Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
friend, Daddy is not my friend” dan murmushi kadan Mommy tayi tace “go and shower kinata zufa” tashi tayi tawuce Mommy tabita da kallo kalaban kanta sun tsufa sosai. Bayi ta shiga wanka tayi tafito ta shirya short black da crop top pink tafito kowa na dinning harda Daddy da yayi mugun kewanta but yana ganinta yahade fuska kaman baya dariya tana zuwa wajen ahankali tace “Daddy good morning” morning ya amsa ba wasa hakan yasa ta kara kallonsa idanunta na cicciko da hawaye, Mommy tace “zauna to” zama tayi Mom tabata tea ta karba tasamata chips ahankali tafara ci bini bini Daddy na kallonta, Mommy ta kalli kanta tace “zamuje saloon anjima this your hair is looking rough” gyadama Mommy kai tayi Daddy ya share baki yamike yana duba agogon hannunsa yace “lemme head to the office bye wife” ciccikowa idanun Ziora sukayi Daddy zai wuceta tarike hannunsa da sauri cus she’s feeling kaman ba itaba sabida Daddy, dakatawa Daddy yayi yajuyo yadan kalleta, ahankali Ziora tace “I’m sorry Daddy please Daddy” hararanta Daddy yayi ya karbe hannunsa yajuya yatafi abinsa Ziora tawuce sama da gudu tana kuka. Around 12 na rana Mommy tabude kofanta tashigo bata dade da tashi daga baccin ba, hakan yasa Mommy tace “tashi muje I will drop you at the saloon nabiya church and see my pastor kafin kugama I’m sure mun gama meeting” tashi tayi duk bamataso ta fitan rashin waya yasa batajin dadin komi, bayi ta shiga kayan jikinta tacire tafito tadauko wani gray Mom jean tasaka tadauko wani milk color shirt mai stripes tasaka ya sauka zuwa cinyanta, hoops earring na gold tasa a kunne sannan tadauki black jersey veil kawai tadaura saman kanta tadauki black flat shoe tasa tadan kalli mirror tana fesa turare tayi bala’in kyau sosai she looks so simple and charming tafito, Mommy tace “let’s go” batada waya and she’s not the one paying for anything hakan yasa ko jaka bata dauka ba tafito Momy dataci gayu ga wig dinta akai tace “let’s go Baby” dasauri tazo tai gaba Mommy sai kallonta take kaman jiya ne fa data haifi yarinyar nan amman jibi yanda taketa girma, wajen wata SUV sukayi security yabude musu baya Ziora tafara shiga Mommy tashiga itama aka rufe sannan aka jasu, tunda Mommy tashiga motan waya takeyi Mom tana daya daga cikin manya manyan special members na church nasu ita kadai ake jira a meeting dinma, kusan tafiyan 20mins yakaisu wani babban saloon AR saloon gate aka bude musu suka shiga ga motoci dayawa a parke dan manyan mutane ke zuwa saloon din, parking akayi Momy ta katse wayan aka bude musu kofa ita tafara saukowa tamikoma Ziora hannu kaman wata yar yarinya kama hannun Mamanta tayi tasauko tana turoma Mommy baki tace “Mommy ni basai kin bini ba” ko kulata Mommy batayiba dan batada lokacinta sauri take hakan yasa kawai taja hannunta suka shiga ciki ga hadaddun mata ana musu abinda sukazo yi mai saloon din na ganin Mommy tace “Madam Chigozie long time welcome Ma” murmushi Mommy tamata tace “see my daughter please amata loosing kan nan a wanke, she has been wanting to dye her hair karki mata” turo baki Ziora tayi kaman zatai kuka tace “Mommmmy I want to dye my hair zuwa oxblood that’s maroon please” hararanta Mom tayi tace “bazaki ba, wuce a atsefe, a wanke, a kitsa” duk da turenci suke maganan, Mommy tace “I have a short meeting, I will be back yanzun nan nadauketa” Matan tace “yes Ma saikin dawo” Mommy tadan kalli Ziora cike da so yanda ta turo baki, tadan taba pink lips din nata tace “stubborn girl oya follow her” binta tayi matan tace “let’s go” suka tafi while Mommy tajuya tafice, Ziora harta zauna kan kujera tana yaye gyale za’a mata tsifa taga ana ma wata mata jan lalle in the next room da transparent glass ne yarabasu, an gama kunshin kwashewa ma ake, yayi ja sosai dawani irin sauri tasauka matan dake kokarin daukan abin tsifa taga Ziora tawuce wajen kawai tashiga dakin ta duka dab dasu tana kallon lallen a kafan yar dattijuwan da zatakai kusan 57-58yrs fara kal da ita kana ganinta kaga bafulatana, tana sanye da hijabi mai bala’in kyau, kallon Ziora data rakube a gefensu tayi tana kallon lallen sosai fa kaman wawiya tace “kinaso amiki lalle kema”? Dasauri Ziora tadago kanta ta kalli matan data mata magana fuskanta cike da fara’a da kamala da natsuwa sai kawai ta gyadamata kai alamun eh dantana gane hausa but ba sosai ba, like a little Baby ta nuna kunshin da hannu tace “I love it so much” tai maganan tanakai hannunta da zuciya daya kawai takama hannun Matan tarike sosai tana kallon kunshin dan an kwashe na hannun an goge sai kallo Ziora take, matan ta tsaya shiru tana kallon Ziora da yanda takama hannunta with so much admiration, anatse tace “ya sunanki”? Ziora na kallon hannun tace “my tribal name is Ziora my Islamic name is Amrah” sosai matan ke kallonta tace “ba mamanki takawo ki amiki tsifa bane Amrah?” Dasauri Ziora ta kalleta dan this time around hausan yamata yawa bata gane duka ba, yanda take kallonta har lokacin tana rikeda hannunta yasa tai murmushi tace “go and loose your hair” murmushi Amrah tayi takara kallon hannunta saita saki hannun tamike tareda washe mata baki tace “bye bye Ma” anatse matan tace “byee Amrah” murmushi tayi tajuya tafita matan tabita da kallo hartaje ta zauna aka fara mata tsifa. Tsifanta yakai kusan rabi tana zaune a wajen taga matar tafito, wani hadaden HK lace ne ajikinta, da hijab dinta a guiwa ya tsaya, hannunta rikeda car key na BMW, kafafunta sanye dawani loafers na bottega, dasauri Ziora tadaga mata hannu tai waving nata itama haka tayi tana mata kyakkyawan murmushi tawuce wajen kofa tana tafiya a natse one by one Ziora tajuyo tana kallonta still saibin kafafunta da hannayenta take da kallo, tana bude kofa tafita Ziora taga yanayin tafiyanta becomes slower, saitaga kaman kafafuwanta na hardewa ahaka takai jikin wata arniyan BMW key hannunta tadaga zata bude kawai Ziora taga matan tai kasa dawani irin sauri ta tashi daga kujeran tana yarda towel tace “she fell that woman” da gudu tafito mai mata tsifan tabiyota da sauran matayen wajen, Ziora na zuwa wajen ta duka ganin jini a hancin matan yasa ta dagota hankalinta atashe tace “Ma’am, Ma Ma” idanun matan suka shiga rufewa. 💫KAUNA DA SO💫 ✍🏻M SHAKUR EPISODE 9️⃣ Hair stylist dakema Ziora tsifa tace “every month ko 2months depends tana zuwa yin kunshi anan but she always looks sick daman, yanzu yazamuyi” duk yan wajen sukai shiru dasauri Ziora tace “give me your phone lemme call Ya Moh” ba musu ta bata dasauri Ziora ta karba har lokacin matan na jikinta ta kankameta tasa personal number Ya Moh tai dialing yana ringing yadaga cus family members kadai keda this his number arude tace “Ya Moh is me, are you in the hospital? Somebody is sick a saloon” zare wayan tayi daga kunnenta tace “yana hospital yace nakawota let’s put her in the car” key motan ta karba tabude, matan suka tayata suka bude baya akasa matan Ziora tasa mata seat belt sannan aka rufe motan kawai tazagaya ta shiga mazaunin driver taja motan da gudu, Matan dakema Ziora tsifa ta kalli sauran mutanen tace “I know the girl, their house da duka yan gidansu ma nasani, yayanta is a Dr so everything is fine this woman will get better” ajiyan zuciya kowa ya sauke aka wuce aka koma ciki. Bini bini tana tuki tana juyowa tana kallon matan that was unconscious har takai private asibitin da Ya Chidi ke aiki, tana shiga tagansa yana waje tsaye da labcoat yana jiranta kafin tai parking ta sauke glass kasa ta kwalamai kira. “Ya Chidi” dasauri yataho zuwa inda tai parking tareda nurses aka bude baya aka dauki matan, Ziora tafito tabisu da gudu, Ya Chidi dake tafiya tareda nurses da sauri sauri yace “did you know her?” Girgiza kai kawai tayi tace “a saloon na ganta” calmly ganin dukta rude yace “okay check her car or her phone or bag, call any family member nata, haka akeyi meanwhile lemme go and save her life” gyadamai kai tayi idanunta na ciccikowa da hawaye, suka shiga room da ita hakan yasa ahankali tajuya tafito takoma mota tabude ta shiga, tashiga neme neme babu wani abu mai mahimmaci a motan taduba ko ina, saita dauki handbag nata tabude drugs tagani cikin wani roba haka na drug holder anyi arranging kaman magungunna dazata sha da rana ne ko dare dan gasunan daban daban, saiga wayanta iphone 16 taciro call log nata taduba, Son1 and Son2 sune the only contact datake waya dasu like almost all the time especially Son1, ajiyan zuciya Ziora ta sauke sannan ahankali tafara dialing number Son 1 amman kwata kwata bai shiga ba kusan sau uku, bayama ringing ne, sannan network basa cewa komi is as if number yashiga flight mode, sai kawai tai dialing Son 2 bai shigaba shima, tana dialing tana duba magungunan a roba suke so babu ma suna, jakan takara dubawa idanunta ne ya sauka kan wani kati haka plastic card, ansa I’m a Cancer Patient! Gaban Ziora yafadi dummm! Dawani irin gudu tasauko daga motan tabar wayan ciki tai cikin asibitin tana zuwa tafada dakin emergency room din inda Ya Chidi da nurses ke kanta dasauri tace “Ya Chidi look, I think she’s a cancer patient I saw this card and this drugs in her purse” dakatawa Dr Chidi yayi yazo ya karbi drugs din yabude anatse yana kallo kafin ya kalli Matan da har lokacin bata dawo hayyacinta ba, anatse tace “that explain everything thank you Smart Ziora you just save her life, excuse us now” ficewa tayi daga dakin tana kara satan kallon matan saita zauna anan wajen dakin tai shiru tai tagumi gabanta kawai sai faduwa yake tawani kalan damu na ban mamaki, cancer data gani ya tsayamata arai, bude kofan akayi dasauri ta dago kai Ya Chidi ne yace “have you spoken to her family?” Girgizamai kai tayi, Moh ya tsareta da idanu yace “call them again” yajuya zai wuce dasauri tace “Ya is she aw…..awa…ke?” Tai maganan muryanta na breaking tana shirin fashewa da kuka, Chidi yawani tsareta da idanu he’s not trying to blame her infact she did the right thing na saving life din mutum, but Ziora is so soft she easily get attach, ga tausayi da saurin kuka yace “when you know bakida zuciyan why didn’t you let saloon people to take her to the hospital? Ba saloon dinsu taje ba”? Bayan hannu takai tayi share fuskanta tass tahana kanta kukan karya mata bala’i sannan tace “I know you’re the best Dr saisa nakawota wajen yayana” hararanta yayi yace “kikamin kuka anan saina tattakaki my friend go and call her family” gyadamai kai tayi tajuya yace “ina zaki?” Ahankali tace “wayanta na motanta” tana maganan tawuce tana goge hawayen, tawuce waje wajen parking space tabude motan ahankali tadauki wayan tana danna screen saitaga 3 missed call from Son1 dasauri tai dialing number back ringing daya aka daga wani nutsassiyar tattausan murya dake cike da izza dakuma dan tsauri kadan yace “Mami nah!” Hakanan gabanta yafadi sai kawai taji maganan datake shirin yi ya karare a wuyanta, and voice din kaman ta tabaji somewhere but she is not certain, sauke ijiyan zuciya tayi mai kara. “uhmmmmm” shiru daga dayan bangaren akayi ba’ace komiba kuma ba’a kashe wayan ba, daurewa Ziora tayi anatse cikin turenci tace “my name is Ziora, I am with your Mom in hospital, I actually brought her her…….” “Which hospital!”? Mutumin ya tambaya babu babu wasa kan muryansa, hakanan kawai saitaji kaman she’s in trouble kirjinta wani kalan dum! Dum! Dum! Yake mata, ahankali tace “ka…..” kawai taji shiru dasauri tacire wayan daga kunnenta taga wayan yamutu ba chaji, Innalillahi yanzu mezata cema Ya Chidi? Ijiiyan zuciya ta sauke kawai ta ijiye wayan ta fito tadawo cikin hospital din direct dakin tawuce danta gayama ya Moh wayan matan ya mutu daidai lokacin matan tashiga bude idanunta Chidi na juyowa yakalli Ziora datazo da sauri wajen gadon sai kawai takama hannun matan tarike sosai cikeda damuwa tace “Mami” cus taji haka danta yakirata, bude idanunta gabaki daya Mami tayi tadaura idanunta dake nuna rashin lafiya sosai akan Ziora da idanunta suka cicciko da hawaye ga gyalenta ya zame kasa, kannan rabi daya a tsefe bari daya ba’a tsefe ba, ahankali Ziora tace “do you remember me Mami in the saloon? I’m Ziora, you fainted u were having nosebleed shine I drive you to hospital na Yayana, this is my brother Dr Moh Chidi, he’s my elder brother, I tried calling your children ta wayanki but wayanki yamutu ba charge, can you give Ya Moh number su yakirasu?” Lumshe idanu Mami tayi tabude kafin ahankali ta yunkuro zata tashi tana salati ahankali. “La’ilaha illallah Muhammadu Rasulullah” riketa Ziora tayi ta tashi zaune anatse, Ziora duk tai wani iri idanunta na cikowa da hawaye sabida yanda jikinta yayi zafi, anatse Mami ta kalleta tace “mesa baki tsaya an gyaramiki kai ba”? Kallon Mami Ziora tayi the woman looks so strong dudda she’s sick amman she’s talking about kanta da ba’a gama tsefewa ba, hawaye sake ciccikowa a idanun Ziora yayi Mami tai murmushi ganin bata amsaba yasa takalli Chidi tace “thank you for saving my life Dr Muhammad, I see inda Amrah ta dauko kirki da kuma taimako” murmushi kadan Ya Moh yamata, cikeda girmamawa yace “how are you feeling Ma?” Ahankali tace “Alhamdulillah! I have Cervical Cancer” tadanyi murmushi kadan tace “ina last stage already, banson needles, kowani damuwa danasan za’a kawoni asibiti ma na hana, I don’t want hospitals again, Doctors said I have 6months to live so I’m just waiting for time” yanda Ya Chidi ke kallonta haka Ziora ke kallonta idanunta sunyi ja and matan looks so strong, ga addini, ga karfin imani, how can you be this strong and comfortable kasan duka duka wata shidda or less yarage maka a duniya? Zuciyan Ziora, ahankali Chidi yace “how can we contact your family Ma”? Murmushi tayi tace “no need yarana duk suna wajen aiki yanzu, discharge me, Amrah kawo jakana akwai card dina kizo kibiya” dasauri Moh yace “you don’t have to pay Ma, lemme just write the discharge papers and sign, but how will you get home? I won’t let you drive in this condition” dasauri Ziora da muryanta harya dan dishashe sabida tausayi tace “I will drive her home Yaya” dan kallon Ziora yayi itama Mami ta kalli Ziora da idanunta sukai ja, duk babu wanda yayi magana yashiga rubuta papers din Ziora ta mike tace “na dauko wheelchair Yaya?” Gyadamata kai yayi da sauri tawuce tafita Mami tabita da kallo, ahankali Chidi yaja kujera yazauna gaban Mami hakan yasa ta kalleshi, ahankali yace “why will you give up so early? I know wani good trial I can enroll you maybe the outcome will be good Hajiya” sosai Mami ke kallonsa saikuma ahankali tace “no wonder kakeda kanwa that’s very very caring da tausayi just like you, look at how worried she is sabida ni da bata sani ba” tasake murmushi tace “I am just so tired! Kasan tun yaushe nake battling da cancer? Tun yarona yana 18yrs old today he’s 35yrs, he’s also a doctor like you, Oncologist and a Surgeon, but I guess haka Allah yaso ya ganni, and I’m very grateful to Allah dayama bani tsawon rai cus I thought bazankai this stage ba” daidai Ziora na bude kofa tana shigowa da keke, tazo har wajen gadon tamika mata hannu tace “Mami zo” ahankali Mami tace “toh yar Mami” dasauri Ziora ta kalleta saitaji kunya kawai tasa hannu takama Mami, Mami ta kalleta sosai saita taso shima Chidi sai kallonsu yake, zaunar da ita tayi a keken sai Chidi yace “let me” gungurata yayi har wajen motansu tare sukasa Mami a baya, yakalli Ziora da zata shiga gaba anatse yace “be careful kikai dropping nata take a taxi back home I still have patient here” yazaro kudi a pocket 5k yabata na hawa taxi ta karba tace “thank you Ya Doctor” tashiga gaba ta tada motan Chidi ya tsaya saida yaga fitansu yajuya yakoma ciki. Suna shiga hanya tace “Mami where is your house”? Ahankali Mami tace “GRA 1st Avenue house number 10” she knows GRA thanks to Mommy datake rakawa unguwa haka tasa wuta bini bini tana tuki tana kallon Mami ta madubi dake lurada ita, har sukakai hadadden layin suka shiga, unguwan shiru kaman ba mutane, gidan dataga number 10 tawuce tace “Mami nan?” Ahankali Mami data lumshe idanu tabudesu tace “eh nan ne, yi horn” horn Ziora tayi ko sakan uku ba’a karaba aka shiga bude gate din wani maigadi ne dake sanye da uniform na security, gidan babban gidane sosai kusan girman gidansu ga lafiyayyun motoci anyi parking, ga Imam tsaye a tsakar gidan dake sanye da 3quater da t-shirt yayi folding hannu a kirji yana kallon motan saikuma yashiga zuwa while Ziora tawuce wajen parking tai parking daidai Imam na karasowa wajen, Ziora tasa hannu tabude kofan tafito batama lurada Imam ba, tundaga kafa yake kallonta zuwa jean da riga dake jikinta da mayafin dake kanta da yake a zame ga gashinta awaje, kallo daya yamata yaganeta dan yanada gane mutane, yahada fuska sosai yana mata wani kallo da hakanan saida Ziora taji kaman ana kallonta tajuyo dasauri suka hada idanu, faduwa gabanta yayi tana kara kallonsa trying to understand waye kuma wannan wani kallo yake mata haka, sai kawai taji dauke kai ta taho baya zata budema Mami kofa kawai Imam yasha mata gaba. 💫KAUNA DA SO💫 ✍🏻M SHAKUR EPISODE 🔟 Chak Ziora ta tsaya tadago kai ta kallesa takasa motsi sabida yanda ya tsaya mata agaba yana kallonta, sai kawai tadauke kai tace “excuse me!” Cikin kakkausan murya Imam yace “why are you here?” Dawani irin sauri Ziora ta kallesa kaman ya why is she here, baki tabude zatai magana kawai yadaka mata tsawa. “What’s a girl like you doing a motan Mamana? Why are you with Mami?” Kafin Ziora tamace wani abu Mami ta lallaba tabude kofan ta dayan side din tunda yatare side din daya kamata tafito da, dasauri dukansu biyu atare suka kalli kofan hango Mami tabude kofa struggling tafito yasa Imam yayi wajen dasauri yaduka kawai agabanta yakai hannunsa kan fuskanta yace “Mami? Meya sameki? Wait? Yar shaye-shayen nan tabugeki da motan ta ne komeya faru?” Kafinma Mami tayi magana kawai Imam yataso yakalli Ziora data zagayo itama wajen amman bata matso kusada Mami ba sabida yana wajen yace “yauma kinyi shaye shaye ne like the other day a golf club? Me kikama Mami? Why is she with you”? Zafi ran Ziora yayi sosai though bata ganesa ba but maganan golf club dayayi made her realizes cewa yaganta hala dasuna golf club taredasu Mira zatai magana dan ranta yabaci Mami ta lallaba tafito daga motan ahankali tana dafa mota tace “Maheer! Imam!” Juyowa yayi dasauri yakalleta zatamai magana Ziora itama cikeda bala’i tana bankama Imam din harara gaban Mami tace “Mami I’m going! I wish you quick recovery and May Allah grant you Shifah” tai maganan zata wuce abinta karaf Mami takama hannunta tace “Amrah wait!” Tsayawa Ziora tayi takalleta zata turo baki kuma saita fasa dan matan look weak and sick she needs rest, cikin rashin kuzari Mami tace “don’t mind all abinda Maheer yace, you can’t trek back home ai, inane gidanku?” Ahankali takama dayan hannun Mami in a very loving way tace “Mami Ya Chidi gave me money for taxi nakai road I will take taxi back home” dasauri Mami tace “no! Take this car with you, gobe saiki kawomin I want to see you tommorow okay” tsayawa Imam yayi yana kallon Mami da wannan yarinyar dayagani a golf club tareda mahaukatan kawayenta irinta Mami na nan nan da ita kaman tasanta da dadewa, sauke kanta kasa Ziora tayi ahankali jin abinda Mami tafadi kana gani kasan bataso ta dauki motan, maganganun yaron sun mata zafi, kaman Mami ta lurada hakan takalli Imam daya tsaya yana kallonsu kaman yasami TV ta hararesa tace “you dont talk to my guest like that Imam” sauke kansa kasa yayi, Mami takalli Ziora tai murmushi tace “don’t mind Maheer haka bakinsa yake ba filter kinsan footballers, don’t take any abu daya fadi to heart, he’s a good person once u get to know him okay” Ziora kin cewa komi tayi, Mami tajuyo takalli Imam dake kallonsu strictly tace “apologize to Amrah right now! Without her help I would’ve been dead by now, she saved my life, she saved me” shiru Imam yayi yana kallon Mami, there’s nothing dabazai iya yima Mami ba hakan yasa yadan kalli Ziora da batama kallon direction dayake yace “I take back my words sorry Amrah!” Hakanan Ziora taji gabanta yafadi dahar saida tadan dago kanta ta kallesa suka hada idanu ta ballamai harara tareda make kafada tace “I forgive you because of Mami if not saina rama” ashagwabe tai maganan tadauke kai sabida faduwa da gabanta yayi takalli Mami sai kawai tai hugging Mami tsam batare datamasan dalili ba, murmushi Mami tayi ta shafa bayanta ahankali tace “I’m fine! Start going kar Dr yadamu same with ur Mom nasan hala tadawo Saloon daukanki” dagowa Ziora tayi daga jikin Mami ahankali tace “take care ko Mami, take your drugs, karki kara fita” sosai Mami ke kallonta kowa na cemata take care take your drugs, but kalman karki kara fita mutum daya ne rak ke fadamata shi a duniya sai Ziora yau tazama tabiyu murmushi Mami tayi mai taushi tace “tom bazan karaba Amrah, shiga mota” bude motan Ziora tayi batare data kara kallon Imam ba, ta shiga ta kunna Mami duk na kallonta tace “banda gudu” gyadama Mami kai tayi ta juya da motan saida tazo daidai saitin Imam takara kallonsa hada idanu sukayi ga mamakinsa ballamai harara tayi harda juya idanu sannan tafice daga gate din da aka bude mata Imam yabi motan da idanu yana mamakin yanda ta ballamai harara, Mami tace “sai muje ko Oga Imamu mara kirki” dan shafa kai yayi yataho yana kamata yace “Mami what are you doing with a Christian girl? This child na shaye shaye kinga yaran datake yawo dasu ne karuwai ne fa….” Wani kallo Mami tamai tace “banson karajin maganan nan, she’s a Muslim, kodama she’s a Christian I don’t care, what matters is heart, ina kaunar Amrah”. Da gudu take driving daidai tana kokarin shan kwana tafita daga layin wata babban Range Rover sport baka kirin na tahowa da mahaukacin gudu da saida sukai clashing yadaki gaban motanta, ihu Ziora tayi sosai tana taka wani mahaukacin brake, tunda tafara driving bata taba accident ba, hannunta saida yabuge sosai tai maza ta kashe motan takasa dawowa daidai ga hanyar ba mutane tadauka unguwansu ne ba mutane but yau for the first time taga unguwar dayaci uban nasu arashin ganin mutanen, bude gaban Range Rover akayi dasauri ta kalla tana mamakin waye ganin mai Range Rover bai reversing back ba, wani black matashi ne da wlh tana kallonsa taga Mami tsaf kawai ita Mami fara ce, amman kaman tayi kaki ta tofar unlike she Imam data gani a gidan baiyi kama da ita ba shi fari ne but baya kama da Mami, hakanan taga kaman ta taba ganinsa, yanada cikan jiki kadan kaman body builder, yanada saje bakin kirin da gemu baki shima daya taru a fuskansa, yanada pink lips that looks kaman ciwo but they’re dead gorgeous exactly kaman mutumin data gani a mall kawai wannan baisa glass ba, gawani dogon hanci da manyan idanu round masu dogayen eyelash ga gashin gira baki kirin, yanada suma akansa baki sunyi coils sosai sunada yawa kana ganinsa kaga bafulatani, bahaushe ne oho dai, ga uwa uba tsayi kana ganinsa akalla zaikai 35yrs yana sanye dawata riga da wando kafafunsa crock ne ga lab coat ajikinsa fara kal an rubuta Dr AH ajiki,

Chapter 5 of 26