Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ae kuwa nan ya duba tare da tabbatar wa na roba ne kamar yanda ya fad'i . A fusace musaddiq ya nufi wurin da Yah sadeeq yake yana tuntsira dariya ganin hka yasa sadeeq ya fara gudu don hka shi ma musaddiq yabi shi a baya nan suka fara gudu cikin d'akin suna tattaka kujerun d'akin da kan bed d'in nan suka dunga xagaye d'akin sadeeq yana yiwa musaddiq dariya don ganin yanda yake huci da hka suka fice daga d'akin suna gudu kamar wasu yara k'anana. Mumy tana 6angaren dinning table tana shirya kan table da kayan breakfast ta ga Yah sadeeq ya fito daga bedroom d'in musaddiq da gudu sakin baki tayi tana kallon su bata ankara ba taji sadeeq ya xagayo ta bayanta yana cewa "Mumy Ki taimake ni na tsokano likita " Cikin dariyar manya Mumy tace "ina ruwa na kai dashi Idan yayi maka allura ba ruwa na " Yana k'araso wa kusa da mumy ta rik'e shi tare da cewa "d'an lele na mai wannan yayan naka sarkin tsokana yayi maka da safen nan? " Sai da ya watsa wa Yah sadeeq harara sannan yace "mumy ina cikin bacci yaxo ya samin miciji a jikin blanket yana tsorata ni" Sadeeq bai ankara ba yaga mumy ta xame daga tsakiyar su daman shi yana bayanta ya lafe musaddiq kuwa yana gaban ta cikin dariya tace "ba ruwa na musaddiq gashi nan yi mishi allurar rashin ji " Ta fad'i tana mik'a wa musaddiq wani k'aramin first aid box wani fari ae kuwa da sauri Yah sadeeq ya rik'e tare da cewa "sorry brother baxan k'ara ba na daina " Yanda Yayi maganar ba k'aramin sa musaddiq da mumy dariya ba don hka baisan sanda ya tuntsire da dariya ba shi ma sadeeq dariyar yake nan suka rungume junan su cikin k'aunar junan su, mumy tana kallon su cikin so da k'aunar su tana addu'ar Allah ya k'ara had'e mata kan yaran nata ya dawwamar musu da farinciki. Musaddiq ne ya cika sadeeq tare da kama kunnen shi kamar shi ne babba ya d'an murd'a tare da cewa "sauran ka k'ara kuma " Kama kunnen shi yayi tare da cewa "baxan k'ara ba ma brother wannan ma tsautsayi ne " "Allah ya kyauta kullum ku dunga wasa kamar wasu k'ananan yara kun k'i fito da matar aure " Cewar daddyn su yana sakkowa daga kan stairs yana dariya da sauri suka K'arasa wajen shi tare da rungume shi suka bashi peck a kumatun shi ,mumy kuwa cewa tayi "ae kai ne kake shagwa6a su shi yasa suka kasa fitar da matar aure " Cikin shagwa6a musaddiq yace " ni har yanxu am a very young nake sai dai Yah sadeeq ". Shi kuwa Yah sadeeq cewa yayi "ni daddy na samu Matar aure wlh" Cikin jin dad'i Mumy da daddy suka ce "da gaske sadeeq? " Har suna had'a baki wajen fad'i cikin murmishi sadeeq yace "Allah da gaske jiya partyn da muka je na Omar anan naga yarinyar " Kama hannun shi mumy tayi sannan tace "Yawwa hka nake son ji a ina take ya sunan ta kuma? " "Kaiii mumy wad'annan tambayoyin hka " Cewar daddy yana dariya don yasan yanda ta damu k'warai da k'in tsayar da matar aure da sadeeq yak'i. "uhm uhm da xafi xafi ake dukan karfe dear " Cewar mumy kenan sannan ta cigaba da cewa "sadeeq fad'a min " Cikin murmishi sadeeq yace "Mumy kanwar Omar ce mufidah" Dummmm gaban musaddiq yayi mummunar fad'uwa lokaci d'aya............... Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* _Wannan page d'in sadaukar wa gare ku admins din exclusive writers Ummiey xeey,Amnoor, neena cool, Aunty haliloss, nafisat anka, ruksad, Aishan umma and aunty Queen mermue, dukkanin ku ina muku fatan alkhairi Allah ya k'ara basirah ya k'ara mana had'in kai Ameeen i really luv u guys_😻❤ *Page 6* Saboda tsananin 6acin rai a fusace yayo kan mufidah kamar wani mayunwacin xaki jikin shi har rawa yake, tuni mufidah ta fara ja da baya tana da nasanin abin da ta aikata mishi ga wani uban tsoro da ya lullu6e ta lokaci d'aya. Kafin ta ankara ta ganshi a gaban ta cikin tsananin 6acin rai ya d'aga hannu ya wanka mata mari a fuska marin da yayi matuk'ar gigita mufidah, hannun ya kamo ya murd'e shi er k'ara ta saki saboda axaba Kafin kuma yace "yanda kika 6ata kayan nan wlh sai kin wanke su " Yana gama fad'in hka yaja mufidah har cikin mota ya cilla ta ciki da k'arfi har sai da ta buge nan ya shiga ya ja motar a fusace duk mufidah ta gama tsorata jikin ta har 6ari yake tayi da nasani yafi sau ba iyaka gashi batasan inda xai kai ta ba ga mangarib tayi addu'a ta dunga yi Allah ya ku6utar da ita daga hannun shi ko kwakwkwaran motsi ta kasa yi saboda firgici. Wata unguwa ce mai Kyan gaske suka shiga yanayin unguwar mai kyau ko'ina tsaf dashi ga haske ta ko'ina kamar duhu bai yi ba gashi babu yawaitar mutane sosai, a gaban wani kyakkyawan gida flat house ya danna horn tuni mai gadi ya bud'e kofar gate di'n nan ya shige da motar shi har xuwa wurin da ake parking sannan ya fito ya bud'e kofar 6angaren da mufidah take ya fisgo ta sannan yaja ta xuwa cikin gidan. Gaskia gidan ba k'aramin had'uwa yayi ba kamar da mutane a ciki komai na more rayuwa akwai a gidan musaddiq ya siya gidan ba don komai ba sai hutawa idan yayi ra'ayi don sai yafi 2 weeks bai xo ba gashi ko'ina tsaf dashi da yake akwai masu gyara mishi gidan. Suna shiga palon ya wurgar da mufidah har sai da ta sake bige wa da kujera saboda tsabar xafin da ta ji sai da ta saki k'ara Kafin kuma ta mik'e tsaye cikin tsiwa ta ce "wai mene nufin ka na kawo ni wannan gidan iyeee? " Cikin kallon wulakanci yace "saboda ki wanke wannan kayan da kika 6ata kin ji na rantse wlh sai kin wanke su " "ni fah malam dakata kaji ko agidan mu wanki ake min ban iya ba don hka baxan yi ba " Tana gama fad'in hka tayi hanyar fita daga falon ae kuwa musaddiq yasa hannu ya janyo ta da karfi har sai da ta bugi kirjin shi idanun shi cike da tsantsar tsanar ta yace "ni ina ruwa na da baki iya ba idan ma baki ta6a yin wanki ba tun da aka haife ki to wlh yau sai kin yi don kin ga ban lallasa miki jiki ba koh?" Fisge jikin ta tayi tare da cewa "ae kuwa baka isa ba ni ka bud'e min kofa na tafi " Cikin murmishin mugunta yace "ae kuwa xaki k'wana a nan don baxa ki bar gidan nan ba sai kin wanke " Yana gama fad'in hka ya nufi wata kofa ya shiga tare da rufe wa wanka yayi ya sauya kaya xuwa jeans blue da t-shirt white mai dogon hannu ya fesa perfumes sannan ya fito xuwa falo da niyyar tafiya masallaci anan inda ya barta a hka ya same ta sai rusa kuka take ganin gashi har lokacin sallahr ishshah yayi kusan karfe 8 kenan tasan yanxu sun tashi daga partyn har sun koma gida ta shiga uku Idan ta koma gida me xata ce wa umma idan ta tuhume ta ina ta xauna sai kawai ta fashe da kuka don bata da amsar tambayar a hka ya fito ya tarar tana kukan. Yana daf da xai fita daga falon ya juyo ya kalle ta tukunna yace "Idan kina son koma wa gida da wuri to Kafin na dawo daga masallaci ki wanke kuma wankin ya fita sosai fah Idan bai fita ba sai kin sake" Yana gama fad'ar Hka ya fice daga falon ya sanya key ya nufi masallacin kusa da gidan. Mufidah kuwa ganin ba yanda xata yi ta nufi bedroom d'in da ya shiga d'aki ne mai kyau wanda aka k'ayata shi sosai kamar da mace a gidan, toilet ta fad'a ta hango kayan a xube a k'asa ganin machine din wankin kaya yasa mufidah jin dad'i amman tuni murnar ta koma ciki ganin shi da tayi a rufe 6am kamar ba'a ta6a amfani dashi ba tsaki taja tare da fad'in "Wannan mutumin mugu ne wlh" cikin takaici ta d'auka ta fara wankin tana yi tana kuka har da majina dak'yar ta samu jan juice din strawberryn ya fita daga jikin kayan sannan ta matse su ta shanya su sannan ta fito sai had'a uban gumi take kallon agogon tayi taga 8:55 tara sauran minti biyar kenan da sauri ta fito daga bedroom d'in turus ta ja ta tsaya ganin har yanxu musaddiq bai dawo ba kasa xama tayi ta dunga xagaye a cikin palon saboda tsabar tashin hankali kuka kuwa ba'a magana sai faman rusa shi take. A can wurin partyn kuwa ko da su Yah Omar da nabila basu ga dawowar mufidah ba sun d'auka ta gaji ta gudu gida don hka basu damu ba, shima sadeeq da yaga musaddiq bai dawo ba yasa shi tunanin ko ya gudu gida gashi key di'n yana hannun shi, lokacin da aka tashi sai su Yah Omar ne suka mayar dashi gida . Musaddiq bai dawo gidan ba sai wurin 9:40 lokacin mufidah har ta dai na kukan sai faman ajiyar xuciya take saki alamar taci kuka ta koshi wani murmishin mugunta ya yi tare da cewa "ohhh my god kiyi hak'uri na mance fah da ke sai yanxu na tuna har naje gida na kwanta na tuna da ke" Kallon shi mufidah tayi da kumburarrun idanun ta cikin takaici da bak'in ciki ta rasa ma me xata ce tabbas maganar shi gaskia ce don gashi har ya canja kayan jikin shi xuwa sleeping dress na maxa farare sol dasu masu d'an kauri don garin akwai d'an sanyi sanyi maganar da yayi ita ta dawo da mufidah daga tunanin da ta lula yace "xaki iya tafiya yanxu naga kayan kin iya wanki kuwa don sun fita " Ashe har ya shiga ya duba su, cikin tsananin tsoro tace "wlh tsoro nake don Allah ka kai ni gida" Hararar ta yayi kafin yace "ban da wannan time d'in don hka get out " Da gudu mufidah ta fita daga falon sai da ta fita tukunna tasa mayafin ta cikin sauri ta fice daga gidan gabanta yana faman fad'uwa don kuwa dare yayi ko'ina shiru kake ji nan fah ta dunga tafiya cikin sauri ga nisa unguwar tsakanin ta da titi dak'yar ta iya k'arasa wa kan titi sai dai ababan hawa sun ragu sosai don dare yayi gashi idan ta tsayar dasu basa tsaya wa ana hka wasu en shaye shaye suka nufi inda take har d'ayan na kok'arin rik'e mata hannu don hka mufidah yasa mufidah tsorata sosai nan dai ta kwasa da gudu ae kuwa su ma suka bi ta da gudu nan fah aka fara tsere tsakanin mufidah da en shaye shayen nan wani wawan birki aka ja da mota a gaban mufidah da sauri na cikin motar ya fito ae kuwa mufidah tana ganin musaddiq ne ta nufi wajen tare da rungume shi tana kuka sosai duk a firgice take. En shaye shayen suna ganin musaddiq suka juya suka gudu, had'uwar jikin shi da na mufidah ba k'aramin canja mishi tunani yayi ba na lokaci d'aya hannun shi yasa ya k'ara rungume ta tsam a jikin shi yana shafa bayanta a hankali ita kuwa sai faman kuka da ajiyar xuciya ta ke saki, shi ma duk laifin shi ne yayi gangancin barin ta taho wa cikin wannan daren a matsayin ta na mace. Dak'yar ya iya raba jikin shi da nata ganin hka yasa mufidah da sauri rik'o hannun shi cikin kuka tace "Don Allah kada ka tafi ka taimaka min kai kai ni gida ina jin tsoro please " Kama hannun ta yayi ya sata a mota a hankali ba kamar d'axu ba shima ya xagaya ya shiga sannan yayi wa motar key ya fara tafiya gaba d'aya tunanin shi ya canja tun lokacin da yaji mufidah a jikin shi wani abu ne ke kok'arin taso mishi a cikin xuciyar shi yana danne wa amman kuma ya kasa dai na kallon ta har xuwa lokacin da ya shiga farfajiyar gidan nasu ta sauka da sauri ta nufi cikin gidan shi kuma ya fita daga gidan har yaje kwanciya yana tunana had'uwar jikin shi da ta mufidah. Mufidah tana shiga gida ta tarar da su umma, Abba da Yah Omar nabila suna xaune hankalin su a matuk'ar tashe sai ganin ta suka yi kamar an wullo ta cikin su nan ta rushe da kuka sosai umma da nabila suka rungume ta da aka tambaye ta ina taje k'in magana tayi sai kuka nan dai dak'yar suka rarrashe ta tayi shiru tana sauke ajiyar xuciya, ruwan wanka nabila ta had'a mata ta shiga wanka bayan ta fito ta shirya cikin kayan bacci ta kwanta xuciyar ta na tunanin abin da yafaru tsakanin ta da musaddiq da hka bacci 6arawo ya d'auke ta.............. _kuyi hak'uri da wannan sai gobe kuma Insha Allah_ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *E.W.F* *Page 8* Dummmm gaban musaddiq yayi mummunar fad'uwa lokaci d'aya nan take yaji wani irin abu na yawo cikin xuciyar shi wanda ya kasa tantance ko mene gaba d'aya sai yaji baxai iya cigaba da sauraren wannan hirar ba ya fara tafiya xuwa cikin bedroom d'in shi xuciyar shi cike da tarin damuwa kuma ya rasa dalilin damuwar tashi tun da Yah sadeeq ya ambaci sunan mufidah yanayin shi ya canja. A can palo kuwa mumy cikin tsananin farinciki tace " Alhmdllh my dear ka ji ashe er gidan aminin ka ya gani " Er dariya irin ta manya daddy yayi tare da cewa "kaiii amman Nayi tsananin murna yanxu daga nan office xan fara xuwa na same shi mu yi magana " Cikin jin dad'i sadeeq ya rungume daddy yana cewa "thank u daddy Allah ya bar mana kai " "Ameeen sadeeq amman gaskia baxa'a ja da nisa ba tunda duk ansan juna ciki da bai " Cewar mumy "k'warai kuwa Allah ya tabbatar da alkhairi Allah ya xa6a abin da yafi alkhairi " fad'in daddy "Ameeen thumma Ameeen " Mumy da sadeeq suka fad'a sannan mumy ta kalli sadeeq tace "je ka kirawo musaddiq mu yi breakfast " "Okay " Sadeeq ya fad'a yana tashi tsaye bedroom d'in musaddiq ya shiga turus yaja ya tsaya ganin musaddiq xaune kan carpet ya had'a kai da gwiwa daga ganin yanda yayi ba k'aramin damuwa ce a tattare da shi ba. Cikin sanyin jiki sadeeq ya k'arasa wurin shi tare da dafa shi yace "musaddiq lafia, me yafaru? " D'ago kanshi musaddiq yayi ya xubawa sadeeq idanun shi da suka yi jawur dasu a firgice sadeeq ya sake cewa "lafia brother me yafaru? " Ya fad'i yana tatta6a jikin shi ko ciwo yaji nan dai bai ga wani alamun ciwo ba da sauri Yah sadeeq ya mik'e xai je ya kirawo su daddy, musaddiq kamar yasan nufin shi caraf ya rik'e hannun shi tare da cewa "na rok'e ka brother kada ka fad'a wa su daddy please " Dawowa sadeeq yayi tare da cewa "okay naji fad'a min damuwar ka Idan kaki xan fad'a wa su daddy" Murmishin yak'e musaddiq yayi tare da cewa "Naji brother " Nuna shi yayi da d'an yatsa yace "are you sure? " "yes " Cewar musaddiq dak'yar don ji yayi xuciyar shi na wani irin xafi, "toh fad'a min " Cewar Yah sadeeq yana rik'e hannun musaddiq. D'an shiru yayi yana tunanin me xai cewa sadeeq xai fad'a mishi yarinyar da yake so ita shi ma yake so nooo i can't ko da kuwa son shi xai xama ajalin shi baisan ya kamu da son mufidah ba sai da Yah sadeeq ya furta yana son ta yanxu shi ya xai yi me xai cewa brother. D'ago kanshi yayi ya kalli sadeeq yaga ya xuba mishi ido alamar shi yake saurare, d'an kwakwalo murmishin yak'e yayi yace "brother daman fah kawai ina tunanin yanda xan bar lecturing na koma hospital da aiki nake don basa son na bar skul d'in sun dame ni da rarrashi so shine na xauna nake tunanin mafita " Tuntsire wa da dariya sadeeq yayi kafin yace "don wannan kuma shine kake sa kan ka cikin damuwa kawai ka share su ka fara xuwa hospital bana son kana wahala " "Yawwa brother thank u Allah ya bar min kai " Cikin dariya sadeeq yace "hka nake so d'an k'anina bana son ina ganin ka cikin damuwa ko ciwo ji nake kamar na dawo dashi jiki na nake ji bana son ganin 6acin ranka nafi son ko yaushe ka kasance cikin farin ciki idan naganka cikin damuwa ji nake hankalina yana matuk'ar tashi bana samun kwanciyar hankali sai naga kai ma ka samu" Musaddiq rungume sadeeq yayi a hankali wasu hawaye suka xubo wa musaddiq yayi saurin sa hannu ya goge su sannan ya saki Yah sadeeq Mumy wadda take tsaye bakin kofar shigo wa bedroom d'in ta saki murmishin jin dad'i Kafin tace "aiken kenan sadeeq ba kai ba wanda na tura ka kirawo nagaji da jira na biyo bayan ku " Murmishi Suka yi bayan sun had'a ido tukunna kamar had'in baki suka ce "sorry mum " Kamo hannun su tayi suka fito daga d'akin xuciyar musaddiq cike da tarin damuwa. Bayan sun kammala breakfast d'in daddy ya tafi office hka shima sadeeq ya fito xai tafi don har ya shiga mota musaddiq ya tsayar dashi suka tafi tare xai sauke shi a buk. Yah sadeeq yana parking ya fito daga motar shi da musaddiq suna magana sai ga mufidah tayi parking d'in motar ta sun fito tare da nabila, gaba d'aya hankalin musaddiq yayi kanta tayi mishi kyau sosae cikin wata arabian gown bak'a ce hka mayafin da tayi rolling d'in kanta bak'i ne da yake fara ce kayan sun amshe ta, musaddiq ji yake kamar ya ta a jikin shi ko yaji sassauci a cikin xuciyar shi yanda yake jin wata xaxxafan son ta na sake kwaranya a cikin xuciyar shi wannan wacce irin masifa ce dak'yar ya iya saita idanun shi daga barin kallon ta. Sai da suka d'an gifta su sannan sadeeq ya ankare da ita don hka cikin sanyin murya yace "mufidah! " Cikin sauri suka jiyo tare da nabila don ganin mai kiran nata da musaddiq ta fara had'a ido sannan ta kalli sadeeq Wanda yake ta xuba murmishin farincikin ganin ta k'araso wa suka yi sannan suka gaisa da sadeeq ko kallon Inda musaddiq yake mufidah bata yi ba ko gaida shi bata yi ba sai nabila shima musaddiq yiwa sadeeq sallama yayi ya tafi xuciyar shi nayi mishi wani rad'ad'i dak'yar ya iya k'arasa wa cikin office ya xube yana wani irin haki kamar wanda yayi tseren gudu. Ganin musaddiq ya tafi yasa ita ma nabila ta wuce don ta basu waje cikin wani salon kallo wanda ya bawa mufidah kunya yace " Naga dai yanxu kamar kina sauri ki ban contact di'n ki zuwa anjima xan xo gida na same ki don akwai muhimmiyar magana da xamu yi " Ya K'arasa fad'i yana mik'a wa mufidah wayar shi kar6a tayi tare da shigar da contact di'n ta sannan ta mik'a mishi tana cewa "Okay ba matsala sai ka xo" Da hka sukayi sallama ya shiga motar shi ya tafi ita kuma mufidah ta shige department d'in su tana cewa tatsuniyar gixo baxa ta shige k'ok'i ba don tsab ta karance shi tun ranar birthday di'n Yah Omar. Bayan sun fito a lecture's mufidah take sanar wa da nabila yanda suka yi da sadeeq Sam nabila batayi mamaki ba don yanda yake bin ta da kallo ranar partyn Don hka nabila tace "Ki gode wa Allah mufidah don samun miji kamar sadeeq a wannan xamanin sai an shirya ya tattara komai gashi kyakkyawa duk da musaddiq yafi shi kyau ga kud'i da mutunci sannan ga fara'a Ba kamar musaddiq ba Allah yarinya Idan ya furta miki so kawai ki bada kai bori ya hau don ni fah mun gama shirya kan mu da Yah Omar " Cikin dariya mufidah tace "ae na d'ago jirgin na ku tuntuni to Allah ya tabbatar mana da alkhairi " "Ameeen sister tashi mu gudu gida don Yah Omar xai xo kuma gashi ke ma Kina da bak'o " "alright mu je " Cewar husna tana yin gaba sun xo wajen da suke parking wurin ba mutane sosai kafin su k'arasa wajen motar sai takalmin mufidah ya gurd'e ta ta tafi xata fad'i k'asa caraf taji an rik'e ta ta fad'o jikin mutum k'amshin turaren shi kawai taji ta fahimci ko wane don hka da sauri ta tashi daga jikin shi tare da kallon shi tana jin wani yanayi tattare da ita Idan ta kalli cikin kwayar idon shi yayin da shi ma musaddiq ya xuba mata ido sai dai yau ba kallon tsanar ta take hangowa acikin kwayar idon shi ba maganar da nabila tayi ne ya dawo dasu hayyacin su don hka da sauri ya shige daman jiran fitowar ta yake domin ya sake sata cikin idanun shi cikin sanyin jiki mufidah take driving tana tunanin irin kallon da yake mata wanda yasha banban da na ko yaushe........... Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM* _Wannan page naki ne k'awata khadijah neena cool (niger), Allah ya bar xumunci ya bar mu tare ina miki fatan alkhairi_🤝😻 *Page 9* Da yammacin ranar da wajen karfe 5 sadeeq ya fito cikin shirin tafiya gidan su mufidah yaci gayu cikin wata tsadaddiyar shadda milk colour an yi mata aiki da brown din xare sai ya sanya takalmi brown da hula brown mai ratsin milk a jiki gaskia yayi kyau sosae daman shi gwanin sa manyan kaya ne k'ananun kaya basu dame shi ba wannan sai musaddiq. A falo ya tarar da mumy da musaddiq suna xaune mumy tana faman lalla6a shi ya ci abinci don yinin yau gaba d'aya ta kasa gane d'an nata K'arasa wa yayi Inda suke ya xauna tare da cewa "me yake damun shi ne Mumy?" "nima yanxu na gama tambayar shi yace min ba komai kuma ban yarda ba don yau gaba d'aya cikin damuwa yake " Cewar mumy kenan fuskar ta cike da damuwa, sadeeq ne ya kalli musaddiq shima fuskar shi d'auke da damuwa ya rik'o hannun shi tare da cewa "Haba brother ka fad'a mana damuwar ka mana ko xamu iya taimaka maka da wani abin " Shiru musaddiq yayi ya rasa me xaice musu "tell me please what wrong with u ?" sadeeq ya sake fad'i duk farincikin da yake cikin xuciyar shi na xuwa wurin mufidah amman sai yaji farincikin ya kau sakamakon ganin tilon k'anin shi cikin damuwa. Cikin murmishin yak'e yace "ni fah kada ku damu mumy and brother bana jin dad'in jiki nane amman ba wani abun ba ne " Sam basu yarda da abin da yace ba amman tun da har yak'i sanar musu to abin babba ne, hka dai suka bashi shawara akan ya dage da addu'a sosai akan abin da yake damun shi godiya yayi musu sannan ya tashi ya tafi d'akin shi ya rufe kofa tare da jingina a jikin kofar xuciyar shi cike da tunanin mufidah. Acan palo kuwa da kallo suka bishi cikin tsananin tausayin shi, kafin kuma Yah sadeeq yayi wa mumy sallama yana sanar da ita gidan su mufidah xai je, nan tayi mishi addu'ar dawowa lafia tare da bashi sak'on ya gaida mata da mufidah. Musaddiq kuwa dakyar ya iya jan kafar shi xuwa bakin bed d'in shi ya janyo drower din jikin bed side ya janyo wani d'an k'aramin littafi wanda kallo d'aya nayi mishi na tabbatar da diary din shi ne Wanda yake rubuta mahimman abun da ya shafi sirrin shi a ciki, biro ya d'auko ya buge tsakiyar page ya fara rubutu kamar hka....... *NAYI SAKE!* _Tun ranar da na fara d'ora kwayar idanuna akan ta nake jin wani

Chapter 3 of 23