Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [13/11, 2:03 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *E.W.F* *BISSMILLAHIR RAHMANUR RAHIM* ( _Da sunan Allah mai rahma mai jin k'ai_). *Page 1* K'was K'was K'was k'arar takalmin ta ya karad'e cikin babban hall di'n da suke d'aukan lecture's, tun Kafin ta k'araso cikin hall di'n k'amshin turaren jikin ta ya cika cikin ajin, gaba d'aya kusan ilahirin student's di'n suka d'ago kansu tare da mayar da hankalin su kan mai Shigowar malamin da yake musu lecturing di'n shi kanshi jiran wacce mara kunyar ce take kok'arin shigo mishi aji bayan ya kafa dokar hana shiga cikin ajin indai ya riga d'aya daga cikin student d'in shiga. Kusan second biyar wata kyakykyawar yarinya ta bayyana cikin ajin kunnen ta mak'ale da waya tana faman tauna chewing gum a bakin ta tana amsa wayar, tana sanye cikin wani less cotton milk colour da touch d'in pink a jiki anyi mishi wani shegen d'inki riga da siket ta yafa wani k'aramin mayafi da takalmin ta hill dashi tasha heavy makeup kamar wata aljana, ta had'u iya had'u wa *MUFIDAH EL HUSSEIN* kenan, ko kallon inda malamin yake bata yi ba ta nufi inda ta sa ba xama cikin wata kakkausar murya taji ance " hey you get out!" Yanda ya buga tsawa shi yasa hankalin sauran d'aliban ya dawo kan malamin gaba d'ayan su a tsorace suke, wadda aka buga wa tsawar bata ma san me yake cewa ba sai da k'awar ta nabeelah ta xungure ta tare da yi mata alama da hannu, wani irin juyi tayi tare da bin shi da wani matsiyacin kallo. Shima cikin kallon wulakanci yake bin ta dashi tare da sake furta " i said get out don't west my time" Cikin muryar ta mai shegen dad'i da yanayin shagwa6a a cikin muryar tace "Ohh! dani kake wai? " Wata harara ya xabga mata tare da yi mata nuni da hannu kan ta fita don ya k'ulu iya k'ulu wa da yarinyar sosai ya fusata da abin da tayi mishi tuni fuskar shi ta yi ja saboda tsantsar 6acin rai, cikin isgili tace "sorry sir " Ta fad'i tana wani langa6e kai gefe tana Mishi irin wani kallo na raini, shi ma a wulakanci ya kalle ta tare da fad'in "idan baki fita wlh xan miki rashin mutunci " Hura hanci ta fara alamar kaxo gidan Indai rashin mutunci ne ta iya shi, ajin dai yayi tsit kamar ba mutane d'aliban sai faman raba ido suke tsakanin junan su da kuma mufidah da malam suna jiran ganin K'arshen dramar nan. Had'a ido mufidah tayi da nabeelah tayi mata alamar don Allah ta fita d'an hararar ta tayi kafin kuma ta fara tafiya alamar xata fita daga ajin, ta gaban shi ta shige tana tafiar kasaita bak'in ciki ya gama rufe shi ganin wannan K'aramar yarinyar tana kok'arin wulak'anta shi a gaban d'aliban shi da suke ganin mutuncin shi wani mtswww yaja wani uban tsaki tare da bin ta da harara kamar idon shi ya fad'o k'asa. Bayan fitar ta ya ma kasa cigaba da lecturing di'n saboda ranshi a matuk'ar 6ace yake, wani d'an tunani yayi na tsayin second uku take ya saki wani shegen murmishin mugunta nan ya rubuta musu test, nan cikin d'aliban ya d'uri ruwa don wlh basu xaci xai musu test yanxu ba, kowa jiki a sanyaye ya xaro paper da biro, yayin da nabilah ta d'ora hannu akai Shikenan yanxu wannan test d'in ta shige mufidah gashi tana bala'in tsoron malamin balle tayi mata hka jiki a sanyaye ta fara rubuta text d'in. Cikin mintuna talatin ya tattara test d'in yayi gaba a fusace fuskar nan babu alamar fara'a a cikin ta. Ta gaban mufidah ya shige da take xaune kan mota tana mak'ale da headphone tana sauraren wak'ar Justin Bieber ta love me love me har wani gid'a kai take saboda son wak'ar da take bata ma kula da shigewar shi ba idanun ta a lumshe suke. Tana cikin hka taji an doke ta a cinya da sauri ta bud'e idon tare da furta "wash Allah na nabilah me nayi miki? ", ta fad'i tana kallon nabilah da take hararar ta "baki da kirki k'awata yanxu kin kyauta abin da kika yi? "Cewar nabilah Mtswww mufidah ta saki tsaki tare da cewa "Wannan ke ya dama ba abin da ya dame ni " "baki da kyau k'awata ai kuwa kin fusata shi, gashi yayi test wlh " D'aga kafad'a mufidah tayi alamar ko ajikin ta Kafin tace "ae Allah sai na dai dai ta mishi sahu a skul d'in nan " Dariya suka tuntsire da ita tare da tafawa can mufidah ta sakko daga saman motar tare da cewa "mu ware koh nabilah? " "yes kamar Kinsan a gajiye nake " Daga hka suka shiga motar mufidah ta yiwa motar key suka fice daga skul d'in suna faman hira har sai da ta sauke nabila a gidan su tukunna ta shige nasu gidan. Tun Kafin ta k'araso dai dai get d'in take faman xuba uban horn don ta tsani jira, ai kuwa mai gadi cikin rawar jiki ya bud'e mata get d'in ta danna hancin motar xuwa cikin k'ayataccen gidan parking tayi sannan ta nufi cikin gidan. Belt door di'n gidan ta danna da sauri house girl din gidan taxo ta bud'e tare da russuna wa tace "Barka da dawo wa aunty " Cikin d'an murmishi tace "Yawwa saudat ki kawo min hollandian milk mai sauk'in sanyi " Cikin girmama wa saudat mai aiki tace "toh aunty " Sannan ta shige da sauri ta nufi kitchen, yayin da mufidah ta K'arasa cikin falon umman ta ta gani xaune tana kallon sunnah tv da sauri taje ta rungume ta tana cewa "i miss u umma nah " Cikin jin dad'i umma tace " i miss u too my sweetheart, ya skul?" "lau ummah " "Yayi kyau ina nabila" umma tace cikin murmishi, cikin murmishi ita ma mufidah tace "yanxu na sauke ta a gida tana gaida ke " "ina amsawa " A dai dai lokacin saudat ta kawo wa mufidah hollandian di'n sai da ta xuba mata tare da mik'a mata sannan ta bar wajen, tana sha suna cigaba da hira da umman tah............ Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:03 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *E.W.F* _wannan shafin sadaukarwa ce ga en exclusive writers forum Allah ya k'ara had'e kan mu ya k'ara mana basirah tare da dukka marubatan mu Ameeen_ *Page 2* A fusace ya tura kofar shiga palon gidan ko sallama a ciki ciki yayi ta ba lallai ma a ji ba ko kula da wad'anda suke xaune a falon bai yi ba ya fara hawa upstairs ya taka mattatakala ta biyu yaji ance "my bro wane ya ta6a min kai yau? " Cikin sauri ya jiyo aikuwa suka had'a ido da Yah sadeeq ai kuwa da sauri ya taho har da d'an had'a wa da gudu ya rungume yayan nashi wanda yau kusan tsayin Sati biyu rabon da su ga juna sai dai waya cikin tsananin murna yace "Yah sadeeq xuwan yaushe? " "xuwan shi kenan tun da ganin yayan na ka ka mance dani " Cewar mumyn su kenan da take xaune, sosa kai yayi cikin shagwa6a yace "Haba mumy taya xan manta da ke just ina farincikin ganin brother ne" Nan kuma suka 6arke da hira a tsakanin su irin ta yaya da k'anin shi xuciyoyin su cike da tarin farinciki duk da shi ranshi a 6ace yake game da abin da yarinyar nan tayi mishi, kuma ya d'auki alk'awarin sai ya wulak'anta ta. _Bayan k'wana biyu_ Yammaci sosai wajen misalin karfe 5 na yamma mufidah da nabilah suka yi parking a wani had'ad'd'an restaurant wanda yawancin suke cin kayan mak'ulashe a wajen don akwai su da shegen kwad'ayi, gashi restaurant ba irin abincin da babu shi anan shi yasa suke samun costumers ta ko'ina. Bayan sun xauna suna er hirar su har aka kawo musu abin da suke son ci bayan sun gama ci ne mufidah ta Kalli nabilah tace "yanxu karfe nawa ne don Allah? " "tabbb Kya tambaye ni bayan duk wayar namu na cikin mota "Cewar nabila Dafe goshi mufidah tayi tare da cewa "oh my god gashi ko watch bamu d'aura ba, don Allah kije ki d'auko mana " Hararar ta nabila tayi tare da cewa " lallai ma yarinyar nan ni zaki aika, idan kin matsu da ganin time d'in kije ki d'auko ko kuma mu tafi ae mun gama komai " D'an murgud'a baki mufidah tayi tare da cewa "kada ki d'auko di'n, kuma banyi ra'ayin tafiya yanxu ba " "toh ae shikenan daman ke kika matsu da ganin lokacin "fad'ar nabila tana kur6ar sansanyan juice di'n pineapple da yake gabanta cikin glass cup. Yayin da mufidah ta fara wurwurga idanun ta kan mutanen wajen, karaf idanun ta suka sauka kan wani kyakykyawan guy ya sunkuyar da kanshi yana kallon k'asa yana sanye cikin blue d'in jeans da red d'in T-shirt mai dogon hannu sosai guy d'in ya had'u ba k'arya duk da bata ga fuskar shi ba idanun tane ya sauka akan wayar dake hannun shi yana lallatsa wa ganin hka yasa mufidah mik'e wa tsaye tare da cewa "nabila bari naje wajen wancan guy d'in naga time Kinsan 5:40 nake son mu bar nan " Kafin nabila ta bata amsa tayi gaba kawai sai ta bita da kallo watak'ila tsokana xata yi Indai tsokana ce mufidah ta K'ware a wajen. K'arasa wa tayi wurin ba sallama ko irin excuse di'n nan kawai tasa hannu ta kar6i wayar daga hannun mutumin kamar ta tace bata kalli fuskar shi ba ta mayar da hankalin ta kan wayar don ganin time d'in. Shi kuwa wanda aka kar6ar wa waya cikin tsananin mamaki ya d'ago kanshi don ganin mai k'arfin halin nan ae kuwa idanun shi suka sauka a kan mufidah tuni ranshi ya 6aci sosai har wani rawa jikin shi yake, ko nabila dake xaune gefe ta tsorata da ganin yanayin yanda ya koma lokaci d'aya da yake idanun ta suna kan mufidah don ganin wa gurin wa xata. Kawai kafe ta yayi da ido wad'anda suka canja launi xuwa ja saboda 6acin rai *MUSADDIQ ABUBAKAR* kenan, tana gama duba time taga 5:35 kenan sauran mintuna biyar su tafi ta d'an yatsine fuska tukunna ta mik'a mishi wayar tare da kallon mutumin mai wayar ae kuwa suka had'a ido da malamin nasu wato musaddiq tuni hantar cikin mufidah ta kad'a amman ta d'aure tace "sorry sir ashe kai........." Kafin ta K'arasa fad'i taji saukar wani gigitaccen mari a kuncin ta dama da hagu wani k'ara ta saki lokaci d'aya don ba'a ta6a yi mata irin wannan axabbaben marin ba tuni hankalin mutanen wajen yayi kansu da sauri nabila ta K'arasa wajen ta rik'e mufidah cikin girmama wa tace "malam don Allah kayi hak'uri batasan kai ne ba please " Cikin tsawa yace "Kad'an ma kika gani tun da ke baki da tarbiyya xan koya miki ita stupid girl" Gama fad'in hka yayi gaba kallon Inda suke bai k'ara yi ba don baxai iya sake kai mata wani marin ba K'arshe ma ya fice daga wajen gaba d'aya. Nabila taja hannun mufidah suka fice daga wurin in ban da kuka babu abin da mufidah take fuskar nan taji jawur da ita hka ma idanun ta wad'anda suka kumbura saboda kuka don ba k'aramin maru wa tayi hannun musaddiq ba, rarrashin ta take yi nabila kan tayi hak'uri tayi shiru cikin tsananin takaici ta d'ago kanta ta kalli nabila tace "hak'uri kika ce fah nayi toh wlh sai na rama ko bata hanyar mari ba ni nasan abin da xan mishi " Cikin mamaki nabila tace "oh yanxu baxa ki hak'uri ba da ganin guy d'in nan bashi da kirki fa" Juyar da kai mufidah tayi bata k'ara magana ba hka ita ma nabila sai da ta sauke nabila a gida kamar kullum sannan taja motar xuwa gida yau duk ma'aikatan gidan sun fuskanci an ta6a er lelen Abba da Mumy ganin duk Sannun da xuwan da suke mata bata kalli su ba balle susa ran amsa musu, wata ajiyar xuciya ta saki lokacin da ta shiga falon taga umma bata nan d'akin ta ta wuce da sauri tana xuwa kan gado ta fad'a sai lokacin ma wani kukan ya xo mata xuciyar ta tana ingixa ta kan me yasa bata rama marin ba har ta barshi ya tafi nan ta fara sak'e sak'en yanda xata rama abin da musaddiq yayi mata. _Washe gari_ Karfe 10 na safe ta gama shirin ta tsaf na tafiya skul wata swiss atampha kalar bak'i da blue ta sanya d'inkin doguwar riga ce ba k'aramin kar6ar kayan jikin ta yayi ba sai tayi light make up bata d'aura d'ankwalin ba don ita ba ma'abociyar son d'ankwali bace sai ta samu veil blue tayi rolling d'in kanta da shi sannan ta fesa different perfumes a jikin ta sannan ta d'auki bag d'in ta wanda yta xuba tarkacen hand out a ciki sai wayar ta da key di'n mota a hannun ta, palo ta fito ta tarar da umma tana xaune tana karanta jarida rungume ta tayi tare da bata peck a kumatu tana cewa "Gud morning umma nah" "morning dota kin tashi lafia?" "Qlau umma nah, ina Abba nah kuma? " "ya fita yanxu " Cikin shagwa6a tace "shine ya fita bai tsaya mun gaisa ba" Dariya umma tayi tare da cewa "kiran gaggawa akayi mishi amman ya lek'a bedroom d'in naki ya tarar sai bacci kike " D'an murmishi tayi tare da cewa "Allah sarki abbana Allah ya barmin ku" "Ameeen " Cikin sauri ta kammala breakfast d'in sannan tayi wa umma sallama ta tafi skul duk jikin ta ba dad'i sakamakon nabila da ta kirawo ta baxa ta samu damar xuwa skul d'in ba bata jin dad'in jikin ta, hka ta K'arasa skul d'in bayan ta gama d'aukan lecture's ta fito tana xaune a saman motar ta suna waya da abban ta adai dai lokacin musaddiq yake kok'arin shiga motar shi kunnen shi mak'ale da waya alamar waya yake da yake taxarar su da inda suka yi parking ba nisa sai taji yana cewa "kada ka damu gani nan xuwa brother " Mufidah ta fara tunanin ko ta bishi ta rama abin da yayi mata bata ankara ba taji ya tashi motar tare da yin gaba da sauri ta dira daga motar ta shige ta ta ita ma ta bishi a baya. Wani shegen murmishin mugunta ta saki ganin wannan restaurant d'in da ya mare ta jiya yayi parking ita ma parking tayi tare da shigewa ciki amman sai bayan ya shige, cikin mamaki tnake bin mufidah da kallo maimakon naga ta wuce ta samu waje ta xauna sai naga ta nufi wajen masu ba da abinci taja wani gefe cikin harshen turanci take ce mishi ya fad'a mata kalolin abincin Chinese food nan kuwa ya dunga fad'a mata su a ciki ta xa6i wani kalar abincin tace mishi "ka ga wancan mai ash d'in t-shirt di'n xaka kai mishi" Cikin rashin yarda yace "ae bai fad'a mana abin da xamu kai mishi ba? " er dariya mufidah tayi tare da xaro kud'i wajen 10k tace "idan har ka kai mishi abincin nan to wannan kud'in ya xama naka " Nan take cikin rawar jiki ya amince ae kuwa ta damk'a mishi kud'in cikin rawar jiki yaje ya had'o abincin ya kawo wa mufidah don ta gani da sauri ta juyar da kanta ganin abincin har sai da taji xuciyar ta na tashi da sauri tayi mishi alama da ya kai mishi ai kuwa ya rufe ya doshi table d'in da musaddiq da yah sadeeq suke xaune suna hirar su cikin kwanciyar hankali. Ajiye abincin yayi kuwa a gaban musaddiq sannan ya tafi ganin ya bud'e plate di'n abincin yasa spoon a cikin abincin yana kok'arin sa spoon di'n acikin bakin shi hankalin shi gaba d'aya yana kan waya yaxo dai dai bakin shi xai xuba ya d'ago don ganin kalar ma abincin da aka kawo mishi ganin abin da yake kok'arin sawa a baki ne yasa shi sakin ihu tare da wurgar da spoon di'n ya fara kakarin amai, da sauri Yah sadeeq ya juyo da kallon shi kan musaddiq ganin abin da ke faruwa yasa shi furta "subhannallah musaddiq me yake faru wa " ganin yanda ya ke kakarin amai yana rik'e da cikin shi............... Aishat A muh'd ✍🏻 [13/11, 2:03 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE*🌲 *written by* Aishat A muh'd ♻ *E.W.F* _A gaskia bani da bakin godia gare ku en exclusive saboda kunyi min abin da naji dad'in,a gaskia ku mutane ne masu hankali da ilimi tare da sanin ya kamata jinjinar ban girma gare ku Allah ya k'ara kare min ku, Allah ya k'ara had'e kan mu daman can mu tsintsiya mad'aurin ki d'aya ne,ina son ku sosai_😻 *my Sumayya salees sadeeq (sumynbash)* _bani da kalaman godia a gare ki hak'ik'a ke masoyiya ta ce Allah ya bar xumunci ameeen_❤ *Page 3* Da sauri Yah sadeeq ya juyo da kallon shi kan musaddiq ganin abin da yake yake faruwa yasa shi furta "subhannallah musaddiq me yake faru wa ? " Ganin yanda yake kakarin amai da rik'e ciki. Ina musaddiq bai masan me yake cewa ba don gaba d'aya ya fara fita a hayyacin shi saboda kakarin aman da yake, gaba d'aya Yah sadeeq ya rud'e nan fah hankalin mutanen da suke xaune ya dawo kansu sai kallon su ake cike da tausayi a fuskar su suna tunanin ko bai da lafia ne. A hankali aman ya lafa mishi Yah sadeeq ya taimaka mishi ya xauna kan kujera yana mishi sannu sake had'a ido musaddiq yayi da abincin ai baisan lokacin da wurgar da plate di'n ba abincin ya xube a k'asa plate di'n ma bai tsira ba sai da ya fashe,ruwa Yah sadeeq ya miko wa musaddiq ya kar6a tare da sha sai da ya shanye ruwan sannan ya ajiye cup d'in tare da lumshe ido yana faman sauke ajiyar xuciya gaba d'aya fuskar shi da idanun shi sunyi ja saboda wahalar da yasha wajen kakarin aman. Sai lokacin Yah sadeeq hankalin shi ya kwanta har ya fuskanci abin da yasa musaddiq cikin wannan yanayin dariya ya tuntsire da ita saboda yasan sarai k'anin nashi akwai shegen tsantsami cikin dariya yace "Haba musaddiq akan wannan abin ka wahalar da kan ka ji yanda ka koma " Kafin musaddiq yayi magana wanda ya kawo abincin nan ya xo wurin ae kuwa Kafin ya ankara musaddiq ya kife shi da wani wawan mari Wanda har yasa ki kusan fad'u wa k'asa tuni mutumin ya rikice durkusa wa yayi a k'asa yana cewa "I'm sorry sir wlh sa ni akayi " Da yake ya gama tsorata da marin da musaddiq yayi mishi, da har ya d'aga hannu xai sake marin shi sai ya dakata jin wannan maganar da yayi cikin 6acin rai musaddiq yace "what! uban wa ya saka? " Cikin rawar jiki ya nuna Inda mufidah take tsaye tana shek'a dariyar mugunta amman sai dai me wayam ba kowa, da sauri musaddiq ya tashi tare da fita a wajen don da alama wanda yasa a yi mishi wannan iskancin bai yi nisa ba, da sauri shi ma yah sadeeq ya rufa mishi baya cike da tarin tambayoyi a xuciyar shi to shin wane yasa ayi wa k'anin shi wannan wulakancin. Suna fito wa farfajiyar restaurant d'in nan ma basu ga kowa ba hkan ya tabbatar da wanda yasa ayi hkan ya gudu daga wurin nan fah bak'in ciki ya rufe musaddiq yaso ace ya ga d'an iskan da yasa ayi mishi hka da yau kashe shi ne kawai baxai yi ba, nan dai Yah sadeeq ya lalla6a shi suka bar wajen. Mufidah kuwa duk abin da ke faruwa ta na gani kuma taci dariya har da hawayen ta ganin a mari wannan mai kawo abincin yasa ta 6uya don hka shi yasa lokacin da ya nuna wajen musaddiq bai ga kowa ba, tana ganin sun fita ita ma ta fito daga wurin motar ta ta shiga kai tsaye gidan su nabila k'awar ta ta nufa bayan tayi parking ne ta nufi ainahin kofar da xata sada ka da cikin gidan. Da sallama ta shiga umman nabila da take tsaye 6angaren dinning table tana shirya abinci akai ta jiyo tare da amsa sallamar ganin mufidah ce yasa ta fad'ad'a fuskar ta da fara'a tare da cewa "Oyoyo my daughter, baki da kirki mufidah yaushe rabon ki da shigowa cikin gidan nan sai dai ki sauke nabila a bakin gate " Umman nabila ta fad'a cikin wasa, Murmishi mufidah tayi tare da kama kunnen ta tace "sorry ammin mu na tuba na dai na" Dariya umman nabila tayi tare da cewa "Okay shikenan ya wuce sauran ki k'ara " Da sauri mufidah tace "baxan ma k'ara ba Insha Allah ammi " Dariya suka yi gaba d'ayan su sannan umman tace "Allah yasa hka ne, ina umman taki ?" "tana gida " Sai a lokacin suka gaisa tukunna ta nufi bedroom d'in nabila a gaban dressing mirror ta same ta tana shirya wa alamar fitowar ta daga wanka kenan nan fah suka sakar wa junan su murmishi sannan mufidah ta xauna gefen bed tana cire mayafin da tayi rolling d'in kanta ta furta "wash Allah na nayi matuk'ar gajiya yau " Cikin mamaki nabila tace "gajiyar me kuma? " "yanxu dai ya jikin na ki? " "ah na samu lafia daman fah ciwon kai ne na tashi dashi " "Ayyah Allah ya k'ara sauk'i sannu " Cewar mufidah "Ameeen

Chapter 1 of 23