Reading Dauɗar Gora by Bilyn Abdull ce Chapter 4 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙuruciyarta tafi hango mata nasararta na
ɗaukar fansar ƴan uwanta fiye da tunanin idan wani abu ya
faru Babiy ne na farkon wanda za'a tuhuma kasancewar
zumar daga hanunsa ta fito. Haka Iffah ta ƙarasa wannan
dare cike da zumiɗin ganin wayewar gari Babiy ya kai zuma
masarauta.
Bayan ta idar da salla yau ko fama da ita Ummu batai ba
akan shirin tafiya makaranta, a da kuwa saita tasota daƙyar
kasancewarta mai son barcin safen tsiya da tayi salla take
komawa barci. Babiy kansa saida yay mamakin wannan
sammakon tashi nata yau, Hanash kam kasa haƙuri yay saida
yay magana. Sai cewa tai ai sunada program ne a makaranta
yau... Koda taje makaramtar ma dai bawai ta nutsu bane,
rabin hankalinta ne kawai ga duk malamin daya kasance da
su har aka tashi.

★A ɓangaren Babiy kam duk da tabon da masarauta
daular ruman ta bar masa a zuciya bai taɓaji koda wani zai
bari ya cutar da su ta hanyarsa ba ko shi ya aikata hakan ta
damar dake hanunsa na kai musu zuma. Tsaf yay shirinsa
kasancewar yau juma'a ce ya ɗiba tulunan zumar nan guda
uku ya nufi daular ruman. Idan yaje ba kaitsaye yake ɗaukar
zumar nan ya kai ga Tajwar ba, dan ganin Tajwar kam babban
abune da sai wanda ya cika ya tumbatsa keda wannan damar.
Akwai wanda keda alhakin amsarta shi ya isar da ita inda ya
dace har ta isa ga sashen Tajwar ɗin. Bayan ƴan bincike a
kansa na kullum da basa ƙarewa ya shiga daular ruman iya
ƙofa ta biyu. Dattijo da kamanni da suturar jikinsa kawai ta isa
tabbatar maka da shima wanine ya iso ga Babiy bayan zaman
jiran kusan mintuna goma da yayi. Cikin girmamawa Babiy ya
gaidashi duk da zasu iya zama kusan sa'anni da shi. Shiko ya
amsa yana hura hanci irin na masu dama ta mulki a hannu.
Umarni ya bama Babiy akan ya ɗanɗana zumar, Babiy da
yasan babu wani abu na razani ko shiga dogon tunani kafin
ɗanɗanawar kansa tsaye ya kai hannu ya ɗauka cokali dake
bisa tire a hanun hadimin dake biye da dattijon nan. Tunda
dama haka ba sabon abu bane garesa duk sanda ya kawo sai
ya ɗanɗana ɗin. Tulun farko ya kwancema baki kasancewar a
ɗaure bakin yake da ganyen ayaba, yasa cokalin nan ya ɗibo
zumar da bismillah ya nufi bakinsa.........✍

7
.........Haniniya da ƙarar takun sawayen wani farin ingarman
doki ta saka Babiy sakin cokalin da yake shirin kaiwa bakinsa
ya miƙe domin ceton kansa kamar yanda Dattijo nan da
hadiman dake tare da su suma sukai nasu waje. Tuni tulunan
zumar uku da Babiy ya kawo sukai nasu gefe suma, gaba ɗaya
zumar ta kelaye a wajen. Cikin daka tsawa dattijon nan ke
duban hadiman da suka biyo dokin domin kama shi...
“Wane mara hankalinne yay sakacin daya kunce?”.
Su dukansu jikunnansu rawa yake, cikin ƙarfin hali
shugaban hadiman dake kula da barga ya zube ƙasa yana mai
girgiza kansa. “ALLAH ya ƙara maka tsahon rai an gama masa
wankane za'a maidashi na rantse maka”. Dattijon ya cije baki
mai nuna alamar takaici, “Na baku mintuna goma kacal ku
madashi shashashu kawai”. Miƙewa hadimin dattijon yayi
cike da girmamwa dan dama sauran sunata ƙoƙarin ganin sun
kama dokin ne, bama su kaɗai ba hadiman da yawa sun ƙaru
saboda bahagon dokine da babu ma iya controling nashi sai
Tajwar Eshaan. Horarran doki ne daga horonsa, da abinsa ya
dawo ƙasar ruman, dokin yafi kowanne doki tsananin ƙarfi a
masarautar. Shiyyasa idan har sukai sakaci ya ɓalle kowa sai
ya jigata kafin a kamashi da ƙyar, kafinma kamashin sai an
samu wanda sukaji raunika da yawa. Akwai randa irin haka ta
taɓa faruwa baƙaramin jigata mutane yay ba harda masu
karaya a hadimai, kuma duk iya wahala da jigata babu wanda
ya iya kama dokin har duhun magriba yayi dan da yamma
al'amarin ya faru. Kowa yayi laushi an rasa in za'a kama sai ga
Tajwar Eshaan ya fito sallar magrib, abu mafi ban mamaki
daya saka masarautar yin shiru na sakanni uku kiran sunan
dokin kawai yay sai gashi gabansa, ya girgiza jikinsa tare da
yin haniniya sannan ya koma kan ƙafafunsa ya tsaya cak
tamkar bashiketa jigata mutane da hargitsa wajen ba.
Wannan abun mamaki ya saka dukan hadiman da suka zube
saman gwiyawunsu kawunansu a ƙasa a lokacin kasa haƙuri
sai da suka saci kallon dokin dama Tajwar Eshan ɗin da hirami
daya yafa a kansa ya rufe rabin fuskarsa.....

★★★★

A ɓangaren Iffah gaba ɗaya idanunta sun kasa barin ƙofa,
babban burinta kawai dawowar Babiy taji zuma ta isa hanun
Shahanshan. Sai dai shiru kakeji har akai sallar juma'a bai
shigoba. Ko abinci babu yanda Ummu batai da ita tai zaman
ci ba amma taƙi, Hanash ma sai da ya mata maganar tazo suci
kamar yanda sukanyi duk juma'a tunma su Fariha nada rai
amma tace batajin yunwa. Ƙyaleta sukai dan sun kasa gane
minene ya hanata nutsuwa waje ɗaya.
Babiy bai shigo gida ba sai bayan sallar la'asar. Azabure
Ummu ta miƙe tana kallonsa. “Innalillahi wa
inna'ilaihirraji'un. Abu Hanash haɗari kayi?”.
Kai Babiy ya girgiza mata yana kaiwa zaune da ƙyar. “Ke
dai bani ruwa na fara sha”.
Kafinma ya rufe baki Iffah da itama jikinta ke rawa ta kawo
masa ruwan, dai-dai nan Hanash ya fito daga ɗakinsa cikin
shirin fita ƙwallo. Shima a ruɗe yay kan Babiy ɗin yana jera
masa tambaya. Babiy ya ajiye kofin ruwan yana mai kallonsu
gaba ɗaya. “Kunga ku kwantar da hankalinku babu abinda ya
faru daga masarauta ne. Wani bahagon dokine fa ya kunce
al'amarin tamkar yaƙi, hatta da zumar dana kai ba'a mora
komai a cikinta ba ma”.
Ummu da Hanash suka shiga jera salati, yayinda Iffah taji
wani ƙududun baƙin ciki ya tokare mata maƙoshi, hakan na
nufin bataci nasara ba sai ma Babiy daya dawo da raunika.
Jitake kamar taga Tajwar Eshaan gabanta ta shaƙesa da
hannayenta har sai ya bar duniya saboda tsabar tsanarsa. Har
Hanash ya gama yima Babiy dressing ciwukan batace komai
ba, daga ƙarshe ma ɗaki ta shige ta shiga faman kaikawo na
tunanin abu na gaba. Dan tayi alƙawarin bazata taɓ haƙuraba
sai ta kai *_Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-majeed_* ƙasa
zata samu salama game da rasa ƴan uwanta.

Sam a wannan dare Iffah bata wani isashen barci ba
saboda ƙullawa da kwancewa aka shiri na gaba. Abinda ta
gama ƙullama zuciyarta yasata shirin fita a gidan da hantsi da
dalilin cewar zataje wajen Ikram duba mamanta bata da
lafiya bazata jima ba. Ummu tayi kamar bazata barta ba
amma taita mata magiya harta amince da sharaɗin karta
jima, kuma dolene ta rufe duk jikinta. Ta yarda da hakan
saboda tana son fitar. A gurguje tai shirin fitar, tare da lalubo
wayar Arfa a cikin kayansu. Koda ta haɗa batteryn ta kunna
tayi sa'a tanada caji, dan haka ta loda number da take
buƙatar kira tana mai addu'ar ALLAH yasa akwai kuɗi ma.
Addu'ar tata bata amsu ba, dan haka ta tura wayar cikin
jikinta bayan ta kashe sannan ta fito tai sallama da Ummu ta
fita bayan ta amsa kuɗin taxi. Sai da ta fito daga cikin
anguwarsu gaba ɗaya sannan ta tsaya ta sai kati, koda ta loda
sai ta sake gwada kiran lambar ɗazun. Cikin sa'a kuwa aka
ɗauka, jimm sukai su duka kafin ta katse shirun da sallama.
Daga can aka amsa a noƙe alamar rashin sanin dawa ake tare.
Fahimtar hakan ta saka Iffah bashi amsa tunkan yay
tambayar.
“Sir! Kana magana da Fareedah bint Zayy......”
“Serious?”.
Ya faɗa cikin katseta da alamar zabura tun kan ta ƙarasa faɗa.
Baki ta ƙyaɓe a ƙasan zuciya tana jan tsuka, a zahiri kam sai ta
saki murmushin da har sautinsa ya kai cikin kunnensa. Cike da
sake ƙanƙan da kai tace “Tabbaci Sir. Ina buƙatar muhaɗune
yanzu yaya za'ayi?”.
“Kai! Iffah! Ke ɗin dai?...”
“Bazan samu damarba ko......?”
Cikin sauri ya katseta. “No ba nufina kenan ba, kawai na shiga
al'ajab ne. Amma bara na ajiye tantamar tawa gefe dai. Inaga
zanzo na sameki gida kawai...”
“A'a sir”.
“Miyasa?”.
“Ba buƙatar hakan, mu haɗu kawai”.
Jimm yayi na tunani, sai kuma ya sauke numfashi. “Okay!
okay inaga bara na tura miki adireshin inda nake a yanzu
haka sai mu haɗu nan in ba damuwa ko”.
“Ya dai kasance babu abinda zai shafi mutuncina a wajen
sir”.
“Wannan shike ƙara samun naji ke ta daban ce Iffah”.
Baki ta sake ƙyabewa. Amsa garesa kuma tace “humm”
kawai.



Kallon baki da hankali mai haɗi da tsoro tun daga ƙarƙashin
zuciya yake mata tun bayan gama masa dogon jawabin da
tayi. Tasan zataga fiye da hakan ga kowa bama shi kawai ba,
dan haka bataji komai ba sai ma murmushi data sakar masa.
Bata san mi yake tattaunawa da zuciyarsa ba, amma tanaji a
ranta yana auna shekarunta da maganganun da kowa zai
auna da wautarta ne kawai. Ilai kuwa sai ta tsinkayi muryarsa
da irin amsar datai tunanin samu.
“Nikam Iffah shekarunki nawa?”.
“Ashirin a kwashe biyu sir”.
Ta faɗa tamkar bata fahimci alaƙar tambayar tasa ba. Kansa
ya jinjina da cije lips nashi, kansa tsaye yace “Nama tunaninki
mai kama da mafarki uziri. Amma zan baki shawara data dace
da waɗanan shekarun naki na ƙuruciya. Ƙoƙarin ya kamata
kiyi wajen cinye jarabawar share fagen shiga jami'a da ke
tunkaroki kamar yanda nasan burinki. Tunaninki kuma ya zam
tamkar baki taɓa yinsa ba, sannan na kasance na farko kuma
na ƙarshe da kika faɗawa. Hakanne zai baki damar cigaba da
ƙyaƙyƙyawar rayuwar da kika fara da ke da ahalinki har nima
na cigaba da saka rasan samunki matsayin uwar ƴaƴana wata
rana dan ALLAH Iffah”. Ya ƙare maganar da haɗe hannaye
alamar roƙo.🙏🏻
“Ƙyaƙyƙyawar rayuwa ta daɗe da yankewa a cikin
rayuwata data ahalina. kuma irinta nake hangowa da son
daƙilewa ga ƴan baya ciki harda ƴaƴan da kaima a karan
kanka zaka iya haifa wataran Sir. Sannan wannan tsoron da
nake gani yanzu a cikin idanunka shine zai tabbatar da hakan,
koda ni bana raye kai zaka rayu ka tuna. Nagode da saurarena
da kayi sir”.
Da sauri yasha gabanta kasancewar ta riga ta miƙe. Tai
takwaf-takwaf da fuska tana mai tsaresa da manyan idanunta
da tuni hasken cikinsu ya koma launin ja. “Ki fahimceni
Fareedah, koba komai na fiki shekaru, na fiki ilimin sanin
rayuwa dama sirrikan dake zagaye da lungu da saƙo na ƙasar
Ruman....”
“Na sani sir, tabbas na sani shiyyasa ma na fara nemanka.
Sai dai nima kayi haƙuri, dan babu shawararka ɗaya data
shiga cikin wannan kan nawa, saboda abinda ke cikinsa
tamkar kundin littafin da aka rubuta labari daki-daki ne, kaga
dole zaizo feji bayan feji. Kuma duk abinda ya shiga ciki bazai
taɓa goguwa ba sai ta hanya ɗaya tak! Mutuwa!. Mutuwa ce
kawai zata goge wannan yunƙurin insha ALLAH. Na barka
lafiya”.
Sororo ya bita da kallo harta tare mototaxi ta shiga, ji yay
ta ƙara masa girma a ido, girma bana shekaru kawai ba na
wata ilhamar kwarjini da cikar mutuntaka. In har yara irinta
da ayanzu suka fara rayuwa zasuyi irin wannan tunani akan
al'ummarsu mi manya kakaninsa, iyayensa, yayunsa dama
sa'aninsa sukeyi ne su? Shin basa ganin abinda take gani ne?
Ko kuwa da gaske tsoron data ambata ta gani a cikin idanun
nasane a idon kowa?. Kenan hatta da sauran sarakunan ƙasar
da mafi yawan cikinsu sun rasa ƴaƴansu suma cikin tsoron
suke? Anya maganar mutane ba tabbatacciya bace akan
danganta Shahanshan na daular ruman da magajin fir'auna
daya shuɗe batare da labarinsa ya gushe ba?. Iffah! Iffah!! Da
gasken gaske ke tadabance kamar yanda nasha faɗa a aji
aduk sanda kika bada amsar data danganci darasi......

★★★

Kwanaki uku kenan da Iffah ta tunkari malaminta batare
da nasara ko ƙwarin gwiwa daga garesa ba. Sai dai hakan
baisa taji ta sare ba ko haƙura da ƙudirinta. Koda ace nata
ajalin take tunkara tayi alƙawarin sai tabi kadin jinin ƴan
uwanta guda biyu. Koda ace bata da ƙarfin ikon ruguza
mulkin sarkin dake kama da mulki irin na fir'auna zata
tabbatar sai kuwwar gunjin kukanta ta fita a duniya, koba
komai tanada yaƙinin a bayanta zata samu masu share mata
hawaye insha ALLAHU.
Hanyar da tabi a farko ita kaɗaice hanyar da tasan tanada
ita wajen bi ta samu nasara cikin sauƙi. Sai gashi kuma ba'a
dace ba. Gashi tabi ta biyu itama, sai dai anƙi buɗemata ƙofar
saboda tsoro da ƙarfin tasirin mulkin azzalumin, a yanzu haka
tunaninta hanya ta uku koda itama bazata samu nasarar ba.
Zata kuma cigaba da bin hanyoyin koda zasu ninka dubu sau
dubu har sai ta dace. Nannauyan numfashin data zuƙa ta
fesar, tare da gyara kwanciyata ta jawo wayar Arfa da har
yanzu bata bari wani a gidansu yasan da tana amfani da ita
ba. Ido sosai ta tsurama wayar, tabbas ba gizo bane tarin
missed call ne daga malaminta. Taruwarsu da rashin jin sanda
suka shigo wayar kuma nada nasaba da kasancewarta a
silent. Tayi kamar zata share amma sai ta kasa hakan. Dan a
yanzu shine kawai madubin da take kallo matsayin damar
dake a hanunta ta isa ga abinda take so da wurwuri. Cikin sa'a
tana kokarin kiransa sai ga kiran nasa ya sake shigowa. A
dakile ta amsa tare da masa sallama murya a cuɗe.
“Kiyi haƙuri”.
Kalmar farko data fara fita a bakinsa. Iffah taja numfashi mai
nauyi tare da haɗiyewa muƙut. “Sir bakamun laifin komaiba
nikam”. Ta faɗa tamkar komai baima faruba. “Humm” ya faɗa
shima, sai kuma ya ɗora da faɗin “Ina son mu haɗu”.
“Babu dalilin hakan sir”.
“Akwai Fareedah, kar kiyi taurin kai”.
“Koba komai kai ɗin malamina ne ai, mi zaisa na maka
taurin kai?. Iya gaskiyata nake faɗa maka”.
“A cikin gaskiyar taki harda haƙura da samun abokina”.
Zumbur ta miƙe zaune tamkar wadda aka kwantsamawa a
radu a tsakkiyar kunne. “Sirrrrr!.....”
“Na amince zan haɗaki da shi”.
Ya katseta da sauri. Jitai tamkar ta sandara ihu ko zaifi
fahimtar farin cikin dake a tare da ita, amma sai tai ƙoƙarin
gimtsewa. “Sir ba dole sai shi kawai bane zaiyi aikin, harma
na samu wan....”
“Fareedahhh!”.
Ya faɗa da wani yanayi a muryarsa. Ajiyar zuciya ta sauke a
ƙasan maƙoshi. Sai kuma ta lumshe idanu tamkar tana a
gabansa tace, “Shikenan ka turamun adireshi. Sai dai inda
bazai taɓa mutuncina ba”.
Murmushi yayi mai sauti, tare da faɗa kamar yanda ya saba
tun acan baya. “Fareedah ke ta dabance ƙwarai da
gaskeeee”.
Baki taɗan laɓe batare da tace komai ba ta yanke
wayar..........✍

8


..........Zaune takai a kujerar dake duban tasa tana mai kallon
agogon hanunanta. Ya saki murmushi cikin kafeta da idanu.
“Daga zuwa sai duba agogo?”.
“Hakan dolene Sir, domin ko lokacin islamiyya zan cinye
anan. Kaga kenan sai da tsantseni”.
“Okay”.
Ya faɗa yana gyara zamansa. “Ba buƙatar maimaita abinda ya
faru baya, na gaba kawai yanzu shine zanyi iya ƙoƙarin ganin
na haɗu da abokin nawa koda ta waya ne, kin san aikin nan
nasu yana hanasu samun isashen lokaci matuƙa
kasancewarsu manya dake tare da babbar kafar yaɗa labarai
mai aiki da kamar duniya gaba ɗaya. Ke yanzu a gareki miye
shirinki?”.
Kafaɗa Iffah ta ɗan ɗage cikin jan iska da hurowa. “Kusan
dukan shirina a kammale yake, burina kawai nasamu yin hira
da African Aye”. “Indai hakane haɗuwa da abokina
kawai ya rage mana, fatana dai bayan ni kar wanda yasan
wannan hatta a gidanku, inba hakaba zamu iya shiga haɗarin
da har burin rayuwarmu ma bazai cikaba bayan wannan.
Nikuma zanyi duk yanda zanyi insha ALLAHU wajen hana
wannan sirrin fita daga gareni....”
“Shi abokinka ɗin fa?”.
“Baki da matsala da shi domin shi aikinsa ne”.
Kai ta jinjina masa fuskata cike da murmushi. Sai kuma ta
rissinar da idanunta alamar jin kunyarsa saboda kallon daya
kafeta da shi. Kunyar nada nasaba da tuna yanda ta dinga
wancakalar da shi da manufarsa a sanda yake malaminta. Sai
gashi shine na farko data fara tunkara da matsalata a yanzu
duk da kuwa tana kallonta a kan matsalar data shafi kowa na
ƙasar Ruman ne. Sautin murmushinsa ya sakata ɗagowa ta
ɗan kallesa, sai kuma ta sake kauda kanta gefe itama tana
murmushin.
“Hummm!”
Ya faɗa yana miƙewa. Itama miƙewar tayi batare data yarda
sun sake haɗa ido ba. “Kije gida zamuyi waya”.
“Nagode sir, ALLAH ya tsare gabanka da bayanka”.
Jin sautin murmushinsa ya tabbatar mata jin daɗinsa,
amma sai tai gaba da sassarfa tunkan ya sake cewa
komai........

★__________________★
*_DAULAR RUMAN (MASARAUTA)_*

Katafaren ɗaki mai ɗauke da ƙayatattun kayan more
rayuwa, kwance take bisa lafiyayyen gado da dukkan nau'in
shimfiɗunsa suka kasance na alfarma. Sautin dariyar dake
tashi cikin kunnuwanta tamkar mafarki ya sata buɗe idanu,
cikin tsumar jiki ta ture lallausan bargon da take ciki, tamkar
walƙiya ta dire ƙasan lafiyayyen kafet ɗin dake malale gaban
gadon tai kneel down tamkar mai neman gafara, kanta a
risine alamar nuna tsantsar girmamawa.....
Tamkar shirin film ko labaran almara tsohuwa tukuf sanye
cikin jajayen kaya ta bayyana bisa baƙar kujerar ƙarfe mai
ɗauke da adon gold a cikin ɗakin. Baƙace matuƙa mai
tsananin muni da jajayen idanu, yanda ta zauna ƙafa a harɗe
kai ka ɗauka itace Shahanshan ɗin.....
“Lafiya da tsahon rai su ƙara kasancewa a rayuwar
*_Uwa_* mai share kukan masu kuka”. Hamshaƙiyar matar
ta faɗa cikin tsantsar girmamawa ga tsohuwar dake harɗe
saman kujerar tata tamkar sarauniyar ingila.
Cike da isa da ƙasaita tsohuwar taja wani kakkauran
numfashi da sake faɗaɗa girman ƙofofin hancinta ta hanyar
hurashi, ƙara harɗe ƙafafunta tai tana mai motsa yatsun
hanunta, idanunta jajaye kafe akan matar. Cike da isa da
ƙasaita mai ɗauke da rashin daɗin muryarta ta tsufa ta fara
magana. “Ta-ƙurya kin kusa cin nasara wajen cika sharaɗi na
biyu akan alƙawarinmu. Na tayaki murna, saura sharaɗinki na
ƙarshe, mafi wahala a cikinsu”.
Ƙasa ta ƙarayi da kanta cike da girmamawa a gareta, da
dukkan ƙarfin zuciyarta ta furta, “Kece madubin nasarata
Uwa!, duk inda akaga naje da jagorancinki na isa. Yanda na
cika na farko shima na biyu zan cika sa, nayi alƙawarin cika na
ƙarshe ma fiye da yanda kike tsammani.....”
Jajayen idanunta masu kama da garwashin wutar gidan
biredi ta ɗago tana kallon ƙyaƙyƙyawar kuma hamshaƙiyar
matar dake gurfane a gabanta. Ta ƙyalƙyale da wata dariya
mara daɗin saurare ga kunen kowa, sai kuma ta gimtse
tamkar ba ita tayi ba tana zaro manyan jajayen idanunta
kamar na dodanni. “Ta-ƙurya nasan zaki iya, sai dai akwai
wani babban ƙalubale dake tunkaro cikar nasararki ta biyu,
kuma gab yake da cimmawa, idan baki gaggauta datsesa ba,
zakiyi biyu babu”.
A razane ta ɗago tana kallonta cikeda bushewar zuciya, sai
kuma ta maida kanta da sauri ta rissinar “A gafarceni Uwa, a
kawar da ko miye mai son yima cikar burina kutse. Na rantse
da ALLAH daya halicceni, koda cikin yankin ahalina ne bana
buƙatar numfashinsa Uwa!!”.
Dariya ta sake ƙyalƙyalewa da shi sai kuma ta gimtse fuska.
Kanta ta shiga girgiza mata da dukkan isa. “Ta-ƙurya wannan
karon akwai banbanci da koyaushe, dama na taɓa faɗa miki
bayan cikar nasararki ta farko akwai ƙalubale dana gani akan
cikar ta biyu, sai dai ba'a buɗe mun komaiba a wancan
lokacin, alamar haka na nuna ƙarfin taurarin mai yunƙurin,
amma a daren jiya dana tsananta bincike akan mafarkinki na
gano wani yanki da ƙyar. Ƴar shilar suda na ƙoƙarin yin cara
irin ta gawurtattun zakaru a kunnen bututu da taimakon wata
zuciya mai son kusantar tata.”
“A taimakeni a kawar mun dasu gaba ɗayansu Uwa. Ko a
bani damar kawar da su da kaina”.
“Hhhhhhh!!!! Ƙaddarar ƴar shilar bata mutuwa bace cikin
sauƙi. Tana kuma da ƙarfin taurarin da zata iya cin nasarar
dusashe naki”.
Bugawar da ƙirjinta yayi ta zata zuciyarta ce zata fito ta
bakinta dan tsabar razana. Ta kafeta da idanu cikin wani irin
yanayi mai wahalar fassara. Sai kuma tai saurin maida kanta
ƙasa ta rissinar tana faɗin, “A gafarceni Uwa”.
Wani irin kakkauran numfashi mai cike da gargaɗi
tsohuwar taja, cike da ƙasaita tana yamutse mummunar
fuskarta ta cigaba da faɗin, “Zamu iya samun mafita sai dai
akwai ruɗani a cikinta. Har zuwa yanzu kuma ban samu
buɗewar ruɗanin ba kai tsaye. Dan haka kina da zaɓi biyu.
Kodai ki ƙara yin duk yanda zakiyi igiya ta ƙullu tsakanin
Ajlaan da wannan ƴar shila muyi duk yanda zamuyi tazama
cikamakin aikinmu na biyu, ko kuma ki barta ta cimma
burinta.......”
Idanunta da suka kaɗa jajur tai ƙoƙarin ɗagowa, sai dai
ta maidasu da sauri zuwa ƙasa. “Uwa amma kin faɗamin na
cinye jarabawa ta biyu da zarar ya aura cika makin matansa
shine matakan nasarata, yanzu haka akwai su su biyu da suka
rage ɗauke da aurensa a kansu, zasu miƙasu garesa a karshen
watannin nan kamar yanda na samu tabbaci. Taya zamu
shigo da wata bayan aikin ya cika. A yanzu ya rage kawai
samun cikar burina na ƙarshe ne a kansa. Miye dalilin
shigowar wannan yarinyar abinda bai shafeta ba? Mizai hana
ai mata wani hukuncin daya dace da ita?...”
Hannu ta ɗaga mata cikin tarar numfashi da ƴar hasala-
hasala, da kakkausar murya tana mai nunata da ɗanyatsa
“Amma har yanzu ban sanar dake wadda ta dace ba, kuma
damun san cutarwace na umarninmu gareki bazamu ce ta
shigo ba”.
“Hakane Uwa, a gafarce ni. Sai dai Mahaifiyar Zak.......”.
Ta faɗa da alamun shiga tashin hankali mai girma, amma
kallon da Uwa ta watso amata ya hanata ƙarasawa.
Bata tanka mata ba, sai dai yanayinta ya nuna a hasale
take, dan cikin kaushin murya da zunzurutun jin zafi ta kaɗa
ƙahon hanunta mai kama da kwarkwaron gidan dodon koɗi.
A take haske ya gilma, sai ga farar takarda a hanunta. “Ƴar
shila burinta shine ɗaukar fansa, domin biyu a cikin masu
ɗakin Ajlaan da suka shuɗe jininta ne. Burinta shine bin kadin
jininsu ta hanyar bayyanama duniya ko kawar da shi.
Bayyanawar tata kafin cikar burinki faɗuwarki ne, a yanzu
haka kuma ta haɗu da mai taimaka matan harma sun gama
magana”.
Sosai zuciyarta ta ƙara harzuƙowa. Amma sai batace
komai ba saboda ganin Uwa a hasale take da ita. Cikin yin
ƙara ƙasa da kai tace, “Da ace bayan cikar burina ne kauɗi da
ƙudirin ɗaukar fansar wannan yarinya ya shigo haske ne ga
cikar burina. Dan zata ƙarasamin aikin ƙarshe da zanyi. Amma
tunda ta shigo a tsakkiyar labarina dolene ta fuskanci
hukuncin daya dace da ita. Idan ita bazata mutun ba shi a
kawar min da shi mana Uwa”.
“Hakan mai sauƙi ne, sai dai shima babu buƙatar
mutuwarsa, dan zai iya mana amfani a gaba. Sannan shi
rabata da shi shine mafi ƙololuwar hukuncinsa. Dan haka
daga nan zuwa safiyar kowace juma'a ta ƙarshen shekarar
nan ki tabbatar an zarga igiya tsakaninta da Ajlaan, a dakatar
da kai masa matan da suka rage a kaita garesa bayan tarewa,
dan da ita zamu cigaba da amfani har samuwar cikar burinmu
ga kowa!!.”
Da sauri ta ɗago kai jin muryar nayin nesa da ita, sai dai
kafin ta iya furta wani abu Uwa ta ɓace daga ɗakin tamkar
guntun girgijen hadari a tsakkiyar fararen gizagizai. Zumbur ta
miƙe tana mai dafe kanta dake sara mata, wani irin tuƙuƙi da
ƙaiƙayin mai zafafa ruhi zuciyarta ke mata. Sai dai sanin
wacece Uwa ya sata jin ɗan sassauci kaɗan, amma ruɗani mai
ɗauke da abubuwa masu matuƙar yawan gaske da fassarasu
a ɗauka shekara dubu bisa dubu ba'a kammala ba na neman
danne wancan ƙwarin gwiwar. Taya ruhin ƴaƴan sarakunan
ƙasar Ruman basu bata matsala ba sai ƴar talakawa
ƙasƙantattu? Dolene yarinyar nan ta ɗanɗana kuɗarta na
hukuncin shiga gonar daba tata ba ƙwarai da gaske, sai tayi
wasa da ita a tsakkiyar titi wasa irin na ɓera a hanun mage,
dan ko ita Malikat bata isaba.....

(Tofa masu karatu, ita kuma wannan wacece ita? Iffah fa
ta taro match ɗin da babu players. Kumuje zuwa dai muga
yaya wasan zai kaya🚴🏼...)

★__________________★

*_IFFAH_*

A ɗan firgice ta buɗe idanunta tare da tura hannu
ƙarƙashin filon data tada kai ta sake danne wayar dake faman
ɓurari cike da tsoron kar Ummu ta jiyo, dan tasan Babiy da
Hanash basa gidan. Ajiyar zuciya ta sauke mai matuƙar ƙarfi
da zaro wayar, cikin rawar jiki ta dannata a silent. Tamkar jira
kiran ya sake shigowa kuwa. Idanunta masu matuƙar girma
da haske ta waro sosai ganin mai kiran, ai batama bari tayi
ring na biyu ba taa ɗaga tare da kaiwa kunnenta tana direwa
a gadon.
“Kina jina?”.
Aka faɗa daga can. Kanta ta jinjina masa tamkar tana gabansa
dai-dai tana leƙawa tsakar gidansu. Daga can gefen da Babiy
ke kiwon tsuntsaye ta hango Ummu, dan haka ta sauke ajiyar
numfashi da fara magana cikin raɗa.
“Ina jinka Sir! Ta samu ne?”.
“Babu lokacin dogon magana Iffah, kiyi ƙoƙari daga nan zuwa
awa ɗaya ki sameni, dan kuwa mun tsinta dami a kala Ajmal
ya shigo Ruman, kuma a yanzu haka mun

Please Login or Register in order to submit comment