Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sai ya koma Australian.................. _fan's kuyi hak'uri da wannan page d'in mu had'u gobe,ina godia da bani had'in kai da kuke ina muku fatan alkhairi masoya naaaaaaaa_😊 Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ £xclusive writers forum Like and drop ur comments fb page #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ *PAGE 45* Sai da mufidah taga ta k'arasa gidan su ta shiga har tayi parking motar ta sannan taji ta samu nutsuwa hankalin ta ya kwanta, har da sakin wata ajiyar xuciyar jin dad'i don tasan musaddiq baxai biyo ta gida. Cikin tafiyar ta ta nutsuwa ta k'arasa side d'in su da sallama ta shiga parlourn, umma wadda take xaune kan kujera tana kallon sunnah tv suna nuna wa'axin sheik isah Ali pantami, ta amsa sallamar mufidah tana mai sakin murmishi najin dad'in ganin 'yar ta ta, fara'ar ta ta kasa 6oyu wa musamman da taga alamun mufidah ta kwantar da hankalin ta yanxu har tayi kyan ganu wa ba kamar kwanakin baya ba. K'arasa wa mufidah tayi inda umma take xaune ta xube gwiwoyin ta a k'asan lallausan carpet d'in parlour ta d'ora kanta da hannayen ta duk biyun akan k'afar umma cikin marairaice wa tace "umma nah i miss u so much" Shafa kanta umma tayi tana murmishi tace "i miss u too baby na, yasu hajia khadija ina afnan ko ta shige side d'in su muhibbat? " Umma ta k'arasa fad'a tana lek'en bayan mufidah, cikin er dariya mufidah tace " tabbb umma yanxu hka afnan tana london ita da mumy da daddy " Cikin mamaki umma tace "dafatan lafia dai ?" "lafia qlau umma sun je duba lafiar abokin daddy ne an kwantar dashi acan yana jinya" "Ayyah Allah ya bashi lafia, su kuma Allah ya dawo dasu lafia " "Ameeen umma nah, don nayi missing afnan wlh ji na ke dama na bi su " Murmishi umma tayi tare da cewa "to me ya hana ki bin su?" D'an yatsina fuska tayi tare da cewa "umma bana son ace ko'ina xasu je da sun nemi na bi su na je shi yasa na k'i yarda na je bana son ina tak'ura musu duk da nasan su ba ruwan su " "kin yi tunani mai kyau " Cewar umma kafin ta cigaba da cewa "ina kika bar musaddiq d'in? " Cikin mamaki sosai mufidah take kallon ta kafin tace "umma kinsan ya dawo ne? " "nasa ni mana tun da Omar shi ya d'auko shi a airport suka biyo ta nan har yaci abinci tukunna ya k'arasa gida " "lallai wannan mutumin d'an rainin hankali har wani shisshige wa iyaye na yake yi " fad'in mufidah a cikin xuciyar ta, "lafiyar ki kuwa? " Cewar umma tana Kallon mufidah ganin ta d'an rage fara'ar ta gashi ta fad'a kogin tunani. Girgixa kai tayi tare da cewa "ba komai umma, nabilah tana nan? " "gani nan a bayan ki Mrs musaddiq " Da sauri mufidah ta jiyo suka had'a ido da nabilah tana fito wa daga kitchen d'in umma, d'an 6ata rai mufidah tayi tare da cewa "ba na hana ki kirana da Mrs wancan mutumin ba" Ta k'arasa fad'i tana hararar nabilah, tuntsire wa da dariya mufidah tayi tare da rik'e baki tace "ikon Allah wato ma baxa ki ambaci sunan shi ba lallai da aiki a gaba na " Umma kuwa d'an 6ata fuska tayi tare da cewa "Ehh lallai mufidah wato a gabana kike furta hakan akan mijin ki koh, har kina kiran shi da mutumin can koh? " Harara mufidah ta dalla wa nabilah don tasan ita xata janyo mata fad'an umma yanxu, yayin da nabilah ta gimtse dariyar ta tare da wuce wa kitchen da sauri. "kada na sake jin kin furta wani abun makamancin haka, don miji yafi k'arfin wasa tsakanin ku girmama wa da da yi mishi biyayya da sauke duk wasu hakk'ok'in sa, magana ma ta girmama wa xaki na yi mishi kuma cikin sanyi kina nuna mishi ke fah mace ce kina da sanyi a ko'ina, don hka kada na k'ara jin irin hka a wajen ki, kina jina" "toh umma insha Allah xan kiyaye " Mufidah ta fad'a kamar xata fashe da kuka, "dafatan Kuna xaune lafia dashi kuma kuna waya? " Da har xata ce bai ta6a kiran ta ba sai kuma tayi wani tunani kafin tace "Ehh umma muna yi " "Alhmdlh ai musaddiq ba ruwan shi kamar marigayi sadeeq d'an uwan shi yake, sam baya suruka da ni ya dauke ni uwa muna yin waya sosai dashi mu sha hira, sadeeq daman mai jin kunya ta Allah ya jikan shi da rahma " Cikin sanyin jiki da murya mufidah tace "Ameeen " "dafatan kafin ki fito kin yi mishi breakfast baki barwa en aiki sun yi mishi ba " Tuni mufidah an fara rarraba idanu don tasan ita kanta ko breakfast bata yi balle tayi wani, kallo d'aya umma tayi mata ta tabbatar bata da gaskia ae kuwa tace "haba mufidah wannan wane irin shashanci ne da xaki bar wa en aiki su yiwa mijin ki abinci, sam wannan ba koyarwar da nayi miki bace, kada ki k'ara yin sakacin nan, kin ji na fad'a miki " Idanun ta cike taf da hawaye tace "tohhh umma " Nan umma ta dunga yi mata nasiha tare da bata shawarwari masu amfani wanda tasan xai taimaka musu wajen kwanciyar hankali da xaman su lafia (wanda wasu iyayen sam basu damu da hkan ba, ace 'yar ki xata yi aure ko kuma tayi auren baxa ki xauna da ita ba a matsayin ki na uwa ki bata shawarwari masu amfani wanda xai taimake ta a rayuwar auren ta, kina nuna mata mahimmancin miji kina nusar da ita abubuwan da ya kamata wanda ya dace da tayi da wanda bai dace ba, ki janyo 'ya'yan ki jikin ki su Saba da ke sosai ta yanda duk wata shawarar ta ke xata tunkara ba sai k'awa ba wadda mybe k'awar ta d'ora ta kan wata hanyar ba mai 6ille wa ba, don hka iyayen mu mata a kula mu kiyaye wajen kula da yaran mu, tarbiyyar su, tsabta, koya musu girki, girmama na gaba dasu, uwa uba basu ilimi na addini dana boko, Allah yasa mu dace Ameeen.) Bayan umma ta gama yi mata nasiha tare da bata shawarwari ne daga karshe tace "ki je dining table akwai abinci sai ki xa6i abin da kike so " Tashi mufidah tayi tana d'aukar bag d'in ta tana cewa "Yawwa umma na kamar kinsan yunwa nake ji " Da kallo umma ta bi ta cikin mamaki kafin tace "wannan jakar fa ta me ce? " D'an waro idanun ta tayi tare da cewa "laaa umma na dawo nan sai su mumy sun dawo xan koma " "shi kuma mijin na ki wane xai kula dashi tun da hajia khadija bata nan? " Tsit mufidah tayi kafin daga bisa ni tace "umma ni wlh tsoro nake ji ni kad'ai, don Allah ki bar ni na kwana anan " Ta k'arasa maganar da shagwa6a, Kallon ta umma tayi kawai tana girgixa kai sam mufidah idan tana gaban ta nuna wa take kamar Er k'aramar yarinya. Ganin umma bata ce komai ba yasa da sauri ta bar wurin bedroom d'in ta ta nufa ta ajiye bag d'in da cire hijab d'in ta, fito wa parlourn tayi a dining ta xauna ta had'a tea tana sha gefe d'aya kuma ta d'ebi plantain and egg tana d'auka da fork tana ci hankalin ta kwance, sai da ta gama ci tukunna ta nufi kitchen wajen nabilah wadda take kok'arin had'a kunun gyad'a don tun da ta samu ciki bata da wani abin so sama da ta sha kunun gyad'a. D'an bugun ta a kafad'a mufidah tayi tare da cewa "ke wannan cikin da son kunun gyad'a ya xo miki, abin da bakya son shi ma" "uhm ke dai bari kawai Mrs musaddiq yanxu idan ban sha wannan kunun gyad'ar ba hka xan yini babu cin abinci don ji xanyi sam bana sha'awar wani abin " Girgixa kai mufidah tayi tare da cewa "wayyo k'awata Allah dai ya raba lafia, amman cikin muhibbat bai baki wahala kamar hka ba " "gaskia kuwa don ban sha wahala ba sai kwad'ayin tsiya don har my dear sai da ya fara yi min tsiya akan kwad'ayin, don bini bini nace abu kaxa nake so sai kuma yaje ya nemo min hankali xai kwanta " Nan dai mufidah ta kar6i aikin kunun gyad'ar nabilah ta samu waje ta xauna suna er hirar su har ta gama dama shi ta xuba acikin flaks Bayan ta xuba wa nabilah a cikin cup ta had'a mata da sugar and milk. "ke baxa ki sha ba? " Cewar nabilah suna kok'arin fita daga kitchen d'in, girgixa kai mufidah tayi tare da cewa "na k'oshe yanxu mybe sai xuwa anjima" A cikin parlour suka xauna hira suke sosai tsakanin su har da umma. *** *** *** Musaddiq bai dawo gidan ba sai wurin 12 na rana don hospital suka fita, yana dawo wa gidan jikin shi ya bashi mufidah bata gidan, kuma yasan gidan su ta tafi don hka bedroom d'in shi ya shiga xama yayi tare da bud'e laptop d'in shi ya fara aiki a jikin ta, sai da ya d'auki a k'alla tsayin mintuna 60 yana aikin kafin ya gama, alwala yayi ya tafi masallaci yayi sallahr axahar, kafin ya dawo gida. Bedroom d'in shi ya koma yunwa yake ji sosai ko breakfast bai yi ba, frige ya bud'e ya lalubo fresh milk mai sanyi yasha kafin ya kwanta a gajiye daman bai samu cikakken bacci jiya ba da dare don hka nan da nan bacci ya dauke shi mai nauyi. Ya dad'e yana bacci don sai wurin 5 na yamma ya tashi wanka ya fara yi agurguji ya xura jallabia sallahr la'asar yayi ya fara gabatar wa a makare ya dad'e yana addu'o'in shi kafin ya tashi ya fara shirya wa. Tsab ya fito cikin wata kuftan blue black d'inkin rigar irin iya gwiwar nan tsayin ta sosai kayan su kar6e shi abin ka fari kunsan kalar tana yiwa farare kyau, agogo da takalmi bak'ak'e yayi amfani dashi hular shi itama bak'a ce mai ratsin blue and white a jiki ya wani turo ta gaban gashi yana Kallon kanshi a mirror ya tabbatar komai yayi yanda yake so sannan ya fesa different colour's perfumes a jikin shi tukunna ya d'auki car key da phone's nashi ya fito, cikin car d'in shi ya shiga tare da yi mata key ya bar gidan. Gidan su mufidah ya nufa yana parking a cikin gidan ana kiran sallahr mangarib, a lokacin ya Omar da abba suka fito xasu tafi masallacin kusa da gidan, musaddiq ya fito har k'asa ya tsugunna ya gaida abba yayin da suka yi musabiha da yah Omar daga nan kuma suka wuce masallaci, sai after ishsha suka bar masallacin suka nufi gida. Da fara'a umma ta tarbi musaddiq suka gaisa kafin a tsunduma hira, mufidah tana bedroom batasan musaddiq ya xo ba, gama girkin daren da suka yi da umma kenan ta taho yin wanka. Bayan tayi wanka ne ta shirya cikin wata gown mai hannun vest purple colour ce tayi mata kyau ta gyara gashin ta tare da sanya mishi ribbon bata yi wata kwalliya ba daga powder sai wet lips mai k'amshin apple Bayan ta fesa perfumes ne ta fito xuwa parlour cikin takunta na nutsuwa. Sam bata kula da musaddiq ba tayi wajen dining table tana cewa "abba, umma ku taho mu ci abinci na fara jin yunwa " A shagwa6e take maganar, har ta k'arasa dining d'in ta fara serving d'in su hankalin ta kwance sai dai sometimes ta d'an jin gaban ta yana fad'uwa. "musaddiq taso mu ci abinci " "toh abba " Ya fad'i hkan yana tashi don Allah Allah yake ya k'arasa wajen da mufidah take don yayi mata Kallon da xai more son ran shi don ba k'aramin kyau tayi mishi ba. Lokacin da suka k'arasa kan mufidah yana sunkuye tana xuba musu abincin, bayan ta gama xuba wa ta d'ago kanta tana cewa "umma na abba n........ " Sauran maganar mak'ale wa yayi a fatar bakin ta dalilin had'a ido da musaddiq da tayi yana yi mata wani irin kallo mai tattare da ma'anoni daban daban.............. Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻£xclusive writers forum Like and comment's fb page #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ *PAGE 46* Sauran maganar ta mak'ale a fatar bakin ta bata k'arasa ba dalilin had'a ido da musaddiq da tayi yana mata wani irin kallo mai tattare da ma'anoni daban daban, ita ma mufidah sai ta kasa dauke idanun ta a kanshi suka tsaya kallon junan cikin wani irin shauk'in junan su don kallo d'aya mutum xai yi musu ya tabbatar suna masifar son junan shi. Abba ne ya ta6o umma tare da yi mata nuni da su mufidah suna kallon junan watak'il ma sun manta a ina suke, murmishi umma tayi kawai tana girgixa kai, gyaran muryar da abba yayi ne yasa su dawowa daga duniyar kallon junan su da suka tafi. Sai kuma musaddiq ya fara sosa kai irin na jin kunya tare da xama, yayin da mufidah ita ma kunya ta Kama ta har sai da ta dalla wa musaddiq harara tare da murgud'a mishi baki, d'aga mata kafad'a yayi irin ko ajikin shi kafin ya rama hararar da tayi mishi. Mufidah kasa sake wa tayi taci abinci daga karshe ta xame ta tsere bedroom d'in ta, sai bayan ta tafi ne tukunna musaddiq ya iya cin abincin don shi fa idan mufidah tana gaban shi kasa yin komai yake, yana cin abincin yana tuna irin kallon da suka yi junan shi yana murmishi shi kad'ai. Bayan sun gama ne suka dawo cikin parlour ana er hira har xuwa 9 na dare, kafin musaddiq ya ce "umma a kirawo mufidah mu tafi na ga dare nayi " Kafin umma tayi magana abba yace "ga bedroom d'in ta can shiga ka kirawo ta " D'an sosa kai tare da cewa "okay abba " Ya wuce cikin nutsuwa ya nufi stairs d'akin mufidah. "yaran nan suna son junan su sosai, amman ban san me ya hana su bayyana wa kansu ba suka barshi cikin xuciyar su " Cewar abba, umma kuma tace "mybe basu yi shak'uwar da xasu furta wa junan su ba, tun da wannan auren had'a su akayi ba tare da ra'ayin d'ayan su ba" "baki san saboda son 'yar ki da musaddiq yake ba har ya kamu da ciwon xuciya " D'an xaro ido umma tayi na mamaki tace "shi musaddiq d'in? " "kwarai kuwa " Abba ya tabbatar mata da hkan, kafin ya kwashe labarin komai ya fad'a wa umma wanda shi ma muh'd ne yake sanar mishi, wani tsananin tausayin musaddiq ne ya kama umma sosai, ta kasa ma magana sai jujjuya kai kawai take irin yanda idan labari ya bugi mutum sosai yake yi. A hankali ya sanya hannun shi kan handle d'in kofar ya murd'a tare da cusa kanshi ciki ba tare da yayi sallama ba, kallon d'akin yake cikin son d'akin don yanda aka shirya shi yayi kyau blue and white ne komai da komai har fentin bangon, kafin idanun shi su sauka kan mufidah wadda take xaune kan stool na dressing mirror tana gyara gashin ta, fitowar daga wanka kenan ta gama shirya wa cikin white sleeping dress mai hannun vest, tsawon rigar iya gwiwar ta ne gata irin mai shara shara ce komai na jikin ta a bayya ne yake Sauran kad'an musaddiq yayi suman tsaye. Wani irin had'iyar yawu yayi wanda har yasa shi kware wa ya fara fitar da tari, a matuk'ar firgice mufidah ta jiyo don ganin wane, da sauri ta mik'e tsaye saboda idanun ta ne suka sauka kan musaddiq wanda yake tari cikin yanayin fusata ta taso irin da saurin nan don yi mishi masifa akan shigo wa d'akin ta da yayi ba tare da ixinin ta ba, sai kawai k'afar ta ta bugi stool d'in da ta xauna akai sai ta tafi taga taga xata hantsala. Carab ta sanya hannun ta da sauri ta cafko rigar musaddiq wanda har yanxu bai daina tarin ba, k'arfin janyo shi d'in da tayi ne ba tare da ya sani ba ya sanya shi biyo ta sai kuma tayi baya tana shirin fad'uwa wata k'ara ta saki tare da runtse idon ta da k'arfi. Kan bed ta fad'a musaddiq ma ya biyo ta don har yanxu tana k'ank'ame da rigar shi, da sauri ya sanya hannun shi duk biyun ya tokare su da kan gadon don kada ya fad'a kanta. Jin shirun da mufidah taji ya sanya ta bud'e idon ta d'aya don jin saukar numfashin musaddiq a saman fuskar ta, batasan lokacin da ta bud'e idanun gaba d'aya ba don ganin fuskar shi dab da ta ta, kallon junan su suke ido cikin ido irin kallon da man da geet suke yi idan soyayyar tasu ta motso. lol Sun kwashe some minutes suna kallon junan su kafin mufidah ta tsuke fuska tace "malam ni ka d'aga ni xan tashi ka gani danne ni kana kallo na " Shima 6ata fuskar yayi tare da cewa "wane xai tsaya kallon ki, kuma ni bani na janyo ki ke kika janyo kan ki " Hararar shi tayi tare da cewa "to d'aga ni " Shima hararar ya rama tare da yatsina fuska kafin yace "cika min riga ta " Sai lokacin idanun mufidah ya fad'a kan hannun ta da yake rik'e da rigar shi k'am da sauri ta cika mishi, ya fara kok'arin tashi. Yana tashi mufidah idanun ta suka sauka kan jikin ta inda rigar ta gaba d'aya ta nannad'e daga kasa ae kuwa cikin sauri ta k'arasa haye wa kan gadon ta tuk'unk'une da blanket har kanta, abin sai ya bawa musaddiq dariyar ma har sai da ya murmusa cikin xuciyar shi ya furta " har yanxu akwai yarinta a tattare da ke mufidah, ina son komai naki i luv u so much " A fili kuma yace "ke malama ki tashi mu tafi gida dare nayi " Tana cikin blanket d'in ta murgud'a baki tare da cewa "tabbb ba inda xan je ina gidan mu " "ki taso mu tafi idan nayi k'irga 5 baki fito ba I'll slap u " Tana jin shi ko uhm bata ce mishi ba har ya fara k'irgen, jin har ya kai 4 ne yasa ta mik'e wa xata fad'a toilet, ae kuwa kamar ya sanya abin da take niyyar yi sai ji tayi carab ya rik'e hannun ta tare da murgud'a su ya jiyo da ita tana kallon shi ya mayar da hannun ta dukka biyun bayan ta ya rik'e su da hannun shi d'aya kallon ta yayi tana xubar da hawaye don ba k'aramin rik'o yayi mata, lumshe idanun shi yayi sam baya kaunar ganin hawayen ta kawai sai ya sanya hannun shi ya janyo hijab d'in ta ya xura mata ganin da yana kok'arin d'aukar ta yasa magana da sauri tana cewa "ni ka kyale ni na shiga toilet xan yi fitsari " Kallo d'aya yayi mata yasan ba wani fitsari da take ji, ya dauke ta cak yana cewa "idan ki matsu kiyi a hka " Nan ta fara wutsil wutsil da kafafun ta alamar ya sauke ta amman bai kula ta ba har sai da suka fito parlour, umma da abba ma basa nan xaune don hka kawai ya fita har xuwa wajen da yayi parking motar shi ya sanya ta kafin ya shiga shima yayi wa motar key suka bar gidan. Saboda takaici sai kawai ta rushe da kuka don ta rasa abin yi sai kukan mybe idan tayi ta samu relief a cikin xuciyar ta, lumshe idanun shi yayi tare da bud'e su lokaci d'aya suka yi ja don baya kaunar ganin kukan ta xuciyar shi na k'una idan yaga hawayen ta, daure wa yayi har suka k'arasa gida tak'i fito wa daga motar sai da ya dauke ya kaita har bedroom d'in ta tukunna ya fita. Sai da ta gaji da kukan ta bacci ya dauke ta, musaddiq sai da ya shigo d'akin ya ga tayi bacci sannan hankalin shi ya kwanta yayi mata addu'a sannan ya kashe mata hasken ya bar d'akin sai lokacin yaji xuciyar shi tayi mishi dad'i hankalin shi ya kwanta. Ko Washe gari ma kulle kofar bedroom d'in ta tayi bata fitowa ba sai da tabbatar ya bar gidan sannan ta fito, abinci iya cikin ta ta girka ta koma bedroom ta rufe don sosai haushi ya bata ba. Sosai hankalin musaddiq ya tashi don ya kasa jure rashin ganin ta, amman sai ya daure don baya son ta fahimci abin da yake cikin xuciyar shi idan ba nesa yayi da ita ba cikin lokaci k'ank'ani xata fahimci abin da xuciyar shi take ciki, hkan yasa shi fara shirin koma wa Australian. Ranar dasu mumy xasu dawo a ranar musaddiq ya bar nigeria ko mufidah bai k'ara gani ba, sai daf da mangarib su mumy jirgin su yayi landing a airport sai ganin su mufidah tayi kawai, nan ta rungume mumy da afnan tana mai farincikin ganin su, hka ma mumy baki yak'i rufuwa na ganin mufidah afnan sai labarin kasar london ake yiwa mufidah. " yau kenan kika dawo 'yata? " Cewar mumy suna shiga bedroom d'in ta, d'an murmishin yak'e mufidah tayi cikin xuciyar ta tana cewa wannan masifafen mutumin ne xai bar ni na tafi gidan mu, a fili kuma tace "ehhh mumy d'axu na dawo " Murmishi tayi tare da cewa "yayi kyau hkan, ae da ma baki dawo ba anjima kad'an xaki ganni" Murmishi kawai mufidah tayi mumy tana sonta shi yasa ita ma take son ta sosai, hka lokaci ya cigaba da tafia suna xaman su cikin kwanciyar hankali ta 6angaren mufidah tana kok'arin yaki ce wani abu da yake son shiga cikin xuciyar ta tana son karya ta xuciyar ta akan abin shi yasa bata kaunar xama waje d'aya tana k'e6e wa ita d'aya tunanin shi xai fara addabar xuciyar ta, shi yasa take k'irk'irar abubuwan da xata hana xuciyar ta tunanin shi don ita a ganin ta sam baxa ta bari son shi yayi tasiri cikin xuciyar ta ba. *AFTER 3 MONTH'S* bayan wad'annan watannin da suka shud'e ne shiru musaddiq yak'i dawowa mumy da daddy sun yi mishi maganar ya xo ya d'auki mufidah su koma Australian d'in amman ya fara yi musu hanya hanya ganin hka yasa mumy da daddy suka yanke lokaci nan da two weeks mumy xata kai mufidah har Australian d'in ba tare da sun bi takan musaddiq ba tun da yak'i tsayawa ayi maganar. Musaddiq kuwa ta 6angaren shi baya son yana ganin mufidah hankalin shi ya tashi yake, ganin ta ba k'aramin canja mishi tunani yake ba xuwa wani abin daban, taya xai iya tunkarar mufidah da buk'atar shi sai yake ganin kamar bai yiwa d'an uwan shi adalci ba wannan tunanin nashi shi yake dad'a nisan tashi da bayyana wa mufidah abin da yake kunshe cikin xuciyar shi shekara da shekaru. Cikin kwanakin nan aka gama shirya tafiar mufidah da afnan, gyaran jiki na musamman mumy ta d'auko don gyara mufidah ciki da waje, ae kuwa tasha gyara ba kad'an ba, tayi wani irin kyau sosai na daban, sam mufidah ba'a son ranta xata tafi ba don kawai tana jin kunyar mumy da daddy ne bata son nuna rashin son tafiyar da bata yi, Sauran kwana biyar su tafi ne taje yiwa su umma sallama don xata kwana uku acan. Sosai umma ta dage ita ma tana gyara d'iyar ta ta duk da ta yaba da gyaran da mumy tayi mata, hka nabilah ma gudummowar ta daban ta wannan 6angaren, umma ta xaunar da mufidah tayi mata nasiha sosai tare da bata shawarwari masu amfani, abba da yah Omar ma kowa da tashi nasihar, mak'ale wa mufidah tayi tak'i dawowa gidan mumy sai ranar da xasu tafi Australian d'in da safe mumy ta xo ta sanya ta a gaba suka koma gida, da kanta mumy ta shirya mata kayan ta sosai da yake tashin dare xasu yi. Xuwa mangarib

Chapter 16 of 23