Reading Dauɗar Gora by Bilyn Abdull ce Chapter 13 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kujerar Shahan-shan tun yana ƙarami kamar
yanda mahaifiyarsa ta horesa a kai, dan haka tayi matuƙar
gwabza ɓoyayyen yaƙi akan marigayi Tajwar Haysam akan
haihuwa har ALLAH ya bashi Tajwar Eshaan. Haihuwar Tajwar
Eshaan wata ɗimuwace a nasararsu, saboda haka sun aikata
abubuwa da yawan gaske na ganin bai kai ga matsayin da
yake a yanzu ba ciki harda karkato da hankalin Miran Arshaan
babban ɗa ga Ameera Aasfah amintacciya a wajen Malikat
Haseena miji kuma ga Jasrah. Miran Arshaan sam bai biyo
ƙyawawan halayen mahaifiyarsa ba, munafuki ne shima kuma
yanada boyayyan nasa sirrin duk da riƙo irin na uwa da
Malikat Haseena tai masa bayan rasuwar mahaifiyarsa,
shiyyasa ya yarda ya haɗa kai da Miran Jasim domin kauda
Tajwar Eshaan. Amma kaico UBANGIJI shi mai bawa wanda
yaso ne, dan gashi dai Tajwar Eshaan ya zama Shahan-shan a
daular ruman. Amma hakan baisa sun bar ƙulla-ƙulla na ganin
cikar burinsu ba. ALLAH yasa kun gane🥲).
Miran Jasim da dama tsumayen isowar Miran Arshaan ɗin
yake ya miƙe daga zaman ƙasaitar da yay a katafaren falonsa
da ya jiku da kayan more rayuwa. Juna suka tsirama ido cikin
nazari dan bayan ƙullin tsakaninsu kowa nada ɓoyayyen sirri
na akan ɗan uwansa. Miran Jasim ne ya fara kauda kansa ya
maida hannayensa baya ya goya ya tako a sannu har
tsakkiyar falon. Hakan yasa shima Miran Arshaan ɗin ƙarasa
shiga suka tsaya gab da juna.
“Arshaan Akh Barka da isowa”.
Kai Miran Arshaan ya jinjina masa, sai kuma shima ya maida
hannayensa ya goya a bayansa tare da ɗan takawa ya koma
ta gefensa yana fiskantar window. Murmushi Miran Jasim
yayi tare da juyowa yana kallonsa. Shima ya ɗan taka ya sake
komawa gabansa. “Arshaan Akh kayi shiru, bayan kuma naga
magana mai muhimmanci a cikin idanunka kamar yanda ka
sanar dani ta waya”.
Huci Miran Arshaan ya furzar, sai kuma ya ɗago suna
kallon juna shi da Miran Jasim ɗin. “Jasim Akh akwai damuwa
ne. Yanzu nakeji wajen Zawjata. A ziyarar Yaron can ta yau
wajen kakarsa akwai shirya ganawa tsakaninsa da yarinyar da
shashashar matar can da ban san amfaninta garemu ba tasa
muka aura masa”.
“What! Waye yay wannan ƙullin?”.
“Bana tunanin kana buƙatar tambaya dan kasan wace
gadararriyar ce zata iya yanke wannan hukuncin. Na gaji da
ganin matar can a raye.”
Murmushi Miran Jasim yayi da cije lips. Cikin ɗacin
murya ya ce, “Ba Bushirat bace ta cancanci mutuwa. Waccan
tsohuwar ce Arshaan Akh. Sai dai kuma su duka bazasu mutu
yanzu ba”.
“To sai yaushe?”.
“Sai sunyi kuka akan gawar wancan shashashan yaron kamar
yanda sukai kuka akan ta ubansa”.
Karan farko Miran Arshaan ya saki murmushi. Sai kuma ya
warware hanunsa da ɗage kafaɗa. “Hakan ma shiri ne mai
ƙayatarwa. Yaya batun uban yarinyar da ɗan uwanta? Dan
sun sami Barrister Abdullah Aas a yanzu haka”.
Da sauri Miran Jasim ya kallesa. “Miyasa ban san wannan
ba?”.
“Saboda bashi da muhimmanci dan na gama musu
talala”.
“Arshaan kasan kuwa wanene Barrister Aas?”.
“Duk yanda saninsa zai iya bani tsoro ai bai kai razanin sanin
muɗin su wanene ba a garesa nake ji?”.
“Ba ina maka magana bane akan ƙarfin iko”.
“Mi kake son na sani?”.
“Ba lokacin sanin tarihi bane. Kawai kayi duk yanda zakai na
ganin ya dakata, su kuma a canja musu wajen zama”.
“Wai miyasa muke bukatarsu a raye?”.
“Saboda sune makamin da zamu juya yarinyar a ƙarƙashin
ikon mu yanda muke so”.
“Kenan bamu da buƙatar matar hadimin can itama, dan
ta gama mana aikinmu”.
“Matsalarta mai sauƙi ce. Daƙile Barrister Abdallah Aas ce
mafi muhimmanci daga daren yau zuwa yinin gobe. Sai dai
ina son a masa talala ta hanyar sanin inda suke kafin ya tsinta
kansa a ramin damisa in har baiji gargaɗin farko ba”.
Miran Arshaan ya lumshe idanu da sakin siririyar dariya
idonsa akan Miran Jasim. Shima dariyar yayi da masa
jinjina.......


★... ★★.... ★....


A sashen Malikat Haseenah ma an gama shirya komai na
tarbarsa, tun daga kan abincin da yake ci tare da kakar tasa
har zuwa tsaftar sashen ma a yau ta kasance ta musamman
duk da a kullum a tsaftace yake. An shirya kalolin abinci da
ƙamshinsu tun duhun magrib ya cika ko'ina na sashen har
maƙwafta ma na iya jiyowa. Abincine da Daneen Ammara ta
girka sa da kanta saboda kar a cutar da shi ta hanyar
girkawar, sai taimakon ƙanwar Malikat Haseenah da suke kira
Yumma.
Gab da ƙofar fadar Malikat Haseena lafiyayyar motar da
yake ciki ta tsaya, cikin rawar jiki ɗaya daga cikin Hadiman ya
buɗe masa, sauran kuwa tuni sun zube ƙasa kan gwiyawunsu
kawunansu a ƙasa domin girmamawa a garesa. Yaja fin
mintuna biyu bai fito ba duk da an buɗe masa, sai da ya mula
dan kansa sannan ya ziro ƙafarsa fara tas dake a cikin
ƙyaƙyƙyawan blue ɗin takalmi mai tsananin taushi da ɗaukar
ido da zai iya birge duk wani mai kallo, half cover irin na masu
sarauta, kusan sakan biyar a tsakani sannan ya ƙara zuro
ɗayar cike da ƙasaita. Tashin ƙamshin turarensa da takun
sawayensa ya tabbatar ma Malikat Haseenah isowarsa. Da
hannu taima dukkan amintattun hadimanta dake zagaye da
ita nunin su fice. Har rige-rigen bin ƙofar da zata kaisu falon
farko dazai fiddasu ta ainahin ƙofar sashen nata suke. A nutse
tsohuwar ta ɗago idanunta ta sauke a ƙofar dai-dai
shigowarsa. Tar-tar yake kallonta a cikin hasken ƙwan
lantarkin daya haske falon kamar yanda itama take kallon
ƙyakyawar fuskarsa dake a tsuke. Tai murmushi da jan
numfashi ta fesar a hankali lokacin da yake isowa gabanta.
Farin hannunta da fatar ta gama tattarewa saboda tsufa ya
ɗan rissina ya kamo tare da kai tausasan lips ɗinsa ya
sumbata.
“Amincin ALLAH da yardarsa su tabbata ga managarcin
tushe mai cike da tsaftatacciyar yabanya”.
Idanunta ta lumshe a hankali da sakin murmushi a lokaci
guda, sai kuma ta buɗesu tare da buɗe masa hannayenta.
Rungumeta yay shima yana sakin ƙasaitaccen murmushi a
karo na farko. Tsahon sakan talatin suna a haka kafin su saki
juna ya dago amma bai ɗaga daga ranƙwafen ba. Hannunta
ta ɗaura saman tausasashiyar sumarsa da a kallo guda zaka
tabbatar da kuɗaɗen da take lashewa bazasu kasance na
wasa ba.
“Aminci da yardar UBANGIJI ta kasance tare da kai kaima
farar yabanya abin alfaharina”.
Idanunsa ya ɗan ƙankance da jinjina kansa yana murmushin
da ita kawai ke iya ganinsa kai tsaye a fuskarsa kamar haka,
sai ko Malikat Bushirat. Daga haka ya miƙe da ƙyau ya zauna
ƙasan tattausar dardumar da aka shirya musu abinci, zama
yay irin zaman sarakai da suka isa suka tumbatsa. Idanunsa
ya zubama kakar tasa da murmushi ya gagara barin fuskarta,
dan duk wannan ranar tanajinta rana ta musamman ne a
gareta, sakamakon tuna mata da mijinta da ɗanta da takeyi
da kuma tsananin ƙaunar jikan nata a yanzu.
“Nannah Kina lafiya?”.
“A zahiri dai lafiya nake, amma a baɗini cike nake da
kewarka da ƙishirwar son ganinka a idaniyata Hafeedi”.
“Uhhm!” ya faɗa da ɗan lumshe idanunsa ya buɗe a
lokaci guda. “To ki koma sashena mana, in har da gaske ne
kina mun irin wannan buƙatar a kusa da ke”.
Yay maganar da yanayin zolaya, sai dai fuskar a kame take
babu alamar hakan tattare da shi. Itama murmushi tai batare
da tace komai ba dai-dai tana miƙa masa kofin data zuba
madara.
“Kwana biyu mike faruwa da kai?”.
Yaja wasu sakanni kafin ya girgiza mata kansa alamar babu
komai. Idanu ta cigaba da tsura masa har hakan ya ɗan
sakashi tsarguwa ya kauda kansa gefe. Itama ɗauke natan tai
gefe cikin rashin bama yanda yay ɗin muhimmanci. Sun
kwashe kusan mintuna uku a yanayin shiru kafin shi ya katse
hakan.
“Mamy fa?”.
Yay maganar a fisge tamkar yinta ya zama tilas ne a garesa.
Ita ɗin ma a ƙasaitancen ta bashi amsa da “Suna zuwa”.
Idanunsa masu girma da haske ya tsira mata. Kanta ta
ɗauke gefe dan tasan kalmar (Suna zuwa) ɗin ce yake
nemawa amsa.. Shima janye nasa idanun yay cike da basarwa
da ƙasaitarsa ya ɗauka kofin data zuba masa madara......

A dai-dai nan Daneen Ammarah ta shigo da sallama
hanunta riƙe dana Iffah dake cikin ƙyaƙyƙyawar doguwar
rigar abaya baƙa datai matuƙar amsar jikinta, Shirine na
musamman da Daneen Ammarah ta zauna domin yinsa
gareta da kanta. Cikin ƙanƙanin lokaci sirrintaccen ƙamshin
jikinta ya shiga rige-rigen isa hancin Malikat Haseena da mai
gayya mai aiki. Shaƙar ƙamshin turaren da zaton Daneen
Ammarah ce kawai mai shigowar ya sashi ɗago idanunsa,
cikin Sa'a kuwa ya sauke su a kanta. Murmushi Daneen
Ammarah da suka haɗa ido ta sakar masa, yayinda shi kuma
fuskarsa ke nuna tsananin ƙaunar da yake mata a zahiri.
Haka itama Malikat Haseena murmushi ne ƙawace a
fuskarta idonta akan Iffah da kanta ke rissine taƙi kallon
komai. Ƙara riƙe hanun Iffah Daneen Ammarah tai da ƙyau
kamar za'a ƙwace mata suka cigaba da takowa a nutse.
Malikat Haseena taima Daneen Ammarah nuni ta zaunar da
Iffah a kusa da ita, sai ya zam suna facing juna da Tajwar
Eshaan, sannan kuma a tsakkiyar su shi da Malikat Haseena
ɗin..
Gaba ɗaya ya tattara hankalinsa ga Daneen Ammarah
tamkar baiga tana tare da wata ba, “Amincin ALLAH da
rahamarsa su tabbata ga Mamy na!”. Ya faɗa akan laɓɓansa
kamar bashi yay maganar ba, dan ko Iffah da Malikat
Haseena ba jinsa sukai ba sai ita Daneen Ammarah da takai
zaune kusa da shi. itama ta sake sakin murmushi da kaɗa
masa kanta. “Tare da kai Abni, Amincin ALLAH da rahama da
kariyarsa su tabbata a gareka. Ina fatan kana cikin ƙoshin
lafiya da nutsuwar zuciya?”.
Kansa kawai ya kaɗa mata, sai kuma ya ɗan ɓata fuska.
Murmushi ta sake saki da maida idanunta kan Iffah da
Malikat Haseena kema magana.
“Hafed-ti! An hanaki barci ko?”.
A hankali Iffah da ƙirjinta ke faman harbawa da sauri-sauri ta
girgizama Malikat Haseena da tai maganar kanta. Cikin sanyin
murya da sauƙaƙa fitar sautinta ta ce, “A'a Mamma ai bamma
kwanta ba”.
“Masha ALLAH yaya jikin naki?”.
“Alhamdulillahi Mamma, Aminci ALLAH ya tabbata a gareki
a wannan lokaci”.
“Amin. tare dake kema Negar”.
Iffah ta ɗan murmusa har yanzu kanta a rissine. Daneen
Ammarah dake kallonsu da murmushi ta janye idanunta ta
maida ga Shahan-shan daya sake ɗauke kansa tamkar bai san
mike faruwa ba ma.
“Ibnati!”.
Ta kira sunan Iffah a tausashe kamar yanda ta saba.
“Na'am Mamy”.
Itama ta amsa mata kamar yanda ta saba. Sai dai ta kasa iya
ɗago kanta, dan duk da bata san wanene ba gaba ɗaya
kwarjininsa ya cika falon har tanajinta a matuƙar matse
kamar ta tsilla da gudu kozata samu nutsuwa....
“Ga yaro na”.
Ta faɗa cikin sigar son ɓiye mata ainahin wanene ɗin. Iffah
da bata damu da son sanin gaskiyar zancen Daneen
Ammarah ɗin ba ta amsa da alamar raunin murya a tare da
ita. “Amincin ALLAH ya tabbata a gareka. Barka da wannan
lokaci”.
Shiru babu alamar zai amsa mata, ran Iffah ya sosu dan a
rayuwa ta mugun tsanar wulaƙanci, duk yanda taso ta danne
sai ta kasa, a karan farko tun shigowarsu falon ta ɗago idanu
cike da jin zafi, dai-dai ya ɗan ɗago shima zai kai kofin madara
bakinsa idanunsu suka rufta cikin na juna...
Zabura Iffah tayi da ware manyan idanunta, yayinda
shima yay ɗan tsai yana kallonta na sakanin da basu gaza
biyar ba, sai kuma ya janye abinsa cikin halin ko'in kula ko
fahimtar yanayin data shiga ya sake gyara zaman
ƙasaitarsa.......✍️
26


........“Ya rabbi. Aljanin can dai”.
Harshen Iffah da zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri ya
suɓuce wajen faɗa batare data shirya hakan ba..Malikat
Haseena da furucin Iffah ya shiga kunnuwansu a bazata duk
suka ɗago suka kalleta.
“Ibnati! Aljani kuma a ina?”.
Cewar Daneen Ammarah a mamakance”.
Yawu Iffah ta haɗiya da ƙyar, sai kuma ta girgiza kanta da
sauri tana ƙaƙaro murmushi. “M... M.. Mamy bance komai
ba”.
Tai ƙoƙarin kare kanta da rawar harshe. Magana Daneen
Ammarah tai ƙoƙarin sake yi Malikat Haseena ta ƙyafta mata
idanu. Dole ta haɗiye ta maye gurbinta da murmushin son
basarwa. Jikin Iffah tsuma yake, amma tanata ƙoƙarin son
hana fitowar hakan ta hanyar matse kanta waje guda da
ambaton sunayen ALLAH a jajjere ko zata farka a ruɗanin da
takema kallon gizo ko tabbacin abinda take tsoro wato
Aljanin can ya cigaba da bibiyarta.
Daneen Ammarah na ƙoƙarin haɗama Tajwar Eshaan
abinci Malikat Haseena ta girgiza mata kai da yi mata nuni da
Iffah ta wutsiya ido. Amsa mata tai cikin lumshe idanu da
buɗesu akan Iffah.
“Ibnati”.
A ɗan zabure Iffah ta ɗago ta dubeta. Itama da idanu tai
mata nuni da abincin. Sam Iffah ba fahimtar Yaren nan nasu
ta cika yi ba kai tsaye, dan haka tai ɗan tsamm tana kallon
Daneen Ammarah ɗin har sai da ta furta mata da baki.
Numfashi ta sauke a hankali bana samun nutsuwa ba, na sake
shiga ɗimuwa da kaikawon bugun zuciya, a saɓule ta motsa
ta miƙe dan tayi ɗan nisa da shi, ta bayan Malikat Haseena ta
zagaya ta koma kusa da shi ta durƙusa. Ta gefen ido ta ɗan
sake kallonsa cike da taraddadi, cikin sauri ta kauda idanun
dan abinda ta gani ɗazun ne dai ta sake gani, ta jawo
numfashin dake neman kufce ma ƙirjinta da ƙyar....
“Ki haɗa masa waɗan nan”.
Daneen Ammarah ta katseta ta hanyar nuna mata abinda ke
cikin kwanikan gabansa.. Da ƙyar ta iya amsa mata da to,
sannan ta kame jikinta dake rawa, ta ɗan duƙo zata ɗauka
abu ƙamshin turaren da bazai taɓa ɓace mata ba ya daki
hancinta, da alama wanda take shaƙar ne tun ɗazun ya
dannesa saboda ba'ayi amfani da shi ba a yanzu ko kuma
wani abu da ban. Da sauri ta ɗan ja jikinta baya jininta na
tsinkewa, yanzu kam duk yanda taso dannewa sai da halin da
take ciki yaso bayyana....
“Hafed-ti! Ko jikin ne?”.
Malikat Haseena ta jeho mata tambayar da har shi kansa sai
da ya ɗan kallesu ta gefen ido. Kanta ta girgiza mata tana
ƙoƙarin danne abinda ke neman fin ƙarfinta na ruɗani.
“Ina cikin godiyar ALLAH Mamma”.
Murmushi Malikat ɗin tayi cikin cigaba da nazartar ta harta
kammala. Sosai kanta ke juya mata, dan haka ta koma
mazauninta da jan jiki tamkar ta tsala ihu ko hakan zai
bayyanama kowa a wane hali take ne...

Ko sau ɗaya Iffah ta kasa kai abincin bakinta, sai faman
juya spoon take da satar kallon yanda yake tsakurar nasa
abincin shima cike da ƙasaita. Lura da bata ci yasa Daneen
Ammarah mata magana. Sai kawai tai murmushi da ɗan ɗiba
kaɗan takai bakinta, juyashi take a hankali kamar mai tauna
magani, dai-dai shi kuma ya ajiye nasa cokalin zai ciri tissue
suka haɗa ido a karo na biyu. Da ƙarfin zuciya taso janye nata
amma yaƙi bata damar hakan, sai ma jan nashi da yay cike da
salo kamar zai lumshe ya sake buɗe su a tsakkiyar ƙwayar
nata. Ƙwarewa tai tsabar lamarin yazo mata a bazata..
Daneen Ammarah da Malikat Haseena suka zabura kanta
baki ɗaya, da kyar ta iya buɗe baki ta amshi ruwan da Malikat
ta saka mata a baki, yayinda Daneen Ammarah ke faman
shafa bayanta tana jera mata sannu.. A dukkan bidirin da ake
idan dutse ya motsa Tajwar Eshaan ya motsa. Har tarin ma ya
lafama Iffah ta samu daidaiton numfashi. Koda ganganci bata
sake yunƙurin duban sashen da yake ba har lokacin tafiyarsa
yay, duk yanda taso zamewa a masa rakkiya da taga Daneen
Ammarah da Malikat Haseena na shirin yi hakan bai yiwu ba,
dole ta bisu har waje. Tana ta faman ɗauke kanta amma
tamkar wani sihiri sai da suka haɗa ido dai-dai zai shiga motar
da aka buɗe masa. Wani irin karsashi da ƙwarin gwiwarta ne
a bazata suka dawo jikinta, ta yamutse fuska da tsuke baki ta
fincike nata.. Yayinda shi kuma ya ɗan motsa bakinsa tamkar
mai son yin murmushi ko magana....

(🤔???)

★★.....

Ruɗani, mamaki, al'ajabi sun taru sun hana Iffah runtsawa
a wannan dare. Kanta ya gama kullewa dangane da abinda
duk suka faru ɗazun. Shin mutumin nan aljanin ne da gaske?
Kokuwa wani abu daban da bata sani ba. Babu abinda ke
mata kaikawo a zuciya sai haɗuwarsu ta baya har sau uku,
kenan idan lissafin ta yayi dai-dai shiɗin jikan gidan nan ne
tunda Daneen Ammarah ta kirasa da ɗanta, kamar yanda
Malikat Haseena ta kirasa da jikanta. Shiyyasa yake komai
cike da ƙasaita da izzar da ko Shahan-shan ɗin da kansa iyakar
wadda zaiyi kenan ai. Ita kam al'amarin wannan gida ya fara
birkita mata lissafi. A lissafin ta dai Daneen Ammarah aka
haifa a gidan nan, Hakan na nufin ta rabu da mahaifinsa ne?
Kokuwa a cikin gidan itama take auren? Dan ita dai tunda
tazo anan take ganinta babu alamar tana da wani miji ko
gidan zama bayan nan ɗin..
“Ya rabbi”
ta faɗa a fili tana mai jan nannauyan numfashi ta fesar.....


*_WASHE GARI_*

A ɓangaren Malikat Haseena ma yanda Iffan ta kusan raba
dare tana juya al'amura a ranta haka itama ta raba dare
wasiwasi akan abinda ta fahimta da wanda ta nazarta. Data
kasa cigaba da riƙe abinda ke mata kaikawo tana idar da
sallar asubahi ta bukaci ganin Daneen Ammarah.
A ɗan rikice ta shigo da tunanin ko ta kwana babu lafiya
ne. Ganinta zaune sumul ya sata sauke ajiyar zuciya takai
zaune kusa da ita.
“Wlhy Mamma hankalina har ya tashi, nayi zaton ko kin
kwana babu lafiya ne”.
Ɗan murmushi tai batare datace mata komai ba. Sai dai
ta miƙa mata maganin da ake shafa mata a kafafu. Amsa tai
babu musu ta fara shafa mata itama tana murmushin.
“Ammarah mi kika fahimta?”.
Ta jeho tambayar tata kai tsaye ga Daneen Ammarah. Cikin
rashin fahimta Daneen Ammarah ta ɗago.
“Mamma akan mi?”.
“Haɗuwar Malik da Zawjata-almilk”.
“Mammah har kin sakani dariya, Miya kawo wannan maganar
kuma?”.
“Ke dai amsa mini ita”.
“Ban san mi kike son sani ba Mammah, amma nidai
nasararmu da dacewarsu matsayin ma'aurata na hanga
tattare da su”.
Murmushi Malikat Haseena ta saki da kauda kanta. “Ni
kuma ba hakan kawai na hanga ba”.
Idanu Daneen Ammarah ta tsura mata batare da tace komai
ba. Malikat Haseena datai shiru itama kamar bazata cigaba
da cewa wani abu ba ta nisa. “A nazarin danai musu tamkar
akwai sanayya tsakaninsu kafin haɗuwar jiya”.
“Sanayya kuma Mammah? Idan da na fahimta sun san
juna kenan kike nufi?”.
“Haka”.
“Haba Mammah a ina to zasu san juna? Karki manta Abni ba
fita yake ba. Ƙaddara ma yana fita, wanda ke zagaye da tsaro
ta ina sani da mu'amula mai ƙarfi irin wadda kike hasashe
zasu ƙullu tsakaninsa da yarinya mai matsayinta. Karfa ki
manta ko'a cikin gidan nan ba kowa ya san fuskarsa ba balle
talakawan dake rayuwa a waje”.
“Wannan shine abinda ya ɗaure kaina nima. Sai dai
azuciyata na faɗamin akwai abinda yake ba daidai ba da
saninmu tabbas”.
“Kamar mi kenan Mammah?”.
“Nima amsar da nake nema kenan”.
Babu wanda ya iya sake cewa komai sukai shiru kowa da
abinda yake tattaunawa da zuciyarsa......
★★..... ★★.... ★★.....


Alhamdullah Barrister yaci nasarar gano inda su Babiy suke,
sai dai ba'a jiya ba kamar yanda ya faɗama su kaka har suka
zauna zaman jira sai da sukaga yamma tayi babu wani bayani
sannan suka haƙura suka wuce. Bai ɓata lokaci ba kuwa yay
kiran Abu Zainab ya sanar masa. Shima cike da zumuɗi ya nufi
gidan Babiy domin sanar ma Kaka. Sai dai kuma ya tarar yaje
masallaci kasancewar lokacin sallar zuhur yayi. Dole ya
shanye zumuɗin nasa shima ya tafi masallacin. Bayan an idar
da salla ƙofar masallaci ya fito ya tsaya yana kallon duk mai
fitowa.
Daga can ciki kuwa Kaka dake a cikin mutanen da suke
sahun farko sai a karshe suka sami damar miƙewa suma. Ya
ɗaga zai miƙe mutumin dake a kusa da shi ya bashi hannu
alamar suyi musabaha. Babu musu ya miƙa masa nasa yana
ɗan murmushi. Mutumin da shima murmushin yake ya tsaida
kwayoyin idanunsa a tsakkiyar na kaka, hakan yasa shima
Kaka cigaba da kallonsa dan ya fahimci akwai wani abu....
“Nasan kasan girman alkairi tsoho. To karka yarda ka
maida shi da sharri ga wanda yay maka. Dan haka ina baka
shawarar hana waɗan can mutanen biyu cigaba da shiga
abinda bai shafesu ba. Inba hakaba kuwa kai da su kuna gab
da zuwa inda surukinka da jikanka suke yanzu. Na Barka
lafiya”.
Mutumin ya kare maganar da zare hanunsa a cikin na Kaka
ya miƙe. Da kallo kawai kaka ya bisa harya ɓacema ganinsa.
Kafin yaja numfashi ya fesar tare da miƙewa zuciyarsa na
faman kaikawo tamkar zata fito. Koda ya fito da Abu Zainab
ya fara cin karo, ya tsira masa ido na wasu sakanni kafin ya
karasa garesa. Abu Zainab da shima ya hangosa cike da
zumuɗi ya tarbesa, ko gaisawa basuyi ba ya rankwafa dai-dai
kunnen kaka ya gwargwaɗa masa saƙon Barrister...
Murmushi kaka ya saki na ƙarfin hali, sai kuma ya jinjina
kansa da ambaton Alhamdullah a hankali. Abu Zainab da bai
gama fahimtar yanayin kakan ba cike da zumuɗi yace, “Baba
muje Barrister na jiranmu yanzu haka”.
Idanu kaka ya tsira masa tamkar zai ce a'a. zuciyarsa na
tuna masa girman alkairinsu garesa, tabbas bazai so saka
rayuwarsu a gariri su da iyalansu ba, idan ma yaga wani zai
zama sanadi zai bada karfinsa wajen karesu. Kalaman wancan
mutumin sun sake tabbatar masa akwai lauje cikin naɗi game
da kama su Babiy, hakama ƙin amsar Ummu a asibiti waccan
ranar. Hakan na nufin kuma duk kaikawon da suke ana biye
da su.......
“Baba kaga gashi ma yana kirana”.
Abu Zainab ya katse masa tunani. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya
sauke, yanda Abu Zainab ya ƙagu ya sashi fahimtar bashi da
isasshen lokacin tunani, zai bari sai ya samu nutsuwa ya bi
hanyar data dace badan masu kurarin sunfi ƙarfinsa ba. Sai
dan kawai baya son bin wata hanya daya jima da kyamatarta
a ransa, amma da su ko inda yake basu isa tunkara ba balle
jininsa.....


*_BARRISTER_*

Barrister Abdallah Aas ya ajiye wayar daya janye manne a
kunensa alamar waya ya gama. Kallonsa ya maida ga
sakatarensa dake ƙoƙarin ficewa saboda ganin yana waya.
“Suhail”.
Ya dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa. Amsawa yay tare
da juyowa cikin girmamawa.
“Akwai damuwa ne?”.
“A'a Sir. Wani mutum ne dai ke buƙatar ganinka. Nayi
ƙoƙarin fahimtar da shi kanada uziri amma bai saurareni ba”.
Ɗan jimm yay kamar mai nazari, sai kuma ya huro iska da
kaɗa kai. “Okay ba damuwa shigo da shi kawai na gansa kona
minti goma ne dan zan fita ne”.
“Okay Sir”.

A yanayin da mutumin ya shigo ya saka Barrister tsira
masa ido, yakai zaune tun kan a bashi izini yana cigaba da bin
office ɗin da kallo tamkar mai irge kayan cikinsa. Sai kuma ya
juya ga Barrister tamkar wanda aka bama umarni ya miƙa
masa hannu. Kamar Barrister zai noƙe sai kuma ya miƙa masa
shima.
“Am sorry Barrister nasan baka Sanni ba. Na kuma shigo
kai tsaye batare da neman damarka ba” ya saki murmushi da
cigaba da maganarsa batare da ya bama Barrister ɗin damar
cewa wani abu ba. “Kar sani na ya zama damuwar abinda ya
kamata ka sani dangane da ni, mafi muhimmanci kawai kasan
miya kawo ni”. Ya kai ƙarshen maganar da ɗakko jakkar daya
shigo da ita ya ajiye saman tebirin Barrister.
“Waɗan nan kuɗaɗene da zasu isheka tsahon wani lokaci
kana amfana, ina son ka manta da zancen aikin da surikinka
ya kawo maka, idan son samu ne ma daga yau ka dakatar da
shi shiga abinda bai shafesa ba”.
“Duk akan wane dalili zanyi hakan?” Barrister da ɓacin
ransa ke yunkurowa ya faɗa cikin son dannewa.
“Ba dalilin ya kamata ka sani ba. Ƙin bin shawarar ne
matsalarka Barrister”.
Cikin bayyanar fushin Barrister gaba ɗaya akan fuska ya
yunkuro zaiyi magana ring ɗin wayarsa ya dakatar da shi
hakan. Atare suka kalli wayar sannan suka kalla juna. Wayar
mutumin ya nuna da sakin murmushi, “Bismillah”.
Barrister yaja ƙaramin tsaki da hararsa

Please Login or Register in order to submit comment