Reading KALBIM BOOK 2 BY MAMUHGEE Chapter 12 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qwai da yayi mata cikin kai.

AZIZ LIMBA cup din hannunsa ya dire da karfi a kan dining din wanda ya saka gaban kowa faduwa tareda dagowa ya sauke idanuwansa da tin jiya basu koma daidai ba akanta.

Nicky ganin hakan da sauri tareda son nuna kokarin datai tace

"Mine na saka ayi maka wani abinda zakaci bayan tea sbd nasan bazaka ci breakfast me nauyiba"

Kallan Jannah tayi tace

"Ki ajiye a gabansa ki tafi"

Mama datake tari har lokacin cikin tsananin baqin ciki tace

"Waye ya bawa me aiki izinin shigowa muna breakfast"

Da sauri Nicky tace

"Nice na sakata ta kawowa Mine abu ne"

Zuciya Mama kejin kaman zata hadiya sbd baqin ciki ta bude baki zatai magana Nicky ta katseta da cewa

"Mama shatin meye a wuyanki?
Rataye kanki kina tashi yi ne sbd abinda ya faru jiya ko me?
Kodai mahaukciya Maman Jannah ne ta sake Miki wani abin kaman wancan Karan?
Mama kin hana a koresu last time gashinan tana neman sake illaki
Mama ki......

Wani irin baqin cikin daya taso ya rufe mama akan Nicky da babu alkhairi ko daya a duk lokacinda zata aikata abu dan haka bazata kashe ita kadai da ciwon zuciya ba sedai su mutu tare dan haka batasan lokacinda tace

"sbd JANNAH ZAD ce matar AZIZ shiyasa"

Daidai lokacin da maganar Maman ta fita daidai AZIZ din na kama hannun Jannah data juya zata bar dining din ya juyo da ita gaba dayanta.

Ita kuwa Nicky dip ta dauke wuta zaune a gurin maganar Mama tayiwa qwaqwalwanta saukar bomb din soji.

Shi kuwa budan bakinsa kalman daya furta itace

"Mimi na raye????

Sayd kuwa bakinsa a rikice yace "4&4"
#MAMUH
#ZAADENS

07019691719*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 25

*SHOP WITH ME BY RANO*
08030811300
Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.


************
Qarasa sarkewa mama tayi da jin abinda AZIZ yace ruwan datasha suna qarasa biyowa ta hanci da yi cikin kanta,

Ita kuwa Nicky maganar Maman da 4&4 din da Sayd ya ambata Yana kallan Jannah suka saka jini fara fitowa kawai ta hancinta habo me karfi na balle mata.

Fiddausi a rikice take bawa Mama ruwa tana kuma daukan tissue da sauri tana dorawa Nicky a hanci da hannunta daya..

Jannah da maganganun Nicky itama suka gama tinzira zuciyarta akan Ummanta Fizge hannunta tayi daga cikin nasa tana juyawa zata fice Nicky tayi wani irin yunquri tana daukan ruwan tea masu tsananin zafi ta watsa mata setin fuskanta Wanda kafin saukansu AZIZ din ya miqe tsaye da sauri Yana rufe fuskan jannah da tafin hannuwansa biyu yana bada bayansa ga ruwan zafin.

Falaq da sauri cikin tsananin tsoro ta miqe tana daukan tissue tafara goge bayansa hnkali tashe tana cewa

"Daddy ruwan zafi ne f sosai?
Daddy ka cire rigan da sauri"

Ko abinda Falaq din ke fada baya ji hannun Jannah din ya sake komawa ya jata kai tsaye suka bar dining din yana janta zuwa palonsa sedai ko taku hudu basuyiba ta qwace hannunta da karfi tana dakatawa tareda dagowa ta kallesa da idanuwanta da sukai ja suna bayyanarda tsanar datakewa duk Wanda yake gidan tace

"Idan umarni ne dakai ka fadamun ba buqtaan zuwa koina,
And Ni me aiki ce inada haqqina na Yar Adam kuma musulma dan haka tabani keta haddin Allah da kuma na addini na ne"

Wani irin zafi da radadin gaske zuciyarsa ke yi ya kalleta da idanuwansa da sukai jajir ya bude baki yace

"Meya samu tinani da hankalinki?
Aiki kike magana?
Ke me aiki a cikin gidana?
Are you mad or just stupid?
Wane son of a bitch dinne ya baki matsayin me aiki a gidan nan?,
Duka Zaadens suna aiki a gidana a matsayin me aiki waye da waye suka San da hakan a gidan nan?

Cikin izgilin maganar da yayi mata ba tsoro ko shakkar kowa ta juya ta kalli Mama da idanuwanta tana bude baki tace

"Wannan maganar ahali ce Ni dai a matsayina na me aiki idan har aka sake wucen iyakata ta hanyar tabani ko sake ambatar Ummana da wani sunan da ba itace ta dace dashiba masu gidan ne to tabbas zamu tafi kaman yanda ake bin dare ana biyanmu dan hakan"


Juyowa yayi ya kalli Maman Wadda gabaki daya ta qarasa rikicewa tana debewa Jannah da Nicky albarka cikin ranta...

Baki ya bude zaiyi magana Nicky ta kalli Mama cikin wani irin tsananin baqin cikin da zarewan kai har lokacin hancinta na jini tace

"Meyasa tin farko kika boyeta kina kallo bayan alkawarin da kikai har abada bazata dawo rayuwarmu ba,
Amma shine Mama kina kallo kika hana a koresu bayan dukan da mahaukaciyar mahaifiyarta tai Miki?
Menene yasa kika hana su tafiya Mama?

Cikin wata irin tsawan data saka kowannensu sake shiga mummunan tashin ya katse Nicky da cewa

"Kina shan weed ne?
Mahaifiyan Jan kike ambatarwa hauka ko me?
Daga lokacinda bakinki ya qara furta mata irin wannan kalman zakisan matsayinki bai gama cikaba a gidan nan......

"AZIZ" Mama ta kirasa da idanuwanta jajir na azabar da bata gama futa ba ta sarkewa zuciyarta na wani irin tiririn fara kare mahaifiyar Jannah da yayi maimakon ita tace

"AZIZ jin nayi kaman Kana daga matsayin Zaadens akan taka Uwar??
Menene matsalanka da duk sunan da zaa kirasu?
Inace Jannah din tsohuwar matarka ce da babu aure a tsakaninku idanma akwai wlh ban yafe yau auren ya kwana ba batareda ka saketa ba"

Dago jajayen idanuwansa yayi y sauke akan Maman yana hadiye maganar da yayi niyar fada sbd idan akwai wnda yake girmamawa da jin nauyi a duniyarsa yanzu d baida mahaifiyar data haifesa to Mama ce,

Fada mata magana a cikin ido ba dabia ko halinsa bane Amma kuma akwai abinda ko bai fadaba mutuwa ce kadai takai can.

Nicky da hawaye ke bin fuskanta jikinta koina na wata irin rawa fita tayi da gudu bta ko ganin gabanta tayi kitchen wanda ba shiri dukkaninsu suka bi bayanta Banda AZIZ din daya qi motsawa ko taku daya sbd yasan dai haukarta ko rabin tasa bataiba ita qananun likitoci take gani shikuwa manyan likitan kwakwalwa yake gani.

Mama datasan bangaren masu aiki Nickyn tayi kuma kowama zuwa zeyi dan haka ganin Fatima ayau din kila ya tabbata dan haka da gudu take bin bayan Nicky din tana kiranta tareda yimata tsinuwar da duk taxo bakinta sbd tana taba Jannah Allah ne kadai me hana AZIZ zuwa bangaren.

Cikin daga sauti Mama ke cewa

"Sisi ki tareta duk tsanani kada ki bari ta qasa bangaren Nan"

Sisi na jin hakan suka fito itada Yan aikin gidan gabaki daya.

Nicky a haukace take bata ji bata gani abu daya takeso ta kashe Jannah idan yaso ko bata auri AZIZ ba tasan dai bazai taba auren kowa ba.

Ammar ne a tsaye Yana goge motar Nicky din y hango Nicky tafe a haukace da kwalban glass cup a hannu.

Jannah dake kokarin fitowa daga bangarensu ta tinkara gadan gadan dan haka da gudun gaske ya tinkari Jannah din

Kafin ya isa Nicky ta daga kwalban da karfi zata bugawa Jannah a kirji Jannah ta kauce sedai cikin tsautsayi kwalban ya yankata sedai ba sosai ba sbd ta kauce.

Cikin mummunan tashin hankali Ammar da idanuwansa suka rufe ya zabgawa Nicky wani mahaukacin marin daya saka Mama tsallakewa da wani irin tsallen gudun gaske sbd tasan shima haukar ta motsa kenan bige bige zaayi.

Madam Sisi da daman a tsorace take itama wani mugun tsallen ta daka tana neman hanyar guduwa kafin uwar Yan haukar itama ta fito jin ihun 'yarta Wanda tasan duka gidan haukacewa zeyi tinda mahaukatan ciki sunfi masu lafiya.

Sayd da gabaki daya hankalinsa ya tashi da wannan tashin hankalin da rikicewa da gidan yayi da sauri ya nufi Ammar shi da Maheer sbd ganin yanata kifaw Nicky Mari ba kakkautawa.

Mama gabaki daya hankalinta ya rabu kashi biyu ga tsoron haukar gaske tuburan datke gani ga tashin hankalin kada Ummah ta fito.

Riqe Ammar akai har lokacin itama Nicky bataji bata gani Jannah take son illatawa..

Ammar hannuwansa na wata irin rawa ya dawo gurin Jannah dake tsaye idanuwanta jajir tana kallansa cikeda tsananin kauna da tausayin halinda yake shiga akanta ya zubawa kirjinta dake jini ta cikin doguwar rigar jikinta.

Qara ja idanuwansa ke yi ya miqa hannunsa kai tsaye zai bude rigarta ta wuya ya duba gurin
Hannunsa na isa kafin ya sauka jikinta aka riqe hannunsa cak.

Wata irin rawa hannunsa keyi Wadda ba tasa rawar hannun ce ba ta hannun daya riqe nasa hannun ne...

Gabaki dayansu tsit sukai tareda tsayawa cak sbd yanayin AZIZ din yayi munin da tsoronsu ya qaru.

Falaq kuka takeyi tin dazu tana jikin fiddausi a qanqame.

Mama kuwa rawa kafafunta suka dauka ganin AZIZ din da bata taba ganiba tin yana yaronsa kuwa.

Alluran dake hannunsa ya jefawa Sayd Yana bude baki da mummunan sautin daya saka haukar Nicky tsayawa cak yace

"A rufeta a daki bayan wannan masu daukanta na zuwa"

Dawo da kallansa yayi kan Ammar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya miqa hannunsa ya kama hannun Jannah a gaban kowa ya jata ze bar gurin Ammar ya riqesa kai tsaye jikinsa na rawa yace

"And where d hell do you think are you going wit my wife?"

Wani irin mummunan sarawa kan AZIZ yayi ya juyo da idanuwansa jikinsa na tsananta rawa ya kalli Ammar din yana hadiye wani irin masifaffen ciwo da wutar data kama kirjinsa take wanda ya sake saka dukkanin masu aikin sake ja da baya
Mama ma da bata hayyacinta idonta na kan kofar fitowan Fatima sake samun kanta tayi da tsananin shakkar AZIZ wanda a yanzu take zargin ba daidai ba.

Kasa cewa komai yayi ya juya ya kalli Sayd
Nicky da sauri cikin tsananin baqin cikin da wutar dake ci kirjinta ta kwace daga madam Sisi tana cewa

"Eh matarsa ce aurenta...... Bata qarasa ba Sayd ya someta da allurar hannunsa ya nufi Ammar yana qwala Kiran securities dan shima Ammar din dole a rufesa kafin zuwan likitocin mahaukatan.

AZIZ na juyawa Mama tayi wuf ta fada dakinsu Jannah dan dubo Fatima sbd daidai lokacin saceta ne yanzu batasan tana dakin Dad ba tareda Dad din.

Jannah kuwa cikin tsananin fushi da ciwon da kirjinta ke mata ta fizge hannunta sedai kafin tayi wani motsin ya dauketa cak dinta yabi ta kofar da shi kadai ne me bi da ita.

Daqyar ya isa Sama da ita sbd yanayinsa dayake tsananta ya sakawa dakin key tareda zarewa yayi jifa dashi da karfin gaske Yana buga bango da hannunsa cikin wani irin tsananin fushi da wutar zuciya.

Baya taja sosai tana kallansa cikin wani irin yanayin tashin hankali sbd gabaki daya ciwonsa ya wuce yanda ta Sani,
Ciwon ya qarasa nisan da abin yayi Muni.

So take ta hanasa jiwa kansa raunin sbd yanda jini ke futa a hannunsa din Amma kuma ta kasa motsawa bare isa garesa sbd zuciyarta dake cikeda tsana har lokacin.

Ganin abin yayi tsananin gaske ya sakata isa gurinsa cikin daga sauti da nata fushin tace

"Ya isa,idan kashe kanka zakayi ka me yasa zakayi hakan a gabana?
Idan ka......

Wata irin tsawa me karfin gaske ya sakar mata Yana juyowa ya kamata da hannuwansa biyu ya girgiza da karfi yace

"Da auren nawa akanki wani yake kiranki matarsa?
Ina raye igiyoyin aurena uku suna raye kika bari wani ya kiraki matarsa?
Kin shirya zarar Dani ne bayan Wanda nake fama da ita?
Kinason maidani makashi ne??

Da wani irin mahaukacin sauti da kararsa ta fice ta me hankali da gabaki daya gidan saida ya amsa jikinsa na wata irin jijjiga yace

"Wayace ya kiraki da sunan matarsa"

Wani irin mummunan firgita tayi sbd tsananin tsoron yanayinsa da kaman ita zai fara kashewan.

Tsit gidan yayi kowa na sake shiga tausayinsa sbd alamu sun fara bayyana me gidan kansa ba lafiyayye bane a tsakanin jiya zuwa yau.

Juyawa yayi sbd wani irin tafasa da wutar dake ci jikinsa da zuciyarsa dake ingizasa ga maidata macensa a yanzu da tsakiyar ranar kowama ya huta Amma kuma a yanda yake zai iya mata illar da zatai Muni dan haka ya nufi toilet baya ko gani ya sakarwa Kansa ruwa yana zubewa qasa suna sauka a jikinsa.

Daqyar ta iya daukan key din dakin ta fice da sauri itama bata ganin gabanta sbd tsananin tashin hankali da firgicin maganganunsa ta nufi daki kai tsaye dan dauko takardar sakinta ta duba.

A daidai wannan lokacin Mama ta isa dakin su Jannah din da kwalban da Nicky ta yadda bayan ta sume dan neman Ummah.
#MAMUH
#ZAADENS
#LIMBAS

07019691719


*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 26

*_SHOP WITH ME BY RANO_*
08030811300
Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.


******************
Mama da hannuwanta ke tsananin rawa idanuwanta na rufewa ga kuka tsananin tsoro da fargaban dayake cike da kirjinta sbd Sanin bame hankali ce zata dosa da makami ba hakama kusan duka ahalin ita ganin takeyi kowama a gidan mahaukaci ne,

Shakkar haukar Umman takeyi sbd taga dukan gaske takeyi gata bata gama wartsakewa daga muguwar azaban datasha a hannun Ammar ba a Daren jiyan Amma bazata bari wannan damar ta wuce taba ta dauke Fatima tabar gidan da itaba sbd matiqar tana gidan batada zaman lafiyar zuciya data kwakwalwa dan itama kila zarewan zatai kaman Su Nicky ta ari hauka ba shiri dan haka gwara ta fiddata gidan tasan yanda zatai da ita bayan barin gidan da ita.

Hannuwanta har qara rawa sukeyi ta bude dakin su Jannah din tana shigowa kai tsaye sbd Sanin babu kowa a bangaren duk suna can.

Duba dakin tahau yi da idanuwanta a zare tana qarasa shigowa da tsoronta na ficewa.

Ummah bata dakin dan haka sake riqe makamin hannunta tayi dakyau tana nufar toilet din dakin.

Da karfi ta budesa tana soko kwalban ciki da karfi tin kafin ma taga waye a ciki sedai babu kowa a ciki.

Zufa ne ya fara gangaro mata ta juyo tana sake riqe makamin da kyau ta nufi dakin Dzad tana ayyanawa a zuciyarta tana dakinsa tareda tsinewa wannan masifaffen auren da a yanzu batama fatan ya mutu so takeyi suyita son junan ta samu suqi rabuwa su dauketa suyita tafiya ko zaa barta taji da 'danta ta dawo Kansa da zuciyarsa dake neman sauka daga inda ta dorasa.

Kokarin fitowa dakin takeyi kaman daga sama Umman ta bayyana gabanta ta fito daga dakin Dzad idanuwanta jajir kuka ne da tsananin tashin da ciwonta yayi suka saka kamanninta gabaki daya sauyawa.

Mummunan faduwa gaban Mama yayi zuciyarta na neman tsinkewa da ganin mummunan yanayin Fatiman dan haka taja da baya kadan tana dago fasashiyar kwalban hannunta tana nuna Maman da ita ta bude baki zuciyarta na bushewa tace

"Fatima kece kika zabi mu zama hakan tinda tin farko kinqi yadda ki bini kika zabi makasan 'yarki,

Kika zabi Wanda suka kashe Ummitah da karfi d yaji suka cire zuciyarta suka bawa tasu Yar Wadda kike yiwa tsananin son asara,

Kin zabi maqiyiyar ABDULAZIZ dina tinda kika zabi maqiyansa akansa,

Kin zabi Wanda suka wargaza rayuwar 'dana suka illata rayuwarsa illar da bazata barsa ba har abada,

Hakanne yasa bakida wani amfanin bayyana a rayuwarsa Fatima,
Ya dade da manta ki,
Ya rufe babinki
Nice uwa kuma mahaifiyarsa da bazai taba sauyani ba har abada,

Kinsan abubuwan dana fuskanta akansa tin yarinyartarsu shida Ummitah har zuwa yanzu?

Tayaya zaki dawo a lokacinda bazan iya baki shi ba,
Bazan taba iya rasa AZIZ LIMBA a matsayin Dana ni kadai ba,

JANNAH itace masifar gabaki daya rayuwar AZIZ Dina dan haka saina tabbatarda dga ke har ita babu Wanda har abada zai iya shiga tsakanina da.....

Kaman a mafarki taji anyi sama da ita an rafkawa tiles din gurin wnada ya daka idanuwanta da kanta juyewa tana kasa gane a mace take ko raye sbd azabar da tinda Allah ya halicceta tin haihuwa bata taba jinta ba irin yau.

Sake shaqurota Ummah tayi ta daga jikin bango ta sake bugata da qasa wanda ya saka wani rikitaccen ihun neman agaji fitowa bakinta jikinta na tsananin rawa sbd dukan rabata da duniya Ummah takeyi idanuwanta a rufe cikin rashin hankali da haukarta daya tashi tuburan sbd sunan ABDULAZIZ da Ummitah dayaketa juya kanta Yana sake haukatar da kwakwalwanta sbd tabbas sunayen sunzo mata a daidai sune sunayen dake mata yawo akai koyaushe ciwonta ya tashi.

Mama balain dataji Yana neman rabata da duniya ya sakata bude baki tana ihu ba shiri sbd hadiye azabar takeyi da farko tana hana kanta ihu sbd kada azo a samesu zancen yaje gaban AZIZ.

Jin Ummah zata rabata da sassan jikinta da duniyar ma gabaki daya ba shiri ta fara ihun neman ceto.

Koda Dzad dake toilet ya juyo ihun da sauri y fito
Ya duba dakin bega Ummah daya bari tana bacci ba da sauri ya saka kayansa ya nufi kofa cikin tsananin tashin hankali.

Maheer ma da tsananin gudu ya baro Ammar dayake kokarin taimkawa ya dawo daidai a dakinsu ya fito.

Mama suka gani a hannun Ummah tayi mata wani irin jina jina dan haka da tsananin gudu sukai kansu Dad ya janye Ummah Yana qanqameta jikinsa da karfi Yana rungume kanta zuciyarsa na bugawa da karfi idanuwansa na jajir sbd ganin gabaki daya ciwonta ya qarasa rikicewa.... tsananin tausayinta ne ya saka idanuwansa tsananta ja ya kalli Maheer yace

"Ka miqata inda zasu bata taimakon gaggawa"

Daki Dad yayi da Umman ita kuma Mama cikin tsananin azaba Maheer ya fito da ita sedai ko nisa basuyiba Madam Sisi tagansu ta qaraso jikinta na wata irin rawa tana neman buga ihun jawo hankalin maigidan yaga abinda ya samu mahaifiyarsa.

Cikin tsananin azaba mama ta hanata ihu tana cewa karta sanar da kowa idanma tayi nauyi tace a stairs ta fado.

Da sauri da mamaki Madam Sisi ta bude baki zatai magana Maman ta yanke jiki ta fadi daidai suna isa palon qasa dan haka dole Madam Sisin ta fito da gudu tana neman Sayd Wanda tini yakai Nicky dakinta aka rufe.

Falaq da fiddausi ne suka fito jin hayaniyar madam Sisi suka tarar da Maman a zube qasa harda jini a fuska da jikinta.

Madam Sisi data dawo jiki na rawa tace stairs Mama ta fado.

Fiddausi na jin hakan ta qarasa gurinta da sauri hakama Falaq.

Daki akai da Maman tareda Kiran likita Falaq ta hana a sanar da daddynta sbd Yana tareda Jannah Wadda a daidai lokacin ne gidan ya dauki ihun tsawarsa data saka kowa sake yin tsit Yana magana da Jannah.

Ko da Jannah ta baro palonsa bata ganin gabanta maganganunsa ne ke neman juyar mata da kai sbd tasan har abada ta gama zama Matar AZIZ LIMBA dan haka bama zai yiyiba abinda kwakwalwansa take basa yana fada.

Zaadens da Garba da suka San abinda ya faru na dukan da Ummah taiwa Mama da kuma yanda jikinta ya rikicen fuskewa sukai kaman ba abinda ya faru basu fadaba kuma basu nuna ba,
Ummah na daki tareda Dad Yana sake kokarin ganin ta dawo daidai ko yaya ne,
Hakama Ammar Maheer sun samu ya koma daidai sedai a cikin kwakwalwansa da zuciyarsa babu sauki ko sassauci ko kadan dan kuwa a wannan Karan idan ya rasa Jannah baisan abinda zai zamaba dan gwara ya mutu yabar duniya da hakan ya faru dashi.

Ko da Jannah ta iso babu kowa duka kowa Yana dakinsa dan haka kai tsaye dakinsu ta shiga ta nufi wardrobe dinta hannuwanta na wata irin rawa idanuwanta na qafewa da rikitaccen tashin hankali sbd bata fatan ko kadan taga komai bayan rubutaccen saki na mutuwar aurenta da AZIZ LIMBA.

Kayan cikin wardrobe din tafara janyowa tana wurgi dasu tsakiyar dakin idanuwanta na sake qafewa jajir...

Bataji bata gani kayan ciki kawai take fitarwa tana jefarwa,

Acan qasan kayanta rigarda ta bayyana wadda envelope din yake nade a cikinta.

Hannuwanta dake tsananta rawa takai da sauri ta fizgo rigar tana budewa bugun zuciyarta na tsananta.

Bayyanar envelope din ya sakata jefar da rigar tana budewa da wani irin rawa da dukkanin jikinta keyi.

Kasa budewa tayi dan haka ta saka karfi ta yagasa gabaki daya..

Takardu uku ne suka zube qasa daga ciki Wanda ta zubawa idanuwa tana kafesu da wani irin kallon da takardan saman itace ta bayyanar mata da ticket ce...

Sarewa qafafunta sukai ta zube qasa da karfi tana jin dukkanin jikinta na daukan wani irin zafi da zazzabi me karfin gaske.

Kasa saka hannuwanta tayi akan takardun sbd yanda zuciyarta ke wani irin juyawa tana kamuwa da ciwo me tsananin gaske.

Daqyar ta iya miqa hannuwanta suna rawa ta dauki takardun duka ukun tana fara bude ta farko Wadda ta sakata damqe takardun da karfi tana qasara zubewa zaune qasa gabaki daya.

Sabon ticket ne aka siya da sunansa da komai na tafiya a wancan ranar da limbas suka bar qasar.

Kafe ticket din tayi da idanuwanta tana kasa kyaftawa zuciyarta na tsananta ciwo da wani irin yanayin dake saka idanuwanta fara cikowa da hawaye masu tsananin ciwo.

Ta biyun ta dago ta bude ahankali Wadda rubutunsa ne a tsare cikinta na kalmomin da basu wuce biyar ba.

"KINYI NASARA AKAN AZIZ LIMBA DA DUK ABINDA YAKE ZUCIYA DA RAYUWARSA,

FATIMA DA FATIMA SUNE RAYUWAR AZIZ LIMBA IDAN ZAN MUTU DA KAUNARSU TO ZAN MUTU NE DA SON WADDA ITACE ASALIN ZUCIYAR,

AUREN AZIZ LIMBA AKANKI MUTUWARSA CE KADAI ZATA RABA WANNAN AUREN"

Rintse idanuwanta tayi hawayen dake cikinsu masu tsananin zafi suka gangaro tana fasa wani irin kukan da babu sauti tana kasa bude takardar karshen hannuwanta na damqe takardun hannunta da karfi suna nadewa.

Kuka takeyi sosai wanda daqyar ta iya dago takardar karshen ta bude...

Address ne na gidansa da qasar dayake na ticket da aka siya mata sai a qasa da aka rubuta.

Zan jira zuwanki a duk lokacinda zuciyarki ta aminta Dani na Miki alkawarin wannan"

Rintse idanuwanta tayi tana cusa kanta cikin kafafunta kukanta na sake tsananta sbd wannan envelope Yana kokarin maidata inda rayuwa take tsawon shekaru biyu da suka wuce,

Tayaya a lokaci daya komai yake neman juyewa ya komar da ita kaddarar da bata fatan komawa?

Tayaya auren data jima da wankesa ta kakkabe a zuciya da rayuwarta zai dawo mata,

Ta gama cirewa da yafe AZIZ LIMBA a rayuwarta,
Da Ammar Zad ta shirya ta yadda fara rayiwa sbd gyara kuskurenta ta baya Amma tayaya ma zata iya kallan ahalinta data cewa aurenta da AZIZ ya rabu kuma a yanzu da suka gama karban sabuwar rayuwa da wanke komai na baya tace musu auren da dukkaninsu sukafi kaunar mutuwa dashi tace Yana Nan?

Dago jajayen idanuwanta tayi tana kallan takardun hannunta wasu hawaye suka sake gangaro mata na wani yanayin me karfi dake fitowa can qasan zuciyarta tana dannewa ta bude baki tace

"Nima ban karbi auren Nan ba bazan karbi duk wannan zancen ba har abada anrufe babin AZIZ LIMBA rayuwata dan haka babu wani sauran abinda ya rage musu bayan rabuwa da juna batareda ma kowa a ahalinsu yasan da akwai aurenba har yanzu.
#MAMUH
#ZADENS
#LIMBAS
#LOVE PSYCHOs
#CRZY LOVERS
#MAMA
#NEW LIMB*_KALBIM_*
Mamuhgee

Book 2
Chapter 27

*_SHOP WITH ME BY RANO_*
08030811300
https://chat.whatsapp.com/IexiuY21PP75lt4yoJtNsK
Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.

************
Miqewa tayi ta sake share fuskanta ta tattara takardun tareda daukan envelope din ta hada dashi ta juya ta nufi kofa ta fice idanuwanta a rufe bataji bata ganin komai bayan sabuwar takardar karshen auren AZIZ LIMBA.

Ko data iso palon qasa babu kowa sai Sayd da zai wuce da likita zuwa zamansu Mama ko kallansa bataiba shima hanya ya bata sbd ganin yanayinta Musamman da idanuwansa suka sauka akan takardun dake hannunta take ya fahimci abinda zai faru dan haka cikin sauri ya wuce da likitan sama dan ya duba mama ya gama ya fice.

Yanda take hawa stairs din idanuwanta a rife ya saka har faduwa takeyi amma bata tsaya ba sai data Isa kai tsyae kuma ta bude kofar palon ta shiga.

Baya palon dan haka bacin rai da tsananin

Please Login or Register in order to submit comment