tsareta da idanu, she’s dead beautiful, and tanada wani irin bewitching aura dake sace zuciyan mutum, is not his fault tunda gashi har itama Mami is loving the girl unconditionally daga haduwa da ita a saloon.
Tana zaune wajen Mira tagani tana tahowa tana sanye da half gown mai bala’in kyau natane kuma ko yaya akayi yadawo nata bata sani ba maybe rannan dasuka so gidansu ta dauka a wardrobe dinta, karasowa tayi wajen Ziora na kallonta Mira ta zauna gefenta cikeda masifa tace “how would you come to this school baki nemeni ba kika kama kika fita? By the way ma ina kikaje cus munje dance academy dinnan baki nan eh”? Kallonta Ziora tayi yanda take mata magana da isa tadai daure tace “I went somewhere” “somewhere where?” Mira tadaga murya dayasa Ziora tasaki baki tana kallonta, saita kara daurewa tace “my parents don’t want me to be friends with you guys anymore” wani abune Mira taji ya daki kirjinta kafin ta gyara zama sosai tana kallon Ziora tace “mene kikace Ziora”? Gabanta faduwa yahauyi but she has to say the truth hakan yasa tace “they said if they see us together again they will lock you girls up after that drug thing, so I think kawai muhakura da friendship din ni school dinma banso zan daina zuwa ne” mikewa Mira tayi ta tsaya agabanta tana kama waist nata kaman wata uwar Ziora tace “repeat what you just said Ziora” sosai kirjin Ziora ke bugawa to wai tsoron Mira take? How can she be afraid of her? Ta tambayi kanta sai bakinta yahau rawa sosai tace “I….I….don’t wanna be your friend anymore!” Hannu Mira tadaga cikeda zafinrai zata kaima Ziora mari atsorace Ziora takai hannayenta saman kanta dan kare fuskanta tace “Daddy!” Mira takai hannunta da zafin nama zata daura mata marin sukaji murya saman kansu strictly yace “ke!”.
💫KAUNA DA SO💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 1️⃣7️⃣
Azabure Mira tajuyo jin muryan namiji akansu itama Ziora tadago kanta ahankali taga Imam ne yana kallonta, ahankali kaman yanama yar yarinya magana yace “are you okay?” Gyadamai kai tayi like a baby idanunta na ciko da kwalla Mira najin wani abu ya tsayamata arai cus this is her crush that footballer Wanda musamman tajasu zuwa golf club sabida shi, why is he here? Why is he talking to Ziora like that? Sunsan juna ne? Yasanta ne? Murmushi ta kakalo tace “Imam the almighty footballer and golf player in our school, Hi” wani matsiyaci kallo yamata na rashin mutunci, yace “are you trying to bully Amrah?” Zafi kirjin Mira yayi jin yanda yakira sunan Ziora a ina yasanta, itama Ziora ahankali tadago idanunta takallesa jin yanda yakira sunanta Amrah, anatse yace “if anything even a scratch nagani ajikinta you will leave this school with immediate effect” bugawa kirjinta yashiga yi tadaura still trying to act cute tabude baki zatai magana kaman wani dan iska yace “dalla ware! Excuse me” kunyan duniya Mira taji sai kawai tawuce ta tafi, yakalli Ziora da idanunta sun cicciko da hawaye tana kallonshi saiya zaro handkerchief daga pocket dinsa yamika mata yace “kin iya rashin kunya but a girl like you now is trying to beat you up you can’t defend yourself, big for nothing Amrah” fashewa da kuka sosai Amrah tayi da wlh saida yama danji tsoro da kunya, wai ita wannan bata da kunyan kuka ne da girmanta, iyye yanzun nan wata na neman dukanta dan yamata fada saitahau mai kuka, wlh baisan sanda ya duka agabanta cikin muryan lallashi sosai yace “why are you crying now?” Cikin kuka harda shesheka tace “you call me big for nothing” cikeda tsokana Imam yace “to tell me wat are you”? Sake rushewa tayi da kuka tana buga kafafunta akasa dasauri yace “okay okay you’re not big for nothing now stop crying ana kallonmu” tsagaita kukan tayi tace “and I will tell Mami you’ve made me cry again, I will not give you my cake again” dan juyamata idanu yayi yace “dazun dinma ai baki bani ba” kasa magana tayi kawai heart nata na racing sabida yanda yamata da idanu ta tsaresa da manyan idanunta shi kansa saida ya lura saiya harareta yace “karba ki goge idanuwan nan naki kaman na Labubu toy” baki tabude zatai kuka dasauri yasa hannu akan lips dinsa yace “shii wai don’t you know you’rea big girl? Hausa big girls like you basa kuka haka saisa ake kiransu da yammata, kice yammata naji” ahankali tana kallonsa sosai tace “emmata” murmushi yayi kadan daya lotsar da dimples nasa dayama fuskansa kyau ta tsaresa da idanu, saiya tashi yamata waving hannu yace “bye Emmata” ashagwabe ganin yana tsokananta talking like her tamikamai handkerchief nasa da hannunta tace “Yaya Imamu your handky!” Chak ya tsaya batare daya juyoba, the way she pronounced his name, d sigan yanda takirasa da tone na shagwaba da kuka baitabajin wata takirasa hakaba, kin juyowa yayi yace “nabaki, your first gift from a boyfriend!” Dan faduwa gabanta yayi saikuma takasa magana ta dinga kallonsa harya shiga mota yatafi sai kallon handky take, kusan 5min da tafiyansa saiga Daddy.
Tana shiga motan Daddy tai hugging nasa murmushi yamata sai kawai yakai hannu aljihun sa yazaro wayanta yamika mata yace “for staying in school today and attending lectures you’ve earned your phone” wani dadi ne ya lullubeta tai hugging nasa tace “thank you Daddy you’re the best” ahankali yace “why are your eyes red?” Murya chan kasa tace “kuka nayi” tai hugging nasa tana sa kanta a kafadansa, dasauri Daddy yace “why wat happened?” Fashemai tayi da kuka tace “I broke up with my friends since all of you hated them, now I’m heart broken” abin yaso yaba Daddy dariya yace “you did a great thing, stop crying I’m so friend, your Mother is your friend too plus brothers naki, nobody is like family” shiru tayi ahaka har sukakai gida, suna shiga taga Mommy a falo tace “good morning Mommy na” Mommy tace “kaniyanki da morning” dariya tayi ta manna mata kiss a kumatu tamike tawuce sama Daddy yabita da kallo yana murmushi harta wartsake yace “I told you I can set my daughter bagashi nan yanzu ta natsu ba” tabe baki kawai Mom tayi bata cemai komiba.
Tana shiga dakinta jakanta tafara budewa tazaro littafin data rubuta number Mami tai dailing number, Mami na bayi tana wanka Aliyu na zaune bakin gadon yaji wayan Mami na ringing babu wata mai kiran Mami hakan yasa yakalli screen din amman ba suna is just number, katsewa yayi aka kara kira still number ne ta katse, kira na uku yasa yadaga wayan yana kallon number batare dayayi picking ba daidai Mami na fitowa daga wanka yabata wayan karba tayi tadanna tasa a speaker kafin tai sallama Ziora cikeda farin ciki tace “Mami it’s me, your Amrah” kafin Mami tai magana tace “Mami Daddy gave me my phone just now I just entered my room nabude jakana and quickly call you Mamiiiii” kyalkyacewa da dariya Mami tayi Aliyu yakalleta adan sace da mamaki, Mami tace “oh ni Amrah, yanzu sabida an baki waya kike murna haka?” Dasauri tace “yes Mami and I told Mira that my parents don’t want us to be friends again it’s over she wanted to beat me but Yaya Imamu stopped her and warned her” Mami tace “Imamu na” dasauri tace “yes he took me to school” Mami tace “okay, karki yarda wata tadakeki okay” muryanta yadan ragu tace “I don’t know how to fight Mami, my brothers don’t fight with me, I’m the only girl in our house, My Mommy have 4boys, my step mom has 5boys” murmushi Mami tayi mai sauti tace “zan koya miki yanda ake fada kikazo gobe” dariya mai karfi Ziora tayi dake fitowa awaya sosai tace “Mami you’re very fine ko”? Zama Mami tayi abakin gadon tace “yes I’m my dear” Dasauri tace “tom where were you inata kira baki dagaba I was worried danacema Daddyna yakawoni naduba ki” dariya Mami tasakeyi Aliyu yakara kallonta dan sosai take dariyan, Ziora tace “you’re now my only friend Mami” this time around saida Aliyu yajuyo complete yawani kalli Mami data kwashe da dariya cus from yanda take maganan da zuciya daya takeyi ga, mamakin Aliyu daya hade fuska sai Mami tace “kwarai I’m your only friend now, nima you’re my only friend Amrah na” kyalkyacewa da dariya Ziora tayi, Aliyu kawai yamike yawuce yayi kofa Mami tadan kalleshi sannan tace “jeki sallan magrib” Dasauri tace “okay but Mami are you on watsapp zan kiraki video call anjima”? Mami tace “ni bansan ina watsapp dinma yayi a wayana ba amman zansa Aliyu yadubamin now go and pray” dasauri Ziora tace “I love you Mami na my best friend byeeee” ta katse wayan kafin ma Mami ta amsa Mami tazare wayan daga kunnenta tana murmushi sosai ta kwalama Aliyu kira. “Aliyu, Son, Haidar” yana dinning yamike yazo dakin tareda bude kofa Mami tamikamai wayanta tace “gyaramin watsapp dina zanyi video call da Amrah, yimin saving number ta kuma” dan kallon Mami yayi sai kawai ya amsa baice komiba, updating watsapp dinta yayi ya gyaramata yabude, yana budewa yaga Amrah harta mata chat “Hi Besty Mami” tsuki yayi dayasa Mami ta kallesa dasauri tace “lpy”? Murya chan kasa ciki ciki akufule yace “you don’t even know this girl Mami…” anatse Mami ta taresa dan taga take takensa tace “andd?” Bai kara magana ba yamata saving number Amrah yabata wayan ta karba yamike zai fice ahankali tace “sometimes you don’t have to know people Aliyu, and being different doesn’t mean you are bad, who knows she might change because of me, wat matters is heart, she’s just a precious innocent girl that doesn’t see me as a sick person saidai normal healthy person, while dukanku na treating dina as a woman that is dying Amrah is treating me like a normal human, babu wannan look na pity nan dakuke min a kan idanunta saidai look na tsantsan excitement da so dakuma kauna, she’s right Amrah is my friend Aliyu, ta shiga raina sosai matuka idan itama kanaso ka korata ne nacigaba da zaman gidan nan banda mai tayani hira inba Imam da Nabeel sunzo ba ai saikayi? Ko kai dabaka iya hiran bane zakamin? Yaro mai shegen bakin hali da miskilanci kaman ubanka” Baice komiba yajuya zai fita harya bude kofa tace “when was the last time kaje gidan mahaifinka ka gaidasa?” Tsayawa yayi chak baice komiba baikuma juyoba, ijiyan zuciya ta sauke tace “one of this days koda Friday ne ka shirya kaje ka gaida mahaifinka Aliyu” murya chan kasa yace “banida time ne” ahankali tace “I know amman dai kaje tunda ai lafiya ta kalau kaji ko” gyadamata kai yayi yafice itakuma tasa kaya tahau kan dadduma dan yin salla.
**
Gidansu nada bala’in kyau, kana ganin gidan kasan sunada rufin asiri, gyara fuskanta tayi tashiga, flat dayane agidan, kofa tabude da sallama ta shiga wata matace a falon tana duba wasu laces dawata dillaliya takawo mata ganin diyarta yasa tace “ah Beeba kene kin dawo ya banji an bude gate ba” murmushi tama mahaifiyarta tace “nabar motana a asibitin mu ne Mama, bari nadan watsa ruwa” Mama data bita da kallo ganin idanunta sunyi ja tace “wai ke kullum sai patient sun saki kuka a asibiti”? Murmushi tayi kawai tawuce dakinta batai magana ba chan aka sake bude falon aka shigo wata budurwa ce kaman Beeba din but tafita girma akalla zatai 29yrs ko 30yrs ita cousin ne su tashigo, diyar yayan Baban su Beeba Mama tace “Farida an dawo” zama tayi tace “Mama na kosa nagama workshop din nan nakoma kano abina nahuta haba” dariya Mama tayi tace “don’t be lazy my friend tashi kije daki yar uwanki na ciki itama tadawo daga asibiti fuskan nan ba annuri” mikewa tayi tawuce corridor tabude wani daki mai kyau ga baban gado ciki, Beeba na zaune bakin gado ko abaya bata cireba share fuska take da bayan hannu tana kuka, dasauri Farida tamaida kofan tarufe tazo wajen gadon tana kallon Beeba tace “Dr are you okay? What happened why are you crying?” Jan majina Beeba tayi da hanci tana haki tsabagen kuka har tip na nose nata yayi ja cikin muryan da baya fita sosai tace “I fought with Dr Aliyu” wani kallo Farida tamata daga sama zuwa kasa tace “yanzu Beeba you’re 28yrs old, a Dr for that matter, an intelligent Dr, a Gyneocologist, Master holder from havard as scholarship, shine zaki zauna kinama wani d’a namiji kuka? Did you even know who you are? Kinsan self worth da value naki? Who is Dr Aliyu? Is he the last man on earth”? Hannu Beeba takai tana share fuskanta hawayen sunki tsayawa sai kawai tasanya hannayenta biyu akan fuskanta ta rushe da kuka sosai tace “ya kikeso nayi? Agabanki Baba yakirani yabani one month nafito da miji, babu yanda banyi da Dr Aliyu kan yafito ba yazo gidanmu yaga Baba, amman yaki wai bai shirya aure ba sabida sick Mom dinsa, Allah ma yakashe shegiyan matan muhuta tazaman mai jaraba arayuwa” sosai Farida take kallonta saikuma tace “kincemin he slept with you da kuna UK?” Dago jajayen rinannun idanunta tayi ta kalli Farida sai batai magana ba, Farida tace “tell me the truth I want to help you ne” ahankali ta girgizamata kai tace “wallahi baimin komiba but I just made it like that” tai shiru kaman mai tunani tace “the only weak point na Haidar dana sani all this years is his Mom, back then muna UK an kirasa kan rashin lafiyan Mamansa and Babansa yasaketa sannan ya koreta out of his house, rannan he was angry kaman zaiyi hauka, kinsan shi PhD yake then ni Master nakan rokeshi ya koyar dani wlh ilimi akansa kaman artificial intelligence I was crushing on him like mad, shine I bought a drink nasami wani dan ajinmu dan kwaya shi daga Mexico yake nace yasamin something that will make him high yadena damuwa and just sleep, yaron yace he got that idan inaso zai iya samin something da zaisa yaji bukatan mace ya nemeni wai ya lura inatabin guy din yanamin wulakanci”dasauri Farida tace “kin amsa”? Ahankali ta gyadamata kai tace “duka biyu nasa yasamin a dark coffee din mai daci na kaimai agidansa cus baici abinci ba, saida na dameshi da magiya yasha kawai ya kwanta yayi shiru I was there chan yatashi yace natafi zaiyi bacci abuge yamin magana, naga yatafi bedroom dasauri yana layi kansa na juyawa” tai dan murmushi tana jan majina tace “that’s how nazo bedroom din I just turn off the light nacire kaya nahau gadon and just hugged him he was pushing me at first baisan meyake ba then from no where he began sucking my boobs….” Beeba tai shiru kaman tana tuna abubuwan sai kawai tace “Ya Ilahi! Kinga Dr Aliyu shiru shiru haka I swear to God he’s a beast he almost took my nipple out yakusan tsinkawa, I was playing with his body dudda I wanted something to happen amman he passed out kaman kwayan yamai yawa bai sababa shine kawai natashi took off his clothes” takara yin shiru tace “I took off mine too dama na nemi razor na yanka tsakiyan tafin kafana na zuba jinin a gadon da cinyoyina and treated my leg da spirit nima na kwanta nayi bacci, da gari yawaye yadawo daidai he couldn’t look at tsiraici na kinsan Ustaz ne, yarude nasaran danaci kenan bai gane everything was a lie ba sabida he couldn’t look at my body, keeee nikuma nadinga kuka ina gayamai he raped me daga zuwa yamin tutorials, he took advantage of my innocence, wlh saiya aureni toh tundaga nan shine muke har yau, yanada alkawari ga gaskiya he will marry me kawai annobar uwarsa ce matsalan mu ayanzu” Farida tace “danine da tuni na karasata wlh” zaro idanu Beeba tayi tace “ke I’m a Dr I save lives not end them” Farida tace “I’m a business analyst, sannan nakalli different medical shows irinsu greys anatomy, the resident , Chicago med da sauransu, I’ve watched Doctors sun karasa kashe patient din da sun san baida ragowan rayuwa, wahala ce kawai zaita sha, dayasha wahalan nan gwara sun karasasa hakan ma is saving life, Matar nan is dying toh why keep her? Kullum kullum she’s in pain, tazama pain for kanta and danta, da wannan rayuwa ba gwara mutuwa ba, ki tsaya nan ga Baba yatasoki gama kina jiran rannan da wannan uwar likitan naki zata mutu kuyi aure, my dear you are not killing her you are saving her, think about it, that woman is pain in the ass, nidai bari naje nai wanka” tayi maganan tana mikewa ta shiga cire kaya kafin tawuce tafada bayi duk Beeba na kallonta sai tunanin maganan datayi mata take, saida Farida tafito daga bayi tashiga sa kaya tajuyo ta kalleta tace “bazaki tashi kije kiyi wanka ba” ijiyan zuciya tasauke tamike tafada bayi tayo wanka tafito wayanta tadauka takirasa yafi sai 10 bai dagaba kirjinta har zafi zafi yake mata kuma tasan bazai dauka ba, watsapp ta shiga tamai typing I’m sorry mijina I trully am kaji i know i said lot of trash but wlh i love you sosai ne” maida wayan tayi ta ijiye saita tashi zaune ta dauki laptop dinta.
EPISODE 1️⃣8️⃣
Browsing Beeba tashiga yi akan ya hallasta a musulunci ka idasa kashe mutumin dake dab da mutuwa, cus tasan a al’ada akanga idan dabba na kakarin mutuwa ko irin mota ya buge dabba tana walagigin mutuwa akance a yankata arage mata wahalan da azaba, is it dsame thing d human too? Nan da nan taga fatawa dayawa, Allah daya hallici rai shi kadai yakeda ikon karban abarsa, dudda ta kakkaranta amman shedan yagama shiga kanta, the only burin rayuwanta is kawai ta auri Aliyu, sau nawa suna sauke Patient dake asibiti dasuke life support from life support, dudda clearly dai Mami is not on life support, tana breathing on her own, feeding on her own da sauransu amman dai she can’t escape death, already tana last stage na cervical cancer, cancer yagama cinyeta, last stage yake yayi spreading yashiga har liver nata, saisa bakowani kalan abinci takeci ba, sannan tana yawan fama da habo, kumburin kafa, jaundice, bloating, yawan bleeding, zazzabi da sauransu, to ina dalilin wannan wahalan da azaba ba gwara ta mutu ba? Shigowa dakin Farida tayi tace “me kikeyi wai har yanzu”? Kallonta Farida tayi tace “zoki karanta da kanki kiji abinda nagani” zuwa wajen Farida tayi ta zauna ta karbi laptop din tana karanta komi tai tsaki tace “sa hijabi na kaiki gun Malam ki tambaya yana bayan layin nan sabida kokonton nan yafita akanki” batai musuba ta mike, hijab tasaka suka fito, Mama bata falo kawai ficewa sukayi sukaje bayan layinsu, a anguwan nan aka haifeta but batamasan da wannan malamin ba sai yau, wani malamin almajirai ne aka musu iso suka shiga dakinsa, 1k Farida ta mikamai tace “Malam tambaya mukazo yi muna cikin duhu” Malam yace “na’am ina jinki” Farida yace “akwai wata wacce takeda ciwon daji ana kiransa da cancer a turenci tana end stage, takai gaban da mutuwa dole ne Malam, likitoci ma sun deba mata wa’adin bazata wuce wata shidda a duniya ba kwata kwata Malam” Malam yace “kwarai ina jinki” Farida tace “to tazamewa danta bala’i da ukuba, da annoba, d’a yanaso yayi aure yacika sunnar ma’aiki yakasa sabida ita, to tambayan damuka zo yi shine ya halasta tunda a asibiti akwai magani da yawanci akan yiwa irin mutunen nan da sukeda wa’adin mutuwa akansu, kawai susha suyi bacci su tafi ba wahala, babu wani fizge fizgen zare rai, ya halasta abata maganin sabida itama ta mutu peacefully ta huta da wahala hakanan, hakama danta yahuta da wahala yayi aure abinsa? Kaga ai ciwon ta yahana dan bautan Allah da yima sunnar ma’aiki biyayya ko Malam? Ya halasta Malam amata alluran yanke wahala kawai ta margaya?” Budan bakın Malam yace “kwarai ya hallata!” Wani ijiyan zuciya Beeba tasauke, Malam yace “Annabi yace shifa addinin musulunci sauki gareta duk wanda ya zafafa ma kansa shiyaso, banda haka Annabi still yace ba’a ma iyaye biyayya awajen sabama mahallici, tunda tazama annoba tahana yaro yayi aure daman kuma mutuwan ta tabbata akanta kaman yanda kwararrun likitoci suka fadi, zaku iya yanke mata wahalan ta garzaya kowa yahuta” murmushi Farida tayi tamike tamikamai ragowan 4k na hannunta tace “Malam gashi arabana dalibai sadaka wannan, mungode” Beeba itama tamike tace “mun gode Malam” suka fito, Farida tace “you know wat to do yanzu, kene likita help that woman so that she will peacefully exit duniyan nan kowa yahuta, ayi fixing aurenku kuyi abunku, to wai tsaya yanzu idan bayan aure yaje baki bude ba fa?” Murmushi tayi tace “tunanin yasa nabar Kamal dinnan dake sona lokacin yayi sau daya shikenan narabu dashi, Aliyu kadai nakeso a duniya ni, ke wai kinsan waye Aliyu? Ke God took his time in creating bawan Allahn nan, Allah yabasa kayan aiki full set” Farida tace “Shegiya nononki ya shawu” akunyace Beeba tace “wlh ko jariri albarka saiya dakata ya karyama Aliyu hula ashan nono, is it even only that kinga kasan sa” Farida tai shewa tace “ah dole ki nace mayya ta, likita bokanya turai” suka kashe suka wuce gida.
Gabaki daya Beeba takasa baccin kirki, tunane tunane take kawai, da sassafe around 8 tabar gidan, Farida ta sauketa a hospital cus tabar motanta anan, today she’s off, but hospital din tashiga tawuce pharmacy nasu tanabin ko’ina da kallo abinda take nema bata samu ba hakan yasa tafito, operation room tashiga luckily babu kowa ciki wajen wani safe taje she’s just so lucky tasan code na safe din she once overheard MD na gayama anesthesiologist dinsu, tabude taciro wani karamin kwalba dawani farin ruwa ke ciki kaman water, tana kallon kofan shigowa operation room din, tasa syringe ta zuko just 1ml, bazama ka gane an debi abin ba, kan roban kwalban ta zuka, ta maida kwalban safe din mai sanyi dasauri ta jefa syringe din cikin jakanta tafito bakowa awajen tawuce tafita daga asibiti tawuce ta shiga motanta taja tanason tai sauri takai GRA around 10 daidai sanda zai fito, shopping tama Mami sosai nagani nafada sannan tafito tasa komi a mota taja motan, wuraren 10 takai kofar gidan bata shigaba tai parking awaje.
Aliyu na zaune a dinning ya shirya tsaf yau yadi yasaka ash color tamai bala’in kyau saidai baisa hula ba, yana sipping coffee, Imam shima zaune awajen yanashan nasa coffee wayansa yayi haske, daga wayan yayi yakalla dayake shi baida password awaya message ne Beeba ta turomai.
“I’m outside your compound nazo gaida Mami na” shiru yayi yana kallon sakon sai ga kiranta bai daga wayan ba yamike tsaye batare daya kalli Imam ba yace “Habiba is outside” dasauri Imam yace “wooo yayanmu kace Inlaw Mami na waje, finally yau Mami zataga budurwan yay….” Juyowa yayi yamai wani kallo hakan yasa maganan ya makale yana murmushi, Aliyu yawuce yabude dakin Mami yashiga yasameta zauna sai matse idanu take tana faman karanta chats na Ziora, ahankali yace “Mami anzo gaisheki” dasauri Mami tadago kai tace “Amrah danake chatting da itane wai hartazo?” Ahankali yace “it’s Habiba from hospital namu” yana maganan yajuya yafita, yabude kofa yafita gaban flat nasu, da hannu yama gateman alamu yabude gate, bude gate, gateman yayi tashigo da motan yana tsaye a compound yamata wani irin kyau sai kallonsa take fuskan nan ahade ba yabo ba fallasa. Parking tayi tafito tana sanye da lace mai bala’in kyau mai red da milk tayafa wani milk gyale akai taci gayu sosai, tarike wani Zara bag, bayan mota tabude tadauko babban ledan super market tarike ta rataya handbag dinta tana kallon Dr daya tsaya daga wajajen entrace na flat nasu yana mata wani kallo ba yabo ba fallasa harta karaso wajen, cikin sassanyan murya Beeba tace “baraka min murmushi ba? I said sorry noww haba Mijina” juyawa yayi baice komiba yabude kofa yashiga yana bude mata kofa ya koma gefe danta shigo, Mami na zaune kan sofa tasaka lace mai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 26