Reading Dauɗar Gora by Bilyn Abdull ce Chapter 19 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙara
miki lafiya”.
“Okay zamu iya tafiya”.
Iffah ta amsa mata kai tsaye. Hadima ɗaya ce tai gaba sosai
Iffah na biye da ita cikin takunta na nutsuwa da wasu kan iya
gani su fassara da abinda zuciyarsu ta basu. Bayanta Hadimai
huɗu na biye da ita cikin taka tsantsan da nuna girma da
ƙarfin ikonta a bayyane...........✍️

37



.........Duk ta inda suka gitta kwarjininta dake ɓoye
shekarunta kansa a bata girma irin wanda ya dace ga
Zawjata-almilk da suka isa a masarautar. Hadimai kam sai
zubewa suke bisa gwiwunsu sakamakon sanarwar da ɗan
kazagin da Iffah bata farga da shi ba sai da suka fara tafiya taji
shelanta tahowarta da yake yi. A yau kam ta ƙara jinjinama
girman wannan katafariyar masarauta mai abubuwan kallo
matuƙa. Sai dai ga mai kallo bazai taɓa fahimtar hakanba a
yanda take faman basarwa kai kace ita ɗin tun fil'azal jinin
sarauta ce. Ba wani nisa bane zuwa books room ɗin, hakan ya
sakasu isowa cikin ƙanƙanin lokaci dan ma tafiya ce ta
ƙasaita....

Cikin ƙankanin lokaci labarin fitowar Zawjata-almilk ya
karaɗe masarautar. Hadimai ƴan leƙen asiri dake watse ta
ko'ina sun gama kai labari ga iyayen gidansu. Da yawa
mamaki ya kamasu tare da gane lallai yarinyar tazo da
tsageranci. Inba tsageranci ba wace Zawjata-almilk ce ta taɓa
fitowa bayan kaita turakar Shahan-shan da kwana ɗaya kacal.
Wasu kuma kai tsaye fassara wannan fita suke da gatsali,
acewarsu Iffah nason tabbatar musu tafi ƙarfin iyawarsu,
ƙarfin ikon su kuma ba komai bane dan ta gagaresu.

★Malikat Bushirat kanta isowar wannan labari a kunenta
sai da tai wani tsamm na nuna mamaki, sai dai bata ce uffan
ba kasancewarta mace mai tsananin jin kai da izza. Tana son
Iffah, kuma ƙarfin halin yarinyar na kawatar da ita. Sai dai
hakan ba yana nufin zata dama damawarta ne a yanda taso
ba ko ƙetare tsarin zama a masarautar musamman ga
Zawjata-almilk irinta da ƙa'ida komai sai da umarnin Malikat
zatayi sa. (Kamar dai ita dake mahaifiya ga Tajwar Eshaan. A
ƙa'ida dole komi Iffah zatayi sai ta nema izinin mahaifiyarsa
kafin ta aiwatar). Jin al'amarin ya cigaba da caccakar zuciyarta
ta sallami duk hadimanta. Kamar ƙiftawar ido suka ɓace
kuwa. Rai a ɓace ta ɗaga waya tai kiran Jasrah da ita bama
tasan wainar da ake toyawa a masarautar ba kasancewar a
ɗan tsakanin nan tana fama da laulayin ciki ne sama-sama.
Duk da a halin rashin jin daɗi da take ciki bazata iya ƙin
amsa kiran ƴar uwar tata da takema kallon uwa a yanzu ba.
Haka ta kimtsa cikin dauriya ta nufi sashen Malikat Bushirat
ɗin. A tsaye ta sameta cikin yanayin ɓacin rai da ya kasa
ɓoyuwa a kan fuskarta. Sai duk taji itama nata ran a jagule...
“Akia kina lafiya kuwa? Miya ɓata miki rai haka har fuskarki
ta kasa ɓoye wa?”.
Malikat Bushirat ta zuƙa kakkaurar iska ta fesar tana
mai kallon ƴar uwar tata. Cikin ɗacin murya tace, “Yarinyar
nan ce”.
“Yarinya kuma? Wace yarinya kenan?”.
Kamar bazata tanka ba, tai taku ɗaya zuwa uku batare data
dubi Jasrah ba tace, “Zawjata-almilk. Da alama tana buƙatar
sai an saita mata zama da tuna mata nan daular ruman ce ba
getto eria ɗin data rayu ba. Komai muna yinsa da ƙa'ida bisa
umarnin na gaba”.
“Kiyi haƙuri Akia. Amma na kasa fahimtar miya kawo
wannan maganar, wace kuma Zawjata-almilk ce a cikin
yaran? Dan nasan dai kinfi kowa so da ƙaunar wadda ke tare
da shi a halin yanzu”.
“Ina sonta bashi zai bata lasisin shimfiɗa abinda ta gadama
na a saman nawa ƙarfin ikon ba. Yanzu labari ya iso gareni ta
fito daga sashen Saiful-malik zuwa books room tare da
hadimai”.
“Tofa, ita kuma da wannan tazo? Mu muna murnar
samunta matsayin wadda zata share kukanmu amma zata
fara da haka?. To amma fa Akia wani hanzari ba gudu ba. Shin
baki ganin salon yarinyar a wani mahangar nasara ce a
garemu. Na farko dai babu wanda yasan ta fito ne batare da
umarninki ba. Na biyu koba komai ta sake jaddada isar da
saƙonmu akan maƙiya. Na uku salonta tamkar barazana ce ga
duk wani shu'umi dake rayuwa a wannan masarautar. Inaga
bai kamata ki damu ba, dan a wani ɓangaren ma kamar mune
masu laifi, karki manta Mammah ta mikata sashen Abni
batare da bin ƙa'idojin da ake kai Zawjata-almilk turakarsa ba.
Sannan inada tabbacin ba'a sanar da ita komai game da tsarin
komai ba fa, sai aikin da muka faɗa mata zatayi a garemu”.
A hankali Malikat Bushirat ta saki wata nannauyar ajiyar
zuciya. Cikin kwantar da murya ta ce, “Hakane kumafa Jasrah,
kin tunatar da ni abinda ya ɓacemin har idona ya rufe. Sai
yanzu na fahimci lallai wannan fitar tata ma da alama tanada
manufa akan umarnin aikinmu. Duk Mamma ce da wannan
kwamacalar da muka kasa fahimtar manufarta a kai, nayi
niyyar zuwa sashen nata ma naji dalili baƙin nan na ɗazun
suka cinyemin lokaci. Amma munyi magana da Ammarah
zuwa anjima zanje ko cikin ɓadda kama ne”.
“Hakan yayi, dan koni ina son sanin yaya akai hakan ta
kasance. Duk da dai Alhamdullah yarinyar ta kuɓuta. Amma
mun kwana a fargaba ai dan ko barci jiya banajin waninmu
yayi wlhy. Hatta da Abu Harith kwana yay tunani”.
Murmushi Malikat Bushirat tayi, dan har cikin ranta tana
ƙaunar ƙanin mijin nata kuma mijin ƙanwarta, tare da yaba
ƙoƙarin sa akan kulawa da kaunar da yake nunawa ga gudan
jinin nata tilo da har wasu ke jin zafinsa a gidan bisa hakan.....

★★....

Katafaren ɗakin daya kasance mai cika ido ga Iffah tsarinsa
ya matuƙar ƙawatar da ita. Ta samu jagorancin shiga lungu da
saƙo na cikinsa bisa taimakon masu kula da ɗakin. Inda a
zagayen nasu suke nuna mata abubuwan tarihi na tun farkon
ƙarnin kafa Daular ruman ɗin da suka shuɗe cike da
girmamawa a gareta. Tafiya kam mabuɗin ilimice haƙƙun dan
Iffah ta ilmantu da abinda yafi wanda ta sani ƙalilan a baya
dangane da tarihin daular ta ruman da akan tsakura musu a
darasin makarantu.
Shugaban masu kula da sashen ya matuƙar nuna jin
daɗinsa da bata shawarwari kan tsarin zama mai nazarin
tarihi data ambata dan abune daba kasafai ake ganinsa ga
matan cikin masarautar ba. Akwai wadda ma bata taɓa taka
ƙafarta cikin ɗakin litattafan ba. Amma ita gata ƙaramar
yarinya da rayuwarta ke kamar akan ɗar-ɗar abinda ta fara
nuna sha'awa na farko akansa kenan. Shine ya fara zaɓa mata
books daya ga ya dace ta fara dubawa, hakan yasa ta basar
da waɗanda ta shigo nema kai tsaye, dan a ganinta bin
shawarar tasa zaifi bata fiye da abinda take buƙata ɗin.
Shugaban da shekaru sunyi matuƙar ja a garesa yaji daɗin
amsar shawarar tasa da tayi, dan yasan duk da zai iya haifarta
matsayinta ya bata ikon yin duk yanda taso a sama da shi...

A cikin farin cikin daya goge duk wani damuwarta a
wannan yini ta fito hadimanta na take mata baya ɗauke da
ɗirka-ɗirkan littafan da ta ɗebo. A yanzu ɗin ma dai tako ina
hadimai faman zubewa suke domin girmamawa a gareta
harta isa sashenta data basu umarnin su kaita saɓanin sashen
Shahan-shan daya kamata ace ta koma tunda a ƙa'ida sati
guda zatayi kamar yanda Malikat Haseena ta sanar da Tajwar
Eshaan. Iffah kam da ba zama akai aka faɗa mata komai na
ƙa'idojin ba haka kawai taji bata bukatar komawa zaman
takura da zuciyarta ta ayyana mata rashin amfaninsa. Shi dai
wanda aka kaita dominsa ko kallo bata ishesa ba, hasalima
baya kallonta da suffar da suka miƙata garesan kai tsaye. Yo
dole ta faɗi haka, tunda wane mijin ƙwarai ne zai jefama
matarsa kalmar tambaya ta ita (wacece?) Bayan da saninsa
aka kai sadakinsa domin aurota. Bazata iya ɗaukar waɗan nan
abubuwan ba, dan bama abinda ya kawota nan ɗin ba kenan
tun fil'azal. A ganinta kuma ba sai dole an kaita garesa an
ƙaskantar da ita ba, zatabi hanyoyin daya dace na haɗuwa da
shi har lokacin da zata cika ɓoyayyen burinta....
Da wannan tunanin suka ƙarasa sabon sashen nata.
Tabbas ta jinjinama ƙoƙarin su, dan ko makaho ya laluba
yasan wannan sashen yayma wanda aka kaita fintinkau a
komai duk da shima wancan ɗin dai ba baya bane a tsaruwar.
Ta ɗan sauke numfashi da kaiwa zaune bisa ɗaya daga cikin
lumbutsa-lumbutsan kujerun da aka shirya falon da su
bakinta ɗauke da bismillah. Suma dai hadiman nata bayan
sun ajiye litattafan a saman Centre table a gabanta suka
zube. Taja tsahon mintuna goma tana mai nazarinsu kafin ta
ɗan sauke numfashi da miƙewa.
“Ina buƙatar zama da duk wanda zai kasance da Ni a
wannan sashen zuwa anjima”.
Cike da girmamawa duk suka amsa mata kawunansu a
ƙasa. Ta ƙara jan numfashi ta fesar batare data farga da salon
izzar da yay kutse ga al'amarin ta na yanzu ba ta kai dubanta
ga agogon falon. “Muna da sauran lokaci yanzu da zai ishemu
zagaya sashen kafin na shige salla”.
Anan ma sun amsa mata ɗinne da girmamawa. Batare
da ta sake cewa komai ba tai gaba duk suka miƙe suna take
mata baya. A yanzu ma dai wadda ta jagorancesu zuwa books
room ce ke mata bayanin sashen da tsarinsa yanda ya
kamata. Cike da gamsuwa batare data furta komai ba koda so
ɗaya take gyaɗa mata kai. Sashen ya ƙunsa abubuwa masu
yawa da zaman lissafinsa zai zama ɓata lokaci da cinye mana
page, bayan sun kammala zaga ko'ina Iffah ta shiga bedroom
ɗin da zuciyarta tafi aminta da shi matsayin master bedroom
ɗin ta.
Mamaki ya kamata lokacin da taci karo da guntuwar
takarda a saman duvet ɗin saman gadon. _Ibnati wannan
ɗakin ki tabbar ya kasance ɗakin sirrinki, shiyyasa nasa a
shirya miji duk wani abu na buƙatar ki._ takardar ta ɗan juya
tana mai jan numfashi da fesarwa. Sai kuma ta saki murmushi
dan ta fahimci saƙon na Daneen Ammarah ne. Wayarta ta
ɗauka a ɗan gaggauce ta aika mata saƙo. Sannan ta nufi bayi
gabatar da al'wala.......


*_★★SHAHAN-SHAN★★_*

Tun bayan faruwar komai daya shige ɗaya daga cikin
ɗakunan barcinsa bai sake fitowa ba sai yanzu a cikin shirin
zuwa Masallaci. Sau ɗaya ya ɗagama hadiman dake zube ƙasa
a dalilin fitowarsa hannu ya fice. Da kallon ƙasan ido duk suka
bisa, kowa da abinda zuciyarsa ke ayyana masa game da shi...

Bayan idar da sallar isha'i bai samu damar shigowa ba yay
zaman ganawa da Aamin sa su biyu da suka buƙaci hakan.
(Miran Jasim da Miran Arshaan). Miran Arshaan shi yafi jansa
a jiki tun fil'azal, sannan kuma kamar yafi kusanci garesa ta
bangarorin biyu kasancewarsa miji ga Khaalti (Aunt) ɗinsa da
yake kallo tamkar yaya. Shima dai Miran Jasim ɗin bai taɓa
nuna masa wani abu mara kyau ba a zahirin rayuwa, a komai
ma da zai taso yakan bada ƙarfinsa wajen karesu ne ga kowa
koda a fada ne. Waɗannan hallayya tasu ya sashi ɗaukar
yarda ya basu har yakan iya tattauna wasu abubuwa da suka
shafi mulkinsa, sai dai abinda duk ya shafesa a karan kansa
duk yanda zasu so sani baya taɓa basu fuskar hakan dan ko'a
zahiri kowa na masa kallon mutum mai wuyar sha'ani,
bahagon mai bauɗaɗɗen hali da zurfin ciki ne.
Bayan ficewar hadimin daya gama hidimar zuba shayi a
gaban kowannensu ya fice Miran Jasim ya fara katse shirun
dan yasan in zasu kwashe awa ɗaya a wajen Tajwar Eshaan
bazai sake tofa komai ba bayan gaisuwar da yay musu. “Abni
nasan zakai mamakin wannan zaman namu, sai dai a dubi da
abinda ya faru ɗazun ba abin mamaki bane. Abinda ya faru
ɗazun ya matuƙar Kona mana zuciya, dan bazamu taɓa so a
aibantaka ba muna ji muna gani kodan amanar da Haysam
Akhi ya barmana taka. Akwai wasu abubuwan da yawa daya
kamata dama mu tattauna da kai kafin wannan ɗin, amma a
yanzu kamar wannan ɗin ne importent”.
“Hakane Jasim Akhi”. Miran Arshaan ya karɓe fuskarsa na
nuna tsantsar damuwa. Ya cigaba da faɗin, Abni lokaci yayi
da nake ganin ya dace wasu a cikin iyayen nan namu dake
zaman fadanci ya kamata su huta ƴaƴayensu su karɓesu.
Duba da kai matashi ne, a koda yaushe ra'ayinka da hangenka
zai cigaba da zama banbanci ne da nasun. Koda yake su a
gare sun ma ba haka bane, dan haka mahaifinka yasha
gwagwarmaya matuƙa da su a yayin nasa mulkin. Amma kai
mi kake gani akan hakan?”.
Shiru babu alamar Tajwar Eshaan zai tanka, sai ma cigaba
da kurɓar shayinsa yake cike da ƙasaita idanunsa akan
television dake aiki a falon..........✍️

38


........Duk da yanda zukatansu ke suya da tsagwaron salon
wulaƙanci da raini da suke jifansa da shi game da wannan
halin nasa da babu komai a cikinsa sai tsantsar miskilanci da
kasancewar jinin mulki da ke yawo a jikinsa basu bari
fuskokinsu sun nuna ba har ya gama shan ƙamahinsa da
basarwarsa ya tanka.
“Amfanin kasancewarsu cikinmu yafi rashin amfanin
muhimmanci Aam. A lokuta da dama nafi son zama da maƙiyi
fiye da masoyi saboda dalilai biyu”.
Wani irin kallo suke masa har fuskokinsu na barazanar
bayyana sirrin zukatansu. Miran Arshaan yay saurin katsesa
da faɗin, “Abni wace irin magana ce wannan? Kakuwa san
illar hakan da kakeyi?”.
Miran Jasim dake masa kallon gefen ido cikin takaici yake
masifa a zuciyarsa. (Shifa wannan wawa ne baima iya jin
ƙarshen zance sam). A zahiri kam kallonsa ya sauke ga Tajwar
Eshaan da yay biris tamkar bashi ya ɗakko zancen ba. “Ihm
kaga Abni ƙarasa, zata iya yuwuwa naka hangen gaskiyar
cikinsa rinjaye ne ga namu. Domin kowa da irin yanda
UBANGIJI ke fahimtar da shi abu”.
Tajwar Eshaan da bai ko motsa ba ga zancen Amin nasa sai
da ya shaƙi iska iya buƙatarsa kafin ya ɗan ɗage kafaɗu a
yanayin ko'in kula. “Ku manta kawai muje kan magana ta
gaba. Wataran zamu ƙarasa wannan ɗin”.
Sosai takaici ya maƙure musu maƙoshi su dukansu. Sai dai
Miran Jasim har Miran Arshaan yake jin takaici kasancewar
shine sanadin katse zancen. Suma shiru sukai kamar bazasuce
komai ba a wannan gaɓar. Kafin Miran Jasim ya nisa. “Abu na
gaba shine farin cikin tsallakewar matarka. Alhamdullah
addu'oin mu sun karɓu, ALLAH yasa ta kasance uwa ga ƴaƴan
da zaka haifa masu albarka”.
A maimakon amsawa da Amin daga garesa ƙasaitaccen
murmushinsa mai ƙara bayyana ƙyawun da ALLAH ya
azurtashi da shine ya saki kaɗan yana mai kauda kansa gefe
babu alamar zaice wani abu. Suma basu nuna alamar sun
damu da sai yace ɗin ba Miran Jasim ya cigaba da faɗin, “Ya
kamata a zauna da Tajwar na jihar Hubab da shugaban tsaro
akan waccan matsalar itama. Kar muyi sakaci dayin biris da
wannan maganar dan bamu san minene manufa ko dalilin
faruwar komai ba. Abu mafi ruɗanin shine makamancin haka
bai taɓa faruwa a ƙasar ruman ba sai dai muji a wasu ƙasashe
har ma mu bada shawara da gudun mawar ganin sun samu
zaman lafiya. Idan haka kuma ta fara faruwa a garemu lallai
maƙiyanmu na barazana akan nasararmu kenan”.
Nan ɗin ma dai kamar bazai tanka ba sai kuma ya dubi
Miran Jasim ɗin da alama zancen ya shigesa. “Na baku damar
yin duk yanda ya dace Aam”.
A take fuskokinsu suka nuna jin daɗin wannan girma daya
basu. Sanin halinsa yasa daga haka sukai masa sallama. Har
sun miƙe Miran Arshaan yace “Af niko kaga na shafa'a da
wannan batun. Abni baka ganin yayi kusa kuwa ace fitar
Zawjata-almilk har cikin books room? Yakamata ace tayi
haƙurin cigaba da killace kanta kodan maƙiyan da bamu san
ta inda suke shirya sabon shiri ba, dan yayi wuri ace mun
shagala da tsallakewar ta ta a nawa ɗan hangen. Ai ƙoƙari a
tsawata mata ALLAH ya cigaba da kare mana ku ku duka dai”.
Miran Jasim ya amsa da Amin yana jinjina kai alamar
tabbatar da maganar, sai dai ganin Tajwar Eshaan bashi da
alamar cewa wani abu suka fice abinsu. Koda suka fitan ya
jima bai motsa a yanda yake ba, da alama dai maganar tasu
ta ƙarshe ce ke masa kaikawo. Hasashen kam sai ya zama
gaskiya dan akan lips ɗinsa daya motsa kaɗan ya ambaci,
“Yarinyar nan ko”. Daga haka ya shanye sauran a cikinsa....
★★.... ★....

Kamar yanda ta faɗa bayan sallar isha'i ta fito cikin abaya
fara tas. Duk da dare ne ƙamshinta da kwarjininta mai ɓoye
ƙarancin shekarunta na tare da ita. Fuskarta ɗauke da
murmushi mai bayyana haƙora take amsa gaisuwar hadiman
da tuni sun kammala taruwa bisa umarninta. Ɗaya bayan
ɗaya ta basu damar gabatar mata da kansu da matsayin
ayyukansu. Har suka gama batace komai ba tana dai
nazarinsu ne. Haka kawai take jin bai kamata ta yarda da
kowa ba a wannan gaɓar, dan duk da tausayinsu dake
nuƙurƙusar zuciyarta tayi imanin akwai masu gurɓatacciyar
zuciya a cikinsu kamar yanda Daneen Ammarah ta karanta
mata komai.
“Okay duk naji bayanan ku, sai dai kuma Ni zan canja
tsarin aikin da bama kowa abinda nake ganin zai fi dacewa da
kasancewar tare da ni. Bazan roƙi kowa ba a cikinku cewar ya
kasance mai gaskiya da riƙe amana, sai dai zan tabbatar muku
zan iya hukunci ga kowa idan na kamashi da waɗan nan
abubuwan biyu. Dan na matuƙar tsanar mai wannan halayar
koda a sama dani yake. Zan kuma iya aikata harma abinda
mutum baiyi zatoba akan hakan.....” ɗaya bayan ɗaya ta
rarrabasu ga ayyukan saɓanin yanda aka turosu suyi, salon
nata ya matuƙar girgizasu a take kuma tasirin gizagonta ya
shigesu, har suke ambaton tsarin da gaba kura baya sayaƙi
kenan, dan kuwa dai kamar yanda Iffah tai hasashe mafiya
yawan cikinsu zasu kasance da itane bisa umarnin iyayen
gidansu na ɓoye bisa ɗabi'ar tura ƴan leƙen asiri da manyan
masarautar suka tasirantu a kansa. Bayan ta sallamesu akan
aikinsu zai fara daga gobe ne ta tattare littafanta da kanta tai
ciki da su. Sai da ta tabbatar ta ƙarema ɗakin kallo yanda ya
kamata fiye da ɗazu bisa zargin za'a iya saka mata camara
kamar yanda Ajmaal ya tabbar mata. Babu alamar akwai
abinda take zargin dan haka ta ɗauka wayarta. A maimakon
WhatsApp yau a text message ta tura masa saƙo, daga ƙarshe
ta ƙara roƙonsa bincika mata lafiyar iyayenta dan zuwa yanzu
zuciyarta na tabbatar mata akwai abinda Sir Fawzan ya faɗa
mata ba dai-dai ba ko yake ɓoye mata. Dan kullum takan
gwada number Hanash da Babiy sama da sau babu adadi
amma babu alamar zata samesu. Ga mafarkinta a kansu duk
kusan bayan kwana biyu cikin maimaita kansa yake gareta.
Bawai tayi imani da hakan bane, kawai dai zuciyarta takan
rinjayu da tsoro akan mafarki musamman idan ta auna da
abubuwan da suka tabbata akan wasu mafarkai da sukai wa
riƙon wasarere ita da iyayenta a baya.......

*_★MALIKAT HASEENAT★_*

Kamar yanda labarin fitar Iffah yaje kunnen kowa a
masarautar itama yaje nata kunnen, sai dai saɓanin malikat
Bushirat ita murmushi tayi batare data furta komai ba akan
zancen. Rashin cewar tata ya Bama Hadimar damar ƙarasa
mata zancen akan Iffah kuma ta koma sashenta bayan
barowarta books room. Anan kam idanu Malikat Haseenat ta
tsurama hadimar Tata tamkar zataga fuskar Iffah a jikinta ne.
Sai kuma ta janye da wani ɗan murmushi a fuskarta ta maida
ga hadima Banou.
“A haɗa abincin karin kumallo da Zawjata-almilk ta uku”.
Cikin tashin hankalin wannan umarni na Malikat Haseenat
kamar Banou zata fasa kuka ta jinjina kai, har hakan ya bama
malikat Haseenat mamaki, sai dai batayi magana ba
kasancewar tasan shirmen Banou fiye da haka. Itama dai tana
zaune da itane batare da tasan dalili ba, amma wasu lokuta
takanji yanayi mai wahalar fassara koda a kallon hadimar tata
ne amintacciya a bangaren girka mata abinci...

7
*_BARRISTER_*


“Su waye ku? Miyasa kuka kawoni nan? Mina muku?”.
Barrister ya faɗa yana mai bin zaratan samarin da kallo
harma da ɗakin da suka kawoshi mai ƙarancin haske gashi a
ɗaɗɗaure a kujera. Fahimtar bazasu bashi amsa ko ɗaya ba
daya bukata ya sashi cigaba da magana a hasale. Dan shi
mutum ne mai saurin fushi musamman akan gaskiya da mai
gaskiya. Baya son zalunci shiyyasa ko baka da ƙarfi zai tsaya
maka akan haƙƙinka in har ka kasance mai gaskiya.
“Idan ma akan case ɗin nan ne kuke ganin sakayeni ko
ɓadda rayuwata zai baku damar yin yanda kuke so akan bayin
ALLAH da basujiba basu gani ba ku sani ni bamai hukunci
bane. ALLAH shine mai hukunta kowa, zai kuma iya kawo
wanda ya fini ƙarfi ya cece su”.
Yanzu ɗinma dai babu alamar wani a cikinsu zai tanka
masa. Idanunsa ya rumtse zuciyarsa na masa ƙuna. Bashi da
wani buri yanzu a duniya sama da yasan asalin tushen
wannan case ɗin nasu Babiy, yayi alƙawarin tsayawa da
ƙarfinsa dana aljihunsa insha ALLAHU.

Har dare babu wani haske daya samu dan har lokacin yana
a ɗaure, sai da aka kira sallar magriba ne suka bashi dama yay
salla harda isha'i. Hakan ya ɗan sassauta masa zuciya, dan
koba komai damar yin salla da suka bashi yaji a ransa masu
sassauci ne. Abinci suka kawo masa basu sake ɗauresa ba, sai
dai yaƙi yako kallesa hakan yasa suka sake zuwa kusan ƙarfe
tara agogon ƙasar suka sake ɗauresa sukai ficewarsu da
kullesa ta baya. Babu irin tunani da takaici da baijiba amma
ya cigaba da ambaton sunan ALLAH dan yasan shine kaɗai zai
kuɓutar da shi a wannan gaɓar.
Kusan ƙarfe sha ɗaya gyangyaɗi naɗan kwasarsa yaji ana
ƙoƙarin buɗe ƙofar, idanunsa ya buɗe duk da baya iya ganin
mai shigowa saboda ƙarancin hasken ɗakin. A ɗan hasken ya
fahimci yanzu mutumin uku suka shigo, wanda ke gaba kuma
da alama ogansu ne dan yanda ya shigo da takun izza cikin
ɗakin. Da sauri suka ajiye masa kujera ya zauna yana mai
facing ɗin Barrister yay wani irin zaman ƙasaita yana ƙarema
Barrister ɗin kallo ta cikin glasses ɗin daya toshe idanunsa....
“Miyasa kuka dauresa?”.
Ya faɗa a kausashe. Kame-kame yaran nasa suka fara kowa
na ƙoƙarin kare kansa. Yaja tsakin daya sakasu nutsuwar dole
yana mai faɗin, “Ku kwance sa”. Bayan an kwance Barrister
ya sake bada umarnin a bashi abinci da ruwa. Barrister dai
kallonsa kawai yake da mamakin wannan izza tasa. Baiyi
niyyar cin wani abu ba dan haka yay saurin faɗin, “Bana
buƙatar wani abinci. Kusanar min kawai dalilin da yasa kuka
kawoni nan da kuma inda nake dan ALLAH”.
Har Barrister ya fidda rai ga samun amsa yaji an karɓama
zancensa a kausashe. “Barrister Abdallah Aas ba shiririta ta
kawoni nan ba. Dan na baro abubuwan da suka fika
muhimmanci nazo nan. Duk da rayuwarka ce ba sanin inda
kake ko sanin mu su wanene ba matsalarka. Dalilin kawoka
nan kawai zaka iya sani, damar hakan kuma na hanunka ta
hanyar bin umarninmu”.
Haka kawai kwarjinin wannan mutum da ko fuskarsa
Barrister baya gani da ƙyau yay matuƙar mamayesa, duk da
yanaji a ransa ba alkairi yasa suka kawosa nan ba sai yaji
bazai iya jayayya da shi ba. Cikin sanyin jiki ya fara cin abincin,
yaci kusan lauma bakwai yasha ruwa duk suna a ɗakin. “Na
gama”. Ya faɗa cikin sanyin murya.
“Good for you”.
Aka bashi amsa cikin halin ko'in kula. Sai kuma yay shiru
kamar baida abin faɗa kafin yaja numfashi cike da isa ya
fesar.
“Lokacina ƙurarrene dan haka bani da lokacin cigaba da
ɓatashi a rikeka nan. Aiki zakamun baka da kuma zaɓin cewa
e ko a'a. Nasan kasan Barrister Akeem Ibn Behnam”.
“Hakane, dan abokina ne ma ranka ya daɗe”. Barrister ya
amsa mishi da kalmar giramamawa a ƙarshe batare da yasan
dalili ba. Kawai dai yana jin matuƙar girman wannan mutum
da ko a murya yasan ya girme masa.
Cikin yaransa ɗaya ya cigaba da faɗin, “Sanin hakan yasa
aikin ya wajaba a kanka. Akwai aikin da Barrister Akeem ɗin
keyima wasu mutane, Boss naso ka maye gurbinsa....”
“Tayaya hakan zata faru, bayan su sun san wanda suke
huɗɗa da shi”. Barrister yay saurin katse mai maganar.
“Ai mun fika sanin hakan shiyyasa muka zaɓeka. A yanzu
Barrister Akeem na hanunmu kamar yanda kake a hanunmu,
munada hanyoyin bi wajen canjaka ka koma shi bisa dalilan
da kaima kasani, yayinda su a wajensu kai ka mutu a yanzu,
zuri'arka kuma basu san inda kake ba. Zakai aikinne na
kwanakin da basu gaza goma ba, idan sun zarta hakan kuma
kai kaso”.
“Kun sani a duhu wlhy, Barrister Akeem fa wani babban
jigone a rayuwata, muna taimakama juna matuƙa taya kuke
tunanin zanci amanarsa ta hanyar yin amfani da kammanin
da mukeyi ace na masa kutse akan aikinsa bayan haka cin
amana ne?”.
“Wannan damuwarka ne. Aikinmu zai fara daga gobe”.
Ogan nasu ya faɗa cikin kausasa harshe yana miƙewa.
“Ranka ya daɗe dan ALLAH ka saurare ni”. Barrister ya faɗa
cikin rauni. Sai dai baiko nuna alamar yama jisa ba yay
ficewarsa yaransa biye da shi..........✍️

39


........A ɓangaren Iffah kam bayan sallamar Hadimanta data
ƙudiri nutsuwa wajen fahimtarsu a tsanake itama ciki ta
shige. Kamar yanda ta saba sai da ta gudanar da duk wani
al'adan rayuwarta kafin barci. Ta haye sabon katafaren gadon
nata bakinta da addu'a.

Please Login or Register in order to submit comment