k'okarin danne abin da yake ji.
Sakin sadeeq yayi tare da k'arasa wa wajen mumy wadda ta sakko daga up stairs da shirin ta na rakiyar musaddiq airport, rungume ta ita ma yayi sosai mumy ta tsorata da yanda taji bugun xuciyar musaddiq, hannun ta tasa ta shafa kanshi tare da rad'a mishi a kunnen shi
"Ka dage da addu'a musaddiq Allah ya yaye maka abin da yake damun ka, nima xan dunga you maka, kada kana sa damuwa a cikin xuciyar ka don Allah kayi min wannan alkawarin"
D'aga kai yayi tare da cewa " xan yi abin da kika ce mumy nah"
Daga hka kuma suka d'unguma don tafiya airport rakiyar musaddiq ko inda mufidah take bai k'ara marmarin kallo ba, sosai mufida abin da yake mata yana d'aure mata kai xai yi magana da kowa ban da ita ko gaida shi tayi baya amsa wa, amman da ta tuna er tsamar da suke yi a skul maybe har yanxu bai hak'ura ba ta6e baki tayi, hannun ta sadeeq ya kama suka fita daga palon da yake duk sun riga su yin gaba.....................
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A muh'd
♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
*PAGE 23*
Tun lokacin da musaddiq ya tafi xuciyar mumy ta kasa samun nutsuwa saboda batasan halin da d'anta yake ciki ba, idan suka kirawo shi a waya muryar shi normal, but ae ba fah ta ganin shi batasan yanayin da yake ciki ba, ta dage da taya shi addu'a sosai, hka a 6angaren daddy da shima addu'ar yake taya musaddiq tare da Kiran shi a waya yana mishi nasiha cikin tausasawa da rarrashi, duk wata kulawa suna yi mishi ta waya.
Sadeeq kuwa bayan en kwanaki da tafiyar musaddiq ya cire damuwar rashin d'an uwan nashi a kusa dashi, don yana samun kulawa sosai a wajen matar shi mufidah, xaman su suke lafia cikin kwanciyar hankali, duk da sadeeq yana da sanyin hali a komai nashi daga kallon yanayin shi kasan bashi da xafi komai cikin sanyi yake shi yasa suke xaman su lafia ba mai jin Kansu.
Mumy ma tana k'aunar mufidah saboda hankalin ta da nutsuwar ta gashi tana matuk'ar kulawa da d'anta shi yasa duk abin da ta samu xata nemi mufidah ta bata.
Saboda kwanciyar hankali mufidah tayi wata er k'iba kad'an ta k'ara haske da kyau abin ta, tana samun kulawa sosai a wajen mijin ta da iyayen shi, bata da wata matsala a yanxu sai wadda ba'a rasa kowanne d'an adam da ita ba.
Tsawon watannin su biyu da aure bata fita ko'ina ba amman a yau tayi niyyar tambayar shi tana son taje gida daga can xata wuce gidan Yah Omar wajen nabila don ita nabila xuwan ta biyu gidan tana yi mata yini, a xuwa na biyun ne tace baxa ta k'ara xuwa ba sai ta je, shi yasa ta yanke shawarar fita gobe.
Wajen K'arfe biyar da rabi ne ta shiga kitchen don yi musu girki dare, abinci mara nauyi tayi niyyar yi musu don hka jeelop na taliya take son yi, nan ta fara aikin ta cikin kware wa ta yayyanka su vegetables da yin blending d'in kayan miya.
Cikin tsawon mintuna ta kammala jeelop d'in ta xuba a food Flak's sannan tayi musu chicken pepper soup, sai coconut juice wanda yasha coconut and pineapple aciki sosai tare da milk ta ruwa tana gama wa ta sanya a frige bayan ta juye shi a jug.
Food Flak's d'in ta d'iba ta kai dinning area ta jera tukunna ta dawo ta kitchen ta d'auki plate's, spoon da glass cup's ta kai su dinning bayan ta gama sannan ta gyara kitchen d'in tare da yin wanke wanke, bayan ta gama da kitchen ne, ta gyara falo tare da sa mishi turaren wuta mai k'amshi tuni ko'ina a falon ya d'auki k'amshi, sannan ta wuce bedroom's d'in su ta gyara, tana gama wa sai ta fad'a toilet tayi wanka tare da d'aura alwala don mangarib tayi.
Bayan ta idar da sallahr mangarib ne ta xauna tana karatun Qur'an har xuwa lokacin sallahr isha'e, bayan ta idar tayi shafa'i da wutiri ne tare da addu'o'in ta tukunna ta tashi ta cire abayat d'in da tasa tayi sallah.
Wajen dressing mirror ta k'arasa ta shafa wani cream tare da yin light make up, tukunna ta k'arasa wardrobe ta bud'e 6angaren English wear's ta d'auko wani jeans white ne da t-shirt pink colour mara hannu bayan ta gama wa kayan ne sai ta gyara gashin kanta ta gefe tayi parking d'in gashin nata tayi kyau sosai kamar wata er baby, perfumes ta fesa tare da shafa humra mai tsananin k'amshi a jikin ta, falo ta fito ta xauna tana kallon film d'in thor a mbc 2.
Ko mintuna bakwai bata yi da xama ba sadeeq yayi sallama tare da shigowa palourn, d'ago kai tayi ta kalle shi tare da amsa mishi sallamar cikin muryar ta mai dad'i.
K'arasa wa yayi tare da xama kusa da ita yana kallon ta yace " my wife kin yi kyau sosai"
Cikin murmishi ta amsa da "thanks my dear, yau ka dad'e fah lafia?"
Yana kamo hannun ta yace " lafia my wife after an idar da sallah ne na tsaya yin waya da musaddiq kiyi hak'uri idan baki ji dad'i ba"
Girgixa kai tayi tare da cewa " ba komai dear dafatan yana nan lafia?"
"Qlau yake yana gaida ke ma"
Kallon shi tayi tare da cewa "Hmmm ina amsawa ", ba don ta yarda da abin da yace ba, nan ta jashi bedroom yayi wanka tukunna suka fito dinning table don yin dinner.
Bayan sun kammala cin abincin ne suka dawo cikin parlour, yana xaune kan kujera 3siters mufidah tana kwance tayi matashin kai da cinyar shi suna er hirar su da kallo, can mufidah tace
" Don Allah dear ina son ka barni gobe na je gidan mu da gidan Yan Omar please"
Murmishi yayi tare da shafa mata kai yace "kada ki damu my wife na bar ki Allah ya kai mu goben"
Cikin tsananin farinciki tace " Ameeen ngde dear"
"Kin wuce komai a waje na my wife, Allah ya sa ki Haifa min 'ya mace ma kama da ke, kafin na mutu naga d'an kai na nima"
Lokacin da ya fara maganar murmishi ne shimfid'e a fuskar mufidah don ita ma tana tsananin son baby's tana son ta ganta da ciki kamar nabila k'awar ta don ita ta harbu tuni, k'arshen maganar da sadeeq yayi shi yasa mufidah ta 6ata fuska cikin shagwa6a tace
"Kai koh dear xaka fara koh, insha Allah xamu rayu tare na haifa maka 'ya'ya da yawa"
Murmishi yayi tare da cewa "haba my wife ae ita mutuwar nan ba sallama take da mu ba, lokaci d'aya xata xo ta d'auke mutum, kuma ana son ko da yaushe bawa ya dunga tuna ta"
Tuni idanun mufidah sun fara taruwa da ruwan hawaye har sun fara xuba, ganin hka yasa sadeeq ya rungumo ta jikin shi tare da rarrashin ta yana gwada mata soyayyar shi mai sanyi wadda take mantar da mufidah damuwa, ae kuwa bai kyale ta ba sai da ya ga babu sauran damuwa a tare da ita sai farin ciki tukunna ya kyale ta.
Washe gari da safe bayan sun gama breakfast ne suka shiga wajen mumy da daddy mufidah tayi musu sallama mumy har da bata perfumes ta kai wa umman ta daddy kuwa kud'i ya bata sadeeq ya kai ta mall ta yi musu tsaraba, sosai tayi musu godia tare da addu'ar fatan alkhairi, sannan suka fito suka tafi.
A sahad store ya tsaya yayi musu tsaraba ko kud'in wajen mufidah bai kar6a ba wanda daddy ya bata, lokacin da aka gama xuba kayan a boot ne ya shiga har yayi wa motar key sun fara tafia mufidah ta mik'a mishi kud'in da daddy ya bata, girgixa kai yayi yana murmishi cikin sanyin muryar shi yace
"My wife ba kud'in ki ne fah, ni wannan wanda nayi niyyar baki ne don hka ki rik'e abin ki"
"A'a ni dai ka rik'e sun yi min yawa ne please"
"Duk da hka ki rik'e xasu yi miki amfani wani lokacin kin ji"
Kasa ce mishi komai tayi, da hka suka k'arasa gidan su mufidah yana gama parking ne ta bud'e kofar motar tare da fita da gudu tayi cikin gidan tana kwalla Kiran umma, sosai abin da tayi ya bashi dariya lallai mufidah akwai sauran yarinta a tattare da ita, fita shima yayi tare da bin bayan ta.
"Umma na kina?" umma wadda ke xaune kan kujera a palour ta d'ago kanta da sauri ta kalli kofar shigo wa don jin muryar er autar ta, kafin ta ankara har mufidah ta fad'o kanta tana dariya, cikin tsananin farinciki umma ta rungume mufidah kafin kuma ta cika ta tace
" ohhh ni mufidah bakya girma ji yanda kika fad'o min kamar wata karamar yarinya"
Cikin shagwa6a tana turo baki tace " toh umma ae ni k'arama ce a gaban ki"
Suna cikin hka sadeeq yayi sallama sai da umma ta amsa mishi tare da bashi ixinin shigo wa sannan ya shigo har k'asa ya tsugunna ya gaida umma, cikin farinciki umma take amsawa ta cigaba da cewa
"Ohhh ashe tare kuke shine ta gudo ta barka a waje"
Shi dai sadeeq murmishi kawai yayi yana kallon mufidah wadda take jikin umma tak'i tashi har yanxu, gaba d'aya sadeeq da umma er suruka ake yi ita kunyar shi take shima hka don hka ba wata hirar kirki da suka yi yayi musu sallama tare da fita daga palour mufidah sai a lokacin ta bishi a baya tana fito wa yasa hannu ya d'an ja kunnen ta kad'an tare da cewa
"Shine kika haye jikin umma duk kin bi kin danne ta koh?"
"Toh ae duk murnar ganin ta ne dear kuma nayi kewar ta sosai"
Murmishi yayi tukunna ya shige mota bayan yasa mai gadi ya fitar da kayan boot ya shiga dasu gidan, sallama yayi mata sannan ya tafi ta koma cikin gidan.
Yinin ranar sun sha hira da umma sosae don anjima ba'a had'u kamar hka ba sai a waya, sai da yamma sadeeq yaxo daukan ta, amman sai da ta jira Abban ta ya dawo suka gaisa sannan suka tafi, gaf da Kiran sallahr mangarib suka k'arasa gidan Yah Omar a lokacin shima Yah Omar dawowar shi kenan daga office nan suka wuce masjid yayin da mufidah ta shiga da sallama cikin palourn, wani ihu nabila ta saki tare da yin tsalle ta rungume mufidah tana cewa " wayyo my friend kece a yanxu?"
"Ni ce kuwa my sister, kina ta tsalle sai kin wahalar mana da babyn mu"
Hararar wasa nabila tayi mata tare da jan ta xuwa bedroom don yin sallah, bayan sun idar ne suka bud'e shafin hira sosai sai da yah Omar yaji shiru basu fito ba ya biyo bayan su nan yaga sai xuba suke, hararar mufidah yayi tare da cewa "kin xo kina ta xuba mata surutu ko tar6ar da aka sabar min ba'a yi ba, gashi da yunwa na dawo"
"Kaiiiiiiii Yah Omar kasan dai nabila ta fi ni surutu ko?" Ta fad'a cikin shagwa6a
"Bana son wani surutun kuma ki tashi ki tafi wajen mijin ki, sweetheart ke kuma mu tafi kitchen a bani a abinci"
Ya k'arasa fad'i yana kama hannun nabila suka fita daga bedroom d'in, mufidah tashi tayi ta bisu ita ma tana dariya ta wuce cikin Palo wajen sadeeq.
Basu bar gidan Yah Omar ba sai wajen 9 na dare, lokacin da suka k'arasa gida bayan sun shiga wajen mumy ne sannan suka wuce part d'in su, wanka kawai suka yi tare da neman makwanci don agajiye suke kuma sun riga da sun ci dinner gidan Yah Omar don hka baccin su suka yi hankalin su a kwance............
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A muh'd
♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_kuna ina k'awaye kirki wannan shafin naku ne Queen mermue dear and Ameerah (Amnoor), wannan shafin sadaukar wa ne gare ku, hak'ik'a ina matuk'ar alfahari da ku abokanan kirki, Allah ya bar mu tare ina muku fatan alkhairi a duk inda kuke_🤝❤
*PAGE 24*
*AFTER ONE YEAR*
Acikin wannan shekarar abubuwa sun faru da yawa, ta 6angaren su mufidah kuwa suna xaune lafia da mijin ta da sadeeq tare da iyayen sadeeq, kuma a hankali xuciyar ta ta fara sabawa da sadeeq duk da ba wani son shi take ba amman sun yi mugun shak'uwa da junan su sosai, komai na kyauta ta wa tana yi mishi bata tauye mid hakkin shi dai dai gwargwado tana kyautata mishi.
Shima sadeeq d'in duk wani hakkin ta da ya rataya a kan shi yana k'okarin sauke mata, sai dai har xuwa yanxu mufidah bata samu ciki ba sadeeq ya dage da addu'a sosai na Allah ya bawa mufidah ciki ta haihu don yana son yaga ta haihu sun samu baby kamar yanda nabilan Yah Omar ta haihu an samu baby girl taci sunan umma suna kiran ta da muhibbat.
Kamar yau suna kan dinning table suna yin dinner d'in dare, mufidah ta kai spoon bakin ta na abincin sai taji xuciyar ta na tashi amman sai ta danne hkan ta cigaba da ci abin ta don wata irin yunwa take ji sosai.
K'ara kai wani spoon d'in tayi bakin ta ae kuwa gaba d'aya sai taji xuciyar ta ta hautsine da sauri ta yarda spoon d'in tare da toshe bakin ta da hannu ta tashi da gudu ta shige bedroom d'in ta cikin toilet ta shiga ta fara yin amai sosai tana dafe da cikin ta da hannun ta.
Tana tashi da gudu sadeeq shi ma ya ajiye spoon d'in hannun shi ya bi ta da sauri, tarar da ita yayi tana ta amai, cikin sauri ya rik'e ta yana yi mata sannu, har sai da ta amayar da abin da taci gaba d'aya ta gama gala6aita, rik'o ta yayi tare da wanke mata bakin ta ya rik'e ta har xuwa cikin bedroom ya kwantar da ita sannan ya koma cikin toilet d'in ya gyara wajen tukunna ya fito.
Wajen mufidah ya k'arasa wadda ta lullu6a da bargo saboda sanyin da ta fara ji, d'an janye bargon yayi tare da ta6a wuyan ta yaji d'umi sosai alamar xaxxa6i ne a jikin ta, cikin sanyin muryar shi mai had'e da damuwa yace
"My wife daman baki da lafia ne?"
Cikin sanyin murya irin ta mara lafia ta bud'e baki tace " nima ban sani ba, nasan dai tun safe ina jin tashin xuciya ne gashi ina son nayi amai amman sai na kasa sai yanxu kuma naji aman ya xo"
"Sannu my wife gashikuma naji jikin naki akwai xaxxa6i, ya kamata na kirawo muh'd ya duba min ke?"
Cikin sauri ta fara girgixa kai tare da rik'o hannun shi ta marairaice kafin tace "ni gaskia ba sai ka kirawo shi ba xan samu sauk'i ka ji don Allah please"
"Toh shikenan"
"Yanxu kaje ka k'arasa cin abincin ni bacci nake ji"
Mufidah ta k'arasa fad'i tana gyara bargon jikin ta, d'an xaro ido yayi kad'an tare da cewa
"Haba my wife tun yanxu xaki baccin sai fa yanxu 9 tayi"
D'an yatsina fuska tayi tare da cewa " Allah da gaske nake bacci nake ji"
"Okay "
Yana nan xaune har bacci ya d'auke ta tukunna ya fito palour ya k'arasa cin abincin shi ya tattara komai ya kai kitchen tare da yi mata wanke wanken kayan da suka yi amfani dasu, don sadeeq shu ba ruwan shi idan yana gida xagewa yake yana tayata aikin gida sosai.
Sai da ya gama tukunna ya nufi bedroom d'in ta ya duba yaga har yanxu bacci take, wanka ya shiga yayi sannan ya shirya cikin sleeping dress ya kwanta kusa da ita addu'a yayi musu sannan yayi switch off d'in hasken d'akin babu dad'e wa bacci ya d'auke.
Cikin dare xaxxa6i mai xafin gaske ya rufe mufidah, gaba d'aya sadeeq ya rikice ganin yanda take shan wahala, har xuwa gari ya waye basu wani runtsa ba saboda jikin mufidah yak'i dad'i.
Garin na waye wa sadeeq ya kirawo Dr muh'd kan yaxo yanxu mufidah ba lafia, babu 6ata lokaci muh'd ya k'araso gidan nan ya dudduba ta tare da yi mata test d'in fitsari anan ya hango tana dauke da ciki a jikin ta, bayan yayi mata allurar bacci ne tare da sanya mata drip bcos jikin nata ba k'wari gashi babu abinci a cikin ta, cikin en mintuna bacci ya d'auke ta sannan suka fito palour.
" me yake damun ta ne muh'd?"
Sadeeq ya tambaye shi yana kallon shi, d'an murmishi muh'd Yayi tare da cewa
"Uhm babban yaya congratulation laulayin ciki ne yake damun ta"
Kallon ban yarda da abin da kace ba sadeeq yayi mishi kafin kuma yace
"Muh'd kana fad'a min ne fa mufidah na da ciki da gaske kake"
Cikin murmishi muh'd yace "Allah da gaske nake babban yaya, na tsawon 3 month's"
Rungume muh'd yayi cikin tsananin farinciki har sai da hawaye suka xubo a idanun shi yana godia ga Allah da ya nuna mishi wannan lokacin da ran shi, bayan Dr muh'd ya tafi ne sadeeq ya shige bedroom ya xauna gaban mufidah tare da xuba tagumi ya kallon ta xuciyar shi fal farinciki da wannan kyauta da Allah ya bashi.
Dr muh'd kuwa part d'in mumy ya shige cikin farinciki ya tsegunta mata mufidah na da ciki, sosai mumy tayi farinciki har muh'd abin ya bashi mamaki ganin yanda take murna, daga hka yayi mata sallama ya tafi, ita ma mumyn k'in xama tayi sai ta wuce part d'in su sadeeq don ganin jikin mufidah.
Lokacin da mufidah ta farka daga bacci taji abin da yake damun ta sosai tayi farinciki da hka don tana son yara sosai, nan fah aka dunga tarairayar ta fiye da baya kulawa sosai sadeeq yake bata da mumy har da daddy ban da umman ta da abban ta ga Yah Omar ma, cikin kwanciyar hankali ta cigaba da renon cikin ta amman tana d'an ta6a laulayi.
********
Kwance yake a gefen swimming pool yana sanye cikin wani 3quater d'in wando white jikin shi babu riga yayi matashin kai da hannayen shi yana kallon sararin samaniya.
Kallo d'aya xaka yi mishi ka tabbatar guy d'in ya had'u ta ko'ina, ya k'ara wani irin kyau da haske alamar hutu a tattare dashi sai dai er ramar da yayi.
Musaddiq kenan wanda bai dad'e da tashi daga gadon asibiti da yayi ba, jinya sosai yayi ta wurin 2 weeks a hospital but su daddy basu da labari sam, tun lokacin da yaxo k'asar bashi da cikakkiyar lafia saboda ya kasa cire mufidah daga cikin xuciyar shi har xuwa yanxu, sosai abin yake damun shi don baya so yana sa tunanin ta a xuciyar shi tun da ta xama matar wani but hkan ya gagara a tattare dashi.
Wannan rashin lafiyar ne da yayi bayan ya samu sauk'i Yayi alkawarin cire son mufidah daga cikin xuciyar shi ta ko wani hali.
Yana nan kwance tsawon mintuna 50 tukunna ya tashi jikin shi a sanyaye ya shige cikin gidan da yake xaune wanda ya kunshi 2 bedroom's da palour babba d'aya, d'akin shi ya shige kai tsaye, toilet ya shiga tare da sakarwa kan shi shower tsawon mintuna 15 tukunna ya fito ya d'aura towel, dressing mirror ya nufa ya gyara jikin shi tare da shirya wa cikin t-shirt ash colour da black jeans belt d'in ma bak'a ce hka takalmin kafar shi, bayan ya fesa perfumes ne ya dauki car key da phone's d'in shi ya fita daga gidan gaba d'aya.
Don tun bayan xuwan shi Australia bai fita sai da dalili, kusan ko da yaushe yana kunshe cikin gida kamar wata mace, yana fama da tunani, a yanxu kuwa ya dau alkawarin cire tunani da damuwa a xuciyar shi, xai na fita don rage wa kan shi damuwa.
Sosai yayi yawo a garin Australia k'asa ce mai kyan gaske, sai dare ya dawo gidan shi da yake ya ci abinci a restaurant yasa shi yin wanka ya shirya cikin pyjamas ya kwanta ko da tunani yaga xai dame shi sai kawai ya kunna laptop d'in shi ya hau amfani da ita, bai ajiye ta ba sai da yaji bacci yaci k'arfin idon shi sannan ya ajiye ya kwanta ya fara bacci.
A yanxu hka ya gama course d'in da xai yi har ya fara aiki a hospital d'in su,amman su daddy basu san da hka ba, don baya son su matsa mishi ya dawo gida ba xai jure ganin mufida ba.........
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A muh'd
♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
*PAGE 26*
Cikin en mintuna Dr muh'd ya k'araso saboda tsabar sauri a wajen get yayi parking ya shigo gidan don ba xai iya jiran mai gadi ya bud'e get ba, kai tsaye part d'in sadeeq ya nufa cikin sauri.
Da sallama ya shiga but ba'a amsa mishi ba sai da ya kirawo wayar sadeeq ya fad'a wa mufidah ya k'araso yana palour, cikin sauri ta fito ta tarar dashi a tsaye jagora tayi mishi har cikin bedroom d'in.
Ba 6ata lokaci Dr muh'd ya fara duba sadeeq cikin kware wa, bayan mintunan da basu gaxa talatin ba ya gama duba sadeeq, drip ya sanya mishi tare da yi mishi allurar bacci babu dad'e wa bacci ya d'auke shi sai lokacin hankalin mufidah ya fara kwanciya ganin ya samu bacci.
Palour suka dawo mufidah xama tayi tare da cewa "doctor me yake damun mijina?"
Shima Dr muh'd xama yayi tare da kallon ta yace " a gaskia yanxu baxan iya takaice miki abin da yake damun shi ba dole sai mun je hospital akwai scanning d'in da xamu yi"
Nan hankalin mufidah ya sake tashi sosai ta fara kuka, rarrashin ta ya fara yi sai da yaga ta d'an samu nutsuwa tukunna yace
"Idan ya farka xuwa anjima ku same ni a hospital, su mumy sun sani"
Girgixa kai mufidah tayi kafin tace "ya fad'a min kada na sanar dasu saboda xasu shiga damuwa"
D'an shiru yayi fuskar shi d'auke damuwa kafin kuma yace " okay yanxu ya xa'a yi kenan, don gaskia a yau ina son akai shi hospital"
"Xan kawo shi Doctor da kaina idan ya tashi"
"Yawwa kin kyauta"
Daga hka suka yi sallama ya tafi, mufidah ta xube kan kujera tare da xabga tagumi tana tunani, ta d'an jima da hka kafin taji cikin ta yana murd'a wa atake ta fahimta yunwa take ji.
Kitchen ta shiga ta had'a tea a cup ta sha sannan ta dawo d'akin har yanxu sadeeq bacci yake kallo d'aya xaka yi mishi kasan ba k'aramin wahala ya sha ba duk ya dad'a rame wa, xama tayi kusa dashi ta rik'e mishi hannun shi tana murxawa a hankali.
Sai after la'asar sadeeq ya farka da mufidah ya fara had'a ido murmishi suka sakarwa junan shi cikin jin dad'i mufidah tace
"Sannu sadeeq ya kake jin jiki"
Murmishin yak'e ya saki don shi kadai yasan abin da yake ji a jikin shi, hannun ta ya rik'o tare da cewa
"My wife kwantar da hankalin ki, jiki na da sauk'i ya lafiyar baby na dafatan kin bashi kulawa?"
Da kai tayi mishi alamar ehhh, taimaka mishi tayi yayi wanka ko abinci ya kasa ci sai coffee yasha tukunna suka tafi hospital, mufidah ce take driving sadeeq na gefen ta hannun shi d'aya dafe da cikin shi ya lumshe ido, da hka har suka k'arasa asibitin bayan mufidah tayi parking ne ta fito tare da bud'e wa sadeeq kofar motar ita ta taimaka shi ya fito tukunna ta rufe motar.
Tana rik'e dashi suka k'arasa cikin asibitin kai tsaye office d'in muh'd suka nufa sai da mufidah tayi knocking, muh'd dake xaune kan kujera yace
"Yes come in"
Nan mufidah ta tura kofa suka shigo ganin sune yasa muh'd mik'e wa da sauri ya taimaka wa sadeeq ya xauna tukunna ita ma ta xauna
"Babban yaya ya jikin na ka?"
Cikin yak'e sadeeq yace " jiki da sauk'i muh'd"
Nan babu 6ata lokaci Dr muh'd da wani likitan daban suka shigar da sadeeq room d'in scanning mufidah tana xaune a gefen shi da yake kwance hannun ta cikin nashi suna kallon komai da ake ta jikin nau'orar computer d'in.
Sun d'auke tsawon mintuna arba'in xuwa hamsin suna scanning d'in, bayan sun gama suka koma 6angaren yin test d'in urine test da blood test har xuwa lokacin da aka kammala had'a result gaba d'aya.
Lokacin da Dr muh'd ya duba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 23