abu a tattare da xuciya ta da jiki na, ban tabbatar da son da nake mata sai ranar da ta xuba min juice a jikina na kaita gida na ta wanke min a cikin daren da na taimake ta daga hannun wasu 6ata gari har jiki na ya had'u da jikin ta a ranar na tabbatar da sonta a cikin xuciya ta ina niyyar neman soyayyar ta............_
_sai dai kash d'an uwana yaya na da nake dashi shi kad'ai ya furta yana son ta yayana mai kauna ta da son bani farinciki a ko da yaushe, na hak'ura da ita har abada saboda nasan nayin saken da nasan baxan ta6a samun ta ba a rayuwa ta_
_son ki ne xai xama ajali na don nasan har na mutu baxan ta6a dai na k'aunar ki ba, i luv yhu so much *M*, i really luv yhu_.
Yana gama fad'in hka ya rufe littafin tare da ajiye wa ya fad'a kogin tunani sosai ga son mufidah yana k'ara nukurkusar xuciyar shi lokaci d'aya wani mugun ciwon kai ya kama shi cikin en mintuna wani xaxxafan xaxxa6i ya rufe shi sai karkarwa sanyi yake sosai jikin shi ya d'auki wani mugun xafi lokaci d'aya kuma ya fara wani jan numfashi wanda dak'yar ya ke fita.
Yah sadeeq bayan yaje gidan su mufidah anan farfajiyar gidan ya had'u da Yah Omar yana kok'arin tafiya gidan su nabila nan suka rungume junan su sannan suka yi musabiha cikin murmishi Yah Omar yace
"Hmmm wannan gayun dai nasan xuwa wurin mutuniyar kayi ba xuwa na ne ba "
Cikin dariya sadeeq yace "yes nawan ashe ka gano hkan "
Tafawa suka sannan suka juya xuwa cikin gidan bayan sun gaisa da umman su mufidah sannan Yah Omar ya kai shi palon saukar bak'i daga hka yace
"toh ni Naga ma aiki na xan tafi wajen tawa matar to be Insha Allah"
"Yayi kyau friend ngde sai ka dawo "
"ba Godiya tsakanin mu sadeeq mun riga da mun xama en uwan juna sai mun yi waya bye "
Yana gama fad'in hka ya fice daga falon da sauri , bai fi mintuna 5 da tafiyar Yah Omar mufidah ta shigo falon cikin sanyayyiyar muryar ta mai dad'in gaske tayi sallama cikin murmishi sadeeq ya amsa sallamar cikin sauri ya mik'e tsaye ya kar6i babban plate di'n dake hannun ta ya ajiye kan table d'in tsakiyar palon tukunna yayi mata nuni da ta xauna ae kuwa ta samu waje ta xauna tare da gaida shi nan ya amsa yana kallon ta don tayi mishi kyau sosae gashi ta suturta jikin ta da hijab babba mai hannu hakan ba k'aramin dad'i yaji ba xuciyar shi ta Kara k'aunar ta bayan sun gama gaisa wa ne ya fara janta da er hira ganin ta kasa sakin jikin dashi daga K'arshe ya fara da yi mata bayanin abin da ya kawo shi
Tsugunna wa yayi a gaban ta amman bai ta6a mata jiki ba ya kwantar da murya a nutse ya fara cewa "mufidah abin da ya kawo ni wajen ki ba komai bane sai neman soyayyar ki tun lokacin da na fara ganin ki kuma auren ki xanyi ki bani dama na nuna miki son da nake miki "
shiru mufidah tayi tana tunani shi kuwa Yah sadeeq cigaba wa yayi da cewa "say something mufidah please "
D'an ajiyar xuciya ta yi cikin jin kunyar shi tace "sai nayi tunani "
"Okay ba matsala Allah yasa naji kyakkyawan result "
murmish kawai yayi ya dan sha juice and snacks din da taka wo mishi suna er hira har xuwa gabannin mangarib sannan yayi mata sallama ya tafi.
Mumy ce ta fito daga bedroom d'in ta xata shiga kitchen ta tuna tun da musaddiq ya shige bedroom d'in shi bai fito ba hka kawai taji gaban ta ya fad'i da sauri ta nufi bedroom d'in tana shiga ta tarar da musaddiq lullu6e da bargo kato ya kudundune a ciki yana rawar sanyi ga numfashin shi dak'yar ya ke jan shi cikin tsananin tashin hankali ta nufi kan bed d'in tana cewa
"Musaddiq!"
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*written by*
Aishat A muh'd
♻ *E.W.F*
*Page 10*
Da sauri mumy ta k'arasa kan bed d'in ta bud'e rufar da musaddiq yayi da bargo da sauri ta janye hannun ta lokacin da ta ta6a jikin shi taji xafi xau dashi cikin kid'ime wa Mumy tace
"musaddiq me yake damun ka? "
Cikin rawar sanyi da murya yace "way... wayyo mumy xax..... xaxxa6i ne yake damunaaa"
Ya K'arasa fad'i yana jan wani irin numfashi da yasa gaban mumy muguwar fad'uwa cikin tashin hankali tace "sannu bari na kirawo Dr muh'd ya duba ka sannu "
Cikin sauri mumy ta d'auki wayar musaddiq da take gefen bedside ta nemo number d'in Dr muh'd bayan ya d'aga yana tsokanar musaddiq ya d'auka shi ne sai da yaji muryar mumy cikin girmama wa ya gaida mumyn yana godewa Allah da bai yi wata maganar da xai ji kunya ba, mumy ce take sanar mishi Yayi sauri ya xo ya duba musaddiq bashi da lafia tuni hankalin Dr muh'd ya tashi ya katse wayar da sauri ya d'ebe kayan aiki ya shiga mota gidan su musaddiq ya nufa .
Dr muh'd abokin musaddiq ne sosai tare suka yi karatu har suka dawo nigeria suna xumunci sosae gashi a gari d'aya suke sai xumuncin Ya k'ara k'arfi har iyayen su suma suka k'ulla xumunci sanadiyyar yaran su, Dr muh'd yana bala'in son musaddiq sosai gashi halin su yaxo d'aya kosan ko yaushe yana gidan amman musaddiq baya xuwa gidan su sosai sai ya kama.
Cikin en mintuna Dr muh'd ya k'arasa gidan kai tsaye d'akin musaddiq ya nufa a bakin kofa yayi kici'bis da mumy tana ta safa da marwa ta kasa xama waje d'aya, d'akin ya shiga nan ya fara duba jikin musaddiq cikin k'ware wa da iya aikin nashi.
Xaune na hango Dr muh'd ya xuba tagumi yana kallon musaddiq wanda yak'i yarda Yayi mishi allurar bacci ko ya samu ya huta cikin damuwa d'auke a fuskar Dr muh'd yace
"my friend mene kasa a ranka hka me yake damun ka da xaka sa tunanin abu a ranka wanda xai janyo mata wata matsalar, haba musaddiq kamar ba likita kake ba kene ma mai bawa wani shawara ma ya rage tunani balle kai "
Kallon shi musaddiq kawai yake cigaba yayi da maganar shi yana cewa "ina son ka fad'a min matsalar ka yanxu na gani ko Allah xai sa na baka wata shawarar ka daina barin abu a ranka kana tunani my friend "
D'an murmishin yak'e musaddiq yayi tare da cewa "me ka gano yake damuna aboki? "
Cikin tausayin musaddiq yace "naga jinin ka ya hau fah sannan yanayin bugun xuciyar ka ya k'aru fiye da yanda mutum mai cikakken lafia take tell me what happened to you my friend? "
Musaddiq ya bud'e baki xai yi magana kenan Yah sadeeq ya turo kofar ya shigo d'akin hankalin shi a matuk'ar tashe kama hannun musaddiq yayi yana cewa "brother me ya same ka ne yanxu mumy take kirana a waya baka da lafia "
Jiyo wa yayi kan Dr muh'd yana cewa "Doctor sanar da ni abin da yake damuwa da d'an uwana kada kace min wani babban ciwo ne please "
Yah sadeeq ya k'arasa fad'i idanun shi taf da hawaye cikin tausayin Yah sadeeq Dr muh'd ya bud'e baki xai yi mishi bayanin abin da yake damun musaddiq sai suka had'a ido da musaddiq ya marairaice fuska tare da yi mishi alama da hannu yana rok'an shi kada ya fad'a wa Yah sadeeq gaskiar abin da yake damun shi.
Cikin sanyin jiki Dr muh'd yace "Yah sadeeq xaxxa6in typhoid fever ne yake damun shi amman Insha Allah xai samu lafia ka kwantar da hankalin ka "
Hannun Dr muh'd ya kamo yana cewa "Okay doctor thank u but ina son ka bashi kula wa sosai bana son wani abu ya faru da k'anina "
"xanyi iyakar kok'ari na yah sadeeq kuma xai xamu lafia da sauri Insha Allah "
Rungume Dr muh'd yayi cikin jin dad'in abin da ya fad'i sannan ya dawo kan musaddiq tare da tatta6a jikin shi jin xaxxa6in ya sauka yasa shi sakin wata ajiyar xuciya nan ya dunga yi mishi sannu duk motsin da yayi hka ma mumy ta shigo suka had'u suna lalla6a shi Dr muh'd yana gefe xuciyar shi cike da tunanin me musaddiq yasa a ranshi har xai kamu da hawan jini yana samun duk wata kulawa a wajen iyayen shi da d'an uwan shi.
Har Dr muh'd ya tafi bai samu damar ke6ewa da musaddiq ba yaji abin da yasa a ranshi kuma me yasa yak'i yarda Yah sadeeq yasan gaskiar abin da yake damun shi yasa shi yin k'arya da wannan tunanin ya k'arasa gida.
Cikin k'wanaki 2 musaddiq yana fama da wani xaxxa6i da ciwon kai duk yabi ya rame ya sake yin fari sosai iyayen shi sosai suke kula dashi don duk a xaton su xaxxa6in typhoid ne basu san gaskiar xancen ba daga Allah sai musaddiq din sai Dr muh'd sune suka san ainahin abin da yake damun shi kuma Har xuwa yanxu Dr muh'd bai samu damar yin magana da musaddiq ba.
A 6angaren Yah sadeeq kuwa ba k'aramin tsorata yayi ba da jikin musaddiq amman ganin ya fara samun sauk'in xaxxa6in yasa shi hankalin shi ya d'an kwanta, yah Omar da husna da nabila sun xo dubiyar shi a ranar da yafi samun sauk'i su kaxo har ya samu damar fito wa palo yana xaune suka shigo palon Yah sadeeq yana musu jagora da mufidah ya fara had'a ido ae kuwa take yaji gaban shi ya fad'i bugun xuciyar shi na sake bugawa da sauri da sauri.
Bayan sun gaisa da Mumy suka yiwa musaddiq Sannu da jiki dak'yar ya iya bud'e bakin shi ya amsa nan aka xauna ana er hira tashi musaddiq yayi ya shiga bedroom din shi mumy ma ta shige kitchen tana had'a wa su mufidah abin motsa baki ganin hka yasa nabila ta bita tana taya ta ,yah sadeeq kuma yaja Yah Omar xuwa part d'in da yake ginawa wanda yake fatan su rayu da mufidah a ciki har sadeeq yana tsokanar mufidah ko xata je ta ga ni ae kuwa ta danna mishi harara dariya suka kyalkyale da ita shi da Yah Omar da hka suka fita daga palon aka bar mufidah ita d'aya xaune.
Tsawon 5 mint tana xaune kamar ance d'ago kan ki sai ta hango musaddiq ya fito daga cikin d'akin shi yana dafe da kanshi alamar ciwo yake mai sai ta ga kuma ya fara layi kamar xai fad'i k'asa ganin yana kok'arin fad'uwa yasa mufidah tashi da sauri ta nufi wajen shi tana xuwa dai dai wajen da yake tsaye yayi baya xai fad'i da sauri ta rik'o shi to da yake k'arfin namiji da mace ba d'aya ba kawai sai yayi jikin ta ita kuma mufidah yafi k'arfin ta kawai sai tayi baya xata fad'i sai taji kuma an fisgo ta xuwa cikin jikin shi ta fad'a kan faffad'en kirjin shi da sauri ta d'ago kanta suka had'a ido yana mata wani irin kallo gaba d'aya idanun shi sun canja Kala sun kai wajen second talatin suna kallon junan su don mufidah hka kawai taji ta kasa d'auke idanun ta daga cikin idon shi.
Ji tayi ya raba ta da jikin shi ya juya ya koma cikin d'akin, ita ma mufidah ta koma kan kujera ta xauna tana tunanin wannan wanne irin mutum ne a taimaka mishi babu godia dama nasani na barshi ya fad'i Cewar mufidah a fili har da Murgud'a bakin ta kamar yana ganin ta.
Tana xaune a hka sai ga mumy da nabila sun fito daga kitchen kowannen su rike da babban plate a hannun su da sauri mufidah taje ta kar6i abun hannun mumy ta ajiye akan table ana hka sai ga Yah sadeeq da Yah Omar sun dawo sun d'an ta6a abun da Mumy ta kawo musu sannan suka yi mata sallama suka tafi tare addu'ar Allah ya bawa musaddiq lafia.
Mufidah ta kar6i soyayyar sadeeq duk da ba wani son shi take sosai ba kunyar shi ce tasa ta amince da soyayyar shi kuma ganin irin son da yake mata ya wuce misali gashi bashi da makusa nan fah iyaye suka shiga xancen.
Cikin kankanin lokaci aka tsayar da ranar auren sadeeq da mufidah, yah Omar da nabila to abune duk ansan juna tun da dad'e wa ana xaune kusan tare sun xama kamar en uwan juna.
Shi kuwa musaddiq iyayen shi sun rasa gane kan shi yau lafia gobe cuta duk yabi ya rame ciwo kullum Cin shi yake gashi yak'i gayawa Dr muh'd ko akwai wani taimako da xai yi mishi, kullum ya hau na jinin shi maimakon ya sauka sai hawa yake har takai Dr muh'd ya duba shi a wata safiya bayan sun gama duba patient din su hankalin Dr muh'd ba k'aramin tashi yayi ba ganin har xuciyar musaddiq ta fara ta6u wa cikin tsananin tashin hankali Dr muh'd ya kalli musaddiq da yake kwance kan bed d'in asibitin yace
"yau baxan iya rabuwa da kai ba musaddiq sai ka fad'a min abin da yake damun ka, ko kuma na sanar dasu daddy Don baxan xuba ido ka mutu a banxa ba "
Murmishin da musaddiq yayi sai da Dr muh'd ya tsorata bud'e baki yayi xai yi magana kenan wani tari ya kama shi ya dunga yin tarin nan lokaci d'aya idanun shi da fuskar shi suka yi ja kanshi Dr muh'd yayi yana mishi sannu gaba d'aya hankalin shi a tashe yake ya tsorata da jikin musaddiq sosai wani jan numfashi musaddiq yayi yaraf kuma sai ya xube kan gadon kamar matacce cikin raxani da kad'uwa Dr muh'd ya fara girgixa yana cewa
"na rok'e ka musaddiq ka tashi please "
Amman ina musaddiq bai ma san abin da yake yi ba.................
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*written by*
Aishat A muh'd
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
*Page 11*
Amman ina musaddiq bai san ma yana yi ba, da gudu Dr muh'd ya fita daga room d'in yaje ya kirawo wasu doctor's guda biyu nan suka had'u kan musaddiq suka fara kok'arin ceto rayuwar shi.
Sun dad'e sosai akan musaddiq Kafin Allah ya taimake su numfashin shi ya dawo dai dai nan suka sanya mishi drip tare da yi mishi allurar bacci tukunna suka fita daga room d'in aka bar Dr muh'd yana xaune a gefen shi ya xuba mishi ido yana kallon shi xuciyar shi cike da tsantsar tausayin shi.
Yini guda cur musaddiq yana bacci sai yamma sosai ya farka da Dr muh'd ya fara had'a ido lokacin da ya farka cikin sauri Dr muh'd ya rik'e shi tare da cewa
"sannu musaddiq ya kake jin jikin na ka? "
Cikin kasala da sanyin murya yace "muh'd na samu lafia ngde sosae aboki "
Duba shi ya k'ara yi sannan ya taimaka mishi suka shige office d'in shi ruwan wanka mai d'umi Dr muh'd ya had'a mishi bayan musaddiq yayi wanka tare da yin alwala ya fito ya gyara jikin shi sannan ya rama sallolin da ake bin shi bayan ya idar ne ya kwanta kan doguwar kujerar da take cikin office d'in ya xurfafa a tunanin mufidah kullum yana addu'ar Allah ya cire mishi son mufidah a cikin xuciyar shi amman kamar k'ara mishi son nata ake ya rasa ya xai yi ya fitar da sonta daga cikin xuciyar shi.
Yana cikin wannan tunanin ne Dr muh'd ya shigo office d'in sau biyu yana sallama amman musaddiq bai ji shi ba yayi xurfi a tunani sosai girgixa kai kawai yayi ya nufi inda yake kwance ya girgixa mishi kafad'a tare da cewa
"Musaddiq!"
Firgigit ya dawo hayyacin shi yana kallon Dr muh'd da idanun shi wad'anda suke a lumshe.
"ga tea nan kasha ga magungunan ka nan Idan ka gama xamu yi magana "
Cewar Dr muh'd yana mik'a wa musaddiq cup d'in da ya had'a tea bai yi musu ba yasa hannu ya kar6a ya fara sha bayan ya shanye Dr muh'd ya bashi magungunan yasha sannan ya jiyo ya fuskan ci musaddiq yasha Kunu sosai don yana son sanin gaskiar abin da yake damun shi ya fara da cewa
"musaddiq ina son sanin me yake damun ka, me kasa a ranka har yana kok'arin haddasa maka mummunan ciwo a jikin ka? "
Kallon shi musaddiq yayi sannan ya kawar da kanshi daga kallon shi yace " babu abin da yake damuna muh'd just ciwo daga Allah ne"
"enough musaddiq baxan ta6a yarda da abin da kace min ni nasan kan ka tuna ba ma 6oye wa junan mu matsalar mu, idan kuma ka k'i fad'a min wlh xan je na gayawa su daddy su tambaye ka ae su dole ka fad'a musu abin da yake damun ka ?" Cewar Dr muh'd kenan.
"kaiii ka yarda fah da gaske nake babu abin da yake damuna"
"Okay shikenan Allah ya baka lafia"
Fad'in Dr muh'd sannan ya nufi fita daga office d'in ranshi a matuk'ar 6ace, caraf yaji musaddiq ya rik'e mishi hannu tare da cewa
"I'm so sorry aboki ni kaina bansan abin da yake damu na ka taya ni da addu'a kawai "
"ka cika ni Idan baxa ka fad'a min gaskia ba na rabu da tambayar ka abin da yake damun ka su daddy xan fad'a wa"
Musaddiq ya rasa ta inda xai kauce wa muh'd a wannan Karon don yak'i tsayawa ya yarda da abin da yake ce mishi idanun shi sun yi ja sosai ga wani irin jiri da yake ji da axabbaben ciwon kai baisan lokacin da ya bud'e baki yace
"ina son ta muh'd soyayyar tace tasa na shiga cikin wannan halin na rasa yanda xanyi na cire ta daga cikin xuciya ta "
Koma wa yayi ya xauna da k'arfi kan kujera sannan ya cigaba da cewa "baxan iya fad'a maka adadin son da nake mata ba amman nayi sake abokina na rasa ta har abada "
Sakin baki Dr muh'd yayi yana kallon musaddiq cikin mamaki don shi tun da yake dashi bai ta6a ganin yayi mishi xancen mace ba a hankali ya k'araso inda musaddiq yake xaune hannun shi rik'e da kanshi da yake masifar yi mishi ciwo kamar xai cire, dafa mishi kafad'ar shi yayi tare da cewa "ita wace musaddiq, taya akayi kayi sake har ta kubce maka? "
Cikin tsananin ciwon kai yace " mufidah ce aboki mufidah wadda Yah sadeeq xai aura itace nake nayi saken da ban sanar mata ba har Yah sadeeq ya ganta gashi yana masifar son ta har iyaye sun yi magana nan da two month's xa'a yi bikin "
Hannun shi yasa ya rik'o kafad'un muh'd da k'arfi yace "ka ji abin da yake damu na kuma nayi wa Kai na alk'awarin baxan ta6a bari Yah sadeeq yasan wannan xancen ba har abada saboda nasan idan ya sa ni wlh xai hak'ura ya bar min ita, kai ma na rok'e ka kada ka fad'a wa kowa wannan maganar har kuwa rashin lafiyar da yake damu na, na hak'ura da ita har abada baxan rusa farinciki d'an uwana ba"
Wani mugun tausayin musaddiq ne ya kama muh'd har wasu k'walla sai da suka xubo mishi na tausayin musaddiq hannu yasa ya goge hawayen tare da cewa
"tabbas nima baxan baka goyan bayan Yah sadeeq yasan wannan xancen ba don ni shaida ne akan irin yanda masifar son ka nasan komai xai iya yi maka ,amman ina rok'an ka don Allah musaddiq ka cire mufidah da ga ranka please"
Wani murmishin yak'e musaddiq ya saki tare da cewa "aikin gama ya gama muh'd don son mufidah ya riga da ya shiga cikin xuciya ta baxan iya cire shi ba ni nasan da sonta xan mutu "
Yana gama fad'in hka ya mik'e tsaye tare da d'aukan briefcase din shi da key di'n mota, yayin da Dr muh'd ya bishi da kallon tausayi tabbas abokin nashi yayi xurfi a son mufidah wannan shi ake kira da *YAYI SAKE*, shi ma Dr muh'd di'n mik'e wa tsaye yayi bi bayan shi.
Ya kai hannun shi kan handle di'n kofar xai bud'e kenan aka turo kofar tare da shigo wa lokaci d'aya gaban musaddiq da Dr muh'd yayi mummunan fad'uwa saboda had'a idon da suka yi da Yah sadeeq yana shigo wa fuskar shi d'auke da tarin damuwa sosai da gani hankalin a matuk'ar tashe yake wajen musaddiq ya nufa kai tsaye..................
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*written by*
Aishat A muh'd
♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
*PAGE 12*
Wajen musaddiq ya nufa kai tsaye sai da yaxo gab da shi tare da kamo hannun shi yace
" why musaddiq da xaka yi switch off d'in phone's din ka duk ka d'aga mana hankali ina office mumy ta kirawo ni naxo na duba ka, gashi har time d'in dawowar ka ya wuce baka dawo ba?"
D'an murmishin yak'e musaddiq yayi tare da cewa " sorry bro ina lafia wani aiki ne ya rik'e ni shi yasa nayi switch off d'in wayar "
"Okay amman kana sa wayar naka a silent ka daina kashe wa, don ka hankalina ya tashi sosai "
"Haba Yah sadeeq ni fah ba yaro ba ne "
Musaddiq ya fad'i yana dan Murmishi, hararar wasa Yah sadeeq yayi mishi tare da cewa "a wurin Mumy, daddy da kuma ni duk kallon yaro muke ma so dole mu tattara dukanin kulawar mu kan ka "
Yah sadeeq ya k'arasa fad'i yana kallon fuskar musaddiq a yau sai yaga musaddiq din ya k'ara haske fiye da koyaushe gashi ya rame amman da yake Yah sadeeq bai fiye irin wannan binciken ba sai kawai ya juya da kallon shi kan muh'd yace
"likita bokan turai ya fama da patients ?"
Cikin murmishi Dr muh'd yace "lafia qlau Yah sadeeq ya aiki? "
"aiki Alhmdllh gashi nan muna ta fama yanxu ma daga office d'in nayo nan "
"Masha Allah, Allah ya taimaka "
"Ameen muh'd "
Daga hka suka fita daga office d'in gaba d'aya Dr muh'd ya shiga motar shi bayan sun yi sallama ya tafi, yayin da Yah sadeeq yaki yarda musaddiq yayi driving dole sai motar Yah sadeeq din musaddiq ya shiga yaja su gida kai tsaye suka nufa.
Hka lokaci ya cigaba da tafiya al'amura sunyi nisa don biki ya matso sosai kowanne 6angare suna shirye shiryen bikin ango Yah sadeeq da ango Yah Omar kuwa kamar su matso da ranar bikin suke tsabar xumud'i.
A 6angaren amarya mufidah da amarya nabila suma sai shirin su suke nabila sai rawar kai ake yi ita kuwa mufidah gata nan dai ba wanda xai iya fahimtar halin da take ciki na farin ciki ko akasin hka.
Mufidah ce a xaune tana tunanin da ta rasa na mene gaba d'aya bata farin ciki da auren nan don ba wani son Yah sadeeq take ba kawai kunyar shi take ji shi yasa ta kar6i soyayyar shi gashi yana mata kwarjini sosai kuma Yah Omar da nabila su ne suka k'ara tunxura ta har ta yarda dashi dad'in dad'awa kuma yana da halayya masu kyau iyayen ta da sauran en uwanta suna matuk'ar kaunar shi, ga biki ya matso don an shiga satin da xa'a fara gabatar da bikin, k'arar Shigowar message ne a wayan ta yasa ta katse tunanin ta tare da janyo wayar tana duba wa cikin mamaki don bakuwar number ce abin da aka rubuta ta fara karanta
" _Nayi matuk'ar rashin furta miki abin da ya dad'e cikin xuciya ta, nayi nauyin baki wajen furta hakan sai gashi wani yaxo ya riga ni har yana kok'arin mallakar ki matsayin matar shi._"
" _ki sani ni mai k'aunar ki ina son ki son da baki baxai iya furta wa nasan har na mutu ina k'aunar ki, Allah ya baku xaman lafia ina miki fatan alkhairi daga mai k'aunar ki_ *M*"
Sosai abin ya d'aure wa mufidah kai abin ya bata mamaki ba Kad'an ba wannan wane shi me ya hana shi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 23