nashi idanun sun yi ja sosai lokaci xuwa lokaci yana goge hawayen fuskar shi, koda suka koma room d'in da aka kwantar da sadeeq basu cewa mumy komai ba.
*AFTER ONE WEEK*
A ciki wannan satin al'amara sun k'ara tsanani don sadeeq ba lafia sosai yau lafia gobe ko anjima ciwo ya tashi duk yabi yayi mugun rame wa, hka ma mufidah sai katon cikin da yake rinjayar don a yanxu ta shiga 9 month's kuma tak'i yarda ta bi su mumy gida daddy ya xauna da sadeeq kullum tana kusa dashi bata son tayi nisa dashi ko na second d'aya, idan ka kalli mufidah sai ka mugun tausaya mata.
Duk wata hanya da musaddiq xai samu labarin rashin lafiyar sadeeq daddy ya toshe a yanxu ma daddy shirye shiryen fitar da sadeeq India yake duk wasu shiri ya gama xuwa gobe da dare jirgin su xai tashi xuwa indian, koda kud'in shi xai k'are xai nema wa sadeeq lafia.
Mufidah ce a xaune kan kujera hannun ta d'auke da Qur'an tana karanta wa sadeeq suratul alrahman cikin muryar ta mai dad'in karatu duk kuwa da yanda muryar ta dashe, idan ta kai k'arshen surar sai yace ta dawo hannun ta d'aya yana rik'e da hannun shi.
Idanun shi a lumshe suke yana sauraren ta, kad'an kad'an take jin mararar ta tana murd'a wa sai ta d'aure bata kawo komai a ran ta ba don tun da cikin ta ya girma take fama da hkan.
Can kamar mintuna goma sai taji ciwon ya k'aru don bayan ta da marar ta suka rik'e lokaci d'aya suna yi mata wani axababben ciwo tuni ta fara had'a uban gumi duk da kuwa sanyin ac d'in da yake room d'in, duk dauriyar da take yi batasan lokacin da ta bar karatun ba ta furta "Wash Allah na"
Tana dafe da kugun ta wanda take jin shi kamar ya 6alle ya rabu da gangar jikin ta, da sauri sadeeq ya bud'e idanun shi ganin yanda mufida take had'a gumi fuskar nan ta ta tayi ja sosai tuni ya mik'e da sauri tare da rik'o ta yana cewa
"Mufidah lafia kuwa mene yake damun ki?"
Duk a rud'e ya tambaye ta hannun shu ta damk'a ta rik'e gam cikin axabar ciwo tace
"Sadeeq ka yafe min mutuwa xan yi ka fad'a wa su umma, Abba, daddy da mumy su yafe min don Allah"
Gaba d'aya ta kid'ima sadeeq sosai lokaci d'aya kan shi yayi wata irin sarawa amman duk da hka cikin dauriya yace
"No mufida bata ki mutu ba nine xan mutu ki tashi please, ina ne yake miki ciwo?"
Ina babu bakin magana shi kuwa ya kasa tafiya ya kirawo muh'd gashi ba kowa a wajen, suna cikin hka Dr muh'd ya shigo kallo d'aya yayi wa mufidah yasan labour take don hka yace
" babban yaya haihuwa xata yi ae"
Yana gama fad'in hka ya fita ya kirawo wasu nurses biyu suka taho akan gadon tura mara lafia suka d'ora ta sadeeq hannun shi yana rik'e da hannun mufidah yana xuba mata sannu duk yabi ya rud'e ya gigice sosai da hka har suka shiga da ita labour room.
Har xai bisu ciki Dr muh'd ya rik'o shi tare da cewa " kayi hak'uri babban yaya xata haihu lafia insha Allah"
Rik'o shi yayi suka fara tafia sai ga Doctor Aishat nan xata shiga labour room d'in hannun ta dauke da hand gloves.
" yawwa Dr Aishat don Allah ki kula da ita sosai"
Murmishi tayi wanda ya k'ara mata kyau tace " Doctor kada ka damu xata haihu lafia insha Allah"
"thanks Dr Aishat"
Fadin muh'd " ka wuce hkan Dr" ta fad'a tana shige wa room din da mufida take.
Suna nan tsaye a wurin muh'd yayi yayi da sadeeq yaje ya kwanta amman yak'i, suna cikin hka su mumy, daddy, Abba, umma, nabila da Yah Omar suka shigo asibitin a tare kamar had'in baki, mumy ce ta fara cewa
"Lafia muh'd na gan ku anan?"
"Uhm mumy mufidah ce xata haihu"
Nan fah kowa yaja ya tsaya suna faman yi mata addu'ar samun lafia, gaba d'ayan su hankalin su a matuk'ar tashe.
Sun d'auki tsawon mintuna hamsin a wurin sadeeq yana tsaye har lokacin jiri ya fara ji yana daukan shi wurin yana juya mishi kafin kuma a hankali ya fara yin baya xai fad'i, duk basu ankara dashi ba sai Yah Omar da sauri ya nufi wajen shi yana k'arasa wa kuwa ya fad'o jikin shi.
Sai lokacin hankalin su mumy ya dawo wajen a matuk'ar rud'e suka yo inda yake gaba d'ayan su, muh'd kuwa doctor's d'in nan da suke duba sadeeq ya kirawo aka d'auke shi suka shiga dashi cikin room.
Wayyo Allah abin tausayi wad'annan familyn idan ka gansu a lokacin xaka yi matuk'ar tausaya musu saboda halin dasu ke ciki babu mai nutsuwa a cikin su gaba d'ayan su babu mai kwanciyar hankali, Matan kuwa irin su mumy, umma da nabila kuka suke yi sosai maxan ma basu da kwanciyar hankalin rarrashin su.
********
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ya fad'a bayan yayi xumbur ya tashi daga mummunan mafarkin da yayi, xama yayi akan gadon tare da kunna hasken d'akin duk da sanyin ac da fankar d'akin amman gumi yake had'a wa, kallo d'aya xaka yi mishi kasan hankalin shi a tashe yake.
Musaddiq kenan yau wajen kimanin wajen sati d'aya kenan yana wani irin mugun mafarki akan sadeeq da mufidah amman na yau yasha bambamci dana ko yaushe.
Idan yayi wannan mafarkin sai ya kirawo kowa ya ji muryar shi hankalin shi yake kwanciya amman ban da mufidah, duk da sadeeq yana gadon asibiti lokacin yana daurewa ya amsa mishi wayar kamar yanda yake amsa mishi da, but yanxu hankalin shi yayi gida kawai baxai iya jure wa ba yakai k'wana biyu bai ganshi a nigeria ba gaban d'an uwan shi da iyayen shi.
Wayar shi ya d'auko ya kira wata number tsayin mintuna goma ya d'auka yana waya da harshen turanci kafin kuma ya ajiye wayar, tashi yayi ya nufi wardrobe ya bud'e ya fara shirya kayan shi cikin trolley sai da ya had'a duk wani abin amfani tukunna ya rufe.
Toilet ya shiga yayi alwala ya fito ya fara nafila yana addu'ar Allah yasa mafarkan da yake kada su xama gaskia, sai da yayi sallahr asuba tukunna ya tashi yayi wanka ya shirya cikin wani black jeans da t-shirt black mai dogon hannu hatta belt da takalmi bak'ak'e ne, bayan ya fesa perfumes ne ya janyo trolley dinshi tare da jakar da take rataye a kafad'ar shi ta laptop da sauran muhimman abubuwan shi, fito wa yayi driver d'in shi ya kai shi airport.
Ko mintuna 30 bai yi da xuwa ba jirgin su ya tashi xuwa nigeria, gaba d'aya a matuk'ar kaguwa yake ya ganshi cikin iyayen shi da d'an uwan shi.
Lokacin da jirgin su yayi landing ya fito ya shak'i iskar k'asar sai yaji ya d'an samu nutsuwa don yana tunanin nan da en mintuna xai ganshi a gida, bai kirawo su ba a waya ya fad'a musu don surprise yake son yayi musu taxi ya d'auka har xuwa gida bayan ya sauka yana k'okarin biyan mai taxi d'in kud'in shi sai ga mai gadi nan ya fito cikin mamaki yake kallon musaddiq kafin kuma cikin girmama wa ya gaida shi, maigdin ne yace
"Yalla6ai as gaba d'aya en gidan basa nan suna asibiti"
A firgice musaddiq ya kalli maigadin yace " lafia, wane bashi da lafia?"
Sai lokacin maigadin yayi da nasanin fad'a wa musaddiq don daddy ya gargad'e su da hkan, cikin ina ina yace
"Bansan wanda bashi da lafiyar ba yalla6ai sai dai kaje suna can asibitin da alhj ya Gina maka"
Kafin ya k'arasa fad'i musaddiq yace "d'auki trolley d'in nan ka shigar min dashi gida"
Cikin rawar jiki maigadin ya d'auki trolley ya shige, shi kuma musaddiq ya shiga taxi d'in ya fad'a mishi inda xai kai shi............
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: [9/19, 3:54 PM] Aishat A Muh'd ✍🏻: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A muh'd
♻ E.W.F
_lokacin da Allah ya sakkowa da bawan shi wata jarabta ya kasance cikin furta innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yayi ta maimaita har sai ya samu nutsuwa, ita rayuwa da muke ganin ta kowanne mutum da irin tashi kaddarar don hka mu kasance cikin takatsantsan da rayuwa da bautawa Allah tare da kiyaye dokokin shi don idan mutuwa ta tashi xuwa daukan mutum ba shawara ake dashi ba, don kowanne ita yake jira tun da Allah swt yana cewa cikin suratul imran (kullu nafsin xa'iqatul ma'ut) kowanne mai rai xai d'and'ani d'acin mutuwa, don hka ina kira a gare ku da mu kyautata mu'amalar da mutane domin ka samu shaida mai kyau a bakunan mutane, sannan mu dage da aikata alkhairi da karatun al'Qur'an, addu'o'i, nafilfilo, istigfari, salatin annabi da sauran su, a dunga kyautata iyaye ana musu biyayya, idan kina da aure ana yiwa miji biyayya, ana yawaita yin xumunci da axumin nafila da sadaka, Allah yasa mu dace duniya da lahira, Ameeen thumma Ameeen_.
*PAGE 30*
Ba k'aramin wahala mufidah tasha ba kafin Allah ya taimake ta ta haihu bayan sun gyara babyn Dr Aishat sai da tayi wa mufidah d'inki don ba k'aramin k'aruwa tayi ba don tubarkallah babyn k'atuwa da ita sai da ta duba ta ita da babyn ta tabbatar suna cikin koshin lafia tukunna suka fito a tare da sanar dasu mumy an sauka lafia an samu baby girl, sosai sun yi murna nan suka kar6i babyn har suka shiga room d'in mufidah da take kwance tana huta wa suna mata sannu, duk bata amsa ba sai ma bud'ar bakin ta tace
"Mumy ina sadeeq?"
Shiru mumy tayi ta kasa magana ganin hka yasa mufidah yunk'ura ta tashi xaune dak'yar saboda d'inkin da aka yi mata cikin tashin hankali ta kuma cewa
"Ina sadeeq ne ina tambayar ku kun yi shiru?"
Abba ne yayi k'arfin cewa "ki kwantar da hankalin ki mufidah ciwon shi ne ya tashi likitoci suna kan shi suna duba shi"
Hawaye ne masu xafin gaske suka xubo daga idanun ta komawa tayi ta xauna tana kuka k'asa k'asa acikin xuciyar ta kuma addu'ar samun sauk'i take yi wa sadeeq, duk d'akin anyi shiru kamar ba mutane babu wanda yayi iya yunkurin rarrashin mufidah sai nabila.
A can kuma room din da sadeeq yake likitoci sun dukufa akan shi wajen ceto rayuwar shi, ana cikin hka nau'orar da take nuna yanda numfashin mutum yake tafiya tare da bugawar xuciya ta fara yin k'asa, a firgice muh'd ya kalli yanayin numfashin shi ya ga yana sauka har xuwa 50 tuni muh'd ya rud'e cikin rawar murya yake cewa
"Babban yaya kalle ni kada ka mutu please gashi mufidah ta haifa maka baby girl"
Kallon shi sadeeq ya tsaya yi kafin kuma yana jan wani numfashi dak'yar yace
"Muh'd taimaka ka d'auko min babyn na gani don Allah"
Cikin rawar murya yake cewa "to...to ina xuwa kada ka tafi ka barmu" murmishi sadeeq yayi mishi na d'aga kanshi, da wani irin gudu Dr muh'd ya fice ya shiga room d'in da mufidah take ciki ya banka kofar da k'arfi ya shiga gaba d'aya su mumy sun firgita da ganin shigowar muh'd bai bi ta Kansu ba ya d'auki babyn ya fita da ita da sauri su ma suka bi bayan shi har da mufidah wadda dak'yar take tafia nabila na rik'e da ita.
Tuni muh'd ya shige room din kafin su mumy su k'araso an rufe kofar dole suka tsaya hankalin su a matuk'ar tashe.
Da sauri muh'd ya k'arasa wajen gadon yana nuna wa sadeeq babyn, bai da ikon daukan ta saboda drip d'in da yake hannun shi hannun shi yasa ya shafi fuskar ta xuwa kanta kafin dak'yar ya furta
"Allah ya raya min ke ya albarkaci rayuwar ki Nana khadijah"
Kallon muh'd yayi tare da yin wani irin murmishi da sake tsurar da muh'd ya bud'e bakin shi dak'yar yace
"Muh'd ina son ka kular min da musaddiq, mumy, daddy, mufidah da kuma 'yata don nasan ke mutum ne nagari, ka rokar min yafiya wajen iyaye na da d'an uwana da matata da duk wasu abokanan hurd'ata, kace su yafe min Alhmdullilah nasan ba me bina bashi yanxu tun kafin ciwon yaci k'arfina na biya kowanne ma'aikacin company na kud'in su, daga k'arshe muh'd ina son ka daukar min alkawari guda d'aya"
Tari ne ya sark'e shi yana yi sosai gaba d'aya doctor's d'in nan biyu hawaye ne yake xuba a idanun su na tausayi, muh'd kuwa kuka yake wiwi cikin rawar murya ya ce
"Fad'i alkawarin ka babban yaya insha Allah xan cika maka shi"
Sai da tarin ya lafa kafin yace "ina son kada ka bari kowanne namiji ya aure mufidah sai musaddiq d'ina don nasan xai kular min da ita da d'an da na haifa don Allah muh'd ka cika min wannan burin"
Cikin kuka ya rik'e hannun sadeeq yace "na d'auki alkawari babban yaya xan cika maka shi amman baxa ka mutu ba xamu rayu tare da kai ka tashi please"
Murmishi sadeeq yayi bai k'ara magana ba sai wasu hawaye da suke xuba a idanun shi yana kallon 'yarshi a hannun sadeeq tana bacci.
D'aya daga cikin likitoci ne yace " muh'd numfashin shi yayi kasa sosai na 20 fah "
A wani irin xabura muh'd ya kai idanun shi kan nau'orar mai nuna yanayin numfashin mutum kafin yayi wani yunkuri yaji sadeeq yana furta Kalmar shahada lokaci d'aya kuma nau'orar nan ta ba da sautin d'il d'il d'il sai kuma ta d'auke, a lokacin shima sadeeq ya gama furta Kalmar shahada shikenan mai raba wa ta raba kullu nafsin xa'iqatul ma'ut (kowanne mai rai sai ya d'and'ani d'acin ta).
Lokaci d'aya fuskar shi ta d'auki wani haske tayi kyau sosai a sake fuskar nan tashi kamar a kira shi ya tashi, ja da baya muh'd ya fara yi da sauri d'ayan likitan ya kar6i jaririyar daga hannun muh'd ganin yana k'okarin sakin ta, girgixa kai yake yana hawaye kafin ya dawo jikin gadon yana rik'e sadeeq yana cewa
"No no sadeeq kada ka tafi ka barmu don Allah ka tashi please"
Ina sadeeq ko motsi bai yi ba, xube wa yayi k'asa ya hau kuka sosai likitoci nan suna rarrashin shin shi d'ayan ne ya rufe jikin sadeeq da wani farin mayafi har xuwa fuskar shi.
Xumbur muh'd ya mik'e yana kuka ya fito daga d'akin da gudu kici6is yayi da su mumy, daddy, mufidah, Abba, umma, Yah Omar da nabila a tsaye suna jiran fitowar su ganin muh'd yana kuka yasa su xuciyoyin su suka tsinke da fargaba.
Shi kuwa muh'd kasa magana yake sai kuka ta ina xai dubi idanun wad'annan bayin Allah ya furta musu sadeeq ya mutu kawai sai gani suka yi ya bar wajen da gudu yana kuka ko ina muh'd ya shige sai ayi ta kallon shi ganin babban likita kamar muh'd yana kuka.
Yaxo dai dai shiga office d'in shi suka yi karo da wani d'ago kan shi da xai yi suka had'a ido da musaddiq dukannin su kallon juna suke cike da tashin hankali, musaddiq wanda yaga muh'd yana kuka ya fara tunanin me yasa shi kuka hka, duk da yanda gaban musaddiq yake fad'uwa yayi yunkurin bud'e baki yayi wa muh'd magana amman ina tuni muh'd ya shige office yasa key a jiki tare da jingina a jikin kofar ya na wani irin kuka mai ban tausayi.
Har musaddiq xai bi bayan muh'd sai ya hango mumyn shi don hka sai ya nufi wajen gaban shi na matuk'ar fad'uwa.
Lokacin da likitocin suka ga muh'd ya fita sai d'aya ya turo gawar sadeeq d'ayan kuma yana rik'e da babyn suka turo kofar suka fito fuskar su babu walwala ko kad'an idanun su sunyi ja sosai ganin an lullu6e mutum da farin mayafi har kanshi lokaci d'aya mumy ta fashe da kuka tana cewa
"Shikenan sadeeq d'ina ya mutu innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
Nan fah waje ya hargitse da kuka d'ayan likitan ne ya mik'a wa nabila babyn ta kar6a ita ma tana kuka sosai.
Cikin dauriya Dr yace "I'm so sorry Allah ya kar6i ran yalla6ai sadeeq"
Jin abin da likitan yace yasa mufidah tayi baya ta xube a sume.
A lokacin musaddiq ya k'araso wajen ganin su mumy suna kuka babu wanda ya kula dashi a wajen, jaririyar ya hango a hannun nabila kuma bai ga mufidah don tuni ta xube a sume wasu nurse's sun d'auke ta don yi mata taimako gaggawa, sai kawai xuciyar shi ta bashi mufidah ce ta mutu wajen haihuwa take gaban shi ya fad'i ya nufi wajen gawar sadeeq wadda take a lullu6e, sai lokacin su daddy suka ankara dashi kafin su tsayar dashi ya sanya hannun shi yana k'okarin bud'e mayafin.............
_ina jiran comment's d'in ku fan's_
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: [9/20, 10:47 AM] Aishat A Muh'd ✍🏻: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A muh'd
♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
*PAGE 31*
Sai lokacin su daddy suka ankara dashi kafin su yi wani yunkurin na tsayar dashi tuni ya k'arasa wajen ya sanya hannun shi kan mayafin yana janye shi a hankali xuciyar shi na wani irin bugawa.
Yana gama janye mayafin fuskar sadeeq ta bayyana kamar an kirawo shi ya amsa, daskarewa musaddiq yayi a tsayen ko kwakkwaran motsi ya kasa lokacin bugun xuciyar shi ya tsanan ta sosai fiye da d'axu mintuna uku yayi a hkan kafin kuma ya bud'e bakin shi da k'arfi ya furta
" Yah sadeeq!"
Lokaci d'aya kuma idanun shi suka fara rufe wa kafin kuma yayi baya ya sulale a k'asa a sume.
Da gudu su daddy suka yi kanshi, mumy kuwa kuka take tana furta " shikenan musaddiq nasan shima yabi d'an uwan nashi ya Allah ka bani hak'urin rashin su"
Kafin ta xube ita ma akan kujera tana shashshak'ar kuka cikin xuciyar ta tana karanta innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Allahumma arjurrni fil musubati wa'akbarni min khairul minha da sauran addu'ar da taxo xuciyar ta gaba d'aya ta wani xabge ta rame lokaci d'aya saboda tsabar tashin hankali.
Dr muh'd kuwa bud'e kofar office d'in yayi kad'an yaga musaddiq baya nan don hka sai ya fito ya nufi inda suke idanun shi na xubar hawaye, yana k'arasa wa ya hango musaddiq a k'asa a sume su daddy da Abba suna k'okarin daukan shi, a rud'e ya k'arasa wajen da gudu ya cakumi jikin musaddiq yana kuka yana cewa
"No musaddiq kada ka bishi kai ma nima xuciya ta xata buga na bi ku baxan jure rashin ka ba"
Maganganun da muh'd yake shi ya sake tsinka xuciyoyin su daddy yana rik'e da musaddiq yana kuka sosai dak'yar Yah Omar ya rik'e muh'd aka shigar da musaddiq emergency room don ceto rayuwar shi.
A cikin ambulance aka sanya gawar sadeeq daddy da Abba suna xaune kusa da gawar, umma, mumy, nabila da jaririyar kuma suka shiga motar Yah Omar suka nufo gida domin sada shi da gidan shi na gaskia, mumy babu uhm babu uhm uhm hawaye ne kawai yake fita a idon ta xuciyar ta tana wani irin xugi da rad'ad'i.
An samu nasarar farfad'owar mufidah Dr Aishat tana k'okarin yi mata allurar bacci don ta huta amman mufidah tak'i yarda cikin kuka take cewa
"Doctor na rok'e ki da kada kiyi min allurar bacci ki bar ni naje na yiwa mijina kallon k'arshe don nasan baxan k'ara ganin shi ba sai a photo"
Wani mugun tausayin ta ne ya kama Dr Aishat don hka ta dafa kafad'ar ta tana cewa
"Baxan miki ba mufidah amman ina son ki bar kukan nan addu'a yanxu sadeeq yafi bukata fiye da komai a wajen ki kin ji"
Gid'a kai tayi nan ta kamo hannun ta suka fito daga room d'in.
Musaddiq ma an samu ya farfad'o yana bud'e idanun shi komai ya dawo mishi sabo don hka ya yunk'ura ya tashi yana jin wani jiri da axababben ciwon kai ga xuciyar shi da take mishi xugi yana dafe da saitin xuciyar ya layi ya nufi kofa xai fita a lokacin muh'd shima ya murd'a handle d'in kofar ya shigo suka tsaya kallon kallon tsakanin su, ganin musaddiq yana yin baya xai fad'i cikin xafin nama muh'd ya rik'e shi cikin wata irin murya yace
"Muh'd da gaske ne Yah sadeeq ya tafi ya barni, kace mishi ya dawo ina bukatar kasance wa dashi dama nine na mutu ba Yah sadeeq ba baxan iya jurar rashin shi ba nima xan bishi muh'd ya Allah nima ka d'auki rai na huta da......"
Cikin kuka muh'd ya toshe wa musaddiq bakin shi don yasan baya cikin hayyacin shi, " kadai na fad'in hka musaddiq Allahn da ya bamu shi ya kar6i abin shi yanxu addu'ar mu kad'ai Yah sadeeq yake bukata ka taso yanxu mu je gida"
Yana rik'e dashi suka fito har farfajiyar asibitin a lokacin kuma Dr Aishat ta sanya mufidah a motar ta xata kai ta gida sai gasu sun fito don hka sai kawai muh'd ya sanya musaddiq a bayan motar shima ya shiga ya xauna kusa dashi don baxai iya driven yanxu ba.
Nan Dr Aishat ta ja motar ta suka fita daga asibitin, karatun Qur'an ta kunna cikin motar don samun nutsuwa ae kuwa duk shiru suka yi suna sauraren karatun Qur'an d'in da hka har suka k'arasa gida.
Dak'yar suka samu damar shiga gidan saboda yanda mutane suka cika tun daga farkon layin ka shigo motoci ne da mutane damk'am har xuwa cikin k'atuwar farfajiyar gidan, don cikin lokaci k'ank'ani mutuwar SADEEQ ABUBAKAR ta kewaya ko'ina a fad'in sassan nigeria xuwa kasashen ketare don sadeeq mutum ne managarci, hankali, tausayi, taimako babu ruwan shi kowa na shine gashi da sanyin hali ga fara'a kai yabo dai sadeeq yasha shi daga bakunan mutane, shi yasa duk wanda yaji mutuwar ba k'aramin girgixa shi take ba wasu har da kukan su.
A cikin palon daddy aka yi wa sadeeq wanka aka had'e shi kuma daddy da abban mufidah sai babban aminin shi abokin shi Yah Omar suka had'e shi shi likkafani suna yi suna xubar hawaye mai k'una.
Bayan sun gama ne aka kirawo mumy don tayi mishi addu'a lokacin da mumy taga sadeeq a hka kusan sumewa tayi numfashin ta ya fara yin sama har daddy xai fitar da ita daga palourn sai kuma ta fara yi mishi addu'ar samun dace wa da rahmar ubangiji daga k'arshe kuma ta ce
"Sadeeq na yafe maka a matsayi na na mahaifiyar ka Allah yayi maka rahma yasa aljanna ce makomar ka"
Tana gama fad'in hka tayi shiru sai kuma ga mufidah da musaddiq nan tare da muh'd sun shigo palon suma.
Musaddiq xama yayi a k'asa kusa dashi ya xuba mishi ido kawai yana kallon shi kamar wanda bai ta6a ganin shi ba sai yau hawaye ma sun dai NA fita a idanun shi sai *K'UNAR XUCi* (littafin ummu safwan), da yake yi.
Muh'd ne yayi k'okarin yi mishi addu'a shima hawaye na xuba a idon shi, mufidah kuwa kuka take sosai ta kasa bud'e bakin ta tayi mishi, har xuwa lokacin da su daddy, Abba, Yah Omar da muh'd suka fara k'okarin d'aga makarar da sadeeq yake ciki.
Sai lokacin mufidah ta rik'e makarar k'am tana cewa " bai fa mutu ba yayi min alkawarin xamu rayu da juna ku dawo da shi"
Kuka take sosai tana sumbatu kamar mai ta6in hankali dak'yar mumy da umma suka janye ta aikuwa suna sakin ta ta xura da gudu ta kuma rik'e makarar tana surutai sosai ta bawa mutanen wajen tausayi don koma wa tayi kamar wata mahaukaciya sabon shiga.
Wannan karon mumy kasa rik'e ta tayi sai umma ce da Dr Aishat suka rik'e ta nabila kuwa jaririyar ce ta tashi tana kuka shine take jijjiga ta a kafad'ar ta tana kallon mufidah tana kukan tausayin kawar ta ta.
Suna rik'e ta sai kuwa tayi baya ta xube a sume nan suka d'auke ta xuwa bedroom d'in mumy nan Dr Aishat ta fara k'okarin ceto rayuwar ta bayan ta farfad'o tayi mata allurar bacci.
Shi kuwa musaddiq har aka fita da gawar sadeeq yana xaune a wurin ya kasa motsi duk kukan da mufidah take da surutun da take bai san ana yi ba, xuwa can kuma ya mik'e xumbur ya fito lokacin har sanya sadeeq cikin mota don da d'an nisa tsakanin su da mak'abartar cikin sauri ya shiga ya xauna kusa da makarar muh'd yana kusa dashi.
Lokacin da aka sanya sadeeq cikin kabari daddy ne da musaddiq suka sanya shi a cikin an fara xuba k'asa akan shi sai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 23