Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yasa hankalin Mufidah kwanciya ta fara gyara jikin ta sai da ta gabatar da sallah tukunna ta d'an yi light make up kafin ta shirya cikin wata pink gown colour d'in pink d'in mai d'an duhu kad'an bata kai har k'asa ba mai k'aramin hannu akwai kwalliyar duwatsu bak'ak'e a jikin gown d'in. Gyara gashin kanta tayi tare da d'aure shi da ribbon irin daga gefen nan tayi parking d'in shi tayi kyau sosai, different perfumes tayi using dashi har dasu humra masu kamshi sosai, ta kalli kanta a mirror ta tabbatar tayi yanda take so sannan ta zura bak'in flat shoes ta fito zuwa parlour tana tafiyar ta a nutse. Tun daga nesa Musaddiq ya hango Mufidah tana taho wa yana zaune kan dining table shi da Afnan suna cin abinci,sakin baki da hanci yayi yana kallon Mufidah gashi ya cika spoon da abinci ya kai kusa da bakin shi amman ya kasa k'arasar dashi cikin yana kallon ta. Har sai da ta k'arasa dining d'in sannan ta rik'e hannun shi da yake dauke da spoon ta k'arasar dashi cikin bakin shi, sai a time d'in ya dawo hayyacin shi gashi ba bakin magana saboda abincin da yake bakin shi. Sai Kallon da yake bin ta dashi tare da yi mata alama da hannun kinyi kyau ita ma da ido tayi mishi alamar nagode suka sakar wa junan su murmishi kafin su mayar da hankalin su kan cin abincin. Bayan sun gama ne Musaddiq ya kalli Mufidah yace "ki shirya zamu fita yanxu" D'an kad'a idon ta tayi tare da harshen ta wanda hakan ya tafiyar da Musaddiq zuwa wani wajen daban tace "ni ai na gama shirya wa mayafi kawai zan d'auka" Cikin salon tsokana tayi mishi maganar, hararar ta yayi kafin yace "ai ba tallan ki zan je yi ba, idan baki son zuwa sai mu tafi da Afnan " Cikin sauri ta mik'e tana cewa "tabd'ijam kama fara ai idan baku tafi da ni kuma ba inda xaku je " Tana k'arasa fad'in hka ta wuce bedroom Musaddiq ya bita da kallo yana had'iyar yawu sai da ta shige bedroom kafin ya dauke idon shi ya furzar da d'an huci yana cewa "huh Mufidah rigima don kinsan bazan jure ba ne shi yasa kika fad'i hkan " "daddy ita ma Mami rigimar ce da ita naji d'axu ma tace maka rigimamme? " Hannun shi yasa yaja karan hancin ta yana murmishi yace "Ohhh Afnan surutu ba na hana ki tambayar komai ba? " Langa6e kanta tayi gefe guda tare da cewa "Sorry daddy na dai na " "Yawwa 'yar albarka " Cikin shagwa6a tace "ni daddy big teddy bear xaka siyo min wadda tafi ta gidan mumy girma " "Angama baby na za'a siya miki " Rungume shi tayi cikin murna tana cewa "thank u so much daddyna " Kissing d'in ta yayi a kumatu yana k'ara rungume ta, yana son Afnan sosai jin ta yake tamkar sadeeq, tunawa da sadeeq da yayi ne ya haifar mishi da kewar d'an uwan nashi addu'a kullum idan yayi sallah sai yayi mishi wani lokacin ma idan tunanin shi ya fad'o mishi xai yi mishi ko kuma idan ya d'auko picture d'in su wanda suka dauka a tare yana kallo yana kewar d'an uwan shi duk jikin shi yayi sanyi surutun Afnan ma sama sama yake jin ta.............. Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *£xclusive Writers Forum* *Likes nd comment's fb page*👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com *PAGE 55* Mufidah ce ta fito cikin wata gown milk colour da adon flowers bak'i tayi rolling kanta da black veil tayi kyau, tana k'araso wa parlour inda suke tace "ai na d'auka kun tafi kun barni? " D'ago kanshi ya kawar da duk wata damuwa a fuskar shi ya kalle ta tare da cewa "kinci darajar Afnan da tace mu tsaya ki amman da tuni mun tafi " Turo bakin ta tayi irin na shagwa6ar nan kafin tace "ni na fasa fitar ma ku tafi " Kallon Afnan yayi tare da cewa "tafi mota ki zauna gani nan " Cikin murna Afnan ta fice da d'an gudun ta, kallon shi ya mayar kan Mufidah yana cewa "haba habibty ki taso mu tafi kinsan bazan ji dad'in fitar ba idan ba k.... " Ganin yanda Mufidah take kallon shi ne yasa shi tuna su6utar bakin da yayi ya wayance da cewa "ba fah da wata manufa na fad'a ba kada kiyi tunanin wani abin " Ya k'arasa fad'i yana tashi tsaye, girgixa kai Mufidah tayi tana murmishi cikin zuciyar ta mai cewa "ina mamakin wannan halin naka Musaddiq, kana barin abu cikin zuciyar ka ni kuwa zan sanya ka ka furta min sona cikin zuciyar ka a yau ba sai gobe ba insha Allah, tun da na gano ko wace sweet babyn ka " Tana k'arasa fad'in hka cikin zuciyar ta ta saki murmishin mugunta tare da mik'e wa tsaye, kallon ta yake yaga tana ta zuba murmishi ita d'aya yace "lafian ki qlau kike murmishi ke d'aya? " D'an murgud'a mishi baki tayi tana cewa "lafiyan kenan " Tana gama fad'in hka ta fice da sauri zuwa compound d'in bin ta yayi a baya yana murmishi shima cikin zuciyar shi yana cewa "yarinya yau zaki yi bayani don sai kin furta min abin da yake kunshe cikin zuciyar ki tukunna zan fallasa miki sirrin zuciya ta ". Sun zazzagaya wajen shak'atawa dasu mall sosai sun yi shopping abubuwa da yawa musamman kayan ci da na sawa abubuwa dai da yawa, tuni Afnan ta gaji har bacci ya kwashe ta a mota tana rungume da sabuwar teddyn ta. Daga k'arshe suka wuce wajen wani beach bayan yayi parking d'in motar shi ya sanya mata key suka jera suna tafiya ba k'aramin kyau da dace wa suka yi da junan su ba, d'an satar kallon Musaddiq tayi taga yana kallon wani gefe guda d'an murmishi tayi tana ayyana me zata yi yanzu wata dabara ce ta fad'o mata. Ai kuwa take ta aminta da dabarar daman hill shoes ta sanya sai kawai ta gurd'e k'afar ta tana sani ta tafi zata fad'i har da wani runtse idon ta kamar da gaske da k'arfin tace "wayyo Allah Musaddiq " Da sauri ya jiyo da kanshi ganin tana kok'arin kaiwa k'asa cikin sauri ya rik'o ta hannun shi yana tallafe da hips d'in ta d'ayan kuma da hannun ta, hango tsananin rud'e wa tayi cikin kwayar idon shi. "wash Allah na kafata" Ta furta hkan tana yatsina fuska kamar zata fashe da kuka, cikin sauri da damuwa kan fuskar shi yace "Ohhh mene ya samu k'afar? " Ya k'arasa fad'i yana kallon ta, cikin shagwa6a tace "ciwo take min " "sorry mu k'arasa mu zauna sai na duba miki" Gid'a kanta tayi sannan ya d'ago ta, sai tak'i take k'afar ya kalle ta yana cewa "ya dai? " "ni ciwo take min bazan iya tafiyar ba " Kamar da gaske take fad'in hka shi yasa bai kawo wani abun cikin zuciyar shi ba ya sanya hannun shi ya dauke cak suka fara tafiya hannun ta dukka biyun suna rataye a wuyan shi, fuskar tana wurin wuyan shi duk wani numfashi da take fitar mai d'umi yana dukan wuyan nashi tuni Musaddiq ya fara jin wani canji yanayi na daban a jikin shi, Mufidah kuwa sai murmishi take abin ta tana kalle kallen mutanen da suke wurin wajen ya birge ta sosai ba ruwan wani da wani kowa harkar gaban shi yake. Sun k'arasa inda zasu zauna ya sauke ta a hankali da sauri Mufidah ta canja fuskar ta irin ta damuwa sai wani yatsina fuska take, zaunar da ita yayi yana cewa "sannu " Ya fad'i yana tsugunna wa a gaban ta tare da cire takalmin da yake k'afar ta bayan ya cire ne ya tsaya kallon kyakkyawar k'afar ta ta kafin kuma ya fara d'an daddannawa kad'an cikin nutsuwa da hankali don kada yayi mata da k'arfi ta sake jin wani ciwon. "wash! da zafi ni ka bari zai warke fah " Ta fad'a tana k'ak'alo hawayen dole. "kinsan bazan jure ganin ki cikin ciwo ba don hka oya ki tsaya na gani " D'ago kanshi yayi ya kalle ta sai yaga tana hawaye cikin rud'ewa ya saki k'afar ya zauna tare da janyo ta jikin shi yana bubbuga bayanta yana cewa "sorry habibty na bari ki daina kukan nan kin ji? " Ai kuwa ta 6are baki ta saki kukan shagwa6a gashi tana kiran wayyo k'afar ta, kuma idan ya sanya hannu zai ta6a ta dad'a k'arfin kukan tana girgixa kai kada ya ta6a da zafi. Nan Musaddiq ya sake rud'ewa sosai shi yanzu ya zai yi mata ne idan zai ta6a k'afar zafi gashi bai ta6a k'afar ba tana mishi kukan zafi kuma shi bazai jure jin kukan ta ba, ganin tak'i shiru duk ta d'aga mishi hankali ne yasa shi had'e bakin shi da nata. D'an tutture shi ta fara yi ya sake matse ta a jikin shi d'if tayi da ita tana kar6ar sak'onnin Musaddiq daman ai kukan na k'ak'ale ne, sai da ya tabbatar ta had'iye kukan nata tukunna ya cikata suna had'a ido ya sanya d'an yatsan shi d'aya ya dungure mata kai yana cewa "rigimammiya ko Afnan bazata yi rigimar ki ba " D'an hararar shi tayi tana turo bakin ta tace "Duk rigima ta dai wani yafi ni " Kallon ta yayi yana cewa "dawa kike? " D'an kad'a idon ta tayi tana cewa "da wanda ya tsargu " Nuna ta yayi yana cewa "lallai yarinyar nan kin rainani da yawa xanyi maganin ki yanzu " Kafin ya k'arasa fad'i ta mik'e da sauri zata gudu ya kawo hannun shi zai kamata sai ta goce tana mishi dariya har da gwalo, nan ya biyo ta suka fara gudu tuni su Mufidah an mance ciwon k'afar karyar da aka yi ta fara gudu tana dariya. Bata yi wani nisa sosai ba ya cafkota suka zube cikin farin yashin da yake k'asan wajen suna dariya tare da sauke numfashi da sauri da sauri, kallon junan su suke kafin Musaddiq ya sanya hannun shi ya d'an lankwasa d'an yatsan ta d'aya har yayi k'ara cikin jin zafi tace "wash ni me nayi maka ne da zafi fa?" Yana kallon face d'in ta yace "tunawa nayi da ciwon da k'afar ki take yi yanzu naga kuma kina gudu " "bata warke ba na dai na jin zafin " Ya bud'e bakin shi zai yi magana wayar shi ya fara k'ara alamar kira zaro wayar yayi ganin sunan Muh'd ya sanya shi picking d'in wayar, d'aya hannun shi kuwa ya janyo Mufidah ya kwantar da ita saman chest d'in shi don yau jin shi yake cikin wani irin farinciki da nishad'i. Muryar Muh'd ce ya tsinkayo yana cewa "Hey lover boy kana ji na?" Murmishi Musaddiq yayi yana cewa "ina jin ka mana ya akayi guy? " "Qlau jin ka nayi wajen 2 day's baka kirawo ni ba na kirawo ka kuma baka yi picking ba " "sorry guy abubuwa ne suka yi min over " Cikin zolaya Muh'd yace "ko kuma an tsaya cin soyayya ba an mance da ni " Er dariya Musaddiq yayi yana kallon idon Mufidah yace "kusan hkne fah guy kasan mutum idan yana moment d'in nan sai a slow " Wata dariya Muh'd ya kwashe da ita yana cewa "Ohhh sake maimaita min ban ji sosai ba " "kai fa d'an air ne wani lokacin nasan ka ji abin da na fad'i " "lallai guy kace kana nan kana fanshe soyayyar ka ta tsayin shekaru, hkan yayi kyau Allah ya kawo mana baby boy ko girl " Hannun Musaddiq yana kan Mufidah yana shafawa yace "Amin aboki tare da kai " "tabd'ijam an fad'a maka zan jira ka ne ai ni an kusa juye min " "Ah haba aboki da gaske? " Musaddiq ya fad'a cikin farinciki, cikin tabbatar wa Muh'd yace "wallahi aboki da gaske na ke " "wowww na taya ka murna sosai guy " Jin d'an hayaniya yasa Muh'd yace "kana ina ne Musaddiq ?" Cikin murmishi yace "me ka ji ne? " "hayaniya na ji kamar ma baka gida " "ina wurin beach muna hutawa " Cikin dariya Muh'd yace "wow lover boy kace kana hutawa, a dai yi a hankali kada ka 6ata mana Afnan don nasan ba hak'uri ne da kai ba ana barin sai bata nan " "Allah ya shirya ka Muh'd" "Amin aboki thank for your du'a" Kafin kuma ya cigaba da magana in seriously yace "Musaddiq ya kamata ka dawo nigeria fah kaga kai d'aya su mumy suke dashi a yanzu duk da basu nemi wani abin sun rasa amman nasan basa son zaman ka a australian, sun fi son zaman ka a tare da su ya kamata ka dawo " Ajiyar zuciya Musaddiq ya sauke a hankali kafin yace "nima nayi tunanin hka friend but insha Allah nan da d'an lokaci xamu dawo" "Yawwa d'an uwa, agaida min da Mufidah nd Afnan, kace wa Mufidah kasa ta mance da ni tun da kuka zo bamu ta6a yin waya ba ina jin zata kirawo k'awar ta (nafisat matar Muh'd),su sha hira amman ban da ni " Dariya Musaddiq yayi kafin yace " hkan ne dai dai guy " Shima Muh'd yana dariya yace "kai koh?, shikenan dai sai anjima " Yana gama fad'in hka Muh'd ya katse wayar lokaci d'aya Musaddiq ya saki ajiyar zuciya yana sake hugging d'in Mufidah zuciyar shi tana cikin farinciki............. Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *£xclusive Writers Forum* *Likes nd comment's fb page*👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com *PAGE 56* Yana gama fad'in haka Muh'd ya katse wayar, lokaci d'aya Musaddiq ya saki ajiyar zuciya yana sake hugging d'in ta zuciyar shi tana cikin farinciki, gaba d'aya ya mance ma inda suke ya mance yana tare da Mufidah a kusa zuciyar shi ta ingiza bakin shi har ya furta kalmar "i luv u Mufidah " Ba tare da ya shiryawa hakan ba, sai da ya gama furta maganar sannan ya dawo cikin hayyacin shi ya tuna su6utar bakin da yayi. Mufidah kuwa kusan suman zaune tayi saboda jin kalmar da ta fito daga bakin Musaddiq kallon shi take fuskar ta d'auke da tarin mamaki. Wayancewa yayi ta hanyar hararar ta kafin yayi magana cikin sautin tsawa yace "malama d'aga ni zan tashi kin wani danne ni " Girgiza kanta kawai tayi tana tashi daga jikin shi, bata ko kalle shi ba ta nufi inda suka yi parking motar su ta tsaya tare da sunkuyar da kanta tana kallon k'asa zuciyar ta sam babu dad'i, don ta tsani ayi mata tsawa a rayuwar ta. Bin ta yayi da kallo jikin shi yayi sanyi sosai wani mugun tausayin ta ne ya rufe shi,akan mene zai yi mata tsawa me tayi mishi, dole yayi yak'i da zuciyar shi don samun zaman lafiyar su, bazai yiwu su cigaba da irin wannan zaman ba. Jikin shi a sanyaye ya fara tafiya zuwa inda take, bud'e motar yayi da key d'in hannun shi, cikin sauri Mufidah ta shiga ta zauna har yanzu still bata kalli inda yake ba, shima shiga yayi ya zauna ya kasa kunna motar su tafi kallon ta yake yi ko zata d'ago kanta ta kalle shi. Sun d'auki tsayin mintuna bai ga alamar zata yi mishi magana ba ko zata kalle shi, sai kawai yayi wa motar key suka bar beach d'in, tafiya suke shiru kowannen su zuciyar shi da abin da take sak'awa, sam dawowar bata yi musu dad'i ba kamar yanda suka taho ba cikin farinciki da nishad'i ba. Suna k'arasa wa gida yana gama parking Mufidah ta bud'e murfin motar ta fita tare da bud'e murfin motar na baya ta d'auki Afnan dakyar ta fito tana tafiya har tana kok'arin fad'uwa. Da kallo ya bita fuskar shi da zuciyar shi d'auke da damuwa yana son yi mata magana but bakin shi yayi mishi nauyi sosai ya kasa yi mata magana, yana kallon ta har ta shige ciki tukunna ya fito daga motar tare da d'ebo shopping d'in da suka yi ya nufi cikin gidan. Ko da ya shiga bata parlour kayan hannun shi ya zube su tare da zama kan kujera yana dafe da kanshi, tunanin hanyar da ya kamata ya bi don ya rarrashe ta yake, yasan bai kyauta ba da tsawar da yayi mata. Mufidah kuwa tana shiga d'aki ta kwantar da Afnan kan bed sannan ta wuce toilet ta d'auki tsayin mintuna 5 a ciki kafin ta fito, fitowa tayi daga d'akin zuwa kitchen don ta had'a musu abincin dare. A parlour ta tarar dashi zaune bata kalli inda yake ba ta wuce kitchen abin ta, da kallo ya bita zuciyar ta gama yanke hukuncin a yau ba gobe ba zai bayyana mata irin tarin son da yake mata. Lumshe idanun shi yayi sakamakon fara jin k'amshin girkin da take yi ya fara dukan hancin shi, yana nan zaune Afnan ta tashi daga bacci ta fito zuwa parlour, cikin jikin shi ta shiga tana kwanciya, shafa mata kanta kawai yake don baya cikin nutsuwar shi. Bayan ta gama girkin ne ta jera a saman dining table, duk zirga zirgar da take akan idon shi d'in yana nan zaune a parlourn, bayan ta gama ne ta gyara kitchen sannan ta fito zuwa parlour ta gyara ta fesa air fresheners masu k'amshi. Tana gama wa da nan ta nufi d'akin Musaddiq ta gyara mishi tsaf, tare da sanya mishi room freshener, sai da taga komai yayi mata yanda take so sannan ta bar d'akin, tukunna ta fito ta nufi d'akin ta gyara shi tayi shima yayi tsaf dashi. Sannan ta fito zuwa parlour inda Musaddiq yake ta nufa, sai da ta zo gaf dashi sannan ta kalli Afnan tace "Afnan zo nayi miki wanka " Tashi Afnan tayi ta nufi inda Mufidah take tsaye, hannun ta ta rik'e suka wuce d'aki, ta bar Musaddiq zaune anan cikin rashin samin mafita. Bayan tayi wa Afnan wanka ta gyara mata jikin ta ne cikin kayan bacci, tukunna Mufidah ta d'ebo musu abincin su ta bar na Musaddiq akan dining table, bayan sun gama ci ne, Mufidah ta kwantar da Afnan kan ta yana kan cinyar Mufidah tana karanta mata wani english novel's mai dad'i. Lokacin da Musaddiq ya wuce bedroom d'in shi yaga bata yi fushi ba ta tsaya ta gyara mishi sosai, sai yaji ya k'ara jin tausayin ta, wanka yayi tare da yin alwala ya fito, jallabiya ya zura ya fara gabatar da sallah bayan ya idar ne ya d'an jima yana addu'o'i kafin kuma ya tashi. Cire jallabiyar yayi ya canja da wasu white sleeping dress ya fesa turaren shi masu k'amshi, tukunna ya fito zuwa parlour dinning table ya nufa, amman wayam ya gani ba Mufidah da Afnan kuma wannan ne time d'in da suke had'u wa wajen cin abincin dare. Jikin shi ne ya k'ara yin sanyi a time d'in da ya tabbatar iya nashi abincin ta bari, bai wani iya ci sosai ba ya d'an ci kad'an ya tashi koma parlour ya zauna, tv ya k'ura wa ido yana kallon film d'in Jack the giant slayer da suka nuna wa a time d'in but zuciyar shi tana tunanin Mufidah. Tun Afnan tana sauraren ta har bacci ya d'auke ta, ganin tayi bacci ne yasa Mufidah gyara mata kwanciyar, ta d'ora kanta saman pillow ta lullu6e ta da blanket tare yi mata addu'a sannan tayi kissing nata a kumatu, d'ayan hannun ta yana gyara mata gashin kanta ganin ya rufe mata face d'in ta. Tashi tayi tsaye taga Afnan tana rik'e da hannun ta, murmishi ta saki tare da sunkuya wa ta cire hannun ta a hankali wanda Afnan ta rik'e, sannan ta rage hasken d'akin ya d'an yi duhu. Toilet ta wuce ta fara yin wanka, bayan ta gama ne sannan ta fito zuwa gaban dressing mirror ta fara gyara jikin ta tare da amfani da body sprays a jikin ta da humra. Sleeping dress d'in ta ta d'auko a cikin wardrobe nata, cire towel tayi tana kok'arin sanya kayan baccin, sai ji tayi an rungume ta ta baya, a tsorace ta saki er k'ara tare juya wa don ganin wane, jikin ta har rawa yake don ba k'aramin tsorata tayi. Saukar sanyayar muryar shi taji cikin kunnen ta yana cewa "calm down matsoraciya ni ne fah " Juyo wa tayi tana hararar shi cikin tsiwa tace "malam baka iya sallama ba ne zaka shigo min d'aki kai tsaye? " Kallon ta yake fuskar shi d'auke da murmishi cikin zuciyar shi yana cewa ta rama kenan, a fili kuma yace "ai ba laifi ba ne da na shigo d'akin mata ta koh?" Cikin mamaki tace "matar ka!" "Ehhh mana, ko laifi ne ?" D'an ta6e bakin ta tayi kawai, sam ta mance a yanayin da take, ganin irin kallon da yake bin ta dashi ne yasa ta kallon jikin ta. Zaro ido tayi tare da d'ora hannu akan ta tana sakin 'yar k'ara tare da zube wa a k'asa, ta had'e jikin ta waje d'aya cikin jin kunyar shi sosai. Dariya ta bashi sosai sai da yayi mai isar shi kafin ya tsugunna a gaban ta yana kallon ta yana cigaba da dariya. Cak ya tsaya da dariyar saboda ganin hawaye yana fita a idon ta, hannun shi ya sanya tare da kama kunnen shi dukka biyun yace "I'm so sorry Mufidah, nasan nayi miki laifi d'azu na tsawar da nayi miki, bazan k'ara ba fushin da kika yi dani, bazan iya jure hakan ba, forgive me please " D'an girgiza kanta tayi kawai bata iya cewa komai ba, langa6e kan shi yayi tare da cewa "please Mamin Afnan" Turo bakin ta tayi tare da cewa "ka fita idan na gama shiryawa ma yi maganar" Kafin ta ankare har ya sure ta gaba d'ayan ta ya nufi hanyar fita daga d'akin nata, don yau yana son ya warware matsalar su.......... Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *£xclusive Writers Forum* *Likes nd comment's fb page*👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com *PAGE 57* Kok'arin sauka take but yak'i sakin ta har ya k'arasa cikin d'akin shi, kan kyakkyawan bed d'in yayi mata masauki, cikin shagwa6a tace "ni fah bacci nake ji malam " D'an zaro ido yayi yana dariyar mugunta kafin yace "yarinya ai yau ke da bacci sai gobe " Ya k'arasa fad'a yana kashe mata ido d'aya, duk da kuwa bata ganin shi sosai saboda d'akin babu wadataccen haske, hararar shi tayi tana kok'arin sauka daga kan bed d'in. Ai kuwa ya sanya hannun shi ya fisgo ta cikin jikin shi, ta bud'e baki zata yi magana taji ya rufe shi da nashi, sai da yayi kissing d'in ta son ran shi, kafin ya cika ta suna kallon idanun junan su. Cikin wani irin shauk'in Mufidah, da wata irin murya da Mufidah batasan yana da irin ta ba yace "ina son ki Mufidah, i luv u Mufidah " Jin saukar muryar shi Mufidah tayi kamar a mafarki yana furta mata wannan daddad'an kalmar, ko kwakwkwaran motsi ta kasa yi, kamo hannun ta yayi tare da had'e su da nashi ya sake cewa "Ina son ki Mufidah, kina sona ke ma, ina son ki furta min wannan kalmar da na dad'e ina sauraren ta daga bakin ki ? " Wasu hawaye ne suka zubo daga idon ta, wanda na kasa tantance su na farinciki ne ko akasin haka, ganin hawaye suna zuba cikin idon ta yasa Musaddiq rikice, ba dai bata son shi ba, kasa magana tayi sai kukan da take tana kallon shi. Idanun Musaddiq sun yi ja saboda tsabar tashin hankali kada Mufidah tace bata son shi, hannun shi ya sanya dukka biyun ya rik'o kafad'ar ta, cikin sanyin murya yace "Mufidah kiyi min magana don Allah, ki fad'a min dalilin zubar hawayen ki " Sam Mufidah tak'i bud'e baki tayi mishi magana sai kukan da take, ba k'aramin rud'e wa yayi ba jikin shi har rawa yake, ga gumin da yake tsatstsafo mishi na tashin hankali,zuciyar shi bugawa da k'arfi take kamar zata faso kirjin shi ta fito. kunna hasken d'akin yayi tare da sakkowa daga kan bed d'in, bud'e locker d'in bedside yayi ya d'auko diary d'in shi, sake hawa kan bed d'in yayi tare da kamo hannun Mufidah ya damk'a mata diary d'in a hannun ta, cikin murmishi yak'e yace "ki bud'e ki karanta abin da yake

Chapter 20 of 23