uban kishi don yasan mutane da yawa sun gane mishi mata, kallon picture's d'in kawai yake ji yake kamar yayi tsuntsu ya ganshi a gaban mufidah, sai da ya kalli picture's d'in son ranshi kafin ya turawa da muh'd Cewar
" _Aboki nagode sosai amman ka tabbatar ka goge picture's d'in nan a wayar ka_"
Ya tura mishi ba jima wa muh'd ya turo mishi da reply na dariya kafin yace
" _Hhhh sarkin kishi ae tuni na goge tun lokacin da na turo maka ba sai ka fad'a min ba, ya kamata ka dauki matar ka ko ka dawo nigeria gaba d'aya yaro don wlh aure da dad'i na baka labari yanxu hka gani rungume da sweetheart dina_"
Ya turo mishi hkan tare da alamar gwalo, wani yarrr musaddiq yaji a cikin jikin shi gaba d'aya ya dauke wuta ji yayi wani abu yana ratsa shi wata kasalar ce ta sake lullu6e shi wanda dakyar ya cewa muh'd
" _kai fa wani lokacin d'an air ne kai abin ya dama ni bai dame ni ba_"
Ganin muh'd yana yin typing alamar akwai abin da turo ya sashi kashe datar gaba d'aya don kada ya hargitsa mishi tunani don shi kad'ai yasan abin da yake ji a yanxu dakyar ya iya tashi ya shiga toilet yana cewa
"Muh'd yana neman hargitsa min tunani xuwa wani 6angare na daban wanda bai kamata ace na kasan ce cikin yanayin yanxu ba"
Da hka ya sakarwa kanshi ruwa idanun shi a lumshe mufidah kawai yake hangowa.............
Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
LIKE AND DROP UR COMMENTS FB PAGE
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
_Happy Birthday my billy ladan dear ina taya ki murnar k'arin shekara, Allah ya k'aro shekaru masu albarka, na sadaukar da duk wannan page d'in don murnar wannan ranar, ina miki fatan alkhairi tawan_😍
*PAGE 43*
Daren ranar mufidah bata samu cikakken bacci saboda tunanin auren ta da musaddiq da aka d'aura a yau, ji take kamar a mafarki yau ita ce matar musaddiq mutumin da basa shiri da junan su, me yasa sadeeq ka furta hkan baka san ba ma shiri da juna da k'anin ka ba, taya xamu iya had'a kanmu mu yi xaman aure irin na mata da miji.
Da irin wad'annan tunane tunanen mufidah bacci yayi awon gaba da ita ba tare da ta shirya yin shi ba, musaddiq kuwa ana shi 6angaren ya samu cikakken baccin wanda rabon da yayi irin shi tun lokacin da sadeeq ya furta yana son mufidah, ranar baccin shi yayi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
Washe gari en uwa suka tattafi gida ya rage daga mumy, daddy, mufidah da afnan sai en aiki, duk wani motsin mufidah akan idon mumy don tana son karantar yanayin da take ciki, sai kuma aka ci sa'a mufidah ta fito xuwa parlour fuskar ta wasai da ita sai dai kumburi da d'an ja da idanun suka yi mata, wasa take wa afnan suna dariyar su sosae hkan ya faranta wa mumy rai tana mai fatan wannan auren ya dawwama cikin amincen Allah da farin ciki.
Bayan sati d'aya da auren mufidah da musaddiq ne daddy yayi mata magana da ta cigaba da xuwa hospital kafin musaddiq ya dawo, ae kuwa tayi farinciki sosae da hkan a ranar kuma da dare Dr muh'd yaxo gidan tare da matar shi nafisat.
Mufidah bata wani kula shi ba sai nafisat d'in suke yin hira tsakanin su har mumy ta tashi ta shiga kitchen ta barsu bayan sun gama gaisa wa.
Alama muh'd yayi wa nafisat da hannu kan ta bi mumy kitchen, d'an murmishi tayi tare da Kama hannun afnan suka shige kitchen.
Cikin sanyin muryar shi yace
"mufidah kiyi hak'uri nasan ni mai laifi ne a wajen"
D'an ta6e baki tayi kafin tace "uhm muh'd me yasa lokacin da sadeeq yake bar maka wasiyyar na auri musaddiq baka kirawo ni ba, wlh ba don sadeeq ne ya nemi da ka had'a auren mu da musaddiq ba, da tun ranar da aka d'aura auren xaka sanya a warware shi"
Kallon ta muh'd yake cikin zuciyar shi yana cewa da kinsan son da musaddiq yake miki da baxa ki furta wad'annan maganganun ba, kinsan adalilin ki ya kamu da cutar da bata warke wa ina addu'a da fatan Allah ya kaimu lokacin da musaddiq xai furta miki abin da yake cikin xuciyar shi.
A fili kuwa cewa yayi "nima mufidah alk'awarin da na d'aukar sadeeq shi yasa na cika shi, tun daga lokacin da aka d'aura auren naji kamar an cire min wani abu a jiki na da kaina lokacin naji hankali na ya kwanta sosae mufidah "
D'an ajiyar numfashi yayi kafin ya cigaba da cewa
" ina sake baki hak'uri ni dai a adaina fushi dani, sannan kuma naji daddy yayi min maganar komawar ki office ranar monday koh ? "
Cikin sanyi tace "ehhh nima d'axu ya sanar da ni"
"hakan yayi kyau Allah ya taimaka, tun da mun shirya a sakar min fuskar mana irin wannan d'aure fuskar ae sai ki sa na dunga rawar jiki saboda tsoro ki sa matata da mijin ki su raina ni "
Dole tasa ta d'an saki fuskar da murmishi wanda har sai da dimples d'in ta suka lotsa kafin kuma ta harare shi jin ya k'arasa maganar da mijin ta musaddiq.
Er dariya muh'd yayi yana fad'in ko ke fah "
Nan kuma suka cigaba da Er hira har xuwa lokacin da su mumy suka fito a kitchen, sun d'an jima a gidan don sai wurin 9:30 na dare suka tafi bayan sun yi dinner har farfajiyar gidan mufidah ta rako shi suka yi sallama suka tafi ita kuma ta dawo gida.
Acikin hka mufidah ta Fara xuwa hospital tana cigaba da aikin ta cikin kwanciyar hankali kuma hkan ba k'aramin d'ebe mata kewa yake ba don ta d'an rage tunani sosai.
Kamar yau ranar weekend ce mufidah babu aiki tana kwance kan bed bata jin dad'in jikin ta tun safe ga wata muguwar fad'uwar gaba da take damun ta tun safe, afnan ma da ta dame ta da surutu korar ta wurin mumy tayi.
Shigowa mumy tayi cikin bedroom d'in hannun ta rik'e da mayafi alamar fita xata yi, Kallon mufidah tayi fuskar ta dauke da murmishi tace
"mufidah na gama shirya wa xamu tafi, na rasa dalilin da ya hana ki bin mu gashi har afnan xamu tafi "
D'an murmishi mufidah tayi tare da tashi daga kwancen da take tace
"kiyi hak'uri mumy kin ga ranar monday ina da aiki na safe kuma xamu yi muhimmin meeting ranar shi yasa "
Da yake london su mumy da daddy xasu je wajen dubiyar wani babban abokin daddy da aka kwantar dashi acan, sun nemi da mufidah ta shirya su je ta k'i yarda kuma kwanaki uku kawai xasu yi su dawo.
"kin fison dai xaman kawai naga alama, xaki xauna anan ko gidan umma xaki je? "
Da sauri mufidah ta girgixa kai tana d'an waro idanun ta tace
"a'a mumy yanxu xan shirya nima na tafi, baxan iya xaman gidan nan ni d'aya ba tsoro nake ji "
Er dariya mumy tayi tare da Cewa ""shikenan 'yata ki kular min da kan ki sai mun dawo "
Tashi tayi ta sanya hijab d'in ta suka fito parlour inda daddy yake xaune,bayan mufidah ta gaida shi ne ya amsa cikin fara'a kamar ko yaushe tukunna suka fito xuwa farfajiyar gidan suka shiga mota driver xai kai su airport.
"ki kula da kan ki 'yata kin ji "
Fad'in mumy a karo na biyu, murmishi mufidah tayi tana jin dad'in yanda mumy take bata kula wa tace
"tohh mumy insha Allah, Allah ya kai ku lafia "
"Ameeen ya rabbi "
Mumy da daddy suka amsa, afnan sai d'ago wa mufidah hannu take alamar bye bye ita ma hannun ta d'aga mata har suka motar su ta fita daga gidan.
Bayan ta dawo cikin gidan ne ta shige bedroom had'a kayan ta tayi wad'anda xata yi amfani dasu, sai ta d'an kwanta don ta huta har kewar afnan da mumy sun fara Kama ta.
Bata ankara ba taji wani bacci mai dad'i yana fisgar ta bata yi wani 6ata lokaci ba ta gyara kwanciyar ta nan da nan bacci yayi awon gaba da ita.
Yini tayi tana baccin idan ta farka ma sai taji wata kasala kafin ta tashi wani baccin ya sake d'aukar ta da yake tana period kawai sai ta koma baccin, har xuwa wajen biyar na yamma dakyar ta iya tashi ta samu tayi wanka ta gyara jikin ta cikin wata arabian abayat ash colour tayi rolling kanta da black veil tayi kyau sosai different perfumes tayi amfani dashi daga body sprays har xuwa na kaya.
Sauri kawai take don ta tafi kada mangarib tayi mata, jakar da ta shirya kayan nata ta dauko tare da car keys sai phone nata, a parlour ta tsaya don jin k'amshin girki cikin mamaki ta nufi kitchen d'in.
Er dattijuwar da take taimaka wa mumy ta hango tana tsaye gaban gas cikin mamaki tace
"Inna wa kike yiwa girki? "
Da yake ko mumy da Inna take kiran ta dattijuwa ce mai kirki, jiyo wa tayi fuskar ta dauke da murmishi tace
"ah mufidah ina xuwa hka gab da mangarib ke da nake yiwa girki ganin yinin yau baki ci komai ba"
"tabbb ae ni Inna nan da kika ganni sai gidan mu kuma "
Rik'e ha6a tayi tare da cewa
"yanxu mufidah baxa ki xauna mu yi xaman mu ba kwana uku kawai xasu yi fah "
Murmishi mufidah tayi tare da cewa
"na kwana biyu ban je naga ummana da abbana kewar su nake gwara na tafi can "
"toh ae shikenan amman sai kin jira na gama miki girkin kici sai ki tafi "
Bata son gardama da babba ba don hka ba ta fison ta tafi taci abincin umman ta, gashi innar tana sonta gata da kirki don hka sai ta ce
"tohh inna ina jiran ki a parlour "
"toh d'iyar kirki "
Fita tayi ta koma parlour tana danna wayar ta sai daf da wurin sallahr ishsha inna ta kawo mata faten dankalin turawa da tayi mata yasha nama da su vegetables sai k'amshi yake ga lafiyayyen kunun aya mai sanyi a gefe, da yake inna tasan yanda mufidah take son kunun aya shi yasa wani lokacin take yi mata saboda kirkin da mufidah take mata.
Xama sosai mufidah tayi tana cin abincin, tuni inna ta wuce 6angaren su na masu aiki, cikin abincin mufidah take cikin jin dad'in shi.
Ko rabin wanda ta xubo a plate bata yi ba taji an turo kofar palourn an shigo kafin ta jiyo taji saukar wata daddad'ar murya a kunnen ta muryar da ta kusan sanya ta suman xaune ko bata jiyo ba tasan ko muryar wane ba wani ba sai *Musaddiq*, muryar da ta fara taso mata da wani kwantaccen abu a ranta, muryar da ta sanya ta tunanin abin da ya dad'e da wuce wa a wajen ta.
Sam ta mance ma da sallamar da aka yi saboda duniyar tunanin da ta lulu cikin ta, wata firgita tayi tare da sakin ajiyar xuciya da k'arfi jin saukar wani abu mai shegen sanyi a jikin ta .
Da sauri ta d'ago kanta suka had'a ido da musaddiq fuskar nan a d'aure, ita ma mufidah d'aure fuskar tayi musamman yanda ya 6ata mata jiki da kunun ayar nan, cikin xuciyar ta take cewa shikenan shima ya tuna ya rama abin da ta ta6a yi mishi, a d'an fusace tace
"waiii malam lafiar ka qlau da xaka xuba min abu a jikina? "
Wata harara ya watso mata tare da cewa
"kina jin ina sallama kin min shiru ne, shine nayi abin da ya kamata"
Haushi ya turnik'e mufidah ta bud'e baki xata yi masifa sai taga har ya juya ya fara hawa stairs wani tsaki taja mtsww saboda ba k'aramin kular da ita yayi ba yanxu sai ta sake wani sabon wankan.
Ita ma a fusace ta fara hau stairs d'in ta nufi bedroom d'in ta a gurguje tayi wanka ta fito tare da sake shirya wa cikin wata black arabian abayat gown tayi da sauri ta gama shirya wa ta fito xuwa parlour.
A xaune ta ganshi kan kujera har yayi wanka ya canja kaya xuwa white 3quater da white vest hannun shi rik'e da waya yana daddana wa, kallo d'aya tayi mishi ta kauda kanta tana k'unk'uni tana cewa k'ato da kai xaka xauna wa mutane cikin parlour ko kayan kirki babu a jikin shi, cikin xuciyar ta take maganar ta.
Bag d'in ta ta dauka tare da phone da car key tayi hanyar fita daga palourn ganin hka yasa shi cewa
"keee ina xuwa da daren nan?"
Banxa tayi dashi ta fice daga palourn da sauri ae kuwa shima ya tashi ya bita.
Tana kok'arin bud'e kofar motar ya cimmata hannun shi yasa ya jiyo da ita da k'arfi wanda saboda k'arfin da ya sanya ya janyo ta sai da ta fad'a kan kirjin shi.
Lokaci d'aya duk wani motsin su ya tsaya cak sai numfashin su da suke iya fitar wa da bugun xuciyar su da ya tsanan ta bugu, sun dauki wajen mintuna biyar a hka kafin mufidah tayi saurin janye cikin ta cike da masifah tace
"lafiyar ka kuwa da xaka janyo ni hka idan da na fad'i naji ciwo fah?"
Shima fuskar shi a d'aure yace " ina xaki je yanxu? "
Cikin hararar shi tace "inda ka aike ni"
Hannun shi yasa ya kamo nata ya murd'e har sai da mufidah ta saki k'ara saboda xaki cikin kakkausar murya yace
"idan baki fad'a min ba i will slap u wlh ina wasa da ke da xan tambaye ki kina min tsiwa "
"ni malam ka cika ni gidan mu xan tafi "
"babu inda xaki je "
Wani kallo ta watsa mishi tana cewa "tabbb ae kuwa ba isa ka hana ni xuwa gidan mu b...... "
Kafin ta k'arasa fad'i abin da xata ce taji ya dauke ta cak ya fara tafia xuwa hanyar shiga palourn gidan.............
Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻Exclusive writers forum
Like and drop ur comments fb page
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
_where are u guys this page is dedicated to u, action baby, beeboh, meelat Ahk, bilkisu BK, Mareeyah baba, wannan shafin na ku ne kyauta ina muku fatan alkhairi a duk inda kuke._😍
*PAGE 44*
Kafin ta k'arasa fad'in abin da xata ce ta ji ya dauke ta cak ya fara tafiya xuwa hanyar shiga parlourn gidan, bakinciki ya Kama mufidah ganin yanda ya wani dauke ta kamar wata yarinyar shi nan ta fara wutsil wutsil da kafafun ta alamar ya sauke ta, amman ko sauraren ta bai yi ba sai da ya dire ta a parlour sannan yaje ya sanya wa parlourn key ya xo xai shige xuwa stairs.
Cikin tsiwa mufidah tace
"wai kai ina ruwan ka ne malam ka kyale ni na tafi gidan mu dare nayi min "
Ganin ko kula ta bai yi ba yasa ta bin shi tana mishi tsiwa unexpected taji tayi karo da k'aramin center table wanda ake ajiye wa a gefen kujera, tafiya tayi luuuu xata fad'i batasan lokacin da ta saki ihu ba.
Jin ihun ta yasa shi jiyo wa da sauri ganin tana kok'arin fad'uwa yasa shi tafiya da gudu xuwa inda take, akan hannun shi ta fad'o, wani ajiyar xuciya ta sauke jin bata fad'i k'asa ba bud'e idanun ta tayi a hankali wanda tun lokacin da taci tuntu6en xata fad'i ta runtse su.
Had'a idanun su suka yi cikin wani irin yanayi suke kallon junan for some minutes kowannen su yana sak'a abu cikin xuciyar shi, gaba d'aya sun tsunduma cikin Kallon junan su kafin mufidah ta fara dawowa hayyacin ta fara kici kicin kwatar jikin ta, hkan da take yi ne yasa shi ma tuna a yanda suke don hka kawai sai jikin shi yayi sanyi lokaci d'aya har ya kasa rik'e ta.
Kawai sai ya sake ta baxato mufidah taji ta a k'asa tummm ta buge kanta da kujera, wani xafi taji ya ratsa ta kafin tayi yunk'urin dawo wa dai dai daga xafin da taji tuni musaddiq ya haura stairs ya shige cikin bedroom d'in shi xuciyar shi tana cikin wani yanayi daban lallai mufidah ita ce rayuwar shi samun ta a rayuwar shi yanxu ba k'aramin samun cigaban shi ba ne ko da ta 6angaren xuciyar shi wajen bata abin da ta ke so.
Mufidah kuwa saboda takaici sai kawai ta rushe da kuka ga takaicin hana ta xuwa gidan su, ga xafin bugewar da tayi ga kuma tsananin tsoron yanda xata iya kwana a wannan gidan babu mumy, daddy da afnan.
Ta dad'e sosai anan xaune tana kuka har daga karshe ta fara gyangyad'in bacci ba wani dad'e wa bacci yayi awon gaba da ita a wurin ta tukunkune jikin ta waje d'aya tamkar mai jin sanyi sai faman sauke ajiyar xuciya take saboda kukan da ta jima tana yi.
Kwance yake kan bed ya kasa bacci sai faman juyi yake ya tunano irin Kallon da suka yi d'axu shi da mufidah, a yanda ya kalli cikin kwayar idon ta bai hango wani abun da xai danganta shi da ko tana son shi, uhm uhm musaddiq kada kayi wannan tunanin yanxu don ba kaini masoyin ta na farko ba, ba lallai ace yanxu ta fara son ka ba tun da kwata kwata yaushe aka yi auren da har xata fahimci ko kai wani dole komai sai a hankali, d'an cije lip's d'in shi yayi na k'asa kafin ya bud'e bakin shi a hankali ya furta
"i luv u mufidah with all my heart "
Kamar an mintsine shi ya tashi xumbur da sauri ya fito xuwa down stairs yana k'arasa wa ya hango mufidah kwance a k'asa tana baccin ta, a hankali ya k'arasa wajen da take ya tsugunna yana k'are mata kallo cikin tsantsar kaunar ta.
Sai da ya Kalle ta son ran shi ya more tukunna ya sanya hannun shi dukka biyun ya dauke ta gaba d'ayan ta ya nufi stairs da ita, idanun shi akan beautiful face d'in ta kafin ya mayar dasu kan cute pink lips d'in ta wanda har sai da ya lashe lip's d'in shi saboda jin yanda wani abu ya tsarga mishi lokaci d'aya, a hankali ya kwantar da ita kan bed tare da gyara mata kwanciyar ya lullu6e ta da lallausan blanket daga kafafun ta xuwa wuyan ta ya bar fuskar ta a waje, hasken d'akin ya rage mata kafin ya tsugunna yana k'are mata kallo cikin tsantsar kaunar ta, xuciyar shi ta ingixa shi har ya kai bakin shi kan lallausan kumatun ta ya sumbace ta tare da saman goshin ta xuwa pink lips d'in ta, wani irin shock yaji a jikin shi lokaci d'aya abin da bai ta6a yi ba a tsayin rayuwar shi da wata mace sai akan mufidah,dukka da mufidah tana bacci sai da taji canjin yanayi a jikin ta da xuciyar ta wanda bata ta6a jin shi ba, motsi ta fara yi da sauri ya matsa daga saitin fuskar ta sai da yaga ta juya ta koma baccin ta tukunna ya sake dawo saitin fuskar ta tare da furta
"i luv u mufidah!"
Yana gama fad'in hka ya fita daga d'akin ya bedroom d'in shi ya tafi ya kwanta, sam kasa bacci musaddiq yayi a wannan daren sai juyi yake kissing d'in da ya yiwa mufidah ne ya taso mishi da wani irin canjin yanayi a jikin shi, ya xama dole ya nemi mafita don ya gaji da jin shi a wannan yanayin xai nutsu ya sami wata babyn ya aura ko ta d'ebe mishi kewa tun da shi ba neman mata yake ba sannan baxai iya tunkarar mufidah da buk'atar shi ba don hka gwara ya nemi mafita, wannan tsayin daren da hka yayi shi cikin tsantsar begen kasance wa da mufidah yana rufe idon shi ita yake hango wa.
*WASHE GARI*
A hankali ta fara bud'e idanun ta xuwa d'an lokaci kad'an ta gama bud'e su tas, cikin sauri ta mik'e xaune da mamaki take bin d'akin da kallon ita tasan a parlour bacci ya dauke ta a k'asa, sai gashi ta tashi ta ganta saman bed acikin bedroom d'in ta har da lullu6e ta da blanket, lokaci d'aya kuma abin da ya faru tsakanin ta da musaddiq ya fad'o mata wani tsaki taja tare da cewa
"watak'il shi ya kawo ni bedroom, d'an rainin wayo ko me ruwan shi da kawo ni d'aki ya rabu da ni inda ya ganni "
Ta k'arasa fad'i tana murgud'a bakin ta nan tayi ta mita har dai ta gaji ta nufi bathroom don tayi wanka tun da wanda take mitar don shi ba jin ya yake ba, ta d'an jima a cikin toilet kafin ta fito shirya kan ta tayi cikin wata blue black swiss atampha d'inkin riga da siket ne sun xauna a jikin ta sosai, light make up tayi tare da d'aura d'ankwalin ta wanda har sai da wani yanki na gashin ta ya fito, tayi kyau sosai abin ta perfumes da humra masu kamshi tayi using dasu kafin ta fito xuwa parlour.
Tana fito wa daga bedroom d'in ta shima musaddiq ya fito yayi gayun shi cikin jeans blue and white T-shirt long sleeves yayi kyau sosai sai tashi k'amshin perfumes yake.
Kallo d'aya kowannen su yayi wa d'an uwan shi suka kau da kai xuciyar su na bugu wa da k'arfi, kusan lokaci d'aya suka fara sauka na steps d'in stairs, sai dai musaddiq ya riga ta sauka xuwa cikin parlour.
Tun daga nesa muh'd ya hango su wanda yake xaune cikin parlour ba k'aramin kyau suka yi mishi sun yi matuk'ar dace wa da junan su, tuni ya hau washe baki don son yin tsokana, ae kuwa musaddiq ya sake 6ata fuska don kada yayi mishi shirme gaban yarinyar nan ta raina shi.
Tsab muh'd ya fahimce shi ae kuwa ya tuntsire da dariya tare da cewa
"guy ka birge ni sai da ka ga mumy da daddy basa nan shine ka taho don ka ci angoncin ka son ran ka koh, anyway duk da hka xan fad'a wa su mumy don su sani su fara shirin tar6ar jika don da ganin yanda kake rawar jikin nan da bayani gashi sai wani shek'i kake alamar jiya an bawa soyayya hak'ik'in tun da nasan abokin nawa ba rago ba ne "
Da muh'd yaga yanda musaddiq yake jefo mishi harara da ya katse xancen da yake xubo wa kamar xarbi ya tsince, wata dariyar k'eta ya sake yi yana Kallon musaddiq tare da cewa
"ae gaskia na fad'a malam ka daina harara, ko don hka ka kirawo ni na gasa ka tun da nasan kai farin shiga ne koh? "
A fusace musaddiq ya kalli muh'd yace "are you stupid muh'd da xaka sani gaba kana yi min wata magana ta daban sai kasa yarinya taxo tana raina ni "
Muh'd ya bud'e baki kenan xai yi magana yaji saukar muryar mufidah tana gaida shi, cikin fara'a ya amsa tare da tsokanar ta kamar yanda yayi wa musaddiq sai dai na mufidah da banbanci da na musaddiq, bata kula shi ba ta wuce kitchen abin ta............
Nan dai muh'd yasa musaddiq a gaba sai tsokanar shi yake tun yana hararar shi har ta kai ya fara murmusa wa ko breakfast bai tsaya yi ba suka fita daga gidan shi da muh'd, wannan damar mufidah ta samu kuwa tayi saurin fito wa daga kitchen daman babu abin da take sai addu'a acikin xuciyar ta Allah yasa musaddiq ya fita, ae kuwa suna fita da gudu ta haura stairs ta d'auko bag d'in ta da hijab sai phone nata da car key ta fito, nan ta shiga motar ta tayi mata key, horn tayi wa gate man ya bud'e ae kuwa taja motar kai tsaye gidan su ta nufa, xuciyar ta cikin farincikin ta samu damar guduwa baxata k'ara dawowa ba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 23