makota da abokan arziki sun shigowa Mami wuraren la’asar aka watse.
Fitowa Mami tayi cikin wani tsadadden lace tasha gwal a wuya da kunne da hannu gawasu mata gefenta guda biyu suna wake suna tafi Chef da nurse anci gayu ana wake wlh bawai karyaba she was sad but jin muryan Mami dan an lullubeta yasa kawai ta dage lullubin ta fizge hannunta daga na Daddy da step Mom tawani rugo da gudu tace “Mamiiiii” tawani hugging Mami hartana baya zata kadata Chidi yace “Amrah” Mami tace “barmin y’ata” Ziora ta kankame Mami sosai saikuma tasa kuka tace “Mami how many days now I didn’t talk to you I’ve missed you Mami are you fine?” Tai maganan tana shafa fuskan Mami, Mami kawai na kallonta saita kara hugging nata tace “I am very fine but I miss you so much you look so beautiful Masha Allah welcome welcome” takama hannunta takalli su Daddy tace “bismillah ku” suka shiga flat din Mami da aka gyara abubuwan hospital dinnan duk babu Micheal sai kallon ko’ina yake atleast ba gidan wahala suka kawo kanwarsu ba duk wani abu da aka dafa saida Mami tasa aka kawo musu shi kansa Daddy saida yace “Hajiya yakamata kihuta” Mami tace “yau rannan yarana ne” sunci waina kam har shi kansa Micheal saida yaci waina Mami tace “sutashi suje side na Ziora” kafin su shiga da Mami da Step Mom suakasa Ziora tai alwala sannan suka shiga da ita flat din Ya Allah wani kamshin turaren wuta ne yamusu sallama falon very big falo ne mai two in one falo combination of kayan dakin da Aliyu yayi ne da na Daddy gidan kaman ba a Nigeria ba, you will not believe everything was put together in just seven days jama’a Allah ya azurtamu kawai haka komi yayi kyau fentin gidan wani kalan fari ne off white off white so many things da daddy yagani ma yatuna bai saya ba he was extremely happy ga akwatuna dasuka gani guda 16 Mami tace “ba Lokaci saisa bamu kawo akwatunan ta ba” Step Mom tace Masha Allah Mami takaisu sama 4 bedroom ne asama kowanne da gado na gani na fada an gyara an shimfida sai kawai Ziora tahau tsalle tace “my flat is sooo fine yayyy” dakuwa Daddy yamata ta kwashe da dariya Mami tace “abarmin ya’ata” to be
Honest kowa cikinsu were happy with the kind relationship dasuka gani between Mami and Ziora komawa falo akayi aka zazzauna, Daddy ya gyara zama yace “to Alhamdulillah the amount of years danai zama cikin hausawa made me understand why bamuga Aliyu ba nasan sai dare ango ke shigowa, dan haka ga yarmu nan mun kawota mun baki amanan ta, Amrah ba tamu bace ba taku ce halak malak yarinya na is still a small girl abubuwa da dama bata iyaba but with your love and constant guidance I know Amrah will learn everything, idan tayi ba daidai ba call me, Chidi collect her phone kasamata number kowa we are all family now we are one muna addu’a may Allah bless this union” komawa yace Ameen
Daddy ya kalli Ziora daketa murmushi yace “follow your husband and obey him, duk randa Aliyu yakawo karanki waje Princess saina cimiki mutunci na sassaba miki, you know I love you but now all the love yakoma kan Aliyu ni da Mamin ki we exchange” Mami tace “kwarai” Daddy yace “Dan haka live peacefully with everyone don’t trouble Mami, take care of her, be good to her okay” dasauri tace “okay” tana hugging Mami sannan suka mimmike Daddy yace “let’s go” dasauri Ziora tace “bueee Daddy, step Mom, Ya Micheal Chidi Obinna bye me this is now my house” dukansu kallonta suke Mami tace “ai ma Dan takamusu ko” Chidi yace “Mami saina ganku hospital gobe”
Mami tace “Toh Allah ya aranana rai” har mota suka rakasu suna waving nasu suna fita Ziora tai wani tsalle tawani rungume Mami tace “Mami I’m very very happy yayyyy, we will stay together now ko Mami I will always be with you” Mami tace “okay muje” suka wuce flat na Mami dakin Mami tawuce tashiga kiciniyan cire kayan Mami tace “ahh barsu barsu nace” suna tare da Mami har akai magrib Mami tasata taci abinci tai kat sannan tace “muje na rakaki flat naki” kallon Mami tayi ahankali tace “I want to stay here” Mami tace “nooo”
Shiga flat nasu sukayi Mami takama hannunta har sama tabude wani daki tace “both you and Aliyu anan zaku zauna, you can come to my side in the afternoon but yamma nayi back to your side remember you are a married woman your husband is number 1 for you not me, now remove your clothes shower and change to any clothes a wardrobe naki” tabude wardrobe nata dayake tasaya mata beskope daga wajen wata yar instagram dayawa hoton Ziora kawai ta tura aka mata cus ba jiki tace “bari naje side dina” ahankali tace “Mami I want to follow u” Mami tace “kul this is marriage yanzun nan Aliyu zai dawo” gyadama Mami kai tayi gabanta na faduwa sosai idanunta na ciccikowa da ruwa ta tafi.
Aliyu yana masallaci an idar da isha’i yaga wayansa na ringing kallon wayan yayi Mami ne hakan yasa yamike yafito yana sanye cikin wata bugaggiyar shadda yashiga motansa ya gangaro zuwa gidansu yayi parking yawuce direct flat na Mami, shiga yayi Mami ne afalo tareda wasu yan aiki da baimasan a ina aka samosu ba yace “Mami gani kin kirani” tashi tayi tace “come with me” tawuce dakinta Aliyu yashigo, tanunamai gefen gado tace “zoka zauna” tahowa yayi yazauna tace “dazu iyayen Amrah suka kawota tana flat dinta, kayanka kap dakaina na hadasu na bada an kai side din naje dakaina na jera maka ko singileti bakada shi a bangarena balle silipas na sallameka” dasauri ya kalleta Mami tace “kwara kajini da kyau”
Idanma tsoron mai kwana dani kake yaran na daka gani yan aiki ne Chef takawo min daya zata dinga kwana a gidan nan dayan kuma yaunw kawai zata kwana sabida aiki yay yawa so ka koma side dinka daga yanzu ko zazzabi nakeji cikin dare zan daga waya na kiraka that’s all yanzu dai tashi kawuce bangaren matarka yarinya ce kada ka barta ita kadai amana ce iyayenta suka baka nima kuma na baka kaci zalin Amrah xalina kaci, ka kyautata mata nika kyautata mawa, matarka ce yanzu Aliyu ka kula da yarinyar nan kaji ko” gyadama Mami kai kawai yayi Mami tace “Toh Allah maka albarka” ahankali yace “Ameen” saiya kasa tashi Mami tace “tashi kaje” tashi yayi ahankali yamike yabude kofa harzai fita yace “we are going to the hospital in the morning” Mami tace “Allah yakaimu” ficewa yayi yamaida kofan zai rufe yakara kallonta yace “if you feel any type of way call me” Gyadamai kai tayi tace “naji Aliyu” zai fita tace “kasami Maheer”? Ahankali yace “a’a wai yayi tafiya inji Abba” ahankali ta gyadamai kai yawuce yafita shidai ba wani first night zaiyiba balle yawani sayi kaza anatse yawuce side Dinka daga yanzu ya tsaya yakali bird din mai kyau green a cage nasa saiya bude kofan ahankali yashiga da sallama abakinsa yamaida kofan yarufe yakalli wata yar karamin takalmi flat shoe na Zara dake wajen doormat dake wajen yacire nasa takalmin awajen yana kallon ko’ina na dakin da sai yanzu yake shigowa tunda aka fara gyara ko’ina kanshi yake kulle kofan yayi yakashe wutan falon yahayo sama.
Ziora na dakin da Mami ta shigar da ita dakin tunda Aliyu yashigo tajisa hakanan kawoa gabanta yahau faduwa kawai saitaji Allah yadaura mata wani irin mugun tsoronsa saitaji gwara tasoshi while leaving with Mami than t soshi leaving with him only him sai kawai taja bargo ta shige ciki ta dukunkune tana jinsa harya hayo sama direct wani daki yawuce yana budewa yaga kuma dakinsa ne sabida laptop dinsa daya gani yamaida kofan dakin yarufe kaman mai nazarin dakin yawuce wajen wardrobe yabude yaga kayansa tsaf Mami tai arranging wani bagpack yadauka yafito dashi ya ijiye kan kujera yawuce yashiga yashiga bayi wanka yayi tsaf yafito ya shirya ya saka wani pajamas navy blue riga da wando yasaka boturan ya fesa turare wasu sababbin slippers dake wajen wanda yasan aikin Mamin sa ne yasaka yafito yasauka kasa praying Allah sa Mami takawo masa abubuwan Coffee sa yana zuwa yagani yashiga kitchen dinsu yabi da kallo shi kansa kitchen din yamasa kyau yahada coffee yafito yazo dinning yaja chair yazauna zaikai baki hakanan kawai saiya tsaya ya dakata yadan kalli sama sai kawai yadan sauke ijiyan zuciya yamike tareda daukan coffee kawai saiya wuce sama baimasan takamaiman wannene dakinta ba saiya shiga bude kofa dakuman har yazo last one din yana bude kofan akan idanunsa Ziora tai wani motsi cikin bargo takara chukurkudewa sai ya tsaya shiruuu kawai yana kallonta dakinta yayi kyau sosai gawani kamshi da dakinta keyi na daban ba irin na falo ba ko na dakinsa kamshin dakinta is so so sweet, da dan karamin murya yace “Kee!” Kin motsi Ziora tayi tana jinsa gabanta na faduwa sosai from yanda take breathing ma kasan she’s awake, cikin kakkausan murya Aliyu yace “Amarahhhh!” Wani zabura tayi ta yaye bargon tasaso zaune gabaki daya kan gadon rigan atampa ne ajikinta da inner skirt fari.
EPISODE 5️⃣9️⃣
Skirt fari kal gajere daya tsaya mata iya guiwa ne ajikinta tuni ta cire lapayan ta ijiye gefe danya isheta, sai dan kunne na gold dake kunnenta da sarka dan kunnen da warwaraye, kanta ba dankwali sai chukun daya sauko, zaro idanu tayi kaman wacce aka kama tana wani abu mara kyau na laifi tana kallonsa, tunda yake baitaba ganinta da rigan atampa ba nor kitso ba, wlh baitaba ganin tamai kyau kaman na yau ba, kawai yacire idanunsa daga kanta, da sauri yadan gyara ganin inner skirt ne jikinta yadanyi gyaran murya da kyar yace “have you eaten”? Amrah nawani irin kallon kallonsa kaman bata taba ganinsa ba sai yau tace “no” juyo da kansa yayi yamata wani mugun kallo dayasa ta sauke kanta kasa dasauri tashiga wasa da yatsunta, ahankali yace “come outside and eat” yana maganan yajuya yafice daga dakin itakuma ta dirko daga kan gadon farin skirt ne kana ganin pant din data saka fari aciki, ita bata taba saka kalan skirt din bama arayuwanta Step mom ne tabata tasaka sai ringin atampan jikinta mai milk da green daya mata kyau, shukun da aka mata ya sauka har gadon bayanta, tafito kawai ba takalmi kafanta, lallen da aka mata yayi bala’in kyau, Aliyu na zaune a nan kujeran dake falon sama yana kurban coffee tana fitowa yadauke kai da sauri daga kallonta, dan tsayawa Ziora tayi takasa mai magana sai kawai tajuya tayi stairs abinta tahau sauka har zuwa dinning, wutan wajen a kunne tabude kofa tashiga kitchen tana bude bude bataga madara ba ko Milo ba saita fito daga kitchen din daidai Aliyu na karasowa last staircase, dasauri tasauke kanta kasa shikuma ya tsaya daga wajen, kallo daya yama jikinta yadauke kai gabansa na faduwa yace “wat?” Murya chan kasa kaman mai tsoron magana tace “no tea” dan tsuki yayi yataho yazo dinning din ya ijiye cup din da wayansa awajen saiya wuce falo yace “wait for me there” yayi kofa yabude key yabude kofan yafita.
Amrah ta kalli cup din daya ijiye, Mommy always pack plates da daddy yayi using tashiga kitchen idan yan aiki basanan ta wanke da kanta and put them back hakan yasa tawuce tasa hannu tadauki cup din takoma kitchen ta wanke cup din ta ijiye tafito tazauna a dinning din takai hannunta wuyanta tana kiciniyan cire sarkan takasa.
Flat dinsu yabude yashiga da Ammi da yaran na zaune falo abinsu suna kallon dadin kowa, Aliyu yashigo Mami ta kallesa tace “ahh Aliyu kayi mantuwa ne”? Mutanen falon ya kalla yace “uhn” saiya wuce dinning yana haderai Mami na kallonsa ta wutsiyan idanu, plate yadauka so unlike him yabude flask daya gani awajen rice me lafiyayye jellof yadeba yasa a plate yasa mata chicken saiya dauki cup yabude madara yasa spoon yadeba da Milo yawuce Kitchen yadauko tray da another plate yarufe abincin yadauki tray yayi kofa uppan Mami batacemai ba saida yabude kofa tafita tai wani murmushi mai kayatarwa.
Amrah na zaune a dinning aka bude kofan da sauri ta dakata da kiciniyan da sarkan datakeyi tajuyo suka hada idanu da Aliyu dasauri ta sauke kanta kasa ta tana wasa da kunba gabanta na faduwa harya karaso dinning fin ya ijiye abincin agabanta kaman mai shakkan magana tace “thank you Ya Aliyu” kafin Aliyu ya matsa ma tasa hannu tadauki cup dataga madara da Milo ciki tamike tai kitchen idanunsa na sauka abayanta ya hango pant dinta, yanda gabansa yabuga baisan sanda yadauki wayansa yawuce falon yakunna tv tareda zama ba, fitowa Ziora tayi tabude fridge dake dinning din tana neman ice babu but akwai cold water saita dauka tajuye a tea tadawo tazauna adinning takai tea baki tana sha cikin 1min ta shanye zata mike Aliyu yace “the rice is for who”? Juyowa tayi ta kallesa adam tsorace dan ko bude rice din batayiba dasauri ta maida idanunta tray tadauki rice din tabude tasa spoon tafara ci ahankali badawani yawa yasamata ba sabida yasan dare ne but kaman zatai amai bata wani son abinci amman haka ta cinye tasssss ta mike tadauki tray tai kitchen Aliyu yakara binta da kallo kafin yadauke kai da sauri ta shiga ta wanke komi sannan tafito ko kallon inda yake batayiba a falon tawuce tahau staircase ta tafi sama Aliyu yadan dago kansa yabita da kallo dasauri yasake dauke kansa saida yaji tabude dakinta ta shiga sannan yamike yakashe kallonyasake kalulle kofa da key da komi sannan yahayo sama tashiga dakinta.
Kaya Ziora tacire tadauki towel fari tadaura a kirji, tacire earrings din tai juyin duniya tacire sarkan takasa gashi tanaso tai wanka bazata taba iya bacci da kayon sarkan nan awuyanta ba hakan yasa tace “bari taje side na Mami tacire mata”
Daga ita sai towel dinta babu dankwalin akanta tabude kofa tafito ko kulle kofan dakin nata batayiba tayi staircase tashiga sauka kasa tai wajen kofan falo tana kiciniyan bude kofa takasa.
Aliyu na zaune dakinsa yaji karan bude kofa aransa yace me kuma fitinanniyan yarinyar nan tafito tayi but jin ana fama da kofan falo na sada mutum da waje yasa ba shiri yatashi ransa na baci yafito yana kallon dakinta inda yaga pant skirt da rigan data cire akasa gaban bayi yayi stairs dasauri idanunsa na sauka akanta tana faman bude kofa cikin husky voice yace “are you a rat?”Dawani irin sauri Ziora tajuyo takalli Aliyu dayake last stairs case dayake akwai haske a dinning yana ganinsa gabanta na faduwa kaman zatai kuka ta nunamai wuyanta tace “I can’t remove this I want to go to Mami place tacireminnnnn” wani takaici daya kama Aliyu ko baisan sanda yace “come here!” Atsawace ba, rawa kawai jikin Ziora yafara sai tabude baki zata fashe da kuka yakai yatsansa tadaura kan lips alamun shiru hakan yasa tahadiye kukan ta taho gabansa ahankali ta tsaya tunda yana last stairs dinne saita taho tana neman take kafafunsa tahayo yakoma baya da sauri gabansa na faduwa.
EPISODE 6️⃣0️⃣
Kamshin datakeyi na wankan turare da akamata na gyaran jiki yadaki hancin Aliyu yakusan shidewa sai yama kasa masifan gabaki daya adan gajiya yace “stand there turn around” dan kallonsa Amrah tayi cus bata taba tsammanin zai offering yacire mata ba, yanda ta tsaresa da mayun idanunta yasa cikeda takaici yace “do i look like candy?” Akunyace ta juya murmushi na subuce mata abaki jin yakira kansa Candy, tadaga hannunta takawo tabaya ta tattare gashinta sama tana jiransa yacire mata, hannayenta Aliyu yabi da kallo dasuka sha lalli sannan yabi wuyanta da kallo akwai wasu gashi masu kyau atawajajen keyanta runtse idanunsa Aliyu yayi da sauri sannan yabude yaki yarda yakalleta yasauke idanunsa daidai wajen sarkan sannan yakai hannunsa wajen batare daya taba skin nata ba yakawo fuskansa bayan wuyanta dan bawai yataba cirema wata sarka bane he just wanna see how the thing is yacire mata yahuta, saukan numfashinsa Amrah taji awuyanta wani yarrrr tsigan jikinta yatashi kirjinta yashiga bugawa bata tabajin hakaba cikinta na murdawa, hannunsa yakai ahankali ya kwance sarkan yazaro daga wuyanta, dasauri tajuyo takallesa wani mugun kallo yamata yamika mata sarkan tasauke idanunta tamikamai hannunta danya samata akai, cikin kakkausan murya Aliyu yace “don’t ever make mistake of stepping out of this flat with something like this or not properly covered, this is not your father’s house!” Yana maganan yajuya yawuce Amrah tabisa da kallo kawai maganan yamata ciwo a zuciya kawai saitaji kuka yazo mata kaman ta wuce tai tafiyanta gidansu, har Aliyu yamika zai bude kofan dakinsa ya shiga sai yaji karan jan hanci alamun kuka take just like that kuma saiyaji zuciyansa tai wani iri kawai saiya tsaya chak yakasa bude kofa yashiga dakin wlh he stood there for like 3min sannan Amrah tashiga haurowa sama hannunta daya rike da sarka dayan hannun kuma tana goge fuskanta dashi idanunta har sunyi jaaa karasa hayowa sama tayi sabida she’s busy tana goge fuska bama ta lurada shi ba tawuce dakinta tabude kofa ta shiga duk Aliyunna kallonta ta wutsiyan idanu taduka tadauki kayanta tsaf ta links ta ijiye sarkan saita shiga bayi.
Tai wanka ta wawwake makeup din fuskan daya isheta tadauro alwala tafito wardrobe na dakin taje tabude ga kaya anyi arranging ga kayan bacci saita dauko wani half iya cinye kawai tadaka tadauki wani black hijab har kasa tasaka ta tsaya tana kokarin gane gabansa from salla datakeyi a side na Mami tagano tai sallan nan magrib da isha’i in 1min tagama tazare hijabi ta linke komi ta ijiye tahau gado ta kwanta tai shiru tana tambayan kanta ita mesa ma tai auren shikenan yanzu? He didn’t come to her room yanda akeyi sai masifa yake mata why did she even marry him ta turo baki ita kadai, she’s missing her Daddy kaman takirasa but Mommy ta karbe wayanta, juye juye tashiga yi na kusan 30min kafin tai wani hamma tana kulle baki ahaka bacci yayi awon gaba da ita.
Dudda he wants to sleep but wlh Aliyu couldn’t sleep kawai wani nauyi yakeji akansa na another responsibility yahau kansa gata yar yarinya mara hankali kiri kiri tsoro ne ko anxiety ma yabana sa bacci before this girl takama hanya tafice tsakar gida this night, sai tsoro yakeji yana tunanin tanama kwana ita kadai adaki agidan su, gabaki daya shi kallon mara hankalin karaman yarinya yakema Ziora yana zaune ahaka har wajajen 11:30 nadare sai kawai yamike yabude kofa yafito yataho dakin bata yasa hannu yabude kofan ahankali akan gado yaganta tai bacci ta dukunkune ta balbala AC wuta a kunne kafafuwan nan nata har zuwa cinya awaje, Ya Allah wani yirrrr yaji dabaisan sanda yajuya dasauri kaman zai fita daga dakin saikuma ya tsaya yana dan tsuki wai mesama Mami tamai haka please please wannan ai wahala ta daura akansa juyowa yay yadaura hannu sakan idanunsa kaman makaho yataho yasa hannu yaja bargon saida yarufa mata cinya sannan yasauke hannun yakalleta ya rufeta da bargon da kyau sannan yadauki remote na AC yarage AC yazo wajen kofa yazare key ta baya yakashe wuta yarufo kofan tagaba yasa key just so that his mind will be at peace yawuce dakinsa ya kwanta akan gado.
He slept har zuwa around 3 nadare sai yatashi yadinga salloli har zuwa around 5 sannan yamike yafito rike da key dakinta yataho wajen kofan ahankali yasa key din yabude kofan dakin duhu so hakan yasa yakai hannu yakunna wutan dakin dawani irin mugun gudu yadauke idanunsa daga kanta sabida riganta data kwaye gabadaya zuwa bayanta yana ganin bombom nata awaje, gawani dan karamin white pant ajikinta hannunsa yadaura akan kirjinsa dake wani irin bugawa yajuya da sauri zai wuce saikuma ya tsaya sabida tunawa dayayi abakin gado yaganta if anything should make her move faduwa zatayi akasa baigama tunanin ba yaji saukan ijiyan zuciyanta da motsi hakan yasa yajuyo dasauri yakallo ta daidai itama Ziora tawani mirgina zatai kasa dawani irin gudu Aliyu yashigo cikin dakin zuwa wajen gadon yace “Amrahhhh!” Da karfi daidai tana fadowa yatareta tafado hannayensa kawai yariketa dasauri hakan yasa Ziora tashiga bude idanunta ahankali kafin takara bude idanunta rass tadaurasu kan Aliyu daya zubamata idanu kawai yana kallon yanda take tashi daga bacci dan lumshe idanunta tayi takara budewa sai kawai ta yunkuro tai hugging nashi ta manna kanta a kirjinsa tace “I love you Yaya Aliyu! My Candy” Wani yirrr Aliyu yaji yace “ke!” Dasauri tafito daga jikinsa ya harareta yace “saukan mini daga jiki” hannayenta takai tadaura saman bakinta tana kallonsa bataso yaji any wari ajikinta murya chan kasa tace “I don’t have power” wani kallo yamata dayasa tashiga kokarin tashi daga jikinsa takasa wlh kaman an zuke mata energy sai kawai Aliyu yasa hannu yadagata batare daya kalli jikinta ba yace “go and pray” yamike yafita daga dakin yajawo kofa Amrah tabisa da kallo falo ya sauko sai kawai tashiga bayin nan kasa yadauro alwala yana tsuki yayi kofa yabude yafito yasa key sannan yawuce flat na Mami yabude dakin Mami yayi yay knocking tareda bude kofa akan dadduma yaganta tana salla dan ijiyan zuciya yasauke yajuya yafice yatafi mosque.
Yayi salla yafito wajajen 6:30 tsayawa yayi yaciro wayansa yayi blocking Beeba and he’s on leave saira naita call nata ba Imam yayi dialing funny enough yayi ringing amman bai dagaba, messege kawai Aliyu yashiga yamasa. “What’s going on with you Maheer? Hope you’re okay” yaturamai yamaida wayan aljihunsa sannan yashiga gida flat na Mami yashigo tawuce dakinta yabude yasameta tana rufe Al Qur’ani zama yayi ahankali yace “ina kwana Mami ya karfin jikin” ahankali tace “Alhamdulillah” sai yatashi kawai zai wuce wajen wardrobe nata tace “ina zaka?” Ahankali yace “zanyi arranging kayanki ne a box bayan anyi breakfast zamu tafi” tace “karka damu zansa ahadamin wuce kadubo diyar mutane, anjima kadan xan aiko muku da breakfast” baice komiba yafita amman kana ganinsa kasan baiji dadi ba yawuce flat nasa yasa key yabude kofa yamaida yarufe yahayo sama zai wuce dakin Amrah saikuma ya tsaya yabude kofan tana zaune kan dadduma sanye da blue hijab tana ganinsa tawani washemai baki da saida yadan ware idanunsa.
Dadi takeji yatareta dazata fadi tace “good morning Ya Aliyu” bai amsataba ba yace “you will be going to Islamiyya today 10-4PM” gyadamai kai tayi yajuya abinsa itakuma tamike tsaye tazare hijabinta yarage just rigan baccin iya guiwa kawai tafito yana kokarin bude kofa zatai hanyar staircase yace “where are you going?” Dasauri tajuyo da kanta taga yana tsaye yana kallonta dasauri tace “Mam…….” Kasa karasa maganan tayi sabida kallon daya mata ga kayan dake jikinta banda maganan daya mata jiya dasauri tai daki hijab dinta na salla tadauka tazura tafito again suka hada idanu dashi tajuya takoma dako dasauri
Tamaida kofan tarufe saikuma tafito tashiga tahowa wajen kofan dakin sa ta tsaya tai knocking shiru aka mata sai chan Aliyu yace “wat?” Murya chan kasa Ziora tace “I want to talk to my Daddyyy” daga ciki yace “call him with your phone” murya chan kasa tace “My Mommy seized my phone I don’t have phone” Shiru Aliyu yayi chan yace “come in” bude kofan tayi ahankali tashigo tana kallon ko’ina a dakin daya mata kyau Aliyu na zaune kan chair dakinsa ya kunna laptop ga wayan kusa da shi yadauki wayan yamika mata yace “sit on the bed and make the call” karba tayi saita wuce gadonsa tazauna ta danna screen din wayan yabudu tai dialing number Daddy sai suna yafito sai taga Father In law.
Dan dago kanta tayi takallesa kadan aikinsa yakeyi saitai dialing number ringing daya Daddy yadaga dasauri tace “Daddy is me” daga bangaren Daddy yace “yes I know it’s you My Princess where is your phone” murya chan kasa tace “Mommy collected it” shiru Daddy yayi yace “hope you’re fine ko” dasauri tace “yes but i miss u Daddy” wani iri Daddy yace “I miss you too princess just be a good girl okay, take care of in-laws naki and obey your husband okay” guadamai kai tayi idanunta na
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 26