kirki da karamci, Anty maijiddah ta cikin group d'in (novella's lodge) da fatyma (Mrs Omar), ina ji daku sosai gashi kuna k'aunar littafin nan sosai, Allah ya bar mu tare ina yin ku sosai, fatan alkhairi a duk inda kuke_🤝😍
*PAGE 16*
Lokaci d'aya suka furta gaban su na fad'uwa tsoron su kada ya kasance ace hasashen su ya xama gaskia, Cikin xak'uwa da son jin cigaban xancen mumy tace
"Muh'd fad'a mana wace mufidah?"
Sai lokacin Dr muh'd ya tuna kato6arar da yayi don baisan lokacin da bakin shi ya furta hkan ba, kallon mumy da daddy yayi wad'anda suka xuba mishi ido suna kallon shi kowannen su ya matsu yaji abin da muh'd xai fad'a, kauda kanshi yayi daga barin kallon su tukunna ya ce
"Am mumy, daddy yarinyar da musaddiq yake so wato mufidah tana xaune a garin katsina karatu ne ya kawo ta buk, so shine iyayen ta suka aurar da ita, gashi musaddiq yana son ta sosai, kasa cire ta yayi daga ranshi shine har ya haddasa mishi kamuwa da ciwon xuciya"
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
Daddy ya fad'a tare da dafe kanshi, yayin da mumy sai taji sam bata yarda da abin da Dr muh'd ya fad'i ba, kuma ta dauki niyyar bincika wa don ta fahimci gaskiar xancen.
Cikin wani irin yana yi daddy yace"kash da ace nasan da hka tun wuri da koda kaf dukiya ta xata k'are sai na nema wa musaddiq auren yarinyar nan"
"Sannan daddy don Allah kada a fad'a wa Yah sadeeq abin da yake damun musaddiq saboda xai iya shiga wani hali kusan makamancin abin da yake damun musaddiq"
"Kwarai kuwa muh'd maganar ka hka take,don idan sadeeq ya sani xa'a yi biyu babu, yanxu mene mafita?"
D'an satar kallon mumy Dr muh'd yayi taga kallon shi kawai take nan gaban shi ya cigaba da fad'uwa don da alama bata yarda da abin da yake cewa ba, d'an shiru suka yi na en mintuna kafin muh'd yace
"Mafita anan shine daddy ya kamata musaddiq yayi nesa da gida don yafi samun nutsuwar xuciyar shi, kuma hkan da xa'a yi xai taimaka wajen kada Yah sadeeq ya gane"
"Kamar ya ya?"
Cewar mumy, gaban Dr muh'd ne ya cigaba da fad'uwa yana tsoron kada su k'i amince wa don xaman musaddiq a gida xai iya kawo baraxana da rayuwar shi, tun da Yah sadeeq a cikin gidan nasu xai xauna kuma musaddiq da mufidah xasu na had'u wa da junan su, shine ya kawo wannan shawarar yana fatan su daddy su amince da hkan.
"Ina nufin musaddiq ya d'an yi nesa da gida, yanda xai fi samun hutu da nutsuwa a tare dashi xuwa na wani d'an lokaci, kuma naji yana cewa akwai wani course da xai yi kun ga hkan xai rage mishi tunani sosai"
"Good idea muh'd hkan xa'a yi kuwa, Allah ya tashi kafad'un shi"
"Ameeen thumma Ameeen"
Cewar mumy da Dr muh'd, nan suka xauna shiru kowannen su da tunanin da yake a cikin xuciyar shi.
Wayar daddy ce ta d'auki k'ara sauran d'auka yayi ganin sunan sadeeq ne yasa shi d'auka, daga can 6angaren sadeeq ya fara magana cikin shagwa6a yana cewa
"Daddy ina ka shiga kai da mumy da my sweet brother ne ban gan ku ba ne?"
D'an murmishin yak'e daddy yayi tare da cewa"muna nan fah, yanxu ina kake my son?"
"Ina kwance a bedroom d'ina ina huta wa, yunwa nake ji daddy gashi ban ga mumy ba"
Kallon mumy daddy yayi kafin yace"okay sadeeq yanxu mumy xata kawo maka abincin"
"Okay daddy, ina musaddiq ne rabo na da ganin shi tun da muka taho wurin d'aurin aure, ina son ganin shi daddy ina ya shiga ne, wayan shi baya shiga?"
Kallon musaddiq daddy yayi idanun shi sun ciko da hawaye, da ace sadeeq xai san halin da musaddiq yake ciki da shima xai iya shiga halin da musaddiq yake ciki, hannun shi yasa ya goge hawayen da suka xubo mishi kafin ya saita muryar shi yace
"Kada ka kasa damuwa a ran ka son, musaddiq yana tare da Dr muh'd a hospital suna wani aiki but xuwa yamma xai dawo"
Murmishi sadeeq yayi tare da cewa "okay daddy bye"
Kashe wayar daddy yayi tare da kallon Dr muh'd yace "xuwa yamma xai iya farka wa muh'd?"
"Ehhh daddy xai farka insha Allah"
Cewar muh'd kenan, juyo da kallon shi yayi kan mumy ya ce" sadeeq yana neman mu fah, yace ma yunwa yake ji ki bashi abinci, yanxu tashi xaki yi mu tafi gida ya ganmu idan yaso ni na dawo hospital d'in"
Girgixa kai mumy tayi tare da cewa "gaskia baxan iya tafia ba, sam baxan samu nutsuwa da kwanciyar hankali ba idan na tafi"
" hak'uri xaki yi mumyn sadeeq addu'a xaki na yi mishi Allah ya bashi lafia, idan kika k'i tafia sadeeq xai iya fahimtar halin da ake ciki"
Nan daddy ya lalla6a mumy dak'yar ta amince suka tafi aka bar Dr muh'd a wurin musaddiq wadda yake kwance ko motsi baya yi.
Bayan sun koma gida mumy ta had'a abinci ta kaiwa sadeeq lokacin yana kwance kan sofa suna hira da Yah Omar a waya, ganin mumy yasa shi katse wayar da yake yi, tsaf ya karanci tsantsar damuwa a fuskar iyayen nashi amman sai suka nuna mishi gajiyar hidimar biki ce ta sa yanayin su ya koma hka, daga k'arshe daddy ya koma asibiti aka bar mumy tana tare da en biki amman gaba d'ayan ta ba'a nutse take ba hankalin ta yana kan musaddiq addu'a sosai take mishi a cikin xuciyar ta lokaci xuwa lokaci tana goge hawaye a idanun ta idan ta ke6e ita d'aya.
Sai 7 na dare musaddiq ya farka lokacin daddy da Dr muh'd suna masjid basu dawo ba, bayan mintuna biyu da farkar wasu ya samu nutsuwa sai ya sanya hannu ya xare drip d'in da ake sanya mishi sannan ya tashi daga kan gadon cikin jarumta da dauriya ya fara tafia xuwa toilet don gaba ki d'aya jikin shi ba k'wari, wanka yayi da ruwa mai d'umi sannan ya d'aura alwala ya fito kayan jikin shi ya mayar tukunna ya fara rama sallolin da ake bin shi, har ya kammala rama su, xama yayi yana laximi, saitin xuciyar nayi mishi wani rad'ad'i, addu'a kawai yake idan tunanin ta ya fad'o mishi a cikin xuciyar shi don k'okarin yakice ta yake gaba d'aya a ranshi don yanxu ta xama matar d'an uwan.
Yana xaune a hka daddy da Dr muh'd suka shigo d'akin, ganin shi a xaune akan abin sallah ya basu mamaki sosai don hka da sauri suka k'arasa wajen shi suna mishi sannu, murmishi yayi tare da amsa wa, kafin kuma Dr muh'd ya sake duba shi, anan kuma suke fad'a mishi shawarar da suka yi, sosai musaddiq yaji dad'in hkan don yana so yayi nesa daga rayuwar mufidah, daga hka suka tafi gida don baya son xaman asibitin, lokacin da suka k'arasa gida a dai dai lokacin en kawo amarya motocin su suka shigo gidan.
Musaddiq bai tsaya ba ya shige part d'in daddy da wani irin mugun sauri har abin ya bawa daddy mamaki, Dr muh'd kuwa ya bi bayan musaddiq da sauri shi ma, duk abin da ya faru da musaddiq da yanda yayi duk akan idanun mumy dake saman bene tana kallon su nan xuciyar ta ta dad'a ayyana mata abubuwa, har sai da suka shige sannan mumy ta iya sakkowa down stairs don tar6ar amarya duk jikin ta a sanyaye.................
_kuyi hak'uri da wannan nayi typing ya goge sai da na sake, xuwa gobe insha Allah xaku ji ni_
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A muh'd
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
_Wannan shafin na kune *BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*, ina mik'a sak'on gaisuwa ta a gare ku, manyan writer's da k'ananun su, Allah ya k'ara had'e kan marubutan mu ya kauda fitina a tsakanin mu, hak'ik'a ina alfahari ku, ina yiwa kowa fatan alkhairi_🤝😍
*PAGE 18*
Har sai da suka shiga cikin part d'in sadeeq, amman musaddiq bai sani ba don gaba d'aya hankalin shi baya tare dashi baisan inda yake jefa kafar shi ba don kawai muh'd yake bi wanda yake rik'e da hannun shi, suna shiga cikin palon sadeeq yace
"Ku xauna bari na kirawo muku ita koh my brothers?"
Cikin murmishin yak'e Dr muh'd yace"toh babban yaya a fito lafia"
Murmishi sadeeq yayi tare da shige wa bedroom d'in mufidah, shi kuwa musaddiq maganar da sadeeq yayi ita ta dawo dashi cikin hayyacin xumbur ya mik'e tsaye tare da wani fisge hannun shi daga rik'on da muh'd yayi mishi yana k'are wa inda yake kallo.
Cikin sauri muh'd yace"lafia musaddiq?"
Kafin ma ya rufe bakin shi musaddiq ya fice daga palon da wani irin gudu, kafin ya ankara har musaddiq ya fice daga part d'in cikin sauri Dr muh'd ya mik'e xai bishi kenan sai ga sadeeq ya fito tare da mufidah, kallon muh'd yah sadeeq yayi tare da cewa
"Sorry k'anina na bar ku ko, ina musaddiq kuma?"
Ambatar sunan musaddiq da aka yi sai da gaban mufidah ya fad'i, shi kuwa muh'd ya rasa mai xai cewa sadeeq, daga k'arshe dai da yaga sadeeq ya tsare shi da ido yasa shi yin murmishin yak'e tukunna yace
"Gajiya yayi da xaman jira gashi kanshi yana ciwo shine ya tafi yasha magani ya kwanta don ya huta"
"Wayyo kanshi ne yake ciwo Allah sarki brother bari naje na ga jikin nashi, ina xuwa muh'd"
Muh'd wanda gaba d'aya hankalin shi yayi kan musaddiq ya rik'o hannun sadeeq yana cewa
"Ah babban yaya ba sai kaje ba xan je yanxu wurin shi kafin na tafi, idan ta kama ma xan k'wana wurin shi don na kula dashi, amman kayi xaman ka"
Dafa kafad'ar shi sadeeq yayi tare da cewa"okay naji amman don Allah ka kular min da shi sosai please"
"Kada ka damu xan kula shi insha Allah"
"thank u so much muh'd ina jin dad'in yanda kake kular min da musaddiq Allah ya bar mu tare"
"Ameeen babban yaya"
Kallon mufidah yayi tare da cewa"Auntyn mu ya hidimar biki?"
Dak'yar mufidah ta iya bud'e baki tace"Alhmdllh"
Don gaba d'aya mufidah ta rasa abin da yake mata dad'i, bayan sun gama gaisa wa ne tukunna yayi musu addu'a sosai ta xaman lafia da xuri'a mai albarka daga hka yayi musu sallama tare da fito wa daga part d'in sauri yake ya k'arasa wajen musaddiq.
Yana tura kofar bedroom d'in musaddiq d'in ya tarar dashi a kwance kan bed yayi ruf da ciki, da sauri muh'd ya k'araso inda musaddiq yake a kwance yasa hannun shi ya jiyo dashi, ba k'aramin firgita muh'd yayi ba ganin hawaye na xuba a idanun musaddiq gaba d'aya fuskar shi da idanun shi sun yi ja.
"Haba musaddiq why da xaka dunga barin abu yana tasiri a cikin xuciyar ka, ina son kayi hak'uri ka cire mufidah daga ran ka gaba d'aya ta riga da ta xama mallakin wani, wanin ma d'an uwan ka yayan ka, tun kafin a fara fahimtar halin da kake ciki, don mumy sam bata yarda da abin da nace musu ba daddy ne kawai ya aminta"
Dr muh'd ya fad'i hka yana goge wa musaddiq hawayen da suke xaba a idanun shi, shima hawayen yake fitar wa, cikin rawar murya musaddiq yace
"Ya xan yi muh'd, ji nake xuciya ta tana wani irin xugi da rad'ad'i, ni dama Allah xai d'auki r........."
Kafin ya k'arasa fad'i muh'd ya toshe mishi baki yana hawaye tare da girgixa kanshi yana cewa" nooo musaddiq kada ka k'ara furta hkan, Allah yana sane da kai xai yaye maka abin da yake damun ka, wannan itace kaddarar ka musaddiq, kasani duk tsanani yana tare da sauk'i, insha Allah *K'ARSHEN WAHALAR* ka ya kusan xuwa k'arshe, ina son wannan abun ka barshi tsakanin ka da *DANGARTAKAR ZUCIn* ka kada ka bari su daddy su gane, yanxu ka tashi ka d'auki alqur'an ka karanta xaka ji sauk'in abin da kake ji insha Allah".
Yunk'ura musaddiq yayi ya tashi xaune sadeeq ya tashi ya mik'a mishi ruwa yasha sannan ya d'auko mishi Qur'an tare da mik'a mishi nan take musaddiq ya fara rera karatun cikin muryar shi mai dad'in gaske tuni ya fara jin abin da yake damun shi ya fara jin sauk'in shi a cikin xuciyar shi, amman duk da hka hawaye na xuba daga idanun shi, muh'd yana gefe ya kallon shi cikin tsananin tausayin shi, ya riga da ya yanke shawarar k'wana a wajen musaddiq don baxai iya tafia ya bar musaddiq cikin wannan yanayin ba bacci ma baxai iya cikin kwanciyar hankali ba son da yake yiwa musaddiq bai misaltu ba jin shi yake kamar d'an uwan shi wanda suka fito ciki d'aya.
Kash rashin sani yafi dare duhu kaf duk wannan maganar dasu musaddiq da Dr muh'd suke yi a kunnen mumy don ta taho kawo wa musaddiq ruwan coffee taji maganar su,duk da mumy ta xargi hkan amman da taji yanxu da kunnen ta sai da ta firgita sosai da sauri ta bar kofar bedroom d'in ta haura stairs d'akin ta ta wuce kai tsaye tana shiga ta rushe da wani irin kuka.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, yanxu ya xan yi yara na guda biyu kacal da Allah ya bani suke son mace guda d'aya so kuma ba na wasa ba, ya Allah na rok'e ka ka cire wa musaddiq son mufidah acikin xuciyar shi"
Kuka sosai mumy take don so shu'umin abu ne don tsaf xai iya hargitsa musu xaman lafiar da suke, dole kuwa ta tashi tsaye ta sake xage damtse wajen kaiwa Allah kukan ta, tashi tayi ta nufi toilet alwala ta d'aura tukunna ta fito ta shimfid'a abin sallah ta fara nafilfilo sai da tayi raka'a shida tukunna ta janyo Qur'an ta fara karatu sai da tayi karatu sosai kafin kuma ta d'aga hannun ta sama tana xubar da hawaye tana addu'a tare da rok'on Allah abubuwan da yake damun ta.................
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A muh'd
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
_wannan page naku ne k'awayen arxik'i, Aunty halilos da sister d'in ta zahra, deejah,tare da en group d'ina Aunty & sadeey novel's group, ina matuk'ar ji daku sosai Allah ya bar mu tare, i really luv u guys, ina muku fatan alkhairi_🤝😍
*PAGE 17*
Cire damuwa tayi a fuskar ta tare da fad'ad'a fara'ar ta don a gaskia mumy tana k'aunar mufidah saboda hankalin yarinyar da nutsuwar ta suna birge ta dad'in dad'awa kuma tana k'aunar ta haifi 'ya mace gashi Allah bai bata, cikin farinciki ta rungume mufidah a jikin ta mutane sai kallon su ake cike da sha'awa da ace hka iyayen miji suke nuna k'aunar matar 'ya'yan su da an samu xaman lafia baxa a fiye tashin hankali ba, amman wasu suna yin k'ok'arin hkan.
Bayan an damk'a amanar mufidah a hannun mumy ne sai kuma aka wuce da ita part d'in su, wanda sai an fita daga part d'in mumy sannan xa'a je nasu, hannun mufidah a cikin hannun mumy har aka shigar da ita bedroom d'in ta da kanta ta xaunar da ita gefen bed, mufidah kuwa kuka take yi sosai.
A gaskia 6angaren mufidah ba k'aramin had'uwa yayi ba yasha had'add'un furniture's en k'asar waje masu kyau da tsada ko'ina ya had'u sai kamshi ne yake tashi a kowanne lungu da sak'o na wajen, bayan en kawo amarya sun gama ganin wurin ne tukunna suka fara tafia saboda dare ya fara yi, kafin kace me part d'in yayi tsit ba alamun motsin mutane sai mufidah ita d'aya a bedroom tana gurxar kuka don ita ba k'awaye ne da ita idan ka dauke nabila itace k'awar ta kawai.
Lokacin da musaddiq ya k'arasa part d'in daddy sai kawai ya had'a kai da bango wani gumi ne yake tsatstsafo mishi a cikin sassan jikin shi gaba d'aya ya rasa inda xai sanya ran shi yaji dad'i, dafa mishi kafad'a Dr muh'd yayi tare da cewa
" kayi addu'a musaddiq xaka samu sauk'in abin da kake ji"
A hankali ya bud'e bakin shi yana addu'a a take ya fara jin nutsuwa na xuwar mishi har ya iya samun waje ya xauna, bai fasa yin addu'ar ba har sai da yaji abin da yake ji ya ragu sannan ya bud'e baki dak'yar yace
"Muh'd taimaka min da bottle d'in ruwa"
Cikin tausayin shi Dr muh'd ya k'arasa frige ya d'auko mishi bottle d'in swan water mai sauk'in sanyi ya mik'a mishi.
Hannu yasa ya kar6a tare da 6alle murfin robar ya fara shan ruwan, yana cikin sha ne daddy da sadeeq suka shigo falon, cikin sauri sadeeq ya k'arasa wajen musaddiq ya rik'e mishi d'ayan hannu tare da cewa
"Haba musaddiq shine kaje kayi xaman ka a cikin hospital kak'i dawo wa da wuri koh?"
Shi dai musaddiq bin shi da kallo kawai yake, ganin hka yasa sadeeq cika mishi hannu tare da juyawa ya daina kallon shi sannan yace
"Kana ji ina maka magana kayi min shiru toh nayi fushi yaro, baxan k'ara yi maka magana ba sai nan da one week"
Ya k'arasa fad'i yana k'okarin tashi da sauri musaddiq yasa hannun shi ya janyo sadeeq ya fad'a kan kujera tukunna musaddiq ya k'ak'alo murmishi yana cewa
"Tuba nake Yah sadeeq ayi min hak'uri baxan K'ara ba"
Juya kan shi sadeeq yayi yak'i kallon fuskar musaddiq shi ala dole yayi fushi, kama kunnen shi musaddiq yayi dukka biyun tare da langa6e kai gefe yace
"I'm so sorry brother baxan k'ara ba please"
Juyo wa yayi tare da hararar musaddiq cikin murmishi musaddiq ya cigaba da cewa
"Kayi murmishi mana yah sadeeq kamar ba sabon ango ba"
Nuna shi da hannu sadeeq yayi tare da cewa"kai koh?"
Bai k'arasa fad'in abin da yake so ya fad'a ba sai kawai ya rungume shi a jikin shi yana fitar da hawaye daman sadeeq bashi da wahalar yin kuka, shima musaddiq k'ara rungume d'an uwan nashi yayi tare jikin shi yana fitar da nashi hawayen don shi abubuwa ne da yawa suka had'e mishi.
Daddy da Dr muh'd tare da mumy wadda shigowar ta kenan su ma hawayen tausayin sune ya fara xubo musu, daddy ne yaje ya raba su tare da shiga tsakiyar su suka rungume shi, bubbuga bayan su daddy yake alamar rarrashi.
Ganin dare nayi yasa daddy ya fara magana da cewa"kai sadeeq maxa tashi k'annen ka su yi maka rakiya xuwa wajen amaryar ta, ni ban ta6a ganin ango bashi da aboki ba sai kai, abokin naka Omar shi ma angon ne sai k'annen naka su yi maka rakiya"
Dariya suka sa gaba d'aya ban da musaddiq da dariyar tashi ta yak'e ce, cikin shagwa6a sadeeq yace
"Ni daman daddy musaddiq da Omar sun ishe ni sai kuma muh'd koh?"
Ya k'arasa fad'a yana kallon Dr muh'd, cikin er dariya muh'd yace"hkane babban yaya, ka taso mu yi maka rakiya xan wuce gida dare nayi, dafatan amaryar baxa ta raina mu ba don muna k'anne"
Kyalkyale wa da dariya suka sake yi kafin mumy tace"haba ae 'yar tawa ba ruwan ta"
"To kun ji abin da mumyn ku tace maxa ku tashi don dare yayi"
Daddy ya fad'i hkan yana kallon su, musaddiq bai d'auka da gaske ba ne sai da ya ga Dr muh'd da sadeeq sun tashi har daddy yana mishi magana akan ya tashi su tafi.
Cikin sanyin jiki musaddiq ya tashi tukunna suka fice daga palon muh'd na rik'e da hannun musaddiq, mumy da daddy suka bi su da kallo kowanne yana nashi tunanin a cikin xuciyar shi...............
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A muh'd
♻ *E.W.F*
_ina kike my BIEBIE DEEE wannan shafin naki ne k'awata ta kirki Allah ya bar mu tare_
*PAGE 19*
Bayan tafiar Dr muh'd ne, sadeeq yasa hannun shi ya rik'o hannun husna wani irin shock suka ji a lokaci d'aya don tun da sadeeq yake xuwa wajen mufidah ko da wasa bai ta6a rik'e mana hannu ba ko ya ta6a jikin ta, hkan ba halin shi bane yanxu kuwa da ta xama halaliyar shi xai iya komai da ita ba tare da fargabar kauce wa mahaliccin shi ba.
Zama yayi kan kujera tare da janyo mufidah akan cinyar shi ya xaunar da ita yasa hannun shi ya xagaye hips d'in ta, tukunna ya sanya d'aya hannun ya cire mayafin da ta lullu6a dashi nan fuskar ta ta bayyana wadda tasha heavy make up tayi kyau kamar ba ita ba amman ruwan hawaye ne kawai suke xuba daga idanun ta, rungume ta yayi wanda har sai da mufidah taji saukar ajiyar xuciyar shi, kafin ya bud'e baki a hankali yace
"Alhmdullilah ayau baxan iya fad'ar irin tarin farincikin da nake ciki ba, Allah nagode ma da ka nuna min wannan muhimmiyar ranar a gare ni da na mallaki abar sona"
Ita dai mufidah shiru tayi mishi kan ta a sunkuye ta k'i d'ago kanta, ha6ar ta yasa hannu ya rik'o tare da kallon fuskar ta yace
"Ya kamata ki daina kukan nan hka kada yasa miki ciwon kai, yanxu tashi mu tafi bedroom don gabatar da sallahr nafila mu gode wa Allah da ya nuna mana wannan ranar da muka mallaki junan mu ta hanyar yin aure"
A nutse ya sauke ta daga kan kafafunshi tukunna ya mik'e tsaye yana rik'e da hannun ta suka rufe ko ina sannan suka shige bedroom, toilet suka shiga suka d'aura alwala tukunna suka fito ita dai mufidah bin shi take duk abin da yace mata saboda wata irin kunyar shi take ji, shi ya shimfid'a musu abin sallah ya d'auko mata hijab ta sanya sannan ya fara jansu yin nafila.
Bayan sun kammala nafilar ne ya rik'e kanta da hannun shi yayi addu'a sosai don ba laifi sadeeq akwai ilimin addini, bayan ya gama addu'ar ne sannan ya sauke hannun shi daga kanta,ya dad'e yana musu addu'ar xaman lafia da samun xuri'a mai albarka kafin kuma su shafa, tashi yayi ya fita daga bedroom d'in, ganin hka yasa mufidah mike wa ta ninnike abin sallahr ta ajiye tare da hijab d'in da tayi sallahr tukunna ta shige toilet don yin wanka saboda ta saba Indai xata yi bacci a gida sai tayi wanka take iya bacci mai dad'i.
Ta d'auki tsawon mintuna 15 tukunna ta fito ta shirya cikin wata sleeping dress irin mai biyun nan ta farko iyakar ta gwiwa ta tsaya tana da siririn hannu ta biyun kuma wadda ake d'ora ta asaman dogowa ce har k'asa hannun ta mai d'an tsayi kad'an sai ka d'aure ta da wasu siririn maxagin jikin rigar, bayan ta gama sanya kayan ne ta fesa different perfumes and body spray's masu matuk'ar k'amshin dad'i tukunna ta nufi kan bed don kwanciya wani irin bacci take ji a idanun ta sosai ta k'udundune jikin ta da wani blanket mai matuk'ar laushi saboda yanda garin ya d'auki sanyi sakamakon hadarin da ya had'u sosai ga kuma sanyin ac dana fanka.
Ko mintuna biyar bata yi da kwanciya ba sadeeq ya shigo cikin bedroom d'in hannun shi dauke da wani babban tire shima yayi wankan shi yasha wasu sleeping dress na maxa sky blue ne masu taushin gaske, ajiye tiren yayi tare da hawa kan bed d'in yasa hannu ya cire rufar da mufidah tayi lokaci d'aya tsikar jikin shi ta tashi saboda ganin mufidah da yayi a hka d'aure wa yayi yace
"My wife tashi kici abinci sai kiyi bacci, kada kice min a'a please, don nasan baki ci abincin kirki ba saboda hidima"
Kasa yi mishi musu tayi nan ta fara k'okarin tashi da sauri yasa hannun shi ya tashe ta xaune tukunna ta tashi xuwa wajen wasu kujeru guda biyu a gefen bed d'in akwai center table a tsakiyar su nan ta xauna shima sadeeq tashi yayi ya koma inda take tukunna ya bud'e plate d'in wasu gasassun kaji ne sun sha kayan vegetables sai tashin k'amshi suke ko ni dana ke gefe ina daukan muku rahoto sai da yawu na ya tsinke lol.
Gefe kuma drinks ne da fresh milk gasu nan kala kala masu sanyi, nan ya fara ciyar da mufidah da hannun shi don yak'i yarda taci da kanta, bayan sun gama ci ne mufidah ta tashi ta shiga toilet brush tayi ta wanke bakin ta da mouth freshener mai k'amshin mint leave's tukunna ta fito bata ga sadeeq anan ba don hka ta koma ta kwanta abin ta lokacin har an fara yayyafi.
Sadeeq ne ya shigo bedroom d'in tare da rufe kofar tukunna ya nufi kan bed ya kwanta kusa da mufidah, lokaci d'aya gaban mufidah
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 23