Reading Dauɗar Gora by Bilyn Abdull ce Chapter 11 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba itace tayin ba. Har ta
ƙurya ta fidda ran samun amsa sai kuma Uwa ta sake
ƙyalkyalewa da dariya tana ambaton “Ajlan! Ajlan!! Ajlan!!!”
ta ƙara kwashewa da dariya tana mai disashewa a idanun Ta-
kurya da zuciyarta ta kasa fassara ma'ana ko dalilin dariyar ta
uwa...

🤔Ko miye naku tunanin a wannan gaɓar kuma masu
karatu???.

★... ★.★.★ ★...

*_GIDAN BABIY_*

Sun dawo har yanzu da ɗan sauran mutane maƙwafta da
aketa ɗan ƙus-ƙus akan lamarin. Cikin ƙanƙanin lokaci aka
baibaye motar, waɗanda suka shige gidaje suka fara fitowa. A
yanayin da aka fidda Ummu mafi yawansu sunma ɗauka dai
bata da rai, dan kuwa da gaske babu alamar rai tare da itan.
Kuka da salatin da mafi yawan mutane suka ɗauka na tunanin
ta mutun ne yasa Abu Zainab saurin dakatar da su.
“Dan ALLAH kowa ya kwantar da hankalinsa. Umm-Arfa
ba mutuwa tai ba”.
Badan hankalin su ya kwantaba sukai shiru, sai dai dama
kukan na wasu na munafurci ne dai. Matane suka kamata aka
shiga da ita, a tabarmar da suka samu tsakar gida suka
shimfiɗeta. Cikin sa'a Abu Zainab yaci karo da wayar Babiy
dake yashe a ƙasa. Da alama sanda jami'an nan zasu fita da
shine ta faɗi. Jikinsa har tsuma yake a duba contact ɗin
wayar, cikin sa'a ya samo number da akai saving da Baba.
Baya raba ɗayan biyu mai sunan nada babban matsayin
baban a wajen Babiy ɗin, dan haka ya danna masa kira kai
tsaye, sai dai harta tsinke ba'a ɗaga ba. Sake kiran yay yana
addu'ar dacewa sai ko gashi an ɗaga...

★A lokacin da kiran Abu Zainab ya riski su kaka ta hanyar
wayar Babiy ba'a ƙaramin tashin hankali suka tsinci kansu ba
shi da Iyyani. Duk da kasancewar yamma tayi kuma yasan a
yau dole ne sai ya dangana da daular ruman dole ya bazama
neman wani yaro mai mota a ƙauyen nasu dake jigila a ko
yaushe, cikin sa'a ya samesa ya dawo kenan ma ko gida bai
shiga ba. Amma saboda mutuncinsa da ake gani yana masa
bayani babu musu ya amsa masa suka ɗauka hanya harda
Iyyani daketa faman sharar hawayen da suka kasa tsaya
mata. Ana sallar isha'i suka iso cikin daular ruman. Basu sami
mutane ba a gidan kamar ɗazun, sai Umm Yazeed da matar
Abu Zainab dake dai tare da ita har yanzun. Zuwa yanzu
Ummu ta farfaɗo, sai dai taƙi magana da kowa sai hawaye da
taketa faman zirarwa ta gefen ido, ga numfashinta baya fita
normal kamar na kowa, tana fitar da shine da fisgosa a
wahale sannan a fiffisge. Kuka Iyyani ta sake fashe da shi da
rungume Ummu a jikinta tana kiran sunanta. Kaka kam tsaye
yay kawai zuciyarsa na harbawa da ƙuna. Suna a haka Abu
Zainab ya dawo, dama sallar isha'i yaje. Cikin girmamawa ya
gaida kaka, shima ya amsa masa da kulawa da godiya. Ya ɗan
murmusa kansa a risine. “Ai ba komai baba yiwa kai ne.
Sannan mun zama ɗaya ai mu da Abu Hanash. Ko mu irin
haka ta faru da mu zai tsaya tsayin dakane a kan komai.
Ruɗanin halin da Umm Arfa ke ciki yasa su bamu bibiyesu
musan miya faru ba har yanzu gaskiya. Dan munata yawo a
asibitoci amma sunƙi amsarta, ga jikin nata kuma yana
buƙatar a duba mata shi, shiyyasa yanzu dana idar da sallar
magrib naje na samo ɗan uwana dake aikin asibiti gashi muna
tare, sai dai ba wani babban likita bane dai....”
Kai kawai Kaka ya jinjina masa da faɗin, “ALLAH ya saka
muku da alkairi, haka ake fatan zaman makwaftaka, domin ita
makwaftaka tanada ƙarfin da zata iya fin ƴan uwantaka
muhimmanci ma a wani ɓangaren. Yanzu gashi abu ya
samesu, kafin mu muzo kun basu ɗauki, da bakwa zaman
lafiya kuma hakan bazai yuwuba. Dan haka duk wani mutum
na ƙwarai daya san kansa ya dace ya rayu da maƙwafcinsa
lafiya da ƙaunar juna”. “Hakane Baba, ALLAH ya saka da
alkairi. Bara na shigo da shi”. Murmushi Kaka yayi da jinjina
masa kai. Koda suka shigo tare da ɗan uwan nasa shima ya
gaida Kaka da girmamawa, hakama Iyyani da har yanzu ke
faman sharar hawaye tana tofama Ummu addu'a. Damar
duba Ummun Kaka ya bashi dan haka ya shiga aikinsa. Ya
tabbatar musu jinin Ummu ya hau matuƙa, amma zai mata
allurar barci ta samu nutsuwa dan barinta a ido biyu akwai
haɗari komai zai iya faruwa. Sai da suka maida Ummu ɗaki
sannan ya saka mata ruwa da allurai aciki, cikin sa'a kuwa
babu jimawa barci yay awan gaba da ita. Sosai Kaka yay musu
godiya da sanya albarka, dan ko sisi ɗan uwan nasa bai
amsaba ma.......


★★.... ★.... ★★.....

An wayi gari da samun canji sosai a yanayin Iffah, dan
zuwa yau kam Alhmdllh. Sai dai jikinta dake wani irin saɓa
saikace wata macijiya. Sai kuma rauni data tsinci kanta a ciki
sakamakon mummunan mafarkin datai akan su Babiy daya
haddasa mata matsanancin faɗuwar gaba da akai-akai. Gata
dai iya gata tana gani wajen tsohuwa Malikat Haseena duk da
bata da lafiyar ƙafa sai a wheelchair take komai. Hakama
Daneen Ammarah tsaye take kan Iffah, yanda take kula da ita
yasa Iffah jin ƙaunarta batare data san dalili ba, ganinta take
tamkar Ummu. Yanda ake tsaye kanta da gata da kulawa yasa
ko damar yin ƙwaƙwaran tunani bata da shi, dan da tayi shiru
Daneen Ammarah zata nuna damuwa taita jera mata
tambayar mike damunta? Ko tamanin wani abu ne a jikinta
har yanzu?. Dole take sassauta damuwarta, sai dai tayi
matuƙar dagewa wajen ambaton UBANGIJI kamar yanda
Babiy da Ummu suka dinga jaddada mata a nasiharsu ta
ƙarshe gareta. Labarin mutuwar hadiman da suka kai mata
rigar nan ta saka yazo kunenta itama, sai dai jin sanadin
mutuwar tasu ya tsaya mata a rai matuƙa, harma ta rasa yaya
zata fassara al'amarin...
Bayan idar da sallar isha'i tana zaune tayi tagumi gaba
ɗaya hankalinta ya tattara ga tunanin iyayenta da
mummunan mafarkin daren jiya a kansu Daneen Ammarah ta
shigo hadimai uku biye da ita. A bakin gadon takai zaune tare
da kai hannu ta janye tagumin da Iffah tai. Nannauyan
nunfashi ta sauke da ɗan ɗagowa ta kalla Daneen Ammarah
ɗin, sai kuma ta maida kanta ta risinar da mata sannu da
zuwa. Daneen Ammarah dake kallonta cikin damuwa taja
numfashi ta fesar batare data amsa ba. Dai-dai nan Hadiman
da suke tare suka zube gaban Iffah bayan sun ajiye kayan
hanunsu. Gaisheta suke da tsantsar girmamawar da ko iya
ɗaga kawunansu basayi su dubi sashen da take. Sam Iffah
batajin daɗin yanda suke matan saboda bata sababa, a ranta
gani take kamar ƙasƙancine. Hannu Daneen Ammarah ta
kaɗa musu alamar suje, zumut suka miƙe tamkar ƙyaftawar
ido suka fice. Iffah ta bisu da kallo cike da jin raɗaɗi a
zuciyarta.
“Ibnati!”.
“Na'am Mamy!”.
Iffah ta amsa cike da girmamawa ga Daneen Ammarah. Sosai
sunan da Iffah ke kiranta da shi ke raunanata da sake jin
ƙaunar yarinyar, dan a bakin mutum ɗaya tak take jinsa kafin
ita. Taja numfashi da haɗiye hawayen da suka cika mata ido
ta maye gurbinsu da murmushi.
“Ibnati bana son cigaba da ganin damuwar nan a fuskarki,
ki kwantar da hankalinki insha ALLAHU babu abinda zai sake
samunki. Wanda ma ya sameki ki ɗauka kaddararkice kinji,
amma inaji a jikina insha ALLAH kece mabuɗin nasararmu, ke
ce hasken da zata haska mana duhun da muke a ciki a Daular
nan kinji”.
Kai Iffah ta jinjina a hankali, haka kawai take jin matuƙar
nutsuwar kasancewa da wannan baiwar ALLAH, sam batajin
irin zafi da tsanar da takema duk wani mai alaƙa da
masarauta a kanta. Kallonta take tamkar wata katanga ta
wani babban al'amari dake tunkarota. “Mamy bana tare da
damuwa in har kina a kusa dani, duk abinda ya sameni kuma
dama ALLAH ya ƙaddara sai ya sameni koda banzo nan ba. Ina
tunanin su Ummu ne da jin tsananin kewarsu saboda
mummunan mafarkin danai akansu jiya, ina tsoron kar wani
abu ya samesu ne suma?”.
Cike da jin tausayita Daneen Ammarah ta shafa kanta,
“Duk ɗa na gari dolene ya kasance cikin kewa a lokacin da yay
nesa da ahalinsa, da ace inada dama da a yau sai na kaiki
kinga su Ummunki. Amma dokar masarauta ce Zawjata-
almilki tana fitane kawai bisa ƙwaƙwaran dalili, zuwa gidansu
kuwa tana yinsa ne sau biyu tak a shekara, ɗaya a sirrance,
ɗaya a bayyane tare da rakkiyar hadimai. Shiko mafarki ai na
gaskiya bane Ibnati, MANZANNI ne kawai idan suka yisa yake
gaskiya a garesu, amma mu namu yakanzo da wasu sigogi ciki
harda sheɗanu”.
A hankali hawaye suka silalo a kumatun Iffah, bawai
lokacin ziyarar bane yay mata nisa, rashin tabbacin kaiwa
lokacin ziyararne ya sata zubar hawaye. Ita dake zaman jiran
ƙaddarar mutuwarta taya zatai tunanin zuwan waɗan can
damarmaki guda biyu na ganin su Babiy, maganar mafarki
kam ta san gaskiya Mamyn ta faɗa, itama kuma ba tana
dangantashi da zama tabbaci bane, kawai tana matuƙar jin
tsoron faruwar wani abu ne a dalilin mafarkanta na baya....
Ganin hawayen Iffah ya matuƙar tada hankalin Daneen
Ammarah, a rikice ta shiga tambayarta kamar yanda ta saba
in har ta ganta a makamancin damuwar nan. Hannu Iffah tasa
ta share hawayen nata da ƙirƙiro murmushi.
“Mamy ki kwantar da hankalinki hawayen sunzo ne kawai
da kansu babu dalili”.
“Haba Ibnati, dama ana kuka babu dalili ne? Ko baki faɗaba
nasan kinada dalilan yin kuka, amma idan kika zama mai
haƙuri da juriya wataran ke zakiyi dariya a gaban waɗanda
suka cancanta suyi kuka.” (ALLAH ya tabbatar da wannan
ranar) Iffah ta faɗa a zuciyarta, a zahiri kam sai ta goge
hawayen tana murmushi. Hakan yasa Daneen Ammarah yin
murmushin itama, kafin kuma ta mike tsaye da kama Iffah
suka koma kan dardumar da aka shirya abinci acan gefe na
ɗakin, dan ɗakine ƙaton gaske mai dauke da komai na jin
daɗin duniya. Tare sukaci abincin, Daneen Ammarah har tana
bama Iffah wani lokacin a baki, jitake inama Iffah ɗiyartace,
dan da'ace tana gidan aurenta har yanzu ɗiyarta ta fari zata
iya kasancewa dai-dai da shekarun Iffah ne. Kulawar Daneen
Ammarah ta sake saka sassauci a zuciyar Iffah harta ɗan saki
jikinta. Bayan sun kammala ta sakata shiga bayi tai wankan
maganin da take amfani da shi, data fitoma da kanta tai mata
hayaƙin turare. Iffah ta hau gado ta zauna, Daneen Ammarah
a gefenta da littafin tarihin annabawa acewarta zata dinga
karantama Iffah har sai taga tayi barci domin ɗebe mata
kewa.
“Yauwa Ibnati kin shirya dai ko?”.
Fuskar Iffah da ɗan murmushi tace, “Eh Mamy na”
“Masha ALLAHU ashe dai Habibty na tare dani”.
Hannu Iffah tasa ta rufe fuska tana murmushi, itama dai
Daneen Ammarah murmushin take. Ta fara buɗe littafin. Iffah
dake kallonta tai dauriyar finciko ɗaya daga ɗunmbin
tabayoyin dake cin ranta ganin zata fara karatun...
“Mamy dan ALLAH na tambayeki wani abu?”.
“Oh Ibnati tambayeni mana kanki ma tsaye kuwa.”
Iffah ta jinjina kanta da sauke ajiyar zuciya..........✍️

22
.......Iffah ta jinjina kanta da sauke ajiyar zuciya, “Immm
Mamy dama...” sai kuma tai shiru dalilin gargaɗin da
zuciyarta ke mata tunda har yanzu fa Bama wai tasan
matsayin Daneen Ammarah ɗin bane a masarautar.
“Dama mi? Kinga karkiji komai kimin duk tambayar da
kike buƙata, insha ALLAH zan kasance mai baki amsa, idan
kuma bata dace ba zan baki shawara kodan nan gaba”.
Kai Iffah ta jinjina “Dama dan ALLAH zance ne yanzu
mutuwar su hadiman can shikenan ta tafi a banza baza'ai
wani bincike a gano ba?”.
Kallo na kusan sakan biyar Daneen Ammarah taima Iffah
da har tama ɗauka tai laifi, amma sai taji taja numfashi da
maida kanta kan littafin hanunta. “Mutuwarsu bazai tafi a
banza ba saboda dalili mai ƙarfi Ibnati. Dan duk wanda ya
kashesu yana gudun tonuwar asirinsa ne akan cutar da ke da
akai yunkurin yi. A yanzu haka Shahanshan ya saka kwamitin
bincike, muna fatan kuma ta wannan hanyar za'a gano koma
wanene ya saka ki a halin da kika tsinci kanki. Kuma dama
kema ana jiran ƙara samun lafiyarki ne aji ko akwai wani abu
da kika sani, ko kuma bayan su ukun can da ɗayar da aka
samu nasarar ceto ranta ko akwai wasu..”
Da sauri Iffah ta dubeta. “Mamy akwai wadda bata mutu
ba dama?”.
“Eh akwai amintacciyar hadimar Umm-Jasrah (haka take
kiran Malikat Bushirat) mai suna Diwa. Ita an kaita asibiti
kafin gubar da suka sha ta karasa katsa ƴan hanjinta.
Alhmdllh kuma an dace dan yanzu haka tana kan shan
magani, tana kuma zagaye da tsatstsauran tsaro”
“ALLAH ya ƙara bata lafiya, sai dai kuma banajin tanada
hannu a cikin al'amarin Mamy, dan da ganinta mutiniyar kirki
ce”.
“Gane mutanen kirki ba'a ido yake ba Ibnati musamman a
wannan masarautar da kowa kansa kawai ya sani, a mafi
yawan lokuta ma ba'a gane maƙiyi da halayya. Akwai
rikitattun abubuwa dake a matuƙar cuɗe a wannan Daular da
gani da ido bazai wadaci mai kallo ba, dan haka nakeso ki
nutsu kisa hankalinki waje ɗaya kafin ki koma sashenki ki koyi
abubuwa da yawa na salon mulki da tsarin matsayinki na
Zawjata-almilki. Saboda kunada matuƙar tasiri da girma a
tsarin ƙarfin iko na masarauta da kaikawon talakawan ƙasan
ruman. Fatana kuma kece Malikat a cikin Zawjata-almilki
insha ALLAHU”.
Sam Iffah bata fahimci komai ba ga kalaman Daneen
Ammarah, amma sai bata sake cewa komai ba dan a ganinta
tana buƙatar samun lokacin yin nazari na musamman a kansu
kafin ta fahimcesu dallah-dallah.......

★★... ★... ★★....

Ana idar da sallar asuba drivern daya kawo su Kaka jiya dan
hanashi komawa yay saboda dare ya ɗauka Iyyani da Ummu
suka wuce. Kaka da Abu Zainab kuma sukai shirin fara neman
inda zasu samo Babiy da Hanash.
Dai-dai suna shiga mota kaka ya dubi Abu Zainab da ɗan
murmushin ƙarfin hali a fuskarsa, “To Zakariyya kai ne ɗan
gari, yanzu ta ina zamu fara kenan?”.
Numfashi Abu Zainab ya furzar, tare da yin ɗan jimm alamar
tunani, “E to Baba banace ba dai, dan al'amari nada wuya,
saboda bamu da tabbacin waɗan nan jami'ai daga wane
station suke. Amma ni yanzu a nawa shawaran ina ganin
kamar mu nema gidan shi marigayi ɗin, tunda matarsa ita ta
kawo jami'an tasan daga ina suke”.
“Hakane, wannan ma shawara ce mai kyau, sai dai inda
gizo ke saƙar kai koka san ina gidan Dawood ɗin yake? Dan ni
dai rabona da shi ma kusan shekara biyar kenan tun suna tare
da Muhammad Zayyan”.
“Ito baba banace ba, dan kusan nima hakan dai take,
amma bayan tashinsa daga anguwarmu nasan inda ya koma,
sai dai bani da tabbacin ko har yanzu acan ɗin yake zaune
tunda ba wani huɗɗa muke ba gaskiya, dama dalilin Abu
Hanash ɗinne ake gaisawa sai kuma idan wani zama na
anguwa ya haɗa kafin ya tashi kenan. Amma yanzu dai bara
mu tafi can ɗin kawai rana ma nayi”.

Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso anguwar, kasancewar ma ta
cika ba kamar da ba da kyar suka iya samo gidan. Duk da
jikinsu ya ɗanyi sanyi ganin ƙofar gidan babu alamar anyi
wani abu daya shafi mutuwa Abu Zainab yay sallama har sau
uku. Ana huɗun wani mutum ya fito. Cikin binsu da kallon
rashin sani ya basu hannu suka gaisa. Abu Zainab da shima
dai jikinsa yay sanyi ya ce, “Kayi haƙuri nasan baka sammu
ba. Muma dai munzo nan ɗinne neman wani bawan ALLAH
daya zauna anan shekara kusan huɗu haka baya. Sunansa
Dawood, amma ana masa alkunya da Abu Moosa. Matarsa
ɗaya bashi kuma da yaro ko ɗaya”.
“ALLAH sarki, gaskiya ban sanshi ba, dan nima dai ban
wuce shekara biyu da tarewa anan ɗin ba. Na kuma sayi
gidanne a hanun wani mutum Ibrahim Askari”.
Abu Zainab zai sake magana Kaka ya girgiza masa kai
alamar kar yace komai. Godiya sukai masa da sallama suka
wuce.
“Baba ban san miyasa ka dakatar dani ba. Dama zan
tambayesa ne ko zai faɗa mana inda zamu samu shi Ibrahim
Askari ɗinne”.
Numfashi Kaka yaja ya fesar, “Dalilin da yasa na dakatar da
kai kenan. Kasan shi al'amari irin wannan yana buƙatar kasan
dawa zakai maganar abu na gaba. Inaji a jikina waɗanda suka
haddasa tushen wannan matsalar dole suma zasu kasance
suna bin bayanmu domin toshe duk wata hanyar da zamu iya
bi. Dalili kuwa shine ina kallon lauje ne cikin naɗi akan
al'amarin”.
“Eh gaskiya hakane kuma Baba. To amma in har hakane
mizai hana mu nema lauya, sai nake ganin cikin sauƙi shi zai
iya binciko mana inda suke ma, kuma koma minene sai yazo
cikin sauƙi tunda ana magana ne akan abinda ya shafi shari'a
ko kuwa?”.
“Itama wannan babbar shawara ce a mahangar hankali
Zakariyya, sai dai shi lauyan ne matsala musanma irin mu
wanda muke bukata. Mai gaskiya da amana”.
“In dai dan wannan ne babu damuwa insha ALLAHU, akwai
yayan matata data rasu, kwararren lauyane kuma mai
nagarta da nasan zakaso aikinsa kuma zai taimakemu
kasancewarsa babba. A yanzu dai nasan bazamu samesa a
gidansa ba. Bara kawai muje ofishinsa”...


★★..... ★... ★★.....

Kamar yanda Iffan ta nema alfarma a wajen Daneen
Ammarah akan ɗakko mata akwatinta da aka kawo ta gidan
dashi ya iso gareta. Taji matuƙar sanyi a ranta da farin ciki.
Hadimar data kawo na fita ta buɗe akwatin ta shiga dubawa.
Alhamdullah komai yana nan yanda yake, hatta takardar da
malam Fawzan ya bata ɗinnan itama tana a inda ta ɓoye ta.
Tana idar da sallar azhar littafin data sako a kayan nata kawai
ta ɗauka da biro ta fara rubutu. Anutse take rubuta komai
daya faru daki-daki tun daga barowarta gida har zuwa
shigowarta cikin masarautar, abinda ya faru da ita dama
wanda ke kan faruwa bayan warkewarta. Da zarar taji motsi
koda ma Daneen Ammarah ne sai ta boye, a haka ta kwashe
kaf yinin har zuwa dare tana abu ɗaya. Da daddare bayan
kammala shirin barci maimakon kwanciya zaman karatun
Alkur'ani tayi, koda Daneen Ammarah ta shigo ta sameta a
hakan bata katseta ba. Tasa Hadimar dake biye da ita ajiye
mata madarar da suka shigo da ita. Daga haka ta fice taja
mata ƙofar da nufin ta dawo zuwa anjima, dan yanzu tana
son zuwa ta duba Malikat Haseena ne da yai batajin daɗi.
Iffah na ganin ta fice ta sauke ajiyar zuciya, addu'a tai ta
rufe Alkur'anin ta mike, kofar taje ta sanyama key bayan ta
leƙa babu kowa a corridor ɗin. Ta ɗan jingina da ƙofar tana
mai ambaton “Alhamdullah” da sakin ɓoyayyen murmushi.
Cikin sassarfa tabar jikin ƙofar zuwa ga akwatinta, ta buɗe
tare da ɗakko wayar Arfa da takardar da Malam Fawzan ya
bata. Number da aka rubuta ta kwashe a wayar, ta haye
tsakkiyar gadon ta kwanta tare da jan lallausan bargon ta
shige ciki har kanta sannan tai dailing number. Gaba ɗaya a
kage take da zumuɗin a ɗauka. Dan haka take bin sautin
shigar kiran da zuciyarta. Sai dai harta yanke ba'a ɗaga ɗin ba.
Kira ta sake yi, nan ma dai shiru, bata gajiya ba ta cigaba da
kira har fin sau goma kafin a ɗaga a karo kusan na goma sha
biyar. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tamkar wadda aka
tsamo daga cikin ƙanƙara. Sai kuma tai saurin faɗin,
“Assalamu alaikum”.
“Wa'ake nema?”.
Aka faɗa daga can maimakon amsa sallamar tata. Da lafiya
lafiya ne sai tayi mitar ƙin amsa sallamar, amma sai tai saurin
faɗin, “Sir Ajmaal”.
“Wa'ake nema?”.
Aka sake maimaita mata tambayar.
Zuciyarta ta ɗan fara zabura amma sai ta danne ta sake
maimaitawa itama.
“Sir Ajmaal”.
“Wa'ake nema?”.
Still aka sake faɗa kamar dai ba'ama jita ba.
Wayar ta janye a kunenta ta tashi zaune ta ɗauka
takardar, number dai dake a jikice dai-dai batai mistake ba.
Sake maida wayar tai kunne aranta tana faɗin (bara naga
ƙarshen ku dai) ta sake amsawa da “Sir Ajmaal”.
“Kin saɓa lamba”.
Aka bata amsa da yanke wayar lokaci guda batare da anjira
cewar ta ba......


★★..... ★... ★★.....

Kasancewar Abu Zainab suruki ga barrister cikin sauƙi suka
samu ganinsa ta hanyar kiran waya. Har office yasa
masinjansa daya fita yay musu iso ya shiga da su. Ganin
lafiyayyen office ɗin nasa dama hukumar tasu ya sake
tabbatar ma da Kaka babbane gaskiya. Sun gaisa cikin nuna
sanayya shi da Abu Zainab. Ya kuma gaida Kaka da
girmamawa kasancewar tsoho dama zai iya haifarsa. Basu
saurari lemo da aka kawo musu ba Abu Zainab ya shiga masa
bayani dalla-dalla. Sai da ya gama tsaf Barrister Abdallah dake
rubuta wa ya ajiye biron yana jinjina kansa. Kaka ya fuskanta
cikin son ƙarin bayani....
“Baba kaima kasan shi Dawood ɗin kenan?”.
“Tabbas na sanshi yaro. Hasalima ga gidan mahaifin shi
Muhammad Zayyanu gana mahaifin Dawood. Sannan ta
ɓangaren mahaifiyata ma munada alaƙar jini da mahaifin
nasa. Shine kuma yay sanadin zuwan Muhammad Zayyanu
garin nan, shi kuma Muhammad Zayyanu ya koya masa
noman zuma daya gada ga mahaifinsa”.
“Eh lallai sanayya ce babba kam. Sai dai kuma inaga ya
kamata nasan miya rabasu? Dan yanzu hujjojin hanunmu
sune zasu taimaka mana wajen kubutar da su saboda wannan
case ne babba kuma da alama shiryayye”
“To nidai kai tsaye banace ga abinda ya zama sanadin
rabuwar kawunan nasu ba. Dan shi Muhammad Zayyanu
mutum ne mai zurfin ciki da rashin kwaramniya. Amma dai
lokacin da naga bana ganinsu tare na tambayesa ko akwai
matsala? Shi da abokin nasa. Sai ya sanar min shi dai a
saninsa bai masa komai ba ya janye daga jikinsa, ya kuma
bisa ya bisa babu adadi danya faɗa masa amma yaƙi, daga
karshe ma ya tattare kayansa da iyalinsa sukabar anguwar,
bai kuma sake ganinsa ba har watanni sunja a lokacin. Na
bashi shawarar ya ƙara nemansa dai, da muka sake haɗuwa
na tambayesa sai yace ai yama bincika yabar gari. Iyakar
abinda na sani kenan gaskiya”.
“Shi kuma Dawood ɗin baka sake ganinsa ba kaima?”.
“Eh to gaskiya ban sake ganinsa ba. Dan ko'a rasuwar
mahaifinsa sai wai-wai mukaji yazo yay gaisuwa ya tafi kawai.
Daga nan kuma dai bamu sake jin ɗuriyar tasa ba dan dama
mahaifiyarsa bata raye tuni”.
Barrister dake faman kaɗa kai ya sake ajiye bironsa.
“Uhhm yanzu to inaga mataki na biyu shine musan wane
station suke. Ko kuma inda ita matar tasa take”.
Cikin damuwa Abu Zainab yace, “Munje inda muke tunanin
samun nata bamu sameta ba. Sai dai an ambata mana sunan
wanda ya saida gidan ga wanda ke ciki yanzu”.
“Miye sunan”.
“Ibrahim Askari”.
“Badamuwa kuje abunku, insha ALLAHU daga nan zuwa gobe
za'a nema mana Ibrahim Askari ɗin. Suma kuma zan ɗan
bincika ta hanyar jami'an dana sani a mabanbanta station na
garin nan”.
Sosai kaka ya dinga ma barrister godiya. Hakama Abu
Zainab. Shi dai faɗa musu yake karsu damu. Aje a cigaba da
addu'a komai zai zama labari insha ALLAHU......

★★..... ★★.... ★★.....

Iffah kamar zatai kuka ta ƙara dailing number amma sai ma
aka sanar mata switch up. Wani irin zafi da lugude ƙirjinta ya
shiga yi, ta shiga neman number Malam Fawzan cikin rawar
jiki tunda dai shine ya bata number..........✍️

23


........Itama ɗin dai switch up. Wasu zafafan hawaye suka
silalo a kumatun ta. Ƙoƙarin sake kiran waccan number ta
gwadayi knoking ƙofar da akai ya katseta. Da sauri ta yanke
kiran da kashe wayar ma baki ɗaya ta ɗaga gadon ta tusasu
har da takardar gaba ɗaya sannan ta sauka dan tasan bazai
wuce Daneen Ammarah ba...
“Ibnati baki barci ba kenan?”.
Kan Iffah a ƙasa tai ɗan murmushi. “Yanzu zanyi Mamy
karatu na kammala”.
“Masha ALLAH, ya kamata ki kwanta to dare yaja, nima
zuwa zanje na kwanta”.
“To Mamy ALLAH ya tashemu lafiya”.
Koda Daneen Ammarah ta wuce Iffah ba kwanciyar tai
ba, sake ɗakko wayar tayi ta cigaba da neman wancan layin
da a yanzu ake cemata not available saɓanin switch up na
ɗazun. Hakama number Malam Fawzan har yanzun. Daga
ƙarshe dai barci ɓarawo gwanin iya sata ne ya saceta akan
dole ta haƙura, sai da asuba ta tsinta wayar a ƙasa yashe....

Yau dai kam ta ƙudiri niyyar fita gaida tsohuwa Malikat
Haseena da kanta, tunda dai jikinta Alhamdullah hatta saɓar
ma sai inda ba'a rasa bane bai gama ba. Bayan hadimar dake
gyara ɗakin ta kammala ta fita key ta sama ƙofar sannan ta
shiga wanka. Dan duk da tausayin hadiman da takeji a yanzu
batajin zata sake yarda da waninsu. Ta fito tana tsaka da
shiryawa cikin ɗaya daga kayanta na gida akai knoking.
Karasa saka abayar tayi sannan taje ta buɗe, a tare suka
sakarma juna murmushi, tai ƙasa da kanta tana faɗin, “Barka
da safiya Mamy”.
Daneen Ammarah takai hannu ta taɓa kanta da faɗin, “Kin
tashi lafiya?”.
“Alhamdullah”.
“Haka ake so. Ga kayanki nan na amfanin yau, mun zaɓi yin
hakane saboda gudun abinda

Please Login or Register in order to submit comment