Reading Dauɗar Gora by Bilyn Abdull ce Chapter 15 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwashe yanda sukai ta sanar
masa saboda ta matuƙar yarda da shi. Shine kuma takema
kallon wanda zai taimaka mata a wannan yaƙin kamar yanda
tai fata. Ya jimanta al'amarin matuƙa, ta wata fuskar kuma
yayi murnar ganin hanyar samun nasararsu ce tazo.
“Lallai mun samu hanya ta jifan tsuntsu biyu da dutse
ɗaya Iffah. Sai dai dole kiyi taka tsantsan da waɗan nan
wayoyin. Ki buɗe account da duk kike ɓuƙata da layin da suka
sanya miki, shi kuma wannan nakin watsap kawai zaki buɗe
da shi, sai dai karki barsa akan wayar, da kuma kinyi magana
da Ajmaal da shi ki goge watsap ɗin ki cire layin sai zaku ƙara
ki maida. Akoda yaushe wayarki ta kasance da security na
idanunki bana wayar ba. Dan inada tabbacin suma zasu saka
ido a kanki. A daren nan ki buɗe watsap ɗin ki sake ma
Ajmaal magana”.
“Nahode Sir, insha ALLAHU zan yi duk yanda kace”.........✍️

29

.........Barrister na ƙoƙarin shiga layin gidan Abu Moosa wata
baƙar mota na ficewa. Babu wanda ya damu da ganinta a
cikinsu, suka ƙarasa kutsa kai har ƙofar gidansa. Ganin gidan
rufe daga nesa baisa sun kawo wani abu a ransu ba duk suka
fita. Abu Zainab ne ya ƙarasa har jikin ƙofar. Kansa tsaye ya
kai hannu ya fara knoking, amma har tsahon mintuna biyu
babu alamar motsin mutum.
Juyowa yay ya ɗan kalli su Kaka dake kallonsa. Cikin
sarewa ya girgiza musu kai. “Banajin fa akwai mutum a gidan
nan, dan babu wani motsi”.
“Kara dai bugawa”.
Cewar Barrister cikin bashi ƙwarin gwiwa. Kai Abu Zainab ya
kaɗa ya cigaba da bugawa, maimakon a buɗe nan sai ƙofar
makwaftansu ce ta buɗe. Wani matashin saurayi ya fito. Abu
Zainab ya maida hankalinsa garesa suka gaisa. Kafinma ya
tambaya saurayin ya bashi amsa.
“Ai banajin akwai kowa gidan nan. Saboda yanzu babu
jimawa matar gidan aka ɗauke a mota harda ƙaton akwati”.
Da mamaki Abu Zainab ya ce, “Kana nufin yanzun?”.
“Eh, dan banajin sunma rufa minti goma. Ta kuma yima
mahaifiyata sallama akan zata koma garinsu ne. Harma
mukayi mamakin hakan ganin duka rasuwar mijinta bai wuce
kwanaki goma sha biyar ba”.
Godiya Abu Zainab yay masa jiki a saɓule ya koma gasu
Kaka. “Waifa kunji babu jimawa tabar anguwar nan. A yanda
tacema makwaftansu ma ta koma garinsu ne”.
“Garinsu kuma?”.
“Haka dai yace. Nifa na fara tsorata da lamarin nan, dan
tabbas akwai abinda ke ɓoye da bamu sanshi ba”.
Tsakanin Kaka da Barrister babu wanda ya iya cewa
komai....

*_MASARAUTA (JASRAH)_*

“Wai ni naga sai faman moso kike, kinma kasa bani labarin
yanda kukai da Akia akan zancenmu na jiya. Kuma naga
wucewarku ke da ita ɗazun zuwa sashin Mamma (Malikat
Haseena)”.
Cike da zolaya ta ɗan hararesa. “Ko kuma dai ƴan leƙen
asirinku sun sanar maka ba”.
“Leƙen asiri kuma? Haba sai kace dai ku. Kudai matan
masarautar nan ne dai da baƙwa iya rayuwa sai dai ƴan leƙen
asiri. Amma mu maza miya haɗamu da wani leƙen asiri kamar
marasa aikin yi”.
Ta ɗan dara kaɗan da taɓe baki. “Muma ɗin ba kowa ne
yake hakan ba kamar yanda kuke zargi. Niko waya dameni a
daular nan dahar zan damu da saka wani bibiyarsa. Ko
lamarin Zaki addu'a ce tamu a garesa kawai”.
“To ALLAH yasa hakan. Yaya zaman naku ya kasance?”.
“Zama an samu nasara. Dan inama Akia bayani a take ta
amince, ta kumace muje sashen Mamma itama muji ta
bakinta. Alhamdullah sai aka dace itama zancen ya ƙayatar da
ita. Na taƙaice maka zance a yanzu haka ma mun zauna da ita
yarinyar. Insha ALLAHU zuwa gobe ma zata koma sashenta.
Sai dai abu ɗaya ne fa Mamma bata amince da shi ba”.
“Minene shi?”.
“Sake kai wata Zawjata-almilk turakarsa. Acewarta za'a ƙara
jinkirtawa aga abinda yarinyar zata samo. Sannan za'a
sakema duka Zawjata-almilk ɗin sabon horo akan kasancewar
su Zawjata-almilk a wannan karon”.
(Wata sabuwa kenan, wannan tsinanniyar tsohuwar ko)
ya ambata a zuciyarsa. A fili kam fuskarsa ya kawata da sabon
murmushi da faɗin, “Woow wannan tsarin yayi, shiyyasa
Mamma ke daɗa birgeni. Hakan ma wani mataki ne da zai
taimakemu matuƙa. ALLAH kuma yasa mu dace”.
“Amin dai Abu Harith. Dan gaskiya a wannan gaɓar ina
tsoron a ce abinda ya faru ya sake maimaita kansa. Saboda
zuwa yanzu hankalin manyan ƙasashen duniya ya fara
dawowa kan ƙasar ruman. Dan ma ana shakkarmu ne da tuni
wani zancen ake ba wannan ɗin ba. ALLAH dai ka bayyana
gaskiya ka kuma wanke wanda ake neman disashewa saboda
son zuciya”.
“Amin Meera. Amma ko yanzu ɗin ma akwai abinda
baku sani ba. Shahan-shan na ɓoyewa ne kawai dan karya
tashi hankalin kowa. A wata mai kamawa shugabannin
manyan ƙasashe bakwai na africa zasu kawo ziyara ƙasar
ruman. Bisa jagorancin shugaban ƙasar Nijeriya, bama raba
ɗayan biyu akan wannan al'amarin ne kuma”.
“Ya Arrahaman”.
Jasrah ta faɗa a tsorace.
“Ki kwantar da hankalinki, dan ALLAH kuma kar kowa yasan
wannan, dan na sanar miki ne kema saboda na yarda da ke”.
Badan hankalin nata ya kwanta ba ta jin jina masa
kanta kawai. Cigaba da kwantar mata da hankali yay cikin
kwantar da murya har barci ɓarawo ya kwashe ta. Sai da ya
tabbatar barcinta yayi nisa sannan ya zare jikinsa cikin sanɗa
ya fice zuwa ɗayan ɗakin dake jikin wanda suke kwance da
waya a hannunsa......

*_ZAWJATA-ALMILK_*

Dukan matakin shawarar da Sir Fawzan ya bata shi tabi, dan
tunda sukai bankwana da Daneen Ammarah tai shirin barci ta
sakama ƙofarta key. Ta fara da buɗe Watsap, sannan ta
lalubo number Ajmaal. Cikin sa'a kuwa yana online, wani
farin ciki ne ya ratsata. Taja kakkauran numfashi da godema
ALLAH.
_Assalamu alaikum_
Ta fara turawa da fatan samun amsa zuciyarta na harbawa
da sauri-sauri. Tsahon mintuna kusan goma babu alamar
zama a buɗe saƙon. Sake tura sallamar tayi a karo na biyu. Ta
dasama wayar ido kamar mai irgan fitan numfashinta. Kamar
a mafarki taga an buɗe, tai kasare tana jiran taga an amsa sai
dai shiru har kusan wasu mintuna goman. A yanzu kam
zuciyarta ta sosu, dan duk yanda take buƙatar abu ga mutum
ta tsani a wulakantata. Ta cije lips da ƙarfi tana danne fushin
dake son mata tasiri.
_Wa'alaikissalam_.
Aka amsa mata a bazata. Nannauyar iska ta furzar, itama ta
buɗe saƙon ta share. Da ƙyar ta iya danne zuciyarta mintuna
bakwai suka cika.
_Sunana Fareedah bint Zayyan_.
Tsahon mintuna kusan goma yanzu ma sannan aka buɗe.
_Na sani_.
Tai shiru tana kallon amsar, sai kuma taja tsaki na takaici. A
fili ta furta, “Aikin banza. Ka sani shine baka san aikinka ba
mtsoww!!”.
Sharewa tai, ta rubuta masa.
_Kwanaki na kira, amma akaimun tarbar da har yau ina
mamakinta. Shin dama manyan ƴan jarida haka suke da
wulaƙanta bukatar marasa ƙarfi?_
Tsahon minti ashirin da buɗe saƙon babu alamar za'a
amsata. Hakan yay mata ciwo matuƙa. Sir Fawzan ta kira,
bugu biyu kuwa ya ɗaga. A ɗan rikice yace, “Iffah baki ganin
akwai matsala yawan kiran nan? Masarauta fa ba irin ko'ina
bane sunada hanyoyin tsaro ɓoyayyu ciki harda cctv”.
“Hakane Sir, amma nima dole ce ta sakani kiran. Anya
kuwa wannan abokin naka da gaske ɗan jaridar ne? Sam baya
ɗaukar al'amarina da muhimmanci, duk ɗan jarida na kwarai
zaka samesa da zumuɗi akan labari, musamman ma irin nawa
daya kasance babba”.

“Miya faru? Bai amsa saƙonki ba ne?”.
“Ya amsa. Amma yanamun yanga. Harna fara jin gundira a
huɗɗa da shi”.
“Karki saurin karaya, amma nayi mamaki dan masan
Ajmaal ba mutum bane mai irin wannan siffar wlhy. Inaga dai
akwai aikin da yake yi a wannan gaɓar shiyyasa. Kin san su
abubuwan nasu da yawa. Kin san kuwa yanda ya ƙagu akan
son jinki, dan ɗazun na fara ƙyara masa abinda ke ranki
kaɗan”.
Ta ɗanji sassauci daga haushinsa. Taja ajiyar zuciya a fili da
faɗin, “Shike nan bara na koma”.
Sallama yay mata ya yanke wayar.
_Am sorry na haɗa wani aikin ne da saurarenki. Yanzu
ina jinki_.
Da wannan saƙon taci karo bayan yanke wayar. Sanyi ta
ƙaraji a ranta. Cikin ɗan karsashi ta maida amsa.
_Ayya kayi jaƙuri na maka gurguwar fahimta._
_Babu damuwa_
Aka amsa mata cikin ƴan sakanni. Cike da karfin gwiwa ta
rubuta.
_Nasan abokinka ya fara maka bayani akan nemanka da
nake ido rufe._
_Hakane. A yanzu haka ma munyi dashi zai bani wani
yankin rubutunki dake hanunsa._
_Alhamdullahi. A yanzuma akwai cigaban wancan rubutun a
hannuna nima. Sai dai ban san ta hanyar da zai zo garesa ba
ko gareka_.
_Wannan mai sauƙine ai. Zaki iya turamin shi tanan_
_Wai! Amma typing ɗin zaimun wahala gaskiya_.
_Karki damu ki ɗauki hoto_
Cike da zumuɗi ta miƙe. Gado ta ɗaga ta ɗakko notebook
ɗinta, a take ta ɗauka hoton duka rubutun ta tura masa.
_Gashi, insha ALLAHU duk bayan kwanaki uku zaka iya
ganin saƙona_
_Masha ALLAH hakan yayi, sai dai a maimakon kwana uku
mizai hana muyi mako-mako. Dan wani abun da zai zo yana
buƙatar bin diddigi da faɗaɗa bincike mu tanan a garemu._
_Yanda kace haka za'ayi. Ni dai fatana ka kasance ɗan
jarida mai gaskiya da riƙon amanar kimar ƙasarsa. ALLAH
shine shaidata na baku dukkan yarda kai da Sir Fawzan. Idan
akasin nasarata ya biyo bayan yunƙurina ku zan zarga. Duk
kuma yarinyar data samu kanta a irin halin da ƴan uwana da
ni muka kasance kuma zaku amsa sunan azzalumai ne kamar
yanda Shahan-shan ɗin ke amsawa a yanzu. Ku kuma dinga
tunawa da mala'iku tare da ku masu rubutawa daga
ayyukanku na zahiri da baɗini. ALLAH ya cigaba da tsare ƙasar
ruman. Idan kanada wata tambaya zaka iya tura min text
message na Barka lafiya_.
Bata jira amsa daga garesa ba ta fita gaba ɗaya. Watsap
ɗin ta goge ta kashe wayar gaba ɗayama tana sakin ajiyar
zuciya a jajjere. Sai takejin wani kaso na damuwarta da
nauyin zuciyarta ya ragu kaɗan. A wani gefe kuma kamannin
mutumin can da wanda ta gani a jiya matsayin Shahan-shan
ne ke ta faman mata kaikawo babu alamar zai barta ta
huta......

★★.... “★★” .....★

“Lafiyarki da tsahon zamani su da ɗa tabbatuwa uwa mai
share kukan masu kuka”.
Ta-kurya dake kai gwuyawunta ƙasa ta faɗa sakamakon
zuwan Uwa gareta a bazata. Kamar ko yaushe, cikin shigarta
ta jajayen kaya, ta gyara zaman ƙasaitar ta. Ƙoƙon dake
hanunta ta miƙama ta ƙurya. Hannu biyu ta karɓa, ta kafa kai
ta shanye abinda ke ciki.
“Tukuycin cika umarninmu na yanka babbar baƙar dabba
da kikai ne. Azamarki da himmarki zaisa bazaki taɓa nema
daga garemu ba ki rasa Ta-kurya (Wa'iyazubillah 😭 ).
“Nagode uwa mai share kukan masu kuka”.
Murmushin daya sake munana fuskarta ta saki tana ƙara
kalmashe ƙafafu a kujerarta.
“Karki damu ke mai nasara ce. Minene makomar ayyukan
da muka barki da su?”.
“Ina kan yunƙurin ƙarasawa. Na kuma samu ƙyaƙyƙyawan
labari a majiya mai ƙarfi yarinyar zata koma sashenta. Sai dai
akwai zaman sirri dasu Uwar masu gida sukai wanda babu
wanda yasan misuka tattauna. Ina dai ƙyautata zaton duk
akan komawar yarinyar ne”.
“Kar tattaunawarsu ta dameki. Tabbatar da ƴan leƙen
asirinki cikin hadimanta shine aikinki na gaba. Dan kunada
yawa masu wannan burin kema kin sani basai na sanar miki
ba. Ina kuma tunatar dake rigar can dake a sashen Uwar
masu gida. Da zaran ta tare ki kasance ɗaya daga cikin masu
janta a jiki. Yardarta gareki ne zai bamu damar amfani da ita
wajen cikar burinmu”.
“Na gode da kasancewar ki haske mai haskamin duk wani
surƙuƙin da zai iya zamemin duhuwa uwa”.
“Biyayyarki garemu ita ce tushen share kukanki Ta-kurya.
Dan haka bazamu taɓa barin kiyi kuka ba maƙiyanki suyi
dariya ba. Sai dai su suyi kuka ke ki kasance cikin dariya a
kullum bisa nasararsu. Karki shagala ƴar shilar suda nada
taurin kai, Karki zama cikin jerin mutane masu raina allura ta
zame musu garma. Muna son tasha madarar nan a ƙalla sau
uku daga gareki da zaran ta tare a sashenta”. Ta ƙare
maganar da miƙama ta ƙurya ƙoƙon da bata san daga ina ya
fito ba. Dan ganinsa kawai tai a hannunta tamkar ƙyaftawar
idanu. Hannu biyu tasa a wajen amsa tana jera mata kirari da
godiya. A hankali ta fara disashewa a idanunta tamkar baƙin
hadarin da masha ruwa (Bakan gizo) ya shanye cikin sakanni.
Ta-ƙurya ta sauke nannauyan ajiyar zuciya. Sai kuma ta
miƙe da ƙoƙon da Uwa ta bata. A guri na musamman da
na'urar sanyi ke aiki ta ajiye madaran, murmushin jin cigaba
da tabbatuwar nasararta na cigaba da ƙawata ƙyaƙykywar
fuskarta. Ji take a ranta yanzu ne fa za'a fara wasan na
gaskiya. Dan dama idan aski yazo gaban goshi masu iya
magana kwance yafi raɗaɗi da zafi. Ta jima bata samu irin
wannan damar ga uwa ba a ɗan tsakanin nan da mafi yawan
lokuta sukafi ganawa cikin ɓacin rai da rabuwa da ɓacin ran.
Amma a yau yanda uwa ta ziyarceta ya sakata jin karsashi da
ƙarin kwarin gwiwar cigaba da ruguza duk wanda ya cigaba
da yunƙurin shiga gaban nasararta.......✍️

30


........Kamar yanda su Malikat Haseena suka faɗa a yau aka
tashi da gyaran sashen Iffah, sai dai abinda ya Bama kowa
mamaki ba inda aka fara kaita bane. Ɗaya daga cikin sabbin
sashen da babu wanda ya taɓa rayuwa a cikinsu ne a
masarautar. Hasalima an jima ana gutsiri tsomar dalilin
gininsu da Tajwar Eshaan yasa ayi batare da ansan dalilinsa
ba. Ba kayan ƙawata gida kawai aka zubama sashen ba, harda
tarin sitturu da kayan ado na sakawar Iffah.
A karan kanta kuma masu gyaran jiki na musamman ne
suka duƙufa kanta a yinin wannan rana. Da dare ta samu
hutawa. Washe gari aka cigaba da mata gyaran da ita kanta
sai da zuciyarta ta fara shiga wasi-wasi. Koda yake dama a ciki
take. Dan gaba ɗaya kwanakin nan aikinta kawai shine nazari
da fasalta abubuwa masu yawa a rai da takasa gane bakin
zarensu sam. Sai dai shawarar malam Fawzan ta waccan
ranar ta ƙara mata ƙwarin gwiwa da maidota a hayyacinta da
matsayin shigowarta daular ruman.....

Tsahon kwanaki uku ta gyaru ta ƙara ƙyau tamkar ba'ita
tayi fama da jiyya na a kwanakin baya. Ƙamshin dake fita a
jikinta ma kawai ya isa ai kiransa na musamman. Ita a karan
kanta har gizago canjawar tata ke mata. Jikinta ya murje ta
ƙara girma da cika ido tamkar ba autar Ummu da Babiy ba.
Ga wani jin kai da takejin ta ƙara masu neman kere
shekarunta. Babu shakka kuma hakan nada nasaba da girman
da ake bata.

Masarauta da jama'ar cikinta zance ya yaɗu yau za'a
maida Zawjata-almilk sabon sashenta tunda ta samu sauƙi.
Shaidar haka kuma nada nasaba da walimar da Malikat
Haseena suka shirya, acewarsu ta aure ce da ba'aiba sanadin
abinda ya faru za'ayi yanzu. Shirya wannan walima ya kawo
ƙananun magana matuƙa, dan kuɗi aka kashe tamkar za'a
sake wani sabon auren. Abin mamaki sauran mata biyu kafin
Iffah ga Tajwar Eshaan sai al'amarin ya sosa musu zuciya duk
da har yanzu zaune suke batare da ko Tajwar ɗin sun san
kalarsa ba.
Sam Iffah bata san da wani taron walima ba, sai da aka
kammala mata shiri cikin wasu ƙawatattun kaya masu
tsananin ɗaukar ido da tabbatar da ita amarya ta gaskiya mai
amsa sunan Zawjata-almilk kanta ya fara ɗaurewa. A ganinta
in har shigace ta iya rakata sashenta baici ace ta ƙawatu har
haka ba kodan kasancewar dare ne ma. Kai mutanen nan fa
sun fara caja mata ƙwaƙwalwa, ta faraji a ƙasan ranta akwai
manufa. Amma dai koma minene zata jure har zuwa lokacin
samun ƴancin kanta na komawa sashen nata dan ta shiryawa
kowa talalarsa. A kwanakin baya ta kwantar da kai ne ga
kowa domin fahimtar manufar wasu koda kalilanne a cikinsu.
Alhamdullah kuma ta dace, dan koba komai ta gama samun
yardar Daneen Ammarah da masu gayya da aiki Malikat
Haseena da Malikat Bushirat. Duk da dai tasan kada mage ba
yankata bane. Amma koba komai raina allura yakan sa ta
zama garma ga wanda yay sakaci ai.
Taji ba daɗi da barin ɗakin data rayu tsahon kwanaki cike
da kewa. Koba komai bazata manta da rayuwar kusan sati
uku da tayi a cikinsa ba. Ta koyi ilimi da yawa, harma da
darasi data ɓoye matsayin sirrinta. Da wannan tunanin a
ranta har aka iso babban ɗakin taro na cikin masarautar,
wanda ya ƙunshi duk wani babba mai faɗa aji. Al'ajab ya
kama Iffah, amma ta dake zuciyarta na sake tauri na nan
dalilin ɓoye mata wannan zaman da akai. Amma a zahiri
rashin ƙarfin cewa yasata yin luff kamar yanda ta kasance a
kwanakin da suka gabata na samun lafiyarta. Daneen
Ammarah data kasance mata ƴar jagora kasancewar fuskarta
a sakaye take ta kaita har mazaunin da aka tanada dan ita a
cikin ƙaton falon bisa tattausar dardumar da aka shirya
walimar. Kamar yanda al'adar take, abinci aka fara ci yayinda
Iffah ta gagara kai ko ruwan madara bakinta. Yanda tayi ɗin
ya sake burge su Malikat Bushirat, suna ji a ransu sun dace da
irin surukar da suke fata. Bayan anci ansha kowa ya nutsu. An
fara buɗe taron da addu'a, tare da saƙon maraba ga sabuwar
Zawjata-almilk, harma da fatan kasancewar ta abinda kowa
ke fata. Kowa dai ya amsa da amin a zahiri, a baɗini kam
sanin sirrin wasu sai ALLAH.
A mataki na biyu shine zagayawa da Zawjata-almilk takai
gaisuwa ga duk wanda ke wajen, kasancewar kakanni ne
makusanta da iyaye, da yayye. A yanzu dai kam da taimakon
Jasrah ta motsa, bayan ta janye hular rigar alkyabbar jikinta
data hana kowa kallon ainahinta a tun farko. Duk da Iffah taji
ta takura, hakan wata damace a gareta na sanin dukkan masu
faɗa ajin, zai kuma zama jagoran abinda zai taimakawa nata
ƙudirin. Idanunta suka cika da hawaye, a lokacin da take
durƙushe gaban Malikat Haseena matsayin bankwana.
Tanajin tsohuwar a ranta, ta kuma samu wani kebantaccen
ilimin zamantakewa da ita. Ta saka mata albarka tare da yaba
ƙyawawan halayenta da jinjinama iyayenta tarbiyyar da sukai
mata. Ta ƙare da fatan alkairi da samun zuri'a mai albarka
tsakaninta da Shahan-shan. Waɗan nan zantika sun zama
abin kaiwa da komawa a zukatan manyan masarauta. Dan
kowa na ganin kamar wata isharace Malikat Haseena ta isar
cewar ta karɓi Iffah ɗari bisa ɗari matsayin Zawjata-almilk fiye
dana baya da suka gabata. Iffah a karan kanta taji tausayin
tsohuwar bisa ƙudirinta na shigowa daular ruman data
tabbatar yasha banban da fatan da Malikat Haseena tayi
gareta a yau gaban duk wanda ya isa a ƙasar ruman ma ba
daular ruman ɗin kawai ba. Har yanzu har gobe da jibi tana
akan bakanta na ɗaukar fansar rasa ƴan uwanta. Abin harinta
kuma ɗaya ne tal shine Tajwar Eshaan, inma da wanda zasu
biyo bayansa sai ta gama da babban dodon nasu. Ta samu
ƙwarin gwiwar hakanne da tabbacin jin sai an kai matan
turakarsa ake fiddosu babu rai. Sai kuma bincike da
shaƙiƙansa guda huɗu sukai yunƙurin ɗaurata a yanzu haka.
Kenan babu buƙatar wasi-wasi koma minene shike ƙullasa...
Malikat Bushirat ma tayi irin makamancin addu'ar Malikat
Haseena ne ga surukar tata. Ta ƙara da faɗin ita ɗiya takejin
ta samu ba Suruka kawai ba, tana kuma fatan ta kasance
kibiyar ajali ga masu ƙudirin sharri a ciki da wajen daular
ruman. Tabbas maganar Malikat Bushirat tafi ta Malikat
Haseena ɗumama zukatan wasu, yayinda mugun ƙudirinsu
akan Iffah ya ƙara hauhawar farashi a zukatansu, amma duk
sai suka ɓoye suma sukai mata irin tarbar data ɓoye dukkan
ainahinsu. Dan Miran Jasim ma da akazo kansa har ƙyauta ta
musamman ya gabatar ga Zawjata-almilk.
Iffah data kasance cikin ladabi da ƙawata harshenta gaban
kowa yayin miƙa gaisuwarta duk da ƙarancin shekarunta
kaifin basirarta da wayonta ya bata damar nazari da adana
cewar kowa a wajen da fuskar daya tarbeta ta hanyar
kallonsu a ƙyalkyalin jikin rigarta datai matuƙar taimaka mata
harta ambata godiya ga Malikat Haseena data zaɓa mata
rigar domin sakawa a yanzun. Ba kalaman kawai ta riƙe ba da
fuskokinsu da suka fita tartar bisa taimakon hasken kwayayen
wutar lantarki. Harda sunayensu sun kasance kamar wani
zane akan dutse cikin ƙwaƙwalwarta da zuciyarta.
Ƙarfe goma da kusan mintuna talatin taron ya tashi na
dare, aka fara fita da Zawjata-almilk da kowa ke tunanin
sashenta za'a kaita kai tsaye. Sai kuma hakan ya bambanta da
tunaninsu a lokacin da Malikat Haseena tabi bayansu akan
wheelchair ɗinta matsayin maiyin wannan rakkiya. Abu ne da
ba'a taɓa gani ba a masarautar. Dan hatta Malikat Bushirat da
Daneen Ammarah sun sake jinjina wannan soyayya mai ƙarfi
data shiga tsakanin Malikat Haseena da Iffah. Sai dai hakan ya
musu daɗi, musamman Malikat Bushirat da take ganin hakan
matsayin ƙarin sanin wanene Shahan-shan a zuciyar Malikat
Haseena ga maƙiyanta.
A lokacin da kowa ke fitowa daga falon da walimar ta
gudana bayan gama sallamar sai da safe gagarumin labari da
ɗumi-ɗuminsa shine cin karo da motar data ɗauka Malikat
Haseena da Iffah a ciki ƙofar sashen Shahan-shan. A wannan
karo hatta da Malikat Bushirat da Daneen Ammarah sai da
sukai turus dan shirine da sam basu san da shi ba. A take suka
koma ƴar kallo a tsakaninsu, cikin tambayar juna yaya akai
haka kuma? Da idanu. Rashin amsa da mai basu amsar ya
sasu shanye komai......
★★.... ★... ★★.....

Komai ya tsaya cak a ɓangaren su Kaka a kwanakin nan da
suka gabata dangane da neman inda su Babiy suke. Barrister
ya sake bin duk hanyar da yake da yaƙinin samu koda na
ƙarfin iko ne amma sai ya risketa a toshe. Zuwa yanzu kam su
duka ukun sun fahimci komai shiri ne bisa la'akari da labarin
da suka bama juna na gargaɗin da akai musu. Sai dai abu mafi
ɗaure kai da ban mamaki, wanene mai shirin? A wane dalili
yay shirin kuma? Miyasa zaiyi shirin akansu Babiy ɗin?.
Waɗan nan tambayoyi sune suka zama abun tattaunawa
tsakanin Kaka da Barrister dama Abu Zainab daya saudaukar
da dukkan lokacinsa domin ganin komai ya daidaita. Bisa
shawarar Barrister Kaka yay shirin komawa Jimna, dan a
cewarsa suna buƙatar bada ƙafa kodan harar rayukansu da
aka farayi suma. Saboda a kwanaki biyun da suka gabata da
ƙyar Barrister yasha a hanun wasu tankunan mai da suka
sakashi tsakkiya bisa titi lokacin da yake tashi aiki. Haka yaron
Abu Zainab a jiya anyi wuff da shi daga hanyarsu ta zuwa
makaranta a cikin ƴan uwansa. Ba kuma a sakesa ba sai a
daren jiya bayan sallar isha'i lokacin kowa ya gama jigata da
nema da hasashen inda ya shiga. Rubutacciyar wasiƙar da aka
haɗosa da shi yayin maidosa ya basu tabbacin daga inda
tsiyar take.
Kaka ya kammala kulle ko'ina na gidan sannan yay
sammala da su Abu Zainab tare da godiya ya ɗauki hanyar
inda zai samu motar ƙauyen Jumna. Harya sauka a mototaxi
aka dakatar da shi, da mamaki yake duban mai mototaxi ɗin
dake miƙa masa ƙaramar jakkar hannunsa. “Baba kayi
mantuwa, ALLAH yasa na farga da wuri”.
Kafin Kaka ya samu damar cewa wani abu saurayin ya
ajiye jakkar gabansa ya koma cikin mototaxi ɗin da baiko
waiwayo ya dubi Kaka dake yunƙurin dakatar da shi ba.
“Kar kai jayayya tsoho, ka ɗauka dan naka ne”.
Aka faɗa ta bayansa dai-dai yana kaiwa duƙe zai ajiye jakar.
Ɗagowa kaka yayi, sai dai bayan mutumin kawai ya gani sai
ƙurar motarsa. Ran Kaka ya sosu, har fuskarsa ta nuna haka.
Alamar ƙosawa da wasan kwaikwayon waɗan nan mutane ya
fara tunzura kawaicinsa da son bin doka a yanda tazo. Amma
ya fuskanci burinsu kawai su kaisa maƙurar da sai ya gwada
ƙwanjinsa akansu. Yay ƙwafa tare da ɗaukar jakar.......


“Boss ya ɗauka fa”.
Wani matashin saurayi siriri dake zaune cikin taxi nesa
kaɗan da Kaka ya faɗa yana ɗan kai hannu a kunensa ya dafe
bluetooth ɗin dake manne a ciki.
“Tabbas akwai alamar ɓacin rai tattare da shi a yau, dan
fuskarsa harta kasa ɓoyewa”.
Saurayin ya sake faɗa da alamar amsawa wanda ya kira da
Boss ɗin a farko idonsa ƙyam akan Kaka da har yanzu ke tsaye
jikin wata mota. Kai ya gyaɗa alamar an sake masa magana
daga wayar, sai kuma ya gyara baƙar facing cap ɗin kansa da
faɗin, “Eh da alama bai samu motar garin nasu bane. Amma
gani ina tunkararsa, komi kenan zan cigaba da riƙe wayar dan
kaji komai”.
Kaka na shirin ɗaukar jakar da mai mototaxi ya barsa da
ita zai bar wajen saurayin ya katsesa ta hanyar masa sallama.
A ɗan daƙile ya amsa dan ransa babu daɗi har yanzun. A
yanda ya kafe saurayin da idanunsa masu kaifi duk sai yaji ya
tsargu. Ya

Please Login or Register in order to submit comment