abin da tace wa mufidah girgixa kai kawai umma tayi cikin xuciyar kuwa tana mai fatan Allah ya bawa 'yarta miji nagari kamar sadeeq.
Dakyar nabilah ta rarraso mufidah har ta fito xuwa parlour suka cigaba da hirar su,har xuwa lokacin da Abba da Yah Omar suka dawo daga aiki bayan sun gaisa suka had'u suna ta6a hira.
Sai wurin 6 na yamma mufidah da afnan suka bar gidan, lokacin da suka dawo sosai mumy tayi farinciki daman duk gidan yayi mata girma ba en hira.
Sai bayan mangarib sannan muh'd ya xo sun yi hira sosai da mufidah kafin daga k'arshe ya xube wa su mufidah da afnan kayan shopping d'in da yayi musu har wurin mota mufidah ta raka shi kamar wasu masoya suka yi sallama ya tafi.
Bayan sun gama yin dinner ne ta nufi bedroom d'in ta wanka tayi wa afnan ta shirya ta cikin sleeping dress ta kwantar da ita tare da yi mata addu'a ta lullu6e ta da blanket, tukunna ta nufi toilet tayi nata wankan ta gyara jikin ta cikin kayan bacci sannan ta kwanta tare da yin addu'a ta janyo afnan xuwa jikin ta rungume ta tayi tare da fad'a wa kogin tunani wanda ya xame mata jiki tun bayan rasuwar sadeeq murmishin shi maganar shi take tunano wa da hka bacci mai nauyi ya dauke ta.
************
Dare ne sosai wajen misalin karfe 2 na dare wani mummunan mafarki musaddiq yake wanda ya haddasa mishi farka wa a matuk'ar firgice ga wani uban gumi da ya had'a xuro kyawawan k'afafun shi yayi k'asa yana xaune kan bed din tare da dafe kan shi da yake matukar sara mishi da ciwo.
Hasken d'akin ya kunna ko ina ya haske d'akin dafe kanshi yayi yana tunano mafarkin da yayi, mufidah ya hango xaune cikin wani kyakkyawan garden tana xaune tasha kwalliya cikin wata red gown mai siririn hannu gashin ta yasha gyara ta sake shi bayan ta bata sanya ribbon ba dariya take tana watsa wasu kyawawan furanni red colour's sama suna dawowa jikin ta sai dariya take mai ban sha'awa.
Kok'arin k'araso wa wajen ta yake shima yana wani murmishi but ya kusan k'araso wa don bai fi sauran taku uku ba sai kawai ganin wani yayi ya k'arasa inda take ya mik'o mata hannun shi ta sanya nata a cikin nashi.
D'agowar da xai yi mutumin musaddiq ya hango fuskar shi tuni jikin shi ya dauki rawa wani gumi ya jik'e shi hankalin shi yayi masifar tashi ganin fuskar muh'd, kafin yayi wani yunk'uri tuni sun bar wajen.
Shine ya tashi a firgice gaba d'aya ya rud'e kada wannan mafarkin nashi ya xama gaskia idan hka ne kuwa da shikenan ya mutu, baisan son mufidah gama da xuciyar shi ba sai yanxu wani masifafen kishin ta yake ji a xuciyar shi yasan yanxu hka suna can suna soyayya da muh'd tun da yasan ba irin rarrashin da muhd bai yi mishi ba kan ya amince ya aure ta ya tubure yak'i yarda har yayi fushi dashi sai dakyar ya rarrashe shi ya sakko daga Fushin da yayi.
So shine ya samu hangar nuna mata so anya muh'd ya san irin adadin son da yake yi wa mufidah ya dauki alkawarin baxai rasa ta a karo na biyu ba ya xama dole ya tattara ya koma Nigeria (hmmm reader's kuji musaddiq da wani tunani ko yaushe muh'd yace mishi son mufidah yake, kuma da bakin shi ya fad'a wa muh'd d'in kan cewa baxai ta6a iya aurar matar da yayan shi ya mutu ya bari ba, muje dai xuwa akwai gwarama).
Ranar kuwa musaddiq bai iya wani koma wa wani bacci ba ya xurfafa a tunani son mufidah ya dawo mishi sabo fil acikin xuciyar shi gaba d'aya gani yayi garin yak'i saurin waye wa don ya matsu yaga ya fara tattara inashi inashi xuwa nigeria auren mufidah xai yi ko tana so ko bata so shi dai ya ganta ta xama mallakin shi ba wanda xai iya auren ta idan yaso sai ya auri wata yayi xaman auren da ita, mufidah kuwa ta rik'e mishi afnan tana kula da ita.
Bayan gari ya waye ko breakfast bai iya yi ba tuni yayi booking din jirgi don hka yanxu shirya kayan shi yake yana cikin hka yaji wayar shi na ringing ganin sunan muh'd yasa musaddiq sakin wani wawan tsaki don gaba d'aya wani bala'in haushin muh'd d'in yake, sai da yayi 3 missed call's a na hudun ne ya dauka ko magana bai iya yi ba sai muh'd d'in yace
"Ya guy dafatan kana lfy?"
Dakyar ya iya bud'e baki yace
"Qlau nake "
D'an murmishi muh'd yayi ganin yanda musaddiq yake amsa mishi maganar.
"Yau na tashi cikin farinciki Friend kasan abin da ya faru?"
Sai da musaddiq ya ta6e baki kafin yace
"Ina fa xan sani ina nan"
Ya fad'a yana yatsina fuska don hirar da muh'd ta fara Isar shi, gid'a kai muh'd yayi kamar yana ganin shi yace
"Kuma hkane fah, aboki ka taya ni murna mufidah ta amince xata aure ni yanxu hka ma iyaye sun shiga maganar"
Daskare wa musaddiq yayi awurin ko motsin kirki ya kasa yi.......
_toh reader's ku jira ni xuwa pagen d'in gaba don kamar yanda musaddiq ya daskare hka nima na daskare saboda tsabagen yanda maganar muh'd ta rud'a ni_
Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_my Asy khaleel ina taya ki murnar xagayowar ranar haihuwar ki Allah k'ara shekaru masu albarka ya kare ki daga sharrin mak'iya, ina kuma taya ki murnar fara new nvl d'in matar fayrouz yanda kika fara lafia Allah ya baki ikon gama shi lafia ni d'in taki ce Aishat ke miki fatan alkhairi._
*PAGE 39*
Daskare wa musaddiq yayi awurin ko motsin kirki ya kasa yi saboda tsabar mamakin abin da muh'd ya fad'a mishi gaba d'aya jin shi yake kamar mafarki ne xai farka yanxu, amman yana rok'an Allah kada ya k'ara nuna mishi wannan mummunan mafarkin har abada.
Amman jin sautin muryar muh'd yana fad'in "hello friend kana jina ?"
Yasa shi tabbatar da ba mafarki yake ba gaske ne, kafafun shine suka kasa daukar shi yasa shi xube wa akan lallausan carpet d'in da yake tsakiyar d'akin, Lokaci d'aya wani axababben ciwon kai ya tsarga mishi gumi ne ta ko'ina yake kamar wanda yake tsakiyar rana mai xafin gaske.
Ya rasa tunanin da xai fara saboda yanda gaba d'aya yaji brain d'in shi ta tsaya da aiki,a hankali wayar ta subce daga hannun shi ta tarwatse a k'asa yana jin muryar muh'd yana mishi magana but bakin shi yayi matukar yi mishi nauyi ya kasa tunanin kalma d'aya da xai furta.
Ya kai wajen mintuna 50 a hka baisan me yake ciki ba don shi wani time d'in yana daukan mafarki ne nan da anjima xai farka, yana kwance rgingine hannun shi d'aya dafe da kanshi wanda yake mishi ciwo sosai yana jin yanda phone's din shi suke k'ara alamar kira but bai da k'arfin tashi har ya dauka yayi magana.
"Aboki ka taya ni murna mufidah ta amince xata aure ni yanxu hka ma iyaye sun shiga maganar"
Maganar da muh'd yayi mishi take mai kuwwa akunne tamkar yanxu yake mishi, lokaci d'aya wani k'arfi yaxo mishi ya yunkura ya tashi xaune cikin karfin sautin magana yace
" Nooo muh'd kada kayi min hka kasan yanda nake son mufidah kafi kowa sanin halin da na shiga lokacin da Yah sadeeq ya aure ta kafi kowa sanin son da nake mata daga karshe abin da xaka saka min dashi "
Sai kawai ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi xuciyar shi tana wani irin bugawa da sauri da sauri wani irin yanayi ya shiga lokaci d'aya dakyar ya iya saita kanshi ya lalubo addu'a a bakin shi yana yi hawaye na xuba daga idanun shi.
A hankali ya fara jin nutsuwa tana saukar mishi xaxxa6i kuma mai xafin gaske ya rufe shi kudundune wa yayi a waje d'aya ya takure jikin shi kamar wani yaro k'arami, can kuma sai naga ya saki wani murmishin yak'e yana cewa
"Muh'd mace baxa ta had'a mu baxa ta iya raba amincin dake tsakanin mu da kai ba na bar maka mufidah har abada gwara na bi Yah sadeeq nima don na huta da wannan duniyar tamu mai cike da tashin hankali"
Hka yayi ta sumbatu shi kad'ai har wani nauyayyen bacci ya dauke shi a wurin da ganin baccin kasan ba wani jin dad'in shi yake ba.
Bai farka ba sai yammaci sosai bathroom ya shiga yayi wanka tare da daura alawala ya fito jallabiya white ya xura tare da gabatar da sallahr da ake binshi bayan ya gama ya kwanta kan abin sallahn yana tunanin ta yanda xai fitar da mufidah daga cikin xuciyar shi gaba d'aya ya huta ma yana tunanin hawaye suna xuba daga idanun shi.
Wayar shi ce ta dauki k'ara akaro na ba adadi sunan mumy ne akan screen d'in picking d'in wayar yayi tare da sawa a hands free cikin sanyin murya mai tattare da damuwa ya gaida mumyn, jin muryar shi da tayi a hka sai taji hankalin ta ya tashi don hka tace
"My son what happened to u naji voice d'in ka very cool ?"
"Mumy ba wani abu just ina fama da ciwon kai ne throughout ko fita ban yi ba"
"No son da akwai damuwa a tattare da muryar ka, fad'a min matsalar ka baka da wadda ta fini don hka tell me "
Shiru yayi ya kasa sanar da ita abin da yake damun shi ,to mai xaice mata shi? Yana son matar Yah sadeeq nooo baxan iya fad'a miki ba mumy never! wannan abin kunya ne na bud'e baki na fad'a.
"Son ina sauraren ka fah"
"Mumy I don't know, just sometimes ina yawan tunanin ku ne kewar ku ce take damuna"
Shiru mumy tayi acikin xuciyar tana mai mamakin d'an nata da kafiya akan abin da yake so tasan dalilin shiga damuwar shi saboda muh'd xai auri mufidah, amman sai ta basar tace
"Okay son kadai na damuwa kaji bana son ganin ka cikin damuwa "
"Okay mumy ina daddy da afnan?"
D'an murmishi tayi kafin tace "daddy yana nan qlau hka ma afnan"
"Kusan 2 day's bamu yi waya fah ya daina damuwa da ni ko mumy?"
Er dariya tayi mumy kafin tace "daddy yana damuwa da rashin d'an sa mana yanxu hidima ce tayi mishi yawa "
Cikin mamaki yace "wacce hidima ?"
"Hmm ta aure mana xai aurar da 'ya'yan shi guda uku nan da two week's"
"Wanne 'ya'yan shi kuma mumy?"
Musaddiq ya tambaya cikin matukar mamakin abin da mumy tace
"Ohhh ya Allah daman bai fad'a mata ba mun xa6a maka matar da xaka aura sannan kuma muh'd da mufidah sun had'a kansu xasu yi aure"
Tun da mumy ta fara maganar musaddiq ya xama kamar mutum mutumi don ko kwakkwaran motsi ya kasa yi kafin kuma yace
"What! Mumy ni xaku yiwa aure da yarinyar da ban sani ba?"
"Yes! son kak'i mai da hankali wajen xa6ar macen da xaka aura don hka a matsayin mu na iyayen ka mun xa6a maka mace mai tarbiyya da ilimi wadda xata xauna da kai tsakani da Allah"
Jin shiru musaddiq bai yi magana ba yasa mumy tace
"Hello son are u on the line?"
Musaddiq wanda hawaye suke xarya akan fuskar shi yasa hannun shi ya gobe tare da saita muryar shi yace
"Mumy ngde da xa6in ku hak'ik'a ina alfahari da ku matsayin iyaye na nasan baxa ku xa6a min abin da xai cutar da ni ba Allah ya saka muku da mafificin alkhairi"
Gaba d'aya jikin mumy yayi matukar yin sanyi da abin da musaddiq yace mata idan ba hka suka yi mishi ba baxai yi aure yanxu ba ita kuma tana son ganin jikokin ta da yawa yanda Allah bai basu yawan haihuwa ba tana rokan Allah ya bawa musaddiq 'ya'ya da yawa, ajiyar xuciyar ta sauke a hankali cikin sanyin murya tace
"Ameeen son Allah yayi maka albarka ya baku xaman lafia da matar ka naji dad'in yi mana biyayya da kayi Allah ya baka yara masu yi maka biyayya ina alfahari da ke, insha Allah duk wani farincikin ka da walwalar ka suna daf da dawowa kamar da ka kwantar da hankalin ka son"
A hankali ya bud'e bakin shi yace "Ameeen mumy"
A cikin xuciyar kuwa cewa yayi mumy yanxu na fara shiga damuwa wane kwantar da hankali xan yi kuma bayan na rabu da farinciki na muradin raina.
Da hka suka yi sallama da mumy, yana ganin kiran muh'd but yak'i daga wayar daga karshe ganin yak'i dauka yasa muh'd rubuta mishi text message kamar hka," _My Friend ka dauki waya na please kasan kuwa halin da nake ciki da kin daga waya ta da baka yi ina cikin damuwa aboki?_
Wani tsaki yaja bayan ya gama karanta wa gaba d'aya wani irin haushin muh'd yake ji, shi yasan damuwar da ya jefa xuciyar shi yasan me yaji lokacin da yake fad'a mishi xai auri mufidah kuwa?, reply yayi mishi da cewa
" _kayi hak'uri aboki baxan iya daukan wayar ka ba sai xuwa wani d'an lokaci akawai dalilin hka kada ka damu, Allah ya tabbatar da alkhairi a auren ka"_.
Yana gama typing d'in message d'in yayi sending bayan ya tafi sai kawai yayi switch off d'in duka phone's nashi ,tukunna ya kwanta yana jin wani irin yanayi atattare dashi shi kenan na rabu da mufidah a karo na biyu na dad'a yin sake kuma nasan wannan saken da nayi na har abada ne, wasu sababbin hawayen ne masu xafi suke fita a idanun shi..........
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
*PAGE 40*
A wani matuk'ar tashin hankali da firgici mufidah ta mik'e tsaye hawaye na fita a idanun ta tana mai girgixa kanta saboda tsabar shiga rud'u da tashin hankali ta kasa magana sai girgixa kai, mumy ce ta tashi tare da rik'o hannun ta xaunar da ita tayi tare da goge mata hawayen fuskar ta da suke xuba da tissue d'in da xaro amman kamar bata goge wa saboda hawayen basu tsaya ba.
Kunnen tane suke amsa kuwwar maganar da abban ta ya gama yi mata yanxu bayan sun gama gaisa ne dashi da umman ta ga mumy,daddy a xaune a palourn sai ita ya fara da cewa
"Mufidah na gaji da yi miki magana akan ki tsaida hankalin ki waje d'aya ki fitar da mijin aure, wajen shekara hud'u da mutuwar sadeeq baxa kiyi hak'uri ki kwantar da hankalin ba, kalli iyayen shi da suka haife shi sun rungumi kaddara sun hak'ura tsakanin su sai dai addu'a kuma nasan duk son da xaki nuna mishi bai kai iyayen shi ba"
Palourn yayi tsit baka jin motsin komai, mufidah tun lokacin da Abba ya fara magana hawaye suke tsere a fuskar ta gaba d'aya ta rasa tunanin yi taya xasu fahimce ta ne?, ita fah gaba d'aya auren ne bata so wa xata aura ita yanxu babu wanda ta ta6a tsaya wa dashi da sunan xance duk wadanda suke son ta bata sauraren su.
Cigaba da maganar shi Abba yayi bayan ya ajiye numfashi yace
"Ganin kin k'i tsayar da mijin aure ne yasa na yanke hukuncin neman wadanda suke xuwa neman auren ki, na sanar da Alhj Abubakar hkn da ya tara su mai auren ki da gaske ya turo manyan shi ayi magana, sai kuma kafin hka Dr muh'd yaxo mana da xancen yana son ki xai aure ki shine nan take muka aminta tun da munsan ko wane muh'd don hka ba wani 6ata lokaci muka tsayar da bikin nan da sati biyu"
A matuk'ar gigice ta d'ago kanta tare da kallon abban idanun ta na xubar da hawaye cikin rawar murya take cewa
"Ab......Abba ka....ka rufa min asiri don Allah kada ka aura min muh'd ni sam bana son yin aure, mumy, daddy ku bawa Abba na hak'uri"
"Inaaa mufidah lokaci kuma ya k'ure don baxan yi magana biyu ba kiyi hak'uri ki cigaba da addu'a kawai amman auren ki kamar anyi angama ne"
Shine fa ta mik'e tana girgixa kanta ta kasa maganar ma har mumy ta rik'o ta tare da xaunar da ita, cikin tsananin tausayin mufidah daddy yace
"Ya kamata aboki atausaya mata kabar ta a hankali ta xa6i wanda take so"
Girgixa kai Abba yayi tare da cewa "baxai yiwu ba Abubakar idan ba hka nayi mata ba baxa ta shiga taitayin ta ba "
"Kwarai kuwa wannan hukuncin shine dai dai "
Cewar umma yayin da mumy ta janyo mufidah suka fita xuwa d'akin ta nan ta rarrashe ta dakyar tayi shiru kukan ya koma na xuci sai ajiyar xuciya take idanun ta sun kumbura sunyi ja hka fuskar ma tayi jawur da ita saboda tsananin kuka, wani axababben ciwon kai tare da wani xaxxafan xaxxa6i ne ya rufe ta ruf lokaci d'aya.
Tun daga lokacin mufidah ta dai na walwala rai a junkushe ko dayaushe bata da wani abin sai dai ta kule cikin bedroom tana aikin tunani da kuka,sosai afnan ta shiga damuwa ganin yanda mameen ta ta canja gaba d'aya ko irin wasan nan da take mata yanxu ta daina, lokaci d'aya mufidah ta wani rame ta xabge ko cikakken abinci bata iya ci sosai, xuwa hospital ma Abba yace ta dakata da xuwa sai bayan anyi auren idan mijin ya yarda sai ta cigaba.
Shi yasa yanxu bata fita ko'ina daga d'aki sai d'aki mumy itama duk ta shiga damuwa saboda tana matuk'ar son mufidah batason tana ganin ta cikin damuwa,kullum cikin rarrashin ta take, gashi a wannan lokacin kusan kullum sai tayi mafarki da musaddiq fuskar shi dauke da tarin damuwa abin ya fara bata tsoro yanda ita ba wani sashi a ranta tayi ba mance wa take dashi sai ko mumy,afnan da muh'd sun ambaci sunan shi take tunawa dashi.
A wannan time d'in tsakanin musaddiq da mufidah baxan iya fad'a muku wanda yafi shiga damuwa ba, shi musaddiq tunanin rabuwa da mufidah yake wanda sonta har yanxu d'awainiya yake dashi ko raguwa bayayi ga kuma auren da su mumy suke shirin k'ak'aba shi tabbas duk yarinyar da tayi gigin auren shi har ya mutu baxa ta ta6a jin dad'in aure dashi ba, don xuciyar shi babu son wata d'iya mace sai mufidah xuciyar shi ta gama kar6ar so akan mufidah ta rufe wannan shafin, yasha rashin lafia sosai don sai da ya kwanta a hospital na tsayin wajen kwana ki uku saboda ciwon shi da ya tashi yasha wahala ba kadan ba duk ya rame abin tausayi.
Duk sintirin da muh'd yake a gidan har ya karaci xaman shi ya tafi baxai ga k'eyar mufidah ba abin ya fara damunshi ko wayar shi ta daina dauka sam hka idan yayi mata message babu reply ko d'aya tana sani take hkan saboda tana son ya fahimta bata son shi bata kaunar auren shi.
Mumy ce xaune a parlour kallo d'aya xaka yi mata ka fuskanci tana cikin tsantsar damuwa,yau wajen kwana ki 5 bata yi waya da musaddiq ba abin yana damun ta sosai ko yaushe wayar a kashe, hannun ta ta sanya ta dauko wayar ta number d'in musaddiq ta sake try cikin sa'a taji wayar ta shiga sai lokacin taji hankalin ta ya kwanta,ajiyar xuciya ta saki ta kwanciyar hankali jin ya dauki wayar muryar shi ta ratsa cikin kunnen ta bayan ta amsa gaisuwar da yake mata cikin sanyin murya tace
"Musaddiq saboda mun xa6a maka wacce xaka aura shine ka kashe wayar ka koh?"
"Sorry mumy ba haka bane ayyuka ne suka yi min yawa, ya daddy da baby afnan?"
Jikin mumy ne ya k'ara yin sanyi sam bata yarda da abin da yace ba kawai sai dai ta bishi a haka bakin ta yayi mata nauyi dakyar ta iya bud'e shi tace
"Suna lafia musaddiq, yaushe xaka shigo nigeria nan da 7 day's ne daurin auren don ranar Friday xa'a d'aura?"
Girgixa kai yayi kamar tana ganin shi kafin ya bud'e baki yace "nooo mumy ba saina xo ba idan aka gama bikin kawai ta xauna a wurin ki nan da next month xan xo insha Allah"
"Toh shikenan son Allah yayi maka albarka ya tsare min kai"
"Ameeen mumy, banji motsin afnan ba hala batanan"?"
D'an murmishi mumy tayi tare da cewa "tana wurin mameen ta mufi......"
Kit taji wayar ta tsinke duba wa tayi taga ba kudin tane suka kare ba sake kira tayi sai tak'i shiga ta dauka network ne sai kawai ta ajiye wayar yanxu hankalin ta ya kwanta tun da taji muryar shi.
Shi kuwa musaddiq a nashi 6angaren kuwa yana sa ni ya katse wayar bata k'arasa magana ba,saboda jin ta ambaci sunan yarinyar da baxai ta6a mance ta a rayuwar shi yarinyar da akan ta ya fara so kuma itace ta karshe lallai mufidah *ITACE KADDARAR SHI*, hannun shi ya sanya ya dauko diary d'in shi rubutu yayi wadanda basu wuce layi shida ba ya rufe littafin ya ajiye kwanciya yayi tare da lumshe idanun shi tunano fuskar mufidah yake tun lokacin da suka fara had'u wa a lecturer hall har xuwa ganin ta da yayi kafin ya taho Australian.
Kwanaki na tafia lokuta ma hka suna tafia kamar kiftawar ido, a hka lokacin bikin ya fara k'arato wa yanxu ya rage sauran kwana ki hud'u, duk wasu shirye shirye su mumy,daddy,Abba,umma dasu muh'd suna gabatarwa ban da mufidah da musaddiq wadanda kowannen su aciki basa farinciki ko kad'an da bikin kowannen su takan shi suke, shi yasa basu wani had'a party ba daga walima sai dinner party wadda xa'a yi har da iyaye wanda abokin Dr muh'd ne ya shirya mishi.
Daddy ne ya had'a lefe na gani na fad'a ya kashe kudi sosai a ciki abin sai wanda ya gani don fad'in yanda haduwar kayan suke 6ata lokaci ne, na mufidah kuwa mumy ko marmarin nuna mata bata yi ba ganin halin da take ciki na damuwa da tashin hankali sai ta killace mata shi waje d'aya don ko gyaran jiki ma ba'a bi takan shi ba don ba cikakkiyar lafia ce da ita ba, yanda mufidah ta koma ba k'aramin tsorata mumy yayi ba don hka ta kirawo umman mufidah don taxo taga halin da take ciki, amman sam umma taki xuwa sai waya da tayi mata tana yi mata fad'a sosai akan saboda aure xata nemi cutar da kanta to tun wuri ta fitar da damuwa a ranta aure babu fashi sai anyi shi insha Allah idan batasan abin da ya kamata ba su sun sani shi yasa suka xa6a mata abin da yafi dai dai a rayuwar ta.......
Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
*PAGE 41*
Mufidah sosai ta shiga damuwa da abin da umma tace mata duk ta sake xama wata iri wai muh'd ne xata aura nan da kwanaki uku xai xama mijin ta abin ba k'aramin dagula mata kwakwalwa yake ba idan ta tuna hkan, nan xata rungume picture d'in sadeeq a jikin ta tana kuka tare da sumbatun surutai idan afnan taxo ta same ta a hka itama sai ta fashe da kuka ta fad'a jikin mufidah, baxa tabar kuka ba sai taga mufidah tayi shiru tukunna kullum cikin tambayar ta take me akayi miki mamee nah? wa ta6a min ke? baki da lafia ne?, hka take jero mata tambayar but mufidah ta rasa ma amsar da xata bata sai kawai ta wayance ta shiriritar da tambayar ta ta sai ta sako wani abin da dauke mata hankalin.
Ganin yanda afnan take damun kanta idan tagan ta cikin damuwa sai ta daina yin kukan a gaban ta idan suna tare sai tana daure wa suna wasan su tare kamar da, hkan ba k'aramin dad'i yayi wa mumy ba ganin yanxu tana d'an fitowa parlour ta xauna har ta shiga kitchen tana had'a musu abinci, tayi kokarin kawar da damuwar kan fuskar ta amman cikin xuciyar ta kuwa uhm abin ba'a magana wajen damuwar da ke tattare aciki.
Ranar thurday su mumy suka gabatar da walima wadda ta shirya ta da kanta, sosai wajen da suka kama wajen gabatar da walimar ya had'u komai cikin tsari da birgewa akayi, malamai mata har guda uku mumy ta dauko suka baje basirar su wajen nasihohi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 23