Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
I love you” tasake hugging Mommy tsamtsam da ita kanta Mommy saitaji jikinta duk yayi sanyi, da yar karaman murya tace “kinfi kowa sona yet kinfi kowa kinjin magana ta, and kinfi kowa troubling dina, you’re just a complicated little girl, very mischievous naughty girl kawai” kankame Mommy tayi tai shiru ko murmushi batayiba cus tunanin Mami take tana kallon gefe daya tana tunani ahankali tace “the woman has last stage of Cervical cancer Mommy, she has less than 6month to live!” Jikin Ziora yakar sanyi itama Mommy haka, ahankali Mommy tace “nakira Pastor Joshua yamata addu’a and anoint her? Yanada power na Miracle healing” Tana cikin damuwa tana kuka ne but maganan Mommy saida yasa Ziora tafashe da dariya harda fadi kujera tace “Mommmmm wat is this please? Allah kadai ke bada lafiya not pastor” Mommy ta harareta tace “har guragu Pastor Joshua ya warkan dasu, ku musulmai don’t believe in miracles, anyways ke kika sani I just wanted to help sabida naga spirit naki is low kin damu, tomorow give our driver the car key kimai kwatancen gidan akai while kije saloon ayi kitson nan” gyadama Mom kai tayi tace “bari naje nai salla” Mommy tace “ku kuka sani da 5daily prayers naku” Ziora tai murmushi tace “you will become a Muslim one day zan baki suna Indo” Mommy tace “God forbid! Tufiakwa sunan ma ba dadi, my name is the best name ever, Florence Adaku” Ziora ta tabe baki tace “ko dadi babu wai Florence, Mommy Indo” ta kwashe da dariya Mom na hararanta, dki tashiga tafada bayi tai wanka tafito tai salla sai tunanin Mami take gashi batada number ta data kirata, Dady ya amshe wayanta ko yaushe zai bata wayan oho. Tana isha’i tai bacci cus tagaji koda Mommy tashigo bata abinci taga tai bacci batajin tun bayan breakfast takara cin wani abincin ba that’s her problem rashin cin abinci. 💫KAUNA DA SO💫 ✍🏻M SHAKUR EPISODE 1️⃣3️⃣ https://www.youtube.com/@mshakur SUBSCRIBE TO MY YOUTUBE CHANNEL 💃💃💃 Around 8 na safe Ziora tafito sanye da rigan bacci iya cinya fari mai kyau sosai, yunwa takeji sosai yau, muryan Daddy taji akasa yasa tafito, the way take missing Daddy kaman she’s missing a part of her, shigowa falon tayi tana kallon Daddy dayaki kallonta wajensa tayi sai kawai ta zauna kan cinyan sa ashgwbe tace “Daddyyyyy” da kyar Daddy ya iya yadake sabida yanda yayi kewanta, hararanta yayi yace “sauke daga jikina” makemai kafada tayi tai hugging nasa sosai zuciyanta na arching tace “Daddy kaya kuri, I will never ever take drugs again, kabani wayana kaji” kai tsaye yace “I will think about it, I want you watch you for 2weeks naga your behavior before I give you back the phone, dagani na wuce” sanyi jikin Ziora yayi idanunta suka cicciko da hawaye sosai daidai Mommy na fitowa daga kitchen dawani flask bottle data hadamai tea ciki, Ziora ta mike daga jikinsa idanunta na saukowa da hawaye, Daddy yakalleta yayi kaman baiga kukan ba yace “make sure kinsa driver ya maida motan mutane they told me what you did jiya I won’t say anything, but make sure driver ya maida motan mutane” gyadamai kai tayi Daddy yamike yawuce yafita abinsa kawai sai Ziora tawuce dinning tazauna tabuga tagumi, tadanba Mommy tausayi, Mommy tasamata fried egg da chips a plate tamata tea takawo gabanta tsakura tayi taci, sannan tasha tea, Mommy tace “jekima driver kwatance yakai motan” gyadama Mommy kai tayi tamike zatai kofa, Mommy tace “ahaka zaki fita”? Juyowa tayi da sauri ta kalli kanta yar rigane jikinta fara iya cinya na bacci, ga spaghetti hand kana ganin fine skin nata da kirjinta ga boobs nata masu kyau a tsaye kaman kwallo awajen, ashagwabe tace “Mommy banasa kaya ba” dakuwa Mommy tamata tace “kinci ubanki tunda kika hadu da shegun yaran nan kika lalace, Maman Jesus Marry batai exposing jikinta ba, I want to take you to Catholic Church kiga yanda Marry ke covering jikinta with something like hijab dinku” turo baki Ziora tayi tace “Mommy ko a Christian dinma ke ustaziyace” rigan Mommy na wajen kawai saita dauka tasaka yamata kato ajiki tafice driver su taba key dayake a falo suke ijiye key agidan su, tamai kwatancen gidan da house number ya gyadamata kai yawuce yashiga mota yatafi. ** Kullum rannan duniya da asuba take tashi, bude idanu tayi ahankali tana karanto addu’o’i, Alhamdulillah babu abinda ke mata ciwo yau, tashi tayi zaune tana kunna wutan dakin babu kowa ciki but taga bargon Aliyu, shiru tayi tana kallon bargon saita mike ta shiga bandaki tana tafiya ahankali, zama tayi kan lafiyayyen kujeran da aka ijiye mata a bayin tadauki brush tafara tana tunani, Amrah kawai tafado ranta, murmushi tayi she can’t wait to see her today, komi tayi tafito daure da alwala tai salla sannan ta taka tabude kofa tafito zama tayi cikin daya daga cikin lumtsastsun kujerun falo tadauki al Qur’anin ta dake wajen tafara karatu anatse, bude kofan akayi da sallama kasa kasa, Mami tadago kanta Aliyu ne yana sanye da jallabiya fara kal da hula akansa itama fara, murmushi tamai tareda mika hannunta still batabar karatun ba, maida kofan Aliyu yayi yataho anutse yazauna gefenta, rungumesa Mami tayi tasa kansa a kafadanta, ijiyan zuciya yayi yay lamo yanajin natsuwa yana sauraron kira’an Mami tacigaba da karatu, he suppose to fix breakfast for her, 10 yake zuwa aiki amman yanda take rera kira’a na basa peace of mind yacigaba da saurara harta idar tai addu’a ta shafa ta kallesa her son is just quiet, Maheer shine gidan radio indai wajen magana ne, hugging nata Mami tayi hakan yasa anatse yace “ina kwana Hajiya Mami” ahankali tace “lafiya lau Doctor, banace ka dinga kwana dakinka ba”? Tamai tambayan tana sakinsa, mikewa yayi batare daya amsa ba yace “lemme make breakfast for you” batace komiba tabisa da kallo ya shiga kitchen tea yamata da omlete na egg daya soya da vegitables yakawo da drugs dinta ya zauna da ita yatabbatar taci yakoma kitchen yana mata fixing mexataci anjima kafin chef tazo by 10 amata lunch cus shine yake dinner. Wuraren 8:30 yagama yakawo dinning ya ijiye yana kallon yanda bini bini take kallon compound nasu ta window dayake labulen a dage ahankali yace “you want to go outside Mami?” Juyowa tayi ta kalleshi saitai murmushi tace “kawai Amrah nake jira dudda bansan sanda zatazo ba amman jinake kaman da safen nan zatazo kasan yara na zuwa makaranta, ta ijiye motan ta wuce school” Aliyu baice komiba kawai yawuce sama dan wanka ya shirya zuwa clinic. Wuraren 9 ya sauko ya shirya tsaf cikin riga da wando dark blue na polo sunmai bala’in kyau yana kamshi sosai ga lab coat a hannunsa ya sauko daidai ana danna horn dasauri Mami ta mike gateman dinsu ya leka waje saiya dawo ciki ya bude gate Mami tace “tazo” tai wajen kofa da sauri Aliyu yadan kalleta saiya wuce kitchen yana taiyaya coffee yafito yazauna a dinning yana sipping, ta window ya hango Mami ta tsaya turus a tsakar gidan fuskanta duk yayi wani iri hakan yasa yakalli motan saiyaga wani ne yafito daga motan yazo yaba Mami key, Mami na mai magana saikuma ta gyadamai kai tajuyo fuskanta yagani yaji zuciyansa ya sosu sosai, when people are sick especially terminal sickness akwai a way da brain nasu ke aiki, inba hakaba akanme zaka hadu da yarinya jiya ta shiga ranka? Shigowa falon Mami tayi tamaida kofa tarufe tazo tazauna, tsaf yagama yamike nurse dinta na shigowa gidan itama da sauri ta gaida Mami tace “good morning Mami ya jikin” ahankali jikinta ba karfi tace “fine” da hannu yama nurse din alamu tazo maganan magani yamata da dosage yakuma gayamata kar abari tafita sannan yamike yazo wajen da Mami take yakalli fuskanta har ransa yaji ba dadi kafin yayi magana ma tace “saika dawo Haidar, Allah yabada sa’a” gyadamata kai yayi yakama hannunta gently yarike cikin nasa yakasa magana, if Mami is happy he’s happy, if she’s sad shima he’s sad, murya chan kasa yace “take care Mami, if you need anything call me” gyadamai kai tayi batai magana ba, mikewa yayi yawuce wajen kofa yabude saiya juyo ya kalleta, she really looks sad ransa kwata kwata baimai dadi ba yadaure yafice yaje wajen mota yabude yashiga yaja ana budemai gate yafice a junction na anguwan yaga Maheer na shigowa layin da motarsa horn yamasa yawuce, wani babban asibiti yaje, asibitin babban gaske ne private kuma yahadu, parking yayi yay shiru saiya dauki wayansa, Maheer yakira ringing daya yadaga ahankali yace “tadan saki ranta yanzu?” Dasauri Imam yace “ohh that means tun agabanka tafara, she’s so down sabida that girl ta jiya, tunda nazo batamin murmushi ba she even cried” shiru Aliyu yayi baice komiba but kasan ya matukar damu, Imam yace “don’t worry, work I will find yarinyar for her zanje saloon din nai tambayan” shiru yayi chan yace “thanks” ya katse wayan yabude motan yafito yafara tafiya anatse batare da ya kalli kowa ba kansa asama, nurses da patient sai kallonsa ake ana gaidasa saidai kawai ya gyadamusu kai dan baida yawan fara’a da magana anma sansa har yakai office nasa da aka rubuta Dr AH ajikin kofan, shiga yayi normal office na consulting patient ne dayake is private asibiti dakin yahadu akwai bed ga AC fridge tv komi, wucewa yayi yazauna yana addu’an shigowa office as usual aka bude kofan office din, bai dago kansa ba dan duka hospital dinnan babu wanda ya isa yashigo office nasa without knocking sai mutum daya, wata budurwace da akalla zatai 28yrs haka ce ta shigo, doguwa ce fara yar mai dan diri dan ba ramammiya bace, tana sanye da normal hospital scrub ga labcoat asama fari an rubuta Dr B awajen aljhun, kanta black veil ne daure akai, sai hoops earrings nata masu kyau dake kunnenta, ga kwalliya a fuskanta sosai, ga janbaki pink, hancinta akwai huji, tasa nose ring mai kyau awajen, kafanta sanye da crocs, hannunta rike da cups din coffee guda biyu tamaida kofan tarufe ta da kafa ta taho tana kallonsa kaman zata hadiyesa takai cup daya gabansa tace “coffee for Mijina, tea for me” ta nuna nata cup din tana kallonsa daidai yagama addu’an ya kalleta kadan saiya kalli coffee dake gabansa ya matsar gefe yace “thanks” murmushi tamai sosai taja kujera tazauna tana facing nasa tace “what are your schedules today?” Computer gabansa ya kunna batare dayace wani abuba, sai kallonsa take idan da sabo tasaba da halinsa na miskilanci, bai iya fira ba, bai iya wasaba, he’s just a serious straight forward mutum, cikin muryansa dake kashe mata zuciya yace “I have just 2 surgeries today sai consultation da ward round” asibitin nan naji dashi shine top oncologist nasu, saisa daya nuna he’s only going to work from 10-4pm suka yarda, this guy is genius he’s a brain box, and he’s the best diagnostician nasu, inhar zaiyi examining patient zai iya gano abinda ke damun patients, so people from different field of medicine come to him especially in hard cases sabida yaduba yatayasu bada diagnosis, Harvard wasa ne? Plus Allah yabasa naturally gifted. Dan rage murya Beeba tayi tana kallonsa kaman zata hadiyesa tace “mufita after closing?” Dago manya manyan idanunsa yayi yakalleta yace “I need to get back home to Mami she’s not happy today” danne zuciyanta tayi da kyar maganan namata zafi shi baiga ita she’s not happy ba ta uwarsa yake, tace “ohh sorry I forgot to ask how is my Mami? Ya karfin jikinta”?“Alhamdulillah” ya amsa a takaici batare daya kara magana ba sai wani case file dake gabansa daya bude yana dubawa, Beeba sai kallonsa take ahaka ma wai duka hospital dinnan ita yake saurara ma wai so ne ahaka? Wai this is soyayya, ahankali ta mike daga kan kujeran saita taho gently tazagayo ta wajen dayake zaune kan kujera yadago kansa ya kalleta, rufe file dayake dubawa tayi ta zauna akan table din taredakai hannunta tadaura kan nasa takama tarike sosai, kallonta Aliyu yayi murya chan kasa yace “what are you doing Habiba”? Wani murmushi tayi sosai zuciyanta ba dadi tace “baka so na” lumshe idanu yayi yabude su yamaida kanta, asanyaye cikin muryan nan dake mugun kashe masa zuciya tace “kaki zuwa gida kaga Baba, this is 5yrs kenan muna dating but kaki maganan aure, we hardly have our time, we hardly shares any moment, I’m just very sad” sai kawai tasaki hannunsa ta sauka daga table din zata wuce, calmly Aliyu yamika hannunsa yakama fingers nata yarike yace “I’m sorry if my actions cause you pain directly or indirectly” juyowa tayi da sauri unexpectedly kawai tai hugging nasa daga zaunen dayake kan kujera yayi shiru he couldn’t wrap hands nasa around her, he knows suna rikema juna hannu basu taba wuce haka ba, cikin wani irin murya mai raunin gaske tace “I love you so much Haidar, I just miss us, we were never like this before, I feel kaman we are gradually drifting apart, I’m the one doing the callings, the texting, komima I’m the one doing, you hardly call, I can’t remember the last time naga kiranka ko sakon ka, we promise each other ourselves, tun kafin muyi aure mun soma falling apart, I’m hurting Aliyu” tai shiruuu but he felt hawayenta akan kirjinsa, sai kawai tafashe da kuka sosai jin jikinsa yayi sanyi tace “please karka yaudareni, for 6yrs ban kula kowa ba i keep chasing duk masu sona away, but for once baka taba zuwa gidan mu ba, Aliyu i will die idan baka aureni ba, please marry me soon, let’s get married please please” sosai take kukan da abin yasa kansa yadauki chargy kawai, baison kuka baiso anamai kuma cus tabamai zuciya yake, hannunsa yadaga ahankali kaman wanda baiso yayi yakai bayanta yasakeyin jimmm kafin anatse yayi patting bayanta like a little baby yace “shiiiii” abun ba karamin mata dadi yayi ba ganin yanda tasa he’s feeling guilty and bad, murya chan kasa yace “I’m sorry about everything Bee” wani sanyi zuciyanta yamata cus this is the pet name he calls her with Bee, cikin sheshekan kuka tace “to kagayamin yaushe zamuyi aure? Yaushe zakazo kaga Abba na?” Dan huci yasauke cus his head is really getting hot baison kukan mace, da sauri yatashi daga kujeran ita ya zaunar da ita, tissue yajawo daga tissue box dake kan table nasa yakai fuskanta yana sharewa but still kara bulbulowa hawayen suke, ya tsaya kawai yama rasa mezaice ahankali yace “I have alot going on right now why are you adding your own akaina what do you want? Nabaki life dina gabaki daya kihuta Bee?” Girgixamai kai tayi ahankali yace “then stop troubling me” yayi maganan yana kallonta idanunsa sunyi ja, suka danyi shiru kafin ya sassauta murya yace “I know you’re hurting but bazan iya miki karya just to please you ba, I can’t get married yanzu Bee!” Sosai kirjinta ke bugawa yanzu duk kukan nan abanza tayishi, Aliyu wani irin zuciyan karfe garesa, ahankali yace “I can’t! Kona aureki I will not have your time, you know everything about me, my mother is seriously sick and I’m her only son, my Mom is an orphan, batada siblings, nor aunties dazasu lura da ita, it’s all me Bee, yaya zanyi dake na aureki? Everyday I sleep a dakin Mami sabida condition nata, sometimes if her condition worsen I bath my Mom I do every single thing for her, do you think zan sami time naki mukai aure? Hakkinki kawai zanta shiga and banson hakan yafaru” cikin wata yar murya tana kallonsa da jajayen idanunta tace “to yanzu yaushe zamuyi aure”? “I don’t know!” Yabata amsa kai tsaye shima yana kallonta, zuciyan Beeba yahau tafarfasa kaman tace Allah ya kashe Mamin gobe ma kowa ya huta amman tasan tana fadin haka that’s the end of relationship nasu, strictly yace “this is not the place for this conversation, we both have patients to attend to, stand up and leave” yanda kirjinta yake mata zafi kaman ta zagesa takeji tamike daga kujeran tace “you’re so heartless Aliyu, you’re so mean and wicked, you have no idea wat love is and I hate myself for loving a strict rigid man like you, I hate you Haidar” tajuya tawuce tayi kofa fuuuu yabita da kallo saida takai wajen kofa ta tsaya tareda kai hannayenta ta gyara fuskanta tsaf sannan tabude kofa tafice, dan ijiyan zuciya ya sauke yay shiruuu na kusan 1min saiya mike tsaye ahankali yawuce bathroom na office din ya tsaya, sai kawai ya wanke fuskansa yafito yabude kofa yace afara turomai patient kafin time na surgery nasa yayi yawuce theatre. 💫KAUNA DA SO💫 ✍🏻M SHAKUR EPISODE 1️⃣4️⃣ https://www.youtube.com/@mshakur SUBSCRIBE TO MY YOUTUBE CHANNEL 💃💃💃 Around 3:30 yagama komi dazaiyi a clinic din, yashiga bathroom nasa yadauro alwala yafito yazare lab-coat na jikinsa yarike a hannu yadauki wayansa da car key da sun shade nasa ya makala yawuce yafita daga office din, ko kadan bai nemi Beeba ba yawuce abinsa yafita yawuce wajen motarsa yabude ya ijiye lab coat nasa a bayan mota yarufe motan yawuce mosque na masallacin su danyi sallan asir. Sai wajajen 4:15 yafito daga masallacin tundaga nesa ya hango Beeba tsaye jikin motansa sanye da abaya mai kyau black, sassanyar ijiyan zuciya yasauke yakaraso wajen sai kallonsa take, baice mata komi yazagaya ta bangaren driver ya shiga itama tabude dayan side din ta shiga tarufo motan, kunna motan yayi yaja yayi reverse yafita daga hospital din, saida yashiga titi sannan tace “my car is faulty yaki tashi, drop me home” still baice komiba gudu kawai yake a motan abin kara kulal da ita yayi sai kawai takai hannayenta kan fuskanta ta rushe da kuka tace “it’s all my fault da ban baka budurcina ba da yanzu na auri wani” wani irin daci zuciyan Aliyu yayi babu abinda ya tsana kaman irin rannan da abu ya shiga tsakanin sa da Habiba suna school shi yana PHd lokacin ita kuma tanayin masters, he was battling da ciwon Mami, he was depress, then she came to him agidansa…. He doesn’t even know what happened and how it happened kawai yadawo hayyacinsa yaga yasadu da Habiba, baitaba iskanci in his life ba sai that only one time. Yanayinsa datagani yasa taji ranta yayi wani irin fari, takai bayan hannu ta goge fuskanta tace “bayan ka yaudareni yanzu saimin wasa da hankali kake kaki aurena shekaruna na tafiya” haryakai anguwansu bai cemata anything ba yayi parking a kofar gidansu, tasan sarai the only thing dazaisa yayi magana shine idan tazauna taki fita daga motan dan yana sauri yaje yaga mahaifiyarsa, kusan 10min taki sauka tana nan zaune hakan yasa yace “get out” wani kallo tamai tace “bazan fita ba saika gayamin yaushe zamuyi aure” lumshe idanu yayi yabude yamata wani kallo da saida kayan cikinta suka kada amman ta daure ai ba tsoronsa takeba yace “idan bazan aureki ba i will tell you, ba tsoronki nake ba cus bakikai naji tsoronki ba, you can’t force me to marry you! Cus aure is my decision, there’s nothing you don’t know about me so i will say this one last time” yayi shiru sannan yajuyo yakalleta da kyau kaman yanda take kallonsa gabanta na faduwa sosai yace “you knew well wat i hate the most is tado da maganan mistake we committed years ago wanda har yau nadaman hakan nake cus that’s not me, if you think blackmailing with that can make me marry you Bee you’re very very wrong, I want to marry you cus i know is the right thing to do not because of wat happened between us in the past, and I’m not getting married now cus i have a very very sick mother at home that needs me more than anything aduniyan nan! Now get out i need to head home” Habiba zatai magana yawani daga mata hannu da batasan sanda tai shiru gabanta yayi mummunan faduwa ba cus tadauka marinta zaiyi, kwayan idanunsa data gani yasa tabude motan kawai tafice yatada motan yaja yabar wajen. ** Dakinta Obinna ya shigo yace “Daddy said get ready he’s dropping you in school” wanka tayi tafito ta shirya cikin shirt mai long hand pink yanada stripes farare tasaka wani white singlet mai aciki tasaka wani simple necklace mai kyau daya sauko, saitasa wani Mom jean black bai kamata ba free jean ne tasaka tadaura kan white singlet din tasaka wani belt na LV white, sannan yazauna bakin gadon tasaka sneakers white na Prada mai bala’in kyau, saita dauki black jearsy veil dinta asaman kanta da dayake a gyare an mata parking tanada black hair mai bala’in kyau, sannan tadauki bagpack da books nata ke ciki black ta rataya ta tsaya gaban madubi tashafa lipgloss tadauki turare tafesa tayi wani irin kyau sai kamshi take tafito Daddy baya falo Mommy dake falo tace “he’s waiting for you a mota fine girl saura ki kara bin yaran nan” turoma Mommy baki tayi tawuce tafice abinta zuwa compound tawuce motan Daddy tabude baya ta shiga ashagwabe tace “phoneeeeee Daddy please” hararanta Daddy yayi yace “let’s go” driver yaja motan. hugging Daddy tayi tai lamo ajikinsa tana turo baki duktai kaman marainiya Dady shima yayi kaman basu ganeba har saida sukakai school har zuwa department nasu driver yayi parking, Daddy yace “tashi ajikina my friend kiwuce school” tasowa tayi tana wani kallon Daddy kaman yar yarinya, Daddy yace “sainaga kin chanza kin rabu da yaran nan then i will give you your phone back” turomai baki tayi zatai magana yace “sauka kitafi I don’t want to hear anything” sauka tayi saikuma tahau murmushi tace “Daddy bye bye I love you my Daddy” washe baki yayi yace “I love you too but change before mu shirya” murmushi tamai tajuya tawuce class nasu ta shiga chan karshen class din ta zauna sai bata rai take ana haka lecturer yashigo class dayake 100 level ne mathematics ake musu, to be honest babu abinda bata ganewa amman ita kawai batason school dinne, saitamayi kwanciyanta ta daura kanta akan desk tai shiru, Mami ne tafado mata arai batasan mesa ba sake tashi zaune tai saita kalli wata yarinya dake gefenta tace “Hi kinada bolt a wayanki?” Kallonta yarinyar tayi, Ziora looks so fine and very cute, dressing nata yamata kyau, gyadamata kai tayi, Ziora tace “dan aramin” bata wayan yarinyar tayi Ziora ta karba tasa address na gidan Mami tai shiru tana tunani sai kawai ta kira bolt din, cikin 3 minutes aka rubuta driver yayi arriving location plate number ta kalla harta haddace tama yarinyar murmushi tace “thank youuu” tabata wayan sannan tamike tana sukutan jakan tafice abinta tana fita taga bolt din tawuce ta shiga yaja mota, gabanta sai faduwa yake toh yanzu tace meya kawota gidan mutane? Mezatace? Bayan yaron ta yamata wulakanci jiya, mema zataje tayi? Kaman tace yajuya ya maidata saita kasa kuma, data koma Shegiyar school din gwara taje wajen Mami abinta, ahaka har sukakai unguwan yayi parking gaban gidan taciro kudinsa 5k tabasa tafito saikuma ta tsaya tana kallon gidan tarasa yanda zatayi, kunya taji tanaji itada ba ruwanta da kunya, wasa wasa takai kusan 5min ahaka tarasa yanda zatayi kawai taji an bude gate an fito batama tsaya ta kalli waye yafito ba ta juya da sauri tafara tafiya, tayi tafiya one two taji ance. “Hey Amrah!” Har cikin ranta taji sunan hakan yasa gabanta ya fadi dum! Ta tsaya chak kaman an dasa kafanta a wajen sai kuma tajuyo ahankali, hada ido tayi da mutumin daya kirata yar shaye shaye jiya yana sanye da kayan gym short da riga mai kaman shimi ga headphone kansa daya sauke a wuya yana kallonta yana zuba kamshi sosai yayi bala’in kyau, da sauri ta dauke kai tahade fuska sosai, tsayawa Imam yayi yana kallonta daga sama har kasa tamai wani irin kyau sosai da shi kansa baisan mesa yaga tamai kyau dinba da kyar yahana kansa kallonta hakanan gabansa sai faduwa yake, ahankali yace “are you here to see Mami?” Akufule Ziora dan haushinsa takeji tace “no” shiru yayi sabida

Chapter 7 of 26