Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fada mata sai yanxu, me yasa bai rubuta mata cikakken sunan shi ba sai M uhm dan ta6e baki tayi kawai tare da furta cewa " koma wane to gaskia *YAYI SAKE!* sai yayi hak'uri ya sami wata kuma " sai ta tsinci kanta da kasa goge mssg di'n a wayar ta ta xurfafa a tunanin wane wannan. Lokacin da musaddiq ya tura wa mufidah messegen din yana kwance kan gado idanun shi cike da hawaye ga xuciyar shi tana mishi wani rad'ad'i sosai kan shi kuwa kamar ya cire saboda a axabar ciwo goge mssg di'n yayi sannan ya d'auko diary din shi ya rubuta abin da ya turawa mufidah sannan ya rufe diary din ya ajiye shi. Koma wa yayi ya kwanta yana wani jan numfashi dakyar da ana cire so Idan ya shiga cikin xuciya da tuni ya cire son mufidah a cikin xuciyar shi ya huta d'aga idanun shi sama yayi tare da cewa "Yah Allah ka kawo min agaji acikin wannan halin da nake ciki, Yah Allah ka cire min son mufidah daga cikin xuciya ta" Yana gama fad'in hka ya lumshe idon shi wasu hawaye ne masu xafin gaske suka xubo mishi daga idanun shi. "Ameeen thumma Ameeen " Yaji an furta hakan da sauri ya bud'e idon shi ya kalli kofar shigowa wata ajiyar xuciya ya saki ganin Dr muh'd ne a tsaye yana kallon shi irin kallon nan me cike da tausayin shi. K'araso wa yayi cikin bedroom d'in ya xauna akan bed d'in tare da dafa hannun musaddiq yace "kayi hak'uri musaddiq wannan itace kaddara Allah ya jarabce ka da son yarinyar da yayan ka xai aura, ina rok'an ka ka cire son ta don Allah ina nan ina tayaka addu'a sosai Allah ya raba ka da wannan son don an kai matakin da xuciyar ka ta ta6u da ciwo ina tsoron faruwar wani abu abokina " Dr muh'd ya k'arasa fad'i yana mik'a wa musaddiq wata takarda, kar6a musaddiq yayi ya karanta yana gama karanta wa yayi wani k'ayataccen murmishi wanda yasa Dr muh'd tsorata sosai ya bishi da kallon mamaki Kafin ya ankara yaji musaddiq ya fara wani irin tari sosai tuni idanun shi suka fara xubar da hawaye saboda axabar tarin da yake sai sannu Dr muh'd yake mishi kafin ya tashi ya bud'e frige ya d'auko mishi faro mara sanyi ya nufo wajen shi dai dai lokacin musaddiq yayi wani tari da karfi sosai wanda sai da jini ya fito ta bakin shi yana dafe da saitin xuciyar shi.............. _kuyi hak'uri da wannan ban da chaji ne wlh_ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* *PAGE 13* Cikin wani irin sauri Dr muh'd ya k'arasa wajen musaddiq hankalin shi a matuk'ar tashe kamo shi yayi ya ma rasa me xai yi mishi tsabar rikice wa, kallon musaddiq yake wanda bakin shi duk ya 6aci da jini idanun shi sai wani lumshe wa suke yi gaba d'aya jikin shi ya saki ba k'arfi a tattare da shi. Cikin dauriya musaddiq ya yago tissue ya goge jinin da ke gefen bakin shi tare da kallon muh'd yace "kayi hak'uri aboki na nayi kok'ari wajen cire son mufidah a cikin xuciya ta hkan ya gagara, bansan ganin ka cikin damuwa " Tuni idanun muh'd sun fara xubar da hawayen tausayin musaddiq hannun shi yasa ya kamo na musaddiq tukunna yace "kada ka damu aboki Insha Allah xaka samu lafia yanxu ka taso muje hospital na duba ka " Girgixa kai musaddiq yayi tare da cewa "umh my friend na samu sauk'i fah " Kura mishi ido muh'd yayi kamar me karantar wani abu a fuskar shi kafin yaja numfashi yace " na rok'e ka ka taso mu tafi akwai abin da nake so na duba, kada kace min baxa ka ba please" D'an murmishi musaddiq yayi kafin yace "Okay aboki ka wuce komai a waje na da ina da ikon cire abin da yake damuna da na cire saboda bana son ganin ka cikin damuwa" Shi ma Dr muh'd di'n Murmishi yayi tare da rungume musaddiq a jikin shi Kafin kuma yaje yayi wanka bayan ya fito ne ya shirya cikin wani white jeans and T-shirt pink colour yayi matuk'ar yin kyau sai dai er ramar da yayi yana gama fesa perfumes ya xura wani silifas na maxa white ne takalmin daga hka suka fita daga d'akin xuwa farfajiyar gidan mota suka shiga asibitin da suke aiki suka nufa kai tsaye. Bayan Dr muh'd yayi wa musaddiq gwaje gwajen da suka dace ya dad'a tausar shi tare da yi mishi nasiha sosae akan ya rage sa tunani a cikin xuciyar ya dage da ibada yana kai kukan shi wajen Allah sosai nasihar muh'd ta ratsa musaddiq kuma ya d'auki alk'awarin amfani da abin da yace. Sun d'an dad'e a asibitin sannan suka dawo gida tare da magungunan da Dr muh'd ya bashi xai yi amfani dasu, muh'd ya dad'e a gidan yana tausar musaddiq sai wajen 9 na dare ya bar gidan. Tun daga ranar musaddiq ya dage da addu'a tare da kai kukan shi wajen mai dukka akan ya cire mishi son mufidah a cikin xuciyar shi kuma Alhmdllh addu'a makamin mumini yana samun sassauci sosai a cikin xuciyar shi. Biki ya matso don an Kai lefen Yah sadeeq xuwa gidan su mufidah yayin da daga gidan su mufidah aka Kai na Yah Omar sun shirya yin dinner, walima da sauran programs masu k'ayatar wa. A cikin wannan lokacin ne iyayen musaddiq suka fahimci bashi da lafia don ganin yanda yayi matuk'ar rame wa sosai hankalin su yayi mugun tashi da ganin halin da d'an nasu yake ciki Hka shima Yah sadeeq ba k'aramin tsorata yayi ba gashi sun yi tambayar duniyar nan ya fad'i abin da yake damun shi, amman musaddiq fad'a musu Yayi ciwo ne kawai daga Allah, Sam basu yarda da abin da ya fad'a ba sun tambayi Dr muh'd don sun san abokin shi ne xai sani amman musaddiq bai bashi umarnin fad'a ba nan fah mumy, daddy da Yah sadeeq suka sama musaddiq ido aduk wani motsin shi don su karanci abin da yake damun shi, yana sane dasu shi dai yayi alk'awarin baxai ta6a fad'a wa kowa ba bayan Dr muh'd. Ranar Tuesday suka shirya yin kamu sosai sun tsara abin gwanin sha'awa, ranar friday kuma arabian night suka yi asabar kuma umman mufidah da umman nabila suka shirya yin mother's day nan ma sun k'ayatar sosai amare sun sha kyau ba irin mufidah ma an ci ansha an watse cikin farin ciki. Rana sunday da safe wajen karfe 10:20 Yah sadeeq ya shigo palon cikin shigar wata tsadaddiyar shadda fara sol da ita yayi matuk'ar yin kyau ya fito a ango sak nan en uwa suka fara tsokanar shi shi dai murmishi kawai yake yi xuciyar da tsantsar farin ciki yau xai mallaki mufidah a matsayin matar shi ta sunnah. Adai dai lokacin musaddiq da Dr muh'd su ma suka shigo cikin falon sun sha ankon shaddar su cikin shadda sky blue da bak'in takalmi har da hula ba k'aramin kyau suka yi ba musamman musaddiq da bai saba sa manyan kaya ko wajen d'aurin auren bai yi niyyar xuwa ba sai da muh'd ya matsa mishi dakyar ya iya shirya wa bai ma san da kayan ba sai da muh'd ya bashi, fuskar shi ba yabo ba fallasa mumy kuwa kallon su ta dunga yi kamar ta mayar dasu ciki don tsabar son yaran nata. Nan suka rungume ta cikin k'aunar mahaifiyar tasu d'an hawayen farinciki tasa hannu ta goge su tare da dafa kan su tace "Allah ya raya min ku 'ya'ya nah, Allah ya albarkaci rayuwar ku Allah ya kare min ku " "Ameeen thumma Ameeen muna godewa Allah da ya bamu ke a matsayin uwa mumy ' Kallon su take cikin so da k'aunar su tana murmishi, Dr muh'd kuwa shi ma kallon su yake cikin sha'awar su wani 6ari na xuciyar shi yana cike da fargaba don baisan yanayin da musaddiq xai shi gaba idan yaji sanarwar d'aurin auren yasan ya rabu da ita na har abada wani tausayin musaddiq ne ya k'ara kama shi sosai, ana cikin hka daddy ya fito shi ma yayi shirin shi cikin manyan kaya na wata milk colour d'in shadda nan suka rungume shi tare da bashi peck a kumatun shi kafin daga baya su dunguma xuwa wajen farfajiyar gidan suka shiga mota d'aya Dr muh'd ne wajen driving musaddiq a gefen shi wanda ya tsurawa waje ido lokaci xuwa lokaci xuciyar shi tana wani mugun fad'uwa, Yah sadeeq da daddy a baya sai sauran en uwa da abokanan arxiki suka rufa musu baya xuwa wajen d'aurin aure............ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *E.W.F* *PAGE 14* Bayan sun isa wurin d'aurin auren mutane sosai sun taru manya manyan kusassun gwamnati da en kasuwa xuwa abokanan ango sai manyan lecture's da likitoci en uwa da abokan arxiki gasu nan birjik, jama'a ta ko'ina gasu nan karfe sha d'aya dai dai aka d'aura auren mufidah da Yah sadeeq akan sadaki mafi cancanta saboda neman albarkar aure, xuciyar Yah sadeeq ta cika da farinciki sosai ayau Allah ya mallaka mishi masoyiyar shi, son ta daban yake a cikin xuciyar shi yana mata wani irin so baxai iya rabuwa da ita ba sai dai k'addarar ubanjigi ko mutuwa ya rabasu. Musaddiq kuwa yana xaune cikin mota ya kasa fito wa saboda baxai jure tsayuwa ba, jikin shi ba k'arfi ga kuma gaban shi yana mugun fad'uwa sam baxai iya shiga cikin mutane a hka ba saboda baxai iya k'ak'alo murmishi a fuskar shi ba, kallo d'aya xaka yi mishi ka hango tsantsar damuwa a fuskar shi, yana dafe da kanshi wanda yake mishi ciwo kamar xai cire. "Alhmdllh hukuncin ubangiji ya tabbata a yau aka d'aura auren Abubakar sadeeq Abubakar da amaryar shi mufidah El hussaen" Abin da kunnuwan musaddiq suka juyo shi kenan daga bakin wani marok'i ma'abocin xak'in murya, wani irin tari ne ya kama musaddiq tari yake ba kakkauta ba daga bisa ni kuma ya fara aman jini hannun shi yana dafe da saitin xuciyar shi, numfashin shi ne ya fara kok'arin d'auke wa gaba d'aya gaban rigar shi da bakin shi ya 6aci da jini. Dr muh'd kuwa wanda yake cikin taron mutane jin an d'aura auren yasa shi tafiya inda musaddiq yake don yasan a wannan lokacin yana cikin wani mugun yanayi, tausayin musaddiq fal cikin xuciyar Dr muh'd ya K'arasa inda yayi parking d'in motar da suka xo yana bud'e wa ya hango abin da yayi matuk'ar girgixa shi ya d'aga mishi hankali, musaddiq ya gani a kwance ga jini ya 6ata mishi jiki kuma gashi babu alamun yana numfashi a tattare da shi. Cikin sauri ya yunkura xai shiga motar yaji an dafa mishi kafad'a a matuk'ar firgice ya jiyo don ganin wane, had'a ido yayi da Yah sadeeq fuskar shi d'auke da farinciki yace "muh'd ina musaddiq yake? " Wani uban gumi ne ya tsatstsafo wa muh'd a jikin shi gaba d'aya hankalin shi ya rabu gida da yawa shin xai sanar wa da Yah sadeeq ga halin da musaddiq yake ciki ko kuma ya shiga mota ya kai musaddiq asibiti don a ceci rayuwar shi ko ya tsaya ba wa Yah sadeeq amsar tambayar shi. Yah sadeeq kuwa tsura wa fuskar muh'd ido yayi don ganin yanda yake a firgice " what happened to you muh'd, kamar akwai wani abin? " Cikin rawar murya Dr muh'd yace " ba...... ba wani abu Yah sadeeq just an kirawo ni daga hospital ne an kawo wani patient yana buk'atar taimakon gaggawa" "Ayyah so ina musaddiq? " "Hmmm yana cikin taron mutane wajen friends d'in mu idan ka duba xaka gan shi " "alright sai ka dawo " "Okay Yah sadeeq Allah ya sanya alkhairi " Cikin murmishi yace "Ameeen muh'd thank u " Yana gama fad'in hka wani cikin abokanan Yah sadeeq yaxo ya janye shi daga wurin suka shiga cikin mutane, da sauri Dr muh'd ya fad'a cikin mota ya ja ta cikin wani irin gudu don gaba d'aya a rikice yake. Cikin kankanin lokaci Dr muh'd da wasu lokaci guda biyu wanda muh'd ya kirawo su, suka duk'ufa akan musaddiq suna kok'arin ceto rayuwar shi. Sun d'auki tsawon lokaci akan musaddiq Kafin numfashin shi ya dawo amman duk da hka da taimakon oxygen tube yake numfashi gashi nan a kwance kamar wani matacce ba inda jikin shi yake motsi a jikin shi, abin da mutum xai san yana raye numfashin da yake fitar wa ne sai buguwar xuciyar shi, kallon musaddiq Dr muh'd yake yana wani irin kukan tausayin abokin nashi dole ya sanar da iyayen shi abin da yake damun shi don kuwa aka cigaba da hka wataran xa'a samu matsala kuma shi xasu xarga da laifin sakaci da lafiar d'ansu mybe akwai wani taimako ma da xasu iya wajen kwantar mishi da hankali. Wayar shi ya d'auko ya nemo number d'in daddy don shine namiji sai yafi nutsuwa ya saurare shi fiye da mumy don ita mace ce akwai rauni yanxu sai ta k'ara hargitsa shi, wajen 2 missed calls yayi but daddy bai d'auki wayar ba watak'ila bai ji kiran ba saboda hayaniyar jama'a. Yana xaune ya xuba wa musaddiq ido tare da yin tagumi lokaci xuwa lokaci yana goge hawayen da yake xuba daga idanun shi. Daddy kuwa yana cikin jama'a hayaniyar su yasa bai ji kiran muh'd ba sai bayan an d'aura auren Yah Omar da nabila ne sun shiga mota suna kok'arin tafiya wajen walima din da suka had'a, sai yaji kira a wayan shi d'auka yayi don duba wane ya ke kiran shi ganin sunan muh'd yasa daddy yin mamaki amman sai ya kawar da mamakin shi ya d'auki wayar. Shi kuwa Dr muh'd har ya fitar da ran daddy bai ji kiran ba sai kuma yaji ya d'auka cikin sauri yayi sallama bayan daddy ya amsa ne sai kuma muh'd ya d'anyi shiru yana tunanin ta inda xai fara sanar mishi da wannan mummunan labarin a ranar farincikin auran d'ansu, gaban shi har wani mugun fad'uwa yake. "lafia muh'd ka kirawo ni kuma naji kayi shiru ko baka ji ba? " Jin saukar muryar daddy a kunnen shi ya sa Dr muh'd fara magana cikin rawar murya yana cewa "daddy da... daman cewa xan yi maka mu.... musaddiq ne ba lafia ciwon shi ya tashi so yanxu muna hospital " Cikin tashin hankali daddy yace "wanne ciwo kake nufi muh'd? " Sai lokacin muh'd ya tuna da kato6arar da Yayi shaf ya mance basu san musaddiq yana da ciwon xuciya ba, don hka cikin fad'uwar gaba yace "am daddy ina son kaxo asibitin musaddiq yanxu xamu tattauna wata magana aka rashin lafiyar musaddiq so bana so Yah sadeeq ya sani ka taho kai da mumy kawai " Tuni hankalin daddy yayi matuk'ar tashi katse wayar yayi tare da bawa mutanen da suke jiran shi exuse akan yana xuwa akwai abu mai mahimmanci da ya taso mishi yanxu, cikin sauri ya fad'a mota ya nufi gida gumi ne kawai yake tsiyayowa daddy wanne ciwo ne da musaddiq da basu sa ni ji yake kamar ya tashi sama ya ganshi gaban Dr muh'd yana fad'a mishi abin da yake damun d'anshi yaron da yafi soyewa acikin xuciyar shi. Yana k'arasa wa gida Ko shiga da motar bai yi ba cikin gidan ya barta a nan waje ya shiga, saboda cikar da aka yi en biki yasa daddy kiran mumy a waya Allah ya taimaka wayar tana rik'e a hannun ta ba 6ata lokaci ta d'auki wayar ganin kiran maigidan ta ne "kixo yanxu ina wurin parking space ki taho da mayafin ki " "toh shikenan " Abin da mumy tace kenan sam bata yi tunanin wani abun ba ta d'auka ko abokanan shine yake so su gaisa, cikin en mintuna mumy ta fito tana yafa mayafi taci gayu sosai cikin wata arniyar shadda an sha adon gwal sai kyalli take yau ranar farinciki ne a gare ta sam baka ce ita ta haifi Yah sadeeq da musaddiq ba. Turus taja ta tsaya ganin daddy shi d'aya a wurin gaba d'aya fuskar shi d'auke da damuwa cikin tashin hankali tace "Abban sadeeq lafia? " D'ago kai yayi ya kalli mumy sai da gaban ta ya fad'i ganin tsantsar damuwa a cikin idanun na shi hannun shi ta rik'o tana cewa "Yah mijina me yake faruwa da kai? " Runtse idanun shi yayi kafin yace "ina son ki kwantar da hankalin ki nutsu da abin da xan fad'a miki " Cikin xakuwa mumy tace "ina sauraren ka? " Sai da yayi dan shiru Sannan yace "musaddiq ne ba lafia yana hospital " "me yake damun shi? " Cewar mumy a rikice, girgixa kai daddy yayi tare da cewa "sai dai mun je xamu sani yanxu dai mu tafi " Gaba d'aya mumy ta kasa tafia ta cak waje d'aya sai da daddy ya rik'e mata hannu har xuwa wajen mota shi ya taimaka mata ta xauna saboda gaba d'aya mumy ba'a hayyacin ta take ba, lokacin da suka K'arasa asibitin a reception din hospital suka had'u da Dr muh'd wanda ya fito kar6ar wata allura da xai yiwa musaddiq. Gaba d'aya jikin su yayi sanyi ganin yanda muh'd idanun shi sunyi ja alamar yaci kuka sosai, shi yayi musu jagora xuwa cikin d'akin suna shiga ganin musaddiq da suka yi kamar gawa yasa su furta kalmar "inallilahi wa'inna ilaihir rajiun " Su kayi kan musaddiq gaba d'ayan su a rikice............ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A muh'd ♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* _Wannan shafin na ki ne *Asy khaleel* fatan alkhairi a gare ki Allah ya bar xumunci, ni Aishat ina k'aunar ki sosai kuma kirkin kine yaja miki dumbin masoya, ina miki fatan alkhairi a duk inda kike_ *PAGE 15* Su kayi kan musaddiq gaba d'aya a rikice, tuni mumy ta fashe kuka tana cewa "wayyo Allah nah musaddiq me ya mayar min da kai Hka wannan wanne irin ciwo ne? " Kuka sosai mumy take har da majina hankalin ta ba k'aramin tashi yayi ba na ganin d'annata a hka, shi kuwa daddy xama yayi tare da k'urawa musaddiq ido yana kallon shi ya ma kasa furta komai tsabar tashin hankalin da yake ciki. "muh'd fad'a min abin da yake damun musaddiq? " Dr muh'd xama yayi kusa da kafar daddy cikin rawar murya kamar xai fashe da kuka ya fara cewa "daddy kayi hak'uri akan rufe ma abin da yake damun musaddiq da muka yi da dad'e wa, saboda amana musaddiq ya bani akan kada na furta abin da yake damun shi, ina kok'ari na wajen kwantar mishi da hankali tare da bashi shawarwari amman yak'i dai na sa damuwa acikin xuciyar shi, so shine kuma d'axu wurin d'aurin auren Yah sadeeq ciwon nashi ya tashi " Duk sun xuba wa muh'd ido suna sauraren shi mumy mai yin kuka ma shiru tayi don ta fahimci abin da ake cewa sai dai hawaye bai bar xuba daga idanun ta ba, cikin xakuwa a fad'i ciwon da yake damun musaddiq daddy yace "toh wanne ciwo ne yake damun shi muh'd sanar da ni?" Sai da muh'd ya d'auki tsawon mintuna kan shi a k'asa Kafin kuma cikin sanyin murya yace "daddy mumy Kuyi hak'uri musaddiq yana cikin wani mugun yanayi, ba wani abu ne yake damun shi sai ciwon xuciya " Lokaci d'aya suka mik'e daddy da mumy suna furta "Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun " Suka furta lokaci d'aya, mumy hannu ta d'ora a kanta tare da rushe wa da wani irin kuka mai ban tausayi, yayin da daddy ya maimaita cewa "ciwon xuciya ne yake damun d'ana, me musaddiq ya nema ya rasa da a rayuwar shi da har wannan mugun ciwon xai Kama shi? " Hannun daddy Dr muh'd ya kamo tare da xaunar dashi kuka muh'd kawai yake ganin yanda wad'annan bayin Allahn yanda suka shiga wani hali mai ban tausayi. "Ya fad'a maka abin da ya sa a ranshi har ya kamu da wannan ciwon? " Cewar daddy yana kallon Dr muh'd, toh fa muh'd ya shiga tsaka mai wuya yanxu xai fad'a musu gaskiar abin da yake damun shi anya kuwa xai sanar dasu yarinyar da yake masifar so ita ce mufidah matar yayan shi sadeeq gaba d'aya ya rasa abin da xai ce gashi sun xuba mishi ido suna kallon shi kowanne yana son jin abin da xai fad'a....... A 6angaren amarya mufidah kuwa tun lokacin da taji an d'aura auren ta da Yah sadeeq sai gaba d'aya jikin ta yayi matuk'ar yin sanyi, sai tsokanar ta aike en uwa suke amman babu bakin magana sai dai tayi musu yak'e, don gaba d'aya baka ce ga yanayin da take ji ba farinciki ko akasin hka, tana kule cikin bedroom d'in umman ta, tun lokacin da aka sa lokacin auren bata iya cin abincin kirki ba sai tunani kuma ta rasa tunanin da take, ita dai tasan wani lokacin tana tunanin musaddiq musamman lokacin da ya kaita gidan shi ta wanke mishi kayan da ta 6ata mishi, da lokacin da take rungumar shi tana neman taimakon shi xuwa lokacin da taje gidan su da ya kusan fad'uwa har ta rik'o shi suka had'a jiki, sosai tana tunano lokacin har wani lokacin tana murmishi, ta rasa gane abin da yake damun ta shi yasa gaba d'aya ta rame saboda da tunani ga rashin son cin abinci. Umma, nabila da Yah Omar sun yi nacin duniya da ta fad'a musu abin da yake damun ta amman sai tace ba komai, to me xata ce musu ita kanta wani lokacin sai ta rasa ma tunanin da take, abinci kuwa sai umma ta sa ta a gaba da fad'a take iya ci, sai dai Kyan da ta k'ara don tasha gyaran jiki ciki da waje don umma ba wasa a wannan 6angaren ta tsaya tsayin daka ta gyara d'iyar ta daman ita kad'ai Allah ya bata mace sai Yah Omar dole ta gyara ta. Shigowar umma cikin d'akin yasa mufidah saurin d'aukar wayar ta tana danna wa don bata son umma ta gane tunani take, amman duk da hka sai da umman tace "Hmmm ana nan ana sana'ar ko mufidah? " Er dariya ta k'ak'alo tayi tare da cewa "Haba umma ba tunani nake ba, hutawa nake na gaji da hayaniya wlh" "ae sai hak'uri taron kenan, gashi can ana d'aukan pictures da en uwa da kuma angwaye sai ki fito " D'an 6ata fuska mufidah tayi tare da cewa "ni gaskia umma na gaji " "Haba er umma d'aure ki tashi kin ga abin tarihi ne " Kafin mufidah ta ce komai sai ga wasu emmata sun shigo sun ci uban kwalliya 'ya'yan k'anin baban su mufidah ne, hannun ta suka rik'o tare da fito wa xuwa main parlour inda ake d'aukan pictures, duk inda mufidah ta gifta idanun Yah sadeeq akanta har sai da Yah Omar ya fara tsokanar shi, shi dai sai murmishi yake don yau ranar farinciki ce a gare shi, ita kuwa mufidah duk ta gaji da kallon da Yah sadeeq yake mata K'arshe sai ta sulale ta gudu d'aki. ****** "kai muke saurare muh'd maxa fad'a min gaskia? " "uhm daddy daman wata yarinya yake masifar so, sai kuma bai furta mata da wuri ba har wani ya riga shi iyaye suka shiga xancen shine abin ya kasa cire shi daga cikin xuciyar shi saboda yana masifar son ta " "Wace yarinya ce muh'd? " Mumy ta tambaye shi cikin mamaki sosai don ko da wasa musaddiq bai ta6a nuna musu yana son wata yarinya ba. "Mumy sunan ta mufidah kuma yau ne d'aurin auren ta ma" "Wacce mufidah kake nufi??? " Lokaci d'aya Mumy da daddy suka furta gaban su na mugun fad'uwa tsoron su kada ya kasance ace hasashen su ya xama gaskia................. Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *E.W.F* _Wannan shafin naku ne ma'abota

Chapter 5 of 23