yasa umma ta rik'o ta suka xauna cikin sigar rarrashi da nasiha tace
"Haba mufidah bana son ganin ki cikin wannan yanayin ke har yanxu baki sa wa xuciyar ki hak'urin sadeeq ba ya kamata ki hak'ura kina mishi addu'a kin ji"
"Toh umma shikenan"
Ta fad'i hka muryar ta na rawa.
"Wane ya kawo ku kuma?"
Cewar umma don tana so ta bagarar da wancen xancen, d'an ta6e baki mufidan tayi tare da cewa
" Hmmm musaddiq ne daddy yace ya kawo mu"
"Okay, yasu hajia khadijahn?"
"Suna nan Qlau tace na gaida ke anjima xata shigo"
D'an shiru umma tayi ta fad'a tunani jin tayi shiru yasa mufidah d'ago kanta tace
"Umma lafia, me ya faru?"
" uhm mufidah wai so suke mu bar miki so ae sun xo da ita daddyn su sadeeq na nuna gaskiya ni ban amince ba tun da nima ba wasu 'ya'yan ne da ni ba da yawa nima ku biyu kad'ai Allah ya ba mu, yanxu kuwa da nayi tunani sai naga kema d'in ba wani dad'e wa xaki yi da wajen su ba aure xaki yi, kuma Omar da abban ku sun ce na hak'ura na bar ki saboda mutanen suna da karamci sosai"
Tun da umma ta fara magana mufidah take bin ta da kallo hankalin ta a tashe sam ita xama gidan su sadeeq bata so yanxun ma a dole take xaune saboda tana yawan tuna wa da sadeeq, kunyar mumyn ce ta hana ta dawowa gida, sannan ita ma sam bata da ra'ayin aure gaba d'aya a tsarin ta.
"Kin ga Omar ya fara yin gini acan 6angaren xasu dawo nan saboda kawai don na barki wajen su kuma yanxu na amince da hkan, ke dai ki cigaba da yi mishi biyayya ki d'auke su tamkar iyayen ki kuma ki cigaba da tsare mutuncin kan ki har xuwa lokacin da Allah xai fito miki da wani mijin na gari".
Gaba d'aya hirar ta gunduri mufidah jin yanda umma take mata xancen aure kawai sai ta silale ta gudu bedroom d'in ta, da kallo umma ta bita tun ba yanxu ba ta fuskan ci mufidah bata son ayi mata maganar aure sam, girgixa kai tayi tare da tashi ta goya Afnan a bayan ta don tayi bacci ta shige kitchen tana cigaba da ayyukan ta.
Sai yammaci bayan la'asar mufidah ta fito daga bedroom d'in xuwa Palo kallo d'aya umma tayi mata tasan tayi kuka, nan ta xauna tana cin abinci suna er hira da umma har daga k'arshe kuma suka shiga kitchen tare don shirya abincin dare.
Sai bayan wurin 8 na dare mumy taxo da sallama ta shigo palon umma da mufidah wadda take shayar da afnan suka amsa mata kafin su rufe bakin su muryar musaddiq ta doki kunnen mufidah yana sallama, fuskar nan tashi a d'aure da gani kasan dole aka yi mishi ya shigo.
Da sauri mufidah ta gyara rigar ta haushi ya kamata taya ya xai shigo musu Palo direct ba tare da an bashi ixinin shigo wa ba, sai wani hararar shi take, Afnan kuwa jin an raba ta da abincin ta yasa ta saki kuka don bata koshi ba, jikin shi har wani rawa yake jin kukan ta kafin su ankara har ya tsallake mumy ya wuce gaban mufidah ya kar6i Afnan d'ora ta a kafad'ar shi yayi yana jijjigata harara ya watsa wa mufidah kafin ya dawo ya xauna kusa da mumy yana cigaba da jijjiga Afnan.
Da kallo umma da mumy suka bishi ita kuwa mufidah bedroom ta shige tana wani cika tana batsewa, sai lokacin hankalin shi ya dawo kan umma ae kuwa kunya ta kamashi don bai xaci tana palon, sosa kai ya hau yi kafin ya iya bud'e baki ya gaida ita.
Hararar shi mumy tayi tana cewa "sai yanxu ka kula da ita kenan"
dariya umma ta d'an yi tare da cewa " ba komai hajia khadijah kukan 'yar tashi ne ya rud'a shi"
Shi dai musaddiq bai k'ara magana ba hankalin shi ya mayar kan Afnan yana yi mata wasa, suna cikin hka daddy, abba da yah Omar suka shigo nan aka gaisa tukunna aka nufi dinning table don cin abinci.
Umma da kanta ta kirawo mufidah ta fito tana wani 6ata rai don musaddiq shine a kusa da kujerar da xata xauna, sai da ta gaida su Abba, daddy da yah Omar sannan ta fara serving d'in kowa ta xuba wa kowa dai dai yanda xai ishe ka musaddiq kuwa don mugunta sai da ta cika mishi plate taf da abinci har sai da yayi tsini wanda kowa ya kalli xuba abincin kasan don dole ta xuba.
Ba wanda yayi magana sai abincin suka fara ci ita xama tayi tana cin nata hankali kwance, musaddiq kuwa bai san me ake ciki ba don danne danne yake kawai a wayar shi ba tare da ya kalli plate d'in da aka xuba mishi jellop d'in cous cous ba ya sanya hannun shi ya janyo don gaba d'aya k'amshin ya cika mishi ciki sai yaji plate d'in yayi d'an nauyi d'ago kan da xai yi yayi ido biyu da tulin uban abincin da mufidah ta xuba mishi..............
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A muh'd
♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
*PAGE 36*
Ranshi ne ya 6aci sosai ganin rainin hankalin da mufidah tayi mishi don yasan ita ce xata aikata hkan, daddy ne ya kalle shi ganin yanda yasha mur yana kallon abinci danne dariyar shi yayi tare da cewa
"Musaddiq lafia kuwa, Ka tsaya baka fara cin abincin ba?".
Girgixa kai yayi kafin kuma yace " daddy wannan abincin yayi min yawa ko rabi baxan iya ci ba fah"
Ya k'arasa fad'i yana huci, hararar mufidah yah Omar da umma suka yi aikuwa ta turo baki gaba ta wani waske kamar ba ita tayi ba, Abba ne yace
" kaci ka barshi musaddiq "
Janyo abincin yayi yana wani cin magani don kawai abincin ya yi mishi kyau a fuska gashi kamshin shi sai dukan hancin shi yake yasan idan yayi xuciya ya hak'ura da ci bai yiwa kanshi adalci ba, don hka yayi bismillah ya fara ci lumshe idanun shi yayi saboda tsabar dad'in da abincin yayi mishi, hka ya cigaba da ci amman idan ka kalle shi baxa ka gane yana jin dad'in abincin ba ko akasin hka don yanda yabi ya d'aure fuska.
Bayan sun gama ci ne nan suka fara maganar da ta kawo su, su mumy da daddy kenan babu 6ata lokaci umma da Abba suka amince da xaman mufidah a gidan nasu, saboda dad'i sai da mumy ta rungume umma nan suka yi ta godia.
Basu bar gidan ba sai wurin 10 na dare gaba d'aya lokacin jikin mufidah a sanyaye har suka k'arasa gida don ita da xa'a bi ta ra'ayin ta baxa ta xauna a gidan ba.
Hka mufidah ta cigaba xama a gidan ba inda take xuwa daga gidan su sai gidan yah Omar shima tun daga lokacin da ya kammala ginin shi ya dawo gidan da xama shikenan, gaba d'aya mufidah ta gaji da xaman wuri d'aya tun da ta gama karatun ta yanxu aiki take ra'ayin fara wa amman tana jin nauyin tunkarar su mumy da xancen tayi shiru kawai ta dage da addu'a.
Musaddiq kuwa sam baya shiga harkar mufidah ko magana ba Yayi mata idan ma tana wajen yaxo xai bar wurin sam ko kallon ta baya yi, tuni ya yanke lokacin da xai koma Australian don baxai jure xama gida d'aya da mufidah ba kwata kwata ga kewar d'an uwan shi da take damun shi don ma Dr muh'd yana debe mishi kewa, nan ya samu daddy da xancen ba 6ata lokaci daddy ya amince da hkan don yanxu ya daina takurawa musaddiq tun lokacin da yaji yana da ciwon xuciya idan ma abin bai yi mishi ba cikin rarrashi da nasiha yake mishi.
Mumy ce ma ta d'an nuna k'in amincewar ta da komawar tashi amman cikin lallami da dad'in baki yayi mata har ta amince amman da sharad'i nan da 6 month's ya dawo ya sami mata yayi aure nan ya amince da hkan kuwa.
Cikin kwanaki uku ya gama shirin shi ya d'aga xuwa k'asar Australian xuciyar shi tana cike da kewar mumyn shi, daddy, Yah sadeeq d'in shi, Dr muh'd aminin shi da kuma Afnan don tafiyar da yayi shi da agan shi ya dawo xa'a dad'e don so yake komai ya wuce a xuciyar shi ya samu kwanciyar hankali da nutsuwa.
Bayan tafiyar musaddiq da two month's daddy ya bawa mufidah office a asibitin musaddiq a matsayin medical Doctor don fannin da ta karanta kenan a skul.
Ba k'aramin farinciki mufidah tayi ba don ta gaji da xaman wuri d'aya, cikin k'ank'anin lokaci komai ya fara canja wa a wajen ta yanxu ta rage tunani sosai yawancin ma sai xata yi bacci kewar sadeeq take damun ta, Dr muh'd ma yaji dad'i sosai da aikin mufidah da ta fara kullum tare suke tafiya hka shiya ke dawo da ita gida, sosai ya sama ta ido don baya son yaga ta fara soyayya da wani don yana son cika alkawarin da yayi wa Yah sadeeq, shima kuma ya kula mufidan bata kula kowa bata da wannan ra'ayin kuma yaji dad'in hkan sosai.
Gashi an kusan kwashe shekara da rasuwar sadeeq amman muh'd bai ta6a jin ko da wasa musaddiq yayi mishi xancen mufidah ba.
Abin yana bashi mamaki har takai akwai lokacin da yayi mishi magana akan mufidah nan musaddiq ya birkice yana yiwa muh'd masifa taya ya xai aure mufidah matar da yayan shi ya aura ace shima xai aura nan ya dau fushi da muh'd sosai ya daina daukan wayar shi abin sosai ya dami muh'd don wannan karon kusan shine na farko rigimar da suka yi.
Dak'yar musaddiq ya hak'ura shima sai da muh'd d'in yaje har Australian tukunna ya hak'ura suka cigaba da mu'amalar su kamar da tun daga lokacin muh'd bai k'ara yi mishi maganar mufidah ba............
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE*🌲
*Written by*
Aishat A muh'd
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
*PAGE 37*
*AFTER 2 YEAR'S*
A cikin wad'annan shekarun abubuwa da yawa sun faru a cikin ta, mumy, daddy,mufidah da musaddiq sun fara saba wa da rashin sadeeq acikin xuciyoyin su ,sun riga da sun sawa axuciyar su wanda ya mutu baxai ta6a dawowa ba sun rabu da ganin shi har abada sai dai a picture daman hka rayuwa take cikin ta cike da kaddarori na rayuwar d'an adam .
Mumy kusan ko dayaushe cikin waya take da musaddiq tana mai tak'ura mishi ya dawo gida ya samu mata don yayi aure, amman musaddiq baya mai da hankali kan abin da mumy take fad'a mishi don shi sam baxai iya dawowa nigeria yanxu ba don baya son tunawa da abin da ya wuce acikin rayuwar shi komawar shi nigeria kuwa yana ganin mufidah hkan ba k'aramin dad'a taso mishi abin da ya shige xai yi ba, kuma ya riga da ya sanya wa xuciyar shi hakurin rashin mufidah tun lokacin da Yah sadeeq ya aure ta baya son ya dawo sai lokacin da ta samu miji tayi aure ta bar gidansu,shi yasa yake kauce wa xancen mumy duk da yana kewar iyayen nashi da muh'd tare da afnan yarinya jin ta yake tamkar sadeeq d'in shi.
Wani irin son ta yake a cikin xuciyar shi irin son nan da ko d'an da haifa ba lallai yayi mishi irin wannan son ba shi yasa kusan koyaushe cikin turo mata kayayyakin sawa da na wasa yana son ganin ta cikin farinciki sosai kulawa sosai yake bata duk da basa kusa da juna kuwa.
Afnan ta xama 'yar gata gaba da baya kowanne 6angare cikin bata kulawa ake da nuna mata soyayya sosai, afnan yarinyar akwai ta da hak'uri kamar mahaifin ta sadeeq ga fara'a.
Kamar yau rana ce ta week end mufidah bata da xuwa hospital tana kwance kan bed cikin bedroom d'in ta baccin ta take cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ,da ganin yanda take baccin kasan ba k'aramin jin dad'in shi take ba.
Afnan ce ta turo kofar bedroom d'in ta shigo tana sanye cikin wata pink gown iya gwiwar ta an gyara mata gashin ta da ribbons pink and white colour.
D'ago kanta da tayi bansan lokacin da na furta subhanallah tabarakallahu ahsanin kaliqeen saboda tsabar kama da sadeeq da tayi ,ja tayi ta tsaya ganin mufidah tana baccin ta ita da ta taxo don ta duba ta ga ta shirya su tafi gidan umma.
Wani 'yar dariya ta saki a hankali tana toshe bakin ta don kada sautin dariyar ta ya tashi mufidah tace
"Tabbb mumy ma har yanxu bacci take bata tashi ba"
Ta k'arasa fad'in hka tana yatsina fuska kad'an , nufar kan bed din tayi ta hau tare da sanya d'an yatsan ta d'aya cikin kunnen mufidah tana yin motsi dashi.
Hannun ta mufidah tasa xata sa a kunnen don jin motsin da take ji aciki, da sauri afnan ta xare d'an yatsan nata tana dariya k'asa k'asa don ganin mufidah ta gyara kwanciyar ta tare da komawa baccin ta hankali kwance.
Ganin hka yasa afnan ta kai bakin ta dai dai kunnen mufidah tace
" Mamee na wake up"
Da k'arfi ta fad'i hkan ae kuwa a firgice mufidah ta tashi sauke ajiyar numfashi don ba k'aramin tsorata tayi ba ,dariya afnan ta kwashe da ita tare da cewa
"Mamee na kin fiye tsoro nice fah"
Hararar ta mufidah tayi tare da d'aure fuska hannun ta tasa ta kama kunnen ta da d'an k'arfi tare da cewa
"Afnan how many times da xan miki magana ki daina yi min ihu a kunne idan ina bacci, kina son na dunga tashi da headache koh?"
Girgixa kai afnan tayi tana mai yin raurau da idanun ta alamar gaf take da ta rushe da kuka ta marairace fuska tace
"Sorry mamee na daina "
K'ara hararar ta mufidah tayi tana kokarin tashi da sauri afnan ta rik'o hannun mufidah sannan ta kama kunnen ta dukka biyun tace
"I'm so sorry mamee na please baxan k'ara ba"
Duk tabi ta wani damu don sam bata son ganin tayi wa mameen nata laifi tana mata fad'a, kallon ta mufidah tayi sai taji wani mugun tausayin ta batasan lokacin da ta rungume ta ba tsam a jikin ta, tana mai jin wani irin sabon sonta na k'ara shiga cikin xuciyar ta.
"Mamee kin hak'ura?"
Cewar afnan murmishi mufidah tayi tare da cewa
"Na hak'ura afnan baxan iya fushi da ke ba "
Kallon mufidah take wadda ta sauka daga kan bed tana tsaye ita kuma afnan tana kan bed din tace
"Mamee an fasa xuwa gidan umma ne?"
Hancin ta mufidah ta kamo tana d'an ja tace
"Sarkin son xuwa gidan umma xamu je bari na shirya ko?"
"Yawwa mamee na thank u "
Gaba d'aya suka sanya dariya sannan mufidah ta shige cikin toilet xuciyar ta cike da kaunar 'yar ta ta.
Cikin en mintuna tayi wankan sannan ta fito ta fara gyara jikin ta suna hirar su da afnan har ta kammala shirya was cikin wata black arabiyan gown mai adon flower's golden a jiki tayi kyau sosai da yake mufidah fara ce kalar ta kar6i fatar ta, ba wani kwalliya tayi ba daga powder sai wet lips mai k'amshin apple bayan ta fesa perfume's ne a jikin ta ta rik'e hannun afnan suka fito xuwa down stair's, d'ayan hannun nata yana rik'e da car key and phone nata .
Tun kafin su k'araso cikin palourn mumy take kallon su xuciyar ta cike da farinciki fuskar ta ma bata 6oye yanayin da take ciki ba saboda yanda take murmishi idanun ta akan su har suka karaso cikin parlour.
Gaida mumy mufidah tayi bayan sun gama gaisa wa ne ta nufi dinning area ta fara breakfast, bayan ta gama suka yiwa mumy sallama suka tafi.
A nutse take driving har suka k'araso gidan su mufidah ,tana gama parking afnan ta fita da gudu daga cikin motar ta nufi cikin gidan da kallo mufidah ta bita tana murmishi kafin ta fito tabi bayan ta.
A jikin umma d'are d'are mufidah ta hango afnan tana mata hira umma na dariya
"Wash Allah na umma nagaji "
Kallon ta umma tayi kafin tace " sai kace wadda tayi wani aikin ko tafiyar k'asa"
D'an dariya mufidah tayi kafin tace Allah umma yanxu bana samun wani hutu sai week end kullum cikin aiki nake "
Ta6e baki umma tayi tana cewa " ae ni da wannan aikin gwara kiyi aure don ni nafison hka daman can nafi k'aunar kiyi auren ki "
Tuni mufidah ta 6ata rai shi yasa wani lokacin take dad'e wa bata xo gida ba saboda kullum zancen umma tayi aure ita kuwa sam aure ya fita a kanta bata sha'awar yin shi kwata kwata tun da har ta rasa managarcin miji irin sadeeq.
Tashi tayi ta nufi bedroom d'in ta umma ta bita da kallo idan da sabo ta saba da hkan da mufidah take nuna mata sam yarinya bata kaunar kayi mata maganar aure idan tana fara'a yanxu sai ta birkice maka kamar mai jinnu.
"Umma bari naje wajen Aunty nabilah mu yi wasa da muhibbat"
Maganar da afnan tayi ta dawo da ita daga tunanin da ta fad'a,shafa kanta umma tayi tare da cewa
"Okay sai kin dawo "
Da d'an gudun ta afnan ta fita tayi side d'in su muhibbat, ganin hka yasa umma ta mik'e ta nufi bedroom d'in da mufidah ta shiga kwance ta same ta rigingine tana tunani idanun ta suna lumshe but hawaye yana fita daga idon ta.
Girgixa kai umma tayi tare da xama a gefen ta ta sanya hannu ta dafa ta ,bud'e idanun tayi a hankali tana kallon umma idanun ta sun yi ja sosai ,kallon ta umman take xuciyar ta cike da tausayin 'yar ta ta tace
"Tashi mu yi magana mufidah"
A hankali ta tashi xaune kanta a sunkuye tana wasa da 'yantsun hannun ta kallon ta umma ta sake yi kafin tace
"Kina ganin kamar na tak'ura miki da maganar aure koh?"
Girgixa kai mufidah tayi cigaba da magana umman tayi tana cewa
" ni nafison naga kin yi aure mufidah shekara wajen uku da rasuwar mijin ki ace har yanxu kin k'i bawa wad'anda suke son ki dama su fito ki xa6i wani kuyi aure?"
Shiru mufidah tayi kanta a k'asa hawaye suna fita daga idanun ta gaba d'aya xuciyar ta babu dad'i wani irin abu take ji ya tsaya mata a mak'ogaron ta yak'i tafiya bakin ta yayi mata nauyi sosai ta yanda ta kasa bud'e bakin ta don tayi magana, hankalin ta ya tashi sosai ita a yanxu wa xata kalla da sunan masoyi ta aure shi ya xama miji a gare ta?...........
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE*🌲
*Written by*
Aishat A muh'd
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
*PAGE 38*
Sauke ajiyar xuciya kawai take don gaba d'aya ta rasa ta yanda xata furta wa umma ta fahimce ta ita fa auren ne bata son yi a barta tayi renon afnan ita kadai ta ishe ta.
"Kiyi hak'uri ki fitar da sadeeq daga cikin xuciyar ki don ya tafi har abada baxai dawo ba, don hka ni dai a matsayi na na mahaifayar ki ina mai baki shawara akan yin auren ki shi yafi miki alkhairi "
Tana gama fad'in hka ta fita daga d'akin, sai a lokacin mufidah ta samu wani kuka mai k'arfi ya kubce mata ita ya xata yi yanxu, tana cikin kukan nabilah ta shigo d'akin don afnan ta fad'a mata da mameen ta suka xo, ganin mufidah tana kuka sosai yasa nabilah tace
"Subhanallah mufidah me yafaru kike kuka lafia?"
Duk wad'annan tambayoyin nabilah tayi mata su cikin damuwa tana mai dafa kafad'ar ta, kasa magana mufidah tayi sai da tayi kukan ta sosai tukunna ta shiga toilet ta wanke fuskar ta tare da fitowa.
Inda ta bar nabilah a xaune hka taxo ta tarar da ita xama tayi agefen ta tana sauke ajiyar xuciya, cikin yanayin damuwa nabilah tace
"Fad'a min abin da yake damun ki ?"
Cikin sanyin murya mufidah tace
"Nabilah na rasa ta yanda xan fahimtar da umma bana son yin aure amman ta tak'ura min sai nayi aure na rasa yanda xan yi wlh"
Ta k'arasa fad'in hka kwalla na sake xubo mata idanun ta akan nabilah don yanxu ita mafita take nema na yanda xata xame umma ta dai na yi mata maganar aure kwata kwata .
Sauke ajiyar numfashi nabilah tayi kafin tace
"Ehh gaskiyar umma kuwa nima ina bin bayan ta wlh don duk uwa ta gari tana son taga 'ya'yan ta sun raya sunnar Annabi (saw), suna da auren su hkan shi xai fi kwantar mata hankali tasamu nutsuwa"
Wani kallo mufidah take watsa wa nabilah, murmishi tayi tare da cewa
"Harare ni da kyau mufidah gaskia ce na fad'a ke kan ki sai mutane sun fi girmama ki idan suka san da auren ki nima shawara ta awajen ki kiyi aure"
"Da kyau nabilah gwara ki fad'a mata taji amman daga fad'a wa mutum gaskia ya xauna yana rusa kuka kamar wanda aka fad'a mishi mummunan labari"
Cewar umma kenan wadda ta shigo hannun ta dauke da wayar mufidah wanda take k'ara alamar kiran ta ake, mik'a mata wayar umma tayi sannan ta fita.
Kafin ta d'aga kiran ya katse don hka sai tayi kok'arin kira sai gashi an sake kira picking tayi tare da sanya wa wayar a hands free cikin sanyin murya tace
"Assalamu Alaikum"
"Waalaikissalam Dr mufidah ina kika shiga ne?"
Cewar Dr muh'd kenan,d'an murmishi yak'e mufidah tayi tare da cewa
"Ina gidan mu doctor"
Shima a nashi 6angaren murmishi mai k'ayatar wa ya saki tare da cewa
"Yau an kaiwa su umma xiyara kenan ?"
"Ehh wlh yanxun ne babu cikakken time sai week end"
Cewar mufidah tana kallon nabilah da ta xuba mata ido kamar ta samu tv,
"Hkne, ina afnan ban ji motsin ta ba?"
D'an yamutsa fuska tayi tare da cewa
" tana palour suna wasa da muhibbat "
"Okay ashafa min kanta xuwa dare xan shigo na kwana biyu ban shigo ba"
"Okay Allah ya kawo ka lafia"
"Ameeen byeee"
Yana gama fad'in ya katse wayar, d'an hararar nabilah tayi ganin yanda ta xuba mata ido kamar yau ta ta6a ganin ta a duniyar.
" wannan kallon fah na lafia ne?"
"Hmm mamaki kika bani ina kula da take taken muh'd alamar son ki yake ganin yanda yake kaffa kaffa dake"
Hararar ta mufidah tayi kafin tace "wa ya fad'a miki muh'd sona yake ?"
"Uhm alama na gani kuma insha Allah sai hashashena ya xama gaskiya, idan muh'd ya aure ki da kin more miji kamar sadeeq shima alamun shi ba ruwan shi ba kamar mutumin mu ba musaddiq"
Daure fuska mufidah ta sake yi kuma gaban ta ya fad'i jin sunan musaddiq kafin tace " hashashen ki kuwa baxai ta6a yiwuwa ki ma daina fad'a "
"Dalla can malama idan bai yiwu da muh'd ba sai a had'a da musaddiq, ni wlh nama fison ki auri musaddiq don kun fi dacewa sosai ya Allah kasa xance na ya xama gask......."
Kafin ta k'arasa fad'in gaskia mufidah ta kawo mata duka da hannun ta cikin fusata ae kuwa da sauri nabilah ta tashi tare da matsawa gefe ta cigaba da magana tana kallon irin kallon da mufidah take mata abin dariya ma yake bata
"Daga yin fatan alkhairi sai ki kawo min duka malama don kin samu ma ina....."
Tuni ta tsai da maganar da take ta fita daga d'akin da gudu ganin yanda mufidah ta tashi tana huci ae kuwa ita ma ta rufo mata baya da gudu.
Sai ganin su umma tayi da gudu sun shigo palon a tsorace umma ta tashi tana cewa
"Lafia me yafaru?"
Tuni nabilah ta shige bayan umma tana 6uya tare da cewa
"Umma daga yi mata addu'ar fatan alkhairi kawai ta biyo ni xata doke ni "
Murmishi umman tayi tare da kallon mufidah wadda take sauke numfashi da sauri da sauri tana hararar nabilah sosai ta bawa umma dariya sai dai ta danne tare da cewa
"Ke kuma daga yi miki fatan alkhairi sai ki doki mutum bayan godiya ma ya kamata kiyi mata"
"Umma kinsan abin da ce min kuwa?"
Cewar mufidah tana xum6uro baki
" a'a sai kin fad'a "
"wai wai hka tace..."
Sai kuma tayi shiru tare da yin kwafa ta shige bedroom a fusace.
Lokaci d'aya umma da nabilah suka kwashe da dariya kamar ba surukai ba tukunna nabilah take fad'a mata
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 23