Reading Dauɗar Gora by Bilyn Abdull ce Chapter 6 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikar adadin waɗan nan daƙiƙu
Muhammadu Zayyanu. Amma inaso ku tuna muɗin
talakawansu ne, masu rayuwa a ƙarƙashin mulkinsu, bamu da
wani ƙarfin iko akan hukuncinsu garemu ko kan ƴaƴanmu.
Dan haka ku bita da addu'a kawai itama.”
Tamkar yana gabansa ya jinjina masa kansa, tare da
ƙoƙarin danne hawayen da yake na zuciya da ƙunarsu gara
ace a zahiri suke zuba bisa ƙyaƙyƙyawar fuskarsa. “Shikenan
Baba, amma furucin Iffah ya girgizani, ina tsoron kar zuciya ta
ingizata tai yunƙurin aikatawa. Kisa fa! Koda bata aikata ba
fitar wannan furucin zuwa kunen wani bayan mu ba ƙaramar
magana bace”
“Kar komai ya dameka Muhammad Zayyan. Ta faɗane
kawai saboda raɗaɗi da takeji da kuma ƙuruciya, kai dai ka
sanar dasu ka amsa daga nan zuwa kwanaki uku. Zan zo a
amsa kuɗin auren da ni dama wasu a cikin zuri'an ka insha
ALLAHU.........✍

11


..........Iffah taci kuka matuƙa da ko maƙiyinta ya dubeta sai ya
tausaya mata. Sai dai kuma iya juyawa su Babiy sun mata
akan su gudu ta kafe akan itafa ta yarda zata aura *_Tajwar
Eshaan ibn Haysam Abdull-Majeed_*. Sosai hankalinsu yake
ƙara tashi da tirjewarta. Gashi gaba ɗaya ta bikice musu ko
isashen lafiya babu a tare da ita. A cikin wannan halin Babiy
ya sake samun saƙon kira daga masarauta. Yana shirin tafiya
sai ga Kaka. Duk sunyi matuƙar mamakin zuwan nasa, dan
abune mai wahalar gaske a garesa zuwa inba da wani dalili
ba. Sun tarbesa kamar yanda suka saba matsayinsa na uba.
Bayan gama gaisawa ya kai dubansa ga Iffah dake kwance
cikin bargo duk ta rame ta sake komawa fayau da ita, dama
tun rasa ƴan uwanta ɗan jikinta ya zube, dan sam ba siririya
bace. Iffah nada jiki murjajje daba za'ace mata siririya ba
kuma babu mai sakata a sahun masu ƙiba. Duk da shekarunta
har yanzu sunada ƙaranci ALLAH ya bata jiki na manyan mata
da'a yanzu komanta yake ciff dai-dai da halittarta. Kaka ya
ɗauke idanunsa a hankali tare da maidasu ga Babiy.
“Muhammadu Zayyanu ka sakama ranka nutsuwa ka cire
batun barin gidan dan bashine mafita ba. Hasalima tun randa
ka amsa kiran masarauta wannan gidan zagaye yake da
dakarun daular ruman harta inda baka zata ba. Ko'a
tunaninka zasu tunkareka da wannan maganar su baka
damar kanka sannan su koma gefe da tunanin kai bazakayi
wani yunƙuri ba”.
Daga Babiy har Ummu da Hanash kallon tsoro da mamaki
sukema Kaka. Ya ɗan jinjina kansa alamar tabbatarwa. “Karku
damu da yanda akai nasan wannan, kai dai kawai kaje ga
kiran da sukai maka. Karka kuma nuna wani ja'inja kace ka
amince musu suzo neman auren”.
Kuka Ummu ta fashe da shi tana kallon mahaifin nata. Yay
ɗan murmushi da ɗauke kansa tamkar bai fahimci mitake nufi
ba. Ganin haka Hanash da idanunsa sukai jajur cikin
cinkushewar harshe yace, “Amma kaka miyasa ka zaɓa itama
mu sake rasata? Wlhy nayi alƙawarin in har itama ta salwanta
sai na salwantar da ran Shahan-shan da wannan hanun nawa
wajen ɗaukar fansa koda nima za ai gunduwa gunduwa da
naman jikina!!”.
“Ba kai ne zaka salwantar da ruhinsa ba, ni nan Fareedah
bint Zayyan nice zan karya ƙarfin ikon azzalumi da hannuna,
zan masa shaƙa irin wadda har sai ya mutu yana mai kallon
tsakkiyar cikin ƙwayar idanuna Hanash Akhi”.
Su duka zuba mata idanu sukayi, dan a yanda take maganar
babu alamar tana a cikin hayyacinta. Babiy zaiyi magana Kaka
ya girgiza masa kai alamar kar yace komai yaje kawai....

★Kamar yanda Kaka ya umarci Babiy ya amsa kiran
masarauta kasancewar a wannan karon an bashi damar zuwa
ne shi kaɗai batare da dakaru sun taho da shi ba. A yanda ya
samu tarba zai tabbatar maka dama a jirace ake da zuwansa.
Kamar ko yaushe a wannan karon ma baiga Tajwar ba, amma
dai a karon farko na tarihin rayuwarsa an kaisa har cikin fadar
Shahan-shan. Inda yaga tsantsar dukiya da ainahin karagar
mulki ta Shahan-shan da akayita da zallar zinare. Hakan
ba'abin mamaki bane ba, saboda girman Shahan-shan koda
da diamonds akai kujerar mulkinsa bazai zama wani babban
al'amari ba, sannan zinare arziƙin ƙasar su ta ruman ne da
bare ma kanzo ya ci balle su ƴan ƙasa musamman Shahan-
shan. Karo na farko da Babiy yaga karramawa daga dattijan
daular ƙasar ruman. Waɗan da ko'a mafarki bai taɓa tunanin
gani ba dan su ɗin ma ba'abune mai sauƙi ga duk wani talaka
ganinsu ba kai tsaye haka. Duk da a birkicen da yake ALLAH
sai ya saka masa nutsuwar yi musu bayani babu ko rawar
harshe a tare da shi. Sun masa godiya da tabbacin a gobe
idan ALLAH ya kaimu masu neman aure zasu zo. Karramawar
da sukai masa ta matuƙar basa mamaki da tsayawa a ransa,
sai dai ta wani gefe na zuciya ya tabbatar da sabuwar hanyar
yaudarace kawai. Cikin danƙareriyar mota aka maidasa har
gida badan yaso haka ba, yayi shiru ne kawai domin bin
unarnin mahaifin matarsa, dan duk da bai taɓa ambatawa ba
ga kowa ya jima da tsanar duk wani abu daya shafi
masarautar daular ruman..
★A wannan dare Babiy yayi zaman kuka irin wanda ake
kira kuka a zahiri da baɗinin rayuwa. Har yanaji bazai iya
cigaba da yima kaka biyayya ba shikam, zai ɗauke Iffah su
gudu daga ruman koda daga shi sai ita ne. Sai dai wani
ɓangare na zuciyarsa na tunatar da shi maganar Kaka, yasan
gaskiya ya faɗa, dan daular ruman bazata zuba ido na barinsa
sakakai ba. Ajiyayyun dakarun dake a ƙofar gidansa ma kawai
tabbaci ne....
A ɓangaren Ummu ma bata runtsa ba, sai dai saɓanin
Babiy ita kwana tai tsaye tana gayama UBANGIJI damuwarsu
da roƙonsa kariya da kuɓuta ga yarinyarta. Shi kuwa Hanash
kwana yay ƙulla ta yanda zai halaka Tajwar Eshaan ibn
Haysam Abdul-majeed da kansa. Hakama Iffah nata shirin
nada alaƙa dana Hanash. Ta gama yankema kanta koda zata
mutu itama sai dai su mutu tare da Tajwar Eshaan. In yaso a
binne gawarta a tsakiyyar ruman matsayin tarihin da za'a
dinga tunawa.......

*_WASHE GARI_*

Washe gari data kasance safiyar laraba da misalin ƙarfe
biyar na yamma sai ga manyan baƙi daga masarauta ruman.
Baƙi masu ban mamaki, dan kuwa wasu manya ne a cikin
dattijai masu faɗa aji a daular ruman. Sannan iyaye ga
Shahan-shan ta ɓangaren jini makusanta sosai ga mahaifinsa.
Tamburan masarauta da ɗunbin tawagar hadimai da jibga-
jibgan motoci da suka ƙoshi ne suka tabbatarma da jama'ar
anguwa dama maƙwaftan anguwar wace tawagace. Tuni
mutane suka fara ƴar rige-rigen fitowa daga gidajensu bama
idanunsu abinci.
Sun tarbesu bisa jagoranci Kaka daya tsara komai tare
da shimfiɗa kakkauran gargaɗi ga su Babiy. Bayan an musu
masauki a cikin lambun Babiy ta ɓangaren garden ɗin da yayi
domin farin ciki ga iyalansa aka cika musu gabansu da ƴaƴan
itatuwa duk da babu tunanin ko zasu ci. Babiy, Kaka, da wasu
dattijai biyu, ɗaya ta ɓangaren Babiy, ɗaya ta ɓangaren
Ummu ɗan uwa ga kaka kenan suka zauna da su. Sun miƙa
gaisuwa a garesu cikin mutuntawa da nuna tabbacin su ɗin
masu ƙarfin iko ne a garesu talakawan ƙasan ruman. Hakan
yayima dattijan matuƙar daɗi da yabama su Kaka. Dan haka
suma suka nuna mutuntawa a garesu da basu ƙarfi matsayin
waɗanda sukazo neman iri wajensu. Hakan ya ɗan bama su
kaka mamaki amma sai babu wanda ya nuna. Sun gabatar da
buƙatarsu, tare da bada duk wani abu na al'adar aure da
ƙasar ruman ta tanada ninki wanda akanyi sau goma. Hakan
sai ya ƙara firgita Babiy da bashi tabbacin yanda za'a
salwantar da rayuwar ƴarsa ɗaya tilo data rage masa zai zama
ƙololuwar girma fiye da ƴan uwanta kenan. To inbaice hakaba
mizaice, dan dukiyar da suka kawo kawai tamafi ƙarfin ma
sayen Iffah idan sayarwar zaiyi. Bai samu damar cewa wani
abu ba, yadai cigaba da kukan zucinsa yabar su Kaka dayin
abinda ya dace.
A wannan zama aka ƙarƙare komai har ranar ɗaurin aure
dama inda za'a ɗaura auren. Daga haka sukai addu'a suka tafi
bayan an shigo da tarin kayayyakin da sukazo da shi. Daga
Babiy har Ummu tagumi kawai sukai suna kallon kayan da aka
baza a tsakar gida. Hakama Hanash da dattijan nan guda biyu
da sai gobe zasu koma tare da kaka. Kaka kuwa na gefe zaune
abinsa tamkar baima san mike faruwa ba a gidan. Yayinda
Iffah ke can ƙuryar ɗakin Ummu kwance cikin zazzaɓi data
yini da shi.....
Washe gari su kaka suka wuce batare daya sake cewa
uffan ga su Babiy ba akan komai. Yadai gargaɗi Babiy akan
karya kuskura yace zai yi wani yunƙuri. Ya kuma sakasu killace
dukkan kayan da aka kawo daga masarauta.....

★★★_______★

Tamkar da gayya cikin kanƙanin lokaci gari ya ɗauka
Shahan-shan zai yi aure, alamu kuma sun nuna ana shiryama
auren da shiri na musamman duk da amaryar bata kasance
ƴar kowa ba. Hasalima ahalinta nada tabon Shahan-shan a
dalilin salwantar ƴaƴansu biyu kafin ita. Dukkanin waɗan nan
ƙananun magana na faruwane a bakunan mutane da ƙaramar
murya, yayinda a kafafen ƴaɗa labarai da fejikan yaɗa
zumunta babu mai iya ɗaga murya yayin faɗa sai fatan alkairi
kawai. Mutane sun sake samun tabbacin wannan aure na
musammne daya sha banban dana baya sakamakon fara
shelarsa a kafafen yaɗa labarai domin gayyatar manya-
manyan ƙasar kamar kowane Tajwar da jama'ar majalissarsa
da talakawan garinsa. Da yanda ake wasu ƴan gyare-gyare a
daular ruman wai duk na tarbar zuwan ranar ɗaurin aure ne.
Humm abin faɗa taf bakunan mutane sai dai babu damar
faɗar. Idan kuma suke ganin zasu sami wani ƙarin bayani an
toshesa dan babu mai ikon shiga gidan Babiy a halin yanzu
kasancewar zagaye yake da dakaru tako ina, acewarsu suna
bama *_Zawjata-almilki_* tsaro ne. A cikin gidan kuma babu
mai fita hatta da Hanash dake zuwa babbar makaranta...
A haka kwanakin biki da suka rage suka cigaba da shurawa
batare da wadda ake iƙirarin zama amaryar ta sake tada kai
ta dubi wani abu daya shafi auren nata ba koda da kallo. Ta
dake matuƙa tamkar ba itaba, hatta da ciwon dake cinta a
tsaitsaye taki bada damar da su Ummu zasu fahimta. Ta
ƙeƙashe idanunta ƙam ta hana hawaye zuba daga cikinsu. Ta
tattare gaba ɗaya hankalinta ta maida ga rubuce-rubuce da
babu wanda ya fahimci na minene a gidan, dan bata bari
kowa ya duba mata shi. Sai dai ga duk mai hankali a duba
ɗaya da zai mata zai fahimci tana cikin matsananciyar
damuwa, mai busar da zuciyar mai ita da zai iya aikata komai
da zai iya zama komai akan komai..
Kamar ko yaushe yau ma bayan ta kammala ayyukan
gidan da take taimakawa Ummu da su ɗaki ta koma tana
kukan zuci daya zame mata abokin rayuwa. A idaniyarta kam
babu alamar ɗigon hawaye, sai dai raɗaɗin wanda ke
kwaranya a zuciya ya maida launin idanunta sirkin ja har kana
iya ganin jijiyoyi a cikinsa. Duƙufe take akan littafinta tanata
rubutu da sakin ajiyar zuciya akai-akai. Ummu data shigo
ɗakin takai zaune a kusa da ita tana mai tsurawa rubutun
idanu na wasu sakanni.
“Ibnati!”.
Karan farko Iffah ta ɗago ta kalla Ummu duk da tun
shigowarta ta jita sarai. Wani irin miskilin murmushi ta saki
tare da maida kanta a hankali ta duƙar..
“Kina ganin laifinmu ko?”.
Cak ta tsaya da rubutun data cigaba, sai kuma ta saki
murmushi. Tsahon sakkani uku kafin ta ɗago ta dubi Ummu.
Ta ɗan girgiza kanta da ajiye biron hanunta. “Ummuna idan
har zanyi zargin wani akan wannan al'amarin to kaina ya dace
na zarga. Ku ɗin nagartattun iyayene abin alfaharin kowane
irin ɗa. Ni ya dace nazo muku da wannan maganar, domin
nice na saka zukatanku a damuwa da ɗunbin fargaba. Na
tabbata a kowane sakan, a kowane minti, a kowane awa, a
kowane kwana na waɗan nan kwanakin kunayinsa ne cike da
fargabar shuɗewarsu da gabatowar su. Kuyi haƙuri ku ƙara
haƙuri ku gafarceni. Koda baku faɗamin ba, baku faɗama
duniya ba nasan irin raɗaɗin da kukeji a zukatanku domin
nima makamancinsa nakeji. Sai dai ina muku albishir
Ummuna, koda zakuyi kuka a wannan gaɓar bazakuyi irin na
baya ba. Na muku alƙawarin kukan ku zai kasance tare da
dariyarkune a lokaci guda. Dan ruhina sai ya amso muku
diyyar su Nina Arfa kafin yabar gangar jikina. A duk randa
saƙon mutuwata zai riskeku insha ALLAHU zai riskekune tare
da na mutuwar azzalumai. Dan haka ina roƙonku kar kuyi
baƙin ciki a wannan karon, zaku sadaukar da ruhin da zaije
muku yaƙin neman ƴancin kai ne ku da al'ummar ƙasar
ruman.....”
Kai Ummu ta shiga jujjuyawa hawaye na kwaranya a
idanunta, “Ibnat...”
“Na roƙeki kar kice komai Ummuna, albarkarki itace mafi
ƙololuwar buƙata ga ruhin daya daɗe da zama cikin tahin
gawa. Ƙaddarata rubutacciya ce tun daga alƙalamin da idan
yay rubutu babu wani duster dake iya gogesa”...........✍
12


.........Kalaman Iffah sun zama mafi ƙololuwar zama famin
gyambo a zukatan Ummu da Babiy harma da Hanash. Sun
zanu da zanen da zuciya ta killace koda tunasu zai zama mai
raɗaɗi a cikinta. Sun karɓa domin karɓar ta zama tilas a
garesu saboda rashin murya da ƙarfin iko da suka rasa a
hannayensu. Sun cigaba da kuka saboda kukan shine kawai
mafita a garesu. A haka kwanaki suka cigaba da tafiya da
raunin zukatansu har zuwan ranar juma'ar da masu ƙarfin iko
suka tsaida matsayin ranar ɗaurin auren ƴarsu. Bayyana ko
misalta kasancewar wannan dare da wayewarsa ma ɓata
lokacine game da halin da ahalin malam Zayyan suka tsinci
kawunansu. Babu wani alamomin biki daga ɓangarensu sai
ma zaman makoki. Dan bayan Iyyani da Kaka da wasu dattijai
da basu gaza biyar ba a cikin zuri'arsu babu wanda ya halacci
wannan makahon aure hatta da maƙwaftansu. Bisa tilastawar
Kaka Babiy da Hanash sukai shirin halartar massallaci yin
sallar juma'a da riskar abinda zuciyoyi ke tsananin ƙuna a
kansa. Sun tafi sun bar Ummu da Iyyani da tazo itama a
yanayi mai ban tausayi. Amarya Iffah kam idanunta ma babu
wanda ya gani a wannan safiya abinci ma Iyyani ta bita da shi
har ɗaki....

*_TAFARU TA ƘARE_*

Bayan gushewar wasu awanni, masu tafiya da ƙarfin bugun
zuciya busa irin ta sarakai da tashin tambura ya karaɗe cikin
birnin Daular Ruman dake cike da manyan baƙi tako ina. Dan
kuwa sarakuna goma cif na ƙasar Ruman duk sun halarta duk
da suma akwai raɗaɗin rasa ƴaƴayensu a zukatansu har
yanzu. Koda yake wasu a ciki sun bada ne da kwaɗayi na
burin zamowar ƴaƴan nasu zama matan Shahanshan, suna
ganin hakan wani ɗaukaka ce a garesu da samun wasu
damammaki......

Iffah dake kwance a ɗaki zuciyarta a bushe, idanunta dake
zubda hawaye a ɗazun a soye ta jiyo bayanin ɗaura aurenta
da Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-Majieed daga bakin su
Kaka. Wani irin dimmm taji a cikin kunnuwanta tamkar
ɗaukewar wutar lantarki daga tashar gidan redio, ta koma ita
ba wadda ta suma ba, ba kuma wadda ke a raye ba tsabar
tsintar kai a wani hali. Ta jima a haka kafin ta dawo
hankalinta kwakwalwata ta fara tantance abinda taji ɗin.
Kenan abinda ya faru da yan uwanta a wasu watanni da suka
shuɗe itama shine ya faru da ita yau? Itama zata mutu
mutuwar rashin gata da ƴanci a hanun azzalumin mai mulkin
Ruman da jama'ar cikinta. Daga yau za'a koma ƙirga mintuna
da daƙiƙun mutuwarta da suka rage mata, daga yau tayi
bankwana da Ummu, da Babiy, da Hanash Akhi da su Kaka.
Anya kuwa zata iya? Anya kuwa sadaukarwar nan ta dace da
rubutattun burukanta? Anya kuwa zata iya jurewa? Kai ina
bazai yuwu ba. (Mizai hanasa yuwuwa? Bayan zakije inda ko
kuwwa kikai babu maijin muryarki?) wata zuciya acan gefe ta
ayyana mata. A karo na farko hawaye masu zafi da raɗaɗi
suka silalo bisa kumatunta da gudu. “Dole ma na jure, jurewa
irin wadda a duk faɗin duniya labarina zai karaɗesa a lokacin
dana hukunta Tajwar Eshaan ibn Haysam ibn Abdul-majeed”.
Ta faɗa cike da ƙwarin gwiwa na tabbatar da burin mai
ɗaukar fansa.
Batare data goge hawayen dake cigaba da rige-rigen zubo
mata ba ta sauka a gadon tana tangaɗin jiri. Wayar data
maida ta ajiye da ƙudirin ta daina amfani da ita ta lalubo,
haɗata tai ta kunna, sai dai tai ɗan jimm namai nazari kafin ta
fara rubuta saƙo. Minti biyu bayan turawa kira ya shigo.
Numfashi ta fesar, sai kuma ta saki murmushin takaici jin
abinda aka faɗa daga can.
“Sir bamu da lokacin tattauna wannan a yanzu”.
“Na sani Fareedah, sai dai inajin matuƙar tsoro, tsoro irin
wanda ko'a ido aka kalla an san tsoro ne. Nasan na rasaki na
har abada a yanzu”.
Murmushin takaici ya suɓuce ma fuskarta, sai dai ta hana
hawayen da suka ciko mata ido zubowa. “Wannan shine
tsoron dana gudar maka fuskanta tun farko dama duk
jama'ar Ruman. Amma bazan gajiya ba, plan A dama yaƙin
sunƙuru ne, plan B mafi haɗari amma da yaƙinin nasara”.
“Ta yaya Fareedah? Kin san kuwa waye Shahanshan?
Kin san minene girman ikonsa?.....”
“Na sani mana tunda nima a ƙasar aka haifeni. Sannan na
zama cikin ahalin da sukafi ɗanɗana ɗacin girman ikon nasa
da zalunci. Karka damu da haɗari sir, taimako ɗaya zakamun
a wannan plan ɗin wanda babu wani abu da zai shafeka da
iznin ALLAH”.
“Amma Fareed....”
“Please sir”.
Kakkauran numfashi yaja ya fesar cike da ƙarfin halin son
danne rauninsa a gareta.
“Okay ina jinki”.
“Ka bani number abokinka”.
“Fareedah mi kuma ya rage?”.
“Abubuwa masu yawa da amfani, hasalima yanzu ne za'a
fara wasan na gaskiya”.
“Karki taurin kai”.
“Na jima da zama mai busashiyar zuciya”.
“Ki fahimceni”.
“Ko kaina ma bana iya fahimta sir”.
“Bana son na rasaki Fareedah”.
“Iyayena sun jima da haƙurin rasa ni, kamar yanda na jima da
sadaukar da kaina”.
“Miyasa kike da taurin kai Fareedah”.
“Shine izzata, ƙarfin gwiwa ta wajen tunkarar maƙiyi na”.
Wani irin cije lips yayi daga can, hawayen da tun randa
labarin auren wadda ya fara so yake kuma kan so yazo masa
da wanda yafi ƙarfinsa suke kwaranya ya kasa sharesu suka
shiga rige-rigen zubowa daga idanunsa, yasan ta ƙare kuma,
abinda ya rage kawai ƙyautatama masoyiyarsa koda hakan zai
kasance sadaukarwa ta ƙarshe da zaiyi a rayuwarsa.
“Na barki lafiya, ki kasance cikin aminci da kariyar
UBANGIJI”. Ya faɗa harshensa a sarƙe da yanke wayar a
lokaci guda.
Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga gudu a fuskar
Iffah, bata san tana son Sir Fawzan ba sai a yanzu. A yanzun
da kowa zai iya kiransa ƙurarren lokaci a rayuwarta. Zata
cigaba da masa fatan alkairin samun madadinta koma wadda
ta fita, jin kamar motsin ana tunkaro ɗakin yasata saurin
kwanciya taja bargo har saman kanta....

★★........

“Muhammad Zayyan!”.
Kaka ya kira Babiy tamkar yana gabansa cikin matsanancin
damuwa da firgici na zahiri dake kan fuskarsa. Ɗago kansa
dake sunkuye yay a hankali shima tamkar yana a gaban
Kakan. Hakan ya bayyana jajayen idanunsa da damuwa ta
rinar. Sun rabu ne tun a wajen ɗaurin aure basu dawo nan
gidan ba suka wuce Jumna.
“Na'am Baba”.
“Kayi haƙuri. Karku zama masu baƙin ciki kai da matarka. Ku
zama masu juriya da karɓar ƙaddara rubutacciya daga
UBANGIJI. Nasan akwai raɗaɗi, nima kuma makamancin
irinsa nakeji a ƙirjina. Sai dai bazan gaji da faɗa maka
*_Kibiyar ajali sulke baya tareta sai ta gitta ba_* kamar yanda
babu wata duster data isa goge abinda alƙalamin ƙaddara ya
rubuta. Mu mun wuce yanzu, dan mungama namu ku ya rage
kuyi naku mu barma UBANGIJI sauran, dan dama duka nasa
ne. Iyyani itace zata shiryata kafin isowarsu ɗaukarta, nau'in
turaren da yake a cikin gidanka kawai nake buƙatar fitar
ƙamshinsa daga jikinta. Ta kuma sha iya adadin madara
datake gidanka kawai daga yanzun har zuwa wayewar gari.
Ta kwana a ɗakin daba shi aka ajiyeta ba. Karta karɓa daga
wanda zuciyarta tai rawa a kansa. Ta zama ƴar kallo a takun
farko, ta zama kurma a shigar farko, ta zama mai rauni a
tawagar farko, tasa a ranta kariyar UBANGIJI na tare da ita.
Na barku lafiya”.
Ummu ta juya ta kalla Babiy dake riƙe da wayar a hannu
tamkar dasashen gunkin da akai ado dashi domin tunawa a
tarihi. “Lafiya kuwa? Baba ma baida wata mafita ko? Shiyyasa
yaƙi dawowa tanan ya wuce gida?”.
Idanu ya cigaba da tsura mata tsahon wasu sakanni harta
fara kuka, ya ciza leɓensa na ƙasa yana mai haɗiye abinda ya
tokare masa maƙoshi. Gefenta ya kai zaune, tamkar mai bitar
karatu ya shiga maimaita kalaman baba a zahiri _“Iyyani za ta
shiryata kafin isowarsu ɗaukarta, nau'in turaren da yake a
cikin gidanka kawai nake buƙatar fitar ƙamshinsa daga jikinta.
Ta kuma sha iya adadin madara datake gidank.......”_
Kallonsa Ummu tai da share hawayenta a lokaci guda, cikin
rashin fahimta tace, “Mi kake son faɗa?”.
Kansa shima ya girgiza mata. “Ba dagani bane ba, Baba ne.
Amma na kasa fahimtar komai Jamaima. Ko ke kin fahimta?”.
Har zatace a'a sai kuma tai ɗan jimm idanunta masu
girma da su Iffah suka gada a kansa. Itama maimaita kalaman
tayi kamar yanda ya faɗa har sau uku, “Idanfa har na fahimta,
Baba yana nufin _Iyyani ta shirya Iffah da kanata, idan sunzo
da wani turare karmu bari tai amfani da shi, sannan ko taje
can an bata wani abu kar taci......, Kaga kenan daga nan mu
saka mata turaren, sannan mu bata abinci taci cikinta ya cika.
Mu kuma......”
Numfashi ya ja daga hancinsa a hankali ya saukar a
ƙirjinsa, itama ta sauke numfashin mai haɗe da zubar hawaye
sakamakon dakatar da ita da yay da hannu alamar ya fahimta
ba sai ta ƙarasa ba. duk da bawai nauyin da zuciyarsa tayi ya
ragu bane, ya dai samu sassauci daga kalaman Baba duk da
basu san manufarsuba kai tsaye. Sai dai bin umarninsa a
garesu tilas ne.......

★ Tsaf Iyyani ta shirya Iffah dake faman zubda hawaye
har yanzu cikin shiga ta alfarma kamar yanda Kaka ya bada
umarni. Wata haɗaɗɗiyar riga ce da akanga irinta kawai a
jikin hamshaƙan matan gidan sarauta na ƙasar ruman mai
kama da alƙyabba da ita kanta Iyyani bata taɓa sanin a kwaita
a gidansu ba Kaka ya kawo yace a saka mata. Duk da shirine
bana daɗin rai ba tayi ƙyau matuƙa. Ga wasu nau'in sirrika na
ƙamshi na tashi daga jikinta har suna hawa kai. Tsaff Ummu
da kanta ta shirya mata wasu abubuwa masu muhimmanci
nata duk da sun san zama ne na taƙaitaccen lokaci ga ƴar tasu
mace tilo data rage yanzu. Daga Babiy har Ummu zama sukai
suna mata nasiha, nasihar kuma gaba ɗayanta tafi ƙarfine
akan addu'a, ta kula da addininta, azkar, karatun alkur'ani kar
tai sakaci da su. Babiy da kansa ya ɗakko wayar Fariha ya bata
yace ta ɓoye kozasuna rinƙa jinta, baima san ta Arfa ma na
hanunta ba. Isowar jama'ar daular ruman ta katse zaman
nasu. Inda mayan matan da suka shigo gidan tare da rakkiyar
tawagar hadimai suka buƙaci a basu amarya da ruwa mai
ɗumi su shiryata. Kan Babiy a ƙasa ya basu amsa da
“A shirye take domin cika umarninku”.
Sosai mamaki ya bayyana a fuskokinsu dajin kalaman Babiy
da kuma fitowar Iffah da Iyyani ta riƙo suka fito. Baki ɗaya
daga cikinsu ta buɗe zatai magana wata ta girgiza mata kai
alamar kartace komai. Badan taso ba tai shiru, sai dai ta juya
ta fita tana mai danna wayar hanunta da alama wani take
ƙoƙarin kira.
Babiy da kansa ya kama hanun Iffah tare da akwatin
kayanta ƙarami har ƙofar gida gaban motar da aka tabbatar
masa itace ta ɗaukar amarya.. Da gayya Iffah tai gaba zata
kifa suna gab da fita a soron kamar tayi tuntuɓe da rigar
jikinta dake jan ƙasa. Da sauri hadimai mazan dake tare da su
sukai mata runfa da bayansu dan kar wanda yaganta, dan
kofar gidan dama cike yake da jama'a, cikin sauri ta gefenta
mai sanye da baƙar abaya harda niƙaf tai ƙoƙarin yin kamar
zata tarota suka duƙe tare, a hankali ta ɗan ɗago suka haɗa
ido, matar dake ƙoƙarin taimaka mata ɗin tai saurin kautar da
nata da sukai jajur tare da ɗaukar littafin da Iffah ta saki ƙasa
yayin da take kaiwa sunkuye. Miƙewa matar tai, itama Iffah
ta ɗauka envelope ɗin da matar ta saki ƙasa dai-dai Babiy na
ɗagota. Da baya-baya Sir Fawzan da yay ɓaddabamin shigar
mata cikin baƙar abaya da niƙab kamar hadiman masarauta
ya dinga jan jikinsa cikin mutane ƴan kallo har ya sulale gaba
ɗaya a wajen.....

*_DAULAR RUMAN_*

Wannan ne karo na farko da Iffah ta shigo cikin masarautar
daular Ruman. Duk da a cikin mota suke kuma har yanzu
hawaye basu daina zirara daga idaniyarta zuwa fiskarta ba
hakan bai hanata tsarkake sunan UBANGIJI ba, yayin da
motocin da suke a ciki suka gama keta katafaren gate ɗin
farko zuwa cikin masarautar mai matuƙar girma da hasashe
ko kintace bazai iya bayyanawa ba kai tsaye sai al'amarin ya
sake girmama zuciyata........✍

Tabɗi jan🙆🏻 Ga aure dai ya ɗauru tsakanin Tajwar Eshaan Bin
Haysam Abdull-Majeed. Da Fareedah Bint Zayyan. Shin itama
zata mutunne kamar sauran matansa ko zata tsira? Wacece
Uwa? Wacece Ta-ƙurya? Wanene shi kansa Tajwar Eshaan da
ƴan ƙasar Ruman baki ɗaya kema kallon Fir'aunan wannan
ƙarnin?.

Please Login or Register in order to submit comment