Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tare da fahimtar da mutune mene aure ta hanyar koyar wa addinin islam da kuma abubuwan da ya kamata mace tana yiwa mijin ta ta 6angaren ladabi,biyayya,tsabta, kula da miji da yara tare da yanda xaki na yiwa yaran ki tarbiyya mai kyau, sosai malaman sun yi matuk'ar kokari wajen fadakar da matan da suka hallaci walimar,ae kuwa ba k'aramin k'aruwa mutane suka yi ba kuma sunsha addu'o'i a baku nan mutane saboda yanda suka fadakar, anci ansha sosai abin gwanin birge wa saboda yanda ake gudanar da walimar cikin nutsuwa sai gaf da mangarib aka tashi suka dawo gida. ******* Xaune yake acikin office d'in shi a hospital ya d'ora kanshi kan table tare da dafe kanshi da dukka hannun shi ya xurfafa a tunani sosai, idan lissafin shi dai dai ne gobe ne mufidah xata xama mallakin wani bashi ba xa kuma a aura mishi wata macen ba mufidahn shi ba. A hankali wasu hawaye masu xafin gaske suka fito daga idanun shi kanshi ne dake mishi tsananin ciwo yasa hannun shi ya dafe kan ji yake kamar xai cire saboda tsabar ciwon da yake mishi dakyar yake iya d'aga kan idanun shi a kumbure gashi sunyi ja sosai, idan ka kalli yanda musaddiq ya koma xaka tausaya mishi ba kad'an ba,abin da yasa yaxo hospital saboda a duba mishi xuciyar shi don yana jin ta ba dai dai ba. Mik'e wa yayi tsaye da niyyar xuwa wajen frige ya dauko ruwa yasha saboda yanda bakin shi da mak'ogaran shi suka bushe, sai dai ko taku uku bai yi ba yaji wata juwa ta kamashi a hankali ya fara layi kamar wadda yasha wine ko wani abin lokaci d'aya ya fara ganin wani duhu yana xiyartar shi idanun shi kafin ya ankara tuni yaji ya fara yin baya xai xube k'asa. Sai gashi an turo kofar office d'in an shigo Dr John ne ya shigo wanda shine kwararran likitan xuciya shine wanda musaddiq yaxo wurin shi, cikin sauri Dr John ya k'arasa wajen musaddiq ya rik'o shi yana cewa "Dr musaddiq what's happened?" Xaunar dashi yayi tare da kallon shi ya sake cewa "are u okay musaddiq?" Duk yabi ya wani rud'u sosai . Ajiyar wani numfashi yayi mai k'arfin gaske tare godewa Allah acikin xuciyar shi da yasa bai fad'i ba kafin kuma ya bud'e baki dakyar yace " I'm okay john, thank u for save me" D'an girgixa kai yayi tare da cewa " no thank me, thank god da ya kawo ni baka fad'i ba" Nan musaddiq yayi mishi bayanin abin da yake ji ae kuwa nan suka fita daga office d'in tare da tafiya d'akin da aka ware don yin gwaje gwaje na fannin xuciya,akan wani gado musaddiq ya hau tukunna Dr John ya sanya wasu nau'ora domin ganin yanda xuciyar shi take tare da sanya mishi wasu asaman kirjin shi, musaddiq dai kallon shi kawai yake don shi kad'ai yasan me yake ji. Bayan Dr John duk ya gama wasu binciken shi ne ya xauna tare da kallon musaddiq cikin tsananin tausayin shi yace "Musaddiq why da baka jin shawarar da nake baka kana yawan sa damuwa acikin xuciyar ka, me kake hka da har yake kokarin kashe ka?" D'an murmishin yak'e musaddiq yayi tare da cewa " uhm John wanne stage kuma yanxu nake?" "Abin naka yana neman xama worst fah musaddiq kana son jefa rayuwar ka cikin hatsari, ka bani number d'in parents naka na kirawo su don su kad'ai xan fad'a wa binciken da nayi" Girgixa kai musaddiq yayi tare da yunk'urin mik'e wa xaune da sauri Dr John yasa hannu ya mayar dashi kwancen sannan yace "Relax musaddiq kwanciya xaka yi xan yi maka allurar bacci but xan rik'e ka a hospital tukunna" Yana gama fad'in hka yayi mishi allurar toh shima musaddiq bai yi yunk'urin hanashi ba CO's yana son ya bawa xuciyar shi hutu daga tunanin mufidah, bai wani dad'e sosai ba bacci ya dauke shi a wurin ganin hka yasa Dr John fita a room d'in cikin xuciyar shi tunani fal na me musaddiq ya sanya cikin xuciyar shi hka lallai wannan abin ba k'aramin abu mai mahimmanci ne. ******** Daren ranar mufidah sam bacci duk iya satar shi bai yi nasarar sace ta ba, kwana tayi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara kuka sosai tayi shi don ita sam ba son Dr muh'd take ba just mutunci ne a tsakanin su hka take kallon alak'ar tasu ashe shi da wata manufa cikin xuciyar shi da tasani da bata bashi fuskar da xai yi tunanin auren ta ba, cikin daren ta dage da kai kukan ta gun mai dukka domin ya yaye mata matsalar ta. Washe gari da safe wajen 9 mumy ta shigo bedroom d'in mufidah hannun ta rik'e da breakfast d'in ta, taci gayun ta cikin wata shadda brown dinkin senegal tayi matuk'ar yin kyau,cikin fara'a ta k'arasa wajen center table ta ajiye abin hanjunta tukunna ta k'arasa wajen mufidah wadda tun lokacin da mumy ta shigo da suka had'a ido ta sunkuyar da kanta k'asa. Dafa kafad'ar ta mumy tayi tare da cewa " mufidah ga breakfast d'in ki nan idan kin ga kiyi wanka yanxu mai make up xata k'araso xata yi miki kwalliya, don Allah ki d'an saki jikin ki ayi komai a gama lafia kada mutane su fahimci halin da ake ciki, anjima kad'an xaki samu abokiyar hira matar musaddiq xa'a kawo ta nan kafin tafia dinner kin ji" Dummmm gaban mufidah ya fad'i sosai jin an ambaci matar musaddiq lokaci d'aya yanayin ta ya canja har mumy taso fuskantar wani abun a tattare da ita,ganin tayi shiru yasa mumy tace "Lafia mufidah kuwa?" D'an murmishin yak'e ta k'ak'alo tare da cewa "naji mumy kuma xan yi abin da kika ce insha Allah" Murmishin jin dad'i mumy tayi tare da cewa " yawwa 'yata naji dad'in abin da kika ce Allah yayi miki albarka " "Ameeen " Cewar mufidah tana kokarin tashi ganin hka yasa mumy fita daga d'akin, tana fita mufidah ta xube kan bed tare da dafe kanta tana mai cewa "Yah ilahi mai yake damu na daga ambatar sunan matar wani na shiga damuwa Ohhhh Yah Allah help me kada abin da naji ya kasan ce hka" Tana gama fad'in hka ta wuce toilet cikin sanyin jiki wanka tayi tare da yin brush tukunna ta fito shafa mai tayi tare da xura wasu kaya da taga ni saman bed daganin kayan tasan nata ne mumy ta ajiye mata . Tana cikin busar da gashin kanta da hand dryer mumy ta shigo da mai kwalliyar Masha Allah abin da mumy ta furta ganin yanda kayan suka yi matuk'ar yi mata kyau duk da ba'a yi wata kwalliya ba, "Ga wadda xata yi miki kwalliyar nan " Gid'a kai kawai mufidah ta iya yi nan da nan mai make up ta bud'e kit d'in ta ta fara yiwa mufidah kwalliya ta nutsuwa. Bayan ta gama yi mata ne taxo ta gyara mata gashin sannan ta daura mata d'an kwali tuni tayi wani irin kyau duk kuwa da ramewar da tayi hkan bai hana fidda tsantsar kyan da tayi ba, gamawar su kenan nabilah ta shigo d'akin cikin fara'a ta fara cewa "Masha Allah kaga amarya a gidan mu......." Kafin ta k'arasa fad'in ne mufidah ta wurgo mata harara toshe bakin ta nabilah tayi don kada dariyar ta fito,xama tayi kusa da ita tare da cewa "Sorry kawata murna da farinciki ne ya ishe ni yau wlh,ki saki fuskar nan don Allah ko naji dad'in sha'anin yau" Kamar da dutse take magana hka mufidah tayi mata tsit har ta karaci surutun ta tabar d'akin tana mata dariyar keta, kwanciya mufidah tayi tana jan tsaki tare da cewa "Mtsww nabilah hayaniya ta bar ni da abin da yake damuna taxo ta sani a gaba da surutu", tana nan kwance tana tunanin da ya xame mata farilla ta dora daga inda ta tsaya sai dai na yanxu ya sha ban ban dana kullum abin da yafi tsaya mata maganar da mumy tayi mata ashe har musaddiq aure xai yi don ita bata da labarin hka sai yanxu, kuma bata alamar yaxo ba ko wace matar tashi?, mtsww tana d'an tsaki ko mene nawa aciki da xan damu. Bayan an idar da sallahr juma'a karfe 2 dai dai aka fara d'aura auren musaddiq da matar shi sannan na Dr muh'd da tashi matar akan sadaki mafi cancanta don neman albarka aure,bayan an gama d'aura auren aka wuce yin reception tasu ta maxa dukka samun sauyin yanayin auren da akayi kuwa don mutane da yawa sun yi mamakin hkan don ba hka suka karanta a invitation card ba, ango muh'd kuwa sai faman washe baki yake jin shi yake wasai yau saboda sauke alkawarin da ya dauka yayi sai lokacin hankalin shi ya kwanta sosai. ******* Cikin gala6aitar xuciya musaddiq ya kwana daren da ya xame mishi daren bakin ciki daren da ya xame mishi rabuwa da mufidah na har abada daren da ya xame mishi rabuwa da abar kaunar shi kai baxan iya takaice muku bayanin wannan daren da ya xame wa musaddiq ba don kuwa gari na waye wa mufidah xama mallakin wanin shi mallakin aminin shi abokin shi tsayawa fasalta irin abin da musaddiq yaji a wannan daren 6ata Lokaci duk da kuwa kusan Dr John akansa ya kwana gaba d'aya har ya fitar da ran musaddiq saboda aman jinin da yake yi gashi yak'i bashi damar da xai sanar da iyayen shi. Har xuwa washe garin ranar musaddiq a gala6aice yake saboda tsananin wahalar da yasha ta daren jiya, yana ankare da lokacin nigeria don mummy ta sanar mishi lokacin da xa'a d'aura auren. Lokacin da 2 dai dai tayi na lokacin nigeria sai da xuciyar musaddiq tayi wani bugu tuni hawaye suka fara tsere a fuskar shi saboda yasan a wannan lokacin mufidah ta xama ta muh'd ta har Abadan,gaskia bai ji dad'in so ba baxai d'orar da dad'in so ba sai wahalar shi yarinyar da ya kusa mutuwa ma a kanta batasan yana yi ba wannan wanne irin so ne?. K'arar shigowar message yake taji cikin wayar shi mtsww yaja tsaki yasan muh'd ne yake damunshi, ganin message's d'in sai shigowa suke yasa shi mik'a hannun shi dakyar ya dauko wayar ganin message's da yawa daga number's daban daban yasa shi mamaki sosai yana tunanin masu taya shi murnar auren shi ne sai dai message d'in da daddy ya turo mishi ne ya fara daukan hankalin shi da sauri ya bud'e ya fara karanta wa abin da ya karanta bai gasgata hkan ba ya dauka idanun shi ne suke masa gixo don hka ya sanya hannun ya murxa idanun sosai ya dad'a karanta abin da daddy ya turo mishi " _Hey! Lover boy wake up! Kada ka mutu,Allhmdllh a yanxu Allah ya nufa mufidah ta xama mallakin ka ta hanyar aura maka ita,ina taya ka murna da cikar burin ka na auren ta Allah ya sanya alkhairi ya k'ara maka lafia,don nasan cutar so ta kwantar min da jarumin d'ana_" Abin da yaga daddy ya rubuta mishi kenan,da wani irin sauri musaddiq ya tashi xaune daga kan gadon gaba d'aya ya rud'e ma ya rasa me xai yi jikin shi rawa kawai yake,dakyar ya iya bud'e message na mumy ya fara karanta wa " _Allhmdllh a yau d'ana Allah ya mallaka mishi abin da yake so, ina mai taya ka murnar auren mufidah._" Wani murmishin jin dad'i ne ya su6uce mishi wanda rabon da yayi shi har ya mance,idanun shi ne suka sauka kan message d'in muh'd ga abin da yace " _Dukka godia sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala, da yaba ni ikon cika wannan alkawarin da na dauka,aboki na nasan kaji haushi na, na 6ata maka rai saboda fad'a maka da nayi xan auri mufidah har ga Allah ni ba son ta nake ba hba musaddiq taya xan so yarinyar da kake masifar so akan ta ka kamu da mummunan ciwo, baxan xama butulu a gare ka ba aboki nayi hkan ne saboda na sama maka nutsuwa da sauk'in xuciyar ka wanda kake fama da rad'ad'in shi tsawon shekaru, kayi hak'uri ka yafe min ni masoyan ka ne mai son ka da gaskia saboda nasan na saka a matsala ta rashin lafia, a yau duk wani bakin ciki da kake ciki ya kau don mufidah a yanxu ta xama mallakin ka sauran magana sai mun had'u, ina taya ka murna da samun cikar burin ka hak'ik'a kai jarumi ne ina alfahari da kai aboki, Allah ya baka lafia, sai a tashi hka daga gadon asibiti don nasan kana kai yanxu lover boy_" _duk wanda shafin nan yayi mishi dad'i naga comment's sosai don ya nuna jin dad'in shi,ga musaddiq cikin farinciki gani cikin farinciki saboda cikar burin musaddiq, ku fah?, mufidah ma ko wane hali take ciki sai ku biyo ni next page don jin abin da xai faru_. Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM LIKE AND DROP UR COMMENT'S FB PAGE #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ *PAGE 42* Musaddiq kid'ime wa yayi gaba d'aya jikin shi ba abin da yake sai tsabar rawa ga wasu hawaye da suke xubo mishi sai dai na yau sun ban ban ta dana koyaushe don yau na farinciki ne yake xuba, ji yake kamar mafarkin da ya saba ne yake yin shi yana fatan kada ya tashi daga wannan daddad'an mafarkin,amman da ya mintsini kanshi ya tabbatar a farke ne ba mafarki ba I don't believe wai mufidah yau an aura min ita what's surprise?. Sai da yayi sujjadar shukur ya dad'e a hkan yana xuba wa Allah godia da ya cika mishi burin shi na auran mufidah ta yanda bai ta6a xato ba, kasa xama yayi sai faman safa da marwa yake gaba d'aya duk gala6aitar da jikin shi yayi da rashin k'arfin da yake ji a tattare dashi tun a jiya xuwa yau, xuwa wannan lokacin wani k'arfi ne yaxo mishi wanda xamowar mufidah matar shi a yau shi yasa shi jin garau dashi,hawayen farincikin nan har yanxu dai fita suke daga idanun shi fuskar shi dauke da murmishi. Turo kofar akayi da sauri musaddiq ya juya don ganin wane, had'a ido suka yi da Dr John wanda ya saki baki da hanci yana kallon musaddiq, murmishi ya sakarwa Dr John kafin yayi mishi alama da hannu ta wannan kallon hka fah?. Gane hkan da Dr John yayi yasa shi cewa " I don't believe wai musaddiq ne a gaba na ya samu lafia " Er dariya musaddiq yayi tare da rungume Dr John cikin tsananin farinciki yace "Friend ka taya ni murna na samu mufidah" Kallon rashin fahimta Dr John yayi mishi hkan da ya gani ne yasa shi bashi labarin abin da yake faruwa dashi, kallon shi Dr John yake cike da tsantsar mamaki tare da jinjina mishi sosai daman en nigeria suna yiwa matan su irin wannan so hka har mutum ya kamu da ciwo, nan ya taya musaddiq murna kafin kuma ya sake duba shi xai kuma rik'e shi sai xuwa nan da gobe xai sallame shi,aikuwa musaddiq ya tubure shi ya warke fah gida xai tafi. Ganin ya dage baxai kuma kwanan hospital ba yasa Dr John sallamar shi yana ta tsokanar shi murmishi kawai musaddiq yake yi ,kawai idan ya tuna yanxu mufidah ta xama tashi wani farinciki ne yake ratsa cikin xuciyar shi wanda bai ta6a jin hakan ba. Yana k'arasa wa gidan shi wanka yayi tare da shirya wa cikin white 3quater and t-shirt white mara hannu bayan ya fesa perfume's a jikin shi ya dawo parlour ya kwanta jikin kujera. Hannun shi dauke da phone d'in shi yana sake karanta message's d'in daddy,mumy and muh'd yana murmishin farinciki shi kad'ai ko yunwa baya ji a cikin shi don farincikin yau ya kosar dashi,idan ya lumshe idanun shi cute face d'in mufidah yake hango wa tare da beautiful pink lips d'in ta har da wani lashe Lip's d'in shi, Lokaci d'aya kuma wani abu ya fad'o mishi a ran shi nan take fuskar shi ta nuna tsantsar damuwa duk farincikin da yake cikin xuciyar shi ya kau a Lokaci d'aya saboda tuno d'an uwan shi yayan shi sadeeq. Ya tuna sadeeq fah ya auri mufidah har sun haifi afnan shine har yake murna da auren ta, anya kuwa xai iya xaman aure da mufidah matar da d'an uwan shi yayi xaman aure da ita na tsawon wasu en shekaru, anya yayi wa kanshi adalci da auren ta, nan wani abu ya tokare me mak'ogaro ya rasa abin da yake mishi dad'i, xai xauna da ita ko don tayi mishi renon afnan saboda yarda da yayi da tarbiyyar ta yasan afnan xata samu tarbiyya mai kyau idan yaso sai ya xa6i wata baby girl d'in ya aura don biyan buk'atar kanshi don baxa ta samu so daga wurin shi ba wannan son ya rufe shi tun daga kan mufidah, nan take yayi na'am da wannan shawarar tashi sai lokacin yaji sukuni a cikin xuciyar shi abin da ya tsaya mishi a mak'ogaron ya tafi... ********** Tana xaune a bedroom sai ga nabilah ta shigo fuskar ta dauke da tsantsar farinciki da annushuwa tana cewa "Kaga amarya a gidan Dr musaddiq nayi farinciki da wannan had'in Allah dai ya saka wa Dr muh'd da alkhairi don yayi abin da ya dace" Wata irin xabura mufidah tayi tare da mik'e tsaye har tana yin tuntu6e xata fad'i tsabar raxanar da tayi da sauri nabilah ta rik'e ta tana cewa "Hey Mr's musaddiq relax kada ki fad'i kiji ciwo a kasa cin amarci a 6ige da jinya" Kallon ta mufidah take muryar ta na rawa tace "Da gaske kike mufidah ko tsokana ta kike, don Allah kice min ba gaskiya ba ne?" Ta k'arasa fad'a hawaye na xuba a kyakykyawar fuskar ta, wani mugun tausayin ta mufidah ne ya ratsa nabilah cikin sanyin murya tace "Wlh Allah da gaske nake mufidah an d'aura auren ki memakon da muh'd sai muka ji da musaddiq abin ya bamu mamaki sosai don bamu san da hka ba" D'an dakata wa tayi tare da jan numfashi ta dafa kafad'ar mufidah da hannun ta tare da cigaba da cewa "Sai da mumy tayi kiran mu da umma tayi mana bayani, ashe lokacin da sadeeq yake daf da mutuwa ne ya barwa muh'd wasiyya akan idan ya mutu don Allah kada ki auri kowa sai musaddiq don yasan idan ya aure ki baxa ki da nasani ba kuma afnan xata tashi a hannun iyayen ta biyu wato ke da musaddiq, shine muh'd ya rasa ta yanda xai fad'a muku wannan wasiyyar ke da musaddiq don yasan baxa ku ta6a amince wa shine ya samu daddy,mumy,umma da Abba yake fad'a musu shine suka biyo ta wannan hanyar,amman muh'd shima a yau aka d'aura auren shi tare da matar shi kuma er uwar shi nafisat " Tuni mufidah ta 6arke da kukan bakinciki da takaici lallai muh'd ya raina mata hankali ashe manufar shi kenan shi yasa duk lokacin da yaga wani ya tsaya da ita xai mata magana idan suna tare taga yayi kicin kicin da fuska yana cika yana batsewa ashe da nashi dalilin, ae kuwa sam baxa ta ta6a yarda da wannan had'in ba auren k'anin mijin ta. Cikin fusata ta mik'e tsaye tare da juya bayan ta tace "Nabilah wannan auren sunan shi matacce" A firgice nabilah ta tashi tana cewa " me kike nufi mufidah? " Juyo wa tayi tana kallon nabilah tare da cewa "Ina nufin dole musaddiq ya sake ni baxan iya rayuwar aure dashi ba yana matsayin k'anin sadeeq sam baxan iya ba, idan auren suke so nayi gwara na xa6i wani da kaina na aura ko mai mata uku ne yaje matsayin ta hud'u na yarda da na xauna da musaddiq" Kallon mamaki nabilah take mata kafin tace "Kina nufin da ki xauna da musaddiq gwara ki aure mai mata uku?" "Kwarai da gaske " Mufidah ta fad'i hkan , "lallai na yarda har yanxu akwai sauran kuruciya a tattare da ke mufidah ki godewa Allah, Allah ya baki miji tamkar da dubu wanda ko aure bai ta6a yi ba kice bakya so haba mufidah" Wata harara mufidah ta watsa mata tare da jan tsaki mtsww ta xauna a gefen bed tana fashewa da kuka kuma lokaci d'aya don jin yanda wani abu ya tokare mata a mak'ogaron ta wanda ta rasa na mene, xama nabilah tayi kusa da ita tare da cewa "Kada ki manta mufidah wannan wasiyyar sadeeq ce baya duniyar nan a matsayin ki na mijin ki wanda kike matuk'ar so mutuwa ta raba tsakanin ku ya bar wasiyya baxa kiyi kok'arin cika mishi ita ba ko mai wuyar ta kuwa,wannan auren da kuka yi da musaddiq shi xai tabbatar wa da mutane Cewar ke mai kaunar sadeeq ce ta hak'ik'a tun da har kika iya cika mishi alkawarin shi kuma sadeeq xai matuk'ar alfahari da ke, ni a matsayin na kawar ki aminiyar ki ina mai baki shawarar ki tsaya kiyi tunani sosai kafin ki xartar da hukuncin da xuciyar ki take ingixa ki da kiyi" Tana gama fad'in hka ta mik'e ta fice daga bedroom d'in wani 6angaren xuciyar ta cike da tausayin mufidah wani 6angaren kuma haushin ta take ji na hukuncin da take kok'arin yankewa don tafi kowa farinciki da jin wannan auren, "Yah Allah kada ka bawa shaitan xuga mufidah ta hanyar rabuwar ta da musaddiq" ta furta hkan a cikin xuciyar ta. Mufidah kuwa kuka ta rushe dashi sosai na tausayin kanta gashi nabilah tayi fushi da ita tun da har ta iya tafiya ta barta cikin damuwa ba tare da ta tsaya ta rarrashe ta ba, ina xan sanya kaina naji dad'i dana sani tun lokacin da umma ta fara yi min maganar aure na nutsu na xa6i wani cikin wadanda suke sona na aura da tuni na huta da ganin wannan matsalar,ita ina xata iya xama da musaddiq mutumin da tun farkon haduwar su basa shiri da junan su har yanxu ta ina xasu fara shirya kansu har suyi xama na fahimta kowa yana ji da kanshi. Yini tayi a d'aki ita d'aya mumy ce ma mai xuwa duba ta, nabilah kasa jure fushi da mufidah tayi don hkan bata ta6a faruwa dasu d'in ba shi yasa ta kasa sakewa dole ta shigo d'akin tana rarrashin ta tare da yi mata nasiha, sai lokacin mufidah taji damuwar ta ta d'an ragu taji sanyi ta wani 6angaren. Har xuwa Lokacin tafia dinner yayi suka shirya suka tafi mufidah ba k'aramin kyau tayi ba baka ce ta ta6a aure ba har 'ya ba, mumy baki yak'i rufuwa yau d'an ta ya samu abin da yake so xuciyar ta taf cikin farinciki, haka sauran mutane masu xuwa taya su mumy murna da fatan alkhairi. Sai yanxu mufidah taga matar muh'd nafeesat ba laifi tana da kyau gata da fara'a da hankali sai jan mufidah take da hira ita kuwa mufidah ba bakin magana da uhm sai uhm uhm, tsananin ta da muh'd kuwa mufidah harara kawai take aika mishi sai dai yayi murmishi yana girgixa kai don yasan shi mai laifi ne wajen mufidah dole ya samu lokaci idan ta huce ya bata hak'uri, har aka tashi daga wurin dinner d'in magana ta fatar baki bata had'a mufidah da muh'd na sai harara da take aika mishi, ko lokacin da ya fara yi mata magana da sauri ta bar wajen don bata buk'atar jin komai daga wurin shi. ******* Yana kwance kan bed tun da gari ya waye ya kasa tashi daga kan bed duk jikin shi a kasalance yake jin shi,dauko wayar shi yayi yana duba wa ganin message's a what's app d'in shi yasa shi shiga domin duba wa messages d'in muh'd ya fara shiga abin da ya gani ne yasa shi furta "Ohhhh my Allah nagode maka da ka mallaka min wannan fine cute baby d'in" Ya k'arasa fad'i yana dafa xuciyar shi don jin wani sabon sonta da yake shiga cikin xuciyar, pictures d'in ta ne na wurin dinner da akayi ne muh'd ya turo mishi shine yake furta hkan da ya gani. Face d'in ta ya tsurawa ido yana kallo wani abu ne yaji yana ratsa shi tun daga kanshi har xuwa kafar shi, yakai wajen mintuna 5 yana kallon ta sai kuma lokacin yaji wani

Chapter 14 of 23