Reading Dauɗar Gora by Bilyn Abdull ce Chapter 18 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙofar ta rufe. Ciki ta koma, sai dai maimakon
zama sai ta koma kaikawo kamar mai Safa da marwa
abubuwa masu yawa na faman mata kaikawo. Ta jima a haka
sosai kafin ta sake kimtsa jikinta cikin wata tsadadiyar abaya
mai adon stones dake ta ƙyalli da ɗaukar idanu. (Wannan
yana cikin horon Daneen Ammarah data tabbatar mata koda
wasa karta zauna da kazamar shiga ko fitowa da ga ɗaki a
raguwar kwalliya. Dolene inhar zata bar cikin ɗakinta ta
tabbatar komai na jikinta ya isa a kalleta da shi. A tsarin
masarautar hakan ba fariyya bane mutunta kaine ga kowa. A
kuma ɗan zaman Iffah cikinsu ta fahimci hakan sarai). A yanzu
ma kamar ɗazun turarrukan sa ta baza har ƙamshinsu na rige-
rigen fita kafin ita ta fita. Ta fito cikin takunta na nutsuwa da
ƙasaita kamar wata budurwar macen ɗawisu (lol)..........
😉 ✍️

35
........Hadiman sashin gaba ɗaya kamshin turaren da sukaji ya
sakasu tunanin Tajwar Eshaan da bai jima da shigowa ba daga
fada ne ya sake fitowa. Sai kuma sukaga saɓanin haka lokacin
da Iffah ke ƙarasowa cikin katafaren falon mai ɗauke da duk
wani nau'in kayan more rayuwa irin na wanda suka isa. A
kujerar da ko ba'a faɗaba tsarin zubinta ya isa tabbatar ma
mai kallo Shahan-shan ne kawai ke zamanta ta kai zaune da
bismillah a bakinta. Ƙafa ɗaya kan ɗaya ta harɗe fiye da salon
sarauniyar Ingila tana kallonsu. Cikin rawar harshe dajin
kwarjininta ya cike falon tsaf suka shiga zubewa suna
gaisheta. Yatsu biyu ta ɗaga musu cike da ƙasaita batare data
amsa ba dan haka kawai yanayin da ta tashi da shi taji bata
buƙatar magana. Basu iya sun motsa ba har ta gama zuƙar
iska da fesarwa tamkar mai lissafin kaɗawarta sannan ta
dubesu, sai kuma ta maida ga tarin abincin da aka shirya
yanzu akan wata lallausar darduma saɓanin na ɗazun akan
teburin cin abinci. Akan farin tambulan na gilashi mai ɗauke
da madara fara ƙal-ƙal ta sauke idanun nata (mafarkina ya
zama gaskiya kenan ko saɓaninsa) zuciyarta ta ayyana har
lokacin idanunta tsaye akan tambulan ɗin..
Hadiman da basu fahimci ma'anar kallon da takema kayan
abincinba cike da girmamawa a gareta ɗaya ke faɗin, “Ya
Zawjata-almilk abincine daga saken mai babban ɗaki, an
shiryashi ne matsayin liyafa gareki ke da shugaba”. A hankali
Iffah ta janye idanunta daga wajen ta maida kan hadimar na
tsahon wasu sakkani, acan ƙasan zuciyarta kuwa nanata
sunan Malikat Haseenat take tamkar mai bitar karatun
hadda. Batare da tace komai ba kuma sai ta kaɗa kanta. Shiru
ya sake biyo baya kafin Iffah ta katseshi da duban hadiman da
har yanzu dai ke tsaye da alama zaman jiransu sukeyi kenan,
dan ta fahimci idan zaici abinci haka suke zagayesa. Kanta ta
kauda da faɗin,
“Maleek fa?”.
Kai tsaye duk suka fahimci wa take nufi, tunda dai duk sun
san minene ma'anar kalmar Malik ɗin. Cikin tsantsan da kai
ɗaya daga ciki ta amsa mata da “Yanzu ya shigo daga fada”.
Bata amsa ba, sai ɗan jimm da tai na tunani akan ambatar
fada da hadimar tayi, amma a zahiri ta basar abinta.


★Kasancewar saƙon haɗa liyafar cin abincin na Malikat
Haseenat da tai akan iya shi da wadda ake kira matar tasa ya
riskesa tunma kafin Iffah, dan kusan shine ma yay sanadin
barowarsa fada duk da Aaminsa Miran Jasim (Aami.
Kawunsa)ya buƙaci zaman tattaunawa da shi. Badan son
ransa ba ya kimtsa ya fito cikin shiga mai sauƙi ta zaman gida.
Kamshinsa da takun sawayensa dake tabbatar da girman
ikonsa tuni ya iso a kunne da hancin Iffah dama hadiman
dake zagaye da ita. Tuni hadiman duk sun zube bisa
gwiwunsu kawuna a ƙasa dan kallon shugaban nasu kai tsaye
haramunne garesu bisa al'adar masarautar, idanma hakan ta
faru gaban Ghazi zaka iya fuskantar tsatstsauran hukunci a
dalilin hakan. Akanta dake harɗe kan kujerar da bayan shi
babu wani mahaluki daya iya kwatanta zama kanta ya fara
sauke ƙasaittun idanunsa. Dai-dai itama ta ɗago nata
sakamakon jin takun sawayensa da zubewar hadiman. Cikin
ido suka kalla juna, hakan yay matuƙar tsikarar zuciyar Iffah
da abinda take faman hasashe da neman tabbaci a kwanakin
nan ya tabbata ɗin yau a idanunta. Dan tabbas shigar jikinsa
ta yanzu ta sake tabbatar mata da waccan fuskar... Shine ya
fara janye nasa kausasan idanun batare data iya tsinto komai
a cikinsu ba. Kamewa da gagara fassara abinda ke kan
fuskarsa kuma ya taka rawar gani wajen ɓoye ainahinsa. Sai
ma kallonsa da ya maida kan ƙaton agogon dake kafe a falon
cike da basarwa kai kace bai ganta bane. Ita madai basar da
shi ɗin tayi kamar ma bata san da fitowar tasa ba, sai
zuciyarta dake faman kai kawo a ƙirjinta cikin sauri-sauri. So
take ta gaskata shi ɗinne kota ƙaryata amma zuciyarta taƙi
bata haɗin kan karkata akan ko ɗaya a cikinsu. Sai ma neman
jefata a ruɗani takeyi......


*_BARRISTER_*

Duk yanda Barrister yaso sanin suwaye su? Mi kuma yay
musu basu saurareshi ba suka turasa cikin jibgegiyar baƙar
motarsu, yayinda ɗaya daga cikinsu kuma ya shiga motar
Barrister ɗin ya fiddo komai na ciki a cikin wata ƙatuwar jakka
suka bar wajen.. Suna ɗan matsawa a wajen wani abu mai
masifar ƙara ya ziyarci kunnuwan kowa. A take aka fara
gudun ceton rai dan duk wanda yasan bomb yasan shine a
yanzun ma.
“Innalillahi wa inna'illaihirraji'un”. Barrister ya faɗa idonsa
nabin motarsa da tai sama ta shiga dawowa pieces ƙasa
alamar dai bomb ɗin daga cikinta ya tashi. Duk da ya firgita
da mutanen yay jarumtar dubansu fuska a dake. “Ku su
waye? Miyasa kuka aikata min haka?”.
Babu wanda ya tanka masa a cikinsu, kamarma basu jisa
ba sukayi. Hakan sai ya ƙara tada hankalin Barrister, dan ya
fahimci ya shiga hannun mugayen mutanen nan kenan.
Yunƙurowa yayi da nufin ƙara magana suka jefa masa
handkherciff a fuska, daga haka bai sake sanin inda yake ba
sai buɗe idanu yay ya gansa a wani ɗaki da bai san inane ba...

Gaba ɗaya jihar Hubab da ƙasar Ruman a rikice ake akan
tashin wannan bomb, dan abune da bai taɓa faruwa da su ba.
Jami'an tsaro sun iso akan lokaci, sai dai Alhamdullah ba'a
samu asarar rai ko ɗaya ba daga mutanen gari, amma ana
tunanin harda drivern motar al'amarin ya rutsa saboda babu
wanda ya lura da sanda mutanen nan suka ƙwamushe
Barrister ɗin kasancewar komai sun yisa ne cikin ƙwarewa...
Jami'an tsaro da ƴan jarida tuni sun iso wajen akan lokaci,
hakama jama'ar gari masu jarumta sun zagaye wajen domin
ganema idanunsu. Babu gawar direban motar a duk iya
bincike da jami'an tsaro sukayi, dan basu ga wani alamar
sassan jikin mutum ba ko ɗan yatsa, hakan sai ya ɗaure musu
kai dan mutanen da abun ya faru a idonsu sun tabbatar sunga
lokacin da mai motar ya ajiye ta a wajen ya shiga masallaci,
koda aka fito kuma mutane da yawa sun tabbatar sunga
lokacin daya nufi motar wasu ma sunce har ya shiga. Wannan
zance ya sake ɗaukar hankalin jama'a kowa yana faɗar
albarkacin bakinsa akan al'amarin...

Isowar wasu samari wajen kusan dai-dai da tashin bomb
ɗin, kallon juna sukai da sakin dariya a tare suna tafawa. Sai
da sukai mai isarsu drivern dake jan motar ya ɗauka waya.
Nuni yay musu da suyi shiru. Take motar tai tsit kuwa. Ya ɗan
rissina cike da girmamawa tamkar yana a gabansa ne yana
kwasar gaisuwa, bai damu da a yanda aka amsa masa a daƙile
ba ya cigaba da faɗin, “An rufe babinsa ranka ya daɗe”.
Murmushi yayi alamar an amsasa da magana mai daɗi daga
can. Sai kuma ya sauke wayar da juyawa yana kallon ƴan
uwansa ya kashe musu ido. Dariya suka shiga kwasa a yanzun
ma, bayan sanyi wadda suka gamsu sun wadata sannan suka
fita suma suma shige cikin taron mutanen dake wajen dan jin
mi'ake tattaunawa.....

★★★..... MASARAUTA ★.....

Sai da ya kai zaune a inda aka shirya tarin abincin da kusan
minti biyu sannan ta motsa itama dalilin maganar da Hadimai
sukai mata. Bata musa ba ta miƙe zuwa inda yaken cikin
takunta na nutsuwa da wasu ke ɗauka yanga ko makamancin
hakan. Zama tai irin nasa na ƙasaita sai dai da alama ita kanta
bata fahimci tayi hakan ba ma. Tsaurin idonta ya sakashi
dubanta ta gefen ido batare da alamar hakan ta bayyana a
yanayinsa ba. Tuni hadiman suka ƙaraso domin shirya abincin
garesu. Iffah batai yunƙurin hanasu ba, dan a ganinta dole ta
nutsu ta fara fahimtar yanda ake masa komai kafin ta karɓa
wannan tsarin shima. Ta ɗan bi madarar da hadimar ta
ɗauka, har yanzu zuciyarta na mata wasiwasi akan madarar
batare data san dalili ba...
“Bar nan”.
Ta faɗa dai-dai Hadimar na yunƙurin zuba madarar a ƙaramin
cup na glass daya gama haɗuwa. Cikin mamaki hadimar ta
sake risinar da kai domin girmamawa ga Iffah tana faɗin, “Ya
Zawjata-almilk madara na ɗaya daga cikin abinda shugaba
yafi buƙatar amfani da shi a irin wannan lokacin”.
Kai tsaye babu ko ɗar tattare da Iffah tace, “Na yau dai
bazai sha ba. A ɗaukesa anan”.
Tsoro ne ya bayyana sosai a fuskar hadimar, gashi bata da
damar ko satar kallon sashin da Tajwar ɗin yake balle ta
fahimci karatun tasa fuskar. A ɗan ɗar-ɗar na rashin madafa
ta ajiye tambulan ɗin a gefe ta ƙarasa aikinta. Duk da abinda
ake yi a gaban Tajwar Eshaan ne, yanaji kuma yana gani.
amma tsabar miskilanci da ƙarfin iko irin na masu ƙasa a
hannu bai ko motsa ba balle bada wata alama akan abinda
Iffah tayi ya bashi mamaki, ko ya ɗimautashi, koya birgesa,
koya bashi haushi. Ko ɗaya babu mai iya tsinta a yanayinsa.
Iffah ma dai bata yarda ta dubesa ba balle ta tsinta komai a
tattare da shi ɗin. Sai ma wani kallon da taima hadiman ya
tabbatar musu bata bukatarsu a wajen. Dan haka tuni suka
ɓace tamkar ƙyaftawar ido.
Ya ɗan ja wasu mintuna zaune batare da ya taɓa komai
ba, Iffah ta ɗan laɓe baki, acan ƙasan maƙoshi ta furta
“Ranka ya daɗe barka da wannan lokaci”.
A hankali ya ɗago ya zuba mata idanunsa, a mamakinsa
bashi take kalloba ma. Kuma ya tabbatar itace tai maganar ba
wani ba dai. Sake tsukewar fuskarsa mai cike da gizago da
motsa hanunsa dake kan spoon ya tilasta Iffah ɗan ɗagowa
garesa. Sai kuma ta tsaya cak tare da ɗago birkitattun
idanunta da ƙyau. Cikin nasa dake kallonta suka shige tamkar
ya tsara hakan da gayya. Muƙut ta haɗiye yawu da ƙoƙarin
kame rauninta dake neman bayyana a fili ta kauda kai gefe..
Shima nasan ya janye a ƙasaitance ya fara cakulal abincin
kamar mai cin magani batare da ya amsa mata gaisuwar tata
ba. Hakan da yay ya sosa zuciyar Iffah, dan haka ta kumbura
fuska lips ɗinta suka shiga motsawa alamar akwai magana a
bakinta sai dai babu damar faɗa...

★★.... ★....

Tun bayan tabbatar da madarar ta shiga jerin abincin
liyafar da aka shiryawa Shahan-shan da Zawjata-almilk ta
kasa zaune ta kasa tsaye, bukatarta kawai taji sakamakon da
take buƙata ga amintacciyar hadimarta akan lokaci. Sai dai
kuma shiru kakeji wai malam yaci shirwa har lokacin da
labarin tashin nakiya a jihar Hubab ya iso cikin masarautar. Ba
wannan ne a gabanta ba, dan haka cikin jan tsaki ta kashe
television ɗin a harzuƙe. Idanunta ta sake maidawa kan
agogon falon tanaji kamar tai tsalle ta ganta a sashen Tajwar
Eshaan ɗin ayita ta ƙare. Dan yanzu a duniyar nan gani take
bata da babban maƙiyya sama da yarinyar nan datai mugun
shige mata hanci amma ta gagara fyatota ta huta a dalilin
gargaɗin Uwa data kasa gane manufarsa har yanzu. Sai dai
yarda da Uwa ɗin ya tilasta mata bin komai ɗin a sannu. Zata
iya rantsuwa tunda ta san kanta bata taɓa cin karo da abinda
ya kiɗima zuciyarta ba irin saƙon Zawjata-almilk na raye
bayan ta kwana a turakar Shahan-shan kuma. Ba ita kawai ba,
hatta Uwa hakan ya kiɗimata da sake tabbatar da yaƙine na
gaske tsakaninsu da wannan yarinyar kenan. Dan haka batai
wani magana mai tsaho da Ta-kurya ba bayan bata umarnin a
isar da madarar data bata ga Iffah ta ɓace cikin tsanani ɓacin
rai daya ƙara birkita dukkan tunanin Ta-kurya ɗin a yanzu har
ta kasa zaune ta kasa tsaye sakamakon hakan........✍️

36


........Isowar labarin tashin nakiya a jihar Hubab ya matuƙar
tada hankalin duk wani mai faɗa a ji a daular ruman. Dan
abune da bai taɓa faruwa ba a kasar ta ruman. Amma abin
mamaki ga Tajwar Eshaan ba hakan bane, dan babu wani
alamar damuwa ko nuna kaɗuwa da lamarin. Kallo ɗaya
yayma akwatin talabijin ma ya ɗauke kai kamar ba'a ƙasar da
yake mulka matsayin shugan kowa da kowa al'amarin ya faru
ba. A karan farko wani abu da tun shigowar Iffah masarauta
bataji akansa ba ya tsikari zuciyarta sakamakon ganin halin da
ya nuna akan wannan al'amari da duk wanda ya kwana ya
tashi a ƙasar ta ruman bazai ce bai shiga ruɗani ba. Duk da
ance ba'ai asarar rai ko ɗaya ba taji kamar ta tashi ta shaƙure
wuyan Shahan-shan ɗin ta huta da ganin wannan azzalumin
shugaba da kansa kawai ya sani sai ahalinsa.
“Mi hakan ke nufi?”.
Ta faɗa tana faman kai kawo a ruɗe itama duk da a labarin an
sanar da ba'a samu asarar rai ko ɗaya ba sai dai dukiya. Abu
mafi caja ƙwaƙwalwa ga kowa ma ba ita kaɗai ba shine jin wai
wanda ya dasa bomb ɗin ya tsere Bayan wasu sun tabbatar
da sunga fuskarsa da shigarsa motar, musamman ma wasu
samari huɗu da suka tanbatar da tare suke da wannan mota
tun daga ƙauyen Lufana da alama mutumin daga can ya fito.
Tabbas sai tayi ajalin wannan mutumin a zuciyarta zataji
salama. Dan a ganinta idan yau ya tashi kowa bai rasa ransa
ba na gobe kuma fa? A wannan gaɓar ta fara zargin anya
wannan sarkin bada wata manufa dama ya dawo ya karɓa
mulkin mahaifinsa ba? Dan alamu sun fara nuna uban nasa
ma shine ya kasheshi.
“Lokaci yayi da zan fara aikina gadan-gadan”.
Ta faɗa a zahiri cikin tabbatarma kanta da yanayin ɗaukar
alwashi....

(Muma kam muna bayanki Iffah, dan muna son sanin mike
zuciyar wannan bahagon sarki haka mai wahalar fahimta😉).

★★★
A babban zauren majalisan manyan masu faɗa aji na
daular ruman kuwa na can yana neman hargitsewa dangane
da faruwar wannan al'amari. Kowa faɗar albarkacin bakinsa
yake a duk yanda zuciyarsa ta ayyana masa musamman masu
sukar mulkin Tajwar Eshaan a fakaice. Duk wannan kace nace
da akeyi Tajwar Eshaan ɗin na zaune cikinsu amma uffan bai
tofa ba har suka ci suka tsire. Sai da suka lafa dan kansu da
kuma maganar Miran Arshaan cikin ɓacin rai a garesu sannan
Tajwar Eshaan ɗin ya buɗe idanunsa dake a lumshe ya gama
ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya..
Akan Miran Arshaan dake cigaba da faɗa rai ɓace kan
kausasan maganganu nasu ga ɗan ɗan uwansa kuma sarkinsu
a yau basu dace ba ya sauke idanunsa. Cikin muryarsa mai
zurfi da ƙasaita ya fara magana a gadarance kuma a fisge...
“Barsu Aami. Waninsu bazai canja komai ba, kamar yanda
bazai tirsasa Eshaan yin komai ba. Abinda kawai nake son ku
sani, Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed guguwace data gama
turniƙeku, kuma babu ruwan kogin da zai iya shayar da ita
ruwan da zata lafa. Ku daina bama kanku wahala ƙasar ruman
da jama'ar cikinta a rubuce suke tsakkiyar tafin hannuna. Idan
na murza kwafsanku kawai duniya zata gani a cikin guguwata,
idan na matsa, jininku ne zai dinga ɗiga a ƙarƙashin sawun
ƙafata na ringa bi ina takawa matsayin kwalta, ya rage naku
ku zauna a inda na baku zaɓi ko ku zaɓo mummunan
ƙaddararku da kanku tun lokacin ɓacewarku a doron ƙasa
baiyi ba”.
Yana gama faɗa ya miƙe cike da takun Izza da kasaita ya
bar falon. Da kallo duk suka bishi ran wasunsu na ƙuna,
zukatansu kam tamkar zasu kifo ƙasa dan firgici. Cikin dauriya
da nuna jarumta wani ƙyamusashen dattijo da tsufansa ya
fara bayyana a cikinsu yay ƙwafa rai ɓace da kausasa murya.
“Lallai wannan yaron ya cika ya tumbatsa kuwa. Wai
kenan haka zamu cigaba da zama yaro ƙarami na tafka
kuskure da mulkin zalunci yana kuma takamu a yanda ya
gadama. Akaf tarihin mulkin daular ruman ba'a taɓa tsageran
yaro kamar wannan ba, amma ubansa ya ɗaura shi matsayin
Shahan-shan bayan babu mai makamancin shekarunsa daya
taɓa zama a wannan matsayin. lokaci yayi da zamuyi bore
wajen tsigesa kafin ya gama halaka ƙasar baki ɗaya tunda
naga shi ran ɗan adam ba'a bakin komai yake garesa ba.
wama ya sani ko shine yasa a dasa nakiyar kamar yanda ya
kashe ubansa da ƴaƴan mutane da aka aura masa. Koda yake
minene ma na tantama tunda ga amsa ya bamu da bakinsa
cewar ƙasar da ƴan ƙasar duk a tafin hannunsa muke”.
A zahiri dai kowa yay tsitt yana sauraren dattijon, amma a
zukatan wasunsu farin cikine fal da zantukan wannan tsoho
ga Tajwar Eshaan ɗin da mafi yawansu shakkarsa ta gama
zagaye tunaninsu duk da kuwa kusan duk sun haifesa dan
babu wani sa'ansa, dan har yanzu tun ƴan majalissar mulkin
mahaifinsa ne bai canja ba. Dattijon na rufe baki Miran Jasim
ya miƙe rai a ɓace shima. Dattijon ya watsama wani
mummunan kallo da faɗin, “A lallai ka cika dattijon banza dan
bazan kalleka matsayin Aami ɗinmu ba yau kam. Mun
godema ALLAH daya fara nuna mana ku a zahiri, ai bamu san
ɗan ɗan uwanmu ya kai muku har haka a zuciya ba sai yanzu.
To ku sani duk ma mai irin wannan tunanin ya makaro,
Eshaan kuma a gareku sai gani sai hange sai hararar nesa,
dan badai mutum ba ku rubuta ku aje”. Ya kare maganar
yana ɗan ƙyaftama Miran Arshaan daya saki baki tsabar
al'ajabin ɗan uwan nasa da kasa fahimtar inda ya dosa. Cikin
sauri ya kaɗan kansa da amshe zancen a fusace shima yana
miƙewa. “Aam ai ban san haka kakeba wlhy sai a yau, ashe
zaka zama na farko a jerin wanda zasu soki jinin Haysam Akhi
kuma ɗan uwanka mahaifinmu dan ƙasa ta rufe idanunsu? To
bazamu ce da ku komaiba a yanzu, amma kusani duk wanda
yake da wannan ƙudirin a ransa jininmu fansa ne ga kare
Eshaan tako wace fuska. Mun barku lafiya”.
Waɗan nan zantuka na Miran Jasim da Miran Arshaan sun
matuƙar saka ruɗani a zukatan duk wanda ke a wannan
zauren taron. A take wasu suka shiga barranta kansu ga
wannan magana ta dattijon Aamin sun ganin waɗanda ma ya
dace suyi hanƙoro da kwarema Tajwar Eshaan ɗin baya
saboda kwaɗayin kujerar da yake kai tunda suma sunada
hakki a kanta na tare da shi su kuma a wa. Anan fa rikici ya
kaure aka tashi baram-baram....

★★

“Nikam na kasa fahimtar dalilin ka nayin hakan”.
Miran Arshaan ya faɗa bayan fitowarsu daga zauren
tattaunawar. Wani shegen murmushi Miran Jasim ya saki cike
da basarwa. Sai da sukai nisa da sashen Tajwar Eshaan gaba
ɗaya sannan yay wata ƴar dariya batare daya kalla Miran
Arshaan ɗin ba. Shimfiɗa kenan daga cikin plan b, harinmu na
gaba shine ƙulla alaƙa da yarinyar nan, dan na san yanzu
abinda zatai yinƙurin farawa shine bincike akan wanene shi”.
“Wai ya akai duk kake sanin hakan?”. Miran Arshaan ya
tambaya cikin mamaki. Dariya Miran Jasim yayi sosai da
faɗin, “Arshaan Akhi har yanzu kai ɗin yaro ne. Waya gaya
maka mai nema yana zaman jiran tsammani. Tashi yake da
ƙwanji da zuciya wajen samowa ai. Karka damu da inda na
sani, kai dai kawai ka tabbatar littatafan nan da mukai
magana kwanaki an kaisu books room an ajiye a daren yau,
dan bana raba ɗayan biyu zuwa gobe zata iya bukatarsu”.
Cikin halin ko'in kula Miran Arshaan ya ɗage kafaɗu da
tabe baki, sai dai acan ƙasan ransa dariya yake dan shima
akwai nasa shirin akan hakan tun randa sukai maganar......

★★

Duk da fuskarsa mai tsananin ɓoye sirrin zuciyace a yau
ɓacin ransa sai da ya bayyana. Huci kawai yake faman
furzarwa a kai-akai. Dan daga ɗakin meeting ɗin nasu da ba'a
samu damar tattauna abinda ya dace ba kai tsaye sama yay
can ƙarshen rufin ginin sashen nasa da aka gyara domin
hutawa kawai. Ko gaisuwar hadiman dake tsare da ƙofar
shiga wajen baiyi ba. Ya jima yana faman kai kawo
hannayensa zube cikin aljihun farin wandonsa. Bakajin komai
tattare da shi sai shaƙa da furzar da numfashi. Sai da ya ɗan
samu nutsuwar da yake bukata ya zaro waya dake cikin
aljihunsa. Kira yay, bugu ɗaya kuwa aka ɗaga, batare daya
amsa gaisuwar da ake masa ba a kausashe ya furta. “A sakaya
min shi, inda babu wani mahaluki da zai taɓa hasashe a
kansa”. Yana gama faɗa ya yanke kiran cikin sake tsuke fuska
da zuƙa ya fesar.....

(Anya kuwa....?? 🤭bakina kanen kafa ta dai🏇).

★★

A ɓangaren Iffah tana tsaka da kai kawonta da ƙullawa da
warwarewa itama wani tunani ya sata tsayawa cak. Miƙewa
tai cikin gamsuwa, sai kuma ta koma ta zauna bisa wani
tunanin da yazo a bayan wanda ya sata mikewar. A kallo ɗaya
zaka fahimci tana cikin yanayin da duk wani ɗan ƙasar zaka
iya ganin ya shiga sakamakon wannan baƙon al'amari daya
shigo musu. Da farko bai lura da ita ba saboda idonsa rufe
yake da ɓacin rai har lokacin, sai da ya kai zaune yay ƙoƙarin
lumshe ido sai kuma ya buɗesu a kanta dai-dai itama ta
kallesan mamakin yanayinsa na yanzun kuma fes a fuskarta.
Ita ta fara janye nata shima sai ya furzar da huci mai zafi yana
maida nasa ya lumshe kamar yanda yayi a farko.
Falon ya ɗauka shiru babu alamar wani zai tanka sai karar
na'urorin ac dana tv da har yanzu ake cigaba da nuna
al'amarin da yanda hankulan jama'a ke tashe. Kiran sallar
la'asar ne ya katse zaman shirun nasu. Iffah ta fara
yunƙurawa ta tashi batare da ta ko sake kallonsa ba dan da
gaske har cikin rai haushinsa takeji yau. Da kallon ƙasan ido
ya bita harta ɓacema ganinsa. Ya ɗan sauke ɓoyayyar ajiyar
zuciya da maida idanunsa ya rufe. Sai da Iffah tai kusan
mintuna huɗu da barin wajen sannan ya mike shima har
yanzu da alamar ɓacin rai tattare da shi....

★★★....

Bayan Iffah ta idar da salla kamar yanda ta tsara tai
shirinta tsaf cikin wata doguwar riga mai tsananin ɗaukar
idon duk wanda zai iya kallonta. Kamshin data gaje batare da
umarnin mai shi ba ta baza tamkar tayi ɓarinsa a jikinta. A
cikin dukkanin shirinta babu bijirema umarnin waɗan da tazo
wannan matakin a dalilinsu, dan haka kai tsaye tai kiran
number Daneen Ammarah. Ana ɗagawa tai sallama cikin
sauƙaƙa murya mai nuna ladabi. Daga can Daneen Ammarah
ta amsa cike da zumuɗi da nuna jin daɗinta da wannan kira.
“Shahrbano ce da kanta haka?”.
Murmushi Iffah tai mai bayyana haƙora jin sunan da Daneen
Ammarah ta kirata da shi. Ta girgiza kai tamkar tana a
gabanta. “Mamy zakisa a tsire ni a tsakkiyar daular ruman
fa”.
Dariya sosai maganar ta bama Daneen Ammarah. Dan
haka ta dara sosai kafin ta tsagaita. “Waya isa ya tsire Ibnati
kuma Shahrbano duk faɗin ƙasar ruman. Babu mai wannan
power ɗin Ibnati, ko maƙiya sun san kin gagara sai kallo daga
nesa, dan kowa ya tabbatar a yanzu ke ɗin ce _Lady of the
city_”.
Komai Iffah bata iya tace ba, sai dai Daneen Ammarah
na iya jiyo sautin murmushinta harta gama kwarzantata.
“Mamy dama na kiraki ne na shaida miki ina ɗan son na
fito zama waje ɗayan ya isheni, daga nan sai na ɗan leƙama
ɗakin karatu kozan samo abin ɗebe kewa”.
“Hakan kam yana da ƙyau Ibnati. Dan haka ki shirya kawai,
hadimanki na sashenki za'a sanar da su su tsumayi fitowarki”.
“Nagode Mamy, ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsohon rai mai
amfani da albarka”.
Cikin jin daɗi Daneen Ammarah ta amsa da Amin tana
mai saka mata albarka itama.

A yau kam Iffah ta ƙara tabbatar da tsantsar ƙarfin ikon
mulkin wannan daula. Dan tunda ta baro hawa na ƙarshe
hadiman sashin na Shahan-shan ke faman zubewa gabanta
batare da dubi da ƙanƙantar shekarunta ba, matsayinta kawai
suke kalla. Duk sai taji zuciyarta babu daɗi ganin kusan duk
shekarunsu zai iya kaiwa dai-dai dana Hanash, wasu ma sun
girme masa. (Nace Iffah danma Tajwar Eshaan yayi sauyi ne
da matasa kikaga hakan, da har sa'an kaka da Babiy sai kin
gani kuwa). Kamar yanda Daneen Ammarah ta faɗa tako
samu hadiman na zaman jiranta. Ta gane hakanne ta hanyar
zuwa da sukai suka zube a gabanta da sanar mata
matsayinsu. Batare da damuwa ba duk ta bisu da kallo, su
biyar ne cif kuma duk yara ƴammata matasa, za'a iya samun
sa'aninta dama wanda suka girme mata kamar su Fariha.
“Ina buƙatar zuwa books room ne akwai wani tsari akan
hakan?”.
Da sauri ƴar babbar dake ta gabanta sosai ta girgiza kai.
“Ga Zawjata-almilk babu wani dokar yin hakan ALLAH ya

Please Login or Register in order to submit comment