Reading Dauɗar Gora by Bilyn Abdull ce Chapter 14 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da kai hannu
akan wayar dake cigaba da ɓurari.........✍️

27



.......“Assalamu alaikum”.
Ya faɗa a daƙile saboda rashin sanin wanene. A maimakon
amsa masa sallamarsa aka ambaci sunansa tamkar a lokacin
ake raɗa masa shi.
“Barrister Abdallah Ibn Adam Aas! Kar kayi taurin kai, dan
zaka iya rasa kanka dama waɗan da kake yunƙurin
taimakawar. Ni umarni nake baka ba shawara ba kamar shi,
domin hatta iyalanka ba zasu tsira ba daga tarko na”..
Ɗan zabura Barrister yay tamkar wanda cinnaka ya ciza.
Daga can aka cigaba da magana cike da isa. “Suna hanyar
zuwa gareka, ya rage naka tun yanzu ka raba gari da su, ka
kuma gargaɗi surikinka. Na barka lafiya”. Yana kokarin yin
magana ƙitt aka yanke kiran. Ciro wayar yay da sauri daga
kunensa, ganin ta yanke yay ƙoƙarin kiran number...
Mutumin dake tare da shi ya miƙe yana dariya. “Barrister
shawara karma ka wahal da kanka dan basake samunsa zakai
ba har abada in har a wannan layin ne. Na barka lafiya”.
Da ƙyar Barrister ya kwato numfashinsa gab da mutumin zai
fice. Cikin jarumtarsa ya dakatar da shi a ɗan tsawace. “Ni
kurari ko gizago basa firgitani ai. Dawowa ka ɗauka trash bag
ɗinka zai fi maka alkairi fiye daka barta anan ta zamewa
rayuwarka BAYA DA ƘURA. wannan shawara ce”.
Har cikin rai maganganun Barrister sun sokesa. Amma
kasancewar sa ɗan hannu a iya bariki sai ya saki murmushi.
Batare da yace komai ba yay salute ɗin Barrister dake masa
kallon ƙasƙanci yay ficewarsa.
Baya Kaka da Abu Zainab dake yunƙurin shigowa office ɗin
suka ja dan kaɗan ya rage suyi gware. Suna masa sallama bai
ko amsa su ba yay musu kallon ƙasa da sama yay wucewarsa.
Basu damu ba, dan daga ganinsa kaga babban mutum.
Barrister da aka bari da juyawar kai ya amsa musu sallama
cike da son danne ɓacin ran dake a fuskarsa. Sun gaisa da
mutuntawa kamar yanda suka saba. Fuskar Kaka da ɗan
murmushi ya ce, “Ashe kuma an dace da sanin inda suke?”.
Murmushin ƙarfin hali Barrister yayi da jinjina kansa, ya
jawo wani file dake gefensa. “Nima banyi tunanin abin zai zo
mana da sauƙi haka ba Baba. Amma Alhamdullah addu'a bata
faɗuwa ƙasa banza. Inaga muyi azamar zuwa ma kar'a samu
wani tazgaro kuma kasan halin ƙasar tamu”.
Daga Kaka har Abu Zainab sunyi na'am da hakan. Duk suka
miƙe babu ɓata lokaci suka fice kowa da abinda ke masa kai
kawo a cikin rai musamman Kaka da Barrister.....

*_MASARAUTA. (MALIKAT BUSHIRAT_*

Cikin zumuɗin son jin yaya haɗuwar Shahan-shan da
Zawjata-almilk ta kasance a jiya Malikat Bushirat tai shirin
ziyartar sashen Malikat Haseena a yau. A ƴan rakkiyarta har
da Jasrah dake son sake duba jikin Iffah. Tuni ƴan leƙen asirin
cikin hadimai sun kwasa zuwa sassan iyayen gijinsu kuwa.
Dan wannan ya zama kamar al'ada a masarautar kowane ɗan
leƙen asiri kan kai wa uwargijiyarsa ko uban gidansa duk wani
motsin wani babba a daular. Ta wannan hanyar ne a mafi
yawan lokuta abubuwa ke yaɗuwa kunnen duk wani mai faɗa
aji na gidan musamman abinda ya kasance na sirri.
Malikat Bushirat ta samu tarba ta girmamawa ga surukar
tasu a fadarta. Tuni hadimai sun cika gabansu da kayan motsa
baki. Kasancewar ganawar ta shafi wani yanki na ɓoyayyen
sirrinsu duk wani hadimi aka sallamesa. Katafaren falon ya
kasance daga Malikat Haseena sai Malikat Bushirat da Jasrah
sai Daneen Ammarah. Tattaunawar ta jasu tsahon lokaci kafin
Malikat Haseena ta aika amintacciyar hadimarta Banou kiran
Iffah....

★Sam Iffah dake cikin wani yanayi na tsananin faɗuwar
gaba da sanyin gaɓɓai sakamakon mummunan mafarkin da
tai akan su Babiy a barcin zuhur daya figeta bata san mi ake
ba saboda bata fita ko'inaba yau iyakarta ɗakinta. Yanzu
hakama da aka idar da sallar la'asar tana tsumayen Daneen
Ammarah ne kamar yanda ta saba, dan duk yinin yau ma
basu haɗu ba tun bayan idar da sallar asuba dai data fita ta
gaishesu kamar yanda ta saba ita da Malikat Haseena.
Hadimai dai sun kawo abinci tare da saƙon gaisuwa daga
Daneen Ammarah ɗin ɗazun da rana akan cewar tana nan
tafe. Malikat Haseenah ma kullum da kanta takan zo ta duba
ta, kasancewarta tsohuwa mai dattako da iya zama da
mutane tuni ta shige zuciyar Iffah itama, dan duk da bata da
sakewa da yawan fara'a har dan jan Iffah take da hira.
Sallayar datai sallar ta linke har yanzu jikinta a sanyaye ga
damuwa fal ranta akan iyayenta, acan ƙasan zuciyarta takeji
akwai wani mummunan abu dake sake tunkarota koma ya
riga ya iso garetan ta hanyar iyayenta batare data sani ba.
Yanayin ɗan zafi da ake ya sata yaye mayafin abayan data
naɗe kanta da shi ta ajiye, ɗaurarren dogon baƙin gashinta
dake reto a tsakkiya ya bayyana. Abincin da aka shirya mata
tun ɗazun da bata ci ba ta nufa, ta bubbuɗe taga komai,
batama jin cin komai har yanzun, dan haka ta tsiyayyi madara
kawai da shanta tamkar al'adar ƴan ƙasar ne. Tana buƙatar
fara canja kayanta zuwa marasa nauyi, dan haka ta ajiye kofin
madarar a bedside drawer. Toilet ta fara shiga ta fito sannan
ta shirya cikin wata yar yololuwar rigar mara nauyi mai zubin
shimi. Iyakar rigar gwiwar ta ne, gata kalar fari da adon
jajayen firanni. Ta matuƙar haskata da fidda ƙuruciyarta
tamkar ƴar budurwar balarabiya. Turarrukan da Daneen
Ammarah ta tule mata ta zaɓa kusan kala uku ta fesama
jikinta. Cikin nutsatstsen takunta ta dawo saman gadon tana
mai kallon fatar hanunta dake jajir saboda saɓar da tayi.
“ALLAH dai ya isana wlhy” ta faɗa cike da halin tsiwarta tana
jan bargo ta rufa iya cinyoyinta bayan ta jingina jikinta da
fuskar gadon. Littafin da take rubuce-rubucenta na duk
abinda ya faru ta ɗauka ta buɗe ko zata ji sassaucin tunane-
tunen da zuciyarta ke mata marasa daɗi akan iyayenta, dan
sam mafarkin nan yaƙi barin ranta koda na sakan ɗaya... A
zahiri rubutun tai shirin fawara, dan yanda ta tsurama littafin
ido da riƙe biron da nutsuwa matuƙa zai saka ka hasashen
haka. Sai dai sam ko kalma biyu ta kasa rubutawa tamkar ma
an mata wankin ƙwaƙwalwa komai ya gudu, hasalima nisan
da tai a tunani yasa bibbiyu take ganin rubutun baya da
tayi....
Knoking ƙofar da akai ya sata jan numfashi ta fesar, sai
kuma taja mayafin dake gefenta ta yane jikinta har saman
kanta tare da amsawa da “Yes! Kowaye ya shigo”.
A ɗarare hadima banou ta shigo, tsananin tsoron Iffah
shimfiɗe akan fuskarta ya kasa boyuwa. Daga bakin ƙofar ta
zube muryarta na ɗan rawa kamar yanda jikinta ke tsuma.
“Amincin ALLAH da lafiya su tabbata ga Zawjata-almilk”.
Harara Iffah dake kallonta ta zabga mata. “Ina tare da
masu lashe kurwar mutane irinku lafiyar zata tabbata a
gareni? mtsoww!! Malama faɗi abinda ya kawoki bana son
gulma”.
Ƙasa Banou ta sakeyi da kanta muryarta na rawa, dan
harga ALLAH tana shakkar wannan yarinya da ko magana
gatsau take yinta babu alamar shakku tattare da ita. “Uhm
uhm dama Malikat ce take buƙatar ganinki”.
Hannu kawai Iffah ta ɗaga mata, dan har cikin rai ta
tsani matar nan matuka. Sai da ta miƙe zata buɗe ƙofa
sannan tai magana a gadarance. “Ki jirani a ƙofa, saura kuma
kafin na fito ki lashe mun hadimai azzalumar bamza”.
Da rawar jiki data harshe Banou tace, “Hakan bazata faru
ba ranki ya daɗe”.
“Uhm munafuka kamar gaske”.
Iffah ta faɗa tana sauka a gadon cikin mita......

★Tunda suka shigo ko sau ɗaya Iffah bata iya ɗaga kai ta
kalla ko ɗaya a cikinsu ba. Saɓanin su da duk suka zuba mata
ido cike da jin ƙaunarta a rayukansu. Cike da nutsuwarta ta
karasa garesu, maimakon kujera da duk suke zaune sai ta kai
ƙasan lallausan dardumar...
“Haba Ibnati tashi ki hau sama mana”.
Jasrah tai yunƙurin dakatar da ita. Kai Iffah ta girgiza da ɗan
murmushi a fuskarta, “A'a nanma ya isa”. Cike da sha'awa da
jin daɗi duk suke dubanta. Ta juya ta gaishe da Malikat
Haseena, da fara'a da kulawa ta amsa mata tana mai sanya
mata albarka. Cikin jin daɗi ta juya gasu Malikat Bushirat ta
gaidasu suma. Suma da kulawar suka amsa mata, dan duk
ƙasaita da jin kan Malikat Bushirat sai ta tsinci kanta da
murmushi da sauƙaƙawa akan yarinyar saboda kwarjini da tai
mata. Shiru na wasu ƴan sakkani ya biyo baya, kafin Daneen
Ammarah ta katse shirun ta hanyar kiran sunan Iffah.
Ta amsa mata da girmamawa sai dai bata iya ta ɗago
kanta ba. Daneen Ammarah ta sake kiran sunanta da faɗin,
“Kinga ɗago ki kallemu”. Da ƙyar ta iya dauriyar bin
umarninta. Dan duk rashin jin Iffah tana da wani hali na
girmama duk mai nuna mata ƙauna koda bai cancanta ga
sauran mutane ba. “Ibnati nasan nan zuwa yanzu duk kin
sammu ko?”.
“Eh Mamy”.
“Amma baki san matsayinmu ba?”.
Nanma tace “Eh Mamy”.
“To Alhamdullah yau duk zaki sani. Ina son ki bani dukkan
hankalinki nan ki kuma saurare ni yanda ya kamata”.
Ta jin jina mata kai.
“Kamar yanda nasan kikaji Mamma a garemu mahaifiya ce,
itace ta haifi Hama (Suruki) ɗin ki, da ni dama wasu biyu da
zaki sani anan gaba sai dai ɗaya ya rasu”.
“ALLAH ya gafarta masa”.
Ta faɗa cike da rauni. A tare suka amsa mata da Amin.
Daneen Ammarah ta ciga da faɗin, “Wannan da kike jin ana
kira Malikat Bushirat itace Hamah (Suruka) ɗinki data haifi
Shahan-shan na yanzu kuma mijinki da yazo nan jiya......”
A razane Iffan ta waro idanu ƙirjinta na wani irin harbawa
kamar zai wantsalo. Cikin subutar baki ta ce, “Shahan-shan!
Na jiy.....” sai kuma tai shiru ta haɗiye sauran maganar
saboda tuna a inda take...
“Kin sanshi ne kafin jiya?”.
Malikat Haseena dake nazartarta ta jeho mata tambayar a
bazata. Da sauri Iffah da zufa ta jiƙema dukkan jiki, ta girgiza
kanta. Kasancewar ta gwanar wayo tai saurin faɗin, “Mamma
ina mamaki ne dai, ban zaci ganin Shahan-shan ɗin nada
sauƙi kamar haka ba”.
Kusan a tare suka saki murmushi saboda hango tsantsar
ƙuruciya a maganar tata. Sai dai malikat Haseena tsaf ta
gama karantar Iffah waskewa tai. Amma kasancewar ta
tsohuwa mai dattako sai ta dake itama ta shiga jerin ƴan
murmushin.. Daneen Ammarah ta cigaba da faɗin, “Wannan
ƙanwa ce ga Malikat Bushirat, Khaalah (Aunt) ga mijinki. Na
baki ne a dunƙule iyamu da muke anan saboda muhimmancin
abinda zakiji a yanzu”.
Kai Iffah ta jinjina mata da alamun gamsuwa. Jasrah ta
cigaba daga inda Daneen Ammarah ta tsaya.
“Ibnati dalilin miki wannan dogon sharhin a kammu
shine fara aikinki matsayin Zawjata-almilk a wannan
masarauta. Alhamdullah tunda kinji sauƙi zaki koma sashenki
kamar sauran Zawjata-almilk guda biyu, sai dai zaki samu
horo daga wasu amintattunmu matsayinki na Zawjata-almilk.
Mun zaɓeki ne saboda nutsuwarki da tarbiyyarki. Basai mun
zaman sharhi akan abinda ya faru ba a baya kasancewar
kema ƴar kasa ce kin san komai na dangane da mutuwar
matan Shahan-shan da suka gabata.”
Iffah ta haɗiye kududun baƙin cikin daya tokare mata
maƙoshi akan famin rasa ƴan uwanta da tai da ƙyar ta jinjina
kanta.
Malikat Bushirat ta amshe da cigaba da faɗin, “Ibnati
kece zaki zama mutum ta farko a rayuwa da zan nema
alfarma a gareta, hakan kuma ta faru ne saboda jinki da nake
a cikin raina da kallon da duk muke miki anan matsayin wani
haske da insha ALLAH zai haska mana duhun da muke ciki.
Muna son ki shiga jikin Saiful-malik domin binciko mana
ainahin minene matsalar, saboda dukkan waɗan can matan
da aka rasa daga kaisu turakarsa ne ake samun matsalar.
Mun miki alƙawarin baki dukkan kariyar da bazamu bari ki
cutu ba....”
(Kariyar UBANGIJINA zata kasance tare da Ni). Iffah ta
ayyana a zuciyarta.
Malikat Haseena ce ta cigaba da faɗin, “Zamu fara ne da
matakai da hanyoyin dinga haɗuwarku daga nan zuwa wani
lokaci, fatanmu ki zama mai saka ido a dukkan wani motsinsa,
a karan kansa, da duk wasu wanda zasu mu'amulancesa har a
cikin hadimai. Kiyi takan tsantsan, dan mutum ne shi mai
wayo matuƙa, sannan mai wahalar sha'ani da fahimta. Ba'a
gane mi yake nufi ko minene a ransa akan fuskarsa, kar ki
yarda ki bashi wata damar da zai iya zargi a kanki. Fatanmu
dai ki zama jaruma a dukkan al'amuransa dama na kowa dake
a wannan masarauta, duk abinda kikaci karo da shi ba dai-dai
ba kiyi maza ki sanar da ɗaya daga cikinmu”.
Zantukan nasu ya saka zuciyar Iffah dinga tsalle-tsalle a
kan dalilai biyu.......✍️

28
........Na farko ji a ranta UBANGIJI ya amsa mata addu'ar ta
akan burin data shigo da shi Daular ruman. Na biyu minene
dalilin waɗan nan mutane na buɗe mata cikinsu?. Na ƙarshe
da yafi kowanne razani da ban mamaki a ƙwaƙwalwarta
dama suma sun san shike aikata kisan kenan? Amma suka
zaɓi yin shiru saboda ba ƴaƴansu ake halakawa ba kokuwa
suma tsoronsa sukeji? A ɗan ƙaramin tunaninta tanaga zasu
iya yin amfani da ƙwanji wajen sanin mi Shahan-shan ɗin ke
aikatawa musamman Malikat Haseena da Malikat Bushirat.
Amma miyasa suka zaɓi yin amfani da ita? Kodai sun gama
gane manufarta ne a kansa.....?
“Ibnati!”.
Daneen Ammarah ta katseta daga nisan da tai a tunani ta
hanyar kiran sunanta da taɓata. Firgigit kuwa ta kawo ajiyar
zuciya. “Karki kasance a dogon nazari, manufarmu ta sakaki a
wannan sabgar tana da nasaba ne da dalilai biyu. Na farko
juriyarki ta bamu ƙwarin gwiwar kallonki a jaruma. Na biyu
jinki wata abu mai muhimmanci da muke fatan nasara ta
dalilinta kodan tsallake tarkon masu aikata wannan ɓarna da
kika tsallake a harin farko da muke jin shine lagon da aka
dinga ɗanawa a farko wajen salwantar da rayukan da suka
gabata....”
“Mamy nima zata yuwu bana tsallake bane dan nafi
ƙarfinsu, maybe na tsallake ne saboda tsayawarku da fatanku
akan ganin na tsallake ɗin. Amma tabbas zan iya sadaukarwa,
zan kuma iya bin umarninku badan inajin ƙarfina ya kai ba sai
dan kun isa ku bani umarni”.
Su dukansu kalamanta sunyi wani tasiri na musamman
a zukatansu tare da ƙawatata a cikin idanunsu. A wani gefen
sunyi amanna irinta ɗansu ya dace ya samu tun farko, dan
ƙarfin gwiwarta sunyi dai-dai da Zawjata-almilk da akafi
buƙata ga kowane Shahan-shan. Sannan Malikat da sukema
kansu fata.
“ALLAH yay miki albarka”.
Suka faɗa kusan a tare su duka huɗun. A kan laɓɓanta ta
amsa da amin.
Sun cigaba da tattaunawar da gaba ɗaya ta saka Iffah cikin
ƙagara, ƙagara mai nasaba da shiga ruɗanin wani furici daga
Daneen Ammarah. Wai jiya Shahan-shan ne wanda ya
ziyarcesu a wannan falon, tana buƙatar samun filin tunani
dan zuciyarta da ƙwaƙwalwarta fa gaba ɗaya sun kulle, ruɗani
ya gama mamaye duk wani hangenta da dama bai wuce iya
tsayin ƙafafunta da shekarunta ba....

★★....

A hankali ta maida ƙofar ta rufe tare da jingina a jikinta ta
lumshe ido da sauke numfashi tamkar mai kokawar jawosa.
Shin murna zatayi a wannan gaɓar ko kuwa shiga ruɗani?.
Idan ance Shahan-shan ne a jiya ta yarda, shi kuma wanda tai
gamo da shi a mabanbanta wajeje kafin shigowarta
masarauta wanene shi?. Wannan tambaya tafi kowace
tambaya girma da girgiza zuciyarta a duk abubuwan dake cin
ranta. “Kai nifa nama ruɗe wlhy”.
Ta faɗa a zahiri tana zamewa cikin sarewa ta zube ƙasa. Ta
jima a wajen cikin halin shiru da ambaton hasbinallahu wa
ni'imal wakil ko zata samu dai-daiton komawa cikin hankali
dan da gaske komai na halittarta mai motsi ya raunana da
rauni mafi ban tsoro da shiga ruɗani. Tsahon lokaci ta kwashe
a wajen tana kokawa da raunin zuciyarta da rashin ƙarfin
gudanar jini. Fahimtar wancan tunanin na buƙatar lokaci ya
sata turesa ta maida hankali akan tattaunawarsu da su
Malikat. Tabbas wannan shine babban ƙudirinta dayin
ƙundunbalar juriya na tunkarar rayuwar da bata da tabbacin
tsallakewa. Duk da tasan anfi ƙarfinta, dama duk wani mai
ƙarfi da take kallon ƙarfinta ta zaɓi fuskantar mutum mafi
girman iko da tsaro domin ɗaukar fansa. A kwanakin da suka
gabata na kasancewarta cikin wannan daula ta fara fidda ran
samun cikar burinta saboda dalilai masu yawa. Ciki harda
rashin samun koda ƙanƙanuwar ƙofar sanin minene ma
daular ruman ɗin ta ƙunsa balle Shahan-shan da kansa. Sai
gashi a yau cikin sauƙi an buƙaci kaita inda zuciyarta ta fara
raya mata zuwansa ba ƙaramin tsalle bane da ba'a da
tabbacin fita idan an shiga, aka kuma sanar mata wani yanki
na sirrin daular ruman mai girman gaske da ko na ciki basu
san da shi ba ƙila. “Anya babu wani abu a ran mutanen nan
saɓanin abinda suka faɗa?” bakinta ya furta a zahiri cikin sake
dulmiya a ruɗani. (Koda akwaisa yardar ki dasu ce zata baki
ilimin sanin hakan) zuciyarta ta faɗa cikin ƙarfafata da ture
raunin dake neman rinjayarta....
Knoking ƙofar daya wanzu a dai-dai lokacin ya sata jan
numfashi a sauƙaƙe. Da ƙyar ta iya miƙewa daga zaman
daɓaron da tayi ta buɗe. Daneen Ammarah ta sakar mata
murmushi. Cikin yaƙe ta mayar mata da murtani da matsawa
ta bata hanya. Rissinawa hadimar da suke tare tai ta gaisheta,
hannu kawai ta ɗaga mata alamar amsawa tana bin ledar
hanunta da kallo......

★★.... ★.... ★★.....

Kamar yanda aka sanar da Barrister kai tsaye station ɗin da
akace su Babiy suke suka nufa. Kasancewarsa babba kuma
sananne basusha wahalar ganin ogan station ɗin ba kai tsaye.
Sunyi gaisuwa irin tasu ta manyan ma'aikata, su kai kuma
gaisuwar girmama juna da su Kaka.
Barrister ya gabatar da kansa, ya kuma gabatar da abinda
suke tafe da shi harda hoton su Babiy domin sauƙaƙawa.
Jami'in yay shiru yana kallon hotunan kamar mai hasashe, sai
kuma ya ɗago ya kalla Barrister “Gaskiya banajin akwai
waɗan nan mutanen a wannan station ɗin Barrister”.
Barrister daya fahimci matsala ce ke neman shigowa yay
ɗan murmushi da muskuta zamansa. “Yallaɓai adai sake
dubawa, zata iya yuwuwa ko akwaisu ɗin baka da labarin
hakan. Amma tabbas suna a wannan station ɗin. A matsayina
na Barrister ba nazo nan dan a bani belinsu bane ba, duk da
nasan basu da hannu a abinda ake zarginsu. Nazo ne dan na
gana da su, sannan a miƙasu kotu saboda nasan dai ita matar
data saka aka kawosu nan burinta a kwatar mata hakkin
mijinta”.
“Iya gaskiyata nake faɗa maka Barrister babu waɗan nan
mutanen a wannan station ɗin. Amma mizai hana ku sami ita
matar na tabbata tunda tare da ita akaje tasan wane station
ne”.
Barrister yay shiru yana kallonsa cike da nazari. Hakama
Kaka da Abu Zainab. Kusan minti biyu shiru babu wanda ya
motsa, kafin Barrister ya miƙe yana ɗan murmushi ya bashi
hannu. Suma su Abu Zainab miƙewar sukai...

Da kallo ya bisu har suka gama ficewa, ya kai hannu kan
wayarsa dake saman desk ɗin sa yana wani murmushi. A
bugu biyu aka ɗauka wayar daya kira. Sallama kawai yay da
faɗin, “Kamar yanda kai hasashe ranka ya daɗe yanzu suka
bar office ɗina”.
Shiru yana sauraren mi'ake faɗa daga can, sai kuma yay
murmushi da amsawa da “Angama ranka ya daɗe”. Daga
haka ya ajiye wayar yana wata ƴar iskar dariya...

Abu Zainab daya kasa fahimtar komai saɓanin Kaka da
Barrister dake hangen wani abu dalilin kashedi da akai musu
kafin zuwansu nan dama ya katse shirun da motar ta ɗauka ta
hanyar nisawa. “Anya kuwa wannan jami'in akwai gaskiya a
maganarsa Barrister. Kagafa yanda yake ƙyaf-ƙyaf da idanu
kamar tsohon ɗan jari hujja. Nifa wannan al'amari ya fara
bani tsoro wlhy”.
Barrister da zuciyarsa ke kai kawo ya fesar da huci,
“Kana tunanin yaƙi faɗa mana gaskiya ne Zakariyya?”.
“Fuskarsa ta nuna hakan ai Barrister, ko kuwa Kaka?”.
Kaka da shima dai yake aune-aunensa a rai ya girgiza kansa.
“Zata iya yuwuwa gaskiyar ya faɗa, sai dai kumin wani
taimako ɗaya dazai warware mana gaskiyar tasa ko
saɓaninta, bayan nan zan sanar muku abinda ya faru kafin
zuwanmu nan”.
Barrister da shima abinda ke'a ransa kenan ya ɗan juyo
ya kalla kaka ta madubi, “Muna jinka Baba”.
“Muyi gaggawar isa gidan Dawood”.
“Shawara mai ƙyau Baba”.
Barrister ya faɗa yana juya motar hanyar da zata kaisa gidan
Abu Moosa.

★★... ★★... ★★...

“Mamy kuma duka wayar da lap-top ɗinne nawa?”.
Iffah ta faɗa da mamaki. Murmushi Daneen Ammarah tayi,
“Ibnati wannan ai ba komai bane ba, sannan ko baki faɗa ba
kina buƙatar su tare da ke kodan ki dinga jin motsin gida. Na
biyu kuma wannan aikin da zaki fara kowa yasan mai haɗari
ne, dolene ki kasance da waya a duk inda kike a masarautar
nan. Da zarar Kinga abinda zuciyarki bata kwanta da shi ba a
cikin mu huɗun zaki iya kiran kowa ki sanar masa. Lap-top
kuwa ni naga ya dace na kawo miki ita domin ɗebe kewa.
Amma kiyi taka tsantsan ki kuma kula sosai, dan samun
waɗan nan na nufin zaki iya mu'amula da kowa musamman a
yanar gizo batare da kin samu tabbacin wanene ɗin ba”.
“Haka ne Mamy, insha ALLAH zan kiyaye. Nagode sosai
ALLAH ya saka da alkairi”.
“Karki damu kin cancanta ne ai”.

★Iffah ta daka tsallen murna bayan ficewar Daneen
Ammarah, harda ƴar rawarta. Duk wani tunani da kaikawon
da zuciyarta ke mata akan Shahan-shan zuwan wannan waya
da lap-top ya kauda mata shi. Domin a ganinta dama biyu ce
tazo mata a lokaci guda kuma zata damata ta yanda dole sai
Shahan-shan ya shata. Yanzu dai abu na farko da zata fara
shine malam Fawzan. Ta tura masa saƙo bayan nemansa da
tai shi da abokinsa wayar Arfa dake hanunta ta mutu ba caji,
tana buƙatar tasan ko yaga saƙon? Ya kuma iyayenta suke?.
Samun wayar da caji yasa tun a daren ta haɗata, duk da
taga akwai sim card batai amfani da shi ba ta cire na Arfa ta
sanya. Tamkar jira saƙon Malam Fawzan ne ya fara shigowa,
jikinta har tsuma yake wajen buɗewa. Batako kai ƙarshen
karantawa ba kira ya shigo. Gabanta ne ya faɗi ganin
baƙuwar lamba, amma tsabar ƙarfin hali sai ta ɗaga.
“Sir!”.
Ta faɗa cikin gwalalo idanu da nufar ƙofa da sauri ta saka
key. Daga can aka amsa mata da “Na'am Fareedah. Ina kika
shiga haka? Tun bayan ganin saƙonki na kasa samunki, har
zuciyata ta karaya da ko wani ya gano ki ne?”.
“Babu wanda ya gano ni Sir, akasi aka samu wayar ta
mutu, na kuma rasa ta yanda zanyi cajinta dan na manta da
cajan a gida”.
“Ayya. Kin ganni akoda yaushe cikin gwada wayarki nake
koza'a dace. Saboda ke na samar da wannan layin na sirri.
Yanzu ma gwadawa kawai nake amma banyi tunanin samunki
ba sam”.
Iffah ta share hawayen da suka silalo mata tana ɗan
murmushi. “Nagode Sir, koda banyi nasara ba bazan taɓa
mantawa da kai ba. Ina fatan ka bincika min su Ummu. Dan
sam na kasa samun kwanciyar hankali na rashin jin su”.
Ɗan jimm yay kamar mai tattaro abin faɗa, sai kuma yay
ɗan murmushin basarwa. “Suna lafiya dan har gida naje, sai
dai ban samu shiga ba kasancewar suna tare da tsaron
dakarun masarautar har yanzu. Amma nayi ƙoƙari mun haɗu
da Hanash....”
“Amma miyasa wayoyinsu basayi?”.
Ta katsesa a ƙagauce. Da ƙyar ya iya tattaro abin faɗa a
wannan gaɓar ma. “Shi Babiy wayarsa ta samu matsala ne.
Hanash kuwa network ne dan yace min shima yasha nemanki
amma baya samunki”.
“Bani da lafiya ne, ba koyaushe kuma wayar ke kunne ba.
Amma yanzu zan sake nemansa insha ALLAHU dan ina
matuƙar bukatar son naji muryoyinsu kozan samu nutsuwa”.
“Hakan yana da ƙyau. ALLAH kuma ya ƙara lafiya. Kinyi
waya da abokina kuwa?”..
“Eh nayi, amma kamar yanda na sanar maka a text message
an ɗaga amma ana mun wani shirmen banza. Daga ƙarshe ma
akace wai na saɓa lamba”.
Karan farko malam Fawzan yay ƴar dariya. “Taku ne
kawai irin na masu iyawa. Amma a yanzu na tabbatar zai
saurareki”.
Iffah ta ɗan taɓe baki kamar tana gabansa. “Ni ALLAH
harna ɗauka ko ka yaudareni ne ka bani number daba itaba
ma”.
“Iffah koda abin wasa kikazo da shi bazan masa riƙon
banza ba balle wannan mai matuƙar muhimmanci da ma'ana.
Yanzu dai ina fatan wayar taki akwai caji?”.
“Ai bama waccan bace, sabuwa fil aka bani a kwali yau
harda lap-top”.
Jimm yay na wasu ƴan sakkani. Sai kuma ya cire wayar a
kunnensa ya duba. Tuna ashema shine ya kirata ya sashi sake
maidawa. “Amma baƙya zargin akwai wani dalili a baki
wayar? Mutanen nan fa sunada haɗari sosai Iffah. Bazan
ɓoye miki ba inajin tsoron ƙarfin ikonsu”.
“Nice zan baka wannan labarin Sir kasancewata a cikinsu
yanzu. Sai dai kuma wanda suka bani wayar yanki ne na
mutanen kirkin cikinsu. Kasan a ko ina akwai ƙyakykyawa
akwai kuma mummuna”. Tsaf ta

Please Login or Register in order to submit comment