Reading KALBIM BOOK 2 BY MAMUHGEE Chapter 5 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

annurin kwarjininsa fuskansa na sake bayyanarda wani irin sirrin kyau da Kamala kamar ko yaushe,

Milk Brioni's ne a jikinsa sosai agogon Cartier dake bayyanarda ba qananun kudine ke siyansaba.

Idanuwansa masu kashe Nicky ya dago ya kalli Mama Yana zama a natse ya bude baki yace

"Good morning Mama,
Mun tashi Lfy?

Kallansa Mama tayi dakyau tana sake jin wani irin ciwo a ranta ta yanda 'danta ya sauya batareda shi Kansa ya San da hakan ba Amma akwai wani irin sauyi tareda shi wanda ita kanta a tsawon lokacin nan ta kasa tantancewa.

Cikeda kulawa da sakewa ta amsa tana cewa

"Barka da fitowa"

Gyada kai yayi Yana maida idanuwansa cikeda kauna me tsananin karfin da har koyaushe take qaruwa ya kalli Falaq wadda itama shi din take kalla tana narke fuska.

Hannunsa ya miqa mata a natse Yana cewa

"Hey my baby"

Kama hannunsa tayi tana qanqamewa cikin nata ta bude baki tace

"Good morning DADDY"

A yanzu duniyarsa gabaki daya itace ke ganin murmushinsa kai tsaye sai abokan aikinsa musu mahimmaci sai kuma fira idan anayi dashi a gidajen tv wanda ba asalin murmushin daya fito daga zuciyarsa ne suke gani ba,

Ita kadai ce take samun murmushinsa dayake fitowa daga qasan zuciyarsa sai kuma personal person nasa dan Amanarsa Sayd Limba.

Sakar mata wani lafiyayyan murmushi me nutsuwa yayi Yana kissing hannunta a natse yace

"Yau zaki samu enough time da Bestynki i promise you that my lady"

Murmushin farin ciki ke son fito mata amma tana kokarin dannewa sbd Wainda ke gurin.

Sayd ne daya iso ya saka hannu akan fuskanta yaja gefen kumatunta Yana cewa

"Yi murnanki anan waye zaki jawa aji tinda munsan lokacinda yarinya take kuka tana bin Daddynta da takarmi daya a hannu akan zata bisa duk inda zasu so just chill Ms Aziz"

Saurin kallan Daddynta tayi tana toshe bakinta batason dariya tace

"Did you hear that Daddy?"

Murmushi ya sake yi yana cewa

"Kyalesa yanason ya taba Miki steeze ne kawai"

Dariya Sayd yayi ganin tana kallansa tana juya masa ido alamar yayi trying next time yanzu baiyi nasara ba tana masa dariyar dayake jinta har cikin ransa sbd kwata kwata yanzu bata cika dariya ko dogon farin ciki ba kamar baya ba dan haka koyaushe yake kokarin tsokanarta sbd tayi dariya da farin ciki.

Nicky da tinda AZIZ LIMBA ya zauna a     dining din bata sake motsin komaiba kallansa takeyi zuciyarta na wata irin narkewa,

Murmushin daya kewa Falaq ne yake sukar zuciyarta tana jin radadinsa har cikin kowane digon jinin dayake yawo a jikinta sbd irin son datake masa har yarsa Falaq jin takeyi tana tsananin kishin irin so da kaunar dayake mata har cikin ranta,

Sonsa takeyi kuma ita kadai WA kanta,
Ita kadai takeson yaso a rayuwarsa
Koda bazai sota ba ya bari to ita kadai taso sa,
Yanda take jin kishin Falaq badan 'yarsa ce ba jininsa da tini ta cireta a rayuwarsa kwata kwata duk da batasan gaba ko xata iya jure ganin irin wannan son dayakewa Falaq din ba,

Duk ranar da AZIZ LIMBA yaso wata macen irin yanda yake kaunar Falaq batasan iya mutanen da zata iya rabawa da duniya ba sbd kaf danginsu zata karar ko sunyi yawan me..

Sayd ne ya gaida Mama Yana zaunawa kafin ya dan kalli Nicky din yace

"Good morning Aysh"

Tana dan dauke idanuwanta daga kan AZIZ Wanda baima kalli inda take ba ta gaida Sayd din itama tana dawo da kallanta kan AZIZ ta bude baki tace

"Good morning Mine"

Saida ya dauki lokaci Batareda ya kalletaba ya amsa a taqaice yana daukan fork ya fara cin Italian breakfast din da fiddausi tagama jerawa a dining.

Shiru gurin yayi kowa na breakfast da masu tinani.

Bai iya gama cin abincin ba yaji ya ishesa ya rasa appetite dinsa gaba daya dan haka ya dauki tissue ya goge bakinsa ya miqe batareda ya kalli kowaba sai Falaq daya ranqwafo yayi pecking goshinta yana cewa mama

"Mu wuni lafiya" ya fice Sayd ma miqewa yayi ya bar gurin Yana manta files dinsa dayazo dining din dasu.

Mama ce ta zubawa files din idanuwanta ta tsayar da idanuwanta akan sunan sabon kamfanin 4&4 din uLIMBAS zuciyarta na tafaso mata wani irin nauyi da damuwa tareda rashin nutsuwa da sukuni ko kadan sbd komai na rayuwar AZIZ LIMBA yana tafiya akan maana da tsari dan haka koma tayaya aka bayyanarda wannan kamfanin akwai babban mahimmaci da girman dayake tattare dashi gashi kamar yanda bai taba fadawa duniya maanar uLIMBAS ba sai bayan shekaru da komai ya fito duniya tasan maanarsa Wanda ita datake uwarsa ma bata saniba sai daga baya hakama wannan din haryanxu babu Wanda yasan maanarsa bakuma Wanda zai taba sani ta Sani sai bayan shekaru kila Amma dai koma menene wannan Karan hankalinta kwata kwata bai kwanta ba Musamman da maganar komawansu Nigeria ta bullo gabaki daya zuciyarta qunci da zafi takeyi sbd har abada bata kaunar AZIZ ya sake kusantar inda ma zasu iya samun labari ko ganin Wanda ma yasan ko labarin ZAADENS dan har abada bazata taba barin Jannah dawowa rayuwar AZIZ LIMBA da Falaq ba sbd babu alkhairi a rayuwar Zaadens da duk Wanda zasu ra6a dan haka zata tsaya komai zatayi zataisa dan hana ko tarihin Zaadens dawowa rayuwarsu dan hakanne ma ta tsani komawa kwata kwata Amma Falaq ta tsaya ita kuma Nigeria takeso hakanne ya saka ya yanke komawar,

Wannan dalilin ne ya saka kusanci da karfin kaunar dake tsakanin Mama da Falaq ragewa sbd a rayuwar Falaq babu inda take so take kuma son komawa tayi rayuwa irin Nigeria Wanda ko daddynta ya tambayi dalilin hakan Amma Sam babu dalilin datake basu Nigeria din kawai takeso.

A bangaren Mama itace ta bada umarnin auren AyshNicky ga AZIZ LIMBA Wanda haryanxu bai bata cikakkiyar amsa akan hakan ba duk da bai taba tsallake umarninta ba dan haka ya bar mata komai a hannunta Amma kwata kwata ba maganar auren a kusa sbd rashin bada fuskansa ga Nicky da kuma rashin bada fuskan sake zancen.

Maganar tafiyansu Nigeria ya saka Mama qin yadda da tafiyar kwata kwata sai anyi auren sbd tanason ko zai sauka Nigeria ya sauka da aurensa akansa ta yanda har abada ba gurin shigowan kowace irin mace sbd AZIZ LIMBA mijin mace daya ne babu tsari ko kadan na auren mace biyu a rayuwarsa kuma itama ta yadda da hakan.


Sayd ne ya dawo da sauri ya miqa hannu ya dauki files din ya juya ya sake ficewa Yana daga wayarsa dake ringing.

Mama da Nicky ne suka bi bayansa da kallo sbd idan har AZIZ LIMBA zai iya yiwa kaunar Ummitah kishiya ta hanyar bude sabbin companies da abubuwa da dama da sunan 4&4 to tabbas 4&4 din nata mahimmancin dake gogayya da kauna tareda girman Ummitah a rayuwarsa tinda bai taba bude komai da sunan Falaq ba ko wani abu daya shafetaba to tanason sanin maanar 4&4 komai tsanani sbd itama zuciyarta girgiza takeyi da koma menene bai kwanta mata a zuciya ba.

Falaq ma miqewa tayi daga dining din ta fice tana kwala sunan fiddausi tanason su fita kafin lokacin zuwanta da Daddynta asibiti yayi.

Binta Nicky tayi da idanuwa tanajin inama itace Ummitah ya haifi Falaq data samu dukkanin soyayya da kaunar AZIZ LIMBA yanda bata buqtaan komai a duniya hakan ma ya isheta.

Bayan ficewan Falaq ajiyan zuciya Mama ta sauke tana jin ciwo da radadin yanda kusancin Falaq ya rage daga gareta duk da suna tsananin kaunar juna na zamtowansu kaka da jika.

Daki Falaq ta isa ta dauki wayarta da mini bag ta chanel ta janyo jacket din Dior black ta saka akan kayanta ta fito fiddausi ma a shirye ta fito sanyeda doguwar rigar Egypt ta sanar da Mama.

Cikin kulawa mama tace

"Ki kula da ita sosai kinsan yanayinta kuma ki kula da hanya"

Gyada Kai fiddausi tayi tana cewa

"Inshallah amma dai Mama ya kamata ki shirya fa da mutuniyarki"

"Kyaleta bata ji ne haryanxu ta kasa sanin ta girma koyaushe shirme ne a tinaninta Wanda nasan inda aka samu matsalar lalacewan tarbiyanta dan haka kuje kawai"

Fiddausi tasan inda maganar Maman ta dosa da abinda take nufi dan haka bata sake cewa komaiba ta juya tabi bayan Falaq wadda maganar Maman ta sosa zuciyarta sbd Jannah da aka kira da wadda ta lalata tarbiyanta.

Suna ficewa itama Nicky ta zari mota tabar gidan sbd shirye shiryen tafiya datake dan a yanda takeso zata riga su LIMBAs din isa dan ta fara shigarda report dinta na aiki da zata fara acan ta gama komai sbd ta shirya bin LIMBA duk duniyar da zashi ko da aurensa akanta ko babu zata bisa har sai lokacin auren yayi.



Karfe 2 na rana motar Ferrari ta shigo LIMBAs din wadda take motar Falaq amma fiddausi ke ja har yanzu bata kai fara ja da kanta ba,

Suna parking motarsa daya fita da ita Porsche cayenne tana shigowa Sayd ke ja Yana gefensa sukai parking,

Atare suka shiga gidan hannunta na riqe dana Sayd tana masa wata gulma Yana murmushi sbd fadanta da Mama kwata kwata ya dena qarewa.

AZIZ kuwa waya yakeyi a natse dan haka kai tsaye wucewa yayi bangarensa Yana cigaba da wayar.


Karfe 4 bayan yayi sallar laasar ya fito a natse cikin black highneck Bally wears da fcap din Calvin Klein komai nasa clean a natse Yana fidda qamshinsa me sanyi da bayyanarda luxury life kawai.

Yayi lunch already dan haka Yana fitowa Falaq ma ta fito cikin black Louis Vuitton dinta masu kyau daidai jikinta suka fice tana gefensa.

Daga shi sai itane suka fita dan haka shine da kansa yake jan motar a natse Yana jin idanuwanta akansa dan haka ya juyo a natse ya kalleta kafin ya bude baki yayi magana ta rigasa da cewa

"Daddy kamun alkawarin idan na cire damuwan komai a raina na samu cikakkiyar lafiyata zaka barni na koma Nigeria dan Allah Daddy pls inason komawa"

Shiru yayi batareda ya juyo ya kalletaba yaci gaba da driving a natse.

Idanuwa ta zuba Masa tana jiran amsarsa sbd baa taba iya gane yanayin Daddyn nata dan haka batasan a wane yanayin ya sake karban zancen nata ba sbd wannan shine Karo na uku tana masa maganar komawansu Nigeria.

"Yaushe kikeson ayi tafiyan?" Shine abinda taji a bazata dan haka cikin rudewa a farin ciki tace

"Ko next week Daddy"

Juyowa yayi ahankali ya kalleta da fararen idanuwansa yayi shiru tsawon seconds kafin ya bude baki yace

"Next week familyn LIMBA zasu koma Nigeria Falaq Aziz nayi Miki wannan alkawarin inshallah"
#MAMUH
#BEST LOVE
#BEST ROMANCE
#JANNAH ZAD
#AZIZ LIMBA
#FALAQ AZIZ
#AYSH NICKY
#AMMAR ZAD

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
Mamuhgee

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss Xoxo

ADUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

09033181070
09032345899*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 10


Wasu hawayen samun abinda zuciya ke tsananin so ne suka gangaro mata tana kasa dauke idanuwanta akan Daddyn nata kawai iya bude baki tayi ta furta "thank you Daddy"

Bai juyo ya kalletaba sbd babu wata magana da zasu iya yi akan duk abinda ya shafi Nigeria da Yan cikinta bayan wannan sbd rantsuwa me karfin gaske da alkawarin dayake kansu na Maman akan babu Wanda a ahalinta zai taba sake maganar zamansu a Nigeria baya bare abinda ya faru acikinta dan hakan ne kwata kwata a LIMBAs aka shafe wannan tarihin a fili da baki.

Shiru ne kawai ya ratsa motar sbd babu me abin fada kuma har suka isa asibiti.

Dayake likitanta ne kai tsaye Wanda shine da Dr Nico tsaye a komai kanta har aikinta da akai da donor da aka ciro aka saka mata dan haka kai tsaye ciki suka wuce dan daman shi din su yake jira.

Suna shiga cikin girmamawa Yana tsaye yana waya ya kashe yana qarasowa gurin LIMBA din ya miqa masa hannu Yana masa barka da zuwa kafin ya kalli Falaq cikeda kulawa yace

"Hi Ms Falaq Aziz barka da zuwa"

Murmushi tayi tana cewa

"Thank you Doc"

Zama sukai Yana Kiran wasu nurses Guda biyu sbd Dr Nico baya nan.

Abubuwan daya kamata ayi mata na duba cikakkiyar lafiyan zuciyar dake kirjinta da bugawanta da duk sauran abubuwa kuma komai ya fito lafiya kalau babu komai a ayanzu shikenan bata buqatan sake zuwa sai taji wasu complications din.

Ajiyan zuciya cikin samun nutsuwa AZIZ ya kalli Dr Sam din yayi masa godia yana miqa masa hannu kafin suka miqe
Itama Falaq din godia Tai masa kafin suka fito ya rakosu har mota yana sake yiwa AZIZ bayanin komai akan masu ciwon.

Mota suka shiga suka bar asibitin Yana shiga tinanin ciwon da yanda yake a yanxu a zuciyarda ta shiga qunci da damuwa.

Numfashi ya sauke a boye Yana dan juyowa ya kalli Falaq dake cikin yanayi na samun nutsuwa kafin ya dauke kansa yanaci gaba da driving kirjinsa na nauyinda Yana buqtaan nasa maganin dayake kai tsawon shekara kusan biyu a yanzu.

Suna isa gida kai tsaye wucewa yayi bangarensa Yana buqtaan kebewa kawai.

Falaq tasan hakan sbd babu ranar da zasu asibiti bai shiga irin wannan halin na baya buqtaan kowa ba sbd ciwon da ake sake maimaita illolinsa ko bayan transplant indai ka shiga kunci me girma ko tashin hankali kan tashin hankali.

Ajiyan zuciya Falaq ta sauke tana bin hanyar palonsa da kallo idanuwanta na cikowa da hawaye sbd zuwa yanzu tasan Daddynta nada matsanancin ciwon depression daya kusan taba kwakwalwansa shima sedai batada yanda zata iya masa sbd a lokuta tashin ciwonsa ba hurumin shigarta bane tin ranar data ga halinda yake shiga idan ciwon ya tashi,ta shiga mafi girman shock da tashin hankali da qunci a rayuwarta sbd a iya shekaru bata taba sanin Daddynta na cikin wannan masifar ba da batada kyan gani,

Tayi kuka,tayi kuka ta kusa zarewa akan hakan har saida Papanta Sayd ya samu ya kwantar mata hankali daqyar ya kuma sanar mata komai akan shekarun rashin Ummitah a rayuwarsa da haihuwarta sune tsawon shekarun dayake cikin wannan mummunan halin batareda kowa ya Sani ba a duniya bayan shi da likitansa sai kuma JANNAH ZAD.

dago jajayen idanuwanta tayi ta kalli papan a lokacin sbd jin sunan Jannah dinta a Karo na farko a bakin wani tin bayan tsawon lokaci kuma Jannah ta San ciwon Daddynta ta zauna dashi ahakan ta tayasu rufewa batareda ko familynta ta fadawaba su da suke neman abinda zasu bata sunansa alokacin koman kankantarsa.

Kusan depression din itama ta kusa shiga sbd damuwa da baqin cikin halinda Daddynta yake rayuwa koyaushe kamar me ciwon hauka Amma ya boye musu sbd kada su shiga damuwa Amma shine Mama zata sakasa a rantsuwa da alkawarin daya qarasa lalata lafiyarsa da Sayd yayi shekaru Yana nema sbd a yanzu ciwonsa yafi baya tsananta a yanda papan ya fada shiyasa tayi alkawarin nemawa mahaifinta lafiya kota halin yaya.


Numfashi ta sauke me tsananin zafi da ciwo a alokacinda take tsaye har lokacin tana kallan kofar palonsa tana gurin tsaye P dinta yazo ya wuce ciki kai tsaye da sauri yana rufe kofar daga ciki
Wasu hawaye masu tsananin zafi suka gangaro mata ta kasa wucewa ta nufi kujeran dake saiti da kofar palonsa ta zauna ahankali tana share hawayenta ahankali ta zubawa kofan ido dukkanin jikinta na sanyi.

Tsawon lokaci me tsayin gaske kafin Sayd ya fito yabar palon batareda ya iya kallan Falaq dinba.

Ajiyan zuciya ta sauke ahankali jiki a sanyaye ta miqe tsaye ta nufi kofar palon ta miqa hannu ta bude ahankali ya shiga.

Kai tsaye bedroom dinsa zata nufa sai gashi ya bude kofar dakin a natse ya fito sanyeda jallabiya black me kyau ta kalli fuskansa ta sauke ajiyan zuciya bata ce komaiba ta kama hannunsa suka zauna a kujera ta kwantar da kanta gefen kafadansa tana bude baki ahankali ta furta

"I love you Daddy"

Lumshe idanuwansa yayi ahankali tareda bude baki daqyar yace

"Thank you for being here Falaq"

Haka ta zauna gurinsa ta tayasa zaman harya qarasa dawowa normal dinsa tukuna ta fice ta basa damar sallar magrib itama taje tayi tata.

Bai fito cin abincin dare ba dan haka babu Wanda ya gansa sai washe gari karfe goma da mintina ya fito a kame cikin navy blue Armani suit da Prada shades black a fuskansa.

A duk lokacinda Mama ta kalli AZIZ alfahari takeyi kai tsaye tareda godiyan Allah data kasance itace uwarsa sbd babu uwar da zata haifi da kamarsa bataiwa Allah godia Tai kuma alfahari da abinta ba dan haka a kowace sallarta bata dena yiwa FATIMA adduar hasken kabari ba idan kuma tana raye Allah ya bayyanar musu da ita sbd kaunarta da Fatima a jikinsu take tana fatan Allah ya hadasu a duniyar nan kafin Allah ya dauki ranta.

Falaq ma cikeda tsananin son mahaifinta tace

"Good morning Besty"

Kallanta yayi cikeda kauna yace

"Morning my precious"

Sayd hannu ya bata suka gaisa tana cewa

"Barka da fitowa our ranka ya dade"

Dariya yayi Yana matse hannunta har saida tayi Yar kara AZIZ yayi masa wani kallan daya sakasa sakinta Yana Yar dariya yace

"Dan duba maka lafiyanta nayi Sir"

Mama ce ta amsa gaisuwarsu a tare fuskanta a sake itama cikeda kaunarsu.

Fara breakfast din sukai AZIZ black lemon tea yasha da shawarma bread da akai toasting da egg.

Yana gamawa tissue ya dauka ya goge bakinsa ya dago ya kalli Mama a natse cikeda girmamawa yace

"Next week ne tafiyanku Nigeria kowa ya shirya komai zai kammala na tafiyan nan da 5days me inshallah
Idan akwai buqtaan da kowa keso Sayd zai kawo raw cash gida"

Ajiye tissue din hannunsa yayi zai miqe Mama ta ajiye spoon din hannunta fuskanta na sauyawa gabaki daya ta kira sunansa kai tsaye wanda hakan ya sakasa fasa miqewa Yana dagowa ya kalleta a natse kafin ya dauke idanuwansa cikin girmamawa.

Tsit table din yayi gashi Allah yasa Nicky bata gidan ta fita tinda safe sbd ita yaune jirginta da daddare zai daga zuwa Nigeria sbd zata rigasu isa.

Kallan Falaq Maman tayi kai tsaye tace

"Ki tashi zanyi magana da daddynki"

Dagowa Falaq tayi zata miqe tabar gurin mama ta kallesa fuskanta babu walwala ko kadan tace

"Idan harka gama yadda da amincewa akan buqatan Falaq na son komawa a duk inda tace tanaso to ka Sani ni kuma uwa a gareka wlh tallahi bazan taba binku ba zan koma kauye ne nayi zamana sbd bazai yiyu muna maida hannun agogo baya ba...

Dagowa yayi ahankali ya kalli Maman da idanuwansa da sukai ja take
ya bude baki zaiyi magana Maman ta daga masa hannu tana rage bayyanar fushinta da yanda ranta yake sake mummunan baci tace

"Har so nawa zaka biyewa duk abinda Falaq takeso?
Baka San ta girma bane tinda ta zama budurwa,
Ka yadda ka zubar da dukkanin tarin ayyuka da huldodinka tareda companies naka ka koma Nigeria sbd kawai Falaq ta fada hakan?

To idanma baka San dalilinta na son komawarba ni na sani bare kaima nasan ka Sani din dan haka tinda duka Kun gama yadda da komawar inason ka Sani daga ranar da muka sauka Nigeria wallahi tallahi duk wanda ya sake tada maganar Zaadens bare neman inda suke wlh ABDULAZIZ AYOUB LIMBA sedai ka sauya wata uwar bani ba dan har abada na cireka daga 'dana,
Ka Sani idan har zaka nema JANNAH ZAD da kanka ko saka wani nemanta ko dan kanka ko dan sbd Falaq na yafeka Ni sakina...."

Ahankali ya rufe idanuwansa da sukai wani irin jajir Yana hadiye wani irin abu daya danne kirjinsa me tsananin nauyi yana saka hannuwansa wata irin rawa me Muni Amma ya kanne ya jima shiru kafin ya bude idanuwansa Jan su na qaruwa ya bude baki ahankali cikin kamewa batareda yanayinsa ko daya ya bayyana ba anatse yace

"Allah ya huci zuciyarki Mama har abada babu Wanda zai iya taka umarninki a nan gidan"

Falaq dake tsaye bata qarasa fita ba tana jin hakan wasu zafafan hawaye masu tsananin zafi da ciwo suka gangaro mata tana dafe kirjinta sbd take wani radadi taji Yana gauraye kirjinta ta daddafa tabar gurin zuwa dakinta tana son fasa kuka Amma radadin wannan danyan hukuncin na mama data daure Daddy dashi yafi karfin kuka sbd zai yadda ya mutu da radadin rashin abinda zuciyarsa ke tsananin haukar so akan ya take umarnin Mam dan haka taji ciwon kirjinta na qaruwa ta rufe dakinta dan itama ta xabi ta mutun ma da ciwon ta huta da ganin halinda Daddynta zai shiga sbd girman wannan alkawarin.


Sayd ma wani irin zufa ne me tsananin gaske ya feso masa sbd tsananin tashin hankali da shock din maganar Maman Wadda ta gama kashe AZIZ dinne da kanta dan har abada kuma ta rasasa sbd bazai taba komawa AZIZ LIMBA dinta ba.

Miqewa AZIZ din yayi yai mata sai anjima ya fice Sayd na miqewa zufa na sake jiqasa yabi bayansa.

Kai tsaye mota ya nufa Sayd yayi saurin bude masa ya shiga ya rufe masa ya zagaya ya bude motar ya shiga ya tayar suka bar gidan.

Sanin waye AZIZ din har suka kai office baice komaiba motar tsit take.

Parking yayi ahankali ya bude ya fice yabarsa a motar ya tsaya daga waje tsawon mintina masu dan tsayi kafin AZIZ din ya bude ya fito bayan ya hadiye dukkanin emotions nasa.

Kai tsaye ciki suka nufa maaikata tako ina suna fitowa gaidasa yana amsawa da kai ko hannu kawai sbd fuskansa dake a kame ba fuska ko kadan.
#MAMUH
#BEST LOVE STORY
#HOT ROMANCE
#JANNAH ZAD LIMBA
#AZIZ LIMBA
#ZAADENS
#LIMBAS


ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
Mamuhgee

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss Xoxo

ADUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

09033181070
09032345899

*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 11

A lokacinda Mama tariga da tasan AZIZ zai iya komai Amma bazai taba iya take umarninta ba dan haka ayau ta samu nutsuwa da kwanciyar hankalin data rasa na tsawon shekaru akan dawowan Zaadens rayuwarsu sbd tana jin shakka da tsoron girman abinda take gani a idanuwan AZIZ gameda Jannah Zad wadda babu alkhairi shigowanta rayuwarsu hakama sbd itane akaiwa tata 'yar kisan gillar da har abada bazata iya mantawa ba.

A yanzu data daure AZIZ da kalamanta, daurin da har abada tasan bazai taba kuncewaba koda Fatima zata dawo duniya kuwa bazata iya warwaresa ba sbd yanda tasan girmanta a zuciya da rayuwarsa.

Hankalinta ya kwanta zuciyarta ta samu nutsuwa da rashin fargaban sauka Nigeria ta zauna dan tasan maganar Zaadens kuma ta rufu kenan har abada tinda Allah ma ya raba duniyarsu ta tasu sbd a yanzu duk inda suke akwai nisan da babu cikewa har abada tsakaninsu.

Babu wani abu daya rage mata a rayuwar AZIZ dinta bayan aurensa da Nicky ta nunawa duniya tayi sirikar da babu gurbataccen jini a jikinta,

Zatayiwa AZIZ auren da a duk inda Zaadens suke zasu gani a labarai Susan sun jima da rufe babinsu na shafe tahirin auren yarsu a LIMBAs a yanzu 'yar da aka kashe mata tata Yar sbd gata da nuna karfin ikon dukiya ba kowa bace face bazawara a gabansu yanzu.

Gidan a ranar tsit babu wani farin ciki ko walwala damuwa ce me girman gaske a zukatansu Musamman Falaq da gabaki daya duniyarta take ganin ta juye a lokaci daya dan badan Mama itace mahaifiyar data haifi Daddynta ba data gama tsanarta ayau Amma dayake tana girmama duk abinda mahaifinta keso dan haka take hana zuciyarta tsanarta sbd daddy na kaunar mahaifiyarsa.

Mama kadai ce a gidan take farin ciki tana zuciyarta kalau sbd matsalarta da tsoronta ya kau dan haka batada sauran fargaba hankalinta kwance saima hidimarta takeyi itada Nicky da zata wuce hakama acan Nigeria tariga ta kira Sayd ta basa umarni ayau din kafin isar Nicky tini aka tanadar mata driver lafiyayye me xamanta tareda sabuwar mota fitinanniyar sabuwar mota daidai raayinta aka kuma sanar da securities da maaikatan gidan isowanta kafin su.

Saida ya sanar da AZIZ umarnin Maman Wanda ko sauraron duka zancen baya buqatan yi yace yayi duk abinda Maman tace kawai baya buqatan ji.

Karfe 7 na dare Mama da kanta ta fito ta saka Falaq binsu dole suka raka Nicky airport tareda Dr Nico Wanda yake rungume da Nicky din kwata kwata bayason rabuwa da ita sbd yasan zata saka kanta ne a motar da zata fito da dana Sani kila da damuwa sbd baisan gaba ba Amma bayajin akwai filin da kowace irin mace zata samu a zuciyar AZIZ LIMBA dan yasan komai na LIMBA ciki da waje tinda shine likitansa.

Dagewan Nicky din ya saka yabarta ta gwada koda akwai damar samun soyayyar AZIZ din tinda zai iya kaunarta ya bata dama ko dan sbd shi.

Mama ma kamar baby haka ta ringa tarairayan Nicky din tana mata fatan sauka Lfy da fadan ta kula da kanta sosai akwai isasun masu aiki da aka zuba kome takeso zasu mata.

Lafewa jikin Maman Nicky tayi tana sake nuna mata irin kewanta da zatai sbd jinta takeyi kaman mahaifiyar data haifeta sbd tsananin son datakewa 'danta ya shafeta.

Falaq Nicky din ta rungume itama tareda sakar

Please Login or Register in order to submit comment