rame, fada dakai is affecting my mental health baka tausayina eh?” Aliyu yayi shiru yana kallonta she looks so lean kam, hannunta ta mika ahankali ta kama hannunsa dake saman table cikin murya dayayi sounding kaman zatai kuka tace “My Doctor please kaji tausayina kaya kuri kayafemin” shiru Aliyu yayi yana tunani ga Abba yace yabasa one month yayi aure with everything going on let him just start getting ready to marry Beeba after all shiya bata mata rayuwa it’s only right shiya aureta, ijiyan zuciya yasauke yace “okay yawuce!” Wani kalan tasowa tayi da sauri ta zagayo ta inda yake tace “da gaske kake kahakura mun shirya?” Gyadamata kai yayi yace “yes” wani irin hugging nasa tayi daga zaune faduwa gabansa yayi not because of her but sabida Amrah data fadomai arai ya runtse idanunsa da sauri but he’s still seeing Ziora sakinsa tayi tana murmushi ahankali yace “one of this days zanzo na gaida parents naki” sandarewa Beeba tayi is she dreaming dasauri tace “Al…..i….yu…..” awani irin hankali yace “let’s get married Bee” kawai kankarewa eeba tayi kirjinta na bugawa sai kallon Aliyu irin is she dreaming, sai kawai tadaura hannu kan fuskanta tafashe da kuka sosai tace “Aliyu I can’t believe this thank you Aliyu, I love you so much Dr” murmushi yayi yace “Mee too” yace “let’s go” gyadamai kai tayi takai hannu ta share fuskanta tass ya tsaya yana kallonta wondering maisa zuciyansa keta kawomai wanchan yarinyar ne kauda tunani ta yayi suka fito tare sai kallonsa take, yace “banaji someone is giving birth ba ba patient naki bane?” Murmushi tayi sosai tace “she’s idan akwai complications za’a kirani midwife na kanta” gyadamata kai yayi yace “okay see you later” dasauri tace “i love you Dr” gyadamata kai yayi tawuce rabon dataji farin ciki haka tun rannan daya shamata nonuwa da baya hayyacinsa dinnan.
Yana cikin tafiya zai shiga ward wayansa dake ringing yaciro da lab coat Imam ne yasan Mami ne ke drama saiya matsa gefe yadauki wayan Imam yace “kaga Mami wai dole saina kawota asibitin kabari muzo mana Yaya saina tafi da ita bazamu dade ba” dan jimmmm yayi saiyace “okay” Imam ya katse wayan while Aliyu yashiga ward abinsa.
Dakin daga Daddy sai Ziora cus Chidi yafita waje, Obinna yaje gida Ziora ta ishe sa dawani kalan rigima daya rasa gane mata, Daddy yace “wai are you trying to take my life Princess? Bazaki barni na huta ba, this kuka bakisan zai iya jawo miki wani ciwon ba” cikin kuka tace “Daddy call Yaya Aliyu for me I love himmmm” wani kallo Daddy yamata yahada giran sama dana kasa yace “did you even know what love is?” Gyadamai kai tayi ahankali tace “yes Daddy I know love, I want to marry him!” Dasauri Daddy ya kalleta, Ziora tace “I want to be his wife the way Mommy is your wife” tasake maganan tana goge hawaye idanunta harsun kumbura tsabagen kuka tace “Daddy he’s a very good person he loves his Mommy so much, he takes care of her, cooks for her, bath her, he does everything for her, me too he will take care of me, Daddy I want to marry him today!” Maganan Ziora ma akwai hauka aciki wlh, ahankali Daddy cikeda lallashi yace “okay naji toh dena kuka” cikin kuka tace “saikace you will get him married to me” ahankali Daddy yace “marriage doesn’t work like that Baby, for marriage to happen the man have to love you, Aliyu na sonki?” Tsare daddy tayi da idanu gabanta na faduwa saita girgixamai kai tace “no but me i love him Daddy, and i want to hug him and be staying with him all the time forever” dasauri Daddy cikeda hikima yace “toh kiji sauki saimu cigaba da maganan kinga yanzu kina hospital” dasauri tace “yes Daddy from here I will follow him and go with him, I don’t want to stay in your house again, I want to go with my husband” kansa Daddy ya dafe yace “okay bari ayi discharging naki gobe toh yanzu mubar maganan let’s keep it between us promise konaki aura masa ke” Gyadamai kai tayi dasauri daidai ana bude kofan dakin ta kallo kofan dasauri, Ya Chidi ne da yar muryanta mara kwari tace “Ya Chidi where is Yaya Aliyu”? wani mugun kallo yamata yayi banza da ita dasauri takalli Daddy tasake rushewa da kuka tace “Daddy call him for me” cikeda fada Chidi yace “wai ke are yoh okay? Kodai ciwon yataba miki brain ne?” Turo baki tayi tace “I want to marry Ya Aliyu and I’ve told Daddy ko” cikin fushi Chidi yace “Daddy kaga let’s not make this guy uncomfortable please with attitude na yarinyar nan, sabida mahaifiyarsa likes her doesn’t mean we should welcome her nonsense, sabida taga ana mata fara’a ke bakida full stop? By fire by force tashiga rayuwan his poor sick mother now look at wat she’s saying again did you even know wat love is? Yaushe aka haifeki does that guy looks like yanama miki kallo as woman enough dakika isa aure? Do you even know what love is Amrah”? Dasauri tana sheshekan kuka tace “yesss I know love because now I love Yaya Aliyu more you, morethan Daddy and even Mommy and everything, he’s the number one person that I love all of you follow back, I love him and me I am going with he’s my husband” Chidi zaiyi magana da idanu Daddy yamai alamu daya kyaleta Chidi kawai yayi shiru takaici na kamasa gabaki daya Ziora batada hankali.
TOH FAH!!
KUNA GANIN ALIYU ZAI AURI ZIORA?
MOMMY ZATA YARDA YARTA TA AURI MUSULMI?
JAMA’A MOSES FA???
IMAM FA??
HURRY AND JOIN TELEGRAM GROUP WITH JUST 1k💃💃💃💃
PAY INTO
6353995766 M SHAKUR WORLD MONIEPOINT
OR
7032934950 AISHAT MUHAMMAD OPAY
OR
0895672695 AISHAT MUHAMMAD GT BANK
YOU CAN WATSAPP ME WITH EVIDENCE OF PAYMENT VIA +2347012181461
THANK YOU FOR SUPPORTING ME❤️
EPISODE 4️⃣0️⃣
Zama bakin gadon Daddy yayi yakai hannunsa ya goge mata fuska yace “I’ve heard everything you said inhar you cooperate kinyi abinda nace zan miki auren, don’t tell anyone, this matter should be between us” hawaye na sake zubowa tace “Pinky promise Daddy?” Dasauri yace “very Pinkish sef” gyadamai kai tayi saitai hugging nasa tana kallon kofa gabanta sai bugawa yake she just wanna see Aliyu wallahi.
La’asar Aliyu yayi a mosque yafito daidai Imam na parking motarsa yabude yafito yana sanye da shadda ash color mai kyau, yakafa hula kaman ango, yabude ma Mami kofa tasauko tana sanye da hijabi mai ruwan kasa har kasa looking very decent and fine yamaida kofan yarufe yazagayo yaciro basket na abinci dawani cup na Stanley da Mami tahada mata ice tea nata, Aliyu na karasowa wajen yakalli Mami datamai mugun kallo tace “idan na duba Amrah zamuyi magana mahaifinka ya kirani” gyadamata kai yayi, Imam daya kosa yaga Ziora yace “muje Yaya” gaba Aliyu yayi suna biye dashi har wajen dakin batare daya shiga ba yace “I have a patient bari naje” Mami ta gyadamai kai tanasa hannu tabude dakin da sallama Daddy ne kadai adakin zaune kan gadon Ziora na kwance tayi pillow da kafan Daddy tadaura kanta akan kafafunsa idanun nan luhu luhu, Daddy na ganin Mami yace “come inside Madam come inside please” jin maganan Daddy yasa Ziora tabude idanunta dasauri tana ganin Mami tawani zabura ta tashi daga jikin Daddy kaman yar yarinya dataga Mamanta tawani bude hannu irin Mami tazo tai hugging nata Daddy kawai ya tsare diyarsa da kallo yana tashi daga gadon sabida Mami tazama comfortable, Mami itama cikeda kaunarta tazo tace “Amreery na Patient oyoyooo” hugging Mami tayi sosai tafashe da kuka tace “Mami everything is paining me, my bombom is sore Mami” kunya Imam yaji, Mami tace “it’s okay za’a sallameki sai agasa jikin da hot water now stop crying” tasaketa tace “tsaya na gaisa da Babanki” takalli Daddy cikin harshen hausa tace “ina yini mai gida ya mai jikin Amrah”Daddy daya gane abinda tace sosai yace “lafuya lafuya Hajiya” Anatse Imam ya duka yana sunnar dakai yace “good evening Sir” “stand up stand up he’s your son too?” Ya tambayi Mami data gyadamai kai alamun eh, Mami tace “ga tea namiki” tabude Stanley cup din tabata dasauri ta karba tafara sha Daddy sai kallonsu yake, Mami tace “nasamiki waina zakici?” Gyadamata kai tayi, Mami tabude flask din Daddy na kallon wainan that looks so rich tasama Ziora ta karba tanaci tadan kalli Imam dake kallonta tace “ga Maheer baku gansa ba” kallonsa Ziora tayi ahankali tace “ina wuni” murmushi yayi yace “Mami Besty ya jikin”? Gyadamai kai tayi batai magana ba danyau takanta take, Mami ta wanko hannunta ta karba da kanta tadinga bata wainan abaki tanaci sosai duk suna ahaka, Obinna yadawo tareda Chidi ma suka shigo duk gaida Mami sukayi suna mata godiya ta amsa suka gaisa da Imam daya kasa daina kallon Ziora da Mami ke feeding like a baby.
Suna ahaka Chidi da wayansa yayi ringing yafice bai wani jimaba sai gasa yashigo dakin Mommy datai zuru zuru hankalinta atashe biyeda shi tashigo dakin kowa juyowa yayi ya kalleta especially Daddy daya mata kallo daya yadauke kai, Mami dakeba Ziora abinci ganin Ziora ta tsaya tana kallon waje guda yasa Mami tajuyo, Maman Ziora tagani taganeta sabida saloon that first time, tana sanye da wani half gown ga wig akanta mai kyau, anatse Mami ta ijiye plate din tamike tasauka daga gadon tace “toh bari mutafi, make sure you take your drugs okay” hannunta Ziora tarike tana dauke kanta daga kallon Mommy tace “Mami don’t goo” Mami tai murmushi tace “zan dawo soon” ta karbe hannunta tawuce ta wanke hannunta tanama Daddy murmushi tace “sai anjiman ku, Muhammad, Khaleel sai anjiman ku, Allah kara sauki” atare dukansu sukama Mami godiya banda Mommy dake kallon Mami sosai, Mami tace “barka da zuwa Maman Amrah” sannan tabi gefenta tafice Imam biye da ita.
Mommy takalli dukansu yan dakin tace “and who is this woman”? Cikin zafin murya Daddy yace “the woman that has been taking care of your daughter for you” Ziora ta kwanta akan gado tana turo baki itama cus she’s angry with Mom” tace “I am going to marry her Son Dr Aliyu and live with them forever” karasowa gaban gadon Mommy tayi tace “what did you say?” Dasauri Daddy yace “this girl is sick banson trouble”zama Mommy tayi bakin gadon batamasan mezatayi ba gabanta sai faduwa yake tana kallon Ziora data nuna ko oho da ganin ta danta Aliyu take yanzu.
Aliyu Imam yakira kan sun gama zasu tafi, yace “su jirasa” wayansa yadaga yakira Beeba ringing daya tadauka dasauri cikin yar karaman muryan nan yace “where are you? Come and greet Mami zata wuce gida” haderai tayi amman tasaki murya tace “okay okay gani nan tana office dinka ne”? Ahankali yace “no parking space” dasauri tace “tom gani nan zuwa” ficewa yayi a parking space yasamesu saiga Beeba itama tana wani murmushi Mami tajuyo tsareta da kallo tahowa tayi ta tsaya dab da Aliyu taduka tace “Mami sannu da zuwa ina yini dubiya kukazo ne”? Ahankali Mami tace “diyata Amrah ba lpy shine nazo gaidata” Beeba tace “Allah kara sauki, Yaya Imammu ina yini” murmushi yamata yace “Dr ya patient” tace “Alhamdulillah” tana murmushi, Mami takalli Aliyu tace “yaushe zaka dawo gida?” Ahankali yace “nan bada jimawa ba Mami” gyadamai kai tayi tace “okay I will see you at home, sai anjiman ku” ta shiga mota Imam na rufewa Beeba na musu bye Imam yaja motan Aliyu yajuya suna komawa cikin asibitin tare Mami ta tsaresu da idanu.
Around 6:30 akai knocking, dakin is just Mommy da Daddy zaune a dakin da Ziora datake bacci mai nauyi dan tuntuni ta addabesu da rigima, Aliyu yabude kofan ya shiga tareda wani Dr Balarabe da nurses guda uku zai musu handing over cus yanzu zai tafi gida, Daddy yace “Dr Aliyu sannu da aiki” batare daya hada idanu da Daddy ba yace “good evening Sir” bai kallo Mommy data tsaresa da idanu ba yace “good evening Ma” hadarai Mommy tayi taki kulasa Daddy yace “yanzun nan tai bacci ko atadata ne”? Aliyu yace “no, no need, I just wanna handover everything to night Dr here, Dr Balarabe” Daddy yace “okay” while Mommy na kallon yanda Aliyu ke magana da Dr and nurses din using English da Medical terms, tundaga kan takalmin kafansa Mommy ke kallo gaskiya ba karya Dr yahadu ga kyau gashi baya turenci like all those local hausa people cus tanama all Hausawa kallon marasa ikili da basu iya turenci ba, gamawa tsaf yayi sannan yakalli Daddy yace “good night Sir” Daddy yayi murmushi yace “good night Aliyu, thank you so so much May God bless you” gyadamai kai Aliyu yayi yajuya yafita Daddy yabisu da kallo same with Mommy data kallesa tace “wlh wlh I’m warning you cus naga the way you’re looking at the Dr, even in your wildest dream ka aurama yarinyar nan bahaushe saina maka tashin hankali, this girl that doesn’t have sense can not choose husband for kanta especially hausa men that marries plenty wives and suke divorce like it’s nothing I’m telling you ooo now Nwunye, hausa men don’t respect women, and my daughter can never be a victim” kadakai Daddy kawai yayi yamata shiru sai kawai yace “lemme go it’s time for Magrib” yafice dakin yarage daura Mommy kadai da Ziora dake bacci hannu Mommy takai tana shafa gashin Ziora tana kallonta damuwa fal ranta tace “Moses is the best Man for you, he’s the best for you kinji”.
*
EPISODE 4️⃣1️⃣
Fitowa Aliyu yayi yashiga mota yana jiran Beeba daya gayama zai sauketa agida da kansa tafito tana murmushi sosai tashiga motan ya kunna yaja har gidansu yasauketa takama hannunsa tana murmushi tace “thank you you’ve made me so happy today” gyadamata kai yayi yace “gud night I need to head back home now” gyadamai kai tayi tace “agaida Mami” tafice yaja motan yatafi Sauda ya tsaya yayi ishai sannan yatafi gida.
Yana shiga a falo yaga Imam na hira da Mami yanashan pepper soup yace “yauwa Yaya kadawo bari natafi gida” gyadamai kai yayi yawuce sama yace “lemme shower” wanka yayi yasaka simple 3-quarter da tahirt yafito babu kowa a falon bazai kara fitaba hakan yasa yawuce yakulle kofa yatafi kitchen coffeee yahada tarike a hannu yafito yawuce dakin Mami yabude kofa yayi sallama Mami ta amsamai kasa kasa.
Tana zaune bakin gado da hijab da Al Qur’ani hannunta shiga yayi yamaida kofan yarufe shima yazauna bakin gadon yanashan tea yana sauraron kira’an Mami harta gama tarufe tajawo drawer ta tamaida Al Qur’anin tarufe takalli Aliyu dake kallonta yace “gani Mami” ajiyan zuciya ta sauke tace “mahaifinka yakirani yau munyi magana na kusan 1hr dazu duka agaban Imam, yace yabaka takardun wasu gida”? Gyadamata kai yayi, tace “mesa baka gayamin ba”? Ahankali yace “sabida konayi abinda yakeso anan gidan zan zauna not that house, I will never leave you alone kizauna ke kadai” Mami tai shiru tana kallonsa, anatse tace “kanada wacce kakeso ne Aliyu?” Dan sunnar dakai Aliyu yayi shi baisan mesa ba the way Imamu ke zama yama Mami hiran banza yana bata labarin this budurwa da that budurwa dayayi shi baitaba ba, Allah yadaura mai wani irin kunya da jin nauyin mahaifiyarsa when it comes to that angle, ganin yayi shiru yasa Mami tace “answer me, yace yabaka one month koshi zai duba dangi yasamo maka wata” Mami tadanyi shiru kafin a nutse tana kallonsa tace “akwai wacce kake gani ne yanzu haka dakakeso ka aura?” Yakai kusan minti daya bai magana ba sai chan murya chan kasa yace “yes Mami” ahankali Mami tace “wacece Aliyu?” Kaman maganan namai nauyi yace “Habiba” yayi shiru yakasa dago kansa kafin ahankali yace “Dr Beeba Mami” Mami tadade tana kallonsa kafin calmly tace “kanason Dr Beeba ne Aliyu?” Maisa Mami tamai tambayan nan? Shiru yayi kaman abu yarikemai baki Mami tace “look at me Aliyu” ahankali yadago kansa yakalli Mami, Mami tace “kafadamin gaskiya, kanason Beeba?” Sauke kansa kasa yayi yay shiru chan kaman dan karamin yaro yace “we’ve been together tun Harvard more than 5yrs ago” yayi shiru ko ansa wuka awuyansa bazai taba iya gayama Mami yataba ketama Beeba haddi ba, Mami knows danta tambaya daya tamai har yanzu bai iya yabata amsa da yes ko no ba, cikin muryan dazai nuna da gaske take tace “Aliyu” dago kansa Aliyu yayi yakalli Mami, Mami na kallonsa itama right in the eye tace “bana sonka da Dr Beeba ko kadan!”Dasauri Aliyu ya kalli Mami cus Mamin sa is one kind of mutum da babu wanda bataso tanada wani irin kyakkywan zuciya dake kaunar kowa so is soo unlike Mami tace batason mutum, anatse tace “kwata kwata jinina bai aminta da Beeba ba tun rannan dana fara ganinta agidan nan, ni karan kaina bansan dalilin dayasa ban natsu da ita ba, kawai ban hangota as mace tagari dazaka samu natsuwa, kwanciyan hankali and support dagata wajenta ba, nasan aure hadi ne na Allah, na kalli Beeba duka duka kanku kusan daya da shekara nawa ka girmeta Aliyu zaka iya tankwarata, zaka iya bi da ita? Zaka iya cemata yi ta yi bari na bari?” Mami tadan sauke ijiyan zuciya tace “All of those things aside Aliyu I’m a sick woman da batada kowa, I’m an orphan I want you to marry a wife da will see me as her mother nima zan ganta as my daughter, koda yaushe muna tare sabida hankalinka kaima ya kwanta kayi aiki da kyau knowing ka barni tareda wata, ba wannan dakake zuwa aiki goman safiya kadawo 4 na yamma ba no Aliyu, naga Beeba na zauna da ita na rannan I don’t hate her but bana sonta a matsayin matarka kwata kwata” Aliyu yayi shiru yana kallon Mami, ahankali Mami tace “I want someone else to become your wife” gabansa kawai faduwa yake bana wasaba, ahankali Mami tace “Aliyu ina kaunar Amrah!” Dasauri Aliyu yakalli Mami gabansa na bugawa, what is Mami saying all of a sudden? Cikin wata sassanyar murya mai rauni cus maganganun daga zuciyanta suke Mami tace “Inason Amrah Aliyu! Yarinyar na matukar kaunata itama! Rabon dana sami soyayyan yaro a rayuwana tun wacce na samu daga gareka kana yaro sai yanzu da Amrah nahadu da ita tazo take sona, I’ve never ever seen a girl of her age that’s so precious, kind, innocent and sweet ba, banda haka inaso dani dakai mu taka rawan gani a rayuwan yarinyar, she lacks so many things in terms of musulunci, duba daga kalan gidan gidan data fito, plus abinda tafada mani rannan kan mahaifiyarta na son ta auri dandan Pastor Aliyu” Mami tai shiru ta lumshe idanu tabude su cikin husky voice tace “Aliyu” bugawa kirjin Aliyu yashigayi, ahankali yace “na’am Mami” anutse tace “nasan kariga kasan request din danake shirin yi but I will still say it” tadan dakata kafin ahankali tace “inaso ka auri Amrah Aliyu!” Dawani irin sauri Aliyu yatashi daga zaunen dayake yana kallon Mami yadan hade fuska, Mami tadago kanta ga kallesa tace “kayi jahadi akanta let’s make her a better muslima, she’s a good obidient girl da bata dauki duniya as anything ba, tanada free zuciya, zaka iya tankwarata duk yanda kazo, ka tafiyar da ita duk yanda kaso, seeing the two of you together will make me very very happy, I choose Amrah for you ita nakeso amman banace dole saikayi bane kona tursasa maka ba wlh wlh duk wacce kace zaka aura zan karbe ta da zuciya daya, kaizaka zauna da matarka not me Aliyu, I know one day zakaso Amrah sama da yanda kake tunani, kuma shi a aure babu yaro, so karka mata kallon she’s too small for you, koka mata kallon ita kabilace ko wani abu don’t think of anything just make up your mind zaka aureta and watch God pave way for u, da musulmi da christa, da bayarabe da bahaushe da inyamuri, bafulatani duk Allah ya halitto mu, being bahaushe doesn’t mean kai Allah yafiso, being bahaushe baya nufin kaine musulmin kwarai inyamuri musulum musulum ne, dukanmu dayane awajen Allah sai wanda yafimu tsoron Allah, Amrah nada christan uwa that’s not her fault or something daya kamata mu kyamaceta akai, kasan ko watarana d same way mahaifijta ya musulunta itama mahaifiyar ta mutdulanta? Allah Al Gafuraru Raheem so I want Amarh for you and I choose her for you idan har you’re ready ka sanar da mahaifinka ka nemi aurenta, but ni ban yarda ka aure Habiba ba at all” tunda Mami ke maganan kansa ke kasa gabansa bugawa kawai yake baimasan takamaiman meyakeji ba, but yasan babu abinda bazaima Mami ba, he loves yanda samin yarinyar keeps making her happy and he loves yanda yarinyar makes her happy, babu abinda bazai iyama Maminsa ba, but this request! Daman a tsaye yake kawai yajuya cus bazai iya kallon idanun Mami yacemata no ba yayi wajen kofa dasauri yakai hannu zai daura kan kofan cikin irin muryan nan da iyaye ke using su kama yaransu tace “Aliyu I have less than 2months fa idan kana calculation!” Chak Aliyu ya tsaya yakasa bude kofan yafita, Mami tayi murmushi tace “I am just a dying mother making one last final request dazaiyi making dina nai farin ciki” Tasake murmushi saitakai hannu ta yaye hijabin jikinta tacire ta ijiye a gefenta takai hannayenta tazare hulan dake kanta ta ijiye shima a gefe takalli Aliyu dake facing kofa ahankali, gabaki daya kanta ba gashi sai wasu yan kwararru dazaka iya kirgawa suma farare dasu, muryanta yayi sanyi karara tace “juyo ka kalleni Aliyu” juyowa Aliyu yayi ahankali yakalli Mami hannu tadaura akan yan suman tazare suna fitowa kaman ana cire tsakuwa ba wahala tayi murmushi sosai tace “you see nothing is left again Aliyu I am dying nan da wata daya da yan kai” kaman maganan yatabata sai kawai tafashe dawani irin kuka dagudu Aliyu yazo sai kawai yaduka agabanta yasa guiwowinsa akasa yace “Mami dan girman Allah stop crying” cikin wani irin kuka tace “Aliyu na azabtu da ciwon nan tun kana dan shekara sha takwas, nine barin jini, zafin al’ada, ciwo zazzabi, mahaifinka yarabu dani, banda kowa banda kai aduniya, Aliyu kanada kannai Samha da Farha basa sona, finally Allah yahadani da yarinya danakeso, yarinya dake mugun son mahaifiyarka, bata kyamaceni ba, batamin kallon mara lafiya ba, with all this” tanuna saikon kanta tace “Amrah will still hug and kiss me, all I want is to see you marry this girl dake kaunar mahaifiyarka na ganku tare amatsayin mata da miji kona rana dayane kafin na mutu Aliyu bazaka iyamin ba? Banason Beeba, bana kaunarta ni Amrah nakeso dakai, amman bakason wacce nakeso” kai Aliyu yaga tashin hankali ganin yanda Mami ke kuka ba kakkautawa, cikin tashin hankali yace “Mami na yarda stop crying please, I will marry her” dasauri Mami dake kuka ta kallesa, hannunsa yakai ya share mata fuska asanyaye yace “idan zan miki abinda kikeso zaki yarda kimin abinda nakeso nima Mami?” Ahankali Mami na jan majina tace “me kakeso Aliyu na”? Anatse yace “my biggest fear is loosing you, akwai wani trail danakeso kiyi daga wajen Yayan Amrah Chidi abun yazo, I know kince bakison wani trail again, kin riga kin fawwalama Allah komi, but inhar kin yarda and try this trail I will marry Amrah Mami Wallahil Azim!” Mami tadade tana kallonsa sai kawai yaga tamai murmushi tace “thank you Aliyu naji zanyi trail din Allah yasa inada rabo, tunda nahadu da Amrah nakeson Allah ya aramin tsawon rai koda jikana guda ne nagani, Allah yasa musami sa’a this time” ahankali yace “Ameen Mami” hannu Mami tabudemai tace “I am very happy come here” akunyace ya sunnar dakai tace “da Amrah ce da tuni ta rungumeni” murya ciki ciki yace “that girl batasan menene kunya ba” yabude kofa yafice Mami ta tabe baki tace “irinta nakeso kasamu a mata dan jakar butan uba, ja’iri kawai”.
EPISODE 4️⃣2️⃣
Wucewa Aliyu yayi yahaura sama, dakinsa yashiga yazauna gaban gadonsa yayi shiru yana tunani, yanzu yazaiyi da Beeba? He literally raped this girl unknowingly and unintentionally wallahi, the least she deserves from him is ya aureta tunda shi ya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 26