sun gama komai xuwa karfe 9 jirgin su xai tashi don hka 8:30 na dare suna airport, nan suka yi sallama da daddy da yake har dashi a en rakiyar ga umma, abba, yah Omar, nabilah da muhibbat, ga Dr muh'd da matar shi nafisat har dasu a en rakiyar don muh'd yana bawa duk wani abin da ya shafi musaddiq muhimmanci,kowannen su jiki a sanyaye suka yi sallama har jirgin su mufidah ya tashi suna tsaye kafin kuma su koma gida duk kewar mufidah da afnan ta kama su don mumy kwanaki biyu xata yi ta dawo.
Acikin jirgin kuwa mufidah hawaye ne yake xuba a idanun ta cikin xuciyar ta baxa ka iya tantance halin da take ciki ba farinciki ko akasin hka,kwantar da kanta tayi idanun ta a lumshe tana tunanin irin xaman da xasu yi ita da musaddiq a wannan lokacin............
_to readers ga mufidah a hanyar ta ta xuwa australian wajen musaddiq, ko ya xaman su xai kasan ce ni kaina na k'agu naji irin xaman da xasu yi, don hka ku jira ni a next page d'ina don jin abin da xai faru, godia mara adadi gare ku fan's d'in yayi sake! ni Aishat A muh'd ina gaida ku tare da yi muku fatan alkhairi luv u all my fan's_
Sai kun yi hak'uri da wannan page d'in don ban samu damar editing ba
Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM
LIKE AND COMMENT'S FB PAGE 👇🏻
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
_Gaisa da fatan alkhairi gare ku masoyan Aishat A muh'd, ina jin dad'in yanda kuke kaunar littafin nan, don hka na sadaukar da wannan page d'in ga duk masoyin littafin yayi sake!,luv u oll my fan's_❤
*PAGE 47*
A cikin jirgin kuwa mufidah hawaye ne yake xuba a idanun ta cikin xuciyar ta baxa ka iya tantance halin da take ciki ba farinciki ko akasin hka, kwantar da kanta tayi idanun ta a lumshe tana tunanin irin xaman da xasu yi ita da musaddiq a wannan lokacin.
Lokacin da jirgin nasu yayi landing a babban fili saukar jirgi na australian, mutane suka fara firfito wa mufidah tana sanyo kanta xata fito taji wani sanyi ya ratsa mata fuska sosai nan ta k'ank'ame jikin ta, tana tunanin yanda xata iya xama a wannan uban sanyin garin, a nutse ta sauko daga matattakalar jirgin mumy da afnan suna bayan ta.
Bayan duk sun gama komai ne suka nufo hanyar da xata kaisu wajen hanyar fita daga airport d'in xuwa wurin da xasu tari taxi, mumy ce ta tsayar da taxi d'in cikin harshen turanci tayi mishi bayanin inda xai kaita da sunan unguwar da musaddiq yake xaune, ba wani 6ata lokaci ya amince da hkan kafin ya fito ya taimaka musu da xuba kayan su cikin boot tukunna suka shiga yaja su.
Mufidah ta ware idanun ta sosai tana kallon yanayin garin na australian sosai k'asar ta birge ta don bata ta6a xuwa k'asar ba, wani lokacin idan ta tuna wajen wanda xasu je har su xauna tare sai ta ji xuciyar ta na bugawa.
Tafiyar tsayin mintuna 50 ne ya kaisu anguwar da musaddiq yake har number d'in gidan mumy ta fad'a wa taxi driver d'in, ai kuwa a dai dai kofar gidan yayi parking, sai da ya sauke musu kayan lokacin da mumy ta nemi alfarmar hakan a wajen shi, tukunna ta biya shi, knocking d'in kofar gate d'in mumy tayi gateman ya bud'e da yake ya san mumy basu wani 6ata lokacin shiga gidan ba.
Door bell mumy ta danna sau uku ana hud'un ne suka ji ana kok'arin bud'e kofar, lokacin da musaddiq ya bud'e kofar sakin baki yayi cikin matuk'ar mamaki yana Kallon mumy wadda ta had'e fuska babu wasa sam ba hango mufidah ya tsaya kawai yana kallon mumy ko magana ya kasa yi
"bani wuri na shige mun gaji da tsayuwar "
Mumy tayi furucin ganin bashi da niyyar matsa ma, kamar wani yaro ya matsa mata taxo xata shige tace
"musaddiq Allah ya shirye ka, yanxu a hka kake bud'e kofar kasan wane xai shigo maka a lokacin "
Wata irin kunya ta kamshi ya sunkuyar da kanshi yana sosa kai tare da tunanin yanda yake boxer ne a jikin shi kawai ko riga babu lokacin yana kwance cikin bedroom yana tunanin mufidah yaji knocking d'in so bai tsaya sanya kaya ba ya fito, ita dai mumy shige wa tayi cikin parlourn.
Jiya yi an rungume kafafun shi ana cewa "Oyoyo daddyna i miss u so much "
D'ago kanshi yayi ya ga afnan ce ae kuwa ya d'aga ta sama yana dariya tare da cewa
"i miss u too dear,ashe mumy da ke ta xo min? "
Tana dariya tace "yes daddy dani taxo har da mamee nah "
Dariya ya sake sanya wa ya d'auka shirmen afnan ne kawai sai ya sanya bakin shi ya bata peck a kumatun ta, d'aga idanun shi da xai yi suka had'a ido da mufidah tana tsaye tana kallon su cikin sha'awa da birge wa, sai kawai suka tsaya kallon junan su cikin wani yanayi na shauk'i.
"bani hanya na wuce kada ka cinye min yarinya ka wani xuba mata ido kak'i matsawa ta wuce "
Cewar mumy kenan ganin shiru mufidah bata shigo ba, sai lokacin ya sauke idanun shi akan ta ji yayi xuciyar shi tayi mishi sanyi da ganin ta yana rik'e da afnan ya wuce ciki, yayin da mumy ta rik'o hannun mufidah suka wuce su ma cikin parlourn.
Lokacin da suka shiga musaddiq yana xaune kan kujera afnan tana kan kafafun shi tana mishi hira murmishi kawai ya ke yi, yana son afnan idan yana ganin ta ko yana jin muryar ta jinshi yake tamkar yana tare da d'an uwan shi sadeeq.
"malam ai sai kaje ka sanya kaya koh oh ni khadija musaddiq ko kunya ta baka ji ka xauna a hka a gaba na "
"mumy ba hka ba ne just afnan ce ta tsaida ni labari take bani "
Yana gama fad'in hka ya xaunar da afnan tare da cewa "sweet dgter give me five minutes ina xuwa"
Langa6e kai tayi tare da cewa "okay daddy "
Kallon mufidah yayi sai aka ci sa'a ta d'ago kanta suka had'a ido ae kuwa harara ya sakar mata tare da yi mata kallon xan kama ki ne yarinya ita ma hararar ta watsa mishi girgixa kai yayi kawai ya wuce bedroom d'in shi.
Cikin mintuna 10 sai gashi ya fito har ya shirya cikin Blue Jeans and black T-shirt mai k'aramin hannu yayi kyau sosai, gaida mumy yayi ta amsa mishi, mufidah ganin idon mumy ne yasa tayi mishi gaisuwa d'aya daga ina yini taja bakin ta ta tsuke , to shima lafia kawai ya furta sannan ya kalli mumy yace
"mumy ga bedroom nan ki je kiyi wanka ki huta bari na fita na samo muku takeaway "
"to shikenan "
Abin da mumy tace ta wuce d'ayan bedroom d'in, daman two bedrooms ne a gidan da parlour d'aya sai kitchen da kuma madaidaiciyar harabar gidan, gida ne mai kyau sosai wanda aka tsara shi da abubuwan more rayuwa.
Mumy tana shige wa bedroom ne afnan ta bita yayin da musaddiq ya sunkuyo dai dai kan mufidah har numfashin su na had'u wa yace
"ba dai har kin gaji da xama babu miji a kusa ba yasa ki tak'ura wa mumy ta kawo ki waje na"
Wayyo wani bak'in ciki ne da takaici ya tokare mufidah kamar ta rushe da kuka saboda abin da ya fad'a mata,kasa magana tayi kawai ta kau da kanta, murmishin mugunta ya saki tare da d'aga kafad'ar shi yace
"anyway duk abin da kike so kin xo inda xa'a share miki hawaye bari naje na dawo 'yammata xan ce ko second hand "
Kasa jure wa mufidah tayi ta tashi a fusace har ta bud'e baki xata yi mishi magana sai kawai ta fasa ta wuce bedroom d'in da mumy ta shiga ashe bashi ne nashi ne sai jin muryar shi tayi yana cewa
"haba mameen afnan saurin me kike ki bari na fara gayyatar ki xuwa d'akin kya shiga "
A xuciye ta jiyo tare da cillo mishi phone d'in hannun ta cikin fusata, yana dariyar k'eta ya cafe wayar a hannun shi, haushi takaici ya k'ume mufidah sai kawai ta rushe da kuka daman kiris take jira, ganin mumy tana kok'arin fito wa daga bedroom yasa musaddiq fit ya fice da sauri yana mamakin saurin kukan mufidah daga tsokana sai kuka.
"lafia mufidah me ya faru ?"
Mumy ta tambaye ta tana d'ago ta daga tsugunnawar da tayi, cikin kukan tace
"ba komai mumy "
"haba mufidah hka kawai mutum baxai yi kuka ba sai da dalili tell me me ya faru kike kuka?
"mumy bige wa nayi a kafa ta "
Kawai ta tsince kanta da fad'a wa mumy hkan, cikin tausayi mumy tace
"Ayyah sannu kin ji "
Gid'a kanta tayi nan mumy ta kama hannun ta suka shige bedroom d'in.
Wanka mufidah take a toilet tana tsiyayar da hawayen takaicin abin da musaddiq yayi mata kuma xai ta rama ita ma, tana tunanin mafitar rama wa har ta gama wanka bata samu mafita ba.
Bayan ta fito ne daga toilet lokacin su mumy da afnan har sun gama shirya wa sun koma parlour, don hka ta shirya a nutse cikin wani wando maroon colour irin wanda yake kwanciya a jikin mutum da wata black T-shirt mai k'aramin hannu akwai kwalliyar xanen heart a gaban rigar da silver colour sai ta sanya wata rigar sanyi wadda tsayin ta iya gwiwa rolling kan ta tayi da black veil kafin ta fesa perfumes ta fito xuwa parlour.
Yana xaune kan dining table ya hango ta kur6ar coffee yake a time d'in da ta fito but sai ya ajiye cup d'in ya tsira mata ido yana kallon ta ba wani make up tayi ba but tayi kyau, da yaga tana kok'arin d'ago kanta yasa shi saurin dauke idon shi daga kanta ya mayar kan afnan .
Har ta k'arasa dining d'in xama tayi kusa da kujerar mumy ko kallon inda yake bata yi ba sai ma wani had'e fuska take abin ma sai ya kusan bashi dariya ganin yanda take cika tana batsewa.
A sace yake jifan ta da wani kallo wanda tsakanin mumy da mufidah ba wanda ya ankara da hkan har suka kammala cin abincin, mufidah ce ta tattare abin da suka yi amfani dashi gyara dining d'in sannan ta wuce kitchen.
Har ta fara wanke kwanukan da suka 6ata ne sai rigar jikin ta ya fara tak'ura mata Co's bata Saba da yin aiki da irin rigar ba sai kawai ta cire ta tare da ajiye ta saman cabinet d'in daga gefe ta cigaba da abin da take hankali kwance.
Musaddiq wanda hankalin shi yayi kitchen inda mufidah take sai kawai ya mik'e tsaye yana cewa
"mumy bari na d'auko ruwa a kitchen "
Yana gama fad'in hka yayi gaba da d'an saurin shi, yayin da mumy ta bishi da kallo tana murmishi tare da girgixa kai tun xuwan shi ta gama karantar shi yanda yake rawar jiki da irin kallon da yake bin ta dashi.
Yana shiga kitchen d'in ya jingina bayan shi jikin bangon kitchen d'in ya hard'e hannun shi a kirjin shi yana aikin kallon ta jin shi yake kamar yaje ya rungume ta a cikin jikin shi ko ya samu relief acikin xuciyar shi da gangar jikin shi, sai da ya kalle ta son ranshi ya more kafin kuma ya bud'e bakin shi yace
"sannu da aiki malama idan kin gama ina buk'atar gyaran bedroom d'ina da bathroom "
Kunnen uwar shegu mufidah tayi dashi ko jiyo wa ba tayi aikin da take ta cigaba kamar batasan da wani mutum a kitchen d'in ba, ganin hkan da musaddiq yayi ne ya sanya shi nufar inda take tare da sanya hannu ya janyo jelar gashin kanta wata er k'arar axaba ta saki tare da runtse idon ta tace
"malam lafiar ka qlau ne da xaka ja min gashi "
Ta k'arasa fad'in hka tana kici kicin kwatar gashin ta da ya rik'e, sai kawai ya janyo ta cikin jikin shi lokaci d'aya ya saki ajiyar xuciya daman abin da yake buk'atar yi kenan shi yasa ya dad'a tsokano ta.
D'aure fuska yayi tare da cewa "ke kina jin ina miki magana ki rabu da ni saboda kin raina ni koh ?"
"ni malam ka cika ni idan ba hka ba xan..... "
Bata k'arasa fad'in maganar ba ya sanya hannun shi ya rufe bakin ta tare da cewa
"me xaki iya yarinya ji yanda kin kasa kwatar kan ki kina wani ma......."
Wata er k'ara ya saki kad'an wadda ta hana shi k'arasa maganar shi ashe mufidah ce ta cije shi a hannun ba shiri ya sake ta kafin yayi wani yunk'urin rik'e ta har ta fice daga kitchen d'in da gudu..............
Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM
LIKE AND COMMENT'S FB PAGE 👇🏻
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
*PAGE 48*
Wani kyakkyawan murmishi ya saki tare da bin hannun nashi da kallo wurin da ta cije shi har wajen ya d'an yi ja, bakin shi ya kai a hankali ya sumbace shi kafin ya fita daga kitchen d'in.
Suna xaune da dare a parlour kallo suke jefa jefa mumy da musaddiq suna er hirar su yayin da mufidah kuma ta fara gyangyad'in bacci a wurin saboda gajiyar da tayi afnan ma tana jikin musaddiq tana bacci.
"mufidah tashi ki tafi bedroom ki kwanta "
Cewar mumy da ta kula da gyangyad'in da take, ai kuwa da sauri ta d'an mik'e ta wuce xuwa bedroom musaddiq ya bi ta da kallo cikin tsantsar kaunar ta.
Maganar da mumy tayi mishi ita ta dawo dashi daga tunanin da ya tafi tana mai cewa
"musaddiq na gaji da maganar da nake maka don ka xo ka d'auki mufidah kak'i tsayawa kana yi wa mutane hanya hanya, dalilin da yasa ni da daddyn ka muka yanke hukuncin kawo maka ita nan, Sauran kuma k'i kula dasu yanda ya kamata ga amanar su nan na baka kada ka wulak'anta min 'ya kaji na fad'a maka "
D'an murmishi ya saki cikin xuciyar shi yana cewa mumy dan bakisan irin son da nake yiwa mufidah ba shi yasa kike fad'in hka, na tabbatar da kinsan irin yawan son da nake mata da baxa ki fad'i hka ba, baxan iya wulak'anta mufidah ba ko wani ne naga xai wulak'anta min ita sai inda k'arfi na ya k'are bare ni, a fili kuma sai yace
"mumy ki kwantar da hankalin ki kada ki damu xan yi duk yanda kike ce "
"Yawwa Alhmdlh naji dad'i da ka fad'i hkan, Allah yayi muku albarka ya baku xaman lafia"
"Ameeen thumma Ameeen mumyn na "
Murmishi mumy ta saki na jin dad'in ganin d'an nata hankalin shi ya kwanta gashi har er k'iba ya d'an yi alamun ya samu kwanciyar hankali da nutsuwa.
"sannan kuma kayi kok'arin sanya afnan a skul "
"angama mumy na "
Sun d'an jima suna hira kafin kuma kowannen su ya tafi d'aki don yin bacci tun da dare yayi.
Ranar musaddiq yayi kwanan farinciki da jin dad'i tun da ga mufidahn shi a cikin gidan, yana son mufidah so irin wanda ba'a iya kwatan tashi so irin wanda baki baxai iya furta shi ba so irin wanda idan ya kama xuciyar mutum baya ta6a iya yi mishi ta sauk'i kai so so ne irin wanda kafin a samu mutum mai irin wannan son akan mace acikin dubban jama'a sai en k'alilan, da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da shi cike da mafarkan mufidah da shi masu dad'i wanda har bai so gari ya waye ba dama xai dawwama a irin hka da yayi farinciki mara misaltuwa.
A hka mumy tayi kwanaki ukun ta, ranar da xata tafi ne da safe suka fita dukkanin su domin raka mumy yin siyayya a mall, da yake jirgin su tashin yammaci xai yi don hka suna gama breakfast suka fito.
A wani babban mall suka yi masauki nan mumy ta fara siyayyan abin da take buk'ata, shi kuma musaddiq ya nufi 6angaren wajen sleeping dress dasu underwears xuwa English wears yana xa6ar duk wanda yayi mishi.
Mufidah kuma da afnan suna tare da mumy suna xa6ar abin da suke so, sam mufidah batasan musaddiq ya nufi 6angaren wajen English wears ba sai ta nufi nan tana d'an dudduba wa, kamar ance ta d'ago kanta ai kuwa tayi mummunan gani da idanun ta, wanda lokaci d'aya wani axababben kishi ya turnik'e mufidah lokacin da ta hango musaddiq rungume da wata mace baturiya a jikin shi.
Gaba d'aya sai ta rasa abin yi har wani duhu duhu take gani a idanun ta sam ta kasa dauke idanun ta daga kansu wani bakinciki da takaici ne ya kama mufidah, d'ago idanun shi yayi musaddiq ya hango mufidah a tsaye waje d'aya kamar wadda aka dasa ta, hannun shi yasa ya janye yarinyar gefe d'aya kafin yayi mata magana ta tsayin second biyar ya nufo inda mufidah take.
Ganin har yaxo inda take batasan ma yaxo wajen ba yasa shi yin tafi da hannun shi biyu a dai dai fuskar ta tare da cewa
"hey are u alright? "
Yana wani shegen murmishi mai da idanun ta tayi kan fuskar shi ai kuwa ya kashe mata ido d'aya tare da d'aga gira, wani bak'in ciki da 6acin rai ne ya sake kama mufidah ganin ko ajikin shi abin da ta kamashi yana yi, ta ma kasa cewa komai ji tayi ya kama hannun ta da hannun shi ai kuwa ta fisge da k'arfi tayi gaba yana yi mata magana amman ko jiyo wa ba tayi ba, wani d'an sanyi yaji cikin xuciyar shi idan dai har hasashen da yayi hka ne to mufidah ta fara son shi tun da abin da ta nuna yanxu yayi alama da kishi, juya wa yayi ya d'auko kayan da ya gama xa6a ya nufo inda su mumy suke.
Waje d'aya mufidah ta samu ta xauna har mumy ta gama siyan abin da take so musaddiq ya biya kudin suka fito, ko kallon inda yake mufidah bata yi ba fuskar ta tayi d'an ja saboda 6acin rai har mumy tana tambayar ta lafia kawai sai ta d'an wayance da fad'in kan ta ne yake ciwo sai sannu mumy take mata har suka k'arasa gida.
Cikin bedroom ta shige ta fad'a toilet ta rufe da key kafin ta kunna shower ruwa ya fara xuba sannan ta fashe da kuka sosai tayi hkan ne don kada a jiyo sautin kukan ta, bata ta6a xaton son musaddiq yayi k'arfi hka a cikin xuciyar ta ba sai yau bata ta6a xaton tana da mugun kishi ba sai yau, taji ana fad'ar kishi amman batasan shi ba sai yau, daman hka musaddiq d'in yake d'an iska ne ma nemin mata, to idan ba ma nemin mata ba mai ya kai shi rungume macen da ba matar shi ba a jikin shi daman abin da yake aikata wa kenan shi yasa ya mak'ale a k'asar waje yak'i dawowa nigeria, ae kuwa baxan iya xama da maxinaci ba dole ya sake ni naje na auri kamilin namiji kamar sadeeq.
Sadeeq baka San halin d'an uwan ka ba ne shi yasa kabar wasiyyar na aure shi me yasa kayi min hka sadeeq ina da kishi baxan iya xama da musaddiq ba, gashi son shi yayi min mugun kamun da ban ankara ba sai da lokaci ya fara k'ure min, tayi kuka sosai mufidah a wannan lokacin abin tausayi gashi sai knocking ake yi a kofar toilet d'in wanda ta sani tsakanin mumy da afnan ne suke yi.
Kan ta ne ya fara wani irin ciwo ga idon ta sun kumbura sosai sun ja dakyar ta iya yin wanka ta sanya wata white d'in rigar wanka kan ta kuma wani k'aramin towel ne ta nannad'e gashin ta, tsayin rigar wankan iya cinyar ta ya tsaya da hka ta bud'e kofar toilet d'in ta fito, d'ago kan da xata yi ta had'a ido da musaddiq a tsaye bakin kofar toilet d'in ya hard'e hannun shi a kirjin shi ya tsurawa kofar toilet d'in ido yana tunani, ganin ta fito ne yasa shi sakin wata ajiyar xuciya tare da cewa
"lafian ki qlau kika shiga toilet kika rufe wajen 1:30 hour kina ciki? "
Wata harara ta dank'ara mishi da idanun ta jawur da suka kumbura, tuni musaddiq ya rikice ya nufi inda take yana cewa
"subhanallah mufidah mai ya sami idanun ki hka? "
Hannun ta ya sake rik'o wa saboda ganin tak'i kula shi ae kuwa ta sanya k'arfin ta ta sake fisgewa cikin dushashshiyar muryar ta tace
"malam ka rabu da ni ina ruwan ka da abin da yake damuna? "
Tana gama fad'in hka ta juya xata cigaba da tafiya ai kuwa ya janyo ta jikin shi ya sanya d'aya hannun shi ta bayan ta ya rik'e ta gam, d'aya hannun kuma ya rik'o fuskar ta 6ata fuskar shi tare da cewa
"ba dai don kin ganni da wata ba ne kika shiga toilet kina kuka, kin fara sona kenan? idan hka ne kuwa ki bawa xuciyar ki shawara ta fitar da sona daga ciki idan kuwa ba hka ba xaki cutar da kanki, don ni musaddiq ba sa'an auren ki ba ne na aure ki ne don cika burin d'an uwa na sadeeq"
Yana gama fad'in hka ya cika ta ya fice daga bedroom d'in, kusan suman tsaye mufidah tayi da jin abin da musaddiq ya furta mata daman ba sona yake ba?, xuciya ta mai yasa kika yi min hka, kika kar6i son mutumin da baya sona, wasu hawaye ne masu xafi suke fita daga idanun mufidah.
Shi kuma musaddiq bedroom d'in shi ya wuce tare da rufe kofar ya jingina bayan shi jikin kofar wasu hawaye ne masu rad'ad'i suka fara xubo mishi dafe kan shi yayi yana cewa
"me... me yasa baki na ka furta wannan furucin wajen masoyiya ta, kamata yayi nayi farinciki mufidah ta fara sona bai kamata nayi mata hka ba, yanxu ta ina xan gyara kuskure na, na rasa yanda akayi na fad'a mata hka nasan xuciya ta da kwakwalwa ta ba hka suke son na furta ba, baki na ne ya furta hkan, I'm so sorry mufidah, ta ina xan fara nuna miki soyayya ta bayan ke matar d'an uwa na ne baxan iya ba baxan iya mufidah ji nake kamar xan ci amanar sadeeq"
Hka ya dunga maganganu cikin mayen son mufidah har xuwa lokacin da bacci ya dauke shi a k'asan carpet d'in d'akin.
Yinin ranar kusan mumy ce da afnan suka yi shi a parlour musaddiq yana bedroom hka mufidah ma har xuwa karfe 5 na yammacin ranar tuni mumy ta gama had'a komai nata ta xaunar da mufidah da musaddiq tana sake yi musu nasiha sosai wanda kowannen su baya kallon d'an uwan shi kansu a sunkuye suna kallon k'asa.
Bayan ta gama yi musu nasihar ne suka fita rakata airport, tun da suka fara tafia mufidah idanun ta suna kan window tana xubar da hawayen bak'in ciki abin da musaddiq ya gama yi mata d'axu gashi mumy xata tafi ta bar su, da hka suka k'arasa airport d'in mumy dai bakin ta bai daina furta musu wad'annan kalaman ba
"kuyi hak'uri da junan ku don Allah ku xauna lafia ban da fad'a da tashi hankali ana yin hak'uri ana kai xuciya nesa, mmusaddiq ga mufidah da afnan nan ka rik'e su amana don su amanar d'an uwan ka ne, ka kula su don kai ne babba kuma namiji a cikin su "
Lokacin da mumy xata shiga jirgi mufidah kasa jure wa tayi ta rungume mumy tana kuka sosai ita ma mumyn kasa rik'e hawayen ta tayi sai da suka fito afnan ma kukan take ganin yanda mumy da mameen ta suke kuka musaddiq ya dauke ta yana rarrashin ta, dakyar mufidah ta cika mumy ta wuce xuwa cikin jirgi ko k'ara waiwaye su ba tayi saboda kada su karyar mata da gwiwa, suna kallo har aka rufe jirgin ya fara tafia kafin ya tashi sama kuma da gudu mufidah ta shige cikin mota tana
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 23