Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
cikin nan, nasan shi zai tabbatar miki da irin so da kaunar da nake yi miki " Ya gama fad'in haka yana kallon ta, idon ta akan diary d'in mene amfanin karanta shi, bayan ta san abin da yake cikin shi, gani yayi ta ajiye diary d'in a gefen ta, tare da matsowa inda yake, hannun ta ta sanya tana mai rik'o nashi hannun duk biyun, cikin sanyin murya tace "Mene amfanin karanta abin da na karanta " Cikin mamaki yake bin ta da kallo, hannun d'aya ta d'auko ta d'ora shi kan saitin zuciyar shi tace "Me yasa kake wahalar da kan ka Musaddiq, nasan abin da yake cikin diary d'in, saboda kukan da nayi na tausayin halin da ka shiga a dalilin sona, shine ya haddasa min xaxxa6i a jiki na, bazan iya butulce wa zuciyar da take yi min wannan son ba " D'an jan numfashi tayi tare da yin murmishi ga hawaye suna zuba, ganin yanda Musaddiq ya bud'e baki da hanci yana kallon ta, muryar ta na d'an rawa ta cigaba da cewa " Na tausaya maka halin da ka shiga sosai duk adalilin so na, gaskiya kai ba k'aramin masoyi na ba ne, wanda yake min so na gaskiya, nima ina...... " Bata k'arasa fad'i ba, sakamakon kukan da kubce mata, rungume ta yayi cikin jikin shi, yana fitar da wani irin hawaye a idon shi. "Mufidah ki dai na kukan nan, ya isa haka kukan ki na ta6a min zuciya ta, na baki diary d'in nan don ki karanta, nasan baki na ba zai iya fahimtar da ke yanda nake son ki ba, ina son ki Mufidah son da ba kowanne namiji ne yake yiwa matar shi ba, ina son ki son da zan iya mutuwa idan ace ban same ki ba, Mufidah ina son ki, son da fatar baki na bazata iya fayyace miki ba, ina son ki son da bazan iya........ " Da sauri Mufidah ta sanya hannu ta toshe mishi bakin shi tana mai sake fashe wa da wani irin kukan tausayin Musaddiq, shima hawayen ne suke zuba a idanun shi, cikin kukan ta dad'a k'ank'ame shi a jikin ta, wani son shi na k'ara ratsa zuciyar ta. D'ago kanta yayi yana kallon cikin kwayar idon ta yace , "ki fad'a min kina sona, ina son jin wannan kalmar" Cikin shashshak'ar kuka tace "ina son ka Musaddiq, i luv u so much irin wanda bakina bazai iya fad'a ba " Wani sanyin dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar shi, ya dad'a rungume ta cikin jikin shi, suna tona wa junan su asirin zuciyar su, acikin wannan lokacin ji suke kamar su fi kowa farinciki, jin su suke kamar su dawwama a hakan, suna masu faranta ran junan su. Daga nan sai wasa ya fara canja salo na daban, cikin 'yan mintuna Musaddiq ya fara aikawa da Mufidah xafafan sak'onnin shi, jikin shi har wani rawa yake, gaba d'aya ya gama fita a hayyacin shi ya mance duniyar da yake ciki ma, zafafan kalamai yake furta mata su cikin wani irin shauk'in son ta. Soyayya da take kunshe cikin zuciyar shi ta shekaru ya gama fayyace wa Mufidah, ba tare da yasan yana hakan ba, kukan tausayin shi kawai Mufidah take zuciyar ta na k'ara son shi, iya wahala kam tasha ta a wannan lokacin, saboda had'uwar ta da jarumin namiji irin Musaddiq, ba ita kad'ai ba ma shi kanshi Musaddiq d'in ya wahala,har zuwa lokacin da mai afkuwa ta afku, kafin daga baya bacci mai dad'i ya d'auke su. *_ASUBA TA GARI MUSFEEDAH_* Tun a cikin daren gaba d'ayan su, kowanne ya kamu da zazzafan zazza6i a jikin su, har zuwa wayewar gari, dakyar Musaddiq yayi k'arfin hali ya tashi, wanka yayi tare da alwala sannan ya fito a toilet. Sallah yayi kafin ya taimaka wa Mufidah ita ma tayi wanka, sai da tayi sallah tana idar wa wani nauyayyen bacci yayi awon gaba da ita, ga jikin ta zafi har yanzu zazza6in bai sauka ba. Shima Musaddiq d'in bacci ne ya d'auke shi mai nauyi sosai, don ba'a samu cikakken bacci ba, gashi kuma an tashi da zazza6i. Knocking d'in kofar da ake yi ne ya tashi Musaddiq daga baccin da yake yi, dakyar ya iya lalla6a wa ya tashi tare da bud'e kofar, Afnan ya gani a tsaye tana kuka da alama ta dad'e tana yin knocking d'in, jikin shi ta fad'a cikin muryar kuka tace "daddy ina kuka shiga kai da mami? " Shafa kanta yayi tare da cewa "Afnan bacci muke yi, sannan mamin ki bata jin dad'i, kada ki tashe ta mu je na shirya ki, akwai skul " Nan yaja hannun ta zuwa d'akin Mufidah ya shirya ta cikin uniform d'in skul, sannan suka fito ya had'a mata tea tare da soya mata eggs, tayi breakfast sannan ya wuce kai ta skul, bayan ya ajiye ta ne ya dawo gida yana addu'a cikin zuciyar shi Allah yasa Mufidah zazza6in jikin ta ya sauka. Lokacin da ya shiga bedroom d'in shi bai tarar da Mufidah ba a ciki ba, sai ya wuce bathroom yayi wanka, sannan ya fito ya shirya cikin wani yellow 3quater and white T-shirt mara hannu, ya fesa different perfumes a jikin shi kafin ya fito zuwa d'akin Mufidah, jin shi yake yau wasai dashi kamar wanda aka sauke wa wani babban abu a kanshi da cikin zuciyar shi. Yana tunanin halin da suka kasance shi da Mufidah a tsayin daren jiya,murmishi ne shimfid'e a saman fuskar shi na farinciki da nishad'i, yana k'arasa shiga cikin d'akin, ya hango ta kwance saman bed har tayi wanka ta shirya cikin wata doguwar riga har k'asa mai hannun vest, irin mai kwanciya a jikin nan ce, idanun ta a lumshe suke but ba bacci take ba, tunanin Musaddiq d'in ta take. Daddad'an k'amshin perfumes d'in shi ne ya ziyarci cikin hancin ta, d'umin jikin shi taji a nata, a nutse ta bud'e idon ta ai kuwa suka had'a ido, yana wani haske ta da kyakkyawan murmishin shi, d'an hararar wasa tayi mishi tare kok'arin tashi zaune. Cikin sauri ya janyo ta zuwa jikin shi yana cewa "sweet baby nah ya zazza6in naki, dafatan ya sauka ?" Ya k'arasa fad'i yana tatta6a jikin ta, jin babu d'umi yasa shi sakin ajiyar zuciya yace "naji jikin naki babu d'umi alamun ya sauka, gashi ni kin shafa min har yanzu ban daina jin shi ba " Kunyar shi take ji ta kasa yin magana, but fuskar ta d'auke da murmishi, ya gama karantar kunyar shi take ji, "Baki tambayi ina Afnan ba ?" Dakyar ta iya bud'e baki tace "Hmm nasan ka kaita skul, tun da na tashi ban gan ku ba " D'an murmishi yayi so yake ta d'ago kanta ya kalli face d'in ta, amman tak'i d'agowa, don haka ya sanya hannun shi ya dafe saitin zuciyar shi yace "Wash! Allah nah zuciya ta" A kid'ime Mufidah ta d'ago kanta tana kallon shi, ganin yanda ya kwanta sai juyi yake yana rik'e zuciyar shi, yasa Mufidah fara hawaye don duk a tunanin ciwon ne ya tashi, cikin rawar murya take cewa "wayyo Allah, sannu Musaddiq don Allah ka tashi mu tafi hospital " Ganin yanda ta rud'e ne yasa shi tuntsire wa da dariya, sakin bakin ta tayi tana kallon shi, ga hawaye na zuba, kawai sai ta d'auko pillow ta fara dukan shi da shi, Musaddiq yana dariya tare da yi mata gwalo kuma yana kare dukan. Gajiya tayi ta zube kan bed tana mayar da numfashi, janyo ta jikin shi yayi yana cewa "nima na rama abin da kika yi min jiya a wurin beach " Murmishi kawai take tana girgiza kanta, wato ashe ya gane karyar ciwo tayi. "ina son ki Mufidah " Ya furta hakan cikin kunnen ta, " nima ina son ka sosai " Ta mayar mishi da amsa suna yiwa junan su murmishi. A haka suka tashi zuwa parlour, kitchen suka shiga tare suka had'a breakfast bayan sun gama ne, suka sake koma bacci.......... Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *£xclusive Writers Forum* *Likes nd comment's fb page*👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com *PAGE 58* Baccin su suka sha sosai, basu ankara da tafiyan lokaci ba sai da aka kirawo Musaddiq a waya daga skul d'in su Afnan kan yazo ya d'auke, don anjima da tashin su, cikin sauri suka shiga wanka tare suka yi, bayan sun fito ne suka shirya a gurguje don tafiya d'auko Afnan. Bayan sun gama shirya wa ne, suka tafi school d'in d'auko Afnan, suna d'auko ta ya wuce dasu restaurant suka ci abinci,sannan suka wuce wayo cikin tsantsar farinciki suke a wannan ranar, sai da dare yayi suka dawo gida a gajiye. Wanka Mufidah tayi wa Afnan ta kwantar da ita, sannan ta shiga nata wankan kafin ta fito har Afnan tayi baccin ta saboda gajiyar da tayi, tana cikin shirya wa Musaddiq ya shigo d'akin yana cewa "My sweet baby laifi me nayi aka bar ni, ni da a parlour? " Jiyo wa tayi tana murmishi tace "ba laifin da kayi my man, wanka na tsaya yi ne " Shima murmishin yayi tare da cewa "Yayi kyau hakan habibty, mu tafi d'akin mu koh ya?" Yayi maganar yana d'aga mata gira, sunkuyar da kanta tayi tana murmishi tace "okay, yiwa Afnan addu'a kafin na k'arasa shirya wa " "toh angama ranki ya dad'e" Cikin sigar tsokana tace "Ohhh har na kai wannan matsayin? " Yana jan hancin ta yace "kin ma wuce haka baby nah " Yana gama fad'in haka ne yayi wa Afnan addu'a a jikin ta, sannan yaja ta suka bar d'akin zuwa nashi, hmmm wannan daren ma an bawa soyayya hakk'in ta sosai, don tsakanin Musaddiq da Mufidah kowanne yana nuna wa d'an uwan shi irin kalar son da yake mishi, kafin daga k'arshe bacci mai dad'i ya d'auke su, suna rungume da junan su, zuciyar kowa fal farinciki. *_ASUBA TA GARI MUSFEEDAH_* *AFTER 1 WEEK* (Agurguje) Cikin 'yan kwanakin nan tsakanin Mufidah da Musaddiq soyayya kawai ake xuba wa, suna bawa junan su kulawa sosai, hankalin su ya kwanta sun yi fresh abin su, suna waya sosai dasu Mumy, Daddy, Umma, Abba, Nabila, Yah Omar dasu Muh'd da matar shi Nafisat, ana jin lafiyar juna. Duk wani shiri Musaddiq ya gama yi na koma nigeria, hospital d'in da yake aiki yayi musu sallama tare da ajiye musu aikin su, sam basu ji dad'in barin Musaddiq asibitin ba, don ba k'aramin taimaka musu yake ba babban likita ne da yasan me yake yi, da haka suka rabu cikin tsananin kewar shi. Sai da Afnan ta samu hutu a school tukunna suka tattara inasu inasu suka bar Australian, suka tafi k'asar switzerland suka samu hutun tsayin sati uku acan. Kafin su nufi k'asar Saudi Arabian su yi umarah, sai da suka yi wajen sati hud'u a Saudi Arabian saboda Musaddiq ya d'an yi fama da mura da zazza6i, kafin daga baya ya warware su fara shirye shiryen dawowa gida Nigeria, sun yi tsarabar su sosai wadda zasu raba wa 'yan uwa, duk k'asar da suka je sai da suka yi tsaraba. Daman tuni an sanar da 'yan uwa dawowar su don haka aka fara shirin tar6ar su, ba irin Mumy da tafi kowa farinciki saboda Musaddiq da ya fad'a mata ya dawo gida kenan bazai koma Australian ba, ba k'aramin jin dad'i da farinciki tayi ba. Jirgin da suka hau saukar yamma yayi sosai daf da mangarib, bayan jirgi yayi landing mutane suka fara fito wa 'yan uwa sai wara idanu suke su hango ta ina zasu gano su Mufidah. Babu jima wa suka hango Musaddiq yana rik'e da hannun Mufidah, ga Afnan a kafad'ar shi tana bacci sun yi matuk'ar yin kyau sosai, fad'ar irin had'uwar da suka yi ma 6ata lokaci ne. Duk sai aka zubo musu ido ana kallon su, ganin yanda suka yi matuk'ar dace wa da junan su, ga wani kyau da suka k'ara da ka gansu kaga fulanin asali. Kunya ce ta rufe Mufidah ganin yanda ake kallon su, zame hannun ta tayi daga na Musaddiq kallon ta yayi kawai ya girgiza kai, tun kafin su k'arasa su Mumy ma suka taho aka had'u cikin farinciki, kowa bakin shi yak'i rufuwa saboda murna, nan aka gaggaisa da juna tukunna aka nufi motoci don tafiya gida. Dr Muh'd wanda ya zuba wa Musaddiq ido ganin yanda yayi k'iba kamar ba shi ba gashi sai murmishi yake saki yana wani jifan Mufidah da wani irin kallon so, sai ya kasa daure wa yayi ya ta6o Musaddiq yana cewa "lover boy adai kula ba mu kad'ai ba ne akwai surukan ka, kada ayi abin kunya a bari sai an ke6e " Hararar shi Musaddiq yayi tare da cewa "ke fah na fahimci d'an sa ido ne na k'arshe, ina ruwan ka da mu naga matata ce " Dariya Muh'd yayi tare da cewa "d'an duniya, naga alama ma mun kusan samin baby da gani baka yi sassauci ba wajen uhm " Bai k'arasa ba ya kwashe da dariya sai kawai Musaddiq ya biye mishi suka yi dariyar tare da tafawa, da haka suka k'arasa gida suna tsokanar junan su, uhm Aminan kwarai kenan, Musaddiq nd Muh'd kullum son junan su suke tamkar wasu 'yan uwa na jini, (ni kaina amintar su na birgine, don a yanzu kafin a samu irin aminan sai an tona, saboda son zuciya yayi mana yawa yanzu, Allah kada ka bamu ikon cin amanar mutumin da ya d'auke ka matsayin aboki, amini kuma d'an uwa, Amin). Bayan sun k'arasa gida ne mamaki ya kama Mufidah da Musaddiq ganin yanda gaba d'aya aka canja fasalin gidan, side d'in da Sadeeq da Mufidah suka fara zama tuni an rushe shi, an sake wani sabon fasalin mai kyau da tsaruwa, komai an canja na gidan tamkar bashi ba. A part d'in su Mumy aka zauna bayan anyi sallahr mangarib da ishsha ne, aka zauna yin kwarya kwaryar walima ta farincikin dawowar su Musaddiq gida lafia, anci ansha anyi musu addu'ar fatan alkhairi, kafin kuma kowa ya kama gaban shi cikin tsantsar farinciki. Bayan watanni biyu da dawowar su Mufidah Nigeria Nabilah matar Yah Omar ta haihu an samu baby girl, ai kuwa sun sha suna yarinya taci sunan Mufidah ba k'aramin jin dad'i Mufidah da Musaddiq suka yi ba, ai kuwa babyn tasha kaya sosai a wajen su. Bayan suna da kwana biyu ne Mufidah ta fara zazza6i sosai mai zafi nan Musaddiq ya rud'e sosai babu 6ata lokaci ya duba ta abin ka da matar likita nan ya hango babyn shi d'an wata biyu da sati uku a tare da ita, ai kuwa ya d'aga ta yana juyi da ita a cikin bedroom d'in cikin mamaki take kallon shi kafin ta bud'e baki tace "lafia dear? " Sakko da ita yayi tare da zaunar da ita kan sofa ya dire gwiwowin shi a k'asa tare da rik'o hannun ta cikin nashi yace "my sweet baby ina matuk'ar farinciki yau saboda na kusan xama uba shine baki fad'a min ba sai da na gano da kaina koh? " Wani murmishin jin kunya ta saki tana kare fuskar da hannun ta tace "ni....ni fah bansani ba da gaske " Tashi yayi ya xauna kusa da ita idanun shi cikin nata yace "ina son ki Mufidah bazan iya rayuwa babu ke ba kiyi min alkawari na kasance wa dani har abadan ba xaki guje ni ba" Bakin ta takai saman le6en shi ta sumbata kafin ta d'ora hannun d'aya cikin nashi tace "nayi alk'awarin kasance wa da kai my man har k'arshen rayuwa ta i luv u musaddiq " "i luv u too habibty " Ya k'arasa fad'i yana shigar da bakin shi cikin nata soyayya sosai suka gwada wa junan su a wannan lokacin don Mufidah ma ta mance da wani ciwo sai da ta dawo dai dai tukunna ta sanya mishi kukan shagwa6a ai kuwa ya dunga yi mata dariya kafin daga bisa ni ya 6ige da rarrashin ta. Su Mumy sunyi matuk'ar farin ciki da wannan albishir d'in da Musaddiq yayi musu na samun jika, daman tuni ta dauke Afnan daga wurin su tana hannun ta duk da kuwa gida d'aya suke zaune, su umma ma sunyi farinciki sosai, amman babu wanda ya kai Muh'd farinciki abokin shi ya samu matar da yake so gashi har zuri'a zata fara shiga tsakanin su, lokacin da Musaddiq yake sanar da Muh'd d'in bayan ya gama taya shi murna ne yace "aboki wai ina ciwon xuciyar taka ne? " "yaro tun da zuciya ta samu abin da take so, ai kuma shikenan " Dariya Muh'd yayi kafin yace "Toh Allah ya k'ara lafia " "Amin, don wani time d'in fah sai a hankali tana yi min ciwo, sai dai ina kok'ari wajen kiyaye abin da zai taso min da ciwo, kaddara tawa kenan Muh'd " Wani mugun tausayin shi ne ya kama Muh'd, nan ya yi mishi addu'ar Allah ya bashi lafia, kafin su yi sallama da junan su............ Aishat A Muh'd ✍🏻 [13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲 *Written by* Aishat A Muh'd ♻ *£xclusive Writers Forum* *Likes nd comment's fb page*👇🏻 #https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/ Email:Aishataudimuhd.as@gmail.com *PAGE 59* Cikin kwanciyar hankali suka cigaba da rainon cikin Mufidah, su Musaddiq sai rawar kai ake za'a samu baby, kula da soyayyar Mufidah kullum k'ara k'aruwa take cikin zuciyar shi. Ta 6angaren Mufidah duk wani kyautata wa tana yi mishi sosai, bata yi duba da irin son da yake mata ta wahalar dashi ba, biyayya sosai take mishi duk wani abin da yake so take yi mishi, tana kok'arin kiyaye abin da zai d'aga mishi hankali har ciwon shi ya tashi. Duk lokacin da ta tuna sanadiyyar son ta ne, ya kamu da ciwon zuciya har kuka take yi mishi na tausayin shi, a haka cikin ta yake ta girma sosai, gashi babu wani laulayi sosai, sai dai yana sanya ta kwad'ayi. Ana cikin haka nafisat matar Muh'd ta haihu an samu baby boy, waiii murna wajen Musaddiq ba'a magana, kamar Mufidah ce ta haihu haka yake jin shi. Ranar suna sun yi hidimar suna sosai inda jaririn yaci sunan Musaddiq, rasa inda Musaddiq zai sa kanshi yayi don farinciki hak'k'a Muh'd aboki ne na gari, ya d'auke shi tamkar Yah sadeeq d'in shi, ya kashe kud'i sosai Musaddiq a wannan sunan,komai yak'i yarda Muh'd yayi sai shi, Mumy, daddy da Mufidah ma sun yi hidima sosai,sai dai fatan Allah ya raya lil Musaddiq. *AFTER 2 MONTH'S* Mufidah zaune take a parlourn Mumy akan kujera, ta mik'e k'afafun ta saman centre table, tana cin wani gashashshen nama ya sha cabbage, tomatoes and onions akai ga yaji mai dad'i a gefe tana dangwala dashi, gefe d'aya kuma ga coconut drink wanda yasha milk gashi yayi sanyi, cin abinta take hankali kwance. Duk wannan hidimar Mumy ce tayi mata, don ta hana ta yin wani aiki ko girki, kuma duk abin da tace tana so Mumy na kok'ari wajen sama mata shi, gaba d'aya ta duk'ufa wajen cin naman, batasan Musaddiq ya shigo parlourn yana tsaye sai kallon ta yake dawowar shi daga hospital kenan. Ta d'auka naman a jikin fork tana kok'arin kai wa bakin ta, taji an rik'e hannun ta da ta da yake d'auke da fork d'in, da d'an sauri ta juya kanta baya suka had'a ido da Musaddiq, sakarwa junan su murmishi suka yi cikin so da kauna, kafin Musaddiq ya juya hannun ta zuwa wajen bakin shi ya sanya naman har da wani lumshe idanun shi saboda dad'in shi, kafin ya bud'e su ya watsa kan fuskar Mufidah. Wadda ta ta6e fuska tana shirin yin kukan shagwa6ar da ta saba yi mishi, ya bud'e bakin shi yace "Wow gaskiya Mumy tana ji da ke, irin wannan cin dad'i haka, sai an bari na tafi hospital take shirya miki abin dad'i don kada na ci koh, aikuwa wannan ya zama rabo na daman yunwa nake ji " Ya k'arasa fad'i yana d'aga mata gira, turo bakin ta tayi gaba tare da cewa "ni dai gaskiya a'a, ai ba laifi na ne ba, babyn kane yake son ci " Mak'e kafad'a yayi tare da cewa "uhm uhm ni ban yarda ba, kullum ai tace wa baby na yake son abu don dai bashi da bakin magana " Yana gama fad'in haka ya kar6e plate d'in hannun ta, zama yayi kusa da ita sannan ya fara ci ,ganin haka yasa Mufidah fara tuttura k'afa zata fara kukan shagwa6a, dariya ya fara yi mata tare da sanya hannun shi ya d'an ja kumatun ta yace "sweet baby rigima ko Afnan kin fita rigima, toh dai wannan duk kukan shagwa6ar ki sai na cinye " Ya k'arasa fad'i yana mata gwalo, ai kuwa ta saki kukan shagwa6ar da babu hawaye sai goge idon da ake, shi kuwa Musaddiq sai tsokanar ta yake yi, gefe d'aya kuma yana cin naman tare da shan coconut drink d'in nan. Ana cikin haka sai ga Mumy ta shigo parlourn, ta tarar da Musaddiq yana faman tsokanar ta, girgiza kanta tayi tana murmishi idan da sabo ta saba da rabon wannan rigimar kullum, k'arasa wa tayi cikin parlourn tare da kallon Musaddiq tace "Ohhh ni, Musaddiq me yasa ka fiye tsokanar ta ne? " Turo bakin shi yayi irin na shagwa6ar nan yace "Mumy kullum sai kin nuna son kai, idan na tafi hospital sai ki ta bata abin dad'i tana ci ni ba'a ajiye min " Murmishi Mumy tayi tare da cewa "kai ai babba ne kuma kaga abin da take d'auke dashi, dole ana bata abin da take so, ina ce jiya wurin karfe 10 na dare ka fita samo mata shawarma da take son ci" D'an sosa kai yayi yana kallon ta, don ya tuna rigimar da tayi mishi jiya da dare, sai da suka kwanta bacci ta tashe shi ita shawarma take son ci, jiki na rawa ya tafi siyo mata, ko da ya dawo rabin d'aya ta iya ci a duk yawan da ya siyo mata, kafin yace "Ehemm na tuna Mumy, but ni ana ajiye min komai aka yi mata tun da ina taya ta rainon babyn " Murmishi Mumy tayi tare da cewa "shikenan za'a ajiye maka, amman na yau a hak'ura a bar mata" Mik'a wa Mufidah plate d'in yayi yana wani langa6e kai, kallon shi tayi sai taji ya bata tausayi, cikin murya k'asa k'asa don kada Mumy taji tace "My M, na bar maka kaci, daman na k'oshi " Ta k'arasa fad'i tana yatsina fuska, murmishi yayi tare da jan karan hancin ta yana cewa "Hmm da gaske kike habibty? " D'aga mishi gira tayi, nan ya d'an huro mata kiss da bakin shi, aikuwa ta lumshe idanun ta tare da bud'e su alamar ta kar6i sak'on nashi, lokaci d'aya suka sakarwa junan su murmishi. Mumy ma murmishin ta saki, zuciyar ta fal farinciki da kwanciyar hankalin d'an nata, kuma tana jin dad'in yanda Mufidah take bashi kula wa sosai. "Mumy ta bar min ba ashe ta k'oshi ma ta tsaya yi min rigima gashi har ya fara sanyi " "Hmm ka dai dame ta shi yasa ta bar maka " "Da gaske nake fah Mumy, koh Sweet baby? " "naji shikenan " Cewar Mumy, nan ya fara ci suna d'an ta6a hira har ya gama, ya sanya hannu zai janyo tissue ya goge bakin shi, da sauri Mufidah ta sanya hannu ta dauko mishi tissue paper d'in ta bashi, kar6a yayi tare da cewa "thank u habibty, Allah yayi miki albarka yasa ki haihu lafiya " Cikin jin dad'in addu'ar da yayi mata tace "Amin sweetheart ". Tashi yayi tare da cewa "Mumy yau na gaji, zan d'an je na huta kafin lokacin mangarib yayi " Gid'a kai Mumy tayi tare da cewa "Okay " Kallon Mufidah yayi suka had'a ido yayi mata alamar da ido ta taso su tafi, langa6e kai tayi tana nuna mishi Mumy na wurin, amman sai ya d'aga kafad'a alamar shi ina ruwan shi . Mumy tana kallon shi sai kawai ta tashi tana cewa "Mufidah ki tafi kema ki huta kin ji 'yata " Tana gama fad'in haka ta wuce kitchen, gwalo Musaddiq yayi mata don yana kula da kunyar da ta kamata, d'an hararar shi tayi irin ta wasan nan. "ta

Chapter 21 of 23