Reading Dauɗar Gora by Bilyn Abdull ce Chapter 20 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Manya-manyan littafan dake jere a
bideside drawer ɗinta data kwaso a books room ta kalla cikin
nazari har idonta ya sauka kan wanda ya kamata ta fara
dubawa. Sai da taja lalausan bargon dake a saman gadon ta
ɗan rufe kafafunta zuwa cinya ta gyara zamanta da ƙyau ta
buɗe littafin da bismillah. A nutse kuma daki-daki ta fara
nazartar littafin da ƙoƙarin dinga fahimtarsa yanda ya kamata
da irin fahimtar dai-dai nata tunanin.
Taja wani tsahon lokaci a nazartar littafin barci gwanin iya
sata ya cigaba da rinjayar idanunta. Haka badan taso ba ta
kife book ɗin a gefen ta zame ta kwanta tana hamma. Da ƙyar
ta kammala haɗa addu'ar barci......

★★..... ★.....
“Uwa komai ya rikicemun wlhy, narasa ina zan kama. Ki
taimakeni kar yaƙin dana sha a baya ya zama wahalar banza
akan cikar burina”.
Ta-kurya ce mai maganar cikin tsananin tashin hankali da
susucewa game da rashin mutuwar Iffah kamar na sauran
matan baya”.
Uwa dake hakimce duk tana saurarenta ta nisa tana mai
girgiza kanta da sake tsuke mummunar fuskarta. “Ƴar shilar
nan bata isa ja dani ba Ta-kurya, kin Sanni kin san aikina kin
kuma san mizan iyayi. Ya kamata ki nutsu tsaf akan bayanin
danai miki tun a baya. Tabbas mutuwarta zata iya zame mana
mai wahala a lokacin da muke buƙata, shiyyasa naji takaicin
suɓucewar waccan damar da muka samu a farko. Gashi kema
sakacinki yasa har zuwa yanzu kin gagara kawo mana rigar
dake sashen mai Babban ɗaki ko zamu iya kamo bakin
wancan zaren dan zuwa yanzu na fahimci akwai masu irin
manufarmu akan yarinyar kamar yanda na sanar miki. An
kuma mana karan tsaye na kaita sashen Ajlaan ta hanyar ƙin
bin dokokin kaita turakarsa, kin san kuma mu munbi
matakanne wajen ɗana tarko akan waɗan ca har mukai na
sara, sun shammacemu sun kaita ne, sai dai abinda basu sani
ba hakan bazai taba tseratar da itaba a tarkonmu na gaba da
kuma mutuwarta”
“Uwa ba sakaci bane, a yanzu haka hadimar dana saka
wannan aikin tana gab da kammala min shi. Ni yanzu tashin
hankalina shine cikar lokacin kalmashe bakin zaren burina na
biyu dake ƙara nisa. Har yanzu da buƙatar cikamakon aikin fa
kafin na tsallaka na uku da shine cikar gaba ɗayan nasarata
akan wannan yaƙin. Uwa ya kamata kiyi wani abu. Idan ita
wannan yarinyar mutuwar tata bazai yuwu ba ta wannan silar
inaga mu ajiye batunta gefe a haɗe wannan bakin zaren”.
“Kema kinzo da magana mai ƙyau kam ta ƙurya. Kuma
inaganin ya kamata cikin Zawjata-almilk biyu da suka rage
ɗaya zata zama cikamakin ayyukanmu na biyu. Kinga sai mu
haɗa aikinmu na uku dana ƴar shilar sudan can, amma duk da
haka a kwana bakwai da zatai bazamu daina gwada sa'ar mu
ba dai”.
“Haka shine dai-dai uwa mai share kukan masu kuka.
Madubin rayuwar duk wani mai buƙatar kallon ƙarshen
ƙyawun nasararsa.”
“Nasara takice Ta-kurya tunda har kina tare damu. Sai dai
maganar yarinyar can dole ki haɗa da kirsa a yanzu kamar
yanda kika saba wajen nasarar haɗa dukkan auren Ajlaan ta
hanyar mai Babban ɗaki a yanda kika so. Ki kusanta kanki da
yarinyar itama sosai”.
“Indai wannan ne angama Uwa”.
“Na barki lafiya”.
Uwa ta faɗa tana mai ɓacema ganinta a sannu-sannu harta
daina ganinta. Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke ranta duk
babu daɗi. Dan zuciyarta kam ta fara ayyana mata ƙarfin ikon
uwa ya fara sanyi. Dole ne ta nema sabon mai taimakonta
duk da bazata taɓa mantawa da gudunmawar da uwa ta bata
ba harta kawo wannan matsayin a wannan daula ta ruman da
ayanzu take kamar mai juyata ta ƙarƙashin ƙasa da zahiri a
yanda take so. Amma ga karamar yarinya da bata wuce
kiyashin da take murjewa a ƙasan tsinin takalminta batare
data sani ba tana neman zamewa rayuwarta wata
ƙadangaren bakin tulu a gabar cikar babban burinta na
ƙarshe......

★★★..... ★★.... ★....
A ɗan firgice Iffah da kiran sallar asubahi ya farkar take
kallon kanta da inda take a yanzu. Cikin shiga razani mai ban
tsoro ta diro a gadon daya kasance saɓanin inda ta kwanta a
daren na jiya. Kamar wadda ake ingizawa ta fice a ɗakin cikin
sassarfa. Tabbas sashen Tajwar Eshaan ne dai take. “Taya
haka zata kasance?”. Ta faɗa cikin bugun zuciya. Sai kuma ta
fara tunanin kodai mafarki take yine. Hannu takai ta ɗan mari
fuskarta. Sai dai babu abinda ya canja daga wanda idonta ke
gane mata a yanzu. Dan lallai da gaske a sashen Shahan-shan
ɗin dai take.
“Ya ALLAH mike faruwa da ni ne haka wai. Taya zan
kwanta a sashen da ba wannan ba na kuma buɗe ido na
gannni? Jiya an ɗaukeni daga ƙasa an maida saman gado na
share, amma shine yau kuma za'a ɗakkoni daga wani sashe
zuwa wani daban. Anya ba matsafan gidan nan ke son min
wasa da hankali na ba?”.
Wannan tunani na karshe ya sata saurin kama rigarta ta
shinshina. Tabbas irin dai ƙamshin turaren jiya ne da karfinsa
harya danne nata. “Ya Arrahaman” ta sake faɗa tana mai
juyawa ta shiga kallon ɗakin da sauri. A kan tarin kayan
turarruka da idonta ya sauka a kai ta nufa, ta buɗe gilashin da
suke ciki kamar dai nacan ɗakin ta fara shinshinasu ɗaya
bayan ɗaya. Sai dai abin mamaki babu wanda ƙamshinsa yay
kama da wanda takeji a jikinta. (Dole ne ma na gano, kuma ta
wannan ƙamshin insha ALLAH). Ta ayyana a zuciyarta cike da
alwashin hakan. Alwala taje ta dauro jin makara na neman
riskarta. Bayan ta idarne kuma ta sake nutsuwa wajen
ƙarema ɗakin kallo yanda ya kamata. sai yanzu ma ta gane ba
inda ta kwana a jiya bane wani ne daban. Sai dai shima
wannan ɗin ya matuƙar haɗuwa fiye ma da wancan ɗin.
Saɓanin wancan da tsarin komai na cikinsa ke fari anan kuwa
komai blue ne, ga wani ƙamshi na fitina na tashi kamar dai
wancan. Abu mafi ban mamaki nan ɗin dai duk da ya nuna
ana tsaftaceshi a hargitse yake kamar anyi dambe a cikinsa.
Ita kanta dama a shigarsa toilet har mamakin yanda taga
kanta a birkice tai, dan tasan dai tsaf ta kwanta kuma bata
buge-buge a barcin. Son yin salla a kan lokaci ya sakata bata
maida hankali ba sai yanzu data idar ta samu nutsuwa. Tayi
tunanin gyara ɗakin da fita binciken turaren nan na jikinta da
alama ya tabbatar mata mai shi ke son wasa da tunaninta, sai
dai wata zuciyarta ta bata shawarar ajiye waɗan nan batun ta
sake kwanciya irin ta jiya tai likimo kozata samu bakin zaren
ta hanyar shigowar wanda take zargin kamar jiya. Ta gamsu
da hakan tako kwanta, sai dai tsahon kusan awa ɗaya babu
wani wanda ya zo ɗakin, babu ma alamar wani ɗin zai zo
harta tashi akan dole ta kimtsa ɗakin ta shiga wanka. Kayan
data samu a lokacin gyaran ɗakin ta sanya babu ko ɗar a
ranta. Tayi ƙyau sosai, ta kuma sake baza turarurrukansa a
jikinta kamar jiya sannan ta fice a sannan kusan ƙarfe bakwai
da rabi...

Da ƙyar yau ma ta iya gano ɗakin data kwana a shekaran
jiya, cikin Sa'a kuma ta samesa a buɗe. Shiga tai da sallama
duk da bata zaton samun kowa a ciki. Tsaf yake kamar batai
bidiri cikinsa ba jiya, an canja zanin gadon ga kamshi na tashi
mai daɗi da sanyin ac. A yanda hadiman suka nuna sun ɗan yi
shock da ganinta ya ɗan sakata a mamaki, amma sai ta dake
babu alamar hakan gareta ta nufi ɗaya daga cikin kujerun
falon tai zaman ƙasaita da ita kanta bata farga da yinsa.
Hadiman da duk ganinta ya sakasu a firgici suka iso gabanta
suka zube domin miƙa gaisuwa. Rayukansu kam cike da
mamaki dan kowa dai yasan a jiya ba sashen ta kwana ba, tun
fitar yamma da tai bata sake dawowa ba har suka rufe waje
suka kwanta. Tun bayan idar da salla asuba kuma suka fito
balle suce koda safen nan ta dawo.
A fisge ta amsa gaisuwarsu tana mai sauke manyan
fararen idanunta akan ƙyaƙyƙywan tray ɗin dake ajiye a table
ɗin gaban kujerar data zauna a jiya wadda koda ba'a faɗa
mata matsayin kujerar ba tasan ta zaman Shahan-shan ce.
Ɗan juyiwa tai ta dubi hadiman da har sun fara miƙewa. Ta
jeho musu tambaya da faɗin,
“Wannan fa?”.
Cikin sauri mai sanye da kayan kuku ta amsa da “Shayi na
farko da Shugaba ke sha bayan gama motsa jiki”...
“Kayan haɗin sa?”.
Ta tambaya a takaice. Nanma da tsumar jiki ta lissafa mata.
Iffah ta yamutsa fuska da sake harɗe ƙafafu. “A canja minsu
da tatattun kayan itatuwa da ganyen koren shayi”.
Cikin tsoro duk suka dubeta, ta sake tsuke fuska da musu
alamar gargaɗi da hannunta. Kamar ƙyaftawar ido kukun ta
ɓace a wajen. Cikin abinda bai fi mintuna goma sha biyu ba
aka dawo da wani sabon haɗin shayin. Miƙewa Iffah tai da
nuna hanya alamar ta kaita inda yake. Anan ma ba karamin
tsoro bane ya bayyana a idanun hadimar har ma da sauran
ƴan uwanta, amma tsayayyun idanunta masu ƙarfi fiye da
girman shekarunta ya hana hadimar iya furtawa a baki. Kai
tsaye hanyar dake acan gefe ta nufa, sai dai suna zuwa ta
dubi Iffah a mariraice sai kuma ta duƙar da kai.
“Tsahon rai da amincin UBANGIJI su zama kariya ga
Zawjata-almilk, wlhy bani da hurumin tsallake wannan
iyakar”.
(Kinyi mai wuyar) cewar Iffah a zuciya. A zahiri kam hannu
ta miƙa ta amshi tray ɗin batare da tace uffan ba. Cikin rawar
jiki hadimar ta buɗe mata ƙofar gilashin dake a wajen, Iffah ta
ɗan tsirama steps na bene daya bayyana alamar shi zatabi
kusan na sakan ashirin kafin ta maida ga hadimar da kanta ke
duƙe, “Zaki iya komawa bakin aikinki”.
Kamar dama umarnin take jira, cike da sassarfa tabar
wajen ƙwaƙwalwarta fal mamakin wannan baiwa har zufa na
taruwa a goshinta.

★Ba karamin sake jinjinama al'amarin wannan masarauta
Iffah tai ba, dan tana ɗaura kafarta a step na farko na'ura ta
fara shelanta kasancewarta a wajen. Abu mafi bata mamakin
kalmar sunan da na'urar ta ambaceta da shi. Kafin ta sami
damar wani waige-waige lifter data kwasota ta direta a wata
ƙofar da hadimai biyu ke tsaye hannunsu riƙe da manyan
bindugu. Tayi mamakin ganin yanda suka rissinar da kawuna
sunka fara gaisheta. (Shin sun yarda da zancen na'urar ne?
Kokuwa sun santa a matsayin Zawjata-almilk ɗin ne dama?).
Da wannan tambayar da babu mai bata amsa ta cigaba da
takawa a hankali kasancewar sun buɗe mata ƙofar wajen.
Iska mai daɗi dake busawa ta sanyin safiya ta fara cin karo, ta
zuƙa a hankali tana mai lumshe idanunta. Sai kuma ta buɗesu
a sannu, a lokaci ɗaya bugawar zuciya da tsinkewar jini suka
nema sarƙe numfashinta, neman daburcewa take sakamakon
abinda tai tozali da shi. Babu shiri ta maida idanunta ta
rumtse tana mai ambaton sunan ALLAH akan wannan
mummunan gani da tai. To mummunan gani mana, dan
tunda take a rayuwarta bata taɓa tozali da namiji a irin
wannan yanayin da idonta ya gane mata ba.. Ji take kawai ta
zura da gudu ta koma, sai dai hadiman dake bayanta fa?
Wane irin kallo zasu mata bayan na'ura ta gama fallasata a
garesu. Tabbas nuna gazawarta na nufin faɗuwarta,
faɗuwarta a matakin farko kuwa na nufin rushewar gaba
ɗaya nasararta.
Da karfi taja numfashi mai kauri ta haɗiye, kamar zatai
kuka ta sake buɗe idanun a hankali, sai dai koda wasa bata
yarda ta kalla gaban nata ba.....

Shigar ƙamshin turarensa da bayan shi babu wani mai
irinsa da sautin takun takalman ƙafarta ya sashi juya
sharɓeɓen takobin dake a hanunsa cike da gwanancewa ya
karci ƙasa ya gocema Aamin nasa da suke wasan tare ya
juyashi zuwa hannunsa na haggu saɓanin na dama sai gashi
akan wuyan Iffah da numfashinta yay wata irin mummunan
fisga.
“Who are yo.....?”.
Yay yunƙurin faɗa cikin alamun bayyanar fushi mai haɗi da
isa da ƙasaita, sai dai kalmar ta gagara ƙarasa fita a harshen
nasa dalilin tozali da abinda bashi yay tsammanin gani ba.
Tar-tar fuskokinsu suka bayyana akan takobin mai matuƙar
ƙyalli da sheƙi da kai tsaye za'a iya kiranta faɗama jini na
wuce........✍️

40


..........Tsam Iffah ta ƙara damƙe trayn hanunta jin rawar
jikinta na neman fitowa, “Barka da safiya ranka ya daɗe”. Ta
faɗa cikin ƙarfin hali da jarumtar saka idanunta cikin tsakkiyar
nasa da ke tsaye a kanta har yanzu ƙyam. Sai dai duk
ƙwaƙwƙwafin mutum bazai iya gane abinda ke a cikinsu ba
balle akan fuskarsa mai cike da gizago akoda yaushe. Ganin
bai amsa ba, bai kuma daina kallon tsakkiyar idanunta da
ayanzu take ƙoƙarin janyewa a nasa ba, bai kuma janye
takobin da kallonta kawai zai iya tada tsigar jikin mutum daga
wuyanta ba ya sata ɗan shammatarsa ta goce makoshinta da
ga tsinin takobin daya ɗaura matan, sai dai a yanda ya wani
lumshe idanu da sauke takobin yasata tabbatar da ya bartane
kawai. Gaba tai yunƙurin yi, da yima hadiman da suka iso
wajen yanzu nan kallon gefen ido a kaikaice ta saki wani
lallausan murmushi mai ma'anoni da yawa a zahiri. A kuma
ƙasan ranta ko ɗar babu.
Duk wannan abun Miran Arshaan fa na tsaye a wajen ne
yana ƙarema Iffah kallo a kaikaice cike da mamakin ƙarfin
halin yarinyar, dan tunda yake a wannan masarauta bayan shi
babu wani mahaluki daya taɓa zuwa wannan wajen sai
Shahan-shan da hadiman dake kula da wajen. Amma a yau
sai ga yarinya ƙarama da babu alamar tsoro a cikin idanunta a
wajen. Sai kuma yanda tayi kamar bata gansa ba yay matuƙar
ƙona masa rai amma ya dake dan yana buƙatar ganin ƙarshen
wasan....

Wajen duk da filine na karshen ginin (rufinsa kenan) ya
ƙawatu da abubuwa kashi-kashi na more rayuwa. Ga wani
ƙamashin furanni da aka ƙawata waje dana fresh air masu
narkar da jinin mutum da sanya kasala. Da sauri ɗaya daga
cikin hadiman da suka shigo wajen da abubuwa a hanunsu ya
ƙarasa ga Tajwar Eshaan dake murza goshinsa kansa a ɗan
rissine ƙasa. A gabansa ya dirƙushe yana mai miƙa masa
kufan takobin hanunsa da babu tantama anyi adon jikinsa da
gold ne. Takobin ya ɗaura masa kan dogon trayn da kufan
yake. Hadimin ya miƙe da sauri yana ja da baya. Na biyu ya
iso da sauri shima, sai dai saɓanin na farko shi bayansa ya
koma yana warware farar rigar hanunsa mai maɗauri.
Hannayensa ya ware da ɗan kai idanunsa inda Iffah ke tsaye
tana tsiyaya shayi a karamin kofi, ya wani irin ɗage kafaɗu da
juya rigar cike da salo ta rufe jikinsa tare da zarge igiyoyin
biyu akan damammen cikinsa. Hadimi na uku ya iso shima ya
durƙushe hanunsa dauke da ƙaramin farin towel. Nan ma dai
ɗauka yay ya rataya a kafaɗa bayan ya ɗan tsane zufan daya
taru masa a gefen wuya da goshi alamar dai jininsa a tsinke
yake a lokacin.
A yanda hadiman suka sani daga haka hanyar da zata
maidashi bedroom ɗin daya kwana yake bi, acan zai samu
shayinsa na ƙa'ida mai dafawa ta kai, bayan yasha zai shiga
wanka kafin ya fito inda aka shirya masa karin kummalo. Sai
dai saɓanin yau yana ɗaga ƙafa domin barin wajen bayan ya
dubi Aamin nasa ya rissinar da kai kaɗan na alamar sallama
da girmamawa a garesa Iffah dake faman baza ƙamshin da ga
Shahan-shan ɗin kawai suka sansa ta isowa wajen ɗauke da
ƙaramin kofin shayi dake tururi fari tar na glass.
Da sauri duk hadiman suka juya bayansu, dan kallon
abinda zai iya biyo bayan wanda suka gani ɗin haramunne a
garesu. Iffah dake taku a nutse kamar wata hawainiya
takalmanta da ba wani tsinin kirkine da su ba na bada sautin
isar da saƙon tahowar tata ta iso gabansa.. Ƙin yarda tai koda
wasa su haɗa idanu. Idanunsa da kallonsu ke canjawa ya
sauke akan kofin shayin da take miƙo masan. Shiru babu
alamar zai amsa, har hanunta na ƙoƙarin fara yin dayi. Sai da
ta fara ambatar sunan ALLAH kafin ta ɗago fuskarta a dake,
“Ƙin sha na nufin rauni da muhimmancin Zawjata-almilk a
gareka. Ko kuwa cigaba da tabbatarma duniya abinda suka
sani shine gaskiya ranka ya daɗe”.
Yanda lips ɗinta da suka sha pink lipstick ke motsawa ya
zubama ido, sai dai maimakon mata sharhi akan zancenta
kamar yanda taso yau gefe ya ɗan maida kansa da amsar
shayin kamar wanda ya shiga halin tarkon kasala. Karan farko
ta sakar masa wani lallausan murmushi da faɗin, “Thanks”.
Basarwa yay ta hanyar ɗan duban gefensa a takaice ya
furta,
“Aami”.
Da sauri Iffah ta duba wajen tamkar sai yanzu ne taga Miran
Arshaan ɗin, “Ya salam”. Ta faɗa a zahiri da nufarsa ta zube
ƙasa domin miƙa gaisuwa a garesa. Ya ɗan murmusa
zuciyarsa taf da al'ajabin wannan figigiyar yarinya da da
auren wuri yayi ya haifa wanda suka fita nesa ba kusa ba.
Cike da salonsa na fuska biyu ya amsa yana mai ƙare mata
kallo ta ƙasan ido. Iffah daba kula da hakan tai ba cike da
girmamawa ta miƙe da faɗin, “Uncle bara a baka shayin
kaima”.
“Zan so kasanwa na farko da zai ci abu daga hanunki
Ibnati”.
Jin daɗin kalamansa yasa Iffah sakin murmushi da ɗan
rissinawa ta furta, “Na gode Aam”. Shima dai shayin ta kawo
masa, nan ma yay mata godiya da sanya albarka yana ɗan
duban sashen da Tajwar yake tsaye dafe da ƙarfen da aka
zagaye wajen ta bakin ginin yake ya tsurama cikin masarautar
idanu yana ɗan kai shayin bakinsa tamkar bai san abinda ke
gudana a wajen ba. A hankali ya taka inda yake shima yana
shan nasa.
“Yanzu ne daular ruman ta tabbatar da samuwar Zawjata-
almilk”.
Sarai Tajwar Eshaan ya jisa. Amma halinsa na ƙasaita da
mafi yawan iyayen nasa suke ambato da girman kai yasa yay
tamkar baiji ɗin ba. Sai ma juyawa da yay bayan wasu sakkani
ya dubi Aamin nasa cikin tausasashiyar muryarsa mara
hayaniya da kamewa ya furta. “A huta gajiya”. Ya bar wajen.
Ga mamakin duk wanda ke'a wajen gaban Iffah dake ɗan
nisa da su ya isa. A bazata taji tattausan tafin hanunsa da yay
sanyi ƙalau sakamakon iskar wajen a cikin nata. Da sauri ta
rumtse idanu tana mai ambaton sunan ALLAH a zuciyarta da
ɗan dubamsa. Ba ita yake kallo ba, sai ma fara takawar da yay
wanda ya tilastata binsa tamkar raƙumi da akala. Batare da
sun luraba takun sawayensu na sauka da ɗagawa a tare
sakamakon shima tafiyar izza da ƙasaita irin na masu mulki
yasa baida garaje a tafiya tamkar wani mace. Anan ɗin ma dai
tana sanya ƙafarta na'ura ta sanar da ita wacece, haka shima.
Da sauri hadimin dake a ƙofar ya zube yana kwasar gaisuwa.
Hannu kawai ya ɗaga masa yay gaba abinsa har lokacin
hannunsa na cikin nata ya riƙe gam kamar wanda aka bama
amanar riƙon nata dan karta suɓuce......

★★..... ★★......

A ɓangaren Barrister kamar yanda mutanen can suka sanar
masa hakance ta faru. Sunyi amfani da kamannin da mutane
suka daɗe da sanin sunayi, wanda shine ma tushen
zamowarsu abokai, aikinsu kuma ya maidasu aminai. Sai dai
muryarsu ta banbanta da wasu abubuwa na ɗi'ar yau da
kullum. Akan wannan ne mutanen suka bashi training na dole
dalilin barazana da sukai masa akan iyalinsa dama kashe
Barrister Akeem ɗin da yake gudun cin amana. Bayan
kimtsawarsa da shiga irin ta Barrister Akeem da bashi wasu
bayanai akan aikin da zai musun suka bashi key ɗin motar
Barrister Akeem. Sun sanar masa dukkan motsinsa akan
idonsu ne, kuskure ɗaya akan ganganci fansar rayuwar ɗaya
daga cikin ahalinsa ne kona Barrister Akeem. Dole Barrister
ya kwantar da hankalinsa dan ya fahimci mutanen sunfi
ƙarfinsa, gashi koba komai yana buƙatar kuɓuta kodan tarin
ayyukan dake gabansa musamman akan aikin da ayanzu ya
tasa a gaba da alƙawarin cika alƙawari.
Su da kansu suka bashi address ɗin inda zaije, yayinda ya
hau titi kuma sai ya fahimci suna biye da shi a mashina wasu
a mota. Ya ɗan rumtse idanu da jan kakkauran numfashi ya
fesar lokacin da ya gama dai-daita parking a inda suka
umarcesa zuwa. Sai da ya karanto addu'ar neman ɗauki ga
ALLAH sannan ya fito riƙe da brefcase ɗin Barrister Akeem a
hannu. Ƙaton gidan ya ɗan ƙarema kallo kafin ya nufi inda
suke sanar masa yabi ta hanyar bluetooth ɗin kunnensa.
Kansa kawai yaɗan gyaɗa tamkar yana gabansu ya nufi
ƙofar......

★★★....... ★★.....

A cikin masarauta kam kusan ƙarfe tara da wasu mintuna
labari mai razanarwa na rashin ganin Sayeed Khairul-Bashar
(Aami gasu Miran Arshaan. Kaka kuma ga Tajwar Eshaan.
Shine wanda yay maganar jiya a ɗakin tattaunawa bayan
tashin Tajwar Eshaan). Zancen rashin ganin nasa ya fito ne
daga iyalansa, da farko an ɗauka yana cikin masarautar ne
dan sun tabbatar daga sallar asuba bai dawo ba. Amma ganin
har lokacin shigarsa gida ya wuce ƴaƴansa kuma sun bincika a
inda suke tunanin ganinsa amma babu shi sai suka fitar da
maganar. A take sojojin gidan masu bada tsaro dama hadimai
suka bazu lungu da saƙo amma babu alamar hakan. Anbi
diddigin wasu daga cikin cctv footage amma fitowarsa kawai
aka gani daga sashen nasa babu komawarsa. Hakan ya
matuƙar bama kowa mamaki da ɗaure kai. Dan ta ko'ina
masu tsaron ƙofofi sun tabbatar basuga fitarsaba sukam.
Gashi kuma an duba lungu da saƙo na gidan amma babu wata
alamarsa.....

★★......

Lokacin da labarin rashin ganin Sayeed Khairul-Bashar ya
iso kunnen Miran Jasim da Miran Arshaan dake tare kallon
juna sukai, sai kuma duk suka kauda kawuna suna murmushi.
Cikin son basar da zancen Miran Jasim ya cigaba da magana
kan zancen da Miran Arshaan ya kawo masa dangane da Iffah
“Lallai wannan yarinyar hatsabibiya ce, aini tun isowar
labarin kasancewarta raye a safiyar jiya al'amarin ta kemun
kai kawo. Zancen ka na yanzu kuma ya sake tabbatar min da
shirinta ta shigo masarautar nan.”
“To ai ta tara ta samu, dan dama mu irinta muke nema”.
Cewar Miran Arshaan yana ɗan murmushi.
Miran Jasim ya jinjina kai shima yana murmushin nasa na
izza da ƙasaita. “Hakane kam ta kawo kanta inda ake jirace da
zuwanta. Dan kam zamu sauke ƙuruciyar dake izata a tunanin
yin rawa da bazarta dake ɗawainiya da ita. Zata ƙarasa mana
aikinmu cikin sauƙi batare da ita kanta tasan a cikin tarko
take ba”.
Nan ma murmushi Miran Arshaan yay idonsa akan ɗan
uwan nasa. “Zuwa yaushe aikinmu zai fara?”.
Miran Jasim ya ɗan ɗage kafaɗa da taɓe baki. “Bazai
ɗauka lokaci ba. Sai dai muna bukatar wani point ne dole”.
“Wanda yake hannunmu fa?”.
Cewar Miran Arshaan da mamaki.
“Kai wannan bashi da wani ƙarfin da zaiyi tasiri ita a
gareta, duk da dai zai iya zama kamar share mana fage ne.
Zaren da nake ganin zamu ja ya kaimu gareta ɗaya ne, duk da
dai har yanzu babu wani shaida dangane da tsallakewarta
itama. Amma zamu yi amfani da damar, a wannan karonma
matarka ce zata mana aikin”.
“A wannan gaɓar fa ya kamata mu canja salo, Jasrah nada
matuƙar wayo, kar yawan bugar cikinta fa yasa ta fara
fahimtar wani abu”.
“Sai idan kaine ka bada ƙofar hakan Arshaan. Shekara nawa
muna amfani da itan bata fahimtaba sai yanzu. Ka dai kawai
ka kasance mai lura”.
Kai kawai Miran Arshaan ya jinjina batare daya ce komai
ba......

★★★......

Suna yin ɗan nesa kaɗan da masu tsaron ƙofar Iffah ta zare
hannunta da sauri tana ɓata fuska. Bai ko juyo ya kalleta ba
balle ya nuna alamar yasan mitayi yay gaba abinsa cikin
takunsa na nutsuwa da tsantsar ƙasaita tamkar baya son taka
kafafun nasa. Da ƴar hararar ƙasan ido ta bisa tana ƙunƙuni a
zuciyarta. (A haka dai kamar na wani limamin masallacin
Saudiyya, sai dai zuciyar ko kafiran farkon ƙarni haka suka
gansa suka barsa. Wanda duk zai iya salwantar da rai yay
barci lafiya babu ko ɗar ai ya dace ka kirasa da duk sunan
daya zo maka a rai dan ya cancanci haka). “Ni zanyi
maganinka da izinin ALLAH”. Ta faɗa a zahiri fuskarta na nuna
gaskiyar ɗacin da zuciyarta ke mata.......✍️
41
.......Shiru yay yana kallon inda ya saba iske shayinsa, wayam
babu komai, ya kai zaune a kujerar cikin alamun gajiyawa, a
gefe kuma tsaurin idon yarinyar da ƙarfin halinta na masa
kaikawo. Shan wannan shayin ya zame masa jiki da in bai sha
ɗin ba sam bama yajin daɗi, har ma yakan tsinta kansa a wani
yanayi da shi kaɗai ya barma kansa matsayin sirri duk da
abun na matuƙar damunsa. Har yayi yunƙurin dauriyar
sharewa tunda ya ɗan sha wani amma jin abinda yake gudun
na taso masa ya sashi furzar da zazzafar iska, babu shiri ya
danna alerm ɗin dake isar da saƙon kira ga amintattun
hadimansa. Cikin mintunan da basu wuce uku ba ko sai ga
ɗaya daga cikin su ya iso. A gabansa ya zube cikin tsumar jiki
yana mai ambaton...
“ALLAH ya ƙara ma Shugabana tsahon rai da ingantacciyar
lafiya, umarninka shine abin jirana”.
A zuciya ya amsa da Amin, a zahiri kam babu alamar zai
tanka kamarma bashi ya bukaci ganin hadimin ba. Tsahon
mintuna uku ƙasaita da izza irinta saraki na dawainiya

Please Login or Register in order to submit comment