Reading Dauɗar Gora by Bilyn Abdull ce Chapter 24 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne kawai, amma sai bata sake musawa ba
sukai sallama.....

★★.... ★.....

Miran Jasim ya sauke wayar dake a kunnensa bayan gama
sauraren abokin wayar tasa, yanda fuskarsa ta canja daga
farin cikin dake shimfiɗe a kanta kafin wayar yasa Miran
Arshaan sake maida hankalinsa garesa. “Wani abu ya sake
faruwa ne?”.
“Zai dai faru”.
Cewar Miran Jasim ɗin a fusace yana miƙewa. Miran Arshaan
da maganar ta dakesa ya miƙe zumbur shima. “Ban gane mi
kake son cewa ba Jasim Akh?”.
Kamar bazai tanka masa ba sai kuma yaja kakkauran tsaki.
“Harun Al-rashid ne dai akan waccan maganar banzar ta
ranar, duk yabi ya tashi hankalinsa yana cigaba da damuna
nima, tun abin bai tasiri a raina ba har ya fara, wai Barrister
da suka bama aikin can kan ɗan iskan can ne ke cigaba da
musu bayani dai kan Barrister Abdallah bai mutu ba dai da
gaske.”
“Wai suna nufin shi ya tabbatar da hakan kenan?”.
“Abinda ke cazamun kai kenan, na rasa wane shirme ne
kuma hakan? Taya wanda bomb ya tashi da shi ace bai mutu
ba?”.
“To amma fa kuma maganarsu fa abin a duba ce Jasim Akh.
Dan koni naji shakku a randa bomb ɗin nan ya tashi amma
jami'an tsaro suka tabbatar babu wani alamar an rasa rai......”
“Amma shine kai shiru?!”.
Miran Jasim ya katsesa a zafafe. “Mi kake so nayi bayan
wanda nayi to? ina son ka tuna tun a ranar na kawo maka
wannan zancen amma ka nuna min cewar zata iya yuwuwa
ƙarfin tashin nakiyar ya cillashi wani waje ne shiyyasa basu
gansa ba. A kuma shekaran jiya da suka kawo maganar na
kuma ƙoƙarin maka nuni ka kalli zancensu a shirme”. Shima
Miran Arshaan ɗin ya karɓa masa a nasa zafin.
Shiru Miran Jasim yayi da dafe kansa yana murza goshinsa
dan ya tuna tabbas anyi hakan. Amma wannan aikin na cikin
gida da rashin sanin mi Tajwar Eshaan ke ciki ya ɗauke
hankalinsa bai nutsu yayi nazari kan batunba kasancewar
akwai abubuwa da yawa da bawai yana buɗema Miran
Arshaan ɗin bane, kamar yanda shima Miran Arshaan ɗin ba
komai yake yarda ya buɗe ma Miran Jasim ɗin ba. Sai dai a
yanzu dukansu sun fahimci yin kuskure, dan haka kowanne ya
ajiye ɓoyayyar manufarsa suka fuskanci juna.
“Ni ina ganin in har an yarda da aikin Barrister ɗin nan
shawararsa ba abar yardawa bace. Sannan dole ne fa mu
gaggauta ganawa da yarinyar can in ba hakaba aikinmu zai
iya buɗewa. Dan idan ya kasance Barrister Aas na raye bazai
samu ɗaki bane ya kulle kansa domin hutu kaima ka sani”.
Miran Jasim ya gyaɗa kai da faɗin, “Hakane maganarka na
kan gaskiya. Yanzu minene abinyi?”.
“Abinyi ɗaya ne bama Barrister Akeem damar shigewa
gaba kafin kwana biyun nan na cikar aikinmu abar ƙasar nan
da mutanen. Bayan ka haye karagar mulki shi kuma shegen
duk inda yake zamu nemishi ne ya ɗan-ɗana kuɗarsa”.
“Ina sake godema ALLAH da kasancewar ka kusa da ni, dan
kana farkar da ni a duk sanda kaina ya shiga duhuwa ɗan
uwana”.
Murmushi Miran Arshaan ya saki a zahiri, a zuciya kam faɗi
yake, (Banza ka gama cusamin ƙayar a rumbu na rufeta da
ɗan boto ina daga kwance).
Ɗaukar wayar Miran Jasim dai-dai da kammala wayar Iffah
da Daneen Ammarah daga can......

★★.....

Tana ajiye wayar wani kiran ya sake shigowa, kamar zata
share dan bata san number ɗin ba sai kuma dai ta ɗauka da
tunanin ko Sir Ajmaal ne kasancewar a saƙonta na ƙarshe ta
roƙesa idan ya gani ya kirata. Daga can aka amsa sallamarta
kai tsaye, hakan ya sata Ciro wayar a kunenta ta kalla tamkar
mai son gano muryar. Miran Jasim da kamar yana ganinta yay
gyaran murya, hakan ya sata sake maida wayar.
“Kina magana da Jasim Ibn Abdull-Majeed Aliy”.
Kai tsaye Iffah ta ganesa, dan haka ta fara gaidashi da
girmamawa. Hakan ya masa daɗi, dan yanda yake amsa mata
da kulawa zai baka tabbaci. Shiru ne ya ɗan biyo bayan
gaisuwar, kafin ya katsesa da faɗin, “Ibnati inata zaman jiran
ji daga gareki amma shiru. Ko baki amince da abinda kika gani
bane ba dai?”.
Iffah da ke jin an taɓo mata inda ke mata ƙaiƙayi hawaye
suka shiga rige-rigen sakko mata. Hannu tasa ta sharesu da
ɗan jan hanci. “Ba yarda ne banyiba ranka ya daɗe, kawai dai
zuciyata na kaikawo ne na son sanin dalilinka na yin hakan a
gareni. Idan ban manta ba kai fa Ammi ne garesa, mizaisa ka
zaɓeni sama da shi? A barshi ma zaka iya hakan kasancewar
ka mai gaskiya ko ƙyamar abinda yake. Amma miyasa su na
baya da aka rasa bakuyi wani yunƙuri ba sai ni a kaina bayan
akwai ƴaƴan Tajwar mafi rinjaye a cikin wanda ya halaka?”.
(Kaga ibilishiyar yarinya) ya ayyana a zuciyarsa. A zahiri
kam sai yay gyaran murya cike da dattako yana kallon Miran
Arshaan da shima ke sauraren komai. “Wato Ibnati duk yanda
zan miki bayani a wayar nan ba lallai ki fahimta ba. Amma zan
tura miki lokaci da adireshi mu haɗu zai fi”.
Jimmm Iffah tayi kamar mai shakku, sai kuma ta nisa
cikin gyaɗa kai tace, “Okay babu damuwa ina jira”. Daga haka
sukai sallama kowa ransa na masa kaikawo...

★★....

Cikin ƴar dariya Miran Arshaan yace, “Amma shegiyar
yarinyar nan fa da zata samu dama a masarautar nan ba
ƙaramin hatsabibiya za'ai ba. Kaji murya cauy-cauy bata ko
tsallaken kalma ga shegen wayo”.
“Shiyyasa dolene tana kammala aikin nan a kaudata
kawai, ai tunda har tana da ƙarfin halin shigowa masarautar
nan da ƙudiri irin na kashe Shahan-shan dama nasan zamuga
fiye da hakan tattare da ita. Irin waɗan nan yaran masu taurin
zuciya a cikin mata basu da yawa, amma kuma kasancewar su
mata ga mai mulki ba karamin ƙara samun power bane.
Badan-badan ba babu abinda zai hanani tabbatar da ita
abokiyar tafiyata. Dama yarinyar ga shegen ƙyau da ƙira
tamkar ita ta zana kanta...”
Ƙaramar dariya Miran Arshaan yay idonsa akan ɗan uwan
nasa. “Wato dai Jasim Akh har yanzu bazaka canja ba, na
ɗauka tuni ka jingine batun son matan nan naka kodan
kujerar da ke gab da zama taka”.
“Bazaka gane bane Arshaan Akh”. Miran Jasim ya faɗa
yana tasa ƴar dariyar shima da komawa jikin kujera ya lafe
ƙyaƙyƙyawar surar Iffah da bata wuce sa'ar autarsa ba na
masa kaikawo. Shima dai Miran Arshaan ɗin hakance a ransa,
dan tun randa suka haɗu da Iffah a wajen wasan takobi da
Tajwar Eshaan yarinyar ta kasa barin ransa. Duk da dai shi
yanzu kam ya ɗan rage bin mata tun aurensa da Jasrah.
Humm masu karatu Bara na ɗan tsakura muku wata gulma
dai karna wuce. (A baya ƙiyayyar ƴan ɗakin su Miran Jasim da
Miran Arshaan a bayyane take fiye data ƴan ɗakinsu Tajwar
Haysam (mahaifin Tajwar Eshaan kenan) amma a wasu
shekaru bayan hawa mulkin Tajwar Haysam sai aka wayi gari
sun ɗinke, ƙiyayyar da sukema juna ta koma ta ƙarƙashin
ƙasa. Wannan haɗin kai nasu kuwa ya samo asaline a dalilin
kasancewar halinsu da yazo ɗaya. Awani lokacin bikin al'ada
kamar yanda duk suka saba sun baza yaransu samo musu
yara matasan ƴammata masu jini a jika da basu gaza sha
bakwai zuwa ashirin ba. Karku ɗauka da yardar yaran wai ake
kai musu su, ko ɗaya, ta karfin tsiya za'a ɗaukeki bayan an
shaƙa miki abu ko an yaudareki, bazaki tashi tsintar kanki ba
sai a ɓoyayyen gurin da in zaki kwana dubu ihu babu mai
jinki. Idan sun gama lalata rayuwar yaran kuma a jefar da su.
Alokacin da labarin yaje ga Tajwar Haysam hankalinsa ya
tashi, dan a shekarar an samu gawar yara ƴammata kusan
biyar da waɗan da aka jikata, iya bincike kuma na jami'an
tsaro ba'a sami komai ba. Da shekara ta dawo kuwa yasa
tsatstsauran tsaro akan kaikawon mata fiye da maza, aka
kuma sake sabon tsarin yanda bikin al'ada zai kasance. Ransu
Miran Jasim ya ɓaci matuƙa, dan ƙarshe sai a yaran
masarauta suka huce haushinsu ƴaƴan talakawa sun gagara
ɗauka. Duk da ba tare suke aikatawa ba sai shirunsu yazo
ɗaya a lokacin, har ya kasance yaransu dake sato musu
ƴammatan sunyi haɗaka akan yarinya rigima ta kaure,
kowanne ya sanarma ogansa, a zafafe Miran Jasim da Miran
Jasim suka buƙaci sanin juna kowanne da tunanin shike da
ƙarfin iko, sunko haɗun a yanayin da hantar kowanne ta kaɗu
dan mamaki, amma ƙwallafa rai da kowannensu yayi akan
yarinyar ya sasu amincewa juna yin tarayya da ita a tare
Wa'iyazubillah 😭 . Haka suka haɗu suka lalata rayuwar
yarinyar daga ƙarshe ta rasa ranta, a cikin masarautar suka
bizneta har a yau kuma babu wanda ya san hakan sai ɗauka
da ake yarinyar ta ɓata ne a taron bikin al'ada. Wannan shine
sanadin zamowarsu inuwa ɗaya dan wannan ya basu ƙofar
dinga kawoma juna mata, sai dai Miran Jasim yafi Miran
Arshaan ƙwarewa a harkar, dan shi har order mata yomasa
ake daga wasu ƙasashen ma🤦). Wanda ya gane na tayasa
murna, wanda bai ganeba ya tsallake kawai😂.
★★ BARRISTER ★★

Kamar yanda su Barrister ke zaman tsammani a yau sai ga
kira daga Sayeed Harun Al-rashid, sun tattauna sosai ciki
harda yarjewar fita da su Babiy zuwa wata ƙasa da kuma
tsananta bincike wajen gani maɓoyar Barrister Abdallah Aas
kamar yanda Barrister suka tsara musu. Abu mafi saka
Barrister a ƙololuwar farin ciki shine damƙa fita da su Babiy
ɗin a hannunsa, amma a zahiri sai ya nuna hakan ba aikinsa
bane, shifa ya bada shawara ne kawai.
A ɓangaren su sun nuna masa sufa sun yarda da shine,
bayan shi kuma bazasu iya bama wani aikin ba gudun abinda
zai je ya dawo. Bayan dai ɗan cigaba da tirjewa da ga ƙarshe
Barrister ya amsa. Hakan ya musu daɗi suma, dan a nasu
ɓangaren sun bashi aikinne domin ƙullama rayuwarsa,
acewarsu koda ta tashi salin alin zasu zare hanunsu su barsa a
ciki.
Barrister da ya gama fahimtar su da ƙudirinsu duk da
basu fito sun faɗa ba yay murmushi yana mai girgiza kansa da
mamakin mutanen wannan duniya mai cike da rikici. “Son
kai shine tushen rugujewar kawunan mu a wannan duniyar.
Mai mulki kansa kawai ya sani. Mai arziƙi kansa kawai ya sani.
Talaka kansa kawai ya sani. Mai ilimi kansa kawai ya sani.
Jahili kansa kawai ya sani. Iyaye kansu kawai suka sani.
Matasa kansu kawai suka sani. Yaro kansa kawai ya sani.
Kowa akan buƙatarsa kansa kawai yake iya kallo. Duk
shaƙuwa irin ta ma'aurata akan son kansu kowanne zai iya
aikata komai. Duk shaƙuwa irin ta ɗa da iyaye akan son kansu
zasu iya komai. A wannan duniyar yanzu samun cikakken
amini sai an tona, ka gama yarda da mutum amma akan son
kansa zai iya komai. Son kai dai! Son kai dai ya rabbi. Ƴan uwa
son kai fa na kawo abubuwa da yawan gaske. Yana gina
hassada a zuciya, ƙyashi, zalunci, raunana imani, ƙarya,
munafunci, kai komai ma wlhy, hatta shirka tana iya shiga a
cikin son kai batare da mun sani ba. Ya rabbi ka ganar damu
gaskiya tun kan ta nisanta a kunnuwanmu da idanunmu.......
✍️

(Wannan zance haka yake Barrister, ALLAH dai ka shiryar
damu🤦).
48


...........Babu kwanciyar hankali gasu Kaka, dan har yanzu basu
sami bakin zaren jin komai ba game da wadda aka rasa a cikin
matan Shahan-shan. Ga tashin hankalin ɓatan Barrister dan
sun je har gidansa amma a rufe alamar iyalansa ma dai basa
nan. Acewar makwafta kuma dai anzo an kwashesune a cikin
dare, yau kusan kwanaki takwas kenan. A lissafinsu kuma ya
kama randa Barrister ya ɓata kenan. Zuciyar kaka ingizashi
take kan abubuwa masu yawan gaske amma yana gocewa,
dan duk tsanani yayi alƙawarin dogaro ga ALLAH majiɓincin
al'amuran bayi a kowane tsanani da sauƙi. Kwanansa ɗaya ya
juya ƙauyen Jumna, dan yasan ya baro su Iyyani a tashin
hankali.

Ilai kuwa koda ya koma sai ya samesu a birkice, dan suma
dai zuwa yanzu labarin halin da ƙasar ke ciki ya isa har
kunnuwansu. Ummu tayi kuka har hawaye sun daina zuba. Ta
gama sadakarwa ta rasa autarta itama. Dama ta jima da fidda
rai ga su Babiy tuni. Kaka rasa ma mizai ce da su yayi, dan
shima dai nasa kan a zafafe yake. Sai kawai ya shige ɗakinsa
ya rufe kansa yana mai safa da marwa.......

★★..... BARRISTER ★★......

Da taimakon masu tsaronsa bisa umarnin ogansu da tun a
ganin farko da yay masa bai sake ganinsa ba sai ta waya tun a
yammacin ranar suka fara tattara abubuwan da zai basu
kariya wajen fita da su Babiy duk da basu zo hanunsu ba har
yanzu. Sai dai a daren ranar su Sayeed Harun Al-rashid sukai
alkawarin danƙasu hannun Barrister, duk da ya nuna musu
shifa yana jin tsoro su bari komai ya kammala sannan suka
nuna masa suna tare da shi da kuma tsaro na musamman duk
da kuwa ƙarya ne a baɗini.
Zancen kam nasu ya tabbata, dan a daren ranar ƙarfe
kusan tara na dare aka damƙa Babiy da Hanash a hannun
Barrister Abdallah Aas matsayin Barrister Akeem da
zukatansu su suka ɗauka. Daga gani kasan sun jigata matuƙa,
sun rame sosai sunyi duhu. Ga rashin ƙarfin jiki da zaman
waje ɗaya harma da ƙarancin abinci dana iska mai ƙyau.
Hankalin Barrister ya tashi matuƙa, ya dinga share hawayen
tausayinsu. Ya sake tabbatar da mutanen nan da suka
kamashi mutanen kirki ne a yau, dan ana iso da su Babiy
hanunsu sai ga likitoci, dan-da-nan suka duƙufa kansu da
kulawa kai kace dama a shirye suke da hakan.......

★★..... MASARAUTA ★★.....

Duk da ƙarancin shekarunta ALLAH ya bata basira irinta
masu hangen nesa. Tun bayan gama wayarta da Miran Jasim
zuciyarta bata aminta da yarda su gana fuska da fuska ba.
Dan haka ana idar da sallar magrib ta tura masa saƙo kamar
haka duk da ita ba sallar zatai ba tana fashi.
_Na amince mu tattauna, sai dai bata haɗuwa ba, muyi
magana ta video call._
Miran Jasim ya karanta saƙon yafi sau ashirin, takaici kam
ba'a magana ga ɗunbin mamakin basirar ƴar ficikar yarinyar.
A take ransa duk ya jagule, ga boka Barbushi ya tabbatar
masa haɗuwa da yarinyar fuska da fuska yafi fa'ida. Dan
kwarjininsa da suddabaran da ya basu zai sakamata tsoronsa
mai tsanani ya dinga yanda yaso da ita har zuwa sanda itama
zasu ɓaddata bayan ta cika musu aikinsu. Gashi yanzu guri ya
ƙure, bazai yiwu masa ba zuwa ga Barbushi ɗin dan zai iya
rasa wannan damar da bokan nasu ya tabbatar musu itace
ranarsu mafi Sa'a akan yarinyar kasancewar tana fashin salla,
tana kuma cikin ruɗanin da ba komai yake iya banbancewa
yanda ya kamata ba zasu iya sarrafata a duk yanda sukaso
musamman akan Shahan-shan. Duk da sallar isha'i data gama
gabatowa haka ya miƙe ya fice a masallacin bayan yayma
Miran Arshaan alama da ido. Bai jima da fita ba kuwa yabi
bayansa....

“ALLAH yasa dai lafiya na ganka duk a wani birkice?”.
Miran Jasim ya sauke idonsa akan Miran Arshaan mai
maganar yana mai jan tsaki. “Wane kwanciyar hankaline da ni
inba gani nai komai ya daidaita ba Arshaan. Yanzu ma ƴar
iskar yarinyar nan ce wai fa ta turamin text message bata
yarda mu haɗu fuska da fuska ba sai dai video call”.
“What! Waini wace irin hatsabibiyar yarinya ce
wannan? Nama fahimci kallon sa'aninta take mana”.
“Ka barta karka damu, zata yabama aya zaƙinta ta dai gama
mana aikinmu. Anan zata gane ko wanda ya ajiyeta a gidan
bai isa ba balle ita karamar halitta. Ni yanzu damuwata ma
shine Barbushi ya tabbar mana da wannan ranar ta sa'a,
haɗuwarmu kuma fuska da fuska wani babban cigabane
garemu.”
“Komai ya kwaɓe kam, sai dai ni a wannan gaɓar ina
masa kallon mai sauƙi. Kaga dai a yanzu bamu da isashen
lokacin komawa wajen Barbushi, na biyu barin wannan
damar ta wuce a garemu kuskure ne. Dan haka kawai mubita
a yanda take so ɗin, da sassafe mu nufi Barbushi”.
Ajiyar zuciya mai nauyi Miran Jasim ya sauke domin
gamsuwa da zancen Miran Arshaan ɗin, daga haka basu
koma masallacin ba sukai zaman kulla yanda zasu tunkari
Iffah bayan sun tura mata saƙon amincewa ayi video call ɗin.

*_10:30pm_*

Ƙarfe goma da rabi na dare agogon ƙasar Iffah zaune
gaban laptop ɗin ta, sanye take cikin suturar ta mai sirrinta
jiki, iya zagayen ƙyaƙykywar fuskarta kawai ake iya gani. Tayi
fayau ga mai kallo baka iya ganin komai sai damuwa da
tsantsar ƙuruciyarta. Cikin girmamawa ta gaida dattijan guda
biyu dake a fuskar lap-top ɗin tata. Miran Jasim da Miran
Arshaan suka amsa mata da kulawa da nuna tausayawa
tsantsa a fuskokinsu. Ita dai idanunta a rissine, dan tun kallo
ɗaya datai musu bata sake yarda ta ƙara ba.
Miran Jasim yay ƴar gyaran murya da fara magana bayan
gaisuwar tasu. “Ibnati mu mun sauke nauyin dake kammu
naki, abinda kika yanke kawai muke buƙatar ji domin tsallakar
da rayuwarki data ƴan baya. Dan a yanzu mun shirya tsaf ba
tsafi ba ko bataliyar ifiritai Eshaan zai sauke a kammu domin
danne cewarmu bazamu taɓa yin shiru ba”.
Iffah ta jinjina kai a hankali da faɗin, “Uncles naji daɗin
hakan, kuma tun farko dama haka ya kamata ku kasance, duk
da dai nasan bai zama lallai kuji irin zafin da iyayenmu sukaji
ba. Amma a yanzu daya fara taɓaku gashi kun zaburo. Duk da
haka bazamu ƙi karɓar taimakonku ba, dan a yanzu bani da
wani abu dana tsana sama da shi, a shirye nake kuma na
zama ajalinsa koda nima zan rasa nawa ranne. Sai dai ina son
dan ALLAH uncle ka faɗamin gaskiya taya ka samu wannan
videon? Ta ya kuma kasan na cikin videon nada alaƙa da ni
ne? Miyasa kuke son taimaka mini? Miyasa duk da kun san
yana kan rashin dai-dai baku taɓa wani yunƙuri ba a baya sai
yanzu?”.
Kallon juna Miran Arshaan da Miran Jasim sukai kowanne
ransa na susa da mamakin tsaurin idon wannan yarinya da
sukema kallon hatsabibiya. Amma a zahiri sai Miran Jasim
yaja ajiyar zuciya ya fesar cikin ƙoƙarin danne razanin da
tambayoyinta suke neman jefasa. “Ibnati duk wannan ai na
abin mamaki bane da har zai saka miki shakku, amma tunda
kina son sani yanzu zakiji komai. Wannan video ɗin da kike
gani na samosa ne a system ɗin Eshaan, bakuna shi kaɗai
bane ba. Akwai ire-irensa da yawa harma dana yanda aka
hallaka matansa na baya. Ina haɗasu ne domin miƙasa kotu a
kwatarma masu hakki hakkinsu duk da ina fargabar ƙarfin iko
irin na Shahan-shan bazai bari a hukunta shin ba kasancewar
komai sai da say ɗinsa ke gudana a ƙasar ruman baki ɗaya.
Sanin alaƙarki da wannan video kuwa ta samune duk a dalilin
bibiyar tasa, sai dai bamu tabbatar ke bace ba sai a ranar da
kika samesa tare da Arshaan Akh suna wasan takkubba.
Sannan kasa tunkararsa a baya Ibnati bazaki gane ba, ƙarfin
ikon Shahan-shan fa bana wasa bane ga kowa....”
“Tabbas hakane” Miran Arshaan ya amshe zancen. Batare
daya jira cewar Iffah ba ya cigaba da faɗin, “Idan baki manta
ba bayan kin basa shayi ya koma gefene yana kallo cikin
masarauta, nima kina bani kuma na koma kusa da shi ina mai
yabama tarbiyyarki da tabbatar masa yayi dace mace tagari
data dace da shi a yanzu. Buɗar bakinsa sai ya sake tsaki da
faɗin, “Tukunna dai, ai shi har yanzu matar da zai rayu da ita
bata iso ba. Naji mamaki harna tambayesa ba'asin hakan
amma sai bai tankani ba kin sanshi da girman kai. Zancen ya
tsaya min a rai nazo na sami Jasim Akh da maganar, shine fa
ya duƙufa bincike harya samu ganawa da kakanki da ke a
ƙauyen Jumna”.
Sosai Iffah ta zabura da jin sun gana da kaka harta ɗago
ido ta na kallonsu. Tabbas sihiri gaskiya ne, kuma yakanci
kowama tunda har yaci ma'aikin ALLAH. A take wani abu mai
sanyi ya dinga shiga jikin Iffah tamkar ana kwararashi cikin
jininta. Hawaye ne suka silalo a idonta ta buɗe baki a hankali
ta furta “Tabbas zan kashesa da hannuna, zan kashesa da
dafin maciji na gaskiya kamar yanda yake halaka mutane
dana tsafi. Nayi alkawarin yanda ya wargaza min ahali nima
sai na wargaza rayuwarsa..”
Miran Arshaan da Miran Jasim suka kalli juna sukai
murmushi. “Zako mu baki dukkan gudunmawar da kike
buƙata Ibnati. Tare da kariya ta musamman ga duk wanda zai
iya kawo miki hari, balle ma a yanzu abinda zakiyi sai dai ya
ƙara kawo miki ɗaukaka dan irinki ƙasar ruman ke nema. Mi
kike buƙata a yanzu?”.
Kai tsaye ta amsa da cewar, “Dafin maciji mai matuƙar
haɗari”.
“Zako ki sami na macizai ma ba maciji kawai ba. Ki saurari
saƙo zuwa safiyar gobe. Mun barki lafiya”.

Wani irin kuka mai taɓa zuciya Iffah ta saki, a hankali ta
zame takai kwance kanta da yay mata nauyi na sara mata.
Gaba ɗaya duniyar tai mata dummm bata gane komai,
burinta kawai shine ta ɓatar da Tajwar Eshaan Ibn Haysam
Abdul-majeed. Gawarsa kawai tafi bukatar gani kwance a
ƙasa fiye da komai. So take taga ahalinsa na kuka fiye da
wanda sukai a dalilin rasa ƴan uwansu saboda son kansa.
Haka ta kwana a wani irin bahagon yanayin da bazata iya
koda tunawa ba. Ita bamai barci ba ita ba ido biyu ba, ita ba
matacciya ba ita ba mai rai ba gadai tanan. Duk da tana
fashin salla ana kiran salla ta miƙe, bayi ta shiga ta tsaftace
jikinta duk da babu wani ƙazanta tattare da ita, tana ƙoƙarin
naɗe gashinta daya ɗan warware takeji kamar magana a
ƙofar ɗakin nata. Cikin shakku ta gyara rigar wankar jikinta ta
nufi ƙofa ta buɗe. Da mamaki take kallon amintacciyar
hadimarta mai suna Abal dake a durƙushe hanunta ɗauke da
ƙyakywan bowl.
Da sauri Abal takai ƙasa tana gaidata. Batare da Iffah ta
amsa ba ta ɗaga bakinta da yay mata nauyi da ƙyar tace,
“Lafiya.....?”
“Lafiya Lau ya Zawjata-almilk. Saƙone daga sashen mai
Babban ɗaki”.
Hakan ya ɗan saka Iffah a shakku da mamaki, amma sai
bakinta yay mata nauyi bata iya ta sake cewa komai ba ta
amshi tambulan ɗin mai ɗauke da sabuwar madara fara ƙal.
Idanu Iffah ta tsurama madarar wani shawa'ar shanta na
fusgarta. Amma sai ta dake ta ajiye ta da nufin sai ta gama
kimtsawa tasha ko kaɗanne kaffin ta sake komawa barci.
Harta nufi kayan data fiddo zata saka kira ya shigo wayarta.
Ruɗewa tai dan abune da bai taɓa faruwa da ita ba, kofa
sallar asubahi ba ayi ba. Kamar wadda ake ingizawa da
remote ta ɗauka wayar, ganin Miran Jasim ta amsa da tsumar
jiki tana gaisheshi kai kace yana a gabanta ne. Bai amsata ba,
sai ma umarni daya bata cikin kakkausar murya saɓanin
wadda yake mata magana da ita a baya.
“Wannan madara ce mai ɗauke da dafin macizai masu
haɗarin gaske har guda biyar, daga yanzu zuwa ƙarfe takwas
na safiya ina buƙatar jin kukan mutuwa. Kukan mutuwar
Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed nake buƙatar ji har gadon
barci na ta dalilinki”.
“An gama ranka ya daɗe”.
Iffah ta amsa da rawar murya hawaye na ciko mata ido ga
girmamawa har tana rissinawa kamar tana a gabamsa.........✍️

*_🤦ALLAH sarki Iffah baki shike yanka wuya. Kin ɗauka
niyya badan zuciyarki zata iya ba a zahiri, gashi masu babban
burin sharri zasuyi jifa da hannayenki batare da kin san illar
hakan ba a gareki._*

49


.........Tunda al'amarin nan ya faru babu wanda zai ce yaji
koda motsinsa a masarautar hatta hadiman dake zagaye da
sashen nasa. Har masu dafa abinci da amintacen hadiminsa
dakan iya ganinsa ko kai masa saƙo ma ba ganin nasa suke
ba. Abinci kuwa yanda suka shirya haka suke kwashesa.
Amma hakan baisa sun gajiya ba kasancewar aikinsu ne. Yau
ma kamar kullum sun tsaftato ko'ina sun kuma bajesa da
ƙamshi mai taɓa kuzarin mai shaƙa. Bayan an haɗa abincinsa
da duk a kwanakin nan yanda ake shiryashi haka suke zuwa
su kwashe duk suka koma hawa na uku da shine dai wajen
zamansu, sai amintacen hadiminsa da kawai ke da lasisin
zama a hawa na karshen ne yay zaman gadin abincin gudun
samun matsala duk da babu wani mahaluki a zahiri daya isa
ketowa har nan ya saka wani abin cutarwa da ake tsoro.
Kusan ƙarfe takwas abinda hadimin bai zaton gani ko
tsammani ba yay matuƙar kidimashi. Tajwar Eshaan Ibn
Haysam Abdul-majeed ne da suka kwashe kusan kwanaki
takwas batare da sanyashi a idonsu ba ke tunkaro falon cikin
takun ƙasaita da izza. Cikin rawar jiki da ruɗani hadimin ya
zube a ƙasa bakinsa har rawa yake wajen miƙa gaisuwa.
Kamar yanda ya saba kai kawai ya ɗan jinjina batare da
damuwa da hadimin ya gani ko bai gani ba ya gittashi ya
wuce. Hadimin ya ɗan lumshe ido da zuƙar daddaɗan
kamshin shugaban nasa yana mai sauke ajiyar zuciya a ƙasan
maƙoshi.
Tajwar Eshaan da baima san yanayi ba

Please Login or Register in order to submit comment