Reading Dauɗar Gora by Bilyn Abdull ce Chapter 22 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganawa da ɗan nata, dan tun ana yi
iya su ahali har abu ya zagaye masarauta yana neman fara
fita waje.
Bayan mintinan da basu gaza talatin ba amsa daga Tajwar
Eshaan ta dawo ga Malikat Bushirat cewar baya buƙatar
ganawa da kowa. Ranta ya matuƙar ɓaci da wannan amsa,
dan take ta kori dukkan hadimanta ta shiga Safa da marwa.
Tasan kota kirashi bazai ɗaga ba, kuma tunda yace bai
buƙatar ganawa da kowan ta san halinsa har zuciya baya
bukatar hakan. A kaikawon nata Iffah ta faɗo mata a rai, babu
ɓata lokaci a karo na biyu ta bukaci ganinta duk da kuwa sune
sukai mata katanga da sake baro sashen Tajwar Eshaan tun a
waccan fitar acewarsu har sai ta cika kwanakin bakwai ciff.
Iffah na zaune a ƴar barandar da takan sha iska da
nazarin littattafan data maida hankali saƙon na Malikat
Bushirat ya risketa, ta ɗanji mamaki, amma sai ta shanye a
ranta kawai, dan tun washe garin kwananta na biyu Malikat
Haseenat ta kirata a waya da kanta ta sanar mata karta sake
cewa zata baro sashen Tajwar ɗin har sai kwanakin bakwai
sun cika. Haƙuri ta bada bisa kuskurenta, daga ranar kuma ta
haƙura duk da a takure take matuƙa da zaman, ganin ranta
zaita ɓaci ma a banza sai ta maida hankalinta ga nazarin
littattafan nan data ɗibo a books room, ko shi Tajwar Eshaan
ɗin ma sai ta ƙulla wasan ɓuya da shi, dan tun faruwar tashin
bomb ɗin nan ta riƙesa a rai, sai kuma maganar ɓatan Sayeed
Khairul-Bashar da a yanzu aketa dangantashi da shi ya ƙara
tabbatar mata da shi mutumin banza ne....
Cikin ƙanƙanin lokaci ta kimtsa, ta saka kamshin data
maida nata ta ƙarfi da yaji. Tana fitowa daga sashen ta samu
hadimanta na jiranta. Gaisuwarsu ta amsa a yau kam da
kulawa, kafin ta shiga motar da zasuje sashen Malikat
Bushirat ɗin a ciki duk da bawani uban nisa bane, amma
akwai tazara gaskiya. Sojan daya buɗe mata yay salute ɗinta
kafin ya maida ƙofar ya rufe, da sauri suma hadiman suka
shiga ɗayar motar bayanta.
A tafiyar da bata gaza mintuna biyar zuwa bakwai ba suka
iso, anan ɗin ma dai buɗe mata akai, yayinda hadimai ke
faman zubewa ƙasa bisa gwiyawunsu. Hannu kawai Iffah ke
ɗaga musu da sakewa. Tausayinsu da sake jin zafin wannan
mulkin iko na kasarsu a ranta. Tun a falo na farko tabar
hadimanta, inda amintacciyar hadimar Malikat Bushirat ta
karasa mata iso har inda take.
“Barka da yamma Mah-mah”.
Iffah ta faɗa cikin girmamawa ga Malikat Bushirat dake
hakimce fuska babu walwala. Hannu kawai ta ɗaga mata,
daga haka falon yayi shiru. Sai da ta gama shan kamshinta
kafin ta tashi zaune da ƙyau idonta akan Iffah da ta rissinar da
kai .
“Ibnati kin san miyasa na kiraki?”.
“A'a Mah-mah”.
Iffah ta amsata da sauri. Cikin ɗacin murya Malikat Bushirat
ta cigaba da faɗin, “Akan mijinki ne, nasan duk abinda ke
faruwa a Masarautar nan kin sani kema”.
“Hakane Mah-mah, amma sai nake ganin kamar ba
haka bane, kawai dai wasu ne ke son ɓata masa suna”.
Har cikin rai kamalan Iffah sun saka Malikat Bushirat jin
sanyi a rai, sai zuciyarta na rawa dan zuwa yanzu al'amarin
ɗan nata da gaske tsoro yake bata. Yayinda ita ko Iffah ta faɗi
hakanne da manufar wayon da ALLAH ya bata domin son
fahimtar abinda take son sani.
Malikat Bushirat ta katse mata tunani da faɗin, “Hakan
zai iya zama gaskiya, sai dai bazamu saki jiki ba dan da gaske
al'amarin mijinki na bani tsoro. A yanzu haka na bukaci
ganinsa amma shi yace bai buƙatar ganin kowa”.
Da mamaki Iffah ta ɗan ɗago ta dubeta, a ranta kam jinjina
rashin mutuncin sa take, a tunaninta ai ko kowa bai tsiraba
mahaifiyarsa ta tsira. “Mah-mah kuma shi ɗinne ya faɗa?”.
A karan farko Malikat Bushirat tai murmushin takaici. “Kar
kiji ko tantama akan hakan Ibnati. Dan duk yanda kike
tunaninsa ya wuce nan ɗin. A yanzu dai tunda ya nuna bai
buƙatar ganin kowan bazai gani ɗin ba. Shiyyasa na kiraki nan
dan kimin wani taimako na haɗani da shi ta waya”.
Yawu Iffah ta haɗiye muƙut, dan itama dai a karan kanta
kwanaki huɗu kenan bata sanyashi a ido ba. Tayaya kuma
zata haɗasu a waya. To wanda ma ya nuna kai tsaye bazai
haɗu da ita matsayin mahaifiyarsa ba ita kuma ƴar karere
taya zatai hakan?. Amma bara ta amsa mata kawai, dan koba
komai itama tana buƙatar jin gaskiyar lamarin ai.......

★★.......

Har lokacin kwanciya barci Iffah bata samu wata makamar
riƙewa na tunkarar Tajwar Eshaan ba. Hasalima bata da
tabbacin a inda zata samesa. Tambayar hadimai kuma tamkar
gazawace a gareta matsayinta na Zawjata-almilk. Kusan ƙarfe
ɗayan dare tana tsaka da kai kawonta da faman jan tsaki saƙo
ya shigo wayarta. Kamar zata share sai kuma ta ɗauka dan
koba komai kullum a cikin tsumayen ji daga su Babiy take.
Mamaki ya sata buɗe saƙon da hanzari ganin Malikat
Bushirat.
_Ina alfahari da kasancewar ki tare da gudan jinina Ibnati.
ALLAH yay miki albarka, yanda kika zama sanadin yaye
damuwata kema ALLAH ya yaye miki taki yanzu na gama
waya da shi_.
“What!!”.
Iffah ta faɗa cikin ɗan zabura tana sakin wayar akan carpet.
To mi hakan ke nufi? Ita da batama gansa ba taya har yay
kiran mahaifiyar tasa da har ta gamsu itace sanadi. “Anya
mutumin nan kuwa ba ifiritin aljani bane?”. Ta faɗa a zahiri
tana waige-waige a ɗakin da tunanin ko dai akwai camara, to
inma camara ɗin ce itada sukai magana a sashen Malikat
Bushirat ma ta ina camara ɗin zatai tasiri kenan...

Har waye war gari babu nutsuwata tattare da Iffah akan
wannan al'amarin, dan ko barcin kirki batayi ba sam. Sai dai
tuna a'a yau zata bar sashen ya saka mata ɗan jin sassauci ka
ɗan a zuciyarta. Tana ko idar da sallar asubahi ta taattara
kayanta waje guda tsaf tana jiran gari ya ƙara haske ta kama
gabanta duk da kuwa wata zuciyar na bata shawarar take
akan zuwa Tajwar Eshaan wai ko zata fahimci wata gaskiya
saɓanin wadda zuciyarta ke tabbatar mata. Amma dai ta dake
dan tana buƙatar damar keɓance kanta ko zata samu
nutsuwa.
A bisa al'adar masarautar kamar yanda ake kai Zawjata-
almilk turakar Shahan-shan haka ake zuwa a ɗakkota cikin
tattali da giramamawa tare da manyan ƙyaututtuka a randa
ta cika kwanaki bakwai cif. Kowa ya ɗauka tunda an kai Iffah
ba bisa ƙa'ida ba baza'ai wannan al'ada ba gareta musamman
yanda tama karya doka a kwana ɗaya ta fito. Ga kuma a
yanda masarautar take harmutse kwana biyun nan. Amma sai
Malikat Haseena ta bama kowa mamaki ta hanyar haɗa
komai na al'ada da akeyi, tare da mukulllin zabgegiyar mota
ƙirar zamani da masu hidima har guda goma, da tarin
turarurruka na musamman, Daneen Ammarah da tsaffin dake
da hurumin gudanar da al'adar a masarautar suka yima
sashen Tajwar Eshaan tsinke cikin busar sarewa mai tabbatar
da isar da saƙon manufar al'amarin.

Tofa wannan fa shine an tsokalo tsuliyar dodo. Dan kuma
masu rajin faɗa aji tuni sun sake buɗe shafin caccakar Tajwar
Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed da kakar tasa Malikat
Haseena kan basu damu da ɓatan Sayeed Khairul-Bashar ba.
Ko kuma ma dai sun san komai ɗin da gaske. Wannan al'ada
ta sake saka jikin Iffah mutuwa da shiga ɗunbin mamaki na
gaske, har aka maidata sashinta babu alamar tana cikin
cikakken tunaninta ma. Bin dai kowa take da ido tamkar
gunkiyar da aka ƙirƙira domin tarihi...

★Ashe duk wan can ƙarami ne a abin mamaki da Malikat
Haseena ta tanada a yau ɗin. Dan ƙarfe tara na dare da kanta
kamar yanda tayi akan Iffah ta sake jagorantar rakiyar ɗaya
cikin biyun Zawjata-almilk dake gidan tun kafin zuwan Iffah.
Duk da bata haɗu da Tajwar Eshaan ba yau bata dawo da ita
ba kuma dan acewarta zai ma gaji ne itama ya kulata idan ya
gama zaman kulle kansa a ɗakin kamar yanda zukatansu ke
basu sakamakon sanin hakan al'adarsa ce a duk sanda ransa
ke ɓace.
A wannan gaɓar kam kowa ya saki jiki waccan matsalar ta
shuɗe tunda ga Iffah tai kwanakinta lafiya ta fito. Maimakon
shiga fargabar rasata itama sai kowa ya ɓige da ƙananun
magana akan rashin dacewar hakan. Yau ɗin ma dai malikat
Haseenat tayi kunnen uwar shegu da su, yayinda Malikat
Bushirat da Daneen Ammarah suka shiga halin mamaki da
hukuncin na Malikat Haseenat a karo na biyu saɓanin dukkan
shirye-shiryen su. A wannan karon kam sun yanke ƙuirin tun
kararta suji ba'asi, sai dai sun barma safiya komai....
★★

Surutai akan ɗimuwar da aka wayi gari da shi a masarautar
ne ya farkar da Iffah dake fashin salla ɗan barcin daya figeta,
dama da ƙyar ta yisa sakamakon kwana da tai neman Sir
Fawzan da Sir Ajmaal a waya amma bata samesu a online ba
hakama a kira. Sai abinda ta karanta da yay matuƙar tada
hankalinta a ɗaya daga cikin littafan da take nazarta akan
Tajwar Eshaan. “Tabbas babu lafiya” ta faɗa a zahiri tana
miƙewa zumbur. Har ta nufi ƙofa ta dawo da sauri, toilet ta
shiga a gurguje ta watsa ruwa ta fito. Sama-sama ta kimtsa
jikinta ta fito. Hadiman ta da alamun sanyin jiki ya bayyana a
agaresu suka dinga zubewa gaisheta. Maimakon amsa ta jefa
musu tambayar da ruɗani ya bayyana kansa a cikin idanunsu
da jikkunansu lokaci ɗaya.
“Mike faruwa a masarautar nan? Da alama babu lafiya?”.
Duk sun rikice babu alamar wani zai amsa mata. Sai
kaɗuwa suke kamar masu jin sanyi. Halin da take ciki ya
assasa mata jin zafin hakan ta daka musu tsawa. Sake
firgicewa sukai, sai dai wajibi ne a gare su bin umarninta, dan
haka cikin ƙarfin hali wadda ke matsayin amintatta a gareta
ta sanar mata cewar an wayi gari da rashin Zawjata-almilk ne
ta farko da jiya ta kwana turakar Shahan-shan sai Sayeed
Khairul-Bashar shima da aka samu gawarsa a wani ɗaki cikin
masarautar. Iffah da bata san da hakan ba ta ƙame ƙam
alamar sumar tsaye ta wucin gadi ce ta risketa. Sai kuma
hajijiya ta fara juya mata falon da hadiman, a hankali duhu ya
dinga lulluɓe idanunta data kafa musu tabbacin bata cikin
hayyacinta..........✍️
44
..........A hankali ta shiga ƙoƙarin buɗe idanunta da takejin
sun mata matukar nauyi, sai kuma ta yunƙura ta tashi da ƙyar
tana mai bin ɗakin da kallo. Dishi-dishi take ganin
amintacciyar hadimar tata dake rukuɓe gefe ta zabga tagumi,
_(An wayi gari da rashin Zawjata-almilk ne ta farko da jiya ta
kwana turakar Shahan-shan sai Sayeed Khairul-Bashar shima
da aka samu gawarsa a wani ɗaki cikin masarautar.)_
kalaman hadimar na ɗazun suka shiga dawo mata tiryan-
tiryan a zuciya. Da karfi ta rumtse idanun nata da sukai jajur,
ga kanta dake matuƙar sara mata kamar zai rabe biyu. Amma
haka ta yunƙura ta sauka a gadon cikin ƙarfin hali da jarumta,
dan idan batai amfani da wannan lokacin ba tabbas damarta
ta kuɓuce mata kenan, batajin kuma zata sake samun wata
cikin sauƙi. Zumbur hadimar ta miƙe itama tana mata sannu,
bata iya amsa ta ba, sai nuni da tai mata ta je. Jiki a sanyaye
ta fice, ita kuma ta jawo mayafi ya naɗama jikinta.
Hadimanta dake falon farko duk suka miƙe, hannu ta
ɗaga musu alamar bata buƙatar rakkiyar ta fice ita kaɗai dan
babu yanda zasuyi. Da gaske masarautar a hargitse take
matuƙa, duk da ba wannan ne karo na farko da aka rasa
Zawjata-almilk ba, sai dai haɗi da mutuwar Sayyid Khairul-
Bashar ta sake girmama ta Zawjata-almilk ɗin itama a
wannan karon, da kuma tsallakewar Iffah da aka fara kaiwa
babu abinda ya sameta. Cikin dabara da amfani da
harmutsewar gidan tai amfani wajen kutsa kai sashen
Shahan-shan. Zuwa yanzu fuskarta ba ɓoyayyar fuska bace ga
masu tsaron sashen, dan haka babu wanda ya dakatar da ita
sai ma gaisuwar girmamawa da suke miƙa mata duk da ganin
nata ya basu mamaki. Su kansu hadimai masu girka abincin
Tajwar Eshaan ɗin data samu a falo na uku saɓanin na karshe
da ta san suna zama ganinta ya girgizasu, musamman daya
kasance har yanzu ba'a fita da gawar Zawjata-almilk ɗin ba.
Hasalima babu wanda yaga Shahan-shan har yanzu balle jin
motsinsa. Kamar yanda tun a ƙasa bata tanka gaisuwar kowa
ba anan ɗin ma bata kulasu ba dan ganinsu ya tabbatar mata
anan abun ya faru kenan, ita wannan Zawjata-almilk ɗin a
ɗakunan barcin falo na uku aka ajiyeta. Duk da bata san ya
suke ba babu ko ɗar tattare da ita ta shige abinta inda take
kyautata zaton ɗakunan barcin nan ɗin suke.
Ido rufe take bin ɗakunan ɗaya bayan ɗaya, sai dai har
kusan uku duk a rufe suke, bata gajiya ba ta cigaba sai a na
biyar ta samu a buɗe. Cikin rawar jiki ta afka ɗakin, yayi kaca-
kaca tamkar anyi dambe a cikinsa, dan wasu abubuwan ma
duk gasu anan a fashe ƙasa, sai ɗigo-ɗigon jini ta wasu
wajajen da dama. Idanunta suka sauka akan ƙyaƙyƙyawar
budurwar da a shekaru zata iya zama sa'ar Arfa shimfiɗe a
ƙasa ta jikin gado. Yanda gashinta da jikinta ke a birkice zai
tabbatar maka da ta jigata matuƙa kafin ta rasa ranta, dan
hanunta na dama dake kaca-kaca da jini riƙe yake da wata
kwalbar filawar doco... Alamar ta riƙe domin kare kanta,
amma duk da haka sai da akaci galaba a kanta. Iffah da jikinta
ke karkarwa ta durƙushe hawaye na rige-rigen sakko mata,
dan ji take kamar Fariha da Arfa ne take kallo kwance. Ta jima
tana kuka akan gawar kafin ta zabura sakamakon maganganu
da takejin suna tunkaro ɗakin, zumbur ta muƙe ta fara daukar
video recording ɗin ɗakin har gawar, sai kuma ta ɗauka hoton
gawar ta kowacce kusurwa. Jin shigowar za'ai da gaske tai
saurin fara neman wajen ɓuya....
Miran Jasim, tare da Miran Arshaan, shugaban jami'an
tsaron masarauta, Daneen Ammarah sai Malikat Bushirat da
a wannan karon ta kasa haƙuri itama suka shigo. Sai da suka
gama bin ɗakin kaf da kallo kafin su ƙarasa kan gawar. Shiru
babu wanda ya iya magana a cikinsu har tsahon wasu
mintuna kafin shugaban jami'an ya nisa.
“Exactly kisan irin na baya ne dai babu wani banbanci
gaskiya, da alama kuma tayi ƙoƙarin kare kanta itama shine
dalilin kasancewar ɗakin a haka harma da wannan jinin”.
“Wannan lamari daban mamaki yake, taya za'ai kisa
amma babu wani alamar yanda akayisan, a wannan karon
kodai za'a canja likita ne? Dan dole dole akwai abinda yake a
ɓoye. Yarinyar nan itace ta goma sha biyar da aka rasa, kisan
kuma iri ɗaya babu wani bambanci sai kace abun tsafi”.
“Haba haba wane irin kuma tsafi? Jasim Akh. Dole dai
akwai abinda bamu sani ba ɗin kam gaskiya”.
“Zancena nakan hanya Ukhti Ammarah. Idan ba aikin tsafi
ba mi zamu kira wannan al'amarin ne? Bagashi ita waccan da
yake ta gagara ko kuma wani abu daban ta tsira babu abinda
ya sameta ko ciwon kai ba”.
“Inaga yanzu duk ba lokacin yin wannan maganar bane,
ayi abinda ya dace, a wannan karon kuma ya kamata Abni
yace wani abu bawai ya cigaba da yin shiru ba kamar yanda
ya saba”.
“Maganarka nakan hanya Miran Arshaan”. Miran Jasim ya
faɗa cikin son sake tabbatar wa. Shiru Daneen Ammarah da
Malikat Bushirat basu tanka ba, hakama jami'in yanata cigaba
da zagaye ɗakin alamar nazari.. duk wannan al'amari Iffah na
maƙure a maɓoyarta tana sauraren komai hannunta danne
kan bakinta kar kukan da take ya fito har su farga da ita. Koda
suka gama abinda suke bayan shigowar doctor da fitar da
gawar kasa fitowa tai, sai dai ta zame ƙasa da sake fashewa
da wani irin kuka mai ban tausayin dan mutuwar yayunta
biyu ta dawo mata ne a rai sabu a yau ganin ta hanyar da
suma suka rasasu a zahiri gabanta......
“Kuka bashi zai kuɓutar dake ba kema...”
A razane Iffah ta buɗe idanunta dake kaca-kaca da hawaye
gasu jajur. Miran Jasim da tun ɗazun ya lura da ƙafar Iffah
amma ya basar har sai da suka fice yayo sau da baya ne a
gabanta. Duk da so ɗaya ta taɓa ganinsa ranar liyafar cin
abinci da aka kawota nan hakan baisa ta shaida fuskarba a
ɗan fisge.
Kai ya jinjina mata cikin ɗage kafaɗu “Yanda ya kashe na
baya kema babu tantama hakance zata kasance. Karki ga ya
ƙyaleki zata iya yuwuwa shirinki na musamman ne. Amma in
har kin shirya kuɓuta daga tarkon sa ni mai iya taimaka miki
ne”.
Iffah dai kallonsa take kamar gunkiya, sai hawayen da suka
kasa tsaya mata ne kawai ke tabbatar da ita a mai numfashi.
Bai nuna ya damu da yanayin nata ba ya cigaba da faɗin.
“Ni sunana Jasim Ibn Abdull-Majeed Aliy. Ƙani ga
mahaifin mijikin kenan. Nasan kina buƙatar sanin abubuwa
masu yawa akansa amma kinƙi samun kowacce irin dama
saboda iyayensa dake zagaye da ke. Duk yanda kike zaton
abin ko tsammani ya wuce nan, Malikat Haseena da Malikat
Bushirat da kike gani sun san komai game da mutuwar
matansa, hasalima da taimakonsu komai ke gudana, zaki iya
lura da hakan a yanzu ta yanda duk muka nuna damuwa
amma su ko'a jikinsu. Abinda zai tabbatar miki da sun sani
kuwa duba da abinda kika ganema idonki ne, taya za'a kashe
mutum amma a kasa gane hakan, sannan kuma a sake kawo
masa gobe ta mutu hakan baisa an dakata ba. Waɗan nan
likitoci da jami'an da kike gani duk an siyesu ne, shiyyasa suke
pretending cewar basu san komai ba ko basu gane komai ba.
Koda yake su a zahiri bazasuga komai ɗin ba, dan ana kashesu
ne ta hanyar tsafi domin ƙarama ƙarfin mulkinsa iko.....” yaja
numfashi tare da fesarwa idonsa a kanta yana nazartar
yanayin tasirin da maganarsa ke samu a wajenta. Da alama
akwai nasara dan haka ya cigaba da faɗin, “Mu ajiye wannan,
dan bashi da amfanin cigaba da faɗa miki. Ko kin san
mahaifinki da ɗan uwanki ma anyi amfani da jininsu a
maimakon naki shiyyasa ke kika tsira saɓanin wannan”.
Zabura Iffah tai jikinta na rawa. Sai dai ta kasa faɗin abinda
ke son fita a bakinta. Ya ɗaga mata hannu da faɗin, “Kinga
kwantar da hankalinki, amshi wannan ki kalla. Idan kin
kammala sai ki yankema zancena hukunci. Amma ki sani
tabbas ta hanyar da aka halaka iyayen nan naki da ita ake bi
wajen halaka waɗan nan matan nasa shiyyasa likitoci basa
gane komai na barki lafiya..”

Harya ɓacema ganinta Iffah bata iya ta motsa ba, sai dai
rawar jikinta da karkarwa a bayyane take. Jin kamar motsin
mutane ya sata ɗaukar flash ɗin daya ajiye mata ta sake ɓoye
wa. Jami'in ɗazunne ya dawo ɗakin, a wannan karon sun
ɗauka hotunan komai a ɗakin da ɗan sake bibbincikawa dan
tare yake da yara biyu jami'ai suma. Dole Iffah ta sake lafewa
har suka fice sannan itama ta fito.

★ A yanzu kam masarautar a harmutse take fiye da
ɗazun, hakan ya sake bama Iffah damar komawa sashenta
cikin matuƙar tashin hankalin abinda ya faru da zantukan
wannan mutumi. Kulle kanta tai a ɗaku ido rufe ta saka flash
ɗin a jikin laptop ɗinta da bawani amfani dake da shi ba. Abin
tamkar wani film video ya fara da shigar Babiy riƙe da Abu
Moosa cikin gidansu a waccan ranar, shimfiɗa tabarmar
Ummu da bayanin Abu Moosa da bai kammala ba har
mutuwarsa. Zuwan matar Abu Moosa da jami'an tsaro abinda
Hanash yay mata da tafiya dasu. Daga nan ya yanke. Da sauri
tai playing na gaba. A yanzu kam su Babiy ne a mawuyacin
hali duk sun rame sunyi baƙi a cikin wani ɗaki. Kan Babiy a
saman cinyar Hanash alamar babu lafiya tare da shi, Hanash
nata faman shafa masa ruwa a fuska yana kuka. Sautin dariya
ne ya fara tashi a ɗakin, kafin shigowar wani mutum da iya
jikinsa kawai ake gani babu fuska. A take su Hanash suka
zabura yayinda sautin dariya ke tashi da tafa hannayen
mutumin. Bayan anyi dariyar mai tsawo aka tsagaita, ƙirjinta
yay wata irin bugawa jin muryar Shahan-shan. “A tunaninku
bayan samun tagomashi a jinin yaronku ƴan baiwa zan
haƙura ne. Ina bazai yuwuba, dan a kaf yaran dana halaka
jinin ƴaƴankune na farko daya bani fiye da nasarar da nake
buƙata, shiyyasa na fara bibiyar ta uku daku kanku saboda
bincikena ya nuna min daga jinin ubansu ne”. Hhhhhhh!
Hhhhh!! Kune nasarata ahalin Zayyan. Kune nasarata dole ne
kuma na samu hhhhhhh!!!”.
Kuka Hanash keyi da roƙonsa amma babu alamar zai
sauraresa. Sai ma wani irin salon siddabaru da yakeyi da
hanunsa a take ɗakin ya turniƙe da hayaƙi, sai kuma wata irin
guguwa mai ƙarfi ta nannaɗe hayaƙin a tsakkiyar ɗakin. Su
Babiy dai tuni sun maƙure a bango. Sai kuma suka shiga ihu
ganin guguwar ta zama wani irin maciji daya kusa cinye kashi
ɗaya bisa ukun ɗakin, sara ya fara kaima su Babiy da suka
dunƙule waje ɗaya shi da Hanash, kafin macijin ya kafa kansa
a wuyar Hanash dake ƙanƙama Babiy. Tuni duhu ya gama
mamaye jikin Iffah dake karkarwa, ta rufe laptop dan zuwa
yanzu ma kukan ya kafe ƙaf a idanunta. Sai wani irin
mahaukacin ja da sukayi kai kace wuta aka haɗa a cikinsu.
Tun tana iya jin surutan masarautar har ta daina jin komai.
Daga haka sai farkawa tai ta ganta a gadon asibiti Daneen
Ammarah tare da ita..
Gaba ɗaya ta tsani komai daya shafi Tajwar Eshaan. Dan
haka tun buɗe idon farko da tai ta ga wadda ke tare da ita
bata sake yarda ta buɗe ba. Hakan yasa Daneen Ammarah
bata san ta farka ba. Dama itama kuma tayi matuƙar nisa ne a
cikin tunani a kallo ɗaya ma zaka fahimci bata tare da
nutsuwarta. Ga wata ƴar rama ta yini ɗaya sakamakon tashin
hankalin da ake ciki tattare da ita. Dan tun kai gawar Zawjata-
almilk da Sayeed Khairul-Bashar makwanci ba daular ruman
kawai ba gaba ɗaya ƙasar ruman a harmutse take. Yau wasu a
cikin talakawa sunyi ƙarfin halin fitowa zanga-zanga a wasu
jahohin suna kiranyen Shahan-shan ya sauka ko su ɗauka
doka a hanunsu.
Fitsari daya takura Iffah ne ya tilastata tashi har Daneen
Ammarah ta farga. Da sauri takai hannu ta riƙota tana mata
sannu, dauriya kawai Iffah tai na dannewa dan tunanin datai
a ɗan farkawar nan Tata zuciyarta ta bata shawarar ɓoye
sirrin ranta domin samun cikar burinta. Dan tayi alkawarin a
wannan karon sai ta halaka Shahan-shan, ta riga ta ƙuna bata
tsoron mutuwa. In har burinta ya cika danta mutu ba komai
bane a gareta a yanzu ma tafi buƙatar mutuwar fiye da
rayuwa tunda har ta rasa sauran ahalinta kuma miya rage
mata.
“Ya akai na zo nan Mamy?”.
Ta faɗa cikin danne komai dake ɓoye a ranta. Daneen
Ammarah da farin cikin farkawar Iffah ya sata sakin
murmushi yaƙe da ita kuma Iffah ta fassara da wani abu
daban ta amsa mata da faɗin, “Sakamakon abinda muke
tunanin ya rikeki aka sameki a sume shine aka kawoki asibiti,
amma Alhamdullah tunda gaki kin farka”.
Maimakon ta amsa mata wannan zancen sai ta jefa mata
tambaya. “Mamy da gaske ta mutu ko?”.
Take idanun Daneen Ammarah suka cika da hawaye.
Cikin ɗaci tace, “Sun kasheta Ibnati, sun sami damar da suke
buƙata akansa. Gaba ɗaya ƙasa ta harmutse da bore akansa
kamar yanda dama suke son cimma buri”.
Iffah ta ɗan lumshe ido ta buɗe zuciyarta na karajin tsanar
Daneen Ammarah ɗin da mamakin salon yaudararsu, amma a
zahiri sai itama ta marairaice fuska. “Mamy ban fahimta ba?”.
Hawaye Daneen Ammarah ta share, “Ibnati a yau ruman
baki ɗaya a harmutse take, talakawa nata zanga-zanga a
wasu jahohin akan sai Abni yayi murabus a kujerar Shahan-
shan inba hakaba zasu ɗauki mataki. Gashi tunda abin nan ya
faru babu wanda yaga idonsa ya kulle kansa a ɗaki anyi-anyi
ya buɗe yaƙi”.
Iffah ta rumtse idanu da karfi tana taune lips ɗinta,
yayinda take faɗi a zuciyarta da kakkausar murya. (Ni zan
ƙarasa musu aikin da kawo musu ƙarshen matsalarsu. Dan ba
murabus kawai ya cancanci yi ba mutuwa gaba ɗaya yabar
duniyar ya cancanta da shi ba kujerar Shahan-shan da ƙasar
ruman kawai ba)..........✍️
45



........Daneen Ammarah dake tunanin yanayin ma Iffah
tashin hankaline kawai sai ta shiga rarrashinta. Dole Iffah ta
cigaba da pretending da matsawa a sallameta taji sauƙi.
Daneen Ammarah na rakata sashen ta wuce dan jikin Malikat
Haseena ma dai babu daɗi sam. Dama Daneen Ammarah ɗin
ta zauna da Iffah ne domin saka ido kar wani ya cuta mata
itama. Hakan yama Iffah daɗi, dan ya bata damar nutsuwa a
kallon videon data ɗauka ɗazun. Sosai tai zooming gawar
Zawjata-almilk tana kai bin jikinta ta inda yake a waje daki-
daki. Wata irin zabura tai ganin abinda take ma ɗin kuwa a
saitin wuyan gawar ta gefen kunenta na haggu. Wato alamar
ɗigon sarin maciji har biyu. Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un
take ambata wata irin zufan na keto mata, dan kuwa tabbas
zancen mutumin can ya zama gaskiya. Amma duk da haka
tana buƙatar sake tabbatar wa. Cikin rawar da jikinta ke mata
ta shiga laluben number ɗin Sir Fawzan. Bugu ɗaya kuwa ya
amsa kasancewar dama a jirace yake da kiran, dan ya

Please Login or Register in order to submit comment