Reading Dauɗar Gora by Bilyn Abdull ce Chapter 8 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wata
lafiyayyar rigar alƙyabba mai tsananin ɗaukar hankali da aka
ɗinkata ta musamman domin Zawjata-almilki da kuma
wannan rana. Sai sauran kayan ado irin na hamshaƙan mata
da akayisu da zallar zinare da diamond.
Sun ɗanyi mamakin rashin samun kowa a sashen, saboda
sanin tunda safe an turo hadimai da zasu mata hidima.
Yanayin tsaftar sashen kuma ta tabbatar musu hadiman
sunzo. Tunanin ko itace ta sallamesu ya sakasu ture zancen a
zukatansu suka bama cikin hadiman umarnin wata ta nema
musu iso. Har hadimar ta nufi ɗakin da aka kai Iffah jiya ta
tsaya cakk sakamakon wani irin kakari da sukeji tare da ɓarin
fashewar abubuwa. Su dukansu dubansu suka maida ga
ƙofar, da alamun mamaki ɗaya daga ciki ta sake bama wata
hadimar umarnin zuwa ta duba. Minti ɗaya baima cika da
shigar hadimar ba ta dawo a guje numfashinta na fita da ƙyar
tana nuna ɗakin da faɗin, “Z...Z....Zawjata-almilki!......”
A kusan tare suka afka ciki. Su dukansu babu wanda bai
firgita da ganin Iffah dake layi hanunta na dama dafe da
ƙirjinta tana laluben hanya dana haggu ba. A dalilin laluben
ne taketa faman zubda abubuwan da aka ƙawata adon ɗakin
da su. Sakamakon hakan kuma duk ta jima hanunta ciwo sai
jini yake yi. Da zafin nama ɗaya daga cikin matan nan ta
riƙota cikin jikinta suna mai ambaton sunan ALLAH a tare.
Ganin yanda ta jiƙe sharaf ga jikinta yayi jajur abinka da fara
sai hankalinsu ya ƙara tashi. A fisge Iffah ta damƙo hanun
matar ta haɗa da nata takai kirjinta tana fadin,
“Ummu wuta, jikina zai babbake Ummu ki sakani a
kanƙara dan ALLAH karna ƙone. Zan mutu Babiy wuta tana
cin jikina....”
Gaba ɗaya kalamanta sake ruɗasu sukayi. Duk sun
daburce sunma rasa miya kamata su mata. Dan wadda ke
rike da ita har hucin zafin takeji a nata jikin itama. Ƙaramar
cikinsu ce tai ƙarfin halin fita da hanzari tana mai musu nunin
tana zuwa. Cikin sauri tamkar zata kifa ta nufi sashen Malikat
Bushirat. A yanayin data shigo ya saka Malikat ɗaga yatsun
hanunta dake ƙawace da jan lalle da adon zabban zinare biyu.
Tamkar ƙiftawar ido duk hadiman dake zagaye da ita suka
fice. Zaune ta tashi da ƙyau, idanunta akan ƴar uwar tata.
Cike da ƙasaita ta ambaci sunanta akan lips “Jasrah!”.
“Na'am Bari-Hamshira”.
“Mike faruwa kika shigo kamar an koroki”.
“Afuwan. Duk abinda kikaga ya koro ɓera daga wuta tofa
yafi wutar zafi ne. Wai kin san kafin zuwanmu har an kai mata
rigar alƙyabbar buɗar amarya ta saka, akwai babbar matsala
Bari-Hamshira, ga yarinyar mutane can a wani mawuyacin
hali”.
“Kamar ya?”.
Malikat Bushirat ta faɗa tana mai miƙewa zaune sosai da
sake ware ƙyawawan manyan idanunta akan Jasrah.
“Bari-Hamshira ba lokacin neman ba'asi bane wannan,
lokacine na neman hanyar ceto ran yarinyar mutane. In ba
hakaba itama zasu kashe mana ita kamar sauran na baya....”
Lokaci guda idanun Malikat Bushirat suka kaɗa sukai
jazur. A kallo guda zaka fahimci ƙololuwar tashin hankalin
daya tsargata. Da ƙyar ta iya ɗaukar wayar landline dake
gefenta hanunta na rawa, ƴan danne-danne tayi kafin ta
miƙama Jasrah. Da hanzari Jasrah ta amsa. Sanin kowa
Malikat zata iya nema a yanzun yasata kai tsaye ambaton
sunansa. “Ghazi! A tattaro duk wani mai magani dake a
daular ruman dama wajenta yanzu zuwa sashen Zawjata-
almilki ta uku”.
“An gama ranki ya daɗe”. Aka faɗa daga can cike da
tsantsar girmamawa....


★★_________★★

Ƙarar marin da azabarsa ya saka hadimar zubewa ƙasan
lallausan carpet ɗin dake katafaren falon. Sosai jikinta ke
tsuma tamkar mazari. Ga hawaye har rige-rigen sauka suke a
fuskarta. Kanta ta shiga girgizawa da sake gurfana a gabanta
sosai tamkar mai neman gafara...
“Ki gafarceni uwar-gijiya. Wlhy nayi iya yina domin ganin
mun mata turaren amma ta nuna sam bata aminta ba.
Wannan ba irin waɗan can na baya bane, akwai wani sirri mai
razani a cikin ƙwayar idanunta da taurin ka....”
Saukar wani sabon bahagon marin ya hanata ƙarasawa.
Ƙara dafe kuncin tai da hannu bibbiyu. “Ina neman gafara a
gareki bisa kuskurena Uwa- gijiya...” hadimar ta faɗa da sauri
tana mai ƙoƙarin gumtse kukan dake son kwace mata dan
harga ALLAH marin ya shigeta matuƙa.
Matar dake harɗe bisa kilisa tana cin inibi cike da ƙasaita
irin ta masu isa ta ɗaga idanu kaɗan ta dubi wadda ke tsaye
kusa da ita tana faman hura hanci, wanda marin ma itace ta
yisa daman. ƙyawawan idanunta ta juya a fuskar amintacciyar
hadimar tata, sai kuma ta janyesu ta maida a yanda take
tamkar batasan mike faruwa a wajen ba. Cike da girmamawa
hadimar ta ranƙwafa. “An gama Uwar-gijiyata. Umarninki
wajibine a garemu”. Kamar yanda bata motsaba a yayinda
hadimar ke kashe fuskar waccan da mari da neman afuwa a
yanzu ɗinma haka. Ga hadimar tata hakan ba sabon abune a
gareta, dan haka bata damu ba. Sai ma nuna waccan hadimar
dake gurfane tana sharar hawaye tai da ɗan yatsa da
kakkausan harshe.
“Shugabata bata yafiya, bata ɗaukar kuskure koda zaka
shekara dubu kana mata hidima kuskurenka ɗaya bazai taɓa
fansarka ba”.
“Innalillahi wa-inna ilaihirraji'un” Hadimar dake a
gurfanen ke faɗa cikin rawar jiki, ta sake kaiwa gurfane gaban
Uwar-gijiyar tasu tana kuka da hurwa irin ta masu neman
afuwa. Amma ko kallo bata ishetaba. Sai ma amintacciyar
hadimar nan tata ce ta kora ta waje tana mai sake kaimata
mari......

★★......

Cikin ƙanƙanin lokaci duk wasu masu ƙarfin faɗa aji akan
magani suka rufu a sashen Iffah da komai ke ƙara rikicewa.
Dan takai ƙoƙarin ma yaga kayan jikinta take saboda azabar
da takeji a jikin. Matan nan dake matsayin ƙanne ga Malikat
Bushirat sai faman zuba mata ruwa mai azabar sanyin da
taketa ambata suke suna hawaye amma tamkarma basa zuba
matan. Fatarta kam tayi wani irin masifar ja kai kace za'a
taɓata ta ɗashe ne da kanta. Dan tayi wani luguf-luguf tamkar
an dafa ganda taji wuta. Abin tausayi duk yanda Iffah ke son
ambaton sunan ALLAH bisa a zabar da takeji hakan ya gagari
harshenta. Sam ƙwaƙwalwarta da zuciyarta ma sunƙi
connecting wajen taimaka mata. Sunan Ummu da Babiy
kawai take ambata akan su zo su taimaketa zata ƙone......

*_MALIKAT BUSHIRAT_*

Diwa da jikinta ke tsuma kamar mazari ta zube gurfane
agaban Malikat Bushirat data saka aka nemota tun kafin a
sanar mata dalilin kiran. Gaisuwa ta mika cike da tsantsan da
kai. Sai dai daga Jasrah dake faman kai kawo a falon har
Malikat babu wanda ya amsa mata. Sai tarar numfashinta da
Jasrah tayi tare da jeho mata tambayar data nema sakata
sakin fitsari a bujenta.
“Bisa umarnin wa kuka aikata, kuma ke da su wanene?”
Kanta ta shiga girgizawa jikinta na rawa. “Wlhy ranki ya
daɗe bansan komaiba, taya za'a haɗa baki dani a aikata
wannan kuskuren. Sam ban san badaga nan aka turasuba, kai
tsaye ma suka shiga wajen Zawjata-almilki batare da sun jira
na musu iso ba saboda bana kusa. Amma wlhy wlhy banida
wani alaƙa ko sani akan wanda ya turasu, hasalima nayi iya
ƙoƙarina na ganin na kama ko ɗaya a cikinsu amma hakan ya
gagara saboda hankalina ya kasu biyu gashi sai ni kaɗai a
wajen”.
“Ƙarya kike yi? K kina ina suka shigan?”.
“Na rantse da UBANGIJI mai zartar da mutuwa akan kowa
iya gaskyata kenan ALLAH ya baki yawan rai, ina kan tattare
abincin da aka shirya mata ne da bata ci ba ma”.
“Zaki iya gane hadiman?”.
“Sosai ALLAH ya taimakeki”.
“Kafin cikar awa biyu muna buƙatar ku anan”.
“Da ikon ALLAH hakan ce zata tabbata”. Hadima Diwa ta
faɗa tana miƙewa da rawar ƙafa ta fice. Sai lokacin Malikat
Bushirat ta ɗago idonta, dan tunda Diwa ta shigo bata sake
motsawa a yanda take ba, duk maganar da sukai da Jasrah
ne.
“Bari-Hamshira! Karsu kashe yarinyar mutane itama. A
daren jiya harna fara murnar ALLAH yasa zuwan wannan
yarinya alkairine garemu, ALLAH yasa itace zata zama mana
hasken da zai haska duhun dake zagaye da mu saboda ganin
rashin tsoro a ƙwayoyin idanunta, Amma yanzu a wani
ɓangaren inajin matuƙar tsoron kar muna akan dokin zaton
wuta a maƙera ne kamar yanda mutanen gari ke ma Zaki. dan
gaskiya a yanzu gaba ɗaya komai neman ƙwacemun yake....”
Wani irin rumtse idanu Malikat Bushirat tayi mai nuna
alamar jin ɗacin zancen, sai dai kuma a duba na gaskiya ƴar
uwarta gaskiya ta faɗa, kuma da itane kawai take iya tattauna
irin waɗan nan matsalar tata taji sauƙi a ranta duk da ba ita
kaɗai bace ƴar uwarta mafi kusaci. Sai dai Jasrah itace
autarsu, ta kuma rayune a hanunta tamkar itace ta haifeta,
dan haka tasan bazata taɓa jifan tilon ɗanta da sharri ba
domin taji daɗi kamar yanda maƙiyansu keyi. Ita a karan
kanta mahaifiyarsa a kullum zuciyarta takan ɗarsa mata kodai
gaskiyane da sanin bahagon ɗan nata mai wahalar sha'ani da
fahimta ake kashe yaran mutane? Saboda al'amarin akwai
matuƙar rikitarwa da ban mamaki a cikinsa, amma a yau tana
fatan a wannan gaɓar su samu wani haske.....

★★________________★

Kai tsaye sashensu na hadimai Hadimar nan ta tasa
ƙeyarta, sai dai suna gab da shiga ta hango Diwa da wasu
hadimai maza masu ƙarfin faɗa aji a cikin dogaran sashen
Malikat Bushirat suna tattaro hadimai. Da sauri taja burki tare
da damƙo hanun hadimar baya. “K dakata, bana raba ɗayan
biyu ku ake nema kuwa”. Sake ruɗewa hadimar tayi, jikinta
sai faman rawa yake gab-gab abin tausayi. “Shugaba Azwa ki
taimakeni”.
“Na taimakeki ni kuma na tozarta. Kinga Jaza babu
wannan maganar, ki ƙarasa garesu zanyi duk abinda ya dace
naga kin ƙuɓuta, sai dai ki sani zaki bani wani kaso a cikin
dukiyarki. Kiyaye harshenki akan amsa laifin dake kaɗai ya
shafa shine tseratar da kanki. Kuskuren ambaton sunana
kona uwar-gijiya shine mutuwarki”.
“Na yarda wlhy, zanma iya mallaka miki komai da nake da
su shugaba Azwa”. Jajayen haƙwaranta ta washe. Tare da
kaɗa kai tamkar ƙadangaruwar data hango mage. “Baki da
matsala, hatta ga uwar-gijiya ma zaki iya tsira, dan haka
faɗamin inda kike ajiya”. Sosai Jaza ta aminta da maganar
Azwa. Dan tasan ita ɗin amintacciyace ga uwar-gijiyar tasu.
Domin duk wani aikin sharri sune suke mata shi a cikin Daular
Ruman. Sai dai bata raba ɗayan biyu akwai ire-irensu da yawa
a ƙarkashin ikonta.....
“Yauwa ga ɗaya nan a cikinsu”.
Cewar Diwa data hango Jaza na rabe-raɓe. A take hadiman
maza suka tasa ƙeyar Jaza tare da Diwa dake biye da su. Kaf
hadiman da abin ya faru a gaban su duk da basu san ainahin
abinda ya faru ba tausayin Jaza da sanin ta shiga uku ne keta
musu kaikawo a cikin zukata......

*_MALIKAT BUSHIRAT_*

Bayan wasu mintuna da batako nuna alamar tasan da
isowar su Diwa ba ta ɗago ƙyawawan idanunta da tsantsar
damuwa ta bayyana a cikinsu. Da sauri Diwa da hadima Jaza
suka sake risinar da kawunansu jikunansu na tsuma. Kallonsu
take tamkar mai neman amsar abinda ke ranta a cikin jikinsu,
kusan minti guda da wasu mintuna ta janye a hankali ta
maida ga Jasrah, sake janyewa tai ta sake maidawa ga
amintaccen hadiminta dake buƙatar umarninta.
“Bayan mintuna goma, a tabbatarmin da abinda nake
buƙatar ji daga garesu”.
“An gama Uwa goya marayu”.
Ya faɗa da tsantsar girmamawa yana mai zabga ma su Diwa
shimfiɗeɗiyar bulalar hanunsa a gadon baya. A zabure suka
miƙe su duka suna mai sosa bayan nasu kowanne idonsa cike
taf da ƙwalla. Ƙeyarsu ya tusa suka fice, Diwa na kuka da
rantsuwar bata san komaiba ita..........✍

16


........Cikin ƙanƙanin lokaci labarin abinda ke faruwa da
Zawjata-almilki ta uku ya gama gauraye daular ruman. A take
ko'ina yay tsit sai ƙus-ƙus da maganar ido kawai. Sauran
Zawjata-almilki kuwa guda biyu dake gidan dama kafin kawo
Iffah tuni sun sake shiga tsantsar tashin hankalin da yafi
wanda suke ciki. Su dai dama rayuwa suke cikin jiran
tsammanin isowar mutuwarsu. Ko lokacin da aka sanar musu
sake ɗaura auren Tajwar da wata matar tsantsar tausayin
kansune kawai ya baibayesu, yanzu kam jin halin da matar da
aka kawo jiya take ciki ya tabbatar musu suma mutuwarsu
tunkarosu take sakeyi kenan.......

Duk wata tuhumar data dace akan hadima Jaza da
sauran hadimai biyu da sukaje ɗakin Iffah suma da aka gano
anyi amma sunƙi faɗar gaskiyar wanda ya sakasu, sai cewa
suke Diwa ce. Yayinda Diwa ke rantsuwa da ALLAH tana kuka
akan ƙarya suke mata ita bata san komai ba. Iya jigatuwa sun
jigatu har takai numfashi da ƙyar sukeyi saboda azabartawar
da ake musu. Sanin rayuwarsu akafi buƙata a yanzu sama da
mutuwarsu yasa hadiman kurkukun dake a cikin daular
ruman tsagaita musu. Amintaccen hadimin Malikat Bushirat
ya koma ya sanar mata halin da ake ciki. Shiru kamar
bazatace komaiba. Sai kuma ta dubi Jasrah da har yanzu ke
tare da ita ta ɗauke kanta.
Jasrah data fahimci mi ƴar uwar tata ke nufi takai dubanta
ga hadimin. “Ghazi! A cigaba da tsaurara musu tsaro har
zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu”.
“ALLAH ya ƙara miki lafiya an gama”. Ya faɗa da tsantsar
girmamawa yana mai rissinawa da gyara takobin hanunsa ya
fice.......

*_ZAWJATA-ALMILKI_*

Tun Iffah na iya motsa jikinta da furta kalmar bakinta har
hakan ya gagara numfashinta ya fara neman barin jikinta. Ga
dai masu magani mata rufe a kanta mazan na daga waje suna
haɗo duk abinda ya dace amma babu alamar wani canji sai
ma ƙwaɓewa da komai ke nemanyi. Tun ana ƙirga awannin
iya shawo kan matsalar har komai ya fara firgita kowa. Daular
ruman tayi tsitt babu mai ƙwaƙwaran motsi a cikinta. Sautin
fitar kiran salla ma dan ya zama dolene. Koda aka idar da salla
ma sake komawa zaman jigum-jigum akayi domin kuwa
abinda bai taɓa faruwa a tarihin masarautar bane ya faru.
Tajwar Eshaan bai fito sallar zuhur ba yau. Hakama da la'asar.
Magrib ma ta shiga babu wanda yaji motsinsa. Zuwa lokacin
kuma akan Iffah an zubama sarautar ALLAH idone wadda ta
girma ta ɗaukaka.
Dan kuwa tana a shimfiɗene jiki duk ya ɗashe tamkar
wadda ta ƙone gurin yay ja kafin ya tashi. Kaɗan-kaɗan
numfashinta ke fita wanda shine kawai ya tabbatar da tana a
raye bata mutu ba. Masu magani kowa yayi iya iyawarsa sun
koma gefe ana jiran ikon ALLAH kuma. Ana idar da sallar
la'asar Malikat Bushirat ta bada izinin maida Iffah
sashenta.....

Kamar yanda Malikat Bushirat ta bada umarni an maida
Iffah sashenta, a kuma cikin ɗakin barcinta da babu wani
mahaluki daya taɓa shiga bayan Tajwar Eshaan da Jasrah.
Hakan ya bama dukkan hadiman sashen mamaki da tabbatar
da lallai wannan Zawjata-almilki ɗin tana da wata daraja ta
musamman ga Malikat. Dan kaf Zawjata-almilki da suka rasa
rayuwukansu a gidan babu wanda ya iya ganin makamancin
damuwar Malikat Bushirat irin ta yau. Ƙarin tabbaci har
hawaye sai da ta share na tsagwaron tausayin Iffah. Lallai
halin da Iffah ke ciki ta cancanci duk mai imani ya zubda mata
hawaye, dan sauran Zawjata-almilki na baya mutuwarsu
kawai akeji bayan kaisu turakarsa. Amma ita ko kaitanma
ba'ayiba, a kwana ɗaya tak da tai a gidan batare da an
kammala gagarumin taron bikin da aka shirya ba dominta
gata a halin da gara mutuwa da shi...
Bayan idar da sallar isha'i Malikat Bushirat na hakimce a
katafaren falonta na uku Malikat Ashwaq ta iso da tawagar
hadimanta duba Iffah. Malikat Ashwaq itace mace ta farko ga
marigayi Tajwar Haysam ibn Abdull-majeed. Hamshaƙiyar
mace ce data isa take kuma amsa suna Malikat. A ƙa'idar
Daular ruman matar data haifi yarima mai jiran gado a cikin
matan sarkice kawai ake kira da Malikat. Mafi yawanci kuma
ana samu ne daga matan farko. Sai dai ga Tajwar Haysam
hakan bata faru ba. Dan matarsa ta farko Ameera Ashwaq
bata taɓa haihuwa ba kamar sauran matansa, tadai taɓa
ɓarin ciki na wata huɗu daga shi kuma bata ƙara ba. A zahiri
mace ce isashiya mai baza mulkin da yafi na kowace mace a
gidan bayan malikat Bushirat, amma kuma bata da damuwa
sam. Ƙaryarka kace ga wani mugun halinta na zahiri saboda
tasan kanta. Rana ɗaya aka ɗaura aurenta dana Malikat
Bushirat matsayin Zawjata-almilki. Amma itace uwargida. Duk
da mulkinta Malikat Bushirat ta fita, ta kuma fita zafi da nuna
kishi a zahiri dan sam ita bata da haƙuri, hakan yasa ake
matuƙar jin tsoronta fiye da kowace Zawjata-almilki, dan
Malikat Bushirat ba kanwar lasa bace ƙwarai da gaske, sai dai
mace ce mai son ƙyautatama wanda yay mata da na ƙasa da
ita, hakan ya taimaka mata samun soyayyar hadiman gidan.
Haihuwar Miran (Yarima) mai jiran gado Eshaan tasa dole
sunan Malikat ya koma kan Malikat Bushirat. Wato Sarauniya
Bushirat kenan. Amma duk da haka sai Mahaifiyar Tajwar
Haysam mai suna Malikat Haseena ta bada umarnin cigaba
da kiran Ashwaq da suna Malikat Ashwaq. Hakan ya ƙona ran
Malikat Bushirat, sai dai babu yanda zatayi. Amma ta sake
tsananta kishin da takema Malikat Ashwaq ɗin fiye da da,
yayinda ita kuma Malikat Ashwaq ke nuna tamkar babu
komai a zahiri, amma a baɗini hummm....
Koda ta shigo Malikat Bushirat bata nuna tasan da
shigowar tata ba. Sai dai ta ɗagama hadimanta yatsu biyu da
ya sakasu rige-rigen fara barin falon. Zaune Malikat Ashwaq
takai bisa ɗaya daga cikin kujerun falon tanama nata hadiman
nuni dasu fita suma. Da sauri suma duk suka fice aka barsu su
biyu kawai. A hankali Malikat Ashwaq ta ɗan sakin murmushi
daya danne zafin yarfin da Malikat Bushirat ɗin tai mata, ita
ta fara gaisheta da tambayar ya mai jiki?. A daƙile Malikat
Bishirat da tai kamar zata basar ta amsa mata cike da isa.
Nanma Malikat Ashwaq dai murmushi kawai tayi da haɗiye
ɓacin ranta. Sosai ta nuna tausayi akan Iffah ta kuma mata
doguwar addu'a da bada shawarar mizai hana a kira likita ma
ya duba ta ko wani abune daban da wanda ake tunani.
Karan farko Malikat Bushirat ta ɗakko manyan idanunta
tai mata kallon tsakkiyar ido. Cikin yamutsa fuska taja
numfashi da fesarwa, “Haihuwar magajin Daular ruman daga
tsatson Malikat Bushirat rubutacciyar ƙaddara ce da duk yaƙi
da gwagwarmayar masu son daƙile hakan. A baya basuci
nasara ba, Taya suke tunanin samunta a yanzu kan
_Saifulmulk_ ɗi na?. Kamar yanda aka haifesa daga matsayin
gudan jinin Shahan-shan, Tajwar Haysam ibn Abdul-majeed.
Shima haka za'a samar da Ɗa daga gudan jininsa da izinin
UBANGIJI masu lissafi su fara...”
Muƙutt Malikat Ashwaq ta haɗiye yawun dake neman
kufce mata, a zahiri kuwa murmushi ta saki da ɗan girgiza
kanta. Batare da tace komai ba tai yunƙurin miƙewa domin
barin ɗakin tana mai ƙoƙarin danne zuciyarta dake
yunƙurowa. Har tayi taku biyu sai kuma ta tsaya, batare data
juyi ba ta saki murmushi. “Idan dai har Eshaan ya kasance
gudan jinin Shahan-shan ne babu gauraye, muma irin wannan
fatanne a bakunanmu garesa kasancewarmu uwaye a
wajensa. Fatan alkairi da samuwar lafiya ga Zawjata-
almilki.....”
Har tsakkiyar kai kalaman ƙarshe na Malikat Ashwaq suka
daki zuciyar Malikat Bushirat, sai dai kafin ta samu wani
damar fassarasu sallamar Ameera Danish-Ara da suka kusan
kiciɓus da Malikat Ashwaq ya dakatar da ita. Itace mata ta
uku ga Tajwar Haysam. itama da tata tawagar hadiman.
Kallon juna sukai da Malikat Ashwaq, Ameera Danish-Ara ta
saki wani malalacin murmushi a kaikaice. Sai kuma ta matso
cikin girmamawa ta gaishe da Malikat Ashwaq ɗin datai mata
kallo guda ta ɗauke kanta. Amsa mata tai cike da ƙasaita,
kafin ta matsa ta bata hanya ta shige, itama ta fice tawagarta
biye da ita.

Saɓanin Malikat Ashwaq ita ta samu tarba daga malikat
Bushirat. Dan duk da take mata itama ga Tajwar kuma
Malikat Bushirat kishiya a gareta hakan bai hanata risinawa ta
gaidata ba da matuƙar girmamawa tana mai tambayar jikin
Iffah. Malikat Bushirat dake kishingiɗe har yanzu a yanda
Malikat Ashwaq ta barta ta amsa mata da sassauci mai haɗe
da jimami. Cike da makirci Ameera Danish-Ara ke nuna
tsantsar tausayin Iffah tana mai yin ALLAH wadai ga duk mai
hannu akan waɗan nan al'amura.
Malikat Bushirat taɗan jinjina kai irin na ƙasaitattun mata
da yamutsa fuska kaɗan, a saman lips ta furta, “Nagode”.
A kaikaice Amera Danish-Ara ta ɗan saƙi murmushi tare da
harararta ta ƙasan ido. A zahiri kuwa zamanta ta gyara tare
da risinar da kanta. “Wannan abunda ya shafemune ai gaba
ɗaya ranki ya daɗe. Domin Zaki ɗammu ne, fatammu dai
ALLAH ya warware waɗannan al'amura cikin sauƙi”.
Har cikin zuciya Malikat Bushirat taji daɗin kalaman
Amera Danish-Ara, dan haka a lips ta amsa da “amin” tana
mai sauke ajiyar zuciya, dan bata cika samun damuwa da ita a
gidanba tunma sunada ƙuruciya. Amera Danish-Ara mace ce
mai tsananin kissa da ba lallai a lokaci guda ka iya gano
wacece ita ba. Duk da kasancewar ita Zawjata-almilki ce a
daular ruman zakasha mamakin irin girman da take bama
Malikat Ashwaq da Malikat Bushirat a gidan a zahiri tunda ta
shigo. Kai hatta da Amera Haifah dake amarya kuma ƙarama
a cikinsu ita bata taɓa bari saɓani ya shiga tsakaninsu ba a
zahiri. Wannan halin nata yasa sanda surukarsu Malikat
Haseena ke da lafiyar ƙafa take sonta da janta a jiki fiye da su
Malikat Bushirat. Wani lokacin har kwatance take musu da
halin Amera Danish-Ara ɗin wai suyi koyi ta fisu dattako. A
yanzu haka da take zaune babu lafiyar ƙafa Ameera Danish-
Ara ɗin tafi kowa sintirin zuwa dubata da mata hidima a
zahirance, duk da itama Malikat Bushirat na kamantawa sai
dai babu ruwanta da sai wani ya gani yace tayi.
Shiru falon ya ɗauka na wasu mintuna, Amera Danish-
Ara na son taga Iffah babu fuska ga Malikat Bushirat, dole ta
miƙe cikin ƴan kame-kame tana tambayar ko Amera Haifah
tazo kuwa?.
Kallon ƙasan ido Malikat Bushirat tai mata tana ƙara tsuke
fuska, dan ita duk yanda take da zafi babu wanda zaice ga
ranar data zauna maganar wani a cikinsu koda da su Jasrah
ne kuwa. A ganinta idan tai hakan sunma isa kenan a
wajenta. Murmushin yaƙe Amera Danish-Ara tayi cike da
basarwa. Sai dai ƙasƙantaccen kallon da Malikat Bushirat tai
mata ya matuƙar sokar mata zuciya. Taɗan risina da faɗin,
“Na barki lafiya ranki ya daɗe”.
Kai kawai Malikat Bushirat ta jinjina mata batare data ko
ɗago ba. Amera Danish-Ara ta cije baki da ficewa hadimanta
dake jiranta daga falo na biyu suka take mata baya.

Sam Amera Danish-Ara bata gaban Malikat Bushirat,
kalaman Malikat Ashwaq ne keta faman mata kaikawo a
zuciya musamman na ƙarshe. (Fatan alkairi da samuwar lafiya
ga Zawjata-almilki) waɗan kalamai bakwai a cikin tarin
kalaman Malikat Ashwaq sunfi komi tsayawa Malikat Bushirat
a zuciya. Dan kuwa tana fassarasu ne da wani abu daban ne.
Haka manyan mutanen masarautar suka cigaba da shigowa
duba Iffah daga sassa daban-daban na gidan. wasu iyaye ne,
wasu yayu, wasu ƴaƴa harma da kakanni maza da mata duk
da basu samun damar shiga ciki iyakarsu wajen Malikat
Bushirat. Bata damu kanta ba sai da dare yaja. Koda
hadimanta suka dawo sallamarsu tai dan tafi buƙatar kaɗaici
a yanzu saboda son ƙara tunani akan kalaman Malikat
Ashwaq da suka gagara haɗiyuwa a gareta. Da kuma nazartar
kowa daya shigo sashen nata domin duba Iffah. Tun tana a
zaune har takai ta miƙe tsaye hannayenta goye da bayanta
tana faman kaikawo tamkar mai safa da marwa..........✍

17


...........Dare yayi nisa, bakajin motsin kowa a daular ruman sai
sassanyar iskar dake kaɗa bishiyoyi kaɗan-kaɗan. Sai kuma
Hadiman da ake kira Ghazi a masarautar ne kawai ke faman
kaikawo domin bada tsaro ta kowacce kusurwa ta gidan
musamman a sashen Tajwar Eshaan.
Iffah dake kwance samɓal a katafaran gadon alfarma na
Malikat Bushirat idanunta a rufe kai kace batama numfashine
ta fara zabura a hankali kamar wadda ake mintsini. Jasrah ce
kawai tare da ita a ɗakin, tana daga gefe barci ya ɗan figeta
mai cike da wani irin mummunan mafarki. Wata gigitacciyar
ƙara da Iffah ta fassa tare da girgizar data saka gadon shima
rinƙa girgizawa yasa Jasrah farkawa a kiɗime. Tsalle tai gefe
jikinta na rawa ganin yanda Iffah da gadon ke girgiza, hatta
shi kansa ɗakin ji Jasrah keyi na mata rawa shida fitulun da
suka haskesa, dan sai daukewa suke suna kawowa. Wani irin
tari Iffah ta farayi mai tahowa da aman jini ta baka ta
hancinta harda ta kunne. Jasrah ta fara ƙwala kiran sunan
Malikat Bushirat a matuƙar firgice tana sake manne jikinta da
bango hanunta na laluben ƙofa amma ta kasa buɗeta...
Malikat Bushirat da dama ba barci take ba saboda tsabar
damuwa ta buɗe idanunta a hankali jin sautin muryar Jasrah
tamkar a sararin samaniya tana yawo. Cigaba da jin sautin ya
sata miƙewa zaune ta sauka a gadon baki ɗaya. Babu wani
hadimi dake da damar shigowa sashen ɗakunan barcinta sai
masu gyarawa kawai suma da safe ne, hakan ya sata ɗora
abaya kawai a saman kayan barcinta ta fito.... Jasrah da ta
gama fita hayyacinta gaba ɗaya ta faɗa jikin Malikat Bushirat,
rungume ƴar uwar tata tayi, a hankali ta shiga hura mata iska
a kunne tana bubbuga bayanta. Jasrah da ƴar nutsuwa ta fara
zuwa mata tai lamo tana sauke numfarfashi a jajjere, sai
kuma ta ɗago a hankali hawaye wanke da fuskarta...
“Mike faruwa?”.
Malikat ta faɗa a hankali. Ɗakin Jasrah

Please Login or Register in order to submit comment