so mu tafi habibty"
"zo ka d'auke ni idan kana son mu tafi "
"kai babyna agajiye nake, gashi kin k'ara nauyi sosai "
"toh shikenan tun da baza ka iya ba, naga kuma babyn ka ne ya samin nauyin tun da ba haka nake ba",ta fad'a cikin shagwa6a .
'Yar dariya yayi kafin ya k'arasa inda take yana cewa
"Sorry 'yammata na, duk nauyin da kika yi Musaddiq d'in ki bazai kasa d'aukar ki ba "
Hannun shi ya sanya tare da taimaka mata ta tashi tsaye, sannan ya d'auke ta cak suka fita daga side d'in Mumy zuwa nasu.
Yana shiga cikin parlourn wani k'amshin turare mai dad'i ya ziyarci hancin shi, ko'ina tsaf dashi cikin zuciyar shi yana godiya ga Allah da ya azurta mishi Mufidah matsayin matar shi, duk da girman cikin da yake jikin ta hakan bai hana ta tsaftace ko'ina ba, duk buk'atar da yazo mata da shi zata kar6e ta ko a fuskar shi baza ta nuna mishi rashin jin dad'in hakan ba, ko da kuwa bata so, shi yasa kullum sonta yake k'ara shiga cikin zuciyar shi.
Bai ajiye ta a ko'ina ba sai a bathroom, kallon ta yayi sai yaga tayi murmishi idan da sabo yaci ace ta saba da hakan, tun da kullum ya dawo daga office idan zai yi wanka tare suke yi, ba ma iya na lokacin ba kullum ma haka suke abin su.
Bayan sun gama wankan sun fito ne, kowanne d'aure da towel akan bed ya zaunar da Mufidah tare da zama kusa da ita yace
"habibty yaushe zamu fara zuwa siyayyan kayan babyn mu? "
Kallon shi take cikin mamaki kafin tace
"Sweetheart ina ce last week ka tak'ura wa Mumy taje dubai ta siyo komai"
Murmishi yayi tare da cewa
"Duk da haka baby na, ina son mu je ki za6i ra'ayin ki "
Girgiza kai tayi tana jan kunnen shi d'aya da hannun ta tace
"Wannan kunnen baya jin abin da nace mishi yau da safe, ba haka nace mishi a bar maganar nan ba "
Yatsina fuska yayi tare da cewa
"Wash habibty it hurts fah, zan rama nima "
Dariya ya bata ganin yanda yake sosa wurin da ta rik'e, kafin tace
"sai dai ka rame d'an samari "
Zaro ido yayi kafin yace "tabd'ijam baby nine d'an samari? "
Cikin dariyar tsokana tace "Ehh mana "
Janyo ta yayi cikin jikin shi yana gyara mata gashin kanta tare da cewa
"lallai baby kin rainani da yawa, ni yanzu daddy ne ina da Afnan ga shi kin kusa haifa min new baby's "
Ya k'arasa fad'i yana shafa cikin ta tare da kissing d'in shi.
"baby's naji kace ba?"
Lumshe idanun shi yayi tare da bud'e su yace
"Yes of course insha Allah baby's zaki haifa min "
Kwa6e fuska tayi tace
"Wayyo Musaddiq ba kasan yanda ake shan wahalar haihu ba ne "
Dariya ta bashi ganin yanda tayi, cikin lalla6a ta yace
"Haba wacce wahala kuma baby, lafiya zaki haihu mybe ma kina bacci zan tashe ki nace kin haifa mana baby "
Sosai maganar shi ta bata dariya, nan ta shiga yin dariyar shima ya taya ta, tsaya wa yayi da tashi dariya ya zuba mata ido yana kallon ta cikin wata irin sha'awar ta,
"I luv u Mufidah "
Ya furta hakan cikin muryar shauk'in ta,
"I luv u too "
Mufidah ta mayar mishi da martanin maganar.
Sake matse ta yayi cikin jikin shi yana lalubar bakin ta, kissing d'in ta ya fara yi, nan fah ya fara aika mata da zafafan kalamai tare da sak'onnin shi zuwa gare ta, cikin en mintuna suka fara shiga wata duniyar ta daban.
*** *** ***
Cikin Mufidah ya shiga watanni na 8 ya girma sosai, duk ta bi ta kumbura ga girman ciki, zama dakyar tashi dakyar don wani lokacin sai an taimaka da tashi tsaye.
Ba k'aramin tausaya mata Musaddiq dasu Mumy suke ba, kullum cikin bata kula wa da addu'ar Allah ya sauke ta lafiya duk wani masoyin ta yake, don cikin yafi na Afnan girma sosai kuma tafi shan wahala.
Gaba d'aya ta k'agu taga ta haihu ko ta huta da wannan wahalar da take faman sha, wani lokacin ita take k'arfafa wa Musaddiq gwiwa ganin duk yanda ya karaya ganin yanda take shan wahala.
Sam hankalin shi yanzu ba'a kwance yake ba, hospital d'in ma yanzu bai fiye zuwa ba sosai, ko yaje ma hankalin shi yana gida, haka zai dawo gidan ya sata a gaba yayi ta kallon ta yana tambayar ta ko akwai inda yake mata ciwo, ko tana son wani abin.
A haka lokaci yana tafiya, rana ku na wuce wa har cikin Mufidah ya shiga wata na tara da sati uku, ta kusan cinye wata na goma shiru babu alamar haihuwa, sai dai ciwon mara da baya da take yi, wannan kuma daman idan ciki ya tsufa haka zaka yi ta fama har zuwa lokacin da za'a haihu lafiya.
Musaddiq gajiya yayi da ganin yanda take shan wahala duk ta rame sai kumburi da k'aton ciki da farin da ta k'ara yi, ya fad'a wa Mumy kawai ayi mata cs a cire cikin, nan Mumy tak'i yarda sam saboda duk wani gwaje gwaje da aka yi mata an tabbatar lafia qlau take da babyn, sai dai kawai lokacin haihuwar ne da bai zo ba.
Sai da cikin Mufidah ya shiga wata 10 dai dai, a wata safiyar monday ta tashi da nak'uda, nan da nan suka wuce hospital d'in Dr Musaddiq, kai tsaye labour room na daban aka wuce da ita.
Musaddiq kasa fita yayi daga room d'in yana rik'e da ita a jikin shi, ga Doctor Aishat nd nurse Billy ladan suna kanta lol, duk wani taimakon da ya kamata su yi mata suna mata.
Mufidah wahala dai tasha a wannan lokacin, don sai ta ga haihuwar Afnan sauk'i gare ta fiye da wannan, Musaddiq har da hawayen tausayin habibty d'in shi, tun safe ake fama har zuwa daf da mangarib sannan Allah ya sauke ta lafiya, ta haihu beautiful baby's boy's d'in ta, masu kama da Musaddiq like father like son.
Tuni Musaddiq mai hawaye ya koma yin dariyar farinciki, bayan angama gyara su tsaf ne an kaisu d'akin hutu, tukunna su Mumy suka samu ganin su.
Kowanne ka kalle shi yana cikin farinciki da murna da wannan k'aruwar da aka samu ta yara biyu maza, Musaddiq wanda baki yak'i rufuwa yana zaune kusa da Mufidah da take baccin wahalar da ta gama sha.
Dr Muh'd wanda ya ke d'auke da d'ayan babyn ya kalli Musaddiq yace
"lover boy sai a daina kukan tausayi a koma na farinciki "
Gaba d'aya aka kwashe da dariya, yayin da Musaddiq ya harari Muh'd, sai washe gari da safe aka sallame su zuwa gida, kafin su k'araso tuni 'yan uwa da abokanan arzik'i sun zo don taya su murnar samun kyautar Allah wanda kud'in ka ko mulkin ka bazai sa ka samu ba, sai dai idan Allah ya baka, Allah ya bamu yara masu albarka ya kare mana su tare da basa ilimi mai amfani, ya tarbiyyantar mana dasu irin tarbiyyar addinin islam, Amin.
Mumy dawo da Mufidah tayi side d'in ta domin bata kula sosai, tana kuma taya ta rainon 'yan biyu don rainon su sai da taimako, hakan kuwa ba k'aramin tak'ura wa Musaddiq aka yi ba, shima sai ya tattara ya dawo side d'in cikin d'akin shi na da, Afnan sai rawar kai ake an samu k'anne har biyu.
Daren ranar Musaddiq ya shiga d'akin Mufidah ya tarar da ita kwance kan bed, ga yaran kwance kusa da ita suna baccin su hankali kwance, k'arasa wa yayi ya zauna kusa da k'afafun ta yana cewa
"Babyna kin yi bacci ne? "
Tashi tayi tana murmishi tare da koma wa kusa da shi ta kwanta a cikin jikin shi, k'ara gyara mata kwanciyar yayi a jikin shi yanda zata fi jin dad'i sosai,
"ban yi bacci ba, ina jiran ka ne don nasan zaka shigo "
Mufidah ta bashi amsa, wani dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar shi, kullum Mufidah k'ara shiga zuciyar shi take, tana bashi duk wata kulawa da ta kamata, shafa fuskar ta yayi da hannun shi yace
"Ngde da wannan kulawar take habibty "
Kafin ya cigaba da cewa
"wanne suna kike ganin zamu sanya wa yaran mu? "
D'an murmishi tayi tana cewa
"Ni ban da wani za6i sai naka, duk sunan da ka sanya musu yayi min "
Wani murmishin jin dad'in abin da tace yayi, sake rungume ta yayi a jikin shi yana shak'ar daddad'an k'amshin turaren yace
"sunan da nake son sanya musu shine, babban zai ci sunan Abubakar sadeeq d'ayan kuma sunan Muh'd ko ya kika gani idan bai yi ba sai ki fad'i wanda kike so"
Wasu hawaye masu zafi ne suka zubo wa Mufidah, tabbas daman kudurta cikin zuciyar ta idan Allah yasa ta samu d'a namiji sunan Sadeeq zata mayar shi, sai gashi Musaddiq ma hakan ne cikin zuciyar shi.
D'ago kanta yayi yana girgiza kanshi tare da sanya hannun shi yana goge mata hawayen fuskar ta yace
"Kiyi hak'uri Mufidah addu'a kad'ai zaki na yiwa Yah sadeeq, don ita kad'ai ce zamu yi mishi mu nuna kaunar shi a gare mu, bana son ganin kukan ki, ki daina please"
Cikin sanyin murya yake maganar, gid'a kanta tayi kafin tace
"na daina, Allah ya jik'an shi da rahma "
"Amin "
Ya amsa, ganin ta shiga damuwa ne yasa shi rarrashin ta har ta dawo normal, kafin su cigaba da hirar har zuwa lokacin da Mumy tazo ta kore shi, don ya bar ta ta huta, haka ya tafi yana mitar hana shi sake wa da matar shi da 'ya'yan shi.
Haka aka cigaba da hidindimu har zuwa ranar suna, lokacin dasu Mumy da Muh'd suka ji sunan yaran sosai sun yi farinciki ba k'arami ba, don sunan da Musaddiq ya sanya musu yayi dai dai, sai fatan Allah yasa su gado masu sunan.
Muh'd a daren sunan ya shirya dinner sosai, ba wanda ya sani tsakanin Musaddiq da Mufidah sai da daren hatta kayan da za su yi amfani dashi ya tanadar musu, Musaddiq sam bai yi musu ba suka shirya suka tafi tare da twin's d'in su.
Wow gaskiya wurin dinner d'in ba k'aramin had'u wa yayi ba, don mutane sosai Muh'd yayi gayyata, har da en Exclusive writer forum, ga en group d'ina Aishat A Muh'd fan's, can na hango momma na ta kaina (Aunty maijiddah) tare da twin's d'in ta, mutane sun yi k'ara wajen zuwa, ga fan's d'in Musaddiq da Mufidah (Musfeedah) nan duk sun zo na hango su gaba d'ayan su a wurin, sun sha gayu sai zuba iyaye ake, lol.
Anci ansha anyi musu addu'ar Allah ya raya su, kafin kuma a tashi kowa ya kama gaban shi, Mufidah kuwa ta cika fam da fushi da kishi saboda yanda 'yammata suka dunga kula wa Musaddiq suna wani shishshige mishi, dakyar ya shawo kan kayar shi suka shirya, don sam bazai iya zaman second's ba da kwanciyar hankali ba idan Mufidah na fushi dashi.
Sun cigaba da rainon twins d'in su har zuwa lokacin da suka yi arba'in, twin's sun yi wayo sosai, sun k'ara girma gasu da wayo yaran, dakyar Musaddiq ya yarda taje gidan su kwana uku tayi ta dawo shima kwanakin ukun kusan dashi aka yi kwanan, don zaman shi yayi ya kasa tafiya ko kunyar su Umma baya yi, Mumy dai taga rashin kunya kam ganin yanda Musaddiq ya tafi gidan surukai kwana................
Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻ *£xclusive Writers Forum*
*Likes nd comment's fb page*👇🏻
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com
_Wannan shafin kyauta ne da duk wani masoyina da masoyin wannan littafin, ina muku fatan alkhairi_
*K'ARSHE* (LAST PAGE)
*PAGE 60*
Suna dawo ne ko kwana d'aya basu k'ara yi a side d'in Mumy suka wuce nasu part d'in, daman tuni Mumy ta gyara d'iyar ta ta don ya taga yanda d'an nata yake rawar jiki, haka ma Umma ta tsaya tsayin daka wajen gyara ta sosai, tanan 6angaren Mufidah bata da matsala.
Ansha soyayya sosai a wannan daren tsakanin Mufidah da Musaddiq, sun kasance cikin farinciki sosai, ji suke tamkar don su aka hallaci duniyar saboda tsantsar farincikin da suka tsinci kan su a ciki, sun yi baccin su cikin kwanciyar hankali.
Washe gari da safe Mufidah ce ta fara kok'arin tashi daga bacci da safe, bayan ta tashin ne ta fara kok'arin gyara gidan, cikin en mintuna ta tsaftace ko'ina ta sanya turaren wuta masu k'amshi tare da air freshener, tana gama wa ta wuce bedroom wanka ta fara yi wa twin's ta gyara musu cikin su tsaf, sannan ta basu abincin su suka sha, bayan ta d'ora su a kafad'a ne tana d'an shafa bayan su har sai da suka yi gyatsa tukunna ta kwantar da su.
Toilet ta wuce wanka tayi sannan ta fito ta gyara jikin ta tare da yin light make up, wata atampha ta dauko tare ta sanya d'inkin riga da siket ne sun zauna a jikin ta sosai, tayi kyau tana cikin fesa perfumes ne Musaddiq ya shigo d'akin ko wanka bai yi ba sleeping dress ne kawai a jikin shi.
Rungume ta yayi ta baya tare da kar6ar turaren hannun ta yana cigaba da fesa mata bayan ya gama ne ya ajiye akan dressing mirror, sannan ya cusa kanshi tsakanin wuyan ta yana shak'ar k'amshin daddad'an turaren ta har wani ajiyar zuciya ya ke saki.
"Baby nah shine kika gudu koh, kika yiwa twin's wanka kema kika yi, aka mance da ni "
Murmishi ta saki cikin k'ara kaunar mijin nata tace "Haba nawan ni na isa, yanzu zan zo na shirya ka, yau akwai zuwa hospital "
D'an yatsina fuska yayi tare da cewa " ni yau hutu nake ba inda zan je"
Cikin mamakin abin da yace d'ago kanta suna kallon face d'in junan su tace
"Saboda me? "
Hannun ta ya rik'o yana shafa su a hankali yace
"dalili kike son sani uhm"
Bai k'arasa fad'i ba ya kashe mata ido d'aya, tuni ta fuskan ci abin da yake nufi, d'an dukan wasa ta kai mishi a gefen kafad'ar shi ya goce yana mata dariya, nan suka fara wasannin su suna ta dariya daga k'arshe suka zube kan bed kusa da twin's suna mayar da numfashi, kafin daga bisa ni ta raka shi toilet yayi wanka, ta taimaka mishi ya shirya, sannan suka zauna yiwa twin's wasa.
A ranar Musaddiq ba inda ya fita sai zuwa gaida su Mumy da suka je, acan ma suka yi breakfast suna gama wa,shima basu wani jima ba ya tak'ura mata suka tafi side d'in su aka bar Mumy da twin's, daman
Afnan ta tafi school.
*** *** ***
*AFTER 7 YEAR'S*
A cikin wad'annan shekaru da wuce zaman lafiya sosai ake tsakanin Mufidah da Musaddiq, haka ma ta 6angaren Mumy babu abin da ya sauya daga soyayyar da take nuna wa Mufidah.
Haka amintakar da ke tsakanin Musaddiq da Muh'd kullum sake kaunar junan su suke, ta 6angaren Mufidah da Nabilah tare da Nafisat su ma kawancen su sosai suke yi sun zama tamkar 'yan uwa.
A cikin wad'annan shekaru Nabilah ta sake haihuwar yara biyu, sun ci sunan Umma da Abba, haka Nafisat matar Muh'd ita ma ta sake haihuwar wasu yaran har guda biyu duk mata.
Mufidah ma ta sake haihuwar namiji yaci sunan daddy ga kuma wani tsohon cikin da yake jikin ta haihuwa yau ko gobe.
Musaddiq da Mufidah kullum k'ara kaunar junan su suke, tattalin juna da kulawar da suke yiwa junan su shi yayi musu jagora wajen shimfid'a kyakkyawar rayuwar su mai cike da jin dad'i da kwanciyar hankali.
Ga kuma kula da yaran su da suke, suna kok'arin gaske wajen basu tarbiyya tare da basu ilimi na addini dana boko, yaran sun girma gashi sun taso cikin soyayyar iyayen su da kakannin su ta kowanne 6angare, amman duk da wannan soyayyar da suke nuna musu hakan bai hana su basu tarbiyya mai kyau ba.
A cikin wani daren alhamis Allah ya sauki Mufidah lafiya, ta haifi baby girl d'in ta, farinciki wajen Musaddiq kamar bai ta6a samun 'ya'ya ba, daman burin shi kenan ya samu mace mai kama da Mufidah, sai gashi duk cikin yaran nan nata ita ce mai kama da ita sosai.
Ansha shagalin suna sosai an kashe kud'i, inda yarinya taci sunan ta Nauwara, haka Mufidah ta cigaba da kula da 'ya'yan ta tare da taimakon jarumin mijin ta Musaddiq, wanda a kullum cikin bata dukkanin wata kula wa yake, baya gajiya da hidimar Mufidah kamar yanda ita ma bata gajiya da tashi hidimar.
Duk hausawa sunce zo mu zauna zo mu sa6a, amman tsakanin Mufidah da Musaddiq akwai fahimtar juna sosai a tsakanin su, duk da wani lokacin daman sai anyi hak'uri da juna, domin ance ko tsakanin harshe da hak'ori ana sa6awa, ko da sun yi fad'a a tsakanin su baya kaiwa wani tsawon lokaci ba tare da sun yi shirya kan su ba don basa jure yin fushi tsakanin su.
*** *** ***
Misalin k'arfe 8 na dare bayan an idar da sallahr ishsha ne, Musaddiq da twin's tare da lil Daddy suka shigo parlourn da sallama dawowar su daga masallaci kenan.
Hannun su d'auke da robar ice cream da chocolate masu dad'i, saboda sun biya yiwa Mumy sallama sai da safe shine ta basu, Afnan ce zaune a parlourn tana rik'e da Nauwara tana yi mata wasa ta amsa sallamar su cikin nutsuwa.
Gaida Daddy Musaddiq tayi cikin ladabi da girmama wa, yayin da k'annan nata suka gaida ita suma, zama suka yi ana hira cikin so da kaunar junan nasu.
Mufidah ta fito parlourn cikin wata gown ta atampha d'inkin yayi mata kyau sosai, k'amshin turaren ta da Musaddiq ya ji shi ya sashi lumshe idanun shi yana saukar da ajiyar zuciya a hankali, kafin ya ware idon shi kan Mufidah sanyayen murmishi suka sakarwa junan su, da hannu yayi mata alamar tayi kyau ta amsa mishi da ido ta gode.
"Oya ku tasu aci abinci a kwanta gobe da school "
Mufidah ta furta hakan ganin yanda yanayin mutumin nata ya canja, tashi suka yi gaba d'ayan su suka nufi dining table suka zauna, Mufidah tayi serving d'in su.
Nan suka yi bismillah cikin nutsuwa suka fara cin abincin su, ba wanda yake magana a cikin su sai dai Musaddiq da Mufidah da suke aikawa junan su murmishi tare da wani irin kallo wanda su kad'ai suka san ma'anar shi.
Bayan sun gama ne Afnan tayi musu sallama ta tafi side d'in Mumy da yake daman acan take sai dai kusan yini take a part d'in Mufidah, Musaddiq bai barta ta tafi ita d'aya ba saboda dare ya d'an yi don 9 ta kusa, yana rik'e da hannun ta har suka zo part d'in Mumy sannan ya bata peck a kumatun ta yace
"Good nyt sweet dgter and sweet dreams "
Cikin murmishi tace
"Okay daddy good night "
Daga haka ta wuce ciki shi kuma ya juyo ya dawo, zuciyar cike da kaunar Afnan yarinyar da kullum kamannin ta da Yah sadeeq yake k'ara fito wa, wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mishi tare da furta
"Allah ya jik'an ka Yah sadeeq, ina cikin kewar ka nasan har na mutu bazan dai na zubar da hawayen rashin ka ba "
Kok'arin saita kanshi yayi don kada Mufidah ta fahimci halin da ya shiga, lokacin da ya shiga part d'in nasu ya rufe ko'ina tare da kashe hasken ko'ina, sannan ya lek'a bedroom d'in yaran shi ya tarar sun yi bacci, murmishi ya saki yasan wannan duk aikin Mufidah ne, wajen sa yara bacci da wuri bin su yayi d'aya bayan d'aya ya basu peck sannan ya k'ara yi musu addu'a ya kashe hasken d'akin, tukunna ya fito yana rufe musu kofa.
Bedroom d'in shi ya wuce ya tarar da Nauwara kwance kan k'aramin bed d'in su na yara tayi bacci abin ta, ita ma kissing d'in ta yayi, sannan ya wuce toilet don yasan Mufidah na can tana had'a musu ruwan wanka.
Bayan sun yi wanka sun fito ne, suka kwanta kan bed tare da rage hasken d'akin, cikin wata irin muryar shauk'i Musaddiq ya ce
"ina son ki Mufidah, kullum son ki k'ara ratsa zuciya ta yake, ina miki son da baki na bazai iya furta miki adadin shi ba, ina alfahari da ke matsayin mata ta"
Cikin sanyin murya tace
"Nima a kullum cikin gode wa Allah nake da ya azurta ni da samun managarcin jarumin namiji kamar ka, ina son ka Musaddiq with all my heart, i luv u so much sweetie darling "
Sake k'ank'ame ta yayi a jikin shi tare da had'a bakin su waje d'aya ya fara bata wani zafaffen sak'onnin shi mai mata wuyar fassara, kullum cikin gode wa Allah take da ya bata Musaddiq, da fari Allah ya bata Sadeeq salihin mutum mara son hayaniya babu ruwan shi, Allah ya d'auki abin shi daga k'arshe ya sake bata wani mijin abin alfahari mai son ta tsakani da Allah, ga nutsatstsun yara da ya bata, shi yasa kullum cikin gode mishi da take da tarin ni'imomin da yayi mata take.
Bayan komai ya kammala sun yi wanka suka kwanta rungume da junan su kowanne yana fad'a wa d'an uwan shi irin yanda yake son shi, kafin daga k'arshe bacci mai dad'i yayi awon gaba da su.
*_ASUBA TA GARI MUSFEEDAH_*
*ALLAHAMDULILLAH*
_K'ARSHE_
*DUKKAN GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH (S. W. A), DA YA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFIN LAFIA, TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU K'ARA TABBATA GA ANNABIN MU,SHUGABAN MU ANNABI MUHAMMAD (S. A. W), KUSKUREN DA SUKE CIKI ALLAH YA YAFE MIN, FAD'AKARWAR DAKE CIKI ALLAH YA BAMU LADAN GABA D'AYA*
*NOTE* _wannan littafin nayi shine don fad'akarwa da nishad'antar wa, kuma k'irk'iran labari ne, abin da yake ciki mai kyau da amfani ayi aiki dashi, mara kyan kuma a watsar dashi_
*KE TA DABAN CE*
_My sweet sadeey ke ta dabance cikin zuciya ta, baki na bazai iya furta miki yanda kike a wuri na, fatana shine Allah ya bar xumunci mu kasance tare har abada,Amin._
*INA YIN KU IRIN SOSAI D'IN NAN ADMINS OF EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
_Aishan umma_
_Dgter ummiey xeey_
_Meelat dear_
_Aishat A Muh'd_
Allah ya bar mu tare 4 sister for ever, Amin.
*GODIYA DA FATAN ALKHAIRI GARE KU SISTER'S NA EXCLUSIVE WRITERS FORUM, HOME OF PEACE HONOUR AND SUPER WRITERS, INA SON KU IRIN SOSAI D'IN NAN WANDA BAKI BA ZAI IYA FAD'A BA, ALLAH YA BAR MU TARE EN UWA*
*INA ALFAHARI DA KU*
_My momma (Aunty maijiddah)_
_My billy ladan_
_My biebie deee_
_My Amnoor dear_
_My queen mermue_
_My zahra ( sister d'in halilos)_
_My halilos_
_zee yabour_
_My Asy khaleel_
_Namecy Ayusha_
_Namcey Aysha Ali Garkuwa_
_Miss zahra mansur_
_ummu safwan_
_khadija neenah cool ke ta dabance_
_Aunty fauxah_
Kaiii gaskiya baxan iya rubuto ku gaba d'aya saboda yawan da kuke dashi, amman ku sani Aishat A Muh'd na matuk'ar kaunar ku da alfahari da ku,Allah ya bar xumunci ina muku fatan alkhairi.
Jinjinar ban girma gare ku en cikin *IDON MIKIYA WRITER'S ASSO*, ina yin ku guy's Allah ya bar xumunci.
*GARE KU MASOYA NA*
_kune abin alfahari na, ina son ku duk inda kuke Allah ya bar mu tare musamman en grp d'in Aishat A Muh'd fan's ina yin sosai guy's_
*GROUP'S D'IN DA NAKE BAZAN IYA LISSAFO KU BA, AMMAN NASAN KU MASOYA NA NE, INA MUTUM FATAN ALKHAIRI TARE DA GODIYA GARE KU, MUSAMMAN ADMINS D'IN SU*.
*_ina kuke masoya na ina muku albishir d'in new nvl d'ina mai zuwa nan babu dad'e insha Allah_*
Aishat A Muh'd ✍🏻
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 23