lokacin musaddiq ya dawo cikin hayyacin shi sai gani akayi kawai ya xube saman kabarin a sume nan aka d'auke shi aka sanya shi a mota aka nufi gida dashi don bashi taimakon gaggawa.
Mutane sun fara tafia a mak'abartar amman daddy ya kasa tafiya kawai yayi xaman dirshe cikin k'asa gaban kabarin sadeeq yana shafa saman kabarin dak'yar Abba da Yah Omar suka janye shi tare da sashi a mota suka tafi gida..........
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A muh'd
♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
*PAGE 32*
Bayan sun dawo gida Dr muh'd allurar bacci yayi wa musaddiq bayan ya farfad'o daga suman da yayi, tukunna ya fito xuwa farfajiyar gidan inda su daddy suke kar6ar ta'axiyya, gefe d'aya ya samu ya xauna yana aikin tunani lallai rai ba'a abakin komai yake ba lokacin da Allah yaso kar6ar abin shi ba wanda ya isa ya hana kamar d'axu ne da safe suka gama shan hira da sadeeq yanxu kuwa baya nan ya tafi tafiyar da har abadan baxai sake jinshi ko ganin shi ba a duniyar wayyo rayuwa Allah yasa mu dace Allah Yayi mana kyakkyawan k'arshe Ameeen, tunanin da muh'd yake yi kawai idanun shi suna hasko mishi fuskar sadeeq kunnuwan shi suna jiyo mishi muryar sadeeq lokaci d'aya hawaye masu xafin gaske suka xubo mishi.
Damuwar da muh'd ya shiga sai kace wani d'an uwan shi shak'i k'in shi ya rasu, Allah ne ya had'a su da musaddiq har suka yi mugun sabo har suka rikid'e suka koma aminan juna na sosai da sosai k'aunar su yake da xuciya d'aya son su yake so irin mara algus d'in nan a ciki, wad'annan tunanin yake har xuwa lokacin da aka kirawo sallahr axahar suka tafi masallaci.
A6angaren su mumy kuwa abin dai sai du'a'i don ko magana bata iya yi a yanxu ta daina kuka sai na xuci idanun ta sun ja sosai tana xaune cikin bedroom d'in ta akan abin sallah tana rik'e da carbi tana addu'a bayan ta idar da sallah, addu'ar samun dace da rahmar ubangiji take yiwa sadeeq tana fatan d'anta ya dace da albarkatun da suke wannan ranar ta alhamis, tana matuk'ar k'aunar 'ya'yan bata son abin da xai ta6a mata su sai gashi mutuwa mai yankan kauna ta raba rabuwa ta har abada shikenan baxa ta kara ganin sadeeq d'in ta ba, mutuwa kenan mai raba d'a da mahaifiyar shi.
Nabila kuwa tana tare da mufidah duk da har yanxu bacci take bata farka ba, jaririyar ma tayi bacci ta kwantar da ita bayan ta gama d'ura mata madarar jarirai, kallon k'awar ta take tana mai tausayin ta mutuwar miji babu dad'i ko dad'e wa basu yi don basu fi shekara biyu da aure ba suna kan ganiyar cin soyayyar su sai gashi mutuwa taxo ta raba hawaye ne suke xuba sosai a idanun ta na tausayin mufidah.
Sai da dare allurar baccin ta saki mufidah lokacin da ta bud'e idanun ta ta ganta a d'akin mumy a lokacin komai ya dawo mata cikin kwakwalwar ta hawaye ne suke xuba a idanun ta jin abin take kamar a mafarki wai sadeeq ya mutu anya ba tsokanar ta suke ba, kuma ae ta ganshi acikin makara har aka d'auke shi aka fita dashi da gaske ne sadeeq ya tafi ya barki da 'yarshi, wayyo sadeeq me yasa ka tafi ka barmu a lokacin da nafi buk'atar ka ni da 'yarka Allah ka jik'an sadeeq d'ina ka gafarta mishi.
Tana cikin hka nabila ta ankara da ta tashi don hka nan ta dunga rarrashin ta da nasiha akan tayi hak'uri ta yarda da kaddara Allah ya kaddara sadeeq lokacin Yayi addu'ar samun rahmar ubangiji xata na mishi abin da yafi bukata kenan.
Dak'yar ta lalla6a ta ta watsa ruwa duk idanun nan sun kumbura sun kod'e saboda tsabar xubar hawaye wata simple gown nabilah ta d'auko ta bata ta saka tukunna ta rama sallolin da ake bin ta, k'ememe mufidah tak'i cin abinci sai da nabilah da umma suka takura mata tukunna tasha tea cikin cup d'aya ba don taso ba duk bakin ta babu dad'i, sai lokacin nabilah ta mik'o mata jaririyar don ta shayar da ita an yi mata wankan ta fes an sanya kayan ta tayi tsab idanun nan nata a bud'e gaba d'aya sai kalle kalle take abin ta.
Kura mata ido mufidah tayi sai taga ta koma kamannin sadeeq tsab, kallon ta take idanun ta suna xubar hawaye suna d'isa a fuskar jaririyar cikin raunin murya da sanyi tace
" kin ga baban ki ya tafi ya bar mu da kewar shi tafiya ta har abada kinxo duniyar shi kuma yana barin ta gaba d'aya, bakisan baban ki ba kuma baxa ki ta6a ganin shi ba har abada sai a photo ya tafi wajen da ba'a dawowa idan aka tafi mahaifin ki mutumin kirki ne sosai babu ruwan shi yana son ki tun kafin kixo duniyar nasan har mutuwa ta d'auke shi bai gan ki ba kuma ganin ki shine burin shi na k'arshe kuma....."
Toshe mata bakin ta nabilah tayi ganin maganar tayi yawa kuma bata da alamar tsayawa, tana kuka tace " haba mufidah ki daina irin wad'annan maganganun ita me ta sani da xaki sata a gaba kina surutu nace miki a yanxu soyayyar da xaki nuna wa sadeeq ita ce addu'ar na rok'e ki kiyi shiru kina karyar min da xuciya"
Wani murmishin yak'e mufidah tayi idanun nan har yanxu hawaye ne suke xuba kafin ta ce " nabilah baki san abin da nake ji bane da kinsani da....."
Da sauri nabilah ta katse ta tare da cewa " nasan da hka mufidah amman kiyi addu'a xaki ji sauk'in koma mene"
Daga hka suka yi shiru mufidah tana shayar da babyn ta ta kura mata ido tayi tana kallon ta xuciyar ta cike da tausayin Kansu don tasan sun yi rashi ba kad'an ba.
Musaddiq kuwa shima acikin daren ya farka lokacin da ya tashi Dr muh'd yana xaune a sofa ya buga tagumi, d'ago kanshi yayi suka had'a ido da musaddiq da sauri ya sanya hannun shi ya goge hawayen fuskar shi tare da tashi ya matsa kusa da musaddiq yana cewa
"Sannu musaddiq ka tashi, me yake damun ka yanxu ba inda yake maka ciwo?"
Muh'd ya jero wa musaddiq duk wad'annan tambayoyin cikin muryar shi mai rawa, kallon shi musaddiq kawai yake ba tare da yayi mishi magana ba, kallon da yake mishi kamar yau ya ta6a ganin shi har muh'd ya tsorata da irin kallon da yake mishi, hannun shi yasa ya ta6a shi amman ko motsi bai yi ba kuma yak'i dai na kallon shi rasa me xaice mishi yayi kawai ya samu waje ya xauna kusa dashi.
Xuwa can sai yaga ya tashi xumbur ya mik'e ya shige toilet bin bayan shi da kallo muh'd yayi yana girgixa kanshi wasu kwalla suna xubo mishi tausayin musaddiq, mufidah, mumy da daddy yake yi sosai.
Musaddiq yana shiga toilet ya cire kayan jikin shi ya sakarwa kanshi shower kafin kuma ya tsugunna a wajen yana wani irin kuka mai ban tausayi ga ruwa mai sanyi yana xuba a jikin shi ya rasa me yake mishi dad'i da gaske ne ashe Yah sadeeq ya mutu ya barshi shi kad'ai ba wa ba k'ani shi d'aya tilo wajen su mumy ta ina xai ji dad'in rayuwa babu d'an uwa rabin jikin shi, kuka sosai ya shashi a toilet kafin ya kashe shower d'in ya d'aura alwala ya fito.
A tsaye ya tarar da muh'd sai safa da marwa yake don baisan a wane yanayi musaddiq yake acikin toilet d'in da tuni ya shiga saboda mugun dad'ewar da Yayi a ciki da kallo muh'd ya bishi ganin ya xura jallabiya ya fara rama sallolin da ake bin shi.
Bayan ya idar ne muh'd yayi dashi don yaci abinci amman ko magana bai yi mishi dole hka ya hak'ura ya barshi yana kallon shi ganin yanda ya had'a kai da gwiwa.
A cikin wannan dare musaddiq, mufidah, mumy,daddy,Yah Omar da muh'd babu wanda ya samu ya runtsa yayi bacci xuciyoyin su cikin alhinin rashin managarcin mutum suke ma'abocin kirki da karamci ba ruwan shi bai d'auki rayuwa da xafi sanyin hali ne dashi wanda Indai mutum yayi xama mintuna dashi sai yaji k'aunar shi a cikin xuciyar shi balle su da suka kwashe tsawon shekaru tare da shi, wannan daren dare ne da baxa su ta6a mantawa dashi acikin kundin rayuwar su ba, dare ne da suka kasance cikin tsananin kewar sadeeq kewar da basu ta6a jin irin ta a tattare dasu ba saboda sun san sun rabu da ganin shi har abadan, suna fatan Allah ya had'a su cikin aljannatul firdaus su kasance a tare, rayuwa kenan rayuwa mai cike da tarin kaddara acikin ta babu bawan da ya isa ya tsallake tashi kaddarar, rayuwa mai cike da tarin k'alubale a cikin ta, rayuwa mai cike da tarin ni'imomin da rahmomin ubangiji,Allah yasa mu dace da rahmar ubangiji ta duniya da lahira Ameeen ya rabbil alameen..........
_kuyi hak'uri da wannan fan's ban da chaji ne sai kuma gobe idan Allah ya kaimu_
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: [9/26, 5:44 PM] Aishat A Muh'd ✍🏻: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A muh'd
♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_Happy birthday my Ummiey Xeey dear, ina taya ki murnar karin shekara wannan shafin sadaukar wa ne gare ki don taya ki murna, Allah ya k'aro shekaru masu albarka ya baki miji na gari mu xo Kaduna musha biki._Ameeen.
*PAGE 33*
Har garin Allah ya waye xuciyoyin su cike da alhinin rashin sadeeq wani lokacin ji suke kamar ba mutuwa Yayi ba xai dawo xuwa anjima, musaddiq da wani irin mugun xaxxa6i ya tashi ajikin shi da ciwon kai mai tsananin gaske wanda dak'yar yake iya bud'e idon shi, ga rashin cin abinci rabon shi da yasa wani abin abakin shi tun jiya yana cikin jirgi da yasha coffee kawai.
Dr muh'd ne ya tsaya sosai akan shi har xuwa yamma xaxxa6in kamar k'ara mishi ake yak'i sauka idan ka kalli musaddiq a time d'in sai ya baka tausayi Yayi masifar rame wa sosai abu ne yake cin shi a xuciya ga yak'i fitar da kukan waje sai na xuci kawai yake sai da kaji yana wani jan numfashi tare da sauke ajiyar xuciya.
Wannan yanin gaba d'ayan su sun yi shi cikin wani mawuyacin hali musamman musaddiq da mufidah har gwara mufidah ana takura mata taci abinci saboda shayar da babyn, musaddiq kuwa muh'd ne yake fama dashi wajen cin abinci amman yak'i kar6a yaci mumy ma k'in xuwa ganin shi tayi don baxa ta jure ganin d'an nata da yanxu ya rage mata ba cikin wannan halin, tasan musaddiq mutuwar sadeeq sai tafi ta6a shi fiye da kowa idan aka yi la'akari da yanda suka yi mugun shak'uwa da junan shi, addu'a kawai take mishi Allah ya sanyaya mishi xuciyar shi ya bashi hak'urin jure rashin d'an uwan shi.
*AFTER 7 DAY'S*
Anyi kwanaki bakwai da rasuwar sadeeq a yanxu, ranar da ya cika kwanaki 7 a ranar daddy yaxo sanya wa jaririyar suna da yake duk suna palon gaba d'ayan su idan ka d'auke musaddiq wanda yake can a d'akin shi yana shan bacci sakamakon allurar baccin da ake mishi.
Kallon mufidah daddy yayi tare da cewa "mufidah ko da akwai sunan da kike ra'ayi a sanya mata?"
Girgixa kai mufidah tayi tana xubar da hawaye kafin ta bud'e baki murya na rawa tace
"Daddy duk wanda ka sanya mata yayi ban da wani xa6i"
Har daddy ya bud'e baki xai yi magana da sauri muh'd yace
"Daddy kafin Yah sadeeq ya rasu lokacin da na kai mishi babyn naji ya furta Allah ya raya ki NANA KHADIJAH ina tunanin shine sunan da yake so"
Da sauri mufidah ta kalli muh'd cikin mamaki lokaci d'aya taji wani d'an sanyi a cikin xuciyar ta jin sadeeq yaga babyn kafin ya mutu.
"Masha Allah kenan sunan mumyn shi kenan to Allah ya raya mana NANA KHADIJAH, Allah ya albarkaci rayuwar ta ya jik'an mahaifin ta da rahma" Cewar daddy kenan.
"Ameeen thumma Ameeen"
Gaba d'aya falon aka amsa idanun su ya cicciko da hawaye, nan daddy yayi mata hud'uba da khadijah tukunna aka yiwa sadeeq addu'a sosai sannan aka watse.
A ranar umman su mufidah da nabilah Yah Omar suka wuce gida aka bar mufidah a wajen mumy, bayan nabilah ta bata shawara akan ana kiran khadijah da Afnan saboda sunan mumy ne, mufidah ta sha kuka sosai lokacin da su umma suka tafi dak'yar mumy ta rarrashe ta tayi shiru, xuciyar ta tana kewar sadeeq kusan kullum da pic d'in shi take k'wana rungume a jikin ta duk dare sai ta xubar da hawayen rashin sadeeq tasan baxa ta ta6a samun miji irin sadeeq ba gaba d'aya ma ita ta sawa xuciyar ta ba xata yi aure ba xata xauna ta kula da Afnan d'in su ita kad'ai ta ishe ta xata xauna ta jira yi har mutuwar taxo ta d'auke ta taje can ta had'u da sadeeq d'in ta.
Musaddiq ma gaba d'aya ya xama wani iri abinci sai an rarrashe yake ciki kullum yana cikin daki a kwance yana faman tunanin rayuwar su ta da tare da d'an uwan shi, mumy ce ta sawa xuciyar ta jarumta wajen rarrashin mufidah da musaddiq.
*******
Haka rayuwa ta mik'a ta cigaba da tafiya a hankali suka fara saba wa da rashin sadeeq addu'a ce kullum cikin yi mishi suke xuciyoyin su sun fara sanyi, da hka kwanaki suke tafiya sannu a hankali har sadeeq yayi k'wana 40 da mutuwa a ranar an yi sadaka da karatun alQur'an da addu'o'i akan Allah y rahma mishi a ranar mufidah tasha kuka sosai don a ranar ta tabbatar sun fa rabu da sadeeq har abada.
Duk wannan xaman da suke gida d'aya tsakanin musaddiq da mufidah basu had'u da junan su kowannen su yana cikin bedroom basa fito wa.
Lokaci yana ja kwanaki suna tafiya har xuwa lokacin da sadeeq ya samu kimanin wata uku da rasuwa, Afnan tayi wayo sosai kamannin ta da mahaifin ta yana sake fitowa sosai a kusan koda yaushe tana hannun musaddiq idan ya xuba mata ido yana kallon ta ko kiftawa baya son yi don gani yake kamar suna tare da d'an uwan shi sadeeq, kullum idan mumy tayi mata wankan safe xata kawo mishi ita ta yini a wurin shi sai dai lokacin cin abincin ta yayi mumy taxo ta kar6e ta don sam baya sha'awar fitowa abin yana damun mumy da daddy da muh'd gashi ya Tara wata gashi a fuskar shi sosai yak'i xuwa a gyara mishi muh'd ma yayi yayi dashi don ya ma gyara mishi yak'i yarda dukannin su a tsorace suke kada shima yabi bayan d'an uwan nashi, don gaba d'aya musaddiq ya koma kamar bashi ba daman gashi miskilin gaske a yanxu kuwa gwara da sau dubu akan yanxu sai ku kusan yini tare amman baxai bud'e baki yayi maka magana ba sai dai yayi ta bin ka da kallo kamar yau ya fara ganin ka..........
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A muh'd
♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
*PAGE 34*
Kamar yau ranar juma'a wanda Yayi dai dai da watanni biyar da rasuwar sadeeq, abin da musaddiq yake mumy ta gaji da ganin shi cikin hka don hka tun safe bayan ta gama abin breakfast ta d'auki nashi ta nufi bedroom d'in shi da sallama ta shiga but kamar koyaushe bai amsa ba and kuma yana kwance still kan bed yayi rigingine yana tunani.
Mumy kallon d'an nata tayi cikin tausayin shi ajiye breakfast d'in tayi tare da k'arasa wa inda yake ta xauna tare da dafashi tace
"Musaddiq tashi xaune"
Ba musu ya tashi ya xauna tare da d'ora kanshi saman kafad'ar ta shafa bayan shi take tana cewa
"Musaddiq na gaji da ganin hka cikin wannan halin ina son ka sawa xuciyar hka hak'urin rashin sadeeq, ganin hka yana d'aga min hankali kai kad'ai ne ka rage min yanxu idan baka sawa xuciyar ka hak'uri ba xaka iya samun matsala ka fison ka dunga ganin mu cikin tashin hankali koh?"
Girgixa kai yayi tare da d'ago kanshi yana kallon mumyn wadda take fitar da hawaye, hannun shi yasa yana goge mata hawayen shima kuma hawayen yake yana girgixa mata kai cikin rawar murya yace
"I'm so sorry mumy Yah sadeeq ya tafi ya bar mu na kasa yarda ya mutu ji nake kamar xai dawo gare ni, bana son ganin ki cikin tashin hankali ki dai na kuka don Allah mumy"
"Idan har kana so na daina damuwa to kayi hak'uri da rashin sadeeq ka d'auki hkan a daman Allah ne ya bamu aron shi xuwa wani lokacin gashi kuma ya d'auki abin shi ka cire damuwa a ranka addu'a sadeeq yafi bukata shine abin da xamu yi mishi mu nuna mishi mu masu son shi ne"
"Okay mumy xan yi abin da kike so"
Cikin hawayen da take ta fara dariya tana cewa
"Da gaske musaddiq xaka koma kamar da?"
Wani murmishi yayi wanda rabon shi da yayi an dad'e kafin yace
"I promise mumy xan dawo miki kamar Yah sadeeq"
Rungume shi mumy tayi tana mai jin dad'in yanda yau ya bata had'in kai nan ta cigaba da yi mishi nasiha cikin sigar rarrashi kafin daga k'arshe ta shiga toilet ta had'a mishi ruwa mai d'umi a bathtub tukunna ta d'ebo kayan aski ta xauna ta gyara mishi fuskar shi fes, tuni musaddiq ya rikid'e ya koma musaddiq d'in shi na da bayan ta gama yi mishi ya shiga toilet yayi wanka sosai wanda rabon shi da yayi irin wannan wankan tun kafin sadeeq ya rasu.
Bayan ya fito ne ya shirya jikin shi cikin wani lallausan yadi sky blue wanda yayi matuk'ar kar6ar shi yana cikin fesa perfumes ya hango wani pix d'in su da suka yi shi da sadeeq ta mirror suna dariya pic d'in yayi matuk'ar yin kyau sosai, hawaye ne ya cicciko a idanun shi bai bari sun xuba ba ya d'aure ya rik'e su hannun shi yasa ya shafa mirror d'in tare da cewa
"Yah sadeeq ka tafi ka bar ni, ina matuk'ar kewar ka "
Ya k'arasa fad'i muryar shi na rawa sosai kamar xai fashe da kuka, yana cikin hka mumy ta shigo bedroom d'in da sauri ya dai dai ta nutsuwar shi don yayi mata alkawarin daina sa damuwa a xuciyar shi.
Dad'i ne sosai ya kama mumy ganin d'an nata ya fito fes dashi ya dawo musaddiq d'in shi rungume shi tayi tana shafa kanshi tana cewa
"Naji dad'in ganin ka a hka musaddiq Allah yayi maka albarka ya jik'an sadeeq"
"Ameeen mumy na"
"Yanxu sauran ka breakfast kasha magani sai ka mu fita palour daddy yana jiran mu"
Cewar mumy kenan idon ta akan shi tana son ganin yanayin yanda ya kar6i maganar ta ta.
Murmishi ya d'an yi kafin yace " okay mumy"
Nan ta fara bashi abincin a baki har yaci ya K'oshi wanda rabon da yayi wannan cin abincin har ya mance bayan ya gama ci ta bashi maganin shi ya sha tukunna suka fito xuwa palon daddy.
Ba k'aramin dad'i daddy yayi ba ganin musaddiq a hka nan shima nasiha sosai yayi mishi nan suka xauna hira har xuwa lokacin tafiya masallaci yayi don yau juma'a tare suka tafi da daddy.
Mufidah ce na hango a bedroom tana k'okarin sanya hijab a jikin ta tana sanye da wata atampha tayi kyau kam don ma har yanxu bata ciko daga ramar da tayi ba, sauri take tana shirya wa don yau gida take son xuwa tuni ta gama shirya Afnan tana Palo hannun mumy.
Bayan ta fesa perfumes mara k'arfi a jikin ta ta fito xuwa falo, ko make up bata yi ba but duk da hka tayi kyau don kyanta natural ne.
A nutse ta fito tana tafiyar ta har xuwa Palo nan ta kar6i Afnan a hannun mumy suka yi mata sallama ta jiyo tana k'okarin bud'e kofar palon adai dai time d'in musaddiq ya sanya hannun shi kan handle d'in kofar ya bud'e gware suka yi da kan su saboda shi musaddiq ya d'an rakwafo kanshi gwaren nan irin na unexpected ne shi yasa suka ji xafin sosai har sai da mufidah ta d'an saki k'ara tana dafe goshin.
Wanda hkan yasa Afnan ku6uce wa daga hannun ta tayi k'asa sauran kad'an ta fad'i cikin xafin nama musaddiq ya taro ta da hannun shi lokaci d'aya Afnan ta tsandara ihu don ta tsorata sosai ta fara kuka, wani kallo musaddiq yayi wa mufidah wanda ya d'an tsorata ta tare da ja da baya don kada ya kawo mata bugu sai wani huci yake.
A tare mumy da daddy suka k'araso wajen suna tambayar su lafia, cikin fusata musaddiq yace
" mumy wajen sakacin ta ne yasa ta kusan fad'uwa"
" anya kuwa musaddiq sai dai tsautsayi?"
Mumy ta fad'i hkan tana kar6ar Afnan tana rarrashin ta har sai da tayi shiru.
"Ina xasu je ne?"
Cewar daddy, " gida mufidah xata je"
Mumy ta bashi amsa, kallon musaddiq yayi wanda yake k'okarin barin wajen yace
"Musaddiq ka kai ta gidan ni yanxu xan sake fita da driver "
Kafin yace komai daddy ya bar wajen, mumy ma mik'a wa mufidah Afnan tayi tare da cewa
"Sai kun dawo ki gaida min su xan shigo anjima da dare sai mu dawo tare"
Tana gama fad'in hka ta wuce ita ma, aka bar mufidah da musaddiq a tsaye, wanda shi tsabar mamakin abin da daddy ne yace ya hana shi kwakkwaran motsi, ita ma mufidan taji babu dad'i don sam bata so daddy yace ya kai su ba haushin musaddiq take ji sosai wai ya wani ce saboda sakaci na xan yarda Afnan kamar wata 'yar shi.
Kwafa tayi tare da jan d'an siririn tsaki, shima tsakin yaja har ya bud'e baki xai yi magana ko mai ya tuna sai yayi shiru tare da fita daga palon a fusace.............
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: [9/27, 11:24 AM] Aishat A Muh'd ✍🏻: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A muh'd
♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
*PAGE 35*
A fusace ya fita daga palon xuwa farfajiyar gidan motar da suka fita masallaci da daddy Ita ya shiga ya xauna yana jiran ta gaba d'aya ranshi yayi masifar 6aci akan abin da daddy yace yana nan xaune sai faman doka tsaki yake shi kad'ai.
Mufidah sai da ta kwashi tsawon mintuna tukunna ta fara k'okarin fito wa daga palon, kallon ta yake tana taho wa ranshi ya k'ara 6aci sosai ganin yanda ta shanya shi sai da tayi ra'ayi sannan ta fito kau da kanshi yayi daga barin kallon ta yana jan tsaki.
A nutse ta sanya hannun ta ta bud'e kofar motar ta xauna babu wanda yayi wa wani magana a tsakanin su yayi wa motar key ya fita daga gidan kowannen su fuskar shi a d'aure, har suka karasa gidan su mufidah a kofar gate d'in ya yi parking ba tare da ya kalle ta ba ko yayi magana.
Haushi ya sake turnik'e mufidah wato a waje ma xai ajiye ta baxai shigar da ita d'an tsaki taja tare da bud'e kofar motar ta fita sannan ta buga mishi murfin kofar da k'arfi har sai da musaddiq ya d'an tsorata ya kallo inda take amman wayam bai ganta ba har ta shige cikin gidan.
"Lallai yarinyar nan ashe har yanxu akwai raini atsakanin mu da ita ae kuwa xan koya mata hankali"
Ya fad'a yana jan tsaki can kuma har yayi wa motar key ya fara tafiya sai kawai ya furta a fili
"Xan kyale ta saboda darajar Yah sadeeq, but dole na kar6e Afnan daga hannun ta kada ta koya mata tsiwa da rashin kunya".
Mufidah kuwa cike da jin haushin musaddiq ta k'arasa cikin palour tare da kwalla wa umma kira tana cewa
"Umma na kina ina?"
Da sauri umma ta fito daga kitchen jin muryar mufidah ae kuwa tana ganin ta suka rungume junan su cikin tsananin farinciki sai mufidah taji duk 6acin ran ta ya kau sai farinciki.
Sakin ta umma tayi tana kar6ar Afnan tace
" Masha Allah Afnan sai girma take ga kamannin ta da mahaifin ta sak kamar yayi kaki ya xubar"
Tuni idanun mufida sun ciko da hawaye jin umma ta ta6o mata wani abun, ganin yanda lokaci d'aya mufidah ta canja yanayin ta cikin damuwa daga farincikin da take
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 23