son musaddiq a tun kafin ta auri sadeeq.
Shigowar sadeeq cikin rayuwar ta shi ya hana son yin tasiri cikin xuciyar ta tun da ta riga da tasa a ranta sadeeq xata aura, amman xuwa yanxu ita kanta har tsoro take ji ganin yanda xuciyar ta take son musaddiq abin har mamaki ya ke bata, ita yanxu mene ne mafita.
Da wannan tunanin bacci mai k'arfi yayi awon gaba da ita bata kai da ta nemo mafitar ba.
Musaddiq kuwa tun da ya kunna wa kanshi shower ruwa yana xuba a jikin shi idanun shi a rufe suke ruf kan shi yayi xafi brain nashi tana tunano mishi da irin yanayin da shiga a en mintuna da suka wuce.
Tunanin mafita shima yake ya gaji da wannan abin yana son kawo k'arshen irin wannan xaman a tsakanin shi da mufidah, ya d'auki tsayin mintuna 20 a hkan kafin ya samu kwarin jikin shi ya kashe shower d'in tare da d'aura towel ya fito.
Ajiyar xuciya ya saki ganin mufidah bata d'akin kafin kuma ya saki wani murmishi yace
"ashe ma tsoron bai kai xuci ba sai da ta gama hargitsa min tunani ta gudu idan na kama ki sweet babynah xaki yaba wa aya xak'in ta "
Yana gama fad'in hka ya sake sakin murmishi yana tunanin yanda xai yi wajen fara janyo mufidah a jikin shi ta saba dashi yana son ta dawo bedroom nashi suna kwana tare ko da wani abin baxai had'a su ba shi dai yana ganin ta kusa dashi hankalin shi sai yafi kwanciya da hka shima bacci ya dauke shi mai dad'i cike da mafarkan mufidah...........
Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻ *£xclusive writers forum*
*Likes nd comment's fb page*👇🏻
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
_ina masoyan my sister *sumayya salees sadeeq*,ina masoyan karanta littattafan ta irin su *rayuwar ashwema,dangartakar xuci, yareema jawad*kun ji ta shiru na kwana biyu hutu ta tafi amman yanxu ta xo muku da sabon wani daddad'an labari mai suna *DARIYA BA SO BA*my sister sumy muna biye da ke har xuwa lokacin da xaki kammala shi, maxa ku garxaya ku nemi shi don kada a bar ku a baya, ni Aishat A Muh'd ina miki fatan alkhairi tare da addu'ar Allah ya k'ara basirah da xumunci a tsakanin mu_ #ana tare
*PAGE 52*
Washe gari da safe tun da mufidah ta shirya afnan xuwa skul ta had'a mata komai ta dawo bedroom ta kwanta duk jikin ta ba k'arfi tana nan kwance taji an turo kofar tare da jin muryar musaddiq yana tambayar afnan
"ina mameen ki afnan? "
"daddy tana bedroom a kwance "
Kafin mufidah ta lullu6e jikin ta da blanket har ya shigo suna had'a ido ya watsa mata wani kallo na daban wanda ya haddasa wa mufidah sake fad'a wa a kogin son shi gashi ya sake k'ara mata kasalar da take ji, kasa d'ago kai tayi ta kalle shi wasa kawai take da en yatsun hannun ta, bata ankara ba taga ya xauna a kusa da ita har suna jin d'umin numfashin junan su.
Mamaki sosai ya sake rufe mufidah bata gama wannan mamakin ba taji ya rik'o hannun ta idanun shi a saman fuskar ta yana kallon ta yace
"mameen afnan xamu fita ayi mana addu'a kuma muna buk'atar rakiyar ki ko xuwa parlour ne, ko afnan? "
Cikin dariya afnan tace "Yes! Daddy, mamee ki taso please "
Ta k'arasa fad'i a shagwa6e, shima cikin muryar shagwa6a yace
"please mamee ki taso kada mu yi late fah "
Gaba d'aya mufidah kasa kwakwkwaran motsi tayi saboda tsabar mamaki tana tunanin anya wannan musaddiq ne kuwa ba irin mafarkan da take yi ba ne, jin yana kok'arin d'aga ta ne yasa ta tabbatar ba a mafarki take ba idanun ta biyu.
D'ago kanta tayi da sauri ta kalle shi suna had'a ido ya kashe mata ido d'aya da sauri ta kawar da kanta sam bata da kuxarin tafia tana tsaye cak ganin hka ne yasa musaddiq rik'e d'aya hannun ta yana cewa
"afnan rik'e d'aya hannun mameen na ki mu tafi naga alama tayi suman tsaye sai mun tallafa mata "
Dariya afnan ta sanya kafin ta rik'e hannun mufidah suna janta kamar mutum mutumi har xuwa compound d'in gidan a wajen motar shi suka tsaya afnan tayi kissing d'in hand d'in mufidah ta shiga mota ta xauna tana yiwa mameen nata bye bye amman batasan tana yi ba.
Musaddiq ne ya matso kusa da ita sosai kafin ya rik'e hannun ta dukka biyun da nashi kallon ta yake fuskar shi dauke da murmishi yace
"mameen afnan ina neman alfarmar gyara min d'aki xan dawo da wuri ina son xamu fita tare "
Mufidah sai ta tsinci kanta da gid'a mishi kanta alamar to, wani murmishi ya saki tare da janyo ta jikin shi ya rungume yana cewa
"thank u mameen afnan "
Sakin ta yayi tare da bata peck a kumatun ta sannan ya shiga cikin mota yaja suka bar gidan yana hango mufidah ta madubin motar anan tsaye inda ya barta hannun ta d'aya dafe da wurin da yayi mata peck murmishi ya saki shi kad'ai wani dad'i da nishad'i yana ratsa xuciyar shi har ya sauke afnan a skul sannan ya k'arasa hospital.
Bayan tafiyar su da mintuna uku sannan mufidah ta dawo daga suman tsayen mamakin da musaddiq ya gama bata, anya kuwa babu wata a k'asa canjawar shi farat d'aya daga daren jiya xuwa yau.
Dole na tsaya na karance shi naga ne abin da yake cikin xuciyar shi kafin na sake dashi, murmishi tayi had'e da lumshe idanun ta tana tunanin lokacin da musaddiq ya rungume yarrr taji tsikar jikin ta ya tashi kamar a time d'in yayi hugging d'in ta.
Da wannan tunanin salon da musaddiq ya fara ne ta nufi cikin gidan, tana xuwa ta fara gyaran gidan tun daga bedroom d'in ta ta fara xuwa parlour kitchen gyaran bedroom d'in musaddiq ne na k'arshe.
Tana cikin kok'arin canja bed sheet ne taga wani k'aramin diary ya fad'o daga k'ark'arshin pillow daukan shi tayi tare da ajiye wa saman bedside, cikin lokaci kad'an ta canja fasalin bedroom d'in musaddiq ta gyara shi tsaf tsaf ko'ina tun daga toilet har xuwa cikin room d'in wani sanyayen k'amshin turaren room freshener yake yi bayan ta gama gyaran ne har xata fito idanun ta suka sauka kan diary d'in musaddiq da ta ajiye.
Sai kawai ta tsinci kanta da son bud'e shi ta karanta shi d'auko shi tayi ta nufi bedroom d'in ta dashi har ta xauna xata bud'e shi ta karanta sai ta dubi agogo taga time yaja sai kawai ta ajiye ta nufi kitchen da niyyar idan ta gama girki ta dawo ta karanta shi.
Kitchen ta shiga ta fara had'a musu abinci Kala biyu da snacks sai drinks d'in da tayi na xallar fruit salad tana gama wa ta jera su a dining table kafin ta gyara kitchen d'in tayi wanke wanke Bayan ta gama gyara ko'ina tsaf ne ta sake fesa air freshener a ko'ina.
D'akin ta wuce ta fad'a toilet tayi wanka da alwala kafin ta fito ta xura jallabia sallah ta gabatar kafin ta gyara jikin ta cikin wani English wears riga pink colour da siket baki irin mai bud'e war nan daga k'asa belt d'in siket d'in ita ma pink ce tayi kyau sosai light make up tayi sannan ta fesa different colour's perfumes a jikin ta da humra kowanne motsi tayi kamshi ne daddad'a yake tashi a jikin ta.
Bayan ta gama shirya wa ne sai ta xauna kan sofa phone nata ta d'auko ta kirawo umma dasu mumy suka gaisa kafin kuma su yi sallama ta ajiye phone d'in, xama tayi tana tunanin abin da musaddiq yayi mata da safe ba k'aramin tsaya mata a rai yayi ba.
Sake hango diary d'in shi tayi a karo na biyu taje ta d'auka son karanta shi kawai take gashi book d'in ya birge ta sosai, hannu tasa tana kok'arin bud'e farkon shafin dai dai lokacin gaban ta yayi wani irin mugun fad'uwa...............
_tohh fah readers ga mufidah da dairy d'in musaddiq ko xata karanta ko kuma xata bari, gashi kuma musaddiq ya fito da wani sabon salon ko me yake nufi da hkan, ku jira ni a next page don jin me xata kasance, ku dad'a hak'uri da ni na kusan gama muku shi gaba d'aya_
Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻ *£xclusive Writers Forum*
*Likes nd comment's fb page 👇🏻
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com
*PAGE 53*
Sake hango diary d'in ta yi a karo na biyu taje ta d'auko shi, son karanta shi kawai take gashi book d'in ya birge ta sosai, hannu tasa tana kok'arin bud'e farkon shafin dai dai lokacin taji gaban ta yayi wani irin mugun fad'uwa jikin ta ne yayi sanyi dakyar ta iya tattara k'arfin da yake jikin ta wajen bud'e first page d'in.
Dummm wata muguwar fad'uwar gaba ta sake yi a karo na babu adadi sai dai wannan karon tafi ta koyaushe sakamakon ganin picture d'in ta wanda idan baxa ta manta ba ranar da suka had'a wa Yah Omar birthday party ne ta d'auka tana dariya tayi masifar yin kyau sosai a pic d'in.
Tsura wa picture d'in ido tayi brain nata yana dad'a hargitse wa mene had'in pic d'in ta da Musaddiq da har xai sanya mata shi a cikin diary d'in shi, next page ta bud'e kuma taga ya rubuta Mufidah ina son ki kece rayuwa ta, na fara son ki tun ranar da na fara had'uwa da ke lokacin da kika shigo hall a time d'in da na ke lecture har na kore ki waje, nan gaban Mufidah ya cigaba da bugawa da k'arfi duk ta wani rud'e jikin ta har 6ari yake yi.
Lokaci d'aya hawaye suka fara xuba a idanun ta cigaba da karanta duk wasu sirrikan cikin xuciyar Musaddiq har da text messages d'in da yake turo mata su duk ta gane su xuwa lokacin da ya fara kamu wa da ciwon xuciya duk a dalilin sonta!.........
Tun kafin Mufidah ta k'arasa karanta wa take xubar da hawayen tausayin Musaddiq najin irin wahalar da Musaddiq yasha akan ta wani irin mugun tausayin shi ne ya dad'a kamata ga wani irin son shi da yake k'ara shiga cikin xuciyar ta.
Ta dad'e xaune anan tana kuka dakyar ta iya jure k'arasa karanta wa, wani irin ciwon kai ne ya dirar mata lokaci d'aya ga idanun ta sun kumbura sun yi sosai saboda axabar xafin da suke mata ma dakyar take iya bud'e su.
Dama Musaddiq hka yake son ta hka yayi dakon sonta da kaunar ta wanda daga k'arshe ya kamu da ciwon xuciya, why why Musaddiq da xaka 6oye min wannan abin kana dad'a cutar da xuciyar ka, daga yau ta dauki alk'awarin kasance wa da Musaddiq xan na kyauta ta maka tare da yi maka biyayya duk abin da xai mata ta dauki niyyar kyautata mishi duk mai yi maka irin wannan mugun son baxai ta6a iya jure wulak'anta wanda yake so ba.
Tunani kala kala Mufidah ta dunga yi akan yanda xata kawo k'arshen wannan irin xaman nasu da Musaddiq, dakyar ta iya tashi tsaye ta nufi bedroom d'in Musaddiq ta ajiye mishi diary d'in kamar yanda ta ganshi, d'akin ta ta dawo kwanciya tayi kan bed ta kudundune da blanket sakamakon sanyin da ta fara ji yana ratsa gangar jikin ta.
Cikin few minutes xaxxa6i sosai ya rufe Mufidah don ba k'aramin kuka tasha ba har ya sanya mata ciwon kai ga xaxxa6i ya rufe ta idanun ta a lumshe but hawaye suna fito wa daga cikin su ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta gaban Musaddiq tana bayyana mishi abin da yake kunshe cikin xuciyar ta.
Jikin ta ya d'auki xafi sosai tana nan kwance taji shigowar motar Musaddiq cikin gidan runtse idon ta tayi lokaci d'aya kamar mai baccin gaske tayi luf da ita ko kwakwkwaran motsi bata yi.
"Mamin Afnan where are you? "
Taji muryar Musaddiq ta doki cikin kunnen ta wanda ya haddasa mata fad'uwar gaba a karo na babu adadi.
Musaddiq da Afnan sai da suka duba parlour, kitchen, garden basu ga Mufidah ba tukunna suka yi tunanin ko tana bedroom don hka suka nufi nan.
Tura kofar bedroom d'in yayi ya hango ta kwance kan bed ta kudundune cikin mamaki yace
"Mamin Afnan lafia? "
Jin tayi shiru bata bashi amsa ba ne yasa shi k'arasa wajen da take da sauri, hannun shi ya sanya tare da yaye blanket d'in da ta lullu6a da shi, hannun shi ya sanya saman wuyan ta da sauri ya janye saboda xafin da jikin ta ya d'auka, sake runtse idon ta Mufidah tayi gam ita a dole bacci take batasan hawayen da suke xuba a idanun ta sun fallasa ta ba.
Cikin gigice wa Musaddiq ya ce
"Mufidah xaxxa6i ne yake damun ki? "
Ya sake tambayar ta a karo na biyu but tayi tsit ta kyale shi, ganin hkan da tayi kuwa ba k'aramin sake hargitsa Musaddiq yayi ba, baisan lokacin da ya xauna ba ya sanya hannun dukka biyun ya d'ago ta tare da yi mata maxauni cikin jikin shi lokaci d'aya suka saki wata ajiyar xuciya.
D'ago kanta yayi yana kallon innocent face d'in ta yace
"Mufidah nasan ba bacci kike ba ki bud'e idon ki ki kalle ni, ki fad'a min matsalar ki please "
Wasu hawayen su suka sake xubo wa cikin xuciyar tana cewa Musaddiq babu abin da yake damuna sai halin da kake ciki ciwon da sona ya haddasa maka shi ya sanya ni shiga cikin wannan yanayin, a fili kasa magana tayi saboda yanda bakin ta yayi mata nauyi sosai.
Muryar shi kamar xai fashe da kuka yace
"na rok'e ki Mufidah ki sanar da ni "
"daddy mai ya samu mami na? "
Yaji muryar Afnan cikin tsakar kanshi, wayance wa yayi da k'ak'alo murmishin yak'e yace
"Afnan babu abin da ya sami mamin ki bacci take yi "
"toh daddy I'm hungry "
Ta k'arasa fad'i tana yatsina fuska, ya rasa yanda zai yi Afnan zai je ya bawa abinci ko kula ya tsaya kula da Mufidah, ganin Afnan zata fara yi mishi kuka ya sanya shi ajiye Mufidah suka fito parlour yana waigen Mufidah.
Sai da ya zuba wa Afnan abinci a plate tare da drink a cup ya zaunar tare da kunna mata tv channel d'in cartoon ya ce
"babyn daddy kiyi xaman ki anan idan kin gama cin abincin ki kalli cartoon yanxu xamu fito da mamin ki, kin ji? "
Afnan wadda take kai spoon na abinci baki ta gid'a mishi kanta tana murmishi, shima murmishin yayi yana jan kumatun ta na gefen dama kafin kuma ya wuce bedroom d'in Mufidah da sauri.
A yanda take lokacin da ya fita a hka ya same ta da sauri ya k'arasa inda take tare da hawa saman bed d'in ya yaye blanket d'in da ta rufa tare da d'ago ta gaba d'ayan ta ya zaunar da ita cikin jikin shi yana tatta6a jikin tare da duba ta don ya fahimci abin da yake damun ta.
Ganin bashi da kayan aiki cikin bedroom d'in ta yasa shi daukan ta ya nufi bedroom d'in shi da ita, yana bud'e kofar wani sassayan K'amshi mai dad'i ya fara ziyartar hancin kafin ya shimfid'e ta saman bed d'in shi da yasha gyara.
Jiki na 6ari ya fara duba ta bai ga wani babban ciwo fiye da damuwa tare da kukan da tayi ne ya janyo mata xaxxa6in da ciwon kai, zuba mata ido yayi yana kallon ta cikin xuciyar shi yana tunanin wacce irin damuwa ce ta haddasa mata ciwo hka, gashi tak'i magana kuma har yanzu idon ta a rufe suke sai dai hawayen da yake zubo mata.
Nan ya fara lalla6a ta don ta fad'a mishi abin da yake damun ta amman kamar da dutse yake magana, ganin baza ta kula shi ba yasa shi tashi bathroom ya nufa ya samu wani bowl mai kyau ya tari ruwa a ciki sannan ya d'auki towel k'arami ya fito xuwa inda take.
Ajiye bowl d'in yayi saman bedside sannan ya fara kok'arin zame kayan jikin ta, ai kuwa da sauri ta mik'e zaune tare da bud'e idon ta tana rarraba su kamar wata mara gaskiya hkan da tayi ba k'aramin sanya Musaddiq dariya yayi ba amman sai ya gimtse ta.
Ya cigaba da cire wa cikin tsoro Mufidah tace
"Musaddiq mene haka kuma? "
D'an murmishi yayi tare da cewa "jikin shi ya d'auki xafi da yawa ina son xan goga miki ruwa ko xafin ya ragu "
Cikin rawar murya tace
"ni.... ni gas.....gaskiya a'a zai daina "
Wani murmishin gefen kumatu yayi tare da girgixa kanshi yace
"bazai yiwu ba Mufidah idan baki damu da rashin lafiyar ki ba wasu sun damu "
D'ago kanta tayi da sauri ta kalle shi cikin mamaki wato bama xai ce ya damu ba sai wasu da akwai aiki a gaban ta kuwa wajen tankwara zuciyar Musaddiq ya sakko su gyara zaman auren su.
Gira ya d'aga mata kafin ya fara cire kayan runtse idon ta tayi gam har ya gama cire wa sai iya underwears kawai ya bar mata, sake runtse idon ta tare da k'ank'ame jikin ta tana jiran saukar ruwa a jikin ta amman taji shiru har tsayin wasu en mintuna.
A hankali ta fara bud'e idanun ta suka had'a ido kuwa sake rufe su tayi da sauri ganin ashe zuba mata ido yayi yana kallon ta son ranshi wata irin kunya ce ta gama lullu6e Mufidah.
Musaddiq wanda gaba d'ayan shi ya fara fita hayyacin shi ya kasa dauke idon shi akanta, gaba d'aya idon shi sun fara canja launi ga wani abu da yake ji yana tsirga mishi daga cikin brain d'in shi xuwa gangar jikin shi, wani tunani na daban ya fad'a 6angare guda kuma wani mugun son Mufidah ne yake dad'a ratsa zuciyar shi.
Dakyar ya iya saita kanshi ya fara goge mata jikin nata had'uwar tattausar fatar jikin shi da nashi, shi ya sake haddasa Musaddiq shiga wani mayuwacin hali wanda ba don yana kok'arin danne abin da yake ji ba da xa'a yi mai gaba d'aya a yanxu.
Bayan ya gama ne ya mayar mata da kayan sannan ya had'a mata tea a baki ya dunga bata har ta d'an sha tukunna yayi mata allura wanda yasha fama da ita kafin ta tsaya yayi mata, hka magani ma dakyar ta sha sannan ya kwantar da ita cikin jikin shi har bacci ya dauke ta mai nauyi tana jikin shi yana aikin kallon ta lokaci zuwa lokaci yana sakin murmishi shi kad'ai yasan zuciyar shi yanzu ta samu nutsuwa tunda ta sami abin da take muradin so.............
Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻ *£xclusive Writers Forum*
*Likes nd comment's fb page*👇🏻
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com
*PAGE 54*
Zame ta yayi daga cikin jikin shi ya tare da kwantar da ita kafin ya tashi ya fito xuwa parlour wurin Afnan sai ya tarar ta 6ingire tana shan baccin ta kan carpet, d'an murmishi yayi tare da daukan ta ya kaita bedroom d'in Mufidah ya kwantar da ita, sannan ya fito ya koma d'akin shi.
Kwanciya shima yayi kusa da Mufidah ya rungumo ta cikin jikin shi k'am kamar wanda xa'a kwace mishi ita zuciyar shi fal farinciki wai yau shine rungume da Mufidah wadda ya fitar da ran samun ta har abada sai gashi Allah yayi ikon shi ya same ta a lokacin da bai ta6a zato ba.
Kallon beautiful face d'in ta yake yana hashashen wasu abubuwa cikin zuciyar shi cikin nishad'i yayi kissing lip's d'in ta yana nan kwance yana faman tunani har bacci mai dad'i yayi awon gaba da shi.
*After 1 hour*
A hankali Mufidah ta fara bud'e idanun ta har ta gama bud'e su gaba d'aya ba inda idon ta ya sauka sai kan kyakkyawar face d'in Musaddiq yana baccin shi hankali kwance, tamkar ba bacci yake ba kamar irin lumshe idanun shi yayi.
Wani smiling tayi kaunar shi tana ratsa ilahirin zuciyar ta da jijiyoyin jikin ta, wani mugun son shi ne yake shiga cikin zuciyar, hannun ta ta sanya saman fuskar shi tana kyakkyawan sajen face d'in shi mai matuk'ar kyau da tsari ga laushi har ta kai saman lip's d'in shi tana zagaye su da 'yan yatsun ta, tana murmishi ita d'aya.
Ba zato taga Musaddiq ya bud'e idon shi ya sauke su kan fuskar ta, suka had'a ido yana mata wani irin kallo mai tattare da ma'anoni daban daban.
"wayyo Allah nah, Allah yasa bai ga abin da nake mishi ba?"
Cewar Mufidah cikin zuciyar ta ga wata azababbiyar kunyar shi da ta rufe, d'aga mata gira yayi da sauri ta sunkuyar da kanta tana mai murmishin jin kunya.
'Yar dariya yayi kad'an yana sake hugging d'in ta a kunne ya rad'a mata
"Mamin Afnan ya kika bari ki cigaba kinsan kuwa yanda nake ji kuwa? "
Nok'e kai tayi tana cusa fuskar ta cikin chest d'in shi tana girgixa kai tare da cewa
"ni fa ba abin da nake maka "
Cakulculi ya fara yi mata tana dariya tare da kok'arin kwace kanta daga jikin shi but ta kasa hkan, cikin shashshak'ar dariya tana jan numfashi tace
"Musaddiq ka bari please".
Yana dariya yace
"ai kuwa sai na rama yarinya tun da kika tashe ni a bacci ko na kirawo Afnan mu had'u mu danne ki kowa ya za6i inda yake so ya ciza "
"wayyo Allah kayi hak'uri baxan k'ara ba "
Ta fad'i cikin yanayin shagwa6a, nok'e kafad'a yayi tare da cewa
"nak'i wayon yarinya "
Nan ya cigaba da yi mata cakulculin sai da yaga tana kok'arin shid'e mishi ya barta tana mai da numfashi, ido suka k'ura wa junan su cikin wani irin shauk'in son junan su suke ke kallon junan su kowanne da irin abin da yake sak'awa cikin zuciyar.
Musaddiq kasa jure wa yayi sai da ya had'a lip's d'in shi da nata ya fara kissing a nutse yana yawo da hannun shi cikin jikin ta, saukar lip's d'in shi a nata ne yasa ta lumshe idanun ta tare da sakin wata ajiyar zuciya ya gama saukar mata da kasala.
Sun d'auki wajen tsayin 6 minutes a hka kafin Musaddiq a hankali ya zame jikin shi ya tashi kallon yayi da idanun shi da suka yi ja yace
"tashi muyi wanka lokacin sallah yayi ".
Mufidah wadda tun da ya tashi suka had'a ta dukunkune kanta cikin kafafun ta tana murmishin jin kunya, tana jin furucin shi ta yunkura ta sauka daga kan bed d'in kafin ya ankare ta kwasa da gudu ta bar cikin d'akin.
Ba k'aramin dariya ta bashi ba amman ya danne dariyar yayi murmishi yana girgixa kai yace
"huh... Mufidah yarintar ki tana birge ni ina son ki da yawa Allah yasa ke ma ki soni koda rabin son da nake miki ne "
Yana gama fad'in hka ya wuce cikin bathroom ya fara wanka.
Mufidah kuwa tana k'arasa wa cikin d'aki ta rufe kofar tare da jingina a jikin kofar tana dafe kirjin ta sai lokacin gudun da tayi ya bata dariya nan ta shiga yin dariyar.
"Mamee lafia kike dariya ke d'aya? "
Taji saukar muryar Afnan a kusa da ita, hannu ta sanya ta d'aga Afnan tana juyi da ita cikin d'akin suna dariya cikin farinciki da nishad'i kafin musamman ma Mufidah, ta sauke ta k'asa ta sanya hannun ta taja kumatun ta cikin dariya tace
"ni da wannan rigimammen daddyn naki Afnan "
Zaro ido Afnan tayi tana kad'a harshen ta tace
"lalala Mamee daddyn nawa ne rigimamme? "
"Ehh mana ya cika rigima kamar wani boy "
Ai kuwa Afnan ta fara tuntsura dariya saboda boy d'in da Mufidah ta kirawo Musaddiq dashi, tana rik'e ha6a kamar wata babba tace
"Mamee daddyn nawa ne boy ai kuwa xan fad'a mishi "
"ba sai kin fad'a min ba Afnan naji da kunne na "
Da sauri Mufidah ta jiyo suka had'a ido da Musaddiq yana sakar mata murmishi, da gudu ta fad'a toilet tare da sanya key tana murmishi ita d'aya kafin ta fara wanka.
Bayan ta gama wankan ne ta d'aura alwala ta fito, ganin basa d'akin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 23