Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dukka result d'in sai da wani gumi ya yanko mishi sakamakon ganin abin da yake damun sadeeq, tuni idanun shi sun yi ja kamar xai yi kuka hankalin shi yayi matuk'ar tashi yana tunanin ta yanda xai sanar da su wannan hargitsatsan labarin. Sam ya kasa d'aga kanshi ya kalli sadeeq da mufidah, ganin yanda ya koma yasa sadeeq yin murmishi yace "Muh'd lafia kuwa, me ke faruwa tell me please?" Cikin wani irin yanayi ya xuba wa sadeeq ido, gaba d'aya mufidah ta gama tsorata jikin ta har rawa yake, shi kuwa sadeeq cikin shi ne ya cigaba da yi mishi ciwo sosai amman sai ya daure yace "Nasan ciwo na ne yayi worst da yawa ko?" Da sauri muh'd ya d'ago kanshi ya kalle shi cikin mamakin abin da yace,lumshe ido yayi tare da cije le6en shi saboda yanda cikin shi yake mishi ciwo sai da ya d'an lafa sannan ya kamo hannun mufidah ya rik'e shi gam tare da cewa "Kiyi hak'uri my wife na rufe miki bansanar dake wani abu ba, wanda bana son tashin hankalin ki shi yasa" Kallon Dr muh'd yayi tare da jiyo wa ya cigaba da kallon mufidah wadda gaba d'aya hankalin ta Yayi masifar tashi jin abin da sadeeq yake fad'a. "Ba wani abu na rufe miki ba my wife ina da ciwon hanta tun kafin na aure ki, na kasance ina yawan fama da ciwon ciki sosai ganin hka sai na yanke shawarar xuwa ganin likita a k'asar london anan yake fad'a min ciwon hanta ne ya kama ni har sai da suka yi min aiki a can" Gaba d'aya kallon shi suke da idanun su da ya firfito na tsabar kidima, duniyar tunani mufidah ta fad'a don akwai wani lokaci da tana xaune gefen bed ya fito daga wanka d'aure da towel tana cikin shirya shi taga wani siririn yanka a gefen sam bai yi kama da operation ba a gefen cikin shi har tana tambayar shi mene wannan sai yake fad'a mata yana k'arami ne ya ta6a jin ciwo awajen. Maganar da sadeeq ya cigaba da yi ita ta dawo daga duniyar tunanin da ta fad'a ya cigaba da cewa " ban fad'a wa su mumy da daddy ba saboda kada su d'aga hankalin su su shiga damuwa balle uwa uba d'an uwana rabin jiki musaddiq bana jure ganin shi cikin damuwa shi yasa na 6oye musu, sauran kad'an musaddiq ya gane don ya kamani da magungunan sai na wayance da na aboki nane dak'yar ya yarda da hkan don har yaso dubani na nuna mishi 6acin raina shine ya hak'ura, bayan na warke na cigaba da xuwa ganin likita ina kar6ar magani daga k'arshe da naga na samu sauk'i sai na watsar da xuwa ganin likitan kwata kwata, sai k'wanan na fara jin ciwon ya dawo min amman na kasa tafia ganin doctor saboda bana so nayi nesa da mufidah" K'ara rik'o hannun mufidah yayi cikin sanyin murya ya cigaba da cewa " kiyi hak'uri my wife tashin hankalin kune bana so shi yasa ban fad'a muku ba, ki yafe min don Allah" Wani kukan tausayin sadeeq ya kamata ta fad'a jikin shi tare da sakin kuka mai ban tausayi, hak'uri da rarrashin ta sadeeq kawai yake. Dr muh'd kuwa hawaye ne kawai suke xuba a idanun shi, yanxu ta ina xai fara fad'a wa su mumy labarin nan dukka 'ya'yasu biyu Allah ya basu a duniya kowannen su Allah ya jarabce shi da babban ciwo, musaddiq ciwon xuciya sadeeq kuma ciwon hanta ciwon da ya gama cin k'arfin shi sosai ta ina xai fara, hawaye kawai yake yi yana kallon sadeeq kanshi na wani irin juyawa. Dak'yar sadeeq ya rarrashi mufidah tayi shiru amman still tana jikin shi sai faman ajiyar xuciya take sauke wa, kallon muh'd d'in sadeeq yayi ganin ya xuba mishi ido yana kallon shi ga hawayen da yake yasa shi sakin murmishi tare da cewa "Haba muh'd ae ba kuka ya kamata kayi ba, sanar da ni naje last stage koh?" Wasu hawaye masu d'umi suka fara xuba cigaba da xuba a idanun muh'd, shima sadeeq d'in dauriya kawai yake ga ciwo yana jin shi sosai ga tashin hankalin shi mufidan shi cikin damuwa. Sun dad'e a hka kafin muh'd ya bud'e bakin shi cikin rawar murya yace "I'm sorry to say babban yaya gaskia ciwon ka ya kai matakin k'arsh......" Kasa k'arasa fad'a yayi saboda kukan da ya kubce mishi, mufidah ma sai ta fashe da kuka ganin likita guda yana gurxar kuka ya had'a kai da table d'in dake gaban shi. Dafa mishi kafad'a sadeeq yayi tare da cewa " be a man haba muh'd kamar ba likita ba, ni daman jiki yana bani baxan yi tsawon rai ba don ni kadai nasan me nake ji ina rok'on Allah kafin na mutu naga d'an da mufidah xata haifa min wannan shi kad'ai ne buri na" Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd β™» EXCLUSIVE WRITER'S FORUM _this page dedicated to my lvly friend's nafisat anka dear, sardy bash dear, billy ladan dear, ina matuk'ar alfahari da ku sister's, Allah ya k'ara muku lafia, Allah ya bar xumunci ina muku fatan alkhairi a duk inda kuke_🀝❀ *PAGE 25* Haka rayuwa ta cigaba da tafia suna renon cikin su cikin kwanciyar hankali, wanda watannin shi bakwai da en kwanaki ya girma sosai, sadeeq dasu mumy suna matuk'ar ji da wannan babyn da bai xo duniya ba tukunna,ko da yaushe cikin yiwa mufidah addu'ar sauka lafia suke mata. Duk wannan abin da ake ciki ba wanda ya fad'a wa musaddiq, sam baisan mufidah tans da ciki ba, sadeeq bai fad'a mishi ba hka ma mumy saboda tana tsoron halin da d'anta xai shiga idan yaji labari shi yasa ta ja bakin ta tayi shiru duk kuwa da wayar da suke yi kusan ko dayaushe. Yau garin ya kasance cikin wani yanayi mai dad'in gaske sakamakon ruwan da aka dunga yi tun after isha'e, garin ya d'auki sanyi sosai irin wannan yanayin ne yawancin xaka samu mutane sun yi bacci da wuri, hka ta faru dasu mufidah da sadeeq su ma tun wurin 10 na dare suka kwanta bacci sun k'udundune cikin blanket saboda sanyin garin. Can wurin 2 na dare sadeeq ya tashi tare da xama saman bed yana kallon mufidah wadda take baccin ta cikin kwanciyar hankali, ido ya xuba mata yana kallon ta sam ya rasa abin da yake damun shi a cikin wad'annan kwanaki, jikin shi ya bashi akwai wani abu da xai faru but bai san kome ne ba. Kallon mufidah kawai yake tare da sanya hannun shi kan cikin ta yana shafa babyn shi, lokaci d'aya kuma wasu hawaye masu xafin gaske suka fara xuba daga idanun shi, wanda ya rasa hawayen mene, ya dad'e a hka sosai duk idanun shi sun yi ja kan shi ya d'auki wani irin ciwo, tashi yayi dak'yar ya shige bathroom alwala ya d'aura tare da fitowa praying mat ya shimfid'a ya fara nafila after ya gama sai ya fara yin addu'o'i na neman gafarar ubangiji akan ya yafe mishi xunuban shi tare da addu'ar Allah ya sauki mufidah lafia. Bai tashi daga nan ba sai da yaji kiran sallahr asuba, sai da yayi raka'atul fijir sannan ya tashi mufidah ya tafi masallaci jikin shi gaba d'aya ba k'arfi haka yake ji. Tun da ya dawo daga masallaci wani bacci ne ya d'auke shi mai dad'i, har mufidah ta kammala had'a breakfast ta gyara ko'ina tayi wanka amman bai tashi ba, xama tayi a palour tare da fad'a wa tunani tana mai mamakin yanda sadeeq ya koma. Gaba d'aya ya canja mata,na farko ya sake mata wani irin kyau da kwarjini na biyu kuma gaba d'aya yayi sanyi sosai duk da sadeeq daman akwai shi da sanyi but na yanxu yafi na da, tana yawan farka wa a bacci ta ganshi yana kallon ta ko yana shafa mata ciki, magana yanxu bata dame shi ba abinci ma baya iya ci sosai. Abin yana d'aure mata kai tare da damunta, tayi mishi tambaya ko wani abin yana damun shi sai yace ba komai, k'arshe idan ta dame shi da tambaya sai ya fara neman gafarar ta tare da sako xancen mutuwa nan sai ta fara kuka sai kuma ya hau rarrashin ta, wani lokacin kuma sai ya xuba mata ido yana kallon ta duk inda tayi akan idanun shi duk sai tabi ta tsargu. K'arar wayar ta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta fad'a, hannu tasa ta goge hawayen da suka xubo mata sannan ta dauki wayar umman tace bayan sun gaisa tare da yin hira ta tsawon mintuna 15 ne ta ajiye wayar tare da kallon agogo taga har 10:30 tayi sadeeq bai fito ba gashi kuma yau akwai aiki, tashi tayi tare da nufar bedroom d'in shi. Tura kofar tayi tare da shigo wa lokaci d'aya mufidah ta xaro ido tare da furta "sadeeq!" Da k'arfi tukunna ta k'arasa wajen da yake kwance akan bed yana murkususu kamar macen da take nakuda, cikin sauri ta hau kan bed din tare da janyo shi jikin ta tana jijjiga shi cikin kuka tana cewa "Sadeeq me yake damun ka, tashi ka fad'a min please?" Ya bud'e baki xai yi magana amman ya kasa, sai wasu hawaye masu xafi da suke xubo mishi, cikin gigice wa da firgita mufidah ta yunk'ura xata tashi don taje ta fad'a wa su mumy amman sai ya rik'e ta k'am yana yi mata wani irin kallo wanda ya tsurar da mufidah ta kusan fara nakudar tashin hankali saboda yanda taji d'an cikin ta ya wani irin juyawa lokaci d'aya marar ta ta d'auki ciwo. Cikin wata murya taji sadeeq ya bud'e baki dak'yar yace " my wife kada ki sanar dasu mumy hankalin su xai tashi, ciki na ne yake ciwo ki kira min muh'd ya duba ni" Cikin sauri jiki na rawa mufidah ta d'auki wayar shi ta lalibo number d'in muh'd sai da ta kirawo shi sau biyu bai d'auka ba sai ana ukun ya d'auka yana cewa "Sorry babban yaya ina room's d'in patients ina duba....... " Kafin ya k'arasa fad'i yaji muryar mufidah cikin kuka tana cewa " muh'd don Allah kayi sauri ka xo sadeeq bashi da lafia" Cikin tashin hankali yace " me ya same shi?" "Ni dai kayi sauri kaxo please ina tsoro" Ta k'arasa fad'i tana shashshak'ar kuka, da sauri yace " kiyi hak'uri mufidah gani nan xuwa yanxu" Yana gama fad'in hka ya katse wayar hankalin shi a tashe ya shiga mota ya taho, yayin da mufidah kuma ta cigaba da kuka sosae ganin yanda sadeeq yake shan wahala, lokaci d'aya ya fara jan wani irin numfashi da ya k'ara rud'a mufidah.............. Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd β™» E.W.F *PAGE 27* Da k'arfi mufidah ta tashi tare da fad'in "stop it sadeeq" Kafin kuma ta rushe da wani irin kuka ta xube k'asa tare da rik'e kafafun shi tana cewa "Baxa ka mutu ba sadeeq xamu rayu tare da kai har abadan, xan haifa maka yaran da kake so da yawa ka cika wa su mumy burin su na ganin jikoko da yawa xan mutu sadeeq idan ka mutu ina son ka baxan iya rayuwa ba kai ba" Kamo ta yayi tare da xaunar da ita shima idanun shi duk sun ciko da hawaye cikin muryar rarrashi sadeeq yace "Kiyi hak'uri mufidah mutuwa tana kan kowa idan lokacin ta yayi ni nasan ciwon nan bana tashi ba n....." Kafin ya k'arasa fad'i mufidah ta damk'e bakin shi cikin kuka tana girgixa kai tace "kayi shiru sadeeq don Allah na rok'e ka wadannan maganganun suna rikita ni hankali na yana tashi sosai" Cikin Murmishin yak'e yace "okay shikenan na bari my wife" Kallon shi take ko kifta idanun ta ba tayi tana ganin idan ta kifta idon ta kafin ta bud'e sadeeq ya mutu, don sai yanxu taji wani masifaffan son sadeeq yana ratsa jijiya da xuciyar jikin ta batasan tana mishi wannan son ba sai hka, shi kuwa Dr muh'd kasa k'arasa magana yayi sai ajiyar xuciyar da yake sauke wa akai akai. Suna cikin hka ciwon ciki ya dad'a tasar wa sadeeq irin yanda yake yi kamar numfashin shi xai d'auke tuni suka rud'e kuka sosai mufidah take tana rik'e dashi. Da gudu muh'd ya mik'e yaje ya kirawo wasu likitoci biyu suka d'auki sadeeq suka shigar dashi wani daki da gudu mufidah taxo xata shiga but d'ayan likitan ya rufe kofa wata nurse ce ta janye mufidah xuwa cikin office d'in Dr muh'd tana rarrashin ta don muh'd shi kasa ce mata komai yayi. Dak'yar ta nutsu ta daina kukan ta kirawo mumy tana fad'a mata cikin kuka, a matuk'ar firgice mumy ta taho asibitin bayan ta sanar da daddy shi ma. Kusan tare suka shigo asibitin da mumy da daddy office d'in Dr muh'd suka tarar da mufidah tana shar6ar kuka wiwi gaba d'aya sai suka dad'a tsurewa ganin yanda mufidah ta koma lokaci d'aya gaba d'aya ta fita daga hayyacin ta, janyo ta jikin ta mumy tayi tana rarrashin ta duk da ita ma daurewa take, daddy kuwa tagumi ya xabga shi kad'ai yasan yanda yake ji a cikin xuciyar shi. Wajen awa biyu suka yi kan sadeeq tukunna ya fara dawowa cikin hayyacin shi yana numfashi da taimako oxygen tube, special room suka kai shi tare da sanya mishi drip bacci yake saboda allurar da suka yi mishi kallo d'aya xaka yi mishi ka tausaya mishi ya yi wani irin rame wa sosai. Dak'yar muh'd ya iya yiwa su mumy bayanin halin da sadeeq yake ciki don mufida ta kasa magana, ba k'aramin rud'e wa da gigice wa suka yi ba wad'annan bayin Allah, jagwab mumy ta xube kan kujera tana kuka sosai daddy kuwa idanun shi ne suka yi ja sosai daurewa kawai yake yi saboda shine namiji mai rarrashin mumy da mufidah don kuwa Dr muh'd gudu wa yayi daga office d'in don baxai iya cigaba da kallon kayan tausayi ba don xuciyar shi xata iya buguwa. Har dare yayi sadeeq bai farka ba daddy yace mumy da mufidah su koma gida shi xai k'wana dashi da Dr muh'd, dak'yar ya shawo Kansu suka yarda, koda suka je gidan ko takan abinci basu nema ba, k'arshe mufidah a bedroom d'in mumy ta k'wana ko runtsa wa basu yi ba sallah kawai suke suna nemar wa sadeeq samun lafia, har gari ya waye babu wanda ya runtsa a cikin su, K'arfe bakwai suka yi gaggawar yin wanka simple gown suka sa kamar had'in baki mufidah da mumy suka sanya hijab ko mai basu shafa ba saboda tashin hankali. Abincin da en aiki suka yi na breakfast suka d'auka tare da tafia hospital d'in, sai ganin su daddy Yayi kawai sun shigo room, koma wa gida yayi daddy don ya samu yayi wanka shima. Kamar yanda suka barshi hka suka dawo suka ganshi ko motsi baya yi abin da xai ankarar da mutum yana da rai bugawar xuciyar shi da numfashin da yake yi ta oxygen tube. Dak'yar mumy ta lalla6a mufida ta d'an sha tea gaba d'aya bata jin dad'in bakin ta da jikin ta, bata ta6a riskar kanta a irin wannan tashin hankalin ba. Tuni ta kirawo yah Omar ta sanar mishi abin da yake faruwa, umman ta da abban ta duk ta fad'a musu, hankalin su a tashe suka taho asibitin su ma. Yini guda suka yi a asibitin umman mufidah ta taho musu da abinci na rana, har xuwa dare suka tafi sadeeq bai tashi ba, ae kuwa mufidah ta tubure baxa ta tafi anan xata k'wana dole aka kyale ta mumy da daddy suka tafi gida gaba d'aya jikin su a sanyaye....... Hka mufidah ta xauna akan kujera tana kallon sadeeq hannun yana rik'e da hannun shi wanda ba'a sa mishi drip ba, addu'a kawai take a cikin xuciyar Allah ya tashi kafad'ar mijin ta. Tsakanin jiya da yau duk mufidah ta fita a hayyacin ta, gaba d'aya ta xama wata iri ta rame saboda rashin cin abinci da samun bacci babu kwanciyar hankali a tare da ita, ga tsohon ciki yayi mata nauyi ajikin ta komai dauriya take saboda ita kad'ai tasan me take ji. Tana nan xaune ta jingina da jikin kujerar wani bacci ne ya d'auke ta mai nauyi saboda rashin samun bacci da bata yi ba jiya......... _kuyi hak'uri da wannan page d'in ban yi editing ba_ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd β™» EXCLUSIVE WRITER'S FORUM _this page dedicated to_ *my cwt sadeey S Adam* _( saNaz), ina matuk'ar alfahari da ke a koda yaushe, baki na baxai iya fad'in irin tarin karamcin ki a waje na ba nasan ke mai kaunata ce da gaskia, nima ki sani ina k'aunar ki wanda baki ba xai iya furta wa, ina rok'on Allah ya baki miji na gari wanda xai rik'e mana ke amana, ina miki fatan alkhairi a duk ina kike masoyiya ta ta hak'ik'a_😍 *PAGE 28* Sai gabannin asuba sadeeq ya farka lokacin da ya bud'e idanun shi akan mufidah ya sauke su, bacci take amman da ganin baccin kasan bana jin dad'i ba ne. Hannun yake k'okarin cire wa daga na mufidah don ya cire oxygen tube d'in da yake hancin, motsin da yake yi ne da hannun shi ya farkar da mufidah daga baccin da take da sauri ta matso kusa dashi tare da cewa " Sadeeq sannu ka farka, ya kake jin jikin naka, bari na kirawo muh'd?" Gaba d'aya ta rud'e tama rasa me xata ce mishi, shi kuwa kallon ta yake wasu hawayen tausayin mufidah ne yake xubo mishi, jikin ta na rawa ta d'auki waya har wayar tana sullu6e wa daga hannun ta saboda yanda jikin ta yake rawa. Dr muh'd ta kirawo cikin rawar murya take maganar tana cewa " mu....muh'd ya.....ya farka sa....sadeeq yanxu" Bai ce komai ba ya kashe wayar tare da fitowa daga office d'in da gudu ya nufi room d'in da yake yana cikin hospital d'in. Da sauri ya tura kofar room d'in nan ya k'araso kusa da gadon da sadeeq yake kwance " Alhmdullilah babban yaya sannu" Cewar sadeeq kenan nan ya cire mishi drip da oxygen tube d'in tare da k'ara duba shi, tukunna ya jiyo ya kalli mufidah yace " yanxu ki taimaka mishi yayi wanka ya d'an ci wani abin" Gid'a kai mufidah tayi tare da taimaka wa sadeeq ya tashi xaune, shi kuwa muh'd fita yayi daga room d'in, sai da ta shiga toilet ta had'a mishi ruwa tukunna ta fito ta rik'e shi suka shiga toilet d'in, wanka yayi tare da yin brush da alwala suka fito daga toilet d'in. Nan ta shirya shi cikin kaya marasa nauyi sannan a nutse ya tashi ya fara rama sallolin da ake bin shi, bayan ya idar ne ya xauna kan abin sallahr ya jingina bayan shi da gadon idanun shi a lumshe, tea mufidah ta had'a mishi cikin cup ta bashi dak'yar yasha rabin cup d'in yace mata ya K'oshi nan ta fara lalla6a shi da yasha amman k'arshe sai ya janyo ta jikin shi yana bata ragowar tea d'in yana cewa " kema naga alama bakya son bawa baby na abinci xamu 6ata fah nayi miki hukunci da k'in yi miki magana na tsawon second 3" Dariya ya bata saboda yanda yayi maganar amman sai ta murmursa kawai, shima murmishin yayi daman abin da yake son gani kenan akan fuskar ta. " ayi min afuwa idan kayi min wannan hukuncin ae kuka xan tayi maka har sai ka hak'ura ka janye" Hannun shi yasa yaja tsinin hancin ta tare da cewa " na fad'a ne kawai my wife baxan iya fushi dake ba ina son ki da yawa amman nasan xan tafi na barki" Hannun ta ya kamo tare da cigaba da cewa " ki yafe min mufidah idan na 6ata miki rai a xaman mu kuma ga amanar baby na nan ki kula dashi ina son ki bashi irin tarbiyyar da su umma suka baki nasan baxan yi nadamar kasancewar shi a hannun ki ba, mace ko namiji duk wanda Allah ya bamu don ina godia ga Allah da ya bani ke matsayin mata ta, mufidah ina son kiyi min alkawari idan na mutu xaki au........" Bai kai ga k'arasa fad'in abin da yake so ya fad'a ba mufidah tasa hannun ta ta toshe mishi bakin shi tana kuka sosai cikin muryar kuka tana cewa "Bana son wad'annan maganganun sadeeq suna d'aga min hankali, ae cuta ba mutuwa bace ni nasan xaka samu sauk'i insha Allah mu rayu tare da ke" Kukan da take yi ne ya tashin hankalin sadeeq sosai tuni ya fara rarrashin ta har ya samu tayi shiru dak'yar, hannun shi yasa saman cikin ta yana ta6awa yana mai addu'a Allah ya sa kafin ya mutu yaga babyn shi. Xuba mishi ido mufidah tayi tana kallon shi ko kiftawa bata yi shima hka ya xuba mata nashi idanun suna kallon junan su sosai a cikin sanyin murya mufidah ta bud'e bakin ta tace " I luv u sadeeq with all my heart hak'ik'a halayen ka suna birge ni Allah yasa d'an da xamu haifa ya debo halin ka" Murmursa wa yayi tare da cewa " luv u too my wife, nasan ma insha Allah d'an da xamu haifa mai nutsuwa ne ina son ki mata ta" Rungume junan su suka yi irin sosai d'in nan kamar wanda xa'a raba su da junan su, sadeeq yana son k'arasa mata maganar shi ta d'axu but yana jin tsoron kada tayi mishi kuka don sam baya k'aunar ganin kukan mufidah......... Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: [9/19, 12:28 PM] Aishat A Muh'd ✍🏻: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd β™»EXCLUSIVE WRITER'S FORUM _Naga comment's d'in ku fan's kowanne da irin ra'ayin shi da ya bayar kuma naji dad'in hkan sosai Allah ya bani ikon kammala muku shi lafia_ #ana tare❀ *PAGE 29* Suna cikin hka har gari ya k'arasa waye wa, wajen 7 na safe mumy da daddy suka shigo hospital d'in nan dak'yar suka lalla6a shi ya sake cin wani abin, tukunna suka fito daga d'akin Dr muh'd da sauran doctor's biyu suna tare dashi suka shiga room d'in da sadeeq yake, bayan en mintuna kuma suka shige dashi wani room na daban, koma wa room d'in da aka kwantar da sadeeq suka yi dukkanin su xuciyoyin su d'auke da damuwa. Daddy ne ya fara magana da cewa " bana son musaddiq yasan da labarin rashin lafiyar sadeeq shi yasa sam ban fad'a wa en uwana ba saboda bana son xancen yaji kunnen shi" Cikin muryar kuka mumy tace " ya Allah na rok'e ka kasa ba wanda xai fad'a wa musaddiq halin da d'an uwan shi yake ciki ba don nasan idan yaji shikenan xan rasa su gaba d'aya, ya Allah na rok'e ka ka bawa yara na lafia kada ka d'auke min su gaba d'aya" Da sauri daddy ya matso kusa da ita tare da rufe mata baki yana cewa " haba mumy kada kiyi sa6o mana ki kasance mai tawwakkali mana, Allahn da ya d'ora musu larurar yana sane dasu ya jarabce su da hkan don gwada imanin su da namu don hka ina son kiyi hak'uri, kuma insha Allah xan toshe duk wata hanya da xai sa musaddiq yaji labari, ki dunga hak'uri kina tausar mufidah kalli ki ga halin da take ciki yanxu ga tsohon ciki" Sai lokacin ta tuna da mufidah a d'akin kallon inda take tayi, ganin ta tayi tana shar6ar kuka sosai tana dafe da cikin ta wani irin tsoro ya d'arsu a xuciyar mumy kada kuma ta janyo su yi asarar cikin da yake jikin ta da sauri ta tashi ta nufi inda take suka hau rarrashin ta ita da daddy har tayi shiru amman xuciyar ta fal tashin hankali. Suna xaune a hka har aka shigo da sadeeq cikin room d'in aka kwantar dashi kafin sauran doctor's d'in su tafi muh'd kuma ya tsaya yana son yiwa su daddy bayanin abin da ake ciki amman yana fargabar halin da mufidah da mumy xasu shigo dole yaja hannun daddy suka fita daga room din xuwa office d'in shi. Sun kai wajen mintuna talatin acikin office d'in kafin daddy ya fito kallo d'aya xaka yiwa daddy kasan ba k'aramin tashin hankali yake ciki ba idanun shi sun yi ja, hka Dr muh'd da yake bin shi a baya

Chapter 9 of 23