Reading Dauɗar Gora by Bilyn Abdull ce Chapter 3 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗayansu
ta haɗa ta dallama harara da manyan idanunta masu matuƙar
haske tamkar madara.
“Kai malam baka san darajar mutane bane?....” Zazzaƙar
muryarta mai taushi da nutsuwa a cikinta ta daki
kunnuwansu cikin faɗa babu ko ɗigon tsoro a tare da ita.
Batare data damu da yanda suka zuba mata ido ba ta
murguɗa musu bakinta da sake dalla musu harara ta cigaba
da masifarta, “Ka kusan bige yaro amma tsabar kanka ba'a
daidai yake ba shine koka fito kaga yaya yake ma saboda ku
masu kuɗin nan ɗaukar talaka kuke baida banbanci da titin da
kuke gurza tayoyin banzayen motocinku da kuka saya da
kuɗinmu”.
“Kai!”.
Drivern ya faɗa da maɗaukakin mamaki Iffah.
Harara ta sake dalla masa da zira hannunta ta zare key ɗin
motar daya riga ya kashe tun ɓuɗe musu murfin da tayi.
“K! K! Dalla bani key kajimun fitsararriyar yarinya kinga
mun taɓashi ne?”.
“Anƙi a bakun, wlhy duk sai kun fito kun dubashi kun bama
kakarsa haƙuri zan baku key ɗin nan, inba hakaba sai dai mu
kwana anan.”
Hannu saurayin ya kai da nufin warto key ɗin taja baya, sai
dai duk da haka saida yaɗan taɓa skirt ɗinta kaɗan. Cikin
matsanancin ɓacin rai ta jinjina yatsarta a kan fuskar
matashin tamkar zata tsone masa ido. “Idan hanunka ya sake
gigin taɓa koda hijjab ɗin jikina ne sai na karyashi, Sannan
koda Shahanshan ne yay wannan aikin bai isa barin wajen
nan ba balle kai shashasha driver”.
“K!!”.
Na gefensa ya faɗa cikin matuƙar waro idanu. A karan farko
wanda ke hakimce zaune a sit ɗin bayansu lap-top a cinyarsa
da tarin takardu a gefe da gefensa ya ɗago ƙyawawan
idanunsa dake tattare da matsananciyar gajiya da ƙosawa
yana yamutsa fuska. Baya ganin yarinyar, sai dai duk abinda
take faɗa raɗam a kunensa zazzaƙar muryarta ke sauka. Baiko
kalla yaran nasa ba ya sauke Lap-top ɗin dake cinyar tasa tare
da kai hannu ya buɗe murfin. A tare suka zabura, sai dai kafin
suyi wani yunƙuri harya fita a motar. Dolo suka fito suma da
sauri...........✍

5

........Kama hanun yaron da Iffah tai da nufin subar wajen duk
da key ɗin motar mutanen har yanzu na'a hanunta yay dai-
dai da isowar wani nutsatstsen taku mai tafiya da sassanyan
ƙamshin turare tamkar shi kaɗai iska ke tsintowa tana
busawa a hancinan mutane. Kamar wani magic wajen yay
tsitt na wasu sakkani, tsirarun mutanen da suka taru a wajen
tun furuwar abun duk suka zuba masa idanu. Ita kanta hajiya
Iffah mai masifar ƙirjintane yay wata irin harbawa lokacin da
mutumin ya sauke nasa lulu idanun cikin tsakkiyar nata. Da
ƙyar ta iya fisgar su daga cikin nasa tana ɗan murguɗa baki da
sauke niƙaf ɗinta cike da dakiya.
Idanun nasa ya janye daga kanta shima da matsawa gaban
yaron ya kai tsigunne dai-dai tsayinsa dan ya fara ɗauka
yarinyar nan aljanace ma dai kawai. Cikin sassanyar muryarsa
mai zurfi da nutsuwa ya motsa lips ɗinsa kaɗan tamkar an
fisgo maganar.
“Kana lafiya?”.
Kai yaron ya gyaɗa masa.
Ya ɗan ɗage gira da motsa bakinsa kamar zai taɓe. “Uhhm!
minene sunanka?”.
“Amjed”.
Yaron ya faɗa cike da kwarin gwiwa.
A hankali ya sake kaɗa fararen idanunsa tare da jinjina
masa👍🏻 ya saki wani sassanyan murmushi a karon farko da
jan kumatun yaron. “Oh my Friend! nice name. Kana sona da
aboki?”.
Da sauri yaron ya jinjina kai yana washe baki. Idanunsa ya
ɗan sake fiddowa suka ƙara girma tare da ƙara sakin
murmushi. Ya riƙo hannu yaron alamar suyi musabaha.
Al'amarin ya birge mutane da yawa, duk da babu wanda
yasan wanene shi, amma ko makaho ya kalla wannan mutumi
yasan babban mutum ne. Suit ɗin dake jikinsa farare tas ma
kawai abin kallone. Balle shi a karan kansa daya kasance
ƙyaƙyƙyawan gasken fatarsa da gogewarta har ɗaukar idanun
mai kallo take. Ga wani ƙamshi na musamman mai saka
nutsuwa ga mai shaƙa, yanayin kamewarsa da cikakkiyar isa
irin ta manyan mutane ke ƙara kawata kwarjininsa da cikar
kamala ga duk mai kallonsa.
A karo na biyu suka sake haɗa ido da Iffah dai-dai ya gama
gaida kakar yaron nan da keta faman washe baki da jera
masa godiya dan kuɗine dunkulallu sabbi ƙal ya damƙa a
hanun Amjed. Harara ta balla masa da janye idanunta da
sauri saboda wani abu mai tsananin sanyi taji yana tafiya
daga ƙafafunta har saman kanta. Cike da takunsa na nutsuwa
da ƙasaita shima ya juya ya bar wajen kai kace akan dole yake
taka ƙasar saboda takun zaratan maza masu cikakkiyar isa da
lafiya ce tattare da tafiyar tasa. Iffah ta jefama ɗaya daga
cikin samarin nan biyu key ɗin motar, dan ɗayan ya tafi da
hanzari ya buɗema ogansu ne. Dai-dai zai shiga ta ballama
wanda ta jefama key ɗin harara da faɗin, “Daga yau ko daga
nesa kuka hangoni to ku canja hanya koda a jirgi kuke kuwa”.
Shigar maganar tata a cikin kunensa dai-dai zai shiga
motar da aka buɗe masa ya ɗan ɗago idonsa, sai dai wadda
ya ɗago da nufin kallar da mamakinta ke cin ransa tuni ta nufi
barin wajen tamkar ba ita ta haɗa dabar wajen ba... Suna
ƙoƙarin shan shataletalen titin idanunsa ya sake sauka a
kanta ta miƙe titi tana tafiyarta a nutse, sai dai fuskarta a rufe
take da niƙab data saki tun bayan haɗa idonsu na farko....


🤔Wannan ƴa ta Babiy wataran sai ta saka an mata
dukan sakwara a titi in har bata canja hali ba😬🚴🏼.

★★......★

“Badai a ƙasa kika tahoba auta? Na ganki a gajiye tamkar an
koroki”.
Zubewa tai a taburmar da Ummu ke zaune, tare da ɗora
kanta a cinyarta tana ƙara narke fuska. “ALLAH a ƙasa na taho
Ummu. Haka kawai naji ina son na taho a ƙafan”.
“Ai gashi nan duk kin gajiyar da kanki, dama keba wata
isashshiyar lafiya ba. Tashi kiɗan watsa ruwa dan sai warin
rana kikeyi”.
“Kai Ummu warin rana fa?”. Tai maganar a shagwaɓe da
kamo rigarta ta kai hancinta. Miƙewa tai tana tura baki gaba
da faɗin, “ALLAH Ummu kinso dai yarfanine amma ƙamshin
ma turare nakeyi”.
Murmushi kawai Ummu tai da girgiza kanta, ita kuma ta
shige ɗaki sai faman cika baki take da iska a dole taji
haushi.....

★Da daddare suna zaune a tsakar gida cikin hasken
farin wata daya raba Hanash na koyama Iffah aikin
makaranta. Daga gefensu Ummu da Babiy ne zaune yana cin
abinci. Hira suke jefi-jefi akan kayan lambunsa da zai fidda a
ƙarshen satin nan ga ƴan kasuwa. Iffah tai karaf jin Babiy yace
zuma batayi kirki ba wannan karon bazata wuce tulu biyu ba.
“Babiy sai a bar mana mu shanye kawai a gida. Kaga dama
Ummu zatamin alkakin saukar islamiyyarmu nan da wata
biyu”.
Murmushi Babiy yayi, “Zanso haka Ibnati, sai dai bazai
yuwuba dan dukanta zan kaita masarauta ne”.
Take murmushin fuskar Iffah ya ɗauke baki ɗaya. Kamar
zatai magana sai kuma tai shiru ta maida kanta ga aikinta
kamar bataji ba. Shima Babiy sai bai sake cewa komai ba akan
zumar suka cigaba da maganarsu da Hanash da Ummu dake
saka baki jefi-jefi.....

Tun wannan magana babu wanda ya sake tada zancen
zumar nan. Babiy da Hanash suka duƙufa tattare kayan lambu
da za'a fitar. Yayinda Iffah ta cigaba da zuwa makarantarta a
zahiri kamar babu wata damuwa tattare da ita. Sai dai kuma a
baɗini tun randa akai maganar kai zuma daular ruman
zuciyarta sam bata huta ba. A duk motsinta cikin ƙullawa da
kwancewa take game da babban burinta na ɗaukar fansa.
Wanda tasan bata da wata hanyar yin hakan sai ta wannan
zuma da Babiy ke kaiwa masarauta. Kuma tasha jin cewa
Tajwar ne ke shanta kawai.
Har ana saura kwana biyu bata samu wata mafitaba akan
ƙudirinta, dan haka tana zuwa makaranta taja wata ƙawarta
da kafin yanzu da ta canja suke sabgarsu da rashinji tare gefe.
Ikram da taji farin cikin ƙawarta ta fara dawowa yanda take
babu musu ta bita suka koma can ƙarƙashin wata bishiya suka
zauna.
“Ko kefa Iffah, ALLAH bana jin daɗin yanda kike shareni
yanzu sam. Dan ALLAH ki manta da komai mu cigaba da yima
su Akia Arfa addu'a”.
“Humm”. kawai Iffah tace da ɗan laɓe fuska. “Kinga ni
ba wannan yasa na kiraki ba, tambayarki nake so nayi?”.
“To ALLAH yasa na sani”. Cewar Ikram tana gyara zama.
“Kinma sani, kwanaki bakin bani labarin sister ɗin mamanku
tasha zuma taita ciwon ciki ba, kafin aje asibiti har hanjinta ya
kakkatse?”.
“Yes anyi haka, bayan kwana huɗu ma ta rasu ai. Sai
daga baya aka gane ashe saurayintane ya zuba mata wani
magani a ciki. Sai dai har yanzu ma ana shari'an, dan a
binciken likitoci sudai sunce basuga komai ba, abokinsa kuma
da suka ƙulla tare ne ya tona masa asiri, ya kuma rantse sun
zuba ɗin dan tare suka sayo maganin”.
Iffah dake saurarenta tace, “Anya kuwa ba abokin na
masa sharri bane?”.
“To mudai bamu san dai-daiba sai ALLAH. Grand mother
ɗinmu ma ita tace dan ALLAH abar shari'ar tunda UBANGIJI
mafi sani ne. Idan anje garesa shi ya rarrabe ƙarya da
gaskiya”.
“Uhm gaskiya kam tayi magana mai ƙyau. To amma ni
abinda ya bani mamaki, shiko wannan wane kalar maganine
haka da har za'ace likitoci sun kasa ganewa, bayan kuma
gashi sunce ya kakkatsa mata hanjinta da kansu.”
“K nifa abinda na fahimta kamar an sayesu ne likitocin, kin
sanfa ɗan manyan mutanene yaron. Amma abokin nasa ya
faɗi sunan maganin sai dai na manta”.
“Komaima zai iya faruwa indai shegun manyan ƙasar
nannne, kansu kawai suka sani azzalumai. Amma ina son
nasan sunan maganin dan ina son nai bincike a kansa ma ni
wlhy.”
“Kedai kawai wani abun adai rufesa kawai. Uhm kina nan
da shegen son bincike-binciken nan naki, anya Iffah idan
ALLAH ya cika miki burinki na zama ƴar jarida bazaki
addabemuba? Dan na kula har hurumin aikin jami'an tsaro
zaki dinga shiga tsabar bin kwaf-kwaf ɗinki”.
“Ƴar sa ido naji, nidai kafin a tashi ki tuno sunan
maganin inba hakaba zanta addabarkine”.
Ikram tai dariya tana miƙewa. “Indai wannan ne zanyi
ƙoƙari. Maganin ma fa ba wani na kirki bane ba ance ana
zubama ƙananun ƙwari ne dakan damu mutane a cikin gida a
ruwa haka ko abinci, dan basajin warinsa sam ko ami aka
zuba sai kiga sunsha ruwa da shi ko abinci.”
“To kinga koda ba bincikeba ai zai mana amfani, dama mu
da muke cikin lambu kullum cikin ganin macizai dama halittu
masu cutarwa iri-iri dake iya zama a cikin gida haka.”
“Eh gaskiya kuma hakane, zai ko taimaka muku insha
ALLAHU”.

Kafin a tashi kuwa Ikram ta cika alƙawarin samowa Iffah
sunan magani. Takoyi farin ciki har haƙwaranta na bayyana
wajen murmushi irin wanda ta jima batayiba a rayuwarta. Iya
kuɗin motarta ne kawai a jikinta. Dan haka ta gama tsara
ƙaryar da zatai ta samu kuɗin sayen maganin idan ta koma
gida. Koda ta koma gida tun kafin takai zaune ta sanarma
Ummu ai an basu wani Assignment mai wahalar gaske. Gashi
bata da littafin dazai taimaka mata tayi har sai ta saya. Ganin
yanda tai maganar a serious yasa Ummu yimata murmushin
kwantar da hankali.
“Karki damu in har ana saidawa anjima sai Hanash ya fita
ya saya miki kema, ko kuma ki bincika a kayan karatun su
Arfa ƙila ki samu ai”.
“Ummu basu dashi sam, dan kwanaki ma da malaminmu
yay maganarsa sannan suna nan ai. Kinga da suna dashi ai da
sun bani”.
“Uhm hakane kuma kam. To ki bari Hanash ɗin ya dawo
sai ya dubo miki”.
“Ummu ni kawai ki bani yanzu da nayi wanka sai naje da
kaina na dubo. Ƙilama daga nan na ƙara ilimi”.
“Kai Iffah kin cika fitina, kin dai san ba son yawan
fitarnan taki muke ba ai”.
“Na sani Ummu, insha ALLAHU babu abinda zai faru
addu'arku na biye dani, kuma ina suturce jikina idan zan fita”.

Badan hankalin Ummu ya kwanta ba ta yarda tabar Iffah
ta fita. dan ta dage akan gobe ake buƙatar sukai Assignment
ɗin, idan tace zata jira sai Hanash ya dawo dare zaiyi tunta
sunje babbar kasuwar cinikayyar ƙarshen watane ta daular
ruman kai kayan lambu. Kamar kullum tai shirinta tsaf tare da
rufe duk jikinta sai idanunta kawai da ake gani. Sosai ash
color na abayar jikin nata mai adon duwatsu blue masu sheƙi
sukai mata ƙyau duk da ba'a iya ganin fuskarta. Cikin
nutsuwarta take takunta tamkar wata tarwaɗa. Dan Iffah tun
tana yarinya irin yaran nanne masu shegen iyayi da kauɗi.
Tun a shekarun baya mutane kance za'ai kallon ƴammata a
wajen nan, dan tafi yayunta son kyale-ƙyale da tsantseni irin
na ƴan gayun mata masu ji da kansu. Da ƙafa tazo har titi duk
da akwai ɗan tafiya a tsakaninsu. Ta tare abin hawa tare da
sanar masa inda zai kaita.
A ƙofar katon kantin da ake saida duk wani nau'in magani
daya shafi gona dana kauda mugayen halittu masu cutarwa
ga mutane dakan shiga cikin gida ya sauketa. Ta biyashi
kuɗinsa sannan ta shige. Kanta tsaye ta miƙa takardar data
riga ta rubuta sunan maganin dan karta manta. Aka faɗa
mata kuɗin ta biya suka bata. Wani irin farin ciki takeji a
ranta, tunin karta koma gida babu littafi ta zama abar tuhuma
ya sata cema mai abin hawan data hawo ya kaita babban
shagon littatafai. Koda suka isa cewa tai ya jirata yanzu zata
fito su wuce. Gargaɗi ya mata akan kuɗintafa ya ƙaru, tace
babu damuwa tana shigewa.
Ganin babu yawan mutane a shagon duk da ƙatone
sosai ba kuma wajen da za'ai hayaniyar da zaka san adadin
mutanen wajen bane yasata ɗage niƙab ɗinta yanda zataga
komai da ƙyau. Kowanne littatafai da sashensu a rubuce
kuma yanda bazakasha wahalar nema ba, maimakon ta nufi
inda zataga irin nata kai tsaye saita fara zagaye. Sai da ta
gama kewaye-kewayenta tamkar ta manta da wanda ta ajiye
a waje kafin ta tsaida hankalinta ga inda zataga littafin daya
dace ta ɗauka. Surutun yara takeji kaɗan-kaɗan ta bayan inda
take, ta ɗan dudduba taga babu ta inda zata leƙasu sai ta
haƙura cikin taɓe baki takai hannu kan wani littafi zata ɗauka.
Daga can ɓangaren ma dai-dai an kai hannu akan littafin za'a
ɗauka dan duk kanta ɗaya ce, littatafan ne kawai suka rufe
wanda ke can baya ganin na nan. Iffah taja, daga can ma aka
ja, jin za'a fisge saboda an fita ƙarfi dama tsaho dan ita harda
su ɗiɗɗishe saita fisga itama a ɗan fusace saboda gani take
wani keson raina mata hankali. Ta cikin ɗan space ɗin data
cire littafin ita da shi suka zubama juna idanu, haka kawai taji
tsigar jikinta ta tashi duk da ita bama wani ganesa tai da ƙyau
ba saboda space ɗin bawai ya buɗe da ƙyau bane.
Kamilalliyar fuskarsa da dama babu wani walwala a cikinta ya
ƙara tsukewa dan shiko sarai ya ganeta...........✍

6

........Baki ta murguɗa da juya idanunta farare tas tamkar
madara cikin nasa da ya kafeta da su. “Inma kai mayene to
wlhy bazan ciyu ba, Babiy kullum addu'a yake min shi da
Ummu”. Tana gama faɗa tabar wajen.
Yaransa na waccan ranar ne dai yau ma a tare da shi.
Kuma suma sarai kalaman Iffah da bazasu manta muryarta da
wuri ba ta shiga cikin kunnuwansu. Dama sune suke dubama
yaran dake tare da su books ɗin, shi ko yana biye da su ne
kawai da binsu da idanu. Ɗaya daga cikin yaranne ya nuna
littafin da Iffah ta ɗauka, su kuma kasancewar suna ɗakkoma
sauranne sai shi da kansa yay yunƙurin ɗakkowa kafin su suyi
hakan. Yunƙurin zagayowa wajen Iffah ɗaya daga cikin
yaransa yayi, dan yay alƙawarin yau sai ya daddala mata mari,
amma sai ya dakatar da shi ta hanyar yima ɗayan alamar ya
tsayar da shi da ido. Da sauri wancan da shima yake jin kamar
suje su haɗu su faffasa mata baki ya kira sunan wancan.
“Azaan!”.
Cak ya tsaya tare da rumtse ido da cije baki dan yasan dai
ogane zaisa Fakhir ɗin ya dakatar da shi. Gashi harya hango
Iffah dake gaban mai biyan kuɗi. Dole ya haƙura badan yaso
ba, amma yaci alwashin duk randa suka sake haɗuwa da
yarinyar can babu oga sai ya mata karyawar gasashshiyar
masara danta tabbatar itace zata gujema haɗuwarsu ba su ba
kamar yanda ta faɗa.
Iffah dai tuni ta biya kuɗin littafi daya cinye mata duka
kuɗinta babu ko na bawa mai Mototaxi (napep). Sai mita take
a ranta Littafin yayi tsada, koda ta fito ta iske mai Mototaxi ya
cika yayi taf. Tana isowa inda yake hannu kawai ya miƙa mata
alamar ta bashi kuɗinsa ya wuce. Fuska ta ƙyaɓe ta cikin
niƙab ɗinta tana wani kif-kif da idanunta da kawai yake gani.
“Oh oh kaiko duk daɗin asara ai ta jira samu ko? Idan mukaje
inda zani nace maka bazan biyaka bane?”.
A fusace yana mai dalla mata harara yace, “Na fasa kaiki,
dalla malama bani kuɗina kije ki hau wata. Kuma har na
zaman danai anan sai kin haɗamun”.
“Lallai sannu shugaban ɓarayin Ruman. Saboda Babiy
yamun baki ko? Idan kaga zaka ɗaukeni muje na baka
kuɗinka ka daukeni, in kuma zaka zauna wage baki kana ihu
ne na tare wata na hau ka biyoni a baya dan bani da shi anan
sai naje gida”.
“Baki da hankali”. Mai Mototaxi ya faɗa a matuƙar
fusace yana fitowa. Harga ALLAH Iffah ta tsorata, dan tasan
wannan mai zubin samudawan ƙarnin farkon fyaɗa daya zai
bazar da itane a titin nan sai dai a kaima su Ummu gawarta.
Amma tsabar ƙarfin hali sai faman fiki-fiki take da idanu da
faɗin, “To sai kayi duk abinda ma zakayi mana”.
“Hakama kika ce?”. Ya faɗa yana matsota. Jikinta taja
baya tana wani zazzaro masa manyan idanunta masu
matuƙar sheƙi tamkar ta tara ruwan hawaye a ciki, “Idan
hanunka ya taɓa koda abayar jikina sai na ɓallashi! Idan kuma
ka isa ka gwada”.
“Kan uban can kayyasa, ke yarinyar nan kin san wanene ni
kuwa? To dan ALLAH gwada ɓallamin hanun nagani”. Ya faɗa
yana yo kanta da gaske. Securitys ɗin dake a bakin bookshop
ɗinne sukai saurin taresa, dama dai ganinsu yasa Iffah
wannan hura hancin, ganin ta samu yanda takeso baki ya
ƙara buɗewa ta buɗe baki zata cigaba da tsiwa idanunta suka
sauka a kan mutumin nan. Yanayin takunsa na isa da ƙasaita
kawai saka rawa a zuciyar Iffah yake, sai dai kasancewarta
yarinya mai ƙarfin halin tsiya da rashin son a ga gazawarta
yasa baka isa ganin wannan tsoron ba a kan fuskarta. Janye
idanunta tayi tamkar bata gansa ba, shima sai ya cigaba da
takowa tamkar bai ganta ɗin ba yaransa da tawagar yara
kusan goma sha biyar biye da su. Kamar waccan ranar yau ma
sanye yake cikin suit da sukai matuƙar fidda ƙyawun
halittarsa ta tsayayyen mutum, saɓanin ranar na yau baƙaƙe
ne, sai dai sunyi matuƙar dacewa da lallausar farar fatarsa
mai matuƙar sheƙi da ɗaukar idon mai kallo. Ga mayataccen
ƙamshinsa irin na ranar mai saka zuciyar mai shaƙa raunana
da nutsuwa. Harya gotasu zai wuce a binsa sai kuma ya tsaya
cak, hannayensa duk biyu ya zuba a aljihun wandonsa tare da
juyowa. Ita ya fara kallo, sai kuma ya janye lulu idanunsa
masu tabbatar da kwarjininsa da kamewarsa ga duk wanda
ya kallesu ya maida kan securitys ɗin nan dake riƙe da mai
Mototaxi ɗin har yanzu. Azaan daya fahimci mi ogan nasu ke
nufi yay saurin faɗin “ku sakesa” duk da har cikin rai baiso
hakan ba. Babu musu suka sakesa, shiko sai huci yake idonsa
akan Iffah data juyar da kai gefe irin bata sanma mi'ake ɗin
nan ba. Hanunsa ɗaya ya zare daga cikin aljihunsa ya ɗan
ɗaga rigar suit ɗin tasa. Kuɗine masu yawa ya zaro ya miƙama
mai Mototaxi ɗin. Cikin rawar jiki ya kai rissine kamar
gwiwarsa zata taɓa ƙasa ya amsa yana godiya kamar zai
haɗiye harshensa. Kansa kawai ya ɗauke zai juya suka sake
haɗa ido da Iffah. Baki ta tura gaba tana fiki-fiki da idanu da
sake ɗauke kanta...
Takaici kamar ya kashe su Azaan. Babu wanda a cikinsu
bai harari Iffah ba kafin subi bayan ogansu da tuni yabar
wajen. Mai Mototaxi da bakinsa ke washe uwa gonar audiga
ya kalla Iffah. “A to hajjaju taho na kaiki koda karshen Daular
Ruman ne ma”. Wata banzar harara ta balla masa da jan tsaki
tabar wajen. Cike da takunta na nutsuwa ta gitta motarsu
dake ƙoƙarin barin wajen. Azzan yay ƙaramar ƙwafa, a ransa
yana raya shine zai zama sanadin nakasa yarinyar nan kuwa
wataran. Mai gayya mai aiki kam da gaba ɗaya zuciyarsa ta
gama tabbatar masa yarinyar nan aljanar ce idanunsa ya
lumshe a hankali yana mai ƙara gyara zamansa na ƙasaita
tamkar ba'a mota yake ba....

Tunda ta samu wata Mototaxi ɗin ta shiga zuciyarta ta
tafi tunani. A karan farko take tambayar kanta waye wai
wannan mutumin a garin nan?, da ganinsa dai kasan ɗan
masu farcen susu ne ko shi a karan kansa ne mai farcen susar.
A ƙasan zuciyarta taji tana buƙatar sanin shi ɗin wanene
badan wani abu nasa ya birgeta ba. Hasalima haka kawai
haushinsa takeji tun akan bige yaron nan da suka kusa yi a
waccan ranar da ƙoƙarin guduwa da sukai. Ko kuma ma dai
aljanin ne?, dan inba aljani ba taya zata dinga ganinsa duk
inda taje gashi har karo biyu.. Tasha ji a bakin mutane ana
faɗin ita ɗin ƙyaƙyaƙyawa ce, tafi kowa ƙyau a gidansu, amma
ƙyawun wannan bawa da dirarriyar halittar jiki data fuska mai
cike da kwantaccen gashi tamkar shiya zaɓama kansa komai
sai dai aljanin kam..... Isowarsu anguwarsu ya sata ture
tunanin ta nunama mai Mototaxi inda zasu ƙarasa ta amso
masa kuɗinsa. Cikin sa'a suna isa ƙofar gidansu sai ga Babiy
da Hanash suma an saukesu da alama yanzun ne suke
dawowa. Su suka biya mai Mototaxi ɗin kafin su shige cikin
gidan bakinta washe tana jera musu sannu da zuwa...

Labarin alkairin da aka samu na kayan da suka kai
kasuwa su Babiy ke basu ita da Ummu, amma ita rabin
hankalinta naga abinda take yunƙurin yine kawai. Ta matuƙar
ƙagara ai kiran sallar magrib su Babiy su fice masallaci Ummu
ta shiga ɗaki. Ana kwaɗa kiran salla kuwa itace farkon
miƙewa yin haramar alwala. Hakan da tai baisa wani yaji
daban ba dan kowa yasan Iffah da himmar yin salla. Komi
take aka kira salla, ko'a ina take inhar wajen zaiyi ibada zata
ajiye abinda takeyi kuwa tayi sallar. Wannan halin nata na
ƙara sakama iyayenta da ƴan uwanta sonta, dan tunsu Arfa
na raye ma sukansu Ummu takan zaburar dasu akan halin
Iffah ɗin na kiyaye ibada da ƙoƙarin yinta akan lokaci. Koda ta
shiga ɗakin bayan tayi alwala bakin gadonsu takai zaune dan
tana fashin salla ne, sai da taji tsakar gidan yayi tsitt sannan
ta ɗan leƙo, babu kowa kuwa Ummu ta shige su Hanash sun
fita massallaci. Da sanɗa ta fito ledar maganinta na ɗazu da
taketa ɓoyo riƙe a hanunta. Wuff ta afka ɗakin Babiy, cikin
sa'a bata wani sha wahalar ganin tulunan da aka cika da zuma
ba sabbi ƙal. Ta saki murmushi dajin kamar tai ihu dan farin
cikin da takeji a zuciyarta. Amma sai ta kanne cikin rawar jiki
da ɗan yin leƙe-leƙe irin na mai tsoron a kamasa yana laifi
tana ƙoƙarin buɗe kwalbar. A tulun farko ta zuba kusan rabi,
sai kuma ta dakata bisa shawarar zuciyarta akan ta zuba duka
tunda bata da tabbacin dukansu Tajwar ɗinne zaiyi amfani da
su. Ƙaramin sandan data shigo da shi tasa ta motsa da ƙyau
har saida ta tabbatar ya gauraye sannan ta sakama ɗaya, tana
tsaka da juyawa ta tsinkayo muryar Ummu na kiranta. Ido ta
rumtse da sauri tana ambatar sunan ALLAH, da hanzari ta
shiga rufe roban sauran maganin saboda jin kamar Ummu na
nufi ɗakin, cikin riga ta saƙa maganin da sandar sannan taɗan
leƙo. Can ta hango Ummu ta nufi kitchen ɗinsu, aiko tai wuff
ta fito ta faɗa ɗakinsu. Ummu data juyo saboda jin kamar
motsi ta sake ƙwala mata kira. Yanzu kam amsawa tai da
fitowa tana gyara mayafin abayarta.
“Yi haƙuri Ummu ina karatune”.
“Shine kuma bazaki mun ko gyaran murya ba zaki barni ina
wage baki”.
“Kiyi haƙuri to Ummuna”.
Ummu ta fito daga kitchen ɗin tana gyara mayafin jikinta
itama. “Jeki ki cigaba da karatunki dama motsi naji kamar,
amma fara duba kosu Hanash sun bar mana ƙofa buɗe ne”.
Da to Iffah ta amsa tana nufar hanyar soro da sauke
ajiyar zuciya...

Tana shiga ɗaki wani uban tsalle tai ta dirga saman gadonsu
dan farin ciki. Mulmula take tana dariya irin wadda ta jima
batayi ba, wauta da

Please Login or Register in order to submit comment