarta karshe ma anan ta kwana da zazzabin dare batareda ta bari Umman ta sani ba.

Washe gari gabaki dayansu suka fita su Biyar Ita, fiddausi,Falaq, Ummah da Fatma fiddausi ce tajasu a mota suka tafi gyaran Kai sbd kowannensu yana buqata.

A wani tsadaddan spa sukai branching Wanda Already fiddausi da Falaq nada Vip card a gurin already Jannah ma tanada shi itada Anny tintini amma yanzu ta rasa card din amma kusan dayake akwai sauran maaikatan baya a gurin suna zuwa suka ganeta tareda tarbanta cikin tsananin girmamawa da rawar jiki.

Bangaren Manyan clients nasu aka kaisu sukai booking gurin gabaki daya sbd Ummah da fatma da ta Dan iya zuwa irin guraren yanzu itama sbd ko Lagos kusan so uku suna zuwa irin guraren.

A gurin suka wuni sai yamma suka baro suka dawo kowannensu fuskansu na daukan ido hakama skins nasu sai qamshi sukeyi me dadi.

Tinda suka dawo Ammar yake bin Jannah da Kallo me sanyi sbd ta sake zama kaman wata tauraruwan rayuwansa amma hakanan yakejin jikinsa na sanyi akan Jannah din da kansa.

Fatma ma garba dayake ganin shi gabaki daya ta sauya Masa tayi wani irin haske da ja ta sauya kaman ba ita ba yauma ganin yayi ta qarasa sauya Masa sai tsokanarta yakeyi da Fatma ce wannan ko baturiyar Fulani.

Dad take fadawa yace ta kyalesa neman magana yake.

Maheer dai Shima magana ne kawai baiyiba amma Fatman ta sauya gabaki daya a idanuwansa dayake tinanin ko shi kadai ya sauyawa Ashe ba shi kadai bane amma gudun ace Shima tsokanarta yayi tinda girmamasa takeyi sosai sai yayi Shiru abinda.

A gajiye suka dawo Dan haka babu wata hayaniya a gidan dukansu kowa yayi daki yai wanka basu fitoba har washe gari.

Kwana biyu Jannah ta samu karfin jikinta duk da kowane dare da qananun zazzabi take kwana amma babu Wanda ta bari ya sani daga ita sai Fatma suketa nuku nukunsu da neman mafitan yanda zasuyi gashi kaman kada su San dashi sai taga cikinta yana kokarin fara Dan kumbura tinda an sake daukan kwanaki da sanin.

AZIZ kowane dare suna wayansu a Wayan Fatma Bata fada Masa ba Kuma tanata tsoron tinanin terminating cikin amma Shima Hakan tana tsoro.

A bangaren Nicky ta rame tayi fayau ta zama kalar tausayi sbd babu me kulawa ta Kanta,
Mama ce take kulawa da ita Shima ba irin sosai ba sai Ummah da itama tana kokari akanta duk da ta Hana kowa ya shiga cikin lamarin ciwonta karshe ma nunawa tayi ta warke ga ciki na kokarin fara bayyana Dan haka ta qarasa zama abar tausayi tinani da baqin ciki da kadaici na neman kasheta a daki ita daya.

AZIZ Sam Baya daga wayanta ko ta kira karshe ma dena samunsa tayi da alama yabar kasar kila.

Ana cikin Hakan ne Fiddausi ta fara lura da sauyin Jannah sbd idonta daya gane mata shafaffen cikinta data Dani ya fara tasowa amma Bata kawo komaiba Dan abune da yake buqatan tabbatarwa indai ma cikin ne zai fito da kansa.

Dad da a yanzu yagama samun kan matarsa sun jame abinsu zam babu komai a tsakaninsu yanxu se soyayya me sanyi da mutunci take yafara tsananta neman aikinsu su duka me Kyau sbd ya bar nan su koma nasu muhallin Dan yama gaji da zama gidan 'Dan matarsa ba girmansa bane.

Ammar ne ya fara samu interview kafin Maheer Dan haka babu Bata lokaci suka tafi aka fara zaman jiran kira.

Yau tin safe Jannah din ta tashi da yanayi na rashin karfi da mutuwan jiki Dan zazzabi qasa qasa yana damunta Dan haka taqi fitowa bare shiga mutane dan kada a ganeta hakama ta nesanta Kanta sosai da Ammar sbd kada y gane halinda take ciki tinda shi likita ne duk da bana mata bane amma dai ko yayane zai iya ganewa Dan haka take Dan nesanta dashi Wanda Hakan yake tsananin damunsa Dan haka ya sake tada maganar aurensu tareda dagewa akan aikin da suketa fatan farawa tinda bazasu tabbata a gidan AZIZ ba a karkashinsa suna zaman Banza.


Kwana biyu tana fama Fatma nata tarairayanta Dan kada a ganesu sunata lallabawa.

Asibiti sukeson zuwa amma ba dama sbd yanda Maheer ya kafa ya tsare akansu su biyun.

Yau tana tashi tayi kokari ta Dan sake ta fito taci abinci cikin family suna gamawa ma ta tsaya akai Dan fira sosai har yamma sai gashi ta samu karfi sosai da sakewa sbd zama cikinsun ya taimaka mata.


*******Zaune yake yana karanta Wani report da Saleem ya kawo Masa shi da Sayd yana Dan dubawa a natse su Kuma suna zaune a kujera daddaya suna facing nasa kowannensu report din yake sake bi.

Wayarsa ce tayi haske tana vibrating ya Dan dauke idanuwansa masu haske ahankali daga kan abinda yake karantawa ya Kalli wayar tana gefensa.

Aysh ne sunan daya bayyana a screen din wayar Dan haka bai motsa ba ya Maida kallansa kan abinda yakeyi.

Sake shigowa Kiranta yai harya tsinke bai dagaba saiga Kiran ya dawo kan wayar Sayd.

Kallan Kiran sayd yayi Shima bai dagaba sbd abinda yake gabansu yanada tsananin mahimmanci.

Sakonta ne ya shigo ta saman wayar Sayd Wanda ya sakasa ajiye ipad din hannunsa yana daukan Wayan ya bude sakon yana kallan AZIZ Wanda bai dago ya kallesaba har lokacin kafarsa daya na kan daya.

"Jannah is pregnant da wani AZIZ na buqatan sanin Hakan"

Shine abinda sakon yake a rubuce sai hotinan scan nata da sunanta baro baro a jiki da satikan cikin.

Bude sakon yayi da Kyau yana sake karantawa ya Kalli Saleem Wanda ya juyo ya kallesa da mamaki kafin ya Dora kansa akan screen din wayar Sayd din yana ganin sakon ya Kalli AZIZ da sauri Wanda sai alokacin ya dago ya sauke idanuwansa akansu Jin idanuwansu akansa suna kallansa.

Bude baki yayi cikin class da kamewa yace

"Me yake faru ne?

Riqe wayarsa sayd yayi yana tinanin ta yanda zai fara fada Masa abinda zai qarasa sauya rayuwansa gabaki dayanta Saleem Kuwa kasa yadda yayi wai princess dinsu zata zama Mum.

AZIZ ajiye iPad din hannunsa yayi yana kallan wayarsa ya Kalli miss call din Nicky yace

"Wani abin ya faru a gidan kenan?

Kafin sayd yayi magana AZIZ din ya daga Masa hannu yana saka Kiran Nicky Kai tsaye.

Tana zaune duk damuwan duniya ta rufeta ga ciki ya fara fitowa rashin mafitan yanda zata fuskanci kowa da cikin ya sakata tona asirin Jannah ga AZIZ sbd fara ganin yanda zata kaya kafin nata.

Kiransa na shigowa ta dauka da sauri ko gaidasa batai ba tace

"Mine nayita baka dauka na kasa riqe kaina ne na turawa Sayd komai Jannah cikine da ita Kuma a tafiyan datai kauye kwanakin baya ta samosa na ganta da idona asibiti inason ka sani ne kafin ta zubar dashi ta rufe kowa sbd kukan datakeyi banajin ma Bata zubar ba.......

Dif taji Kiran ya yanke ya kashe wayarsa yana kallan Sayd da idanuwansa da suke wani sparking din abinda shi kansa bai saniba hannu kawai ya miqa masa.

Wayar Sayd ya miqa masa yana karba abinda ya gani ne ya sakasa dagowa ya Kalli Sayd yace

"A siya ticket din komawa na yau dinnan ina buqatan zuwa Dan tabbatarda Zancen samun arzikin dayafi kowane arzikin duniya"

Saleem daya kasa gasgatawa har lokacin kallan AZIZ yai yana miqewa Shima yace

"Inaga nima zan taho I can't wait"

Kasa cewa komai AZIZ yayi sbd wani feeling dayake gauraye xuciya,jini da numfashinsa.

Babu abinda yake tsananin buqata irin ya shaqi qamshi da numfashin dayake fitowa tin daga cikin Jannah din har cikin kansa Dan haka ya ajiye komai yana jiran a duba ticket din jirgin da zai diresa a Abuja a Daren yau.
#MAMUH
07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 60

*_ZUZEAM VENTURES_*
Best kayan Mata
08144015291
*NEW ALERT*
*END OF DISCUSSION PACKAGE*
~25k~ promo 12k
Barka da Sallah promo pack
1. Tabajen kankana da fruit
(Mai saukar da niima nan take ta kara miki dadi na musamman keda oga sai kunyi kukan dadi ranar )
2. ⁠gumbar chakwala dadi
(Hmm yar uwa daga jin wannan kema kinsani basai anbaki labariba wannan hadin na zallar dadi ne da ciko da gaba)
3. Turare kyauta dole
(Wannan turaren na amsar kyauta ne ina masu fama da miji mai mako wanda ba a cin kudinshi Ga shi da abun amma ba a ci to yar uwa matsalarki tazo karshe da izin Allah Sai kinci abunshi ina yan kasuwa duk kina amfani da wannan turaren sai Kinga budi da izinin Allah)
4. Zumar bata gaban kishiya yar asali
( wannan zumar Ga mata wanda kishiya ta shiga gabansu mijinki baki gane kanshi ya fifita yar uwarki akanki baya son mu’a mala dake ko wadda mijinta ke biye biye yar uwa kukanki yazo karshe duk kikayi amfani da ita duk machen da yayi sex da ita zaijita salab kamar dusa don haka aji tsoron Allah banda wanda suke zaune lfy da kishiyoyinsu)
5. End of discussion powder
( wannan garin karshen zance kenan hajiya oga ya taba miki kukan agwagwa ko mussoshi 😁to ranar duk da kika sha wannan hadin garin hajiya sabbatu sai kin rufe mishi baki ihu da kururuwa ba sauki kuma garin wata 7 yake ajiki yana aiki )

Hajiya karki bari wannan promo ya wuceki 25k ne promo saboda sallah 12k kacal

TikTok: Zuzeam.ventures5
Instagram: Zuzeam_ventures
WhatsApp: 08144015291



************
Saukan yamma jirginsu yayi Dan haka kai tsaye motan Bentley continental Aka zo daukansa da ita wadda tin gurin ficewa da ita daga gidan Maheer na ganin an fiddota yasan AZIZ dinne ya sauka daga duk inda yaje sbd motocinsa daban ne Dan haka ya sanar dasu Dad AZIZ na gari sai kowannensu ya Dan kame kansa ma daga fitowa.

Ko daya iso 4&4 din magrib tayi dan haka baya securities na gate dasu su Dad din da suka hade dashi ya gaida Dad suka gaisa dasu Maheer din ya shige suka wuce masallaci su Kuma babu Wanda yasan ya dawo gidan sbd hanyarsa ta hayewa sama palon daban ne hakama Saleem bangarensu daban ne Dan haka babu Wanda ya gansu bare asan sun dawo din gashi basuyi waya da kowaba suka sanar har gwara fiddausi Sayd yayi ta Kiranta ya sanar Mata amma baa daa wayanba.

Su Jannah da fatma na sama dakinsu fiddausin sunata fira Banda Jannah din dake kwance jikin 'yarta sbd Falaq kaman itace babyn Falaq ce uwar sbd dumin da jikinta yayi Dan kasalan zazzabi takeji kadan Dan haka ta lafe jikin Falaq dake tarairayanta tana suna kallansu fiddausi da Fatma dake zuba surutu suna musu dariya.

Cookies da toffee suka gama yowa a kitchen kafin zaman shine sukaci suka bari me dadi da yawa a gabansu sunata sake zuba abinsu hankali kwance Mama da Ummah Kuma suna tare a dakin Umman suna tasu firar.

Sallan magrib sukai suna gamawa Jannah ta sake lafewa cikin sofa tana Dan duba abu a Wayan Falaq dake hannunta.

Hoton gaban Wayan Falaq din ta zubawa idanuwanta da sukai laushi tana kallan fuskar Wanda Bata iya taba dena tsananin sonsa me sanyi da tsafta tana kewansa ma kawai yana rufeta musamman data Tina cikinsa dayake jikinta Jin tayi inama zata iya sanar Masa amma bazata iya ba sbd zai iya bayyanawa kowa ya sani ta shiga tashin hankali Dan bata kaunar fushi da bacin ran Dad dinta ko kadan musamman da duka kowa baisan da aurensu ba kowa yasan babu aure tsakaninsu ya Dade da mutuwa kawai sai a sameta da ciki.

Sanyi jikinta yayi daga wannan tinanin take taji tsoronta yana dawowa da fargabanta Dan haka ta ajiye Wayan gefenta ahankali tana Dan rufe idanuwa kaman zatai bacci a gurin.

Fiddausi data miqe daga inda tai sallah wayarta ta nufa dake ajiye kan dresser ta dauka a natse tana dubawa taga misscalls din S da iya shi tai saving numbernsa dashi sai emojin heart fara agaban S din.

Dawowa tayi ta zauna gefen Jannah tana saka kiransa.

Ringing tayi harta yanke bai

Please Login or Register in order to submit comment