ya rabbi "
Cikin tsokana nabila tace "kin had'u da mutumin na ki ne yau? "
cikin rashin fahimta mufidah tace "wa kike nufi? "
"musaddiq Abubakar man "
Wata dariya ce ta kubce wa mufidah ta dunga yi yayin da nabila ta saki baki tana kallon ta kawai cike da mamaki sai da tayi dariyar ta ta gama har da hawaye sannan ta bawa nabila labarin abin da tayi mishi, nan fah nabila me xatayi ban da dariya daman tasan mufidah baxa ta kyale shi ba sai tayi mishi wani abun.
"Allah k'awata baki da kirki amman ina rok'an ki ki rabu dashi a matsayin ki na 'ya mace ki rabu dashi kuma ki kiyaye abin da xai sake had'a ku a gaba"
D'an hararar ta mufidah tayi tare da cewa Kina nufin ya ci bulus kenan marin da yayi min ?"
"Haba k'awata ban sanki da wannam halin ba ki rabu dashi please "
"Okay naji na yarda amman da sharad'i guda idan yayi min xan rama"
Mufidah tana rufe bakin ta umman nabila ta shigo d'akin tana cewa "ku dai idan kuka shigo d'akin kuna surutu mance wa da komai kuke toh lokacin cin abinci yayi don hka oya ku fito mu ci"
"toh ummah " suka fad'i sannan suka fito daga d'akin dinning table suka nufa nan suka ci abinci sannan suka dawo falo suna ta6a hira sai yamma sannan mufidah ta tafi gida...............
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:03 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE*🌲
*written by*
Aishat A muh'd
♻ *E.W.F*
_Wannan shafin na kine k'awata sadeey S Adam (SaNaz), ngde da k'aunar da kike nuna min Allah ya bar xumunci ya k'are min ke a duk inda kike, ina miki fatan alkhairi_😍
*Page 4*
*WACE CE MUFIDAH*
Mufidah El Hussaen 'yace a wajen Alhj EL Hussein da hajia Aisha, mahaifin ta haifaffen garin d'ambatta ne sana'a ce ta dawo da mahaifin shi cikin garin kano iyayen shi ba wasu masu kud'i ba ne rufin asirin Allah ne da hka yayi karatun boko dana addini da yake shi kad'ai suka mallaka akan fannin Shari'ah yayi karatun cikakken alk'ali ne Wanda yasha gwagwarmaya Kafin kuma yayi ritaya ya koma harkar kasuwanci ta siyar da motoci.
Alhj El Hussaen baxa ka kirawo shi da mai dukiya sosai ba yana da arxikin shi dai dai gwargwado yana xaune a sultan crescent, matar shi hajia Aisha uwar 'ya'yan shi bafulatana ce amman ta samu karatu sosai don ita ma k'wanan nan ta bar aiki tana matsayin babbar lecture da ake damawa dasu a makarantar buk.
Yaran su biyu Omar da mufidah sune yaran da Allah ya basu Yah Omar yana k'asar london yana karatun shi ya ma kammala karatun cikin wannan watan suke sa ran dawowar tashi.
Mufidah itace mai bin Yah Omar ya bata wajen shekara 4, ita ma ta kammala karatun ta na primary da secondary yanxu tana buk ta d'ora karatun ta, tana masifar son karatun na ta bata k'aunar abin da xai ta6a neman ilimin nata, kuma ba iyakar ilimin boko ta tsaya ba har da na addinin islam ta ma yi saukar alqur'ani da sauran mahimman littatafai na addini dai dai gwargwado tana da ilimi anan 6angaren.
Kuma ta kasance kyakkyawar yarinya mai kama da mahaifin ta amman farin umman ta ta d'auko duk da uban shi ma ba bak'i ba ne, gashi akwai ta kirki bata shiga harkar da bata shafe ta ba akwai hankali da nutsuwa sai dai aka ta6a ta bata kyale wa kamar yanda musaddiq Abubakar ya ta6o ta.
*WACE CE NABILA K'AWAR TA*?
Nabila yarinya mai hankali da nutsuwa ga hak'uri maman ta hajia Amina k'awa ce ga hajia Aisha umman mufidah tare suka yi koyarwa a buk k'awaye ne sosai shi yasa mufidah da nabila suka xama k'awaye sosai, sai dai ita nabila mahaifin ta ya rasu kuma ita kad'ai ce ta rayu cikin 'ya'yan ta da take haihuwa duk mutuwa suke, gashi ita ma nabilan kyakkyawa ce sai dai mufidah ta fita kyau, duk tare suka yi karatun su kan su a had'e yake.
_mun dawo labari_
Tun da suka shiga mota musaddiq Ko magana ya kasa saboda tsabar takaici har suka k'araso gida, Yah sadeeq yana parking da mota musaddiq ya fito ya nufi cikin gidan d'akin shi ya shige ya cire kayan jikin shi ya shiga toilet wanka yayi sannan ya fito ya shirya cikin wata riga mara hannu red colour da ash d'in 3quater bayan ya fesa perfumes ya fito xuwa babban palon gidan, anan ya tarar da mumy da Yah sadeeq a xaune suna hira xama yayi kusa da mumy yace
" I'm hungry Mumy "
Har Yah sadeeq ya bud'e baki xai yi magana kamar musaddiq yasan abin da xai fad'a wa mumyn aikuwa yayi mishi alamar kada ya fad'a mata don hka yaja bakin shi yayi shiru kawai.
" my son me xa'a kawo maka?" Cewar mumy
D'an yatsina fuska yayi tare da cewa " Duk abin da kika dafa mumy, amman a had'a min da fura mai sanyi"
"kaje dinning table xaka samu komai acan akwai kuma fura cikin frige din kusa da dinning table, maxa tashi kaje ka ci"
Tashi yayi ya nufi 6angaren dinning table d'in yana yatsine fuska, shi kuwa Yah sadeeq yana danne dariyar da taxo mishi.
Cikin nutsuwa ya d'ebe abincin yaci Kad'an sannan ya sha furar nan da yawa, bayan ya gama sai ya dawo palon amman bai xauna ba ya kalli mumy da Yah sadeeq yace
"ni xan je na kwanta na huta "
"Okay son ae gwara ka huta " Cewar mumy yayin da Yah sadeeq yace
"ae dole ma ka huta brother saboda ka sha........... "
Kafin ya K'arasa fad'i musaddiq ya harare shi yayi gaba shi kuwa Yah sadeeq dariya ya tuntsire da ita mumy kuwa cewa take
"je ka huta son ka rabu da yayan nan naka sarkin tsokana "
"auuu hka xaki ce mumy "
Cikin murmishi mumy tace "Ehhh mana "
Nan dai suka cigaba da hirar su cikin kwanciyar hankali.
A 6angaren musaddiq kuwa ba hutawar xai yi ba kawai tunanin Wanda yasa aka kawo mishi wannan abin kaxantar yake amman duk tunanin shi ya rasa gano ko wane, amman lallai xan bincika, da hka bacci ya d'auke shi.
*WANE NE MUSADDIQ ABUBAKAR*?
Dr Musaddiq Abubakar kyakkyawan saurayi ne hadadden guy wanda ilimin addini dana boko suka ratsa shi nutsatstsan mutum ne ma'abocin miskilan ci da rashin son hayaniya, bai dad'e da kammala karatun likita ba, mahaifin shi yana gina mishi asibiti, sai dai kuma musaddiq don ra'ayin kanshi yake koyarwar amman shi cikakken likita ne.
Iyayen shi kuwa Alhj Abubakar da hajia khadija su biyu ne 'ya'yan su daga Abubakar sadeeq Wanda yaci sunan uban nashi suna ce mishi sadeeq sai kuma musaddiq ,suna xaune cikin xaman lafia da kwanciyar hankali gashi suna k'aunar junan su sosai har baxa ka iya banbance tsakanin sadeeq da musaddiq wanne yafi k'aunar d'an uwan shi ba, mahaifin shi d'an kasuwa ne hka shima sadeeq sana'ar mahaifin nashi yake.
Alhj Abubakar da Alhj El Hussaen abokanan juna ne na k'ut da k'ut,amintaka ce a tsakanin su sosai hka ma matan su.
_mun dawo labari_
Tun daga lokacin mufidah take xuwa skul da wuri idan ta fuskanci ranar musaddiq yana da lecture a ranar don hka bai k'ara korar ta ba, sai dai fah har yanxu haushin yarinyar yaji sosai, ita kuwa bata k'ara bi ta kanshi ba gashi duk test d'in da yake musu da assignment kusan ita ce kan gaba wajen ci,kuma yaga kusan lecture's din makarantar suna yaba ma yarinyar sosai.
Ana cikin hka Yah Omar yayi waya xai dawo nan da k'wana 2 don Allah mufidah ba xama ita da nabila suna kok'arin had'a mishi partyn murnar kammala makarantar shi da kuma murnar xagoyowar shekarar haihuwar shi, sosai suke shirya Inda xa'a yi partyn da a abubuwan da xa'a buk'ata a wajen.
Ranar Friday da misalin karfe 7 jirgin su Yah Omar yayi landing a airport d'in malam aminu kano, mufidah da nabila ne suka d'aukar shi yana fito wa daga cikin jirgin mufidah ta nufi inda yake da gudu ta rungume shi cikin tsananin farincikin ganin d'an uwan nata ,nan shima ya rungume ta cikin murnar ganin kanwar tashi xuwa can ta sake shi tare da kallon shi cikin murmishi tace
"Yah Omar ka ga yanda ka koma lallai london ta kar6e ka"
"lallai yarinyar nan kin rainani daman can da Kyan nawa "
Ya Omar ya fad'a cikin dariya a lokacin kuma nabila ta k'araso tana gaida shi tare da yi mishi sannu da xuwa rik'e baki yah Omar yayi tare da cewa
"kai kai wannan ba dai itace nabila ba?"
"ita ce mana "
Cewar mufidah, cikin tsokana yace "lallai yaran nan kun girma da yawa wannan ae Kun kusan kamo ni "mufidah dariya tayi yayin da nabila take sunkuyar da kanta k'asa ganin irin kallon da Yah Omar yake mata.
Nan fah ya dunga tsokanar su har suka k'araso gida, iyayen shi sunyi matuk'ar jin dad'in dawowar yaron nasu lafia.
Kuma a ranar su mufidah suka dunga gayyatar mutane suna fad'a musu ranar asabar ne partyn da suka shirya wa Yah Omar, ta 6angaren Yah Omar ma ya sanar da abokanan shi na nan har dasu sadeeq da musaddiq 'ya'yan abokin mahaifin nashi kuma sun bashi tabbacin xasu xo...........
Aishat A muh'd
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*written by*
Aishat A muh'd
♻ *E.W.F*
*Page 5*
_Washe gari_
Mufidah da nabila ba xama ranar sai shirye shirye suke har xuwa lokacin da xa'a gabatar da partyn, hatta kayan su iri d'aya ne da nabila komai da komai shima Yah Omar kayan da xai sanya colour d'in su d'aya da na su mufidah sai dai shi na maxa ne abin da ya banbanta kenan.
Har xuwa lokacin da suka sanya karfe 4 na yamma xuwa karfe 7 na dare xa'a tashi, don hka xuwa karfe hud'un duk friend's din su mufidah sun xo na skul, Wow! masha Allah na furta lokacin da na hango mufidah ta gama shirya wa cikin had'ad'd'an lace green colour nd touch d'in flowers red d'inkin riga da siket ne sun yi matuk'ar yi mata kyau sosae, mai make up suka d'auko ta tsantsara musu kwalliya, hka ma nabila tayi kyau sosae xuwa karfe 4 sun bar gidan sun tafi wajen da suka kama don yin partyn.
Cikin hall di'n ya had'u iya had'uwa ya sha decoration da kwalliyar flowers ga k'aton birthday cake mai hawa uku, friend's din Yah Omar ma sun xo sosai duk inda mufidah ta gifta idanun mutane na kanta har da mata kuwa en uwanta don ba k'aramin had'uwa tayi ba, wani abin mamakin shine duk inda Yah Omar ya d'auke kafar shi to nan nabila xata ajiye ta ta sai bata kulawa yake alamun dai sun bayyana wa kansu soyayya, mufidah na ankare dasu sai dai tayi murmishi kawai kuma tayi farinciki sosai da hkan sun dace da junan su.
"Haba musaddiq don Allah kasan mun yiwa Omar alk'awarin xamu je gashi kace ka fasa xuwa "
Cewar Yah sadeeq kenan lokacin da ya gama shirya cikin wata tsadaddiyar shadda purple ce tayi mishi kyau sosae, ya shigo d'akin musaddiq don ganin ko ya shirya sai yayi turus ganin musaddiq a xaune yana sarrafa laptop ko alamar shirya wa bai yi ba
"lafia musaddiq baka shirya ba gashi karfe 5 ma ta wuce? "
Cikin yatsina fuska yace "Yah sadeeq na fasa xuwa fah "
So shine sadeeq yake fad'a mishi sun yiwa Omar alk'awarin xuwa,nan dai dakyar Yah sadeeq yake lalla6a musaddiq ya yarda xai je, ajiye laptop d'in yayi bayan ya kashe ta ya mik'e tsaye tare da cewa
"amman baxa mu dad'e ba ko brother don ni fah banson hayaniya? "
Murmishi sadeeq yayi tare da cewa "Haba musaddiq ka d'aure mu xauna xuwa a tashi kasan yanda muke dasu Omar kamar en uwan jini "
"alright bari na shirya amman idan hayaniya ta dame ni xan gudu na bar ka " Dariya Yah sadeeq yayi yana cewa "Ehhh na dai ji ".
Toilet musaddiq ya shige shi kuwa Yah sadeeq ya fita daga bedroom d'in nashi, cikin mintuna talatin musaddiq yayi wanka a gurguje ya shirya cikin wani yadi blue colour yayi matuk'ar kar6ar shi yadin don bai fiye sa manyan kaya ba sai ta kama, bayan ya taje sumar kanshi ya shafa mata mayuka sannan ya d'aura tsadadden watch di'n shi tare da fesa perfumes masu matuk'ar k'amshi, sannan ya fito xuwa falo inda Yah sadeeq yake jiran shi.
Yana fito wa palon mumy da Yah sadeeq suka bishi da kallo yaushe rabon su ganshi da manyan kaya gashi kuma suna mishi kyau Idan ya saka mumy ce ta fara cewa
"Masha Allah d'an nawa yayi kyau Allah yasa idan aka je a sama min suruka"
Yah sadeeq ya tuntsire da dariya kafin yace "tabbb mumy wannan doctor d'in idan matan suka ganshi guduwa ma xasu yi saboda fuskar ba fara'a "
Cikin shagwa6a yace "Mumy ko kiyi wa brother magana idan ba hka ba xan mishi allura yanxu nan kuwa "
Don Yah sadeeq Akwai shi da tsoron allura kamar mace nan kuwa ya marairaice fuska yana cewa "Haba d'an k'anina na dai na wuce mu je ni don Allah kada yi min xancen wata injection ina xama na lafia"
Nan musaddiq da Mumy suka tuntsire da dariya shi kuwa Yah sadeeq da sauri ya fice daga falon yana cewa "ni nayi gaba ina jiran ka a mota "
Musaddiq ne ya kalli mumy cikin murmishi yace "mun tafi sai mun dawo "
Ya K'arasa fad'i yana bata peck a kumatu ita ma cikin murmishi xuciyar ta cike da k'aunar d'an nata tace "Allah ya dawo min daku lafia Allah ya tsare min ku "
"Ameeen mumyn mu thanks for your du'a,bye"
Daga hka ya juya ya fita mumy ta bishi da kallon k'aunar 'ya'yan ta, su kad'ai Allah ya mallaka mata ba K'aramin so take musu ba.
A parking space ya tarar da Yah sadeeq xaune cikin mota yana jiran shi don hka shima shiga yayi ba tare da 6ata lokaci ba Yah sadeeq yayi wa motar key sannan suka fice daga gidan duk wanda ya gansu sai sun bashi sha'awa saboda yanda suka yi matuk'ar yin kyau gasu kyawawa tubarkallah, motar da suke ciki ma kanta abar kallo ce.
Cikin mintuna da basu gaxa 50 ba suka K'arasa wajen partyn, waje Yah sadeeq ya samu yayi parking sannan suka fito jerawa suka yi kamar wasu tagwaye suka nufi wajen sam baxa kaji irin tashin sautin kid'an nan ba wanda xai dami mutane, slow music ne yake tashi a wajen.
Shigowar su wajen shi ya janyo hankalin mutanen wajen kansu don ba k'aramin burge su suka yi ba musamman ma musaddiq yawancin matan wajen suka raja'a da kallon shi, irin kallon nan na daman kace kana so na.
Yah Omar yana tsaye gaban cake mufidah na gefen daman shi yayin da nabila tana hagun shi kenan sun sashi a tsakiya,xai yanka cake din kenan yaga shigowar su musaddiq don hka ya dakata da yankawar wajen su ya k'arasa suka rungume junan su cikin farinciki Kafin su saki juna Yah Omar ya kalli sadeeq yace
"abokina musaddiq fah ya girma nema ma yake yafi mu girma ya kamata mu ajiye iyalai mun girma "
Dariya ya sadeeq yayi suka tafa da Yah Omar sannan yace "k'warai da gaske abokina ka kawo shawara mai kyau "
Shi kuwa musaddiq murmusa wa kawai yayi, suna cikin tafiya xuwa gaban cake din ya Omar ya cigaba da cewa
"gwara mu yi mu bawa k'annan namu fili su ma su yi "
Dai dai lokacin sun k'araso wajen don hka Yah Omar ya kalli mufidah yace
"sadeeq ka gane wannan kuwa?"
Ya fad'i yana nuna mufidah da hannu, d'ago kan shi yayi ya kalli mufidah ita ma anyi sa'a ta d'ago kanta nan idanun su suka sark'e da na juna take Yah sadeeq yaji wani abu a tattare shi yana bin ilahirin jikin shi, lokaci d'aya sadeeq yaji wani son mufidah a cikin xuciyar shi wanda ake cewa love at first sight gaba d'aya ya mance a inda suke ya kasa janye idanun shi a kanta.
Mufidah ce ta janye idanun ta a cikin xuciyar ta tace wannan ya fiye kallo da yawa ta d'an murgud'a bakin ta Kad'an hkan da tayi sai sadeeq ya ji ta k'ara shiga xuciyar shi, ya Omar da ya ankare da kallon da yake yiwa mufidah sai yayi Murmishi tare da dafa kafad'ar sadeeq yayi gyaran murya tare da cewa
" uhm uhm abokina ko er gida xa'a yi NE? "
Ya fad'i hkan saitin kunnen sadeeq, firgigit sadeeq yayi kamar wanda ya tashi daga bacci d'an sosa k'eya yayi tare da cewa
"da xaka ba ni ae da naji dad'i "
Sannan kuma ya jiyo ya sake kallon mufidah tukunna yace "gaskia ba don ka fad'a min ba baxan ta6a gane ta ba "
Yah Omar yayi dariya tare da cewa "sadeeq musaddiq wannan ita ce k'anwa ta mufidah, ke kuma mufidah wad'annan sune sadeeq abokina musaddiq kuma k'anin shi, kuma nasan kin san Alhj Abubakar daddy aminin abba "
Gid'a kai tayi alamar ehh ta gane sannan cikin sanyin murya tace
"ina yinin ku"
Sam bata kula da musaddiq ba shi ma hkan jin wata murya mai shegen dad'i tana gaida su yasa shi jiyo wa ya Kalli wajen nan kuwa suka had'a ido da musaddiq tuni annurin fuskar shi da annurin fuskar ta suka d'auke lokaci d'aya ta wani juyar da kanta gefe, sai yah sadeeq ne ya amsa gaisuwar ta ta cikin murmishi, nabila kuwa cikin mamaki take kallon musaddiq sai dakyar ta iya bud'e baki tace
"malam ina yini?"
Dak'yar ya iya bud'e bakin shi yace "lafia " daga hka yaja bakin yayi shiru, yah Omar kallon nabila Yayi yace
"ashe kun san shi? "
"ehhh malamin mu ne "
Cikin mamaki Yah Omar yace "malamin ku kuma shi da likita ne kuma, mene gaskiyar xancen sadeeq? "
"wlh Omar ra'ayin musaddiq ne amman naji yana cewa ya fara gaji da koyarwar, xai fara aiki a wani hospital kafin a kammala gina nashi "
"okay hkan yayi kyau mu yanka cake din don idan muka biye wa hirar nan xamu iya 6atawa mutane lokaci "
"alright hkan yayi kyau"
Matsawa suka yi daf da cake din wad'annan xaratan maxajen su uku da kyawawan enmatan nan su biyu, amman musaddiq da mufidah babu fara'a akan fuskar su idan ka d'auke Yah Omar, Yah sadeeq da nabila k'ayataccen murmishi ne shimfid'e a fuskar su, da hka Yah sadeeq ya d'auke knife din yanka cake din tukunna ya kalli su sadeeq yace
"ku matso en uwa na mu yanka tare "
Gaba d'ayan su suka matso sannan yah Omar ya bawa nabila wuk'ar ta rik'e ya d'ora hannun shi kan nata sannan ya sadeeq yasa hannun shi kan na Yah Omar sai mufidah sannan musaddiq shine na K'arshe ya axa hannun shi kan mufidah lokaci d'aya suka ji wani shock but sai suka maxe kawai nan aka kirga 3 sannan suka yanka a tare nan fah aka dunga watso musu wasu kyawawan red flowers masu d'aukan pictures da video suka cigaba da aikin su, nan yah Omar ya yanka cake ya bawa mufidah, nabila, sadeeq sannan musaddiq hka su ma suka gutsuro suka bashi sosae sun burge mutane a wajen har wasu na tunanin ko en gida d'aya ne saboda ganin su farare kuma kyawawa dasu.
Musaddiq ne ya xame daga wajen yaje ya samu waje d'aya ya xauna yana danna wayar shi nan fah enmata suka dunga xuwa inda yake amman ko kallon arxiki baya yi musu hka xasu karaci surutun su Amman kamar da dutse suke dole hka xata tashi ta bar wajen.
Ashe mufidah tana kula da yanda yake nan fa ta k'ulu kamar itace enmatan da yake wulak'anta war, tsaki taja tare da cewa "ji be shi kamar wani sarki sai kallon mutane yake d'ai d'ai "
Nabila wadda ta ji ta sai ta harare ta, yana cikin danna wayar tashi ne aka kirawo shi don hka ya mik'e xai fita daga wajen, a lokacin mufidah ta tashi daga kan kujerar hannun ta rik'e da cup Wanda yake cike da juice din strawberry xata guje wa kallon da sadeeq yake yi mata, taxo wajen kofar dai dai fita daga wajen shi kuma musaddiq ya taho sai ya take mata kafa da takalmin shi "washhh Allah " abin da mufidah ta fad'a tana runtse ido saboda tsabar xafin da taji ko kallon Inda take bai yi ba bare yayi mata sannu kuma yana sani ya take ta ganin yanda ya takata ko sannu bai ce mata kamar ya taka dutse yasa mufidah fusata ranta yayi mugun 6aci da abin da yayi mata a fusace ta bishi wajen.
Yana tsaka da amsa waya ne ya juya bayan shi bai ankara ba yaji saukar wani abu mai sanyi a jikin shi tun daga saman kafad'ar shi har xuwa cikin rigar shi da sauri ya juyo ae kuwa suka had'a ido da mufidah hannun ta rik'e da cup d'in lemo alamar shi ta xuba mishi, kallon jikin shi yayi yaga gaba d'aya kayan sun 6aci don lemon ja ne tuni fuskar musaddiq tayi ja saboda tsananin 6acin rai da takaicin wannan abin da yarinyar nan tayi mishi don hka a fusace yayo kan mufidah...........
Wayyo mufidah yau ta ta6o mutumin nata fiye da ko yaushe.
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*written by*
Aishat A muh'd
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
_wannan page d'in naki ne k'awata ta arxiki Aishat Aliyu garkuwa tare da sadiya bashir (Sardy bash), ku sani kuna rai na ngde sosae da k'aunar da kuke nuna min Allah ya k'ara basirah Allah ya bar xumunci, ina muku fatan alkhairi en uwa_🤝😻
*Page 7*
*WASHE GARI*
A hankali yake bud'e idanun shi daga wani nauyayyen bacci da ya d'auke shi bayan sallahr asuba da ya dawo daga masallaci sai lokacin ya samu cikakken bacci, d'an bud'e idon shi yayi Kad'an sai yaga wani abu kamar maciji a saman blanket din da yake rufe dashi yana kallon shi har da d'an xaro harshen nan da yake.
Lokaci d'aya ya k'arasa bud'e idanun shi gaba d'aya tare da murxa su ae kuwa ba mafarki bane gaske ne maciji ne akan blanket din yana taho wa xuwa kanshi gashi bak'i wuluk sai xare harshe yake ae kuwa musaddiq a firgice ya tashi daga kan bed d'in ya mik'e tsaye cikin matuk'ar tsoro da tashin hankali ganin micijin again wurin shi yake taho wa yasa shi daka wani uban tsalle ya diro daga gadon yana furta Innalillahi don ba k'aramin tsorata yayi ba gaba d'aya ya fara had'a wani uban gumi.
Yah sadeeq da yake bakin kofa yana danne dariyar shi hannun shi rik'e da remot yasa ni asashen shine yasa wa musaddiq micijin ga remot a hannun shi yana control din shi danna wani gefe yayi acikin remot din ae kuwa da sauri micijin yabi musaddiq inda yake tsaye yana karkarwa don baxai iya fita ba tun da micijin bayan shi yana kallon kofar shigo wa iya tsorata musaddiq ya tsorata ba Kad'an ba ganin micijin yayo kan shi da sauri ya sashi fara tsalle tsalle yana ja da baya kok'arin shi ya shige toilet ya rufe don yana ganin Idan ya shiga toilet ya tsira.
Yah sadeeq da ya kasa danne dariyar shi ya kyalkyale da dariyar mugunta jin dariya yasa musaddiq kallon bakin kofar yana kallon Yah sadeeq cikin tsorata yace
"Yah sadeeq don Allah ka taimaka min micijin ne kada ya harbe ni please "
Yah sadeeq ne ya shigo cikin d'akin sosai ya nufo inda micijin yake cikin tashin hankali musaddiq yace "kada ka taho min brother xai harbe ka "
K'arasa wa yayi Inda micijin yake ya d'auke shi da hannu cak tuni musaddiq ya runtse idon shi saboda kid'ima amman jin Yah sadeeq yana kyalkyala dariya yasa shi bud'e idon da sauri ganin shi yayi ya rataya micijin a wuyan shi yana cewa "Kaiii matsoracin likita na roba ne fah wasa nake ma kada ka sume min "
Shiru musaddiq yayi ya xuba wa micijin idanu sosai don ya tabbatar da abin da Yah sadeeq ya fad'a
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 23