Reading Dauɗar Gora by Bilyn Abdull ce Chapter 25 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a hankali ya kai
zaune cikin kujera ya harɗe ƙafafu cikin salon zama irin na
sarakan da suka isa. Sai a lokacin hadimin ya zaburo ya sake
zubewa gabansa.
“Ya shugabana ko ana bukatar shayi?”.
Kansa kawai ya ɗan jinjina alamar eh yana kauda fuskar sa
gefe. Da sauri hadimin da ke satar kallonsa ta gefen ido ya
miƙe, haɗaɗɗen daning table ɗin mai cike da kayan breakfast
ya nufa, cikin abinda baifi mintuna biyu ba ya dawo ɗauke da
ƙaramin tray da butar shayi a samansa. A ɗan tebirin gaban
kukerar da yake zaune ya ajiye. Ya tsiyaya shayin a ƙaramin
kofin. Baya yaja sosai kansa a ƙasa cikin ƙanƙan da kai yace,
“An kammala ya shugabana”.
Baiyi magana ba, bai kuma motsa ba har bayan wasu
mintunan biyu. Bayan ya kai shayin bakinsa kusan sau biyu ya
ɗan dubi hadimin dake tsaye kai a risine ya sake kauda kai.
Maganace a bakinsa, amma sai da ya sake jan wasu sakkani
kafin ya furta ta a fisge.
“Mike faruwa a daular ruman?”.
Tambaya mafi rikitarwa, mamaki, al'ajabi harma da ruɗaki
ga duk wanda ya jita a bakin da ba'ayi tunani ko tsammani ba
ce ta riski hadimin. Falon ya shiga waw-wai-gawa cikin tsumar
jiki. Tabbas shine dai akaima tambayar ba wani ba. Sai duk ya
sake ruɗewa ba shiri ya zube ƙasa akan guyawunsa. “Kariyar
UBANGIJI da ingantacciyar lafiya su kasance ga shugabana,
abubuwa da yawa sun faru marasa daɗin faɗi da sauraren ji.
Sai dai ban san wanne ake bukatar na isar ba”.
Tamkar ma bashine ya buƙaci jin ba, tsahon wasu
mintuna da zasu iya kai huɗu ya sake amsawa ciki-ciki.
“Komai”.
Kai hadimin ya jinjina yana mai sake ƙan-ƙan da kai, ya fara
zayyano komai tiryan-tiryan tun daga randa aka ɗauke Iffah
sashen har zuwa yau ɗin nan da yake gabansa. Ya kare da
faɗin, “Idan na faɗi abinda ba shi shugabana ke buƙatar ji ba
ina mai neman afuwa”.
Idan gunki ya motsa bayan ƙare abinda ya buƙaci ji to ya
motsa. Hadimin dama dai baya tsammanin samun sharhi ko
tambaya ko fashin baƙi daga abinda ya faɗa, dan haka yaja
bakinsa yay shiru yana ɗan satar kallonsa ta gefen ido. Ba yau
ya fara ganin Tajwar Eshaan ɗin ya danna wani abu a gefen
kujerar da yake zama computer ta bayyana ba kamar yanda
yayi a yanzu, sai dai a iya hasashensa da dube-dube idan yana
gyaran saman ya kasa gano komai......
★★... KAUYEN JUMNA ★★

Hukuncin da kaka ya yanke, sakamakon tashin hankalin da
suka kwana a ciki shi da Ummu da Iyyani tun da sassafe suka
fito da nufin komawa gidan Babiy na daular ruman gaba
ɗayansu. Kaka ya gama shirya tunkarar kowa gaba-da-gaba a
yanzu, dan haka babu ko ɗar tattare da shi. Saurayin nan na
kwanaki dake ƙoƙarin shigowa layin gidansu yay saurin taka
birki idanunsa a kansu. Tabbatar da su ɗinne dai ke tafe a
ƙafa ya sashi ɗaukar wayarsa da sauri-sauri ya latso wata
lamba. Sai da tana gab da tsinkewa aka ɗaga, da ƙyar ya iya
haɗa haruffan sallama bai jira an amsa masa ba ya ɗora da
faɗin, “Oga abin mamaki gasu nan suna fitowa da alama ma
garin zasu bari”.
“Woow interesting”.
Aka faɗa daga can cikin nuna ci da birgewa. Sai kuma aka
ɗora da faɗin, “Maza ka juya ka koma kan ainahin hanya kafin
su isa. Ka tabbatar nan da mintunan da basu wuce hamsin ba
na gansu a gabana”.
“An gama boss”.
Saurayin ya faɗa da tsantsar girmamawa. Sam su Kaka dake
tafiya hankalinsu bai kai kan motarba saboda Ummu dake
tafiya a wahale, idan ma ta taka ɗaya biyu sai sun tsaya ta
huta kafin su cigaba. Yayi jira na kusan mintuna goma sha
ɗaya kafin su iso inda tuni ya iso shi yay fakin. Da sauri ya fito
daga lungun daya laɓe hanunsa riƙe da leda yana ɗan cillawa
yana ƴar wakarsa. Kamar wani shiri sai ko idon Kaka dake ma
Ummu nasiha ta daure su ƙarasa akan wannan saurayi. Yay
ɗan jimm alamar shan jinin jiki, sai kuma ganin yanda
saurayin ya gittasu babu alamar ya gansa ya sashi zabura.
“Ƴan samari na ce ba...?”
Kamar saurayin bazai kula ba sai kuma ya juyo a ɗan yatsine
yana faɗin, “Kace mi....?” sai kuma ya ƙi ƙarasawa da nuna
alamar shock kamar gaske. “Ya ALLAHU wa nake gaji haka
kamar Baba?”. Kaka ya sauke ajiyar zuciya da jin shakkunsa
gaba ɗaya ya gudu yay ɗan murmushi. “Kaga ja'iri ni ne ɗin
dai, yaushe haka a gari babu labari?”. Kai a sunkuye saurayin
ya shafa ƙeya yana murmushi. “Afuwa kaka uziri ne ya ciyoni
har nai ƙudirin shallakeku a karo na biyu batare dana leƙa ba.
Yanzu haka ma nan jirana ake saƙo na amsa anan ɗin fatana
na kai Dahab (Daular ruman) kafin cikar awa ɗaya da rabi”.
Cikin jin daɗi Kaka yace, “Kai Alhamdullah da wannan
zance. Ka ganmu muma can ɗin muka nufa a she da rabon ba
sai mun sha wahala ba na jiran mota ma”.
Saurayin ya ɗago irin da mamakin nan, irin sai yanzu ya
lura da su iyyanin nan. Gaishesu ya fara da ban haƙurin bai
lura da su ba ne wai. Iyyani ta amsa masa da kulawa tana
faɗin babu komai.
“Idan hakane Baba ai ku shiga kawai mu wuce,
gaisuwar ma a karasata a hanya”.
“Af, e to kaima kayi zance na gaskiya. Amma ai zamu
dakushe maka uzrinka”.
“Ai babu komai baba, sahun giwa ya isa take na
raƙumi”.
Fuskokinsu ɗauke da murmushi duk suka shiga, Iyyani da
Ummu a baya. Kaka ya shiga ta gefensa. Sai da ya tabbatar
sun hau hanya ya gyara zaman norse mask ɗin fuskarsa da
ƙyau, handkherciff ɗin gefensa ya matsar jikin ac kamar zai
goge ya danna ac'n motar ya ƙure. A take ya busa tare abinda
ke jikin handkherciff ɗin gasu Iyyani da kaka suka shaƙa har
suna sakin ajiyar zukata kusan a jere. Kashewa yay da sauri
yana faɗin, “Af kajini da karambani zansa Baba mura”.
Nauyin da kawunansu ya fara musu ya hanasu damar
magana duk suka dafe kai kusan a tare, kaka ne ke ƙarfin
halin cewa wani abu amma ya kasa, su Ummu kam tuni sunyi
luuu jikin kujera alamar barci ya bugar da su. Kakan ma yay
luuu a tasa kujerar. Nannauyan numfashi saurayin ya sauke
da ɗan juyawa ya dubesu ta mirror. Tabbatar da sun suma
yanda yake buƙata ya sashi janye Norse mask ɗin fuskasa da
sakin murmushi ya latse wayarsa. Ana ɗagawa bai jira komai
ba ya furta, “Done! boss”.
“Proud of you”.
Aka bashi amsa a taƙaice da ga can da latse wayar......

(Ta faru ta ƙare)😱

★★.... ★★.... ★★.....

Tajwar Eshaan da bai sake bi takan hadimin ba kam
hankalinsa gaba ɗaya ya tattara ne ga computer ɗin gabansa
a yanda yake harɗe. Cikin nutsuwa yake sarrafata a take
saƙonnin da yake buƙatar gani suka bayyana kansu. Hannu ya
kai ya sake daidaita gilashin idanunsa da ɗan yamutsa fuska
ganin dogon text message ɗin daya buɗo... Dai-dai nan
takunta da ƙyamshin sassanyan turarenta ya fara rige-rigen
isowa hancinsa tun kafin bayyanarta. Wani irin harbawa daya
tilastashi ɗaga ƙwayoyin idanunsa kaɗan ta cikin gilashin yay
sai ko suka sauka akanta. Sanye take cikin shirinta da baza'a
kirasa mai matuƙar ƙawa ba, ba kuma mai ƙasƙantarwa ba.
Babu ko ɗigon kwalliya a fuskarta, ƙamshin turarenta ma a
yau ƙasa-ƙasa ake iya jinsa. A zahiri zaka ɗauka yanayin da
masarautar ke cikine ya sata kasancewa haka, sai dai a
haƙiƙanin gaskiya komai a sukurkurce yake gareta. Duk
wanda ya san alwashinta akan Tajwar Eshaan zai kalla
wannan lokaci ne matsayin na farinciki a gareta domin ta
kusanto hanyar cikar nasararta, sai dai zuciyarta danƙare take
da wani irin ruɗani da ƙunci. Amma ta kasa dakatar da kanta,
komai yana sarrafa kansa tare da ita ne tamkar wadda ake
sarrafawa da na'urar remote. Yanda ta ɗanyi turus kamar
wadda ta firgita da ganinsa ne ya sashi maida idanun nasa
ƙasa cike da basarwa ga screen ɗin computer ɗin kai kace
baima san da ko motsinta ba a wajen.
Da ƙyar Iffah ta iya jan numfashi, yayinda bugun da
zuciyarta ke faman yi tsananinsa ya ƙara hauhawa. Sai dai mi,
bata iya jin zata dakata duk da wani irin rauni da kasala dake
cigaba da mamayeta. Tamkar wata hawainiya haka ta cigaba
da takowa da sanɗa har inda yake, ta ɗan rissino ta gabansa
ta dire tambulan ɗin hannunta a tebirin gaban nasa batare da
tayi magana ba.
Amintaccen hadimin nasa da al'amarin ya zame masa
kamar wani sabon abu, yay saurin dawowa hayyacinsa cikin
rawar harshe ya fara miƙa gaisuwa gareta. Hannu kawai ta iya
ɗaga masa a kasalance dai-dai tana kaiwa a kujerar dake
gefen Tajwar Eshaan zaune. Dole ya miƙe da sauri ya fice a
falon, dan cigaba da zamansa haramunne. Iffah dake jin
kamar ta fasa kuka a dai-dai wannan gaɓar ta ɗaga idanunta
da girmansu a yau gaba ɗaya ya shanye da ƙyar ta saukesu
akan Shahan-shan da yay tamkar bai san da wani mahaluki
mai numfashi a falon ba bayan shi.
“Bar... ka da sa.. fi... ya”.
Ta faɗa a rarrabe tamkar mai koyon magana. Da gaske yau
ƴan izzar ne a kasan, dan haka bai nuna alamar yaji ba, dan
bai ko motsa ba balle ɗauke ido akan abinda ke gabansa har
kusan tsahon mintuna biyu kafin ya ɗaga mata hannu da ƙyar
ya cigaba da abinda ke gabansa. A ƙalla da a ainahin Iffahr ta
take salon nasa zai soke ta, bakuma zata iya haƙuri ba sai ta
maida murtani. Amma abin mamaki sai ta miƙe jiki a saɓule
ta nufi daning babu jimawa ta dawo da glass cup. Da kallon
ƙasan ido ya bita zuciyarsa da jijiyoyin jikinsa na wani irin
tsitstsinkewa tamkar suna masa ishara da abinda ke
tinkarosa. A karo na farko takai durƙushe gabansa, tare da
buɗe tambulan ɗin data shigo da shi mai ɗauke da tatacciyar
madara dake gauraye da dafin macizai daban-daban har kala
biyar. Jikinta rawa yake, har shi kansa sai da ya lura da hakan
ta kallon gefen ido da yake mata. Madarar da bata wuce
rabin kofi ba ta miƙa masa tana mai rumtse idanunta wasu
hawaye da ƙarfinsu ya zame mata nauyi a ƙirji na gangarowa
da gudun tsiya bisa ƙyakykyawar fuskarta.
Cak ya tsaya daga abinda ya keyi, duk da bai juyo gaba
ɗayansa yana kallonta ba, hankalinsa kaf ya koma gareta.
Kusan a tare zuciyarsa da jininsa ke tsitstsinkewa. Bashi da
bukatar shan madara a wannan gaɓar dan a nasa tsarin da
rana ko dare kawai yake shan madara. Sauran lokuta shayi ne
mafi rinjaye da ruwa. Amma a yanzu duk da bahagon yanayin
da yake jin jikinsa, da wanda yaga yarinyar a ciki sai ya kasa
nuna bazai sha ba, tamkar shima ana ingizashi da remote
ɗinne ya kai tattausan hannunsa saman nata a karo na biyu.
Zabura tayi kamar wadda ke son dawowa hayyacinta sai
kuma ta koma laƙwas tare da buɗe idanunta da sukai jazur ta
sauke a kansa. Kallon cikin ido sukai ma juna na kusan tsahon
minti ɗaya cirr batare da ɗaya su ya motsa ba abinda bai taɓa
faruwa da su ba. Shi ya fara janye nasa a kasalance tare da
hanunsa da ya zaro kofin daga cikin nata...
A yanzun ma firgigit tayi tamkar wadda ta farka a barci
harda ɗan zabura ta kai hannu kamar zata riƙo kofin sai dai
abin mamaki shi har ya kaisa kan baki...........✍️

(😭
Da zaka iya jina daga tawa duniyar da nace karka sha😭).


(50)



........Dire kofin da ke empty a hanun Tajwar Eshaan dai-dai
da komawar Iffah daɓas zaune ƙasan lallausan kafet ɗin
kamar wadda aka zarema dukkan numfashi. Ta matse jikinta
tana mai ƙoƙarin riƙe tsumar da takeyi tare da miƙewa
zumut. Ya kafeta da ido lips ɗinsa na ɗan motsawa alamar
son cewa wani abu amma jin kai da ƙasaita ya hanashi yin
hakan. Sai kawai yay ƙoƙarin janyewa cike da basarwa amma
hakan ya gagara. Shi kansa bai san yaya akai ba, bai san
tayaya ba kawai ya samu kansa ne da riƙo hannunta. A tare
suka rumtse ido bisa mabanbanta dalilai. Karan farko na fara
tasirin dafin macizan da suka gama gauraye jininsa ya
matsota a hankali garesa. Babu zato Iffah tajita saman jikinsa
da ke fitar da wani irin sirrintaccen ƙamshi mai karya
zuciya. Numfashinta ne ya fisga da ƙarfi kamar mai cutar
Asthma, ta buɗe ido da sauri dan gaba ɗaya hankalinta ya
dawo jikinta. Zumbur ta mike jikinta na wani irin kaɗawa ta
fara jan ƙafafunta da baya-baya siraran hawaye da batasan
na minene ba na rige-rigen sakkowa. Cikin son danne tashin
hankalin dake cigaba da gauraye jijiyoyi da tsokar jikinsa ya
ɗago idanunsa da launinsu har ya fara canjawa ya zuba mata,
gab taci tuntuɓe da centre table, kaifin idanunsa da tasirin su
gareta a wannan gaɓar ya sata zubewa gaba ɗayanta akan
tebirin...
Wata irin zufa ce ta fara keto masa a dukkan ƙofifin
gashinsa, yayinda tun yana iya ganin Iffah a kusa da shi har ta
fara masa nisa. (Tabbas a kwai matsala) ya ayyana a zuciyarsa
yana mikewa da ƙyar. Da kallo ta bishi zuciyarta na wani irin
mahaukacin bugu tamkar zata buntsiro ta bakinta. Ganin ya
shige ta miƙe itama cikin sassarfa, harta nufi ƙofa ta dakata,
tamkar an janyo idanunta suka sauka kan computer ɗinsa,
janyewa tai dan burinta tabar sashen kawai amma sai
zuciyarta ta dinga ingizata ga computer ɗin. Bayanta ta ɗan
waw-wai-gawa irin dai na rashin gaskiya kafin ta koma da
baya ta zauna a kujerar tasa ta dasama rubutun fuskar
computer ɗin ido. A karan farko ƙirjinta yay wani irin masifar
motsawa. Tsabar kaɗuwa batama san takai hannu ga
computer ɗin ba har rawar jikinta na bayyana. Babu tantama
saƙon data turama Ajmaal ne na karshe, kaɗan ya rage
zuciyar Iffah ta ɓaro waje a wannan gaɓar, babu shiri ta fara
sama dukkan saƙonin data tura masa ne babu ko ɗaya daya
goge, kowanne kuma babu canji a date ɗin data tura ne. Ai
babu shiri ta fito ta shiga settings ɗinsa na WhatsApp. A
Profile ɗinsa, dp pic.. ɗinsa, da komai na dai Ajmaal ɗin data
sani ne... “Allahumma ajirni fi musibati wa'akhlifni khairin
minha”. Iffah ta ambata a karon farko numfashinta na
barazanar barin gangar jikinta, computer ɗin tai ƙoƙarin
singumowa gaba ɗaya dan maidata cinyarta akai rashin sa'a
ta danna abinda bata sani ba kamar ƙiftawar ido suuu ta
shige cikin table ɗin. Ƙwaƙwalwarta neman bugawa tayi
tsabar rikicewa, ta shiga leƙe-leƙe a wajen sai dai babu
abinda ta gane. Babu shiri ta zabura hanyar da Tajwar Eshaan
ya bi tana haɗa hanya.....

A ɓangaren Tajwar Eshaan kam da kyar ya iya kai kansa
ɗaki, dan jefa kafar kawai yake batare da yasan inda yake
takawa ba. A ƙasan lallausan carpet ɗin ɗakin ya zube yana
mai jingina jikinsa da yay sharkaf da zufa jikin gado, duk wata
addu'ar da tazo bakinsa ambata yake, a haka Iffah data gano
ɗakin da ƙyar ta shigo a ɗimauce. Idanunsa dake a lumshe ya
buɗe a hankali suka sauka a kanta. Dukkan ƙarfin halinsa da
jarumta ya tattaro ya adana tashin hankalin da ke tattare da
shi. A ɓangaren ta itama ruɗanin da take ciki ya bada
gudunmawa wajen makantar da ita yanayinsa, cikin rawar
harshe idanunta dake tsiyayar hawaye a kansa ta durƙushe
ɗan nesa da shi.
“Dan ALLAH na roƙeka ka faɗamin wanene kai? Miye
alaƙar ka da Ajmaal?!”.
Babu alamar zai tanka mata, sai dai idanunsa dake sake
rinewa jajur na tsaye a kanta ƙyam. Tsahon wasu mintuna ya
lumshe su da sake buɗe su a kanta yana cije lips ɗinsa. Ya
kauda fuskarsa cike da ƙarfin hali, da son saisaita muryarsa, a
maimakon ta samu amsar tambayarta sai saɓaninta ya fito da
ga garesa.
“Ki canja madarar da kika bani da wadda ke akan dining.
Hatta kofin da na sha daga cikinsa karki bari”. Ya ƙare faɗa a
wahale cikin cije baki da rumtse idanunsa.
(Iffah ki nutsu karki tonama kanki asiri) zuciyarta ta ayyana
mata. Idanunta ta rumtse da karfi tana gyaɗa kai kamar
wadda ake faɗamawa a cikin kunne. Sai kuma ta shiga goge
hawayen nata da maida kallonta garesa a yanayin son kare
kai.
“Ni ba batun madara na tambaye ka ba. Wanene
Ajmaal?!!!”. Ta faɗa a matuƙar tsawace.
Birkitattun idanunsa ya rumtse da ƙarfi dan sam baya son
hayaniya, balle ma a irin wannan halin da yake ciki a yanzu.
Ya buɗesu kanta shima a fusace har sai da kallon cikinsu ya
sakata zabura. Shima cikin tsawar da fisgar numfashi ya ce,
“Babu abinda zai amfanar da ke a jin amsoshin da kike buƙata
a yanzu. Kije kiyi abinda nace!! Kije!!!!”.
Ba ƙaramin firgici Iffah ta shiga da yanayin nasa ba. A
zabure kuwa ta miƙe, batama san taya ta nufi ƙofa ba ganin
kanta kawai tai a falo, harta nufi ƙofar lifter ta dawo da baya,
tambulan ɗin madarar ta ɗauka, ta nufi dining wajen wanke
hannu ta juyeta, kofin ta ɗauraye jikinta nata ƙyarma, gaba
ɗaya ta nema jarumtarta ta rasa, sai da ta tabbatar ya fita ta
dawo kan dining ɗin inda aka shirya break fast, madarar dake
a jiye a wani tambulan ta ɗaga ta juye a wanda ta wanke ɗin,
ta sake komawa ta wanke wannan, sai kuma ta rasa ina zata
ɓoyesa kamar yanda zuciyarta ke bata shawara. Da kyar ta
samu nutsuwar samun wajen makalasa, ta dawo harta sake
nufar hanyar fita ta sake dawowa da baya, kofin da ya sha
madarar ne, shima ɗauka tai ta wanke ta zuba sabuwar
madarar ta kauraya ta maida inda ya sha. Sake nufar ƙofa tayi
sai kuma ta sake dawowa ta nufi ɗakin dai da ka ganta kasan
tana a cikin halin ɗimuwa....

A ɓangaren Tajwar Eshaan kam tana fita tari ya sarkesa, jin
saukar abu a tafin hannunsa da yake tare bakin ya sashi
saurin kallon hannun. “Jini..” ya ambata a hankali saman lips,
sai kuma ya saki wani irin wahalallen murmushi da mai da
kansa ya kwantar jikin gadon yana ambaton “Sunci nasara,
sun sami nasara ta dalilinki *_My Sohaa_*....” tari ya kuma
sarƙesa a hankali, sai dai murmushin na nan maƙale a
fuskarsa har yanzu, sai faman lumshe idanunsa da suka
birkice yake yana ƙoƙarin buɗesu da ƙyar fuskar Iffah da
hawayenta ne tsaye ƙyam a cikinsu. Ba mutuwa yake tsoro ba
a yanzu, baya da ƙurar da zai barta a ciki, ya tabbatar itace
zata sha wahala, wahala irin wadda ba ita yay mata tanadi ba.
Hakanne ya zaburar da shi, yaja jikinsa da ke saki gaba ɗaya
da ƙyar zuwa telephone..
Ana ɗagawa ya fara magana cikin son ɓoye yanayin da
yake ciki. “Duk wani cctv footage na safiyar yau zuwa yanzu
na sashe na ka kwashe sa, amana ko kai na haramta maka
ganinsa ka ajiyesa gareni, idan kuma na rasa raina ka
damƙashi ga Zawja Fareedah....”
Bai bada damar cewa komai ba ya yanke kiran, da ƙyar
ya maida akalar wani zuwa Malikat Bushirat....

*_MALIKAT BUSHIRAT_*

Yanayin tashin hankalin da masarautar ke ciki koma a ace
ƙasar baki ɗaya dan yau mutanen da suka fito zanga-zanga
akan murabus ɗin Tajwar Eshaan sunfi na kullum yasa ko fita
batayi. A kallo ɗaya zaka iya ƙirga damuwarta saman
ƙyakykywar fuskarta data koɗe matuƙa a cikin kwanaki ukun
nan. Tayi duk wani ƙoƙarin ta iya iyawa domin ganin gudan
jininta amma al'amarin ya gagara. Kuka bata san iya adadin
da tayi ba ba kuma ta san wanda zatayi a gaba ba, dan anzo
gaɓar da ko'a mafarki bata taɓa sakata a lissafin ƙaddararta
ba.....
Shigowar kira a landline ɗin ɗakin barcin nata ya sata
zabura dan yazo mata ne a bazata, dole ta ambaceshi da
bazata dan Tajwar Eshaan ne kawai ke da wannan hurumin.
Har tuntuɓe taci amma bata damuba ta caɓi kan wayar
tunkan ta karasa gareta da ƙyau. Rawar jikinta dana harshe
na faruwa ne a lokaci guda, sai dai muryar data doki tsakkiyar
dodon kunnenta ta saka numfashinta tsaiwar wucin gadi....
“Ammie!...”
Aka faɗa da ƙyar cikin kuma rawar harshe mai fidda sautin
nakasashshiyar murya mai tabbatar da amon razani ga mai
saurare.
“Saiful-malik!!...”
Ta ambata itama tare da fisgar numfashinta dake kaikawo
a iya maƙoshinta zuwa cikin baki kawai. Shi bai sauka a huhu
ba, bai kuma fita ta hanci ba. Bata ma san ta saki wayar ba ta
fice...
“Ya ALLAH Akia!...”
Jasrah dake shigowa ta faɗa da sauri tana riƙo Malikat
Bushirat da gaba ɗaya idonta ya rufe da ruɗani. Son ƙwacewa
take tana ambaton “Eshaan.. Jasrah Eshaan.. Eshaan zasu
kashe min shi”.
Sam Jasrah bata fahimci inda ƴar uwar tata ta dosa ba,
dan haka tai saurin katseta da faɗin, “Na shiga uku Akia dan
ALLAH nutsu kimin bayani, mi ya dakesa?”.
Ina Malikat Bushirat ta kasa amsata, dan numfashinta ma
har ya fara fisga. Bata haɗa soyayyar Tajwar Eshaan da komai
ba a duniya. Tana masa wani irin makahon so mai wahalar
fahimta. Duk yanda Jasrah taso tanƙwarata ta kasa, sunan
Eshaan kawai take ambata da son fisgewa ta fita. Bazai yiwu
ta barta ta fita a haka ba, dan haka tai saurin danna ƙofar
bedroom ɗin da ƙafa. Hankaɗata Malikat Bushirat tayi, duk
da taji zafi dama gata ba wani ƙwarin jikin take ji ba amma
haka ta daure ta murza key. Da ƙyar ta iya zarewa ta sake riƙo
Malikat Bushirat tana mai fashewa da kuka. “Akia dan ALLAH
ki sanar min, fitarki a haka ba itace mafita ba, idan ma akan
masu zanga-zanga ɗin nan ne ki kwantar da hankalinki
jami'an tsaro bazasu barsu su ɓalla koda gate na farko
ba........”
“Jasrah ki fahimceni.....!!!”
Malikat Bushirat ta katseta cikin ƙaraji sai kuma ta fashe da
kuka. Tabbas babu lafiya, ƴar uwarta a haka lallai akwai
matsala. Har taune harshe take wajen ambaton, “Zan
fahimceki faɗamin ko a taƙaice ne Akia dan ALLAH”.
Da ƙyar Malikat Bushirat ta sanar mata a dunƙule, nan fa
hankalin Jasrah ya tashi itama babu shiri ta zabura ta buɗe
ƙofar......

★★....

Suɓucewar kan wayar a hannun Tajwar Eshaan dai-dai da
sake faɗowar Iffah ɗakin a birkice. Gaba ɗaya ma ta mance
matsayinsa da nata, tai kansa babu alamar hankalinta na tare
da gangar jikinta. Tana zubewa gabansa yana faɗowa jikinta
hannunsa dafe da kansa yana ambaton “Ammie...” a hankali,
ga wata irin zufar da tai masa sharkaf kai kace wanka yay a
lokacin.
“Na shiga uku ni Fhareedah!”. Da Iffah ta faɗa cikin kuka
ya saka shi ɗago idanunsa dake matukar jazur zattashin
hankali. Akanta ya tsaidasu a wani irin bahagon yanayi, ya
lumshesu da ƙyar ya sake buɗewa a kanta. Lips ɗinsa da suka
koma jajur saɓanin pink a da suna motsa a hankali ya saki
wani wahalallen murmushi da har Iffah ta koma ga ALLAH
bazata taɓa mantawa ba, dan ya zauna a allon zuciyarta
tamkar rubutu akan dutse. kafin idon nasa ya koma ya
lumshe gaba ɗaya tattausan hanunsa na dama saƙale cikin
nata da bata san sanda ya riƙo ba...........✍️

*_ALHAMDULLAHI!!🙏_*

Ina godiga ga ALLAH daya bani ikon kawo ƙarshen littafin
DAUƊAR GORA CIKI KA SHATA kashi na farƙo. Ina roƙon
UBANGIJI ya bani tsahon rai da lafiya ni da ku har zuwa bayan
salla da zan ɗora kashi na biyu insha ALLAHU. Ina mai baku
haƙuri da ƙari saman haƙuri da tangarɗa da jinkiri da aka
samu duk da Alhamdullah ban taɓa fashin posting ba, sai dai
labarin yayi tafiyar hawainiya saboda yanayi, hakan ta
samune dalilin babban dalili daya shafi uzirin rayuwata. Insha
ALLAHU bayan salla zakuga canji ayi haƙuri amin afuwa dan
ALLAH yau da gobe kenan kun san Bilyn taku ba haka takeba
a da.🙏🥲.

Himmm!! Ban san ma mizan ce mukuba daga ƙarshe,
amma ku sani DAUƊAR GORA part 2 zai zama na musamman
ne da salo mai..... (🤭hummm badai sai nace komai ba..)

★Yaya kuke tunanin rayuwar Iffah zata kasance ne?.

★Mizai faru da Tajwar Eshaan zai mutu ne kokuwa?.

★Waye saurayin daya kwamushe su Kaka?.

★Taya Tajwar Eshaan ya zama Ajmaal?.

★Wacece ta ƙurya?.
★Miran Jasim da Miran Arshaan zasu ci nasara?.

★Anya ƴan ƙasar ruman akwai mai iya kwantar da fushinsu a
wannan gaɓar?.

★Yaya makomar su Babiy da Barrister?.

Kai tambayoyin da yawa suke karna cikaku da zance Ni
ban baku cigaba ba. Kudai kawai muyi addu'ar ALLAH ya
kaimu a gama azumi lafiya. Ya rabbi kasa muyi karɓaɓɓiyar
ibada.

Ina ƙaunarku masoya, zan cigaba da ƙaunarku kuma. Duk
wanda ya soni domin ALLAH shima ALLAH ya soshi haka😭 😍
😍😘 .

Taku Bilyn Abdull ce😉😄.

09032345899

********************************************
Visit http://novelselite.com.ng for more books

About Novels Elite
Novels Elite is a website consisting of Hausa Novels Books
such as Text, Documents, Audiobooks, and Videos, the
purpose of creating this site is to Entertain, Motivate and
Educate our readers.


Novels Elite provided so many kinds of Hausa Novels of

Please Login or Register in order to submit comment