Reading Dauɗar Gora by Bilyn Abdull ce Chapter 16 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haɗiye yawu da ƙyar cikin ɗan harɗewar harshe
yace, “Baba tafiya ne?”.
Kaka dake nazartarsa ya ƙyabe baki cikin masa kallon
sama da ƙasa yace, “Kaima nasun ne?”.
Sai da gaban saurayin ya faɗi, amma yay jarumtar ƙwaɓe
fuska da faɗin, “Nasuwa kuma Baba? Ni fa mai taxi ne, na
hangokane kawai na iso”.
Kaka ya cigaba da masa kallon nazari, sai kuma ya furzar
da isaka da kauda kansa yana kallon mutanen daketa faman
kai kawo a titin cikin son watsar da lamarin saurayin...
“Bar wajen kamar kayi fushi”.
Aka faɗa daga cikin bluetooth ɗin dake manne a
kunensa........✍️

31


.......Takun da baifi uku ba Kaka ya juyo ya bisa da kallo,
kamar a bazata saurayin ya tsinkayi muryarsa na faɗin,
“Jumna zanje”.
Yi yay tamkar bai jisa ba. Hakan yasa Kaka sake ɗaga murya
amma ya cigaba da sharesa shima. Yana ƙoƙarin shiga
motarsa Kaka daya biyosa a baya yace, “Haba ɗan nan baka
jini bane?”.
“Sarai na jika Baba. Na fahimci ba tafiyar zakai ba, ba
kuma hurimina bane tilastaka”.
A karan farko kaka ya saki murmushi. “ALLAH sarki, to
ayima tsoho haƙuri ɗana”.
“Baba kamin laifin komai ba ALLAH, ai aikina ne. Dama
naji kana sanarma wancan ne ni kuma hanyatace shiyyasa ma
naje gareka. Zanje ƙauyen Yamanu ne dama”.
“A Alhamdullah, lallai hanyarmu ɗaya Bara na ɗakko
kayana.”

Mutum biyu kawai saurayin ya ƙara ɗauka bayan kaka
suka ɗauki hanya. Hakan baisa kaka ya ji wani zargi game da
shi ba. Sai ma hira da suka dingayi kai kace sun san juna.
Bayan sauke mutum biyun daya ɗakko har ƙofar gida ya kai
Kaka. Yaji matuƙar jin daɗin wannan karamci dan haka yay
masa tayin shiga ciki yasha ruwa. Saurayin ya ɗan nuna
tirjewa amma Kaka ya janye ra'ayinsa a dole ya bisa suka
shiga, sai dai dama a ransa hakan yake fata.
Ummu na zaune a tsakar gida ita da Iyyani, ta rame
matuƙa tayi duhu irin na wanda ya shiga damuwa. Tamkar an
sare gwiyawun Kaka ya ƙarasa shiga idanunsa akan Ummu
data tsurama bayansa ido. Iyyani ma jiki a sanyaye ta miƙe
dan tasan komai tunda kullum sai sunyi waya da Kaka. Itace
tai ƙarfin halin masa sannu da zuwa. Ya amsa a sanyaye yana
waiga bayansa.
“Yaro shigo mana”.
Kaka ya faɗa domin samawa Ummu nutsuwa. Da sallama
saurayin ya shiga. Ummu tai ƙasa da kanta a hankali.

Bayan sun gama zama a tabarmar da Iyyani ta shimfiɗa
musu saurayin ya fara gaishe da Ummu. Bata amsa ba, hakan
ya sakashi shan jinin jikinsa yay shiru a sanyaye. Iyyani data
sake kawo musu ruwa ce ta amsa masa da “Bata magana
yaro”.
“ALLAH sarki” ya faɗa cikin sauke ajiyar zuciya ita ya
gaisheta. Da kulawa ta amsa masa dukkan hankalinta a kan
Kaka dake kallon Ummu tamkar ya samu television. Ummu
da hawaye suka cikama ido ta miƙe a hankali, ɗaki ta shige
duk suka bita da kallo. Kaka baice komai ba hakama Iyyani
data zarce kitchen sai gata da kwanon abinci.......

★★... ★★★ ....★

Tamkar raƙumi da akala haka Iffah ke tafiya bisa
jagorancin Malikat Haseenat. Kasancewar dare ne babu
yawaitar hadimai masu hidima. Sai dai masu tsaro tako ina
kai kace zasu iya kare ran wanda suke tsaye a dalilinsa daga
ziyartar mutuwa. Tsirarun hadiman da suka samu nata
zubewa kwasar gaisuwa, Malikat Haseenat ce kawai ke iya
jinsu da ganinsu. Iffah dake ta faman sauke ajiyar zuciya da
al'ajabin dukiyar dake narke a wannan gini ji take komai ya
ƙwace mata. Ta kasa fasalta komai ta kasa auna komai a
ma'aunin rinjayen aikin zuciya dana ƙwaƙwalwa....
“Bismillah”.
Malikat Haseenat ta katse mata ɗimuwar da take ciki ta
hanyar nuna mata ɗaya daga cikin kujerun katafaren falon
mai cike da abubuwan da bazasu lissafu ba. Da gaske Iffah
bazata ma iya tantance yanda akai ƙafarta tazo nan ɗin ba.
Komai Malikat Haseenat batace ba, dan ta gama karance
ɗimuwar dake jagorantar fitar numfashin Iffah. Amintattun
Hadiman dake a falon na uku suka zube gaban Malikat
Haseenat kawunansu a ƙasa. Hannu kawai ta iya ɗaga musu.
Babu buƙatar sai ta faɗa abinda tazo dan shi, shugaban
hadiman dake a wannan falon ya miƙe zuwa ga landline
domin isar da saƙon zuwanta...
“Tsahon rai da lafiya su tabbata ga Uwa a garemu,
shugaban na tsumayen isarku a falon sama”.
Shiru malikat Haseenat batace komai ba. Yayinda Iffah da
zuciyarta ke luguden ke saurarensu cikin juyewar tunaninta
da har yanzu bai dawo dai-dai ba. Kusan mintuna uku Malikat
Haseenat taima Iffah nuni data miƙe, ita kuma ta birka
wheelchair ɗinta suka shiga lifter. Mintuna biyu ne kacal suka
iso da su katafaren falon da yafi kowane falo ƙawatuwa a kaf
daular ma da sashen kawai ba. Iffah tai ƙoƙarin danne
harbawar ƙirjinta sakamakon tozali da wanda ke zaune a
falon cikin zama na ƙasaita da izzar masu mulki. Tafiya take
tamkar hawainiya saboda tsabar kasala da sanyin gaɓɓai.
Zuwa yanzu wannan fuskar bata aljani take fassarata ba,
neman ƙarin bayani take a kanta a dalilin ganinta a waje biyu
da basu da alaƙa da juna a zahirin rayuwa...
Tajwar Eshaan da ke kishingiɗe bisa ƙayataccen kujera mai
kama da wani madaidaicin gado gabansa butar shayi ce da
ƙaramin kofin da alamu suka nuna yasha ko zai sha, idanunsa
ya janye daga kan television da yake kallo ya ɗan waigo
garesu. Akan Iffah dake tafiya tamkar hawainiya ya fara
saukewa, fuskarta a sakaye take, hanunta dake riƙe da rigar
jikinta ne ta ƙasa kawai a bayyane. Janye wa yay ya maida ga
Malikat Haseenat. Ta ɗan hararesa da salon kulawa da nuna
damuwa. Idanun ya janye a sannu daga kanta itama yana
sakin kasaitaccen murmushi....
Harya gama gaisawa da kakar tasa a yanda yake kishingiɗe
batare da ya motsa ba Iffah na tsaye ƙyam tamkar an dasata.
Malikat Haseenat ta maida kallonta gareta tare da ambatar
sunanta. A dake Iffah ta amsa dan tayi alƙawari ma kanta
bazata taɓa barin rauninta sake bayyana ga kowa ba a
yanzun. Kafinma Malikat ta sake cewa wani abu tai ƙasa a
hankali, cikin rashin ƙwarin jiki ta zube ƙasan lallausan carpet
ɗin da ko jikin zomo bazai nuna masa laushi ba. Ƙamshi ko
ba'a magana dan ko'anan ake shukashi iyaka kenan.
“Amincin ALLAH ya tabbata a gareka”.
Ta faɗa badan har zuciyarta abinda take son faɗar kenan
ba. Sai dai kwarjininsa daya mamaye falon da duk girmansa
take jinta a matse yaƙi bata damar fitar jin zafinsa dake a
ƙasan zuciyarta a zahiri. Kamar a waccan ranar yau ma bai
amsa ba, babu ma alamar yajita tattare da shi. Daga cikin
hular alkyabbar jikinta ta cije lips ɗinta da masifar ƙarfi
tamkar zata hudasu da haƙori.....
“Ai ma Zawjata-almilk rakkiya ɗakin da Tajwar zaiyi barci
a yau”.
Furucin Malikat Haseenat ga hadiman dake rakuɓe gefe
zube a ƙasa kawunansu rissine tun shugowarsu ya nema
sarƙe numfashin Iffah da Tajwar Eshaan a lokaci guda. Babu
wanda Malikat Haseenat ta kalla a cikinsu sai ɗaya daga cikin
Hadiman ce da suke girki ta miƙe da rawar jiki zuwa inda Iffah
take. Dole ta mike dan a furucin Malikat Haseenat babu wasa
ko ɗaukar turjiya ga kowannensu....
Shiru falon babu wanda ya sake ƙwaƙwƙwaran motsi har
hadimar data raka Iffah iyakar ƙofar ɗakin ta dawo Malikat
Haseenat ta sallamesu. Da ga shi sai ita suka rage, dan haka
ya kafeta da idanunsa. Kai Malikat Haseenat ta ɗauke gefe
tamkar bata gansa ba ko fahimtar kallon.
“Anan zata zauna, sai ka zaɓi inda kake buƙatar ta
kasance har tsahon sati ɗaya, dan zuwa gobe idan ALLAH ya
kaimu masu mata hidima zasu kasance tare da ita. Na damƙa
amanarta a hannunka, ina kuma fatan ta kasance ƙarƙashin
kariyar UBANGIJI. Fatan alkairi da shiga sabuwar rayuwa, tare
da tayaka murnar sabon aure. Na barku cikin amincin
ALLAH”.
Da alama gushewar numfashi da rikicin wannan tsohuwa
ya gama daskarar da jinin Shahan-shan. Dan harta fice a falon
ko gashin idonsa bai ƙyafta ba, kai kace wani butun butumine
aka dasa a wajen domin tarihi.......

(🤔Tsohuwar nan kuwa na lafiya? Zata kai mana Iffah har
ƙuryar Dodon Mayu🥱🤦).

★★... ★★....

Duk da dare ne gaba ɗaya masarautar ta ɗauki ɗumi bisa
wannan bahagon hukunci na Malikat Haseenat. Basu da
al'amarin yazoma a bazata ba, hatta Malikat Bushirat da
Daneen Ammarah da Jasrah da akai zaman da su komai ya
musu cak. Abinda suka sani kawai komawar Iffah sashenta,
bawai kaita turakar Shahan-shan ba. Miyasa Malikat
Haseenat ta canja lissafin a kan kansu suma?. Wannan itace
tambayar daketa musu kaikawo su duka.

“Ni kam dai a wannan gaɓar na kasa gane komai wlhy
Akia. Shin minene dalilin Mamma nayin haka? Miyasa lissafin
ya canja daga yanda muka tsara gaba ɗaya?”.
Kamar malikat Bushirat bazata tanka har ta kai ta kawo
kusan sau uku kafin ta dubi Jasrah mai maganar. “Kaina ya
kulle Jasrah”. Ta faɗa a takaice da kaiwa zaune bakin gadon
ta dafe kanta.
“Ya ALLAH! Wlhy zuciyata ta fara kai ni ga hasashen wani
abu daban?”. Jasrah ta sake faɗa tana dafe nata kan itama.



A ɓangaren Daneen Ammarah ma dai a rikicen take. Sai
dai ita nata lissafin yasha banban da nasu Malikat Haseenat.
Daga ɗakin taro bedroom ɗin Malikat Haseenat ta wuce
zaman jiranta. A zaman da bai wuce mintuna arba'in ba kuwa
sai gata. Kallo ɗaya taimata ta ɗauke kai. Hadimar dake biye
da ita ta ajiye madarar hanunta da zubewa ƙasa tana gaida
Daneen Ammarah. Hannu kawai ta ɗaga mata....
“Na matuƙar gajiya, kwanciya kawai nafi buƙata”.
Malikat Haseenat ta faɗa tana wulla kekenta hanyar
bathroom ɗinta batare data sake kallon Daneen Ammarah
ba. Da kallo ta bita cikin shakku da shan jinin jiki. Dan duk da
a dunƙule tai magana tana nufin bata bukatarta a ɗakin
kenan. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fice zuciyarta na faman tsalle-
tsalle...

Duk yanda taso kwanciya ta kasa hakan, fargaba da
tausayin Iffah ne ke matukar ɗawainiya da ita. Har cikin
zuciya bata son rasa yarinyar dan ta matuƙar shiga ranta.
Soyayya take mata irin ta ƴa da uwa. Ita kanta har takanyi
mamakin yanda takejin Iffah a rai matuƙa, amma tasan
wannan ƙaunar daga ALLAH ne kawai. Wayar dake a
hannunta ta ƙara rumtsewa, ta gwada kiran Iffah ya kai sau
huɗu kenan amma tana fasawa, so take taji lafiyarta ko zata
samu ƴar nutsuwa, amma wata zuciya na gargaɗarta da
kalmar rashin dacewa....

★★.....

“Mi wannan tsohuwar ke nufi wai shin? Ko itace abin
neman mu kamar yanda barbushi ya sanar mana?”.
Miran Arshaan yaja numfashi ya fesar, kamar bazaice
komai ba sai kuma ya kafe Miran Jasim da kallo yana girgiza
kai. “Wlhy kaina ya kwance Jasim Akhi. Na kasa gane komai a
wannan gaɓar, abinda na sani kawai shine mutuwar yarinyar
nan a wannan gaɓar tamkar mutuwar cikar birinmu ce, dan
na gama ɗora dukkan hope ɗinmu a kantane. Bai kamata ta
mutu a yanzu ba har sai ta ƙarasa mana aikin da muka kwashi
tsahon shekaru muna ginawa”.
“Miye mafita?”.
Cewar Miran Jasim a firgice, dan zantukan Arshaan ɗin kamar
sun zaburar da shi ne abinda ke gabansu. Kai tsaye Miran
Arshaan yace, “Ziyartar Barbushi a wannan daren, kafin
waccan sankaran matar da ban san amfaninta a tafiyarmu ba
tazo ta ishemu da tsarin banza”.
“Hakan yayi mun, babu amfanin ɓata lokaci kaje kayi
shiri”.
Kai Miran Arshaan ya gyaɗa masa, tare da mikewa ya fice.
Da banzan kallo Miran Jasim ya bisa, cikin ƙanƙance idanu da
wani shu'umin murmushi a fuskarsa “Ba matar can bace
kawai abin banza a cikinmu, har da kai Arshaan, daka gama
mun amfani zan kawar da kai, dan ni kaɗai nake son mulkar
daular ruman batare da ɗan uba ko ɗaya ba da zai zame min
abokin gaba, nasan idan har na barka kaima zaka zamemin
maƙiyi dan burinka wannan kujerar ne na sani shashasha”...

(🥱Waɗan nan mutane dai to bara nayi shiru dai🤫)

*_ZAWJATA-ALMILK_*

Duk da akwai wani ɗan ɓurɓushin tsoro a ƙasan zuciyar Iffah
ta matuƙar dakewa da addu'a ta shiga ɗakin bayan ta gama
ƙarema bangon dogon corridor ɗin da suka biyo kallo, ta
jinjina kai cikin jin matuƙar ƙuna da tausayin talakawan ƙasan
ruman baki ɗaya. Tayi imanin akwai dubbunan mutane dake
barci akan titi cikin yinwa da ƙishirwa da yawa. Amma abin
mamaki yau ga bangon ɗakin barcin Shahan-shan yasha ado
da zinari matsayin fenti, “Taya ma imani zai zauna a zuciyar
mutanen nan har su ɗauka rai wani abun mai daraja?” ta faɗa
a zahiri idanunta na cika da ƙwallar baƙin ciki da ƙara jin
tsanar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed..........✍️

(😭Hikenan Iffahr mu an shigo ɗakin mutuwa😱).

32


........Ni'imtaccen ƙamshin dake tashi a katafaren ɗakin ta
zuƙa ta fesar da cigaba da bin komai daki-daki. Ɗaki kam ya
cika a kirasa ɗaki ga masu arziƙin dake ɗaukar duniya gidan
zama. Sai dai ta gama ayyanawa a ranta babu wani ƙyale-
ƙyale da zatai sakacin da zai ruɗeta har ya dakatar mata da
ƙudirinta data fara taka tsanin nasararsa a yau insha ALLAH.
Ta saki kasaitaccen murmushi da ware hannayenta iskar
na'urar ac ta busota tare da ƙamshi, idanunta ta lumshe ta
buɗe tare da tsuke fuska. Cikin wani kakkausan sauti daya
bambanta da nata na baya ta furta.
“Yanzu ne za'a fara wasan na gaskiya. Dodon matsafa
MATAN ƘWARAI bisa kanka!!”...

(🥱 Iffahn mu irin wannan alwashi haka🤔 kinfa fara bani
tsoro😱 ).

★★...
Tun wucewar Malikat Haseenat ya bar falon shima. Tsaye
yake jikin windown ƙaramin falonsa na hutawa da babu mai
shigarsa sai shi ɗaya tak da amintacen hadiminsa mai
gyarasa. Dan a doka ma hatta matarsa bata da hurumin shiga
wannan falon a tsari da ƙa'idar masarautar. Hasken daya
ƙawata cikin masarautar ya bashi damar iya ganin abubuwan
dake kusa daga inda yake, sai dai kuma a zahiri idanun nasa
ne kawai ke kallon zuciyarsa sam ba'a nan take ba. Ya kwashe
tsahon lokaci a wajen kafin ya warware hannayensa dake
goye a bayansa ya furzar da numfashi. Ƙofar ɗakin barci
ƙwaya ɗaya dake a falon ya nufa. Shima tsaf yake tamkar
anan yake zaman din-din-din. A maimakon kwanciya anan ɗin
ma zaune yakai cikin kujerar dake ajiye a gefe domin hutawa
kawai. Tun agogon ɗakin na juya sakanni da mintuna har ya
koma awanni yana zaune idanunsa lumshe, ya kwantar da
bayansa a makarin kujerar dake ɗan juyawa a hankali. A
kallon fuska baka isa gane yanayinsa ba balle ka samu damar
masa fassara. Bugawar agogon ɗakin mai nuni da cikar ƙarfe
biyu dai-dai ta sakashi buɗe idanunsa da ƙarancin hasken
ɗakin ya hana damar iya tantance launinsu a yanzu. Agogon
ya tsurama ido tamkar mai lissafa daƙiƙun da suka cigaba da
motsawa.....

A ɓangaren Iffah wannan lokaci na dai-dai da kai goshinta
ƙasa domin yima UBANGIJI suduja a karo na babu adadi. Tun
bayan kammala lissafe-lissafenta da ƙidaye-ƙidaye ta zanzare
rigar jikinta, ƙaramin akwatinta ta buɗe babu alamar damuwa
tattare da ita ta sauya kayanta zuwa abaya. Daga haka ta nufi
bayi bakinta ƙunshe da tarin addu'oin da taketa yi tun
shigowarta ɗakin. A karan farko data buɗe fanfo da nufin yin
alwala saɓanin zubar ruwa sai taci karo da jan abu tamkar
jini. Tabbas taji firgici, amma sai tai yaƙi da rauninta wajen
cigaba da addu'a da son daidaita harbawar da zuciyarta keyi
da sauri-sauri. Tamkar almara kalar jan ya ɓace a idanunta
ainahin ruwa ya maye gurbinsa. Numfashi taja ta fesar
zuciyarta na tabbatar mata ta ƙara dakewa. Tsaf ta ɗaura
alwalarta kuwa ta miƙe, tana ƙoƙarin gyara ɗan kwalinta taji
tamkar an gitta ta bayanta. Anan ɗinma dai zuciyarta ta
tsinke, amma sai ta cigaba da ambaton sunan ALLAH ta basar.
Bata damu da nan wanin abin salla ba, dan tsaftar dardumar
da aka ƙawata ɗakin da ita ya gamsar da ita. Mayafinta ta
naɗa tai nagartacciyar tsayuwar salla domin fuskantar
UBANGIJIN talikai mai jin kukan wanda ma basu fara kukan
ba, mai bada kariya ga wanda ya yarda babu abin dogaro
sama da shi...
Taja tsahon lokaci a sujidar tana mai zubda hawaye da
ƙaskantar da kai ga mai gani a duk inda ka ɓuya. Bayan ta
sallame tai zaman karatun Alkur'ani a cikin wayarta dan
batajin zata samu Alkur'ani a wannan ɗakin da ƙyaleƙyalen
cikinsa ya tabbatar mata zamowa fadar aljanu ba komai
bane. Sai da ta gama karance baƙara har zuwa inda suka
tsaya a makaranta sannan tai addu'a mai tsawo itama. Sosai
taji wata iriyar nutsuwa na ratsa dukkan jikinta, ta sauke
ajiyar zuciya da miƙewa. Hankalinta kwance ta haye
katafaren lafiyayyen gadon da Shahan-shan ne kawai ya taɓa
hawansa a tarihi. Nanma zama tai tai addu'ar barci ya shafe
jikinta ta gyara lausasan filos ɗin da aka ƙawata adon gadon
da su ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Barci mai daɗi ya
fara fisgar idanunta a sannu-sannu sai gata tana sauke
numfashi.......

★★...... ★★..... ★★.......
Bayan wucewar saurayin da Kaka ya shimfiɗama sha tara
na arziƙi gidan yay shiru. Kamar yanda bai cema Iyyani komai
ba itama batace ba, tsahon wasu mintuna sannan ya miƙe ya
shiga ɗakinsa. Tashi Iyyani tai ta bisa, dan ta fahimci
maganarce baya buƙatar ayi sam..
A ɗakin ma baice mata komai ba har tsahon wani lokaci,
ganin haka ta katse shirun da faɗin, “A haɗa maka ruwan
wanka?”.
Batare da ya bar abinda yake ba ya jinjina mata kai. Fita tai
jiki a sanyaye, babu jimawa ta koma ta sanar masa an haɗa.
“ALLAH yay miki albarka”. Ya faɗa kamar yanda ya saba. Ta
ɗan ji sanyi a ranta, dan haka ta amsa da “Amin tare da kai”
cikin sauke ajiyar zuciya....

“Ai bakaci wani abincin kirki ba”.
Iyyani ta faɗa idonta akan kwanikan gaban Kaka da ya gama
cin abincin data kawo masa bayan fitowarsa wanka. Kai ya
jinjina mata da sakin murmushi a karan farko tun bayan
shigowarsa gidan. “Alhamdulillahi wanda naci ya wadatar
dani”. Kai kawai ta jinjina masa jikinta na ƙara sanyaya. Duk
wanda zai sam mijinta a bayanta yake, ta san murmushin sa
ba yana nufin farin ciki bane na tsantsar damuwa ce.....
“Yaya jikinta?”.
Ya katse tunaninta da abinda taketa zumuɗin san ji a bakinsa.
“Alhamdulillahi da sauƙi”.
“ALLAH ya ƙara afuwa. Bara na ganta”.

Ummu na zaune shiru ta tsurama waje ɗaya idanu suka
shiga. Har suka kai zaune gefenta babu alamar tana san da
zuwan nasu. Kaka ya kafa mata idanu na wasu sakanni sai
kuma ya kauda kai. Taɓata Iyyani tayi, ta kawo nannauyan
numfashi da ɗan zabura na ganinsu a ɗakin dan da gaske bata
san da shigowar tasu ba. Kaka ta kalla idanunta na cikowa da
ƙwalla, sai kuma ta duƙar da kai ta fara gaishesa. A hankali ya
nisa kafin ya amsa a taƙaice kamar yanda tai gaisuwar.
“Jumaimah!”.
Ya kira ainahin sunanta.
“Na'am Baba”.
Ta amsa akan laɓɓanta.
“Damuwa ko ƙuntata kai bata sauya ƙaddarar bawa.
Juriya da tsantsar jarumta baya hana ƙaddarar zuwa. Haƙilo
ko nuna ƙarfin iko baya ture ta a lokacin da aka so. Rauni ko
rashin tawwakali bazai dawo maka da abinda dama can ba
naka bane ba. Haƙuri shike samar da komai koda kuwa a
zahiri yafi ƙarfin ƙarfinka”.
“Hakane Baba”.
Ta faɗa cikin rawar murya.
Murmushi ya saki da matsawa kusa da ita sosai. Ɗa a gaban
iyayensa baya girma koda ace yayi furfura a saman kai. Kaka
ya riƙo hanun Ummu cikin nasa, ɗayan kuma ya shafa kanta.
“ALLAH yayi miki albarka. Yasa ƙaddarar su ta zama kaffara a
garemu baki ɗaya.”

“Baba mun rasa su suma ko?”.
Ummu dake dubansa idanu cike da ƙwalla ta faɗa.
Murmushin ya sake sakar mata. Sai kuma ya girgiza kansa da
kwanto da kanta bisa kafaɗarsa. “Bamu rasa su ba, ba kuma
mu fidda rai da samunsu ba”.
A hankali hawayen da suka kasa fita a idonta tsahon
kwanaki suka fara sauka a kafaɗarsa.......
★★.... ★★.... ★★.....

Mummunan mafarkin da ALLAH ya bata ikon cin galaba a
cikinsa ta farka a zabure, cikin amincin UBANGIJI harshenta
ya ambato addu'ar tashi daga barci kamar yanda musulinci ya
ɗoramu akai. Ajiyar zuciya ta sauke da saka gefen bargon
data lulluɓa ta yarce gumin da yay ma goshinta jalab, sai
kuma ta sake lumshe idanu jin sautin kiran salla da take
ƙyautata zaton a masallacin cikin masarautar ne. Hasken
ɗakin ta kai hannu ta ƙara, ta bi ko'ina na cikinsa da kallo
tamkar zataga munanan halittun data gani a cikinsa a
mafarki. Rashin ganin komai a zahiri ya bata ƙarin gwiwar
sakkowa a gadon ta nufi toilet. Bata damu da rashin ganin
Tajwar Eshaan a ɗakin ba duk da taji Malikat Haseenat ta
ambata nan ɗin matsayin ɗakin barcinsa na daren jiya.
Ƙarancin shekarunta da wautarta yasa bata ɗauki tsallakewar
komai ba. Abinda kawai zuciyarta ke mata kaikawo a rai shine
ta tsallake daren na jiya dai koma yaya ne, ta tsallake tarihin
mutuwa a daren kwana turakar dodon matsafa. Dalilin
tsallakewar, ko barinta da yay da ranta ne bata sani ba, ba
kuma tasan tayaya ya kamata ta sani ba. Abinda kawai take
da damar yi shine buɗe kunne da idanuwa taga mizai biyo
baya ga kowa da kowa. A yanzu ɗin ma tayi zaton ganin jinin
kamar jiya dai, sai dai babu alamar hakan har ta kammala
uzirinta tayo alwala ta fito. Tana idar da salla wani irin
nannauyan barci ya dinga fisgar idanunta. Dakewa tai cikin
dauriya tai zaman yin azkar, da ƙyar ta iya kammalawa barci
yay mata baban fisga a wajen dole takai kwance tana
ambaton sunan ALLAH. A hankali ta fara sauke numfashi
alamar barcin nata mai nauyi ne....
★★.... ★★.....

A cikin masarauta tako ina an gama baza kunnuwan jin
fito da gawar Zawjata-almilk. Hatta da Malikat Haseena bata
tare da nutsuwarta gaba ɗaya. Tun ana ƙirga sakanni a bayan
sallar asubahi har aka koma mintuna, mintuna suka koma
awanni babu wani labari. A take aka koma ƴar ƙus-ƙus tun
daga kan hadimai har manyan masu faɗa ajin masarautar.
Yayinda suma Hadiman sashen Shahan-shan suke zaune
jigum-jigum na jiran tsumayen abinda kowa keda tabbacin zai
kasance. bakunansu cike yake taf da abubuwan faɗa akan
abinda suka wayi gari da shi mai matuƙar rikitarwa da zai
maimaita faruwa bayan ya faru ga duk wata Zawjata-almilk
data kwana ta tashi a wannan sashen. Duk ɗunbin yawan
abin cewar iyakarsa zukatansu dan ko'a tsakaninsu bai
faɗuwa balle gulmantawa a waje saboda tako ina camara ce
zagaye da su.....

*_★MALIKAT BUSHIRAT★_*

Ba'a safiyar yau ba, ita tun ma a daren jiya tai hanun riga
da nutsuwa. Gaba ɗaya a daren ko sau ɗaya bata iya ta rintsa
ba. A maimakon barci ma idanunta akan sashen Shahan-shan
da kowa ke iya gani daga nasa sashen a cikin masarautar suka
kwashe mafi yawan awannin daren na jiya. Tayi yunƙurin
kiransa amma wayar a kashe, hakanne ya sake ɗaga mata
hankali da jin zafin wannan hukunci na Malikat Haseenat a
karo na farko. A ganinta ganganci ne miƙa nagartacciyar
yariya irin Iffah hannun gudan jinin nata bayan Mamma tasan
minene makomar yin hakan ga rayuwar yarinyar. Duk
jarumtarta a duk sanda ta tuna zuwa safiya gawar yarinyar ce
zata fito takanji ƙwalla sun cika idonta. Amma takan danne ta
hanasu fitowa har garin ALLAH ya kammala wayewa...
Tun idar da sallar asubahi bata iya ta motsa ba, ƙirjinta ne
ke matuƙar bugawa da jiran tsammanin mummunan labari.....


*_★DANEEN AMMARAH★_*

A ɓangaren Daneen Ammarah itama a kwatankwacin irin
halin da Malikat Bushirat ta kwana ta tashi take ciki. Dan ita
kwana tayi ma tana hawaye. Har ƙarƙashin zuciya takejin
matsanancin ƙaunar Iffah. Tana jin yarinyar a matsayin cikon
wani gurbi data rasa irin na kowace uwa mai shekarunta. Sai
gashi Mamma da ta fara bata tsoro a daren jiya ta rusashi da
maye gurbinsa da fargaba mai matuƙar tsanani da razani.
Wani mutum saɓanin jininta bai taɓa mamaye zuciyarta da
ƙauna mai ƙarfin haka ba kamar yanda yarinyar tayi mata.
Sosai take jinta a rai da jinin jikinta. Itama dai tun daga sallar
asuba bata sake iya kataɓus ba tai zaman jiran tsammani irin
na duk wanda ya kwana ya tashi a cikin masarautar.......

★★... ★★.... ★★....

Harya gota ɗakin cikin shiga ta blue ɗin jallabiya mai
tsananin ƙyau da ƙyalli mai ɗaukar ido da nuna taushinta a
zahiri dake nuna daga masallaci yake ya tsaya cak. Kamar
bazai motsa ba sai kuma ya juya kansa a sannu yana kallon
ɗakin. Kallon kusan minti ɗaya da wasu sakanni ya motsa
gaɓɓansa cikin takunsa na izza da kame kai ya tura kai ciki. Da
farko rashin lura da ita ya sakashi yin tsamm, sai dai fuskarsa
ta nuna dakewa kamar koyaushe. Ya ɗaga ƙafa da niyyar
juyawa ya fita idanunsa suka sauka a kanta. Yay tsai yana
kallonta na tsahon mintuna kusan huɗu tamkar mai rarrabe
ita ɗin ce ko wata? Dan a kallo ɗaya zaka fahimci salla ta idar
a wajen barci yay awon gaba da ita. Ya ɗan furzar da
numfashi da kauda kansa gefe ya sake bin ɗakin da kallo kai
kace baƙonsa ne har ya sake direwa akan fuskar Iffah dake ta
barcinta numfashinta na fita a hankali.........✍️

33


.........Ƙarfe takwas da rabi

Please Login or Register in order to submit comment