Reading Dauɗar Gora by Bilyn Abdull ce Chapter 17 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai-dai agogon ƙasar ɗaya daga
cikin amintattun Hadiman dake gyara ɗakunan barcin na
Tajwar ta iso cikin faɗuwar gaba hanunta ɗauke da akwati da
aka kawo yanzun nan daga sashen Malikat Haseenat
matsayin kayan da Iffah zatai amfani da shi. Zuciyarta har
wani zallo take na fargabar abinda take da tabbacin tozali da
shi kamar yanda sukayi a baya ga sauran Zawjata-almilk da
suka shuɗe. Ta tura ƙofar cikin sanɗa tana mai ambaton
sallama da rawar harshe badan tana tunanin samun amsa ba.
Ganin Iffah kwance a saman gado, lulluɓe da lallausan bargo
baisa taji ƙwarin gwiwa ba. Tai yunƙurin ajiye akwatin
hanunta, cak ta tsaya dukkanin idanunta na fitowa waje dan
firgici ko sumar tsaye sakamakon juyi da Iffah tai alamar
gyara kwanciya. Akwatin ta saki ƙasa ta shiga jan jikinta dake
ɓari baya-baya harta dangane da ƙofa gab.....
Iffah dake ƙoƙarin gyara bargo idanunta rufe ta buɗesu da
sauri saboda jin ƙarar bigewar hadimar. Da mamakin jinta
kamar a gado ya sata shashshafa hannunta. (Tabbas
gadonne) ta ayyana a zuciyarta tana sake buɗe idanunta da
ƙyau tana mai yunƙurin tashi zaune. Tuni hadimar nan ta sake
firgicewa, da lalube ta murɗa handle ɗin ƙofar ta fita a guje.
Kallon ƙofar Iffah tayi, sai dai hadimar ta gama ficewa
bayanta kawai ta ɗan gani kaɗan da wulgawar mayafinta. da
sauri ta yaye bargon da bata san ya akai yazo jikinta ba. Ta
dire ƙasa mamakin duniya na cigaba da dabaibaye ta.
“Wacece wadda ta fita? Mi tazo yi? Wai ta yaya ma na dawo
saman gadon nan bayan a ƙasa na kwanta?”. Ta shiga jerama
kanta tambayoyin da bata san inda zata samu amsarsu ba. Sai
kuma ta ɗan kamo rigar jikinta ta kai hancinta. “Ya ALLAH, da
gaske fa wannan mayataccen ƙamshin a jikina ne?”. Ta sake
faɗa a fili tana sake shinshinar rigar......

A ɓangaren jama'ar masarauta dake a zaman jigum-jigum
kam fitar hadimar nan ya isar da saƙon Zawjata-almilk na
raye. Da farko duk wanda zancen yaje kunensa ɗaukewar
numfashi na wucin gadi ne ke riskarsa, sai kuma rashin
gaskatawa a zahiri ya biyo baya. Hatta da Malikat Bushirat da
Daneen Ammarah yanayi da ruɗanin jin hakan bai tsallakesu
ba suma. A kusan tare suka ɗauka wayoyinsu domin neman
Iffah ko zasu samu jin gaskiyar zance. Cikin Sa'a kuwa ta
Daneen Ammarah ta fara shiga....

Iffah na zaune har yanzu cikin ɗaurewar kai akan wanda
ya maidata saman gado da wulƙawar fitar wadda bata sani ba
wayarta ta katseta. Numfashi taja ta fesar da ɗan ƙarfi tana
kai hannu akan wayar. *_Mamy_* ta gani rubuce ɓaro-ɓaro.
Ganin zata katse tai ƙarfin halin ɗagawa ta kai kunne tana
faɗin, “Assalamu alaikum. Amincin UBANGIJI da rahamar sa
su yalwatu a gareki Mamy barka da safiya”.
A matuƙar razani da motsuwar zuciya Daneen Ammarah
taja numfashin dake neman ƙwace mata. “Ibnati!”. Ta
ambata cikin son tabbatarwa.
“Na'am Mamy”.
Iffah ta amsa kanta tsaye babu alamar irin fargabar dake
harshen Daneen Ammarah ɗin a tattare da ita. Dan ita wanda
ya ɗauketa daga ƙasa ya maida saman gado da fitar macen
data ganine kawai damuwarta a yanzu. Daneen Ammarah da
taji al'amarin tamkar a mafarki ta lumshe ido hawaye na
silalo mata saman ƙyakykywar fuskarta a hankali. Ƙasa takai
durƙushe tana mai godema UBANGIJI ta hayar kai goshinta
ƙasa tai sujjadar shukur...

Iffah da mamaki ta cigaba da ambaton “Hallo Mamy!
Mamy kina jina kuwa?”. Shiru babu alamar za'a amsa. Yanke
wayar tai da yunƙurin sake kira a zatonta matsalar network
ce sai ga kiran Malikat Bushirat ya shigo shima. Ɗan jimm tai
tana kallon wayar, sai kuma ta ɗaga takai kunne da sallama
nan ma. Malikat Bushirat da idanunta ke cikowa da ƙwalla
sakamakon jin muryar Iffah tar-tar a kunenta ta kai zaune
tana ambaton sunan ALLAH. Iffah na son tambaya tana jin
nauyi, sai kawai tai shiru tana sauraren kalmomin godiya ga
ALLAH da Malikat Bushirat ɗin ke ambata daga can.
(Ya rabbi! Wai mike faruwa ne haka?) Ta ayyana a
zuciyarta da al'ajabi. Knocking ƙofa da akai ta hanyar danna
alerm a dai-dai lokacin ya katse tunanin nata. Ta kai dubanta
ga kofar babu alamar zata tanka har aka sake danna alerm
ɗin sannan tai ƙarfin halin amsawa da bada umarnin shigowa
tana gyara mayafin data yanama kanta.. Hadimar ɗazun ce
dai ta shigo ɗauke da ƙaramin tray mai ɗauke da butar shayi.
Kanta a ƙasa ta ajiye a inda ya dace tana mai zubewa ƙasa
durkushe. “Amincin ALLAH da tsahon rai mai albarka su
kasance tare da Zawjata-almilk Barka da safiya”.
Iffah da ke kallonta ta amsa cikin motsa lips ɗinta kaɗan.
Sabo da hakan yasa hadimar bata damu da rashin amsawar
Iffah ba. Cikin sake rissinar da kai tace, “Ya Zawjata-almilk
yanzu lokacin wankanki ne, bayan nan karin kummalo na
jiranki tare da Shugabana”.
Yanzu ɗin ma kamar Iffah bazata amsa ba sai kuma ta
jinjina kanta. “Kije abinki zan fito”.
“Umarninki shine abin jirana. Amma a gafarceni zan haɗa
ruwan”.
“Kije abinki zan yi komai da kaina”.
Babu yanda hafimar ta iya dole ta miƙe domin bin umarni
shine kawai huruminsu. Da kallo iffah ta bita abubuwa masu
yawan gaske na son fara mata kutse a ƙwaƙwalwa da zuciya.
Ƙwarin gwiwar da take bama kanta akan turesu ya sata
miƙewa ta nufin toilet tana mai ambaton addu'ai a bakinta
saboda tuna abinda taci karo da shi a daren jiya a toilet ɗin.
Ko'ina tsaf, kuma cikin ƙamshi irin na daren jiya. Sai da ta
ƙarema komai kallo fiye da jiya kafin ta ɗage kafaɗa irin na
koma miye ta shirya masa. Tsabagen rigima da wuce wuri ko
tsageranci za'ace ta haɗa ruwanta mai ɗumi da zuba duk
wani nau'in turaren wanka da aka jera domin Shahan-shan ta
shige cikin kwamin wankan tai luf. Sai da taji ko'ina nata ya
miƙe yanda take buƙata sannan ta fita a ruwan domin fara
wanka...

Tsaf ta kammala shirinta cikin doguwar rigar material sky
blue da akaima ɗinkin daya fidda ainahin halittarta tamkar
ƴar tsanar roba. Rigar ta zauna mata ɗas, siririn mayafin da
aka haɗa rigar da shi ta naɗa tamkar yanda larabawa keyi, ta
ɗakko after dress shara-shara mai kamar alƙyabba ta ɗora a
sama kalar blue sosai. Ta ɗanji babu daɗi na rashin
turarurrukanta tare da ita, dan ko waɗan nan kayan ganinsu
kawai tai, cikin ɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa a zahiri ta dinga
kwasar turarrukan da taci karo da su a ɗakin cikin wani
ƙyaƙykyawan glass dake kusa da mirror ta dinga zazzagama
jikinta har sai da ta gamsu ƙarfin kamshin zai kai duk inda mai
rai ke numfashi a sashen sannan ta haƙura. Idanunta ƙyam a
mirrorn ta saki ƙayataccen murmushi da kanne ido ɗaya a fili
ta furta “Irin wannan haɗuwa haka autar Ummu”. Tai salute
ɗin kanta....

Sautin ƙarar takun takalman ƙafarta da mayataccen
ƙamshin tiraren da shi kaɗai aka sani da shi ya sashi tsayawa
cak daga ƙoƙarin kai hannu a abincin da aka gama haɗawa
gabansa. Fararen idanunsa tar-tar tamkar madara ya ɗago ya
sauke a kanta. Hakama hadiman dake a tsaye ta gefe da
gefensa kawunansu a ƙasa cikin yanayin mutuwar tsaye data
rikesu suka zube ƙasa kan gwiyawunsu illahirin jikkunansu na
ƙyarma akan dalilai guda biyu. Na farko ganin tabbatar da
wadda suka gama fidda rai da jiran tsammanin ganin an shigo
fidda gawarta tamkar Zawjata-almilk na baya dai na raye ɗin
kamar yanda Hadimar ta gano. Na biyu ƙamshin turaren
jikinta da ga mutum ɗaya tak ake iya jinsa a duk faɗin ƙasar
ruman ma bawai a daular ruman ba...
Tamkar Iffah bata fahimci halin da suke a ciki ba ta ƙaraso
cikin katafaren falon batare data dubi ko ɗaya a cikinsu ba
balle mai gayya mai aikin. Cikin sauri ɗaya daga cikin hadiman
ya miƙe ya gyara mata kujera, zaune ta kai tana mai dubansa
a karo na farko. Tuni shi kuma ya maida kansa ga abinda yake
yi tamkar bai san da zuwan tan ba. Ta taɓe baki da juya
idanunta ta maida ga hadimar dake ƙoƙarin fara haɗa mata
abincin. Nunin abinda take buƙata tai mata da ɗan yatsa.
Hadimar na kammalawa ta koma cikin ƴan uwanta ta tsaya
itama kanta a rirrine.
Gaba ɗaya jinta take a takure, kwarjininsa ya cika ko'ina a
falon. Cikin dakewa da kaucewa gizago sa ta ɗan ɗago ta ɗan
saci kallonsa da nufin gaishesa idanunta suka shige cikin nasa
da ya ɗago da nufin kallon nata...
“Who are you?”
Ya fara faɗa cikin basarwa yana kaɗa idanusa da har yanzu
ke cikin nata tamkar bashi yay maganar ba. Badan a idanunta
tausasan lips ɗinsa suka motsa wajen ambaton wacece itan
ba zata iya gaddamar hakan. Kaifin idanunsa sun neman sage
duk wani ƙwarin gwiwarta. Ƙoƙarin fara sassauta nata idanun
tai yunƙurin yi cikin ƙanƙance su sannu a hankali. Shima sai ya
kankance nasa kamar yanda takeyi, fuskarsa na sake tsukewa
babu alamar sassauci tattare da ita. Nata ta fisga da ƙarfi ta
lumshe su, sai kuma ta buɗe a kansa tana mai sake tsuke tata
fuskar itama, bazata iya jure salon nasa ba dake neman ƙone
ƙudirinta, dan haka ta kauda kanta gefe babu alamar zata
bashi amsar da yay yunƙurin ji daga garetan..
“Barka da safiya”.
Ta faɗa a ƙoƙarinta na basar da tambayarsa ta farko.
Bai motsa ba, babu alamar kuma zai amsa ta. Hakan sai ya
sake sukar zuciyarta harta ɗan saci kallonsa, da sauri ta kauda
idanunta, dan da gaske fuskarsa ruguza mata lissafi take, da
gasken gaske shi ƙyaƙyƙyawa ne, irin ƙyawun dako a cikin
ƙasar tasu ake yabawa da shi, koda yake batai mamakin
hakan ba, dan Malikat Bushirat ba'a magana, duk da girma ya
fara zuwa gareta tsantsar ƙyawunta a bayyane yake. Hakama
Malikat Haseena dake matsayin kakarsa data haifi babansa
tunda ita dai bataga baban nasaba ko'a hoto har yanzun,
amma zubin Malikat Haseena dana Daneen Ammarah ya
tabbatar mata shima ɗin dai zai kasance ƙyaƙyƙywan ne......
“What is your goal in life?”.
Kalmomi guda shida suka katse mata tunani a bazata. Ta
kallesa tana ƙoƙarin danne mamakinta kan waɗan nan
tambayoyi da yake faman yanko mata kai tsaye. Ganin yanda
ya zuba mata ƙasaitattun idanunsa masu firgita mara gaskiya
ta janye nata tana yamutse fuska. (Damarki ce wannan) wata
zuciya ta ayyana mata. Cike da gamsuwa ta sake kauda kai
gefe dan har yanzu tanajin kaifin idanunsa a kanta. “Ni ban
kasance kowa ba sai talakar dake a ƙarƙashin mulkinka ranka
ya daɗe. Abinda nake son cimmawa kuwa a rayuwata irin
abinda shugaba ke fatan cimmawa ga talakawan ƙasarsa ta
hanyar mulkarsu da fuska biyu ne”.
Yanda tai maganar kanta tsaye babu ko ɗar ya sashi jin
mamakinta. (Tabbas wannan abar ba mutum bace) zuciyarsa
ta tabbatar masa. A zahiri sai ya ɗauke kansa cike da
basarwa. Shiru babu alamar zai sake tankawa har Iffah tama
fidda rai ta cigaba da tsakurar abincinta kamar yanda yakeyi
shima.
“Wasa da rayuwarki kuskurene ga ƙarfin halinki, ƙin
kasancewar ki tarihi a wannan safiyar bashi ke tabbatar miki
nasarar tsallakewa ba”.
A yanzun kam zantukansa sun zama masu matuƙar tasiri a
fitarsu da saurarensu gareta, jin bazata iya dannewa ba ta
amsa batare data ɗago ta kallesa ba,
“Hakane shugabana, sai dai fa _Fate is some thing
undeniable”_
Ya basar babu alamar yanzu ma zai amsa, shayin sa ya
kai baki cike da ƙasaita. Itama sai bata sake cewa komai ba ta
cigaba da cin abincin tana mai kallonsa ta gefen ido, sannu-
sannu tabi sautin motsa plate ɗin gabansa da kallo har kan
lallausan farar fatan hanunsa masu ɗauke da tsaftatattun
fararen dogayen farce, baya tai ƙoƙarin jan jikinta batare data
yarda idanunta sun wuce kallon hanun nasa ba. Yanda ya
basar da ita ɗin kuma sai yay matuƙar sukar zuciyarta, dan
bata buƙatar tattaunawar tasu ta tsaya iya haka. Amma sai
bata yarda fuskarta ta nunaba. Sai ma mamakin ƙasaita da
tsantsar izzar wannan bawa da zuciyarta ke faman yi. A wani
ɓangaren ita kanta dakewa kawai take, amma kwarjininsa da
gizago na firgita ta matuƙa. Tana ƙara tsarkake sunan ALLAH
akan yarda da jinin mulki gaskiya ne. Duk da ta shigo daular
ruman da wani ƙudiri a ranta hakan bazai hanata girmamashi
ba, koda ace tayima yunƙurin hakan kwarjinsa bazai bata
damar yin saɓanin girmamawar da kowa ke masan ba. So
take taji tsanarsa a ranta kamar yanda takeji kafin ganin
wannan fuskar matsayin shi amma zuciyarta taƙi bata haɗin
kai. Numfashi taja a hankali ta fesar a ƙasan maƙoshinta.
“Kokawa da ƙaddara a fuskar iyawa na nufin faɗuwa!
Kinga ko what you get is, what you have?”.
Ya faɗa cikin katse mata tunani dai-dai yana ɗagowa.......
✍️

“Fareedatu kibar danginmu su tsinkayi yini da kwana cikin
sallama, Banda taro dutsen zuma inake ina kace nace da
dodon may...🥱🏇”.

34
........(Mi wannan mutumin ke ƙullawa?). Ta faɗa a zuciya
batare data motsa ba. (Keda ke neman kusanci da shi dama
miye matsalarki da koma mi yake nufi) wata zuciyarta ta sake
ayyana mata. tamkar wadda aka zaburar sunan Arfa da Fariha
ya fara amsa kuwwa a zuciyarta har tana jinsa yana tashi bisa
sararin samaniya.
Kaifafan idanunsa masu nuna tsaurinsa ya zuba mata ganin
ta basar da shi itama. Kusan mintuna uku babu alamar zata
tankama zancen nasa har ya fara jin haushi. Ta taɓe baki da
kauda kanta gefe, cike da dakewa ta furta, “Da gizago na
tsorata ƙwarin gwiwata da bazan amincewa shigowa ramin
zakin da ɗanyen nama shine abincinsa ba. Karka damu a
kaina ranka ya daɗe, dan a wannan gaɓar *_cuta ce ta ɗakko
cuta, ɓarawo ya ɗakko akwatin maciji”._*
Fuska ya ɗan motsa kamar zaiyi murmushi, sai kuma ya
basar. “Bana haɗa ƙwanji da mage duk da kamaninta na
yanayi da nawa matsayina na ZAKI har a hallaya. Ki kama
kanki dan kina buƙatar rayuwa mai tsaho wajen moran
ƙuruciyarki”.
Ya faɗa da muryarsa mai zurfi da ƙasaita yana miƙewa ya
zagayeta ya wuce abinsa. Shiru bata motsa ba har ta gama jin
ɓacewar sautin takunsa a wajen, ta ɗan cije bakinta “Zaki
zako ka magantu fiye da haka”. Ta faɗa a fili cike da
kwaikwayo salon maganarsa tana sakin wani lallausan
murmushi da kai kofin shayi a bakinta, duk da zafinsa ta
rumtse ido ta kwankwaɗe abinta sannan ta juya taima
hadiman dake tsaye har yanzu kallo ɗaya ta ɗauke kanta
batare da damuwar komai ba, dan tasan basuji komai ɗin ba
da suka tattauna. A yanda suke maganar ma wani sai ya
ɗauka wani zancen soyayya ne ya haɗasu. Komai batacema
kowa ba itama ta miƙe tabar wajen, duk suka bita da kallon
ƙasan ido kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa.
A tafiyar tata tana ɗan kalle-kalle taci karo da camara,
komai bataji a ranta ba, dan tayi tsammanin hakan tun farko,
saboda babu yanda za'ai sashen mutum mai ƙarfin iko kamar
Tajwar ace babu wani tsaro makamancin hakan koma fiye da
hakan. Da ƙyar ta iya gane ɗakin data kwana. Tana shiga ta
zube a kujera da sauke nauyayan numfashi, ɗakin da akaima
gyara ɗan gaske tabi da idanu, sai taga ma kamar ba'a cikinsa
ta kwana ba, ganin akwatin kayanta kawai ya tabbatar mata
da shi ɗin ne. Tunani mai ƙarfin gaske ta faɗa kusan kashi uku
zuwa huɗu musamman akan kawota da Malikat Haseena tayi,
mi tsohuwar ke nufi da haka bayan su suka sanar mata an
rasa matan baya ne a dalilin kawosu turakar Shahan-shan ɗin.
Sai kuma akan Tajwar Eshaan ɗin, na farko waccan fuskar
data gani a waje kafin shigowarta masarautar matsayin
matarsa. Na biyu wannan fuskar ta yanzu da bata da
banbanci da waccan ɗin, na uku hanyar da ya kamata ta
cigaba da bi domin sanin ainahin wanene Tajwar Eshaan Ibn
Haysam Abdul-majeed a baɗini da zahirin rayuwa. Domin da
gasken gaske tana a cikin ruɗani akan fuskokin nan biyu data
gani a mabanbanta muhallai. Su ƴan biyu ne? Kokuwa shi
ɗinne ke ɓadda kama yana fita?. Abu na uku kuma abinda ya
faru a daren jiya da sai a yanzu yake bata matuƙar mamaki,
tun a jiyan bawai ta ajiyesa a gefe bane dan bashi da
muhimmanci ga haɗarin da tasan ta kawo kanta ciki, kawai
dai bata san dalilin da yasa bataji ko ɗar ba a zuciyarta na
tsoro, kuma har yanzu batajin tsoron sam, dama kuma tun
asali bata da tsoron. Dan Iffah irin mutanen nan ne masu
ƙesashiyar zuciya mai iya tunkarar komai koda yanada haɗari
a garesu, tanada naci da zama kaifi ɗaya akan zimma da
cimma buri duk da ƙarancin shekarunta. Na ƙarshe
tattaunawarsu ta yanzu da shi da girman kalaman da yay
amfani wajen jifanta da su. Ta ɗan murmusa da cije lips ɗinta
tana mai lumshe idanu a hankali......

★★.... ★★.....

Zuwa yanzu tako ina maganar tsallakewar Iffah ce ke
kaikawo a cikin masarautar. Kowa ya nutsu wajen tattauna
abinda ke bakinsa da abokin maganarsa. Wasu jin daɗine
game da hakan, wasu ko baƙin cikine a ransu, dan mutuwar
Zawjata-almilk ɗin kamar wani makamine a hannayensu na
dukan nasarar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ɗin.
Tsallakewar Iffah kuma zai kasance kamar damar
ƙalubalantarsa da suka riƙe ya kuɓuce musu kenan. Ita kuma
yarinyar kimarta da nunawa duniya tafi ƙarfin masu ƙarfin zai
yi tasiri a zukatan jama'a.....

★Komai dake faruwa yana isa da shiga a kunnen manyan
masu faɗa aji ta bangaren iko da kusanci da Tajwar Eshaan
ɗin. Wato Malikat Haseenat da Malikat Bushirat. Sai dai sunyi
biris babu alamar zasu tofa nasu akan hakan bayan bayyanar
farin cikinsu akan fuskokinsu daya gaza boyuwa ga kowa. Dan
a dalilin wannan al'amari Malikat Bushirat har ƴafiya tayi ga
wasu firsinoni dake a cikin kurkukun masarautar akan wasu
laifuka nasu da basu kai sun kawo ba. A cikin sunne kuma aka
sallami harda Diwa a dalilin bincike daya tabbatar da bata da
hannu game da abinda ya faru ga Iffah a waccan ranar.

★A ɓangaren Malikat Haseenat kuwa maimakon bama
abinda ke zuwama kunenta muhimmanci hankalinta ta maida
wajen tantance hadiman da zasu koma aiki a karkashin Iffah
ne bisa taimakon Daneen Ammarah da farin cikinta itama
yake a bayyane. Dan itama dai har kyaututtuka na
musamman yau ta bada ga hadimai tare da sakawa a tattaro
mata dukkan malaman masarautar zuwa sashen Iffah da
bukatar suyi saukar Alkur'ani mai girma. Ta kuma miƙe da
karfin jikinta wajen shirya lunch na musamman ga Tajwar
Eshaan da amarya Iffah Zawjata-almilk...

*_★BARRISTER★_*

Abubuwan da suka faru sun sakashi dakatawa a zahirance
bisa shawarar Kaka. Sai dai yana cigaba da gudanar da wani
binciken sirri dan yayma kansa alƙawarin binciko duk mai
hannu akan wannan al'amarin nasu Babiy da ma inda aka
ɓoye su.
Kamar yau ma tun jijjifin safiya ya fito daga gida. Kai tsaye
hanyar jihar Hubab ya nufa inda bincikensa ya tabbatar masa
nanne ainahin jihar da matar Abu Moosa ta fito. Jihar Hubab
makwafciyar Dahab city ce (Daular ruman kenan) dan haka a
cikin ƙanƙanin lokaci ya isa. Bai tsaya sanyaba ya ɗauka
hanyar ainahin kauyensu kuma. Kasancewar anan ma
hanyace shimfidaɗɗiya a kanƙanin lokaci ya isa. Da farko ya
sha wahalar binciken inda gidansu yake, sai da yay dabarar
nuna hotonta sannan.

Kusan mintuna goma bayan isar da saƙon tanada baƙo
gareta ta fito cikin irin shigarsu. Tayi ɗan tsamm alamar shan
jinin jikinta kafin ta ƙaraso a yanayin son basarwa. Barrister
shi ya fara gaidata, tare da sanar mata sunansa. Lokaci ɗaya
ruɗani ya bayyana akan fuskarta ta shiga waige-waige irin na
rashin gaskiya da ƙoƙarin ja baya daga garesa...
“Bawan ALLAH ina baka shawara ka taimaki kanka ka bar
ƙauyen nan, babu wani abu da zaka iya ji a gareni dan ban
san komai ba”.
A fusace Barrister yay tsalle gabanta yana huci. “Baki san
komai ba amma akaje da ke har gida aka kamasu. Karki sha
mamakin bayan sanin inda kike har wasu abubuwa na sani a
kanki Mss Farishta. Rashin bani haɗin kai kuma na nufin na
tonasu kowa yasan ke ɗin wacece har ma da dalilin auren
Dawood, sani kankine wannan babban koma baya ne a gareki
kuma harma da zuri'arki”.
Yayu ta haɗiya masu kauri tana kallon Barrister, sai kuma
ta sake wawwaigawa tabbacin dai akwai abinda take shakka.
“Naji Barrister zan baka dukkan bayanan da kake buƙata,
amma ina roƙonka kabar wajen nan, idan ma zai yuwu
kauyen nan gaba ɗaya nake son ka bari. Wlhy na maka
alkawarin zan zo na sameka na kuma faɗa maka komai da
kake buƙata harma wanda baka sani ba”.
“Miyasa bazan sani ba a yanzu?”.
“Saboda zamanka anan yana da matuƙar haɗari”.
“Taya zan tabbatar da zaki zo ɗin?”.
“Na baka dama kabi duk hanyar da zata bibiyi al'amarina”.
Kafaɗarsa ya ɗan ɗage sama da faɗin, “Okay inaga bana
bukatar hakan, kije kawai ni na san ta hanyar daya dace na
bibiyekin. Amma yaushe ne zamu haɗun?”.
“Inasha ALLAH a daren yau ka sameni a ƙauyen Jumna”.
“Garin su Abu Hanash da Dawood kenan?”.
“Insha ALLAH”.
Tafiya yake zuciyarsa na faman masa kaikawo akan
haɗuwar tasa da Farishta (matar Abu Moosa datazo har gida
da ƴan sanda aka kama su Babiy. ALLAH yasa kun gane🥱). Duk
da yasan zata iya ƙin aikata abinda ta faɗa na haɗuwar tasu a
garin Jimna ya zaɓi barinta su haɗun can bisa lumana. A cikin
Hubab ya tsaya yaci abinci tare da sallar azhar. Ya fito
masallaci idanunsa suka sake sauka akan wata mota da tun
fitowarsa ƙauyen su Farishta ya lura da ita tana biye da shi,
sai dai duk da ya ganta suna tafiya kafaɗa da kafaɗa bai kawo
komai a zuciyarsa ba. Janyewa yay cike da rashin bama abin
muhimmanci ya shige motarsa da zummar zai cigaba da
tafiya kawai yaga an zagaye motarsa da bindigu.......

★★★.... ★★.... ★...


A firgice ta farka a ɗan barcin daya figeta bayan ta idar da
sallar azhar. Ta dafe kanta dake sara mata. Irin mafarkin da
tai da dare ne dai babu banbanci. Huci ta furzar da faɗin,
“Wace madara ce haka? Tabbas kodaga ina zata fito babu
alkairi a cikinta tunda har mafarkin nan ya sake maimaita min
kansa. Ya ALLAH”. Ta furta a fili zuciyarta duk babu daɗi, dan
zuwa yanzu Iffah ta fahimci wani ɓoyayyen al'amari game da
ita, tabbas in har zatai mafarki taita kuma maimaita irinsa sai
wani abu ya biyo bayansa mai taɓa zuciya, ta gane hakanne a
ɗan zamanta cikin masarautar nan, sai kuma auna abubuwan
da suka faru a baya kafin yau ɗin. Sai dai tana ƙoƙarin ƙin
gasktama kanta hakan dan kar zuciyarta ta shagala kan
abinda zai sakata kaucema umarnin mahaliccinta kuma. Ga
kanta jingim kamar yanda yakeyi a duk lokacin datai mafarki
makamancin haka, sai zufa data jiƙeta sharkaf tamkar wadda
tai wanka. Shigowar saƙo a wayarta da ke gefenta ya sakata
tsurama wayar ido na kusan mintuna biyu, kamar wadda aka
zaburar wani abu data shafa'a kuma sai ta jawo wayar. Data
ta kunna a take tai downloading WhatsApp app..., Bayan ta
kammala dai-daita komai tai searching number Sir Fawzan da
zuciyarta ke ayyana mata ta fara nema, cikin rashin sa'a taga
kusan kwana uku ma baya online ta hanyar lastsin ɗinsa. Duk
da hakan bai mata daɗi ba batai wani yunƙurin kiransa ba ta
maida akalarta kan number abokinsa Ajmaal. Cikin sa'a
shikam dai yana online. Sallama tai masa a taƙaice ta tura, sai
dai har kusan mintuna biyu babu reply (yana aiki) zuciyarta ta
ayyana mata. Aminta da hakan ya sata cigaba da ajiye masa
saƙo kawai a kan duk abinda ya sake faruwa bayan wanda ta
tura masa ranar. Daga karshe ta aika masa da roƙon ya
bincika mata iyayenta dan har yanzu hankalinta ya kasa
kwanciya dangane da su. Ta haɗa masa da adireshin gidansu,
da faɗin (In har kaci amanata ko yaudarata na barka da
mahaliccin rana da wata yay maka hukunci da alhakin dukkan
al'amuran ƙasar ruman da zalincin mulkin wannan shaiɗanin
dodo ke tafin hanunsa). Daga haka ta fito shima Sir Fawzan
ɗin ta tura masa gajeran saƙo ta goge WhatsApp ɗin gaba
ɗayansa ta ajiye wayar.
Da ɗan layin nauyin jikin dake tare da ita ta miƙe, tana
ƙoƙarin shiga toilet taji kamar an gitta mata ta baya. Idanunta
ta ɗan rumtse sai kuma ta waigo. Komai babu dai a zahiri dan
haka ta kaɗa kanta kawai ta shige bakinta da addu'a....

Fitowarta kenan bayan ta watsa ruwa alerm ɗin ƙofar yay
ƙara alamar ana knocking. Sai da ta zira doguwar rigar abaya
data ɗakko cikin kayanta sannan ta ƙarasa ƙofar ta buɗe.
Hadimar dake tsaye ta zube ƙasa cikin girmamawa tana
kwasar gaisuwa. Amsa mata Iffah tai, zuciyarta babu daɗi
akan yanda suke ƙasƙantar da kansu, ta amsa cikin sauƙin
muryarta dake a sanyaye sakamakon mafarkin da duk ya
sakar mata kasala..
“Wani abu ya faru ne?”.
Ta tare hadimar tunkan tace komai. Kai ta gyaɗa mata tana
sake rissinar da kanta. “A gafarceni ya Zawjata-almilk. Dama
abinci ne aka kawo daga sashen mai Babban ɗaki”.
Iffah tai ɗan jim tana hasashen wace kuma mai babban
ɗaki? Kamar hadimar ta fahimta tai saurin mata fashin baƙi
da “Malikat mai babban ɗaki”.
(Malikat Haseenat) shine abinda zuciyarta ta ayyana mata.
Ta kaɗa kanta da faɗin, “Okay ba damuwa zan fito”. Daga
haka ta maida

Please Login or Register in order to submit comment