Reading Dauɗar Gora by Bilyn Abdull ce Chapter 9 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tabi da kallo, kafin ta
fara mata bayanin komai har yanzu hawayenta sun kasa
tsayawa. Sosai hankalin Malikat ya ƙara tashi, sai dai
kamewarta yasa ba lallai ka fahimta a kan fuskarta ba. Cikin
takunta na ƙasaita ta isa gaban gadon inda Iffah take. Kwance
take samɓal tamkar ba itace ta gama buge-buge ba yanzun.
Idanu ta tsura mata a karan farko, yarinya ce ƙarama sosai
kuma ƙyaƙyƙyawa matuƙa, duk da halin ciwo da take ciki da
canjawar fatar jikinta ƙyawunta da kwarjininta basu gushe ba,
tausayinta mai tsanani da ƙaunarta suka sake ratsa zuciyarta.
Zaune ta kai gefen gadon ta kai hannu ta shafa yalwataccen
gashin Iffah daya gama bajewa a kan filon.
“Ibnati kiyi haƙuri zaki samu lafiya bazasu taɓa samun
galaba ba kinji”.
Iffah da sarai take jin maganar Malikat dan ba barci take ba
azaba ce kawai ke ratsata tai murmushin ƙarfin hali a
zuciyarta, a karan farko taji ƙaunar matar a ranta da sake
ganin kima da girmanta.......

★★_______★★

“Sun jiƙa mana aiki! Sun ɓata mana shiri! Ya ƙwace mana
damarmu wadda sake samun samuwarta a garemu cikin
sauƙi haka zata iya zame mana mai wahala!!”.
Kakkausar muryar Uwa mai matuƙar rashin daɗin saurare
ta fara karaɗe ɗakin cikin amon sauti mai tashi sama. A firgice
ta miƙe a zabure tare da zube gwuyawunta ƙasa jikinta na
tsuma dan dama zaune take ido biyu tana jiran tsammani. “A
gafarce ni uwa ba laifina bane, ni kaina ina cikin damuwar
tangarɗar da aka samu”.
“Bana buƙatar jin komai daga gareki Taƙurya. Domin
sakacinki ne ya jawo hakan. Nasha faɗa miki ki san suwa zaki
bama aikin da ke bazaki iya yinsa kai tsaye ba. Su kuma
waɗan can sakarkarun barinsu sukai wayewar gari tamkar
rasa sauran damar data rage miki ne....”
Ɗan zabura tayi da nufin cewa wani abu, sai dai tamkar
walƙiya Uwa ta ɓace a ɗakin. Hakan na nufin ranta a ɓace
yake. Itama kanta ta dafe nata ran na suya da ƙara girmamar
baƙin cikinta. Miyasa kowa bai bata matsala ba sai wannan
ƴar shilar yarinyar da bata wuce sauron gidanta ba da feshi
ɗaya take kawar da shi. Zuciyarta ta fara raya mata Uwa
kodai tsoron yarinyar nan takeyi, yo inba tsoro ba taya zata
dinga wani gewaye-gewaye bayan bai wuce da ƙyaftawar ido
kawai ta shafe babin rayuwarta ba. Dama mutum na gagarar
aljani ne banda ta fara maidata susu......


WASHE GARI..

Duk wanda ya kwana ya tashi a masarauta a yau ya tashi ne
da tashin hankalin da yafi na jiya sakamakon mawuyacin
yanayin da Iffah ta wayi gari. Dole tun gabatowar sallar asuba
aka maidata cikin clinic ɗin dake a masarautar saboda
ɓallewar jini ta kowane sashe na jikinta. Da farko aman jini ta
fara, sai kuma ta hancinta, sai gashi ta ido da kunne harda ma
ramin cibiyarta. Hankalin Jasrah da Malikat dake tare da ita
ya kai matuƙar ƙololuwar tashi. Duk da kowa yasan ciwo ne
bana asibiti ba haka likitoci suka rufu a kanta domin ƙoƙarin
ganin sun tsaida jinin amma abu na neman gagara. Har kusan
goma na safe a gogon ƙasar babu wani cigaba, jikin Iffah ma
ya fara saki alamar jininta yayi ƙasa matuƙa....

★★...

“Bari-Hamshira! Inaga ya kamata a bama masu maganin
dake waje dama suma suzo su gwada sa'arsu tunda ba'a dace
dana cikin masarauta ba.”
Malikat da damuwar duniya ta tattaro a kanta yau ko
fadarta bata iya fitaba tana cikin ɗakin barcinta har zuwa
yanzu ta ɗago idanunta dake jajur ta sauke akan ƙanwarta ta
uku mai suna Zaimah, cikin nuna sallamawa ta jinjina kanta.
“Wannan ma shawara ce mai ƙyau Akia, ruɗewa tasa sam
wannan tunanin bai zomin ba. A sanar da Ghazi su faɗama
Baba Yaro. Sai dai komai ya kasance cikin sirri da amana dan
kar maƙiyanmu suyi amfani da wannan damar wajen ruguza
ɗan sauran ƙwarin gwiwar mu akan wannan yarinya”.
Kai Zaimah ta jinjina mata, sai kuma ta miƙe da hanzari
domin isar da umarnin.....

*_ƘAUYEN JUMNA_*

Tafiya saurayin yake tamkar zai tashi sama dan gaggawa,
wani lokacin har tuntuɓe yakanci sai dai kafin ya kai ƙasa yay
azamar taro kansa ta hanyar dafe duk abinda ke kusa da shi.
Wurjanjan ya isa ƙofar gidan Dattijon da kowa yafi sani da
suna Abu Huzaifah ya kwaɗa sallama da iya ƙarfin muryarsa
har sau huɗu babu ko jiran a amsa masa.
Dattijo Abu Huzaifah Da mukafi sani da Kaka ya dakata
da ga ɗinkin kwalliyar doki daya duƙufa yi ya dago suka kalla
juna da Iyyani dake shara a tsakar gidan. “Kamarfa sallama
naji Abu Jamaima a ƙofar gidan nan”
Kafaɗa yaɗan rausayar gefe da ajiye zungureriyar allurar
da yake ɗinkin da ita. Kafin ya ce wani abu aka ƙara zungura
sallamar a jajjere tamkar yaƙi. Kansa ya ƙara jijjigawa ya miƙe
dajan tsaki. “Kai wasu dai mutanen sam basu da lissafi, irin
wannan ai saka ɗauka tashin hankali ne”. Kaka ya faɗa cikin
mita yana gyara takalmansa. Iyyani da takaici ya ƙulle itama
ta bisa da kallo harya fice a soron gidan...
“Ayyub! dama kai ne kake ƙwaɗa irin wannan sallama
haka? Lafiya dai ko?”.
“Da sauƙi dai Baba, amma amin afuwa bani da wani zaɓi
bayan hakan. Saƙone daga Baba yaro”. Ya ƙare maganar da
miƙama Kaka takardar hanunsa. Kaka ya amsa takardar yana
ɗan juyata, sai kuma ya nuna hanyar shiga da faɗin, “Kaga
shigo daga ciki”.
A tare suka shiga cikin gidan, Kaka ya buɗe takarda yana
dubawa, yayinda Iyyani ta kawoma baƙo dake gaisheta ruwa.
Kaka ya ɗan murmusa bayan gama karanta takarda tare da
girgiza kansa. “Ayyub naga saƙo, sai dai kuma inaga basai
naje da kaina ba. Zan baka saƙo ka kai masa nima. Ita kuma
ALLAH ya bata lafiya yasa ya zama kaffara a gareta”.
Ɗan jimm Ayyub yayi, sai dai kafin yace wani abu Kaka ya
miƙe. Ɗakinsa ya shiga, kusan mintuna ashirin sai gashi ya fito
da wata jakkar fata. “Kayi maza ka kai masa wannan. Kace
kuma ina gaishesa”.
Cike da girmamawa Ayyub ya amsa da faɗin “Angama
Baba. A huta lafiya”. Kai kawai Kaka ya jinjina masa yana
murmushi. Sai da ya rakasa har ƙofar gida sannan ya dawo.
Iyyani da duk ta shiga damuwa ko zama baiyiba ta jeho masa
tambaya, dan tasan ma'anar wannan murmushin nasa bana
farin ciki bane, yakan yisane a lokacin da wani abu ke masa
ƙuna a zuciya.
“Itama sun taɓata ko?”.
Bai bata amsa ba sai da ya zauna. Ya jawo allurarsa zai
cigaba da ɗinkinsa. “Dama ai bazasu barta haka ba saboda
wasu dalilai”.
“Dalilai kuma? Nami to?”.
“Kinga sarkin tambaya bani zaren cen dana manta kan bunu”.
Iyyani tasan tambayarce baya son amsa mata, dan haka
taja bakinta tai shiru bayan ta kawo masa zaren. Sai dai sam
zuciyarta babu nutsuwa......


★★.MASARAUTA.★★
Bayan sallar azhar Ayyub ya iso masarauta. Zuwa yanzun
har an fara raɗe raɗin mutuwar Iffah, duk da kuwa ya tadda
masu maganin da suka isa suka tumbatsa da matuƙar yawa
an tarasu kowa nata gwada ƙoƙarinsa da baiwar da ALLAH ya
basa.
Baba Yayaroya furzar da nannauyan numfashi bayan ya
amshi saƙon kaka a hanun Ayyub “Dama nasan da wuya
Dattijo ya zo”.
“Amma duk da haka ka aika masa Baba?”.
“Ya cancanci a aika masan”.
“To amma miyasa yaƙi zuwa? Bayan kuma alamu sun nuna
kai tsaye ma yasan abinda ke faruwa anan ɗin”.
Baba ya tsurama ɗan nasa ido na wasu sakanni, sai kuma
ya girgiza kansa. “Ba lallai sani irin wanda kake tunani yayi ba.
Dan nidai nasan baida wata alaƙa da abinda ke faruwa anan.
Sai dai ya sani ta dalilin baiwar da ALLAH ya masa duk da shi
yana gudunta ne”.
“Amma Baba....”
“Kaga Ayyub wannan ba lokacin tambayoyi bane. Bara naje
muga ko za'a dace anan.”
Da kallo Ayyub yabi mahaifin nasa. Sai dai ƙasan ransa fal
tambayoyine da yasan samun amsarsu zaiyi wuya a lokacin
da yake buƙata. Yasan mahaifinsa gawurtaccen masanin
magani ne irin na gargajiya dama na gusar da junnu.
Shahararsa tasa Daular Ruman ɗaukarsa da bashi matsayin
(Mai magani a gonar yaro) amma ya rasa minene dalilinsa na
bama wancan dattijon girma mai tsanani duk da shi kowa bai
sanshi ba sai da sunan mai ɗinka kayan doki.....

*_ZAWJATA-ALMILKI_*
Zuwa yanzu numfashin Iffah ma yana fitane da taimakon
na'urori, yayinda jinin dake fita a jikinta har yanzu yake fita ta
kunenta. Na ido da hanci da baki ne kawai likitoci suka samu
nasarar tsaidawa. Baba yaro shine shugaba na masu
maganin, dan haka ake basa damar shiga kai maganin da duk
aka bayar dan ai mata amma da taimakon Jasrah kai tsaye.
Yanzu ɗinma dai hakance ta kasance. Bayan neman iso aka
bashi iznin shiga inda Iffah take, sai dai babu mai iya ganinta
kasancewar zagaye take da glass.....

*_SHAHAN-SHAN_*

Bani kaɗai ba, nasan duk masu karatu tambayarsu zata
rinjayane akan wai shin duk abin nan dake faruwa ina
_Shahan-shan_ yake ne a matsayinsa na shugaba ga ƙasar
ruman baki ɗaya bama daular ruman ba?. To amsar itace
yana nan a cikin masarautar, sai dai kuma tun a yammacin
jiya bayan dawowa daga sallar juma'a babu wanda ya sakejin
motsinsa. Duk da dama fitarsa a zahiri ta zuwa massallaci ce
kawai. Yana kuma da ƙofar dake kaisa har massallaci daga
sashensa batare daya fito wani ya gansa kai tsaye a
masarautar ba. Shiyyasa har zuwa yanzu wanda suka san
fuskarsa ko'a cikin masarautar ma ƙalilanne musamman a
cikin hadimai. Duk abinda ke faruwa a masarautar kuma
kowa nada yaƙinin ya sani, sai dai ba'an miyasa ya zaɓi yin
shiru ba.
Kamar jiya yau ma labari yajema Malikat Bushirat akan
Shahan-shan bai fito sallaba har ta asubahi. A yanzu kam
hankalinta ya tashi ba kamar a jiya ba data ɗauka dan yana
fushi da auren da yaso bijiremawa ne. A take ta bada
umarnin shirya mata zama da shi. Dan ita a karan kanta na
uwa garesa bata da hurumin ganinsa a duk sanda taso ko kai
tsaye bisa doka da al'adar masarauta da ƙarfin iko na Shahan-
shan. Sai zuwa ɗaya tak na kowanne wata da yakanyi kawai
na zahiri. Amma duk da haka Tajwar Eshaan kan saci jiki wani
lokacin ya kawo mata ziyarar tsakkiyar dare cikin ɓadda kama
batare da wani ya taɓa fahimtaba har yanzu a cikin
masarautar.
Shiri ta farayi duk da batada tabbacin samun damar ganin
nasa a yanzu, sai dai sanin duk ƴan majalissar fada na'a
masarautar yau yasa bata fidda tsammani ba. Cikin sa'a kuwa
cikin abinda baifi mintuna ashirin ba Ghazi ya zo ya isar mata
da sakon ƙarɓuwar buƙatarta. Dan dama suma ƴan majalisar
fadan nada buƙatar samun wanda zai duba shi, hakan kuma
bamai yuwuwa bane dan ita dake amsa suna mahaifiyarsa da
Malikat Haseena (Kakarsa) da matansa ne kawai ke da
wannan hurumin saboda an tabbatar tun jiya baiko zo falo na
uku ba. Sannan duk abincin da mai dafa masa ya shirya tun
daga kan na daren jiya har safiyar yau da rana haka yake
zuwa ya kwashesa ba'a taɓa ba.
Cikin shiri na alfarma da rakkiyar tawagar hadimai maza
da mata Malikat Bushirat ta doshi sashen Tajwar Eshaan ibn
Haysam Abdull-majeed.........✍

18


..........Tuni labari ya kai kunnuwan sauran matan gidan
musamman Malikat Ashwaq da Ameera Danish-Ara da
Ameera Haifah cewar Malikat Bushirat ta ziyarci Shahan-shan
saboda rashin jin motsinsa. Hakama wasu a cikin matan
manyan masu faɗa aji a gidan harma da mazan, wasu iyaye,
wasu ƴaƴa, wasu jikoki. Hakan yasa aka kafa gungu-gungu na
cigaba da tattaunawa tare da sukar cewar yasan tsiyar daya
aikata ai shiyyasa ya ɓoye kansa. Kokuma dodon tsafin nasa
ne ya bashi wannan umarnin naƙin fitowa har sai yarinyar
mutane ta mutu... Wasu kuwa murmushine kawai nasu dan
su kaɗai suka san kansu. Yayinda wasu ke tausayama Tajwar
Eshaan ɗin da ganin abubuwa ne suka masa zafi da yawa dan
suna kallon komai a matsayin makirci da mafi yawa akafi
dangantashi da matan ubansa, da kuma ƴan uwan mahaifin
nasa na jini masu zawarcin son hawa wannan kujera... (To
koma dai miye ALLAHU shine mafi sani).

Duk inda ta gitta hadimai zubewa suke akan
gwuyawunsu suna miƙa gaisuwa. Ko sau ɗaya bata ɗaga ido
ta kalla kowa ba, sai hadimanta ne ke amsawa duk wanda yay
gaisuwar. Tun'a harabar shiga sashen dukkanin hadimanta
suka dakata. Sashen Shahan-shan shine mafi ƙyawu da
ƙawatuwa na ƙyale-ƙyale a daular ruman. Gini ne da kusan
zamuce an yisa da zallar gilashi. Yanada hawa huɗu dan haka
sai da lifter. Zaman lissafin dukiya da daular da aka zuba a
cikinsa da kuma ainahin fadar da Shahan-shan ke zaman
fadanci ma ɓata lokacine. A lokuta da dama duk abinda ke
faruwa a cikin masarauta Tajwar na kallo daga cikin sashensa
musamman idan a hawa na ƙarshe yake, hatta da wajen
masarauta yana iya hangowa. Hadiman dake tsaron sashen
matsayin sojoji suka maye gurbinsu wajen take mata baya
har falon farko. Anan ɗin ma hadiman zubewa suka dingayi
ƙasa kawunansu a risine domin girmamawa a gareta har
zuwa falon farko. Wanda suka rakota ciki suka dakata, na
falon farkon dake a hawa na ɗaya suka take mata baya har
zuwa falo na biyu a hawa na biyu, suma iyakarsu nan, wanda
suke a falo na biyu sukai mata rakkiya har zuwa falo na uku
dake a hawa na uku. Anan soja ɗaya ne, shine amintacce da
yake iya haurawa har zuwa falo na huɗu hawa na huɗu a
falon dake can. Anan ma akwai hadimi ƙwara ɗaya sai masu
dafa masa abinci su biyu suma. Sune amintattun na ƙarshe
dake iya zuwa hawa na can ƙarshe na huɗu kenan, suke iya
ganin Tajwar kai tsaye kuma, suke iya sanin a wane ɗaki ya
kwana, suke iya shiga ɗakin barcinsa suyi gyara ko kai abinda
yake buƙata, ko isar da wani saƙo. Bayan gaisuwa a gareta
Ghazi ya nema afuwa da bashi damar zuwa nema mata iso ga
Tajwar. Hannu kawai ta iya ɗaga masa.
Mintuna da basu wuce huɗu da shigar tasa ba ya dawo ya
zube a gabanta. “ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsahon rai mai
amfani, shugaba ya bada damar shiga dake har ciki”. Shiru tai
kamar bazata motsa ba, dan a duk sanda ta kama zasu gana
anan sashensa yakan fito ne su haɗu a wannan falon ko
ƙaramin falon hutawarsa dake a hawa na uku. Wannan kuwa
a ƙa'ida ko matarsa bata shigarsa, dan haka jin wannan
amasa yasata fahimtar akwai matsalar da gaske.
Bayan buɗe mata ƙofa Ghazi yaja da baya. Cikin takunta
na ƙasaita da isa ta ƙarasa shiga cikin matsakaicin falon mai
fidda wani irin ƙamshi da wadataccen sanyin na'urar ac.
Rashin girman falon ba komai bane, haɗuwarsa da
tsaruwarsa ce mafi ɗaukar hankalin mai kallo. Dan an
ƙawatashine da wasu irin tausasan tumtum na ainahin
sarakan asali, dardumar falon kanta abin kallo ce, komai ya
tsaru dai-dai da tsaruwar manyan mutane. A hankali takai
zaune tana mai sauke ajiyar zuciya, sosai takejin matuƙar
kewar gudan jinin nata, sai dai tsarin masarautar tasu ya
tilasta mata haƙura akan dole tamkar kowace uwa ta Tajwar
irinta da akai a cikin wannan daula....
Motsin buɗe ƙofa da ƙamshin turarensa mai rige-rigen
isowa hancinta da sautin takumsa ya sata ɗago ƙyawawan
idanunta ta sauke a kansa. A hankali ya cigaba da takowa
cikin ƙasaita da nutsuwa har ya ƙaraso gareta. Daga tsayen da
yake ya ɗan risinar da kansa alamar girmamawa. “Amincin
ALLAH ya tabbata a gareki *_Ammie!_*”. Nutsatstsiyar
muryarsa mai zurfi da rashin hayaniya ta fita a fisge, dan
yanda ya motsa lips ɗinsa a hankali zama ka iya ɗauka bashi
yay maganar ba. A hankali ta sauke ajiyar zuciya mai haɗe da
nannauyan numfashi ta jinjina kanta da lumshe idanunta ta
buɗe a kansa alamar amsawa. A nutse ya kai zaune a gefenta,
yay zama irin na ƙasaita da kame kai da kuma girmamawa a
gareta matsayin mahaifiya. Hanunta ta ɗaura bisa tattausar
sumar dake kansa kwance, tare da ɗan ranƙwafawa ta
sumbaci goshinsa da yay zafi zau alamar baida lafiya.
Lumsassun idanunsa da ƙanƙancewarsu ya hanata ganin
hasken cikinsu ya buɗe, ya motsa lips ɗinsa kaɗan alamar
murmushi a gareta. Murmushin ta saki itama a karo na farko
da gyara zamanta na ƙasaita.
“Kaima amincin ALLAH ya tabbata a gareka *Bugun zuciyar
Ammie'n sa*”.
Ɗan luuu yay da idanunsa ya lumshesu tare da sake
buɗewa a kanta da ɗan risinar da kai na girmamawa. Sai
kuma ya kamo hanunta data janye a saman sumar kansa ya
sumbata. Ajiyar zuciya ta sake saukewa mai kauri da jin ƙarin
ƙaunar tilon gudan jinin nata da maƙiya suka sako a gaba.
Tana matuƙar ƙishirwar rashin ganinsa a kusa da ita ko
yaushe, sai dai babu yanda ta'iyane.....
“Ammie kina lafiya?”.
Ya katse mata tunanin da take neman yin nisa a ciki.
Numfashi ta ɗan fisga ta fesar alamar dawowa. Sai kuma ta
girgiza kanta da raunana fuskarta. “Kasancewarka lafiya itace
tawa Saiful-mulk”.
A karo na biyu ya saki murmushi yana ɗan jinjina kansa
shima, sai kuma ya ɗago ya ɗan kalleta ya kauda kai. “Ina
lafiya Ammie”.
“Ni ba haka na gani a cikin idanunka ba *_Negar_*”.
Baice komaiba kusan minti ɗaya, hakan ya fahintar da
ita bazai ce ɗin ba, tai murmushi kawai tana kaɗa kanta. Ta
yarda jinin mulki gaskiya ne, dan tana ganinsa yana yawo a
cikin gudan jininta. Duk ƙasaita da miskilanci irin na Tajwar
Haysam da ita kanta da ake faɗi Eshaan ɗinta ya takasu ya
shanye. Irin miskalayen mutanen nan ne shi masu matukar
ban mamaki da wuyar sha'ani, dan kai tsaye baka isa gane
ainahinsu ba balle farin cikinsu ko damuwarsu kai tsaye, a
matsayinta na mahaifiya a garesa da ake ganin yafi sakewa da
ita fiye da kowa sukanyi zaman awa guda bai firta jimlar
magana sau goma ba, murmushi kam ita da Malikat
Haseenah kawai ke gani daga garesa sai mahaifinsa kafin
yabar duniya......
Lurar da yay tayi nisa a tunani ya sashi kai hannunsa cikin
ƙyaƙyƙyawan bowl ɗin da aka cuɗa dabino da zuba ya ɗakko
tsagin dabino ɗaya daya naɗi zuma yay luntsum, ya tare da
ɗayan hanunsa ya kai bakinta. A hankali taja numfashi ta
sauke alamar dawowa. Babu musu ta matso tare da buɗe
bakin ya saka mata. Sai da ta cinye a nutse tana mai kallonsa
da murmushi sannan itama ta ɗauka kamar yanda ya bata ta
bashi har sau uku. Tasan yunwa yake ji, amma yaƙi cin komai
saboda damuwa. Tun yana yaro haka yake, a duk sanda
sukaje dubashi a inda ya girma ita da Tajwar Haysam ta
wannan hanyar take gane yanada damuwa, ko kuma yana
fushi. Dan in har yana jin yunwa yaƙi cin abinci suka matsa
masa akan yaci zai ɗiba abincin ya saka a bakinsu, sukuma
hakan da yayi zai nusashesu zama su bashi da kansu har sai
ya ƙoshi. Tissue tasa ta goge masa bakinsa idonta dake kansa
na cika da ƙwalla.
“Kanajin yuwa Negar?”.
Gajeren murmushisa ya sakar mata da kauda kansa gefe
maimakon amsar data buƙaci ji daga garesa. Itama bata sake
cewa komaiba, sai wayar landline dake gefensa ta ɗauka.
(Inba akan Tajwar Eshaan ba waya isa ganin Malikat Bushirat
a haka😑). Cikin ƙanƙanin lokaci aka iso da abinda ta buƙata.
Shi dai kallonta yake a harɗe kamar yanda itama take zaune a
harɗen. Abincine na musamman, wanda tasan shine mafi
soyuwa a garesa...
“Idan kana zama da yunwa bazan yafema kaina ba”.
Idanunsa yay kamar zai rufe sai kuma ya buɗe a kanta.
Ƙasaita jininsa ce, kamewa da tsumewa nagartarsa ce.
Kwarjini da cikar haiba mutuncinsa ne. Miskilanci gadonsa ne.
inba ita ɗin bama wake ganin murmushin kojin furucin
bakinsa, dan babu abu mafi wahala da girma ga Tajwar
Eshaan kamar magana. Dariya kam ko'ita a karan kanta zata
iya rantsuwa bata taɓa gani ba tunda ba'a gabanta ya tashi
ba, sai lokaci-lokaci suke zuwa su gansa.
Abincin ta haɗa masa a gabansa da kanta, babu musu
kuwa ya amsa tausasan idanunsa na kallonta da jin ƙaunarta
kamar kowane ɗa akan mahaifiyarsa. Tsahon mintuna yana
tsakurar abincin cike da ƙasaita kamar wani magani, kafin ya
ɗauka tissue ya goge bakinsa da janye jikinsa da ga kwanikan
alamar ya ƙoshi.....
“Ya take yanzun?”.
Tambayar da take son jin tun ɗazu daga bakinsa ta fito
tamkar an fisgota. Idanunta ta ɗan kafe kansa, amma sai ya
kauda kai gefe kamar bashi ya buƙaci ji ba. Taja numfashi ta
fesar, itama batare data sake cewa komai ba ta cigaba da
nazartar sa. Kusan mintuna uku tsakani sannan ta nisa...
“Ban san mikafi buƙatar ji ba. Sauƙin ko akasin sa. Amma
dai zan iya cewa muna jiran ikon UBANGIJI ne”.
Shiru babu alamar zai sake cewa komai, itama bata sake
cewar ba. Kansa ya ɗan risinar gefe bayan ɗan kallon gefen
idanu da yay mata. Miƙewa Malikat Bushirat tayi, ya bita da
kallo harta isa bakin ƙofa sai kuma ta juyo, “Ina jin tsoron ace
alaƙar da maƙiyanmu ke alaƙantawa da kai ta zam haka take
Saiful-mulk”
Kansa ya ɗauke gefe, itama sai ta ɗauke nata kan daga
garesa tana danne lips ɗinta da haƙori. Shiru kusan na minti
ɗaya, ita bata fitaba ita bata juyo ba, shi kuma bai amsa mata
ba bai kuma motsa ba, sai kawai ta buɗe ƙofar zata fice.
“A huta lafiya”.
Ya faɗa dai-dai tana ficewa. Bayan kusan minti uku da fitarta
ya furzar da nannauyar iska, miƙewa yay hannayensa goye da
bayansa ya fara tattaki zuwa gaban window ta saitin inda zai
iya hangota. Dai-dai kuwa hadimanta dake zaman jiranta na
zagayeta. Duk da nisan da sukema idanunsa bai bar wajen ba
har sai da yaga ta shige sashenta da tawagar hadimanta..
Wani irin ƙasaitaccen murmushi ya saki da lumshe idanu, sai
kuma ya buɗe cike da isa yana mai barin windown ya shige
ƙofar daya fito ɗazun....
Lafiyayyen bedroom ne mai ɗauke da kayan more rayuwa
irin nasu na manya. Ƙamshi dai kam ba'a magana dan Tajwar
Eshaan ko gonar turare haka ta gansa ta bari saboda yanda
yake wanka da shi a duk motsinsa, son ƙamshi da zama
cikinsa tamkar al'adarsu ce data zama dole ga talaka da mai
kuɗi, sai dai banbancin tsada da ƙamshi ya banbanta maka
wanene tare da kai. Amma dai-dai da banɗakin jinin Ruman
ko shagon sai da kaya a kasuwa ka shiga saika san kazo ƙasar
ƙamshi, duniya ta sansu da wannan tun shekaru aru-aru, dan
suna a sahun farko na ƙasashen dake yin turare, yana kuma
ɗaya daga cikin tattalin arziƙinsu dake shigar musu da kuɗi da
bayyanasu a ko'ina suka shiga a duniya. Zaune ya kai a
kujerar dake ɗan gefe ta jikin window, ya kai bayansa kwance
a kujerar, tare da kwantar da kansa ya kalli sama ya lumshe
idanunsa. Daga ƙasa ƙafafunsa a harɗe, hannayensa duk biyu
akan hanun kujerar ya ɗan fara lila kansa. Sai da ya ɗauki
tsahon mintuna ashirin a haka dan zakama iya ɗauka barci
yake yi kafin ya buɗe idanunsa da suka kaɗa sukai jajur,
zaune ya tashi da ƙyau, ya kai hannu drawer'n dake gefen
kujerar ya buɗe, ƙaramar waya ƙirar nokia ya ɗakko. Danne-
danne yay tare da kaiwa kunnensa yana wani yamutsa fuska.
Bugu ɗaya kuwa aka ɗaga daga can, cikin bada umarni da
ƙarfin ikon ya furta..
“A kawar da ukun bana buƙatarsu. Haɗuwa, da lokaci
zaizo a saƙo”.
Ya janye wayar daga kunnensa da dafe kansa yana cizar lips
ɗinsa a lokaci guda fuskarsa babu alamar ɗigon wasa ko
sassauci a cikinta sai razani mai ban tsoro da saka firgicin ga
duk wanda zai iya ganinsa a hakan...........✍

(Tofa! Tajwar......🤔 bara dai nai shiru🤫).

19


..........Shigar Malikat Bushirat sashen Tajwar da yanayin data
fito ya sake zama wasu ƙananun maganganu a masarautar,
musamman ga masu ikon faɗa aji. Dan ta ko'ina suna da
masu leƙen asiri a cikin hadimai da masu tsaron gidan kamar
yanda itama Malikat ɗin ke dasu a kowanne sashe. Ga
hadimai dai babu damar yin faɗa da kuwwa sai ƴar ƙus-ƙus,
ƙus-ƙus ɗin ma sai ka samu wanda kafi yarda da shi kuɗan
zanta gudun karka faɗa tarko.

★★......

Tun barowarta sashen Tajwar ta kasa zaune ta kasa tsaye.
Abubuwane birjik ke faman mata kaikawo a zuciya. A karo na
farko kenan da zuciyarta ta fara rawa akan al'amarin dake
faruwa tun daga randa aka ɗora tilon ɗanta karagar mulkin
kujerar Shahan-shan. Anya kuwa ba'akwai lauje cikin naɗi ba
a wannan al'amarin?. Sannan ba zaton wuta a maƙera
sukema komai ba alhalin yana a masaƙa?. Ta rumtse
idanunta da sukai matuƙar ja da ƙarfi, saboda zuciyarta ke
hasaso abun, amma ƙirjinta ne keci da wutar ƙunar
dangantashi da abinda tafi so fiye da komai a duniya. Sai dai
ya zatai, hakan kamar dole ne a gareta kodan rashin samun
wani bakin zare har yanzu....
Kalmar bakin zare data faɗo a tunaninta ce ta sata buɗe
idanu da sauri, sai kuma ta jawo ɗaya daga cikin wayoyinta
da dan tsumar jiki tana gyara zama. Danne-danne tai tare da
kaiwa kunnemta. Daga can akai sallama tun kafin ita tayi. A
taƙaice ta amsa da faɗin, “Jasrah ina buƙatar hadiman nan
yanzun nan”.
“An gama Akia”.
Jasrah ta amsa

Please Login or Register in order to submit comment